The paper is a historical review of Hausa studies in Nigerian
academia. In the struggle, relevant related literatures were critically examined
to justify the dare need of an updated progress report. In this study, an advanced
Hausa study is the desired target to conjugate Hausa on the rating scale of
Nigerian academic standard. Similarly, tertiary institutions, Universities and
research centers handling Hausa academic Activities are the umbilical cord of
the paper. To be more precise, the paper concentrates on the Nigerian factor in
the subject under review. Gladly, it peeps through nineteen Nigerian Universities,
thirty eight other tertiary institutions and four research centers to update
the progress report of the journey so far. The review captures forty indigenous
Nigerian Professors of Hausa studies, and forty…
Title: Bitar Karatun
Hausa A Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙrn.
21): (Wurin Da Babu Ƙasa Ake Gardamar Kokuwa)
Translation: Hausa Studies in
Nigerian Academic Memorandum of the 21st Century
(The Arithmetic of the Struggle)
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
0803 431 6508
Jagorar Takardar
da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa na farko kan karatun Hausa a Ƙarni
na ashirin da ɗaya (Ƙrn. 21) a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero, Kano a ƙarƙashin Jagorancin Dr. Bukar Usaman, Dlitt, OON a
harabar Musa Abdullahi (Auditorium), BUK, Sabon mazauni, ranar Litinin 10 zuwa Talata
13 ga Nuwamba, 2014.
ABSTRACT
The paper is a historical review of Hausa studies in Nigerian
academia. In the struggle, relevant related literatures were critically eɗamined
to justify the dare need of an updated progress report. In this study, an advanced
Hausa study is the desired target to conjugate Hausa on the rating scale of
Nigerian academic standard. Similarly, tertiary institutions, Universities and
research centers handling Hausa academic Activities are the umbilical cord of
the paper. To be more precise, the paper concentrates on the Nigerian factor in
the subject under review. Gladly, it peeps through nineteen Nigerian Universities,
thirty eight other tertiary institutions and four research centers to update
the progress report of the journey so far. The review captures forty indigenous
Nigerian Professors of Hausa studies, and forty academic journals in the domain
of Hausa academic Activities. Furthermore, four hundred MA and eighty PhD
degrees of Hausa studies were awarded in Nigerian Universities as at 2013/2014
session’s records. Certainly, Hausa studies has reached the pyramid of academic
standard and hence qualified to demand total emancipation and freedom against
clutches of all the linguistic imperialism in Nigerian academic context. Thus,
the prayer is teaching Nigerian language in Nigerian language is the only
arithmetic to balance the eƙuation.
Gabatarwa
Ga al’adar ilmi, kowane fanni na
ilmukan da muke da su a duniya, da tarihinsa yake garkuwa domin daidaita akalar
cigabansa.[1]
Harshen Hausa, wani furen kallo ne da duniyar Afirka ke tinƙaho da shi idan
ana zancen nagartattun rayayyun harsuna na Afirka.[2] A
duniyar ilimi, taurarinsa na da dogon hasken gwada tsawo da bunƙasa a ilimin
harshe da fasahar adabi da walwalar al’ada. A tarihin karatun boko a Nijeriya,
Hausa ba ta taɓa maraici gidan
kowane harshe ba, hasali ma, da ita ake tuwassuli idan gari ya ci wuta.[3] Ƙudurin wannan
takarda a kan turaku uku zai shanya talalar waɗarinsa; na farko, za ta yi amfani
da yau ta yi wa jiya kallon ciniki, domin ba don jiya ba, da yau ba ta shiga
tarihi ba. Na biyu, wainar da ake toyawa
a yau a kan tandar mazan jiya, yaya guiɓin ƙullunta yake? Ya
yi tsararo ko ya yi kauri, domin a riƙa sara ana duban
bakin gatari? Na uku, tilas mu kula da cewa, yau lokaci ne, Hausawa ko cewa
suka yi lokacin abu a yi shi. A tunanin Bahaushe, lokaci riga ce, don haka yake
sunnata wa wanda ya samu lokaci ya yi tsayin daka ya shanya garinsa. Fashin baƙin tunanin
Bahaushe a nan shi ne, lokaci abokon tafiya ne. Haka takardar take son karatun
Hausa ya kasance wandon roba daidai da kwankwason kowane irin zamani. Don haka
na yi wa takardar take: Bitar Karatun Hausa a Ƙarni na Ashirin da
Ɗaya:
(Wurin da babu ƙasa ake gardamar kokuwa).
Bitar Ayyukan Da
Suka Gabata
Magabata da dama sun hangi irin
amfanin da ke cikin tafiya da waiwaya musamman a fagen karatu. Masanin farko da ya share fagen
wannan fahimtar shi ne Siergio Baldi[4].Aikin
Baldi wata fuska ɗaya ya kalla daga
fuskokin karatun Hausa. Haka kuma, yana da gajeren lokaci yayin gudanar da shi
wanda ya yi masa tarnaƙi ga a buɗe gaba ƙwarai. Bugu da ƙari, yau aikin
nasa ya yi tsufan shekara talatin da tara (39).[5]
Paul Newman, ya ba da muhimmiyar gudummmuwa wajen tattaro ayyukan da aka yi na
ilimin harshe.[6]
Littafinsa gawurtacce ne sosai a bagiren musamman idan aka kalli ƙwazon marubucin a
fagen. Ɗan cikas da na hanga ciki a kan nawa ƙuduri shi ne,
Newman kwasan karen mahaukaciya ya yi fagen[7].
Haka kuma, shekarun da aikin ya yi wata babbar tazara ce da ta bar babban giɓi.[8]
Furniss da ya ga rawar Newman a harshe sai ya taka irin tasa a adabi. Akin
Furniss kamar tsakure ne, domin takardu biyu ya gabatar, ɗaya mai ɗauke da tarihin
karatun adabi, ɗaya kuwa ayyukan
da aka yi a kan adabi.[9]
Dukkanin ayyukan shan ruwan tsuntsaye suka yi wa nazarce-nazacen adabin Hausa
da aka yi. Idan muka waiwayi shekarun ayyukan, za mu ga ana buƙatar a yi kakkkaɓan gara. Na
tabbata ganin haka ne ya faɗaɗa aikin zuwa littafi babba. Shi kansa littafin lokaci
ya ci zarafinsa.[10]
Madalla da shakundun ƙoƙarin Ibrahim Yaro Yahaya da za a
iya kira tauraron gabas mai haske. Yahaya ya buɗe gaba sosai ya ɗauko ta daga
tushe, kuma ya yi tsayin daka na ganin bai rago komai a baya ba.[11]
Ga shekaru aikin ya tsufa kimanin shekara ashirin da shida (26). Haliru Ahmad
Amfani ya ɗan leƙo kai ya harari
ayyukan digirin MA da MPhil da PhD da aka yi a
fannin harshe cikin gida da waje.[12]
Matsalar ita ce, aikin an gabatar da shi a matsayin takardar bincike aka kuma
wallafa takardar. Kasancewar aikin mai ido ɗaya, shi ya kawo masa kasala ya kasa gwada
tsawo ga aikin malamin malamansa Paul Newman. Aikin ya kusa kai shekara goma
sha biyar (15).
Malam Ɗalhatu Muhammad ya
yi irin wannan rawar amma a kan gidajen rediyon da ke aiwatar da shirye-shiryen
Hausa bisa hasashen shirin game duniya.[13]
Sabi’u Bukkuyum ya yi wa fagen susa gurbin ƙaiƙayi ya ƙayallaro
gudummuwar gidajen rediyo ga bunƙasa Hausa.[14]
Ya yi sharar fage sosai a kan gidajen rediyon duniyar ƙarninmu da Hausa
ke baje kolinta a shirye-shiryensu. Umaru Aliyu Bunza, mujallu da jaridun Hausa
ya tunkara gadan-gadan, tsofaffinsu da sababbinsu.[15]
Waɗannan ayyuka duka
aikin jarida suka fuskanta. Aikin jarida
kuwa, ruhinsa kamar fincen ɓera ne a tugufar da ake bandan naman toron giwa. Bugu
da ƙari,
duk waɗannan abubuwa sun
yi tsufan da wasu abubuwa muhhimmai sun wakana bayansu.[16]
Idan aka waiwayi ayyukan da suka
gabata, za a ga aikin Paul Newman da Furniss da Ibrahim Yaro Yahaya su ne
wallafafu littattafai. Aikin Newman cikin Turanci aka yi shi, kuma a US aka
wallfa shi, bai bazu a duniyar ƙasar Hausa ba.
Aikin Furniss cikin Turanci aka yi shi, kuma a UK aka wallafa shi, da baya ya
fara bazuwa ga hannun ɗaliban karatu.[17]
Aikin Ibahim Yaro Yahaya cikin Hausa aka yi shi, tsufansa yake sa ƙamfarsa a ɗakunan karatu.
Sauran ayyukan na su Ɗalhatu da Amfani da Bunza da Bukkuyum takardu ne wallafaffu
masu gajeren nazari da gajeren haske ga irin sabuwar tafiyar da karatun Hausa
yake kan ƙuduri a duniyar ƙarninmu. Idan na
ci nasarar fitar da suhe wuta, buƙata ta a fahimci
gara yaso da haka sabon ramin rijiya.
Mene
Ne Karatun Hausa?
Na sha dawara da kai da kawo kamar mai
neman gidan Alhaji a birnin Kano domin samun ƙamusun da zan ga
amsar wannan tambaya, abu ya ci tura. Duk da haka, ‘yan dara cewa suka yi, ko
bayan tiya akwai wata caca. Don haka, na fara hararar ma’anar Hausa ita kanta,
domin sai an san nauyin kaya ake jingar ɗaukar su. A ganin masana tana da fassarori
da yawa. Daga cikinsu akwai harshen da Hausawa ke sadarwa da shi.[18] A
wata fahimta, Hausa ita ce ƙasar da Hausawa suka tsira suka
mamaye ta da daulolinsu da al’adunsu.[19]
Wasu na hasashen cewa, Hausa suna ne da ake bai wa ƙasashen Hausawa da
ke ƙarƙashin mulkin
Fulani.[20] Wannan shi ya ba wasu damar hasashen cewa,
farfajiyar da daular Sakkwato ta mamaye ita ce Hausa.[21]
Tsirarrun harsuna da ƙabilun da Hausa ta mamaye su ke kiran ƙasar Hausa gabas.[22]
Su kansu Hausawa, suna yi wa harshensu suna “Hausa” bisa ga fasahar da ke
tattare a ciki.[23]
A tsaftace, Hausa ƙasa ce da ke da
dauloli da mutane da ke magana da
harshen Hausa suna tinƙaho da al’adun Hausawa. A fafitikar
laluben karatun Hausa za mu ce; karatun Hausa a duniyar karatun boko shi ne:
Ɗalibtar koyo da
koyarwa a kan fasahohin da ke ƙunshe cikin harshen Hausa ta fuskar
sarrafa shi a lafazance da ƙololuwar nahawunsa ta kowace fuska,
da fannonin adabinsa jiya da yau, da rassan al’adunsa na ƙarnukan da ya
ratso da wanda ake ciki. Kowane irin nazari ya tunkari fasahohin Bahaushe da
kimiyyar fasaha da tattalin arziki da siyasar zamantakewa da addini da kimiyyar
kiyon lafiya da ƙere-ƙere da tsaro da dabashirin yaƙi da ya shafi
Bahaushe, da ƙasarsa, da tunaninsa na rungumar duniyar zamaninsa.
Duk wani bincike mai kama da haka sunansa karatun Hausa.
Idan an fahimci hasashen fashin baƙin karatun Hausa,
za mu ce, karatun Hausa suna ya tara amma kowane bakin wuta a irin nasa hayaƙi. Masu taƙaita karatun Hausa
ga masu takardun shaidar karatun Hausa kawai, sun yi wa karatun Hausa sanin
damisar Bunu.[24]
Masu nazarin Bahaushe a wajen nahiyar karatun Hausa, Hausa suke yi wa aiki,
kushe karatun Hausa gare su rashin sani ne karen gwauro ya kori bazawara.[25] A
fahimta ta, ilmi duk aka sarrafa cikin wani harshen wata al’umma ko aka ari
wata fasaharta ko kimiyyarta aka haƙa tubalin ginin
wani ilmi, to ilmin na masu harshen ne, domin wanda ke kusa ga wuta ya fi kowa
sanin zafinta. Haƙiƙa, idan aka tsura wa wannan ra’in
idon natsuwa, za a gane kura da shan bugu gardi da karɓe kuɗi. Don me bayan an
ci moriyar ganga a ce mata koren banza?[26]
Magabata cewa suka yi, wurin da babu ƙasa nan ake
gardamar kokuwa. To! Sai in ce, bismillah an haɗa malamai faɗa.
Karatun
Hausa Da Assasa Ilmin Nijeriya Ta Arewa
Ilmi biyu suka agaza wa Nijeriya
ga haye tudun-mun-tsira na yi wa duhun jahilci barazana, ilmin addini da ilmin
boko. A ƙarƙashin addini, addinai biyu suka fi
amo da tasiri da bazuwa a kowane saƙo na ƙasar, addinin Musulunci
da na Kirista.[27]
Harshen Hausa ya karɓe wa harsunan waɗannan addinai
tuta.[28]
Ya yi ruwa, ya yi tsaki, wajen fashin baƙin saƙonninsu da yaɗa su, ba tare da
ba hamuta iska ba. A ɓangaren Musulunci,
karatun ibada da adabi da nahawu da Hausa ake gudanar da su.[29]Daga cikin harsunan Nijeriya harshen Hausa kaɗai ke bugun gaban:
i.
Tarjamar
ma’anonin Alkur’ani mai tsarki daga Larabci zuwa Hausa a rubuce daban-daban iri
kusan bakwai.[30]
iii.
Fassarar
littattafan furu’a na mazhabar Malikiyya da suka yi fice a duniyar ilmin addinin Musulunci.[32]
iv.
A
ɓangaren addinin
Kiristanci, Hausa kaɗai ke da fassarar
Linjila kashi biyu. Ga dukkanin alamu, cikin harsunan Nijeriya da Hausa aka
fara fassara Linjila (Bible).[33]
v.
Littaffan
addinin Kirista da ke cikin harshen Hausa sun fi na kowane harshen Nijeriya
yawa jiya da yau.[34]
Haƙiƙa wannan ce ta ba
harshenn Hausa da Hausawa damar fice a duniyar addinin Musuluci.[35] A
ɓangaren Turarawan
Mishan, littattafai na adabi da addini da suka wallafa cikin harshen Hausa, ba
su wallafa ko ɗaya bisa goman su
ba a cikin kowane harshe daga cikin harsunan Nijeriya.[36]
Waɗannan dalilai su
suka tabbatar da cewa, saukakkin addinai da suka bayyana a Nijeriya da Hausa
suka yi garkuwa wajen tabbatar da dugadugansu. Ke nan, ba don Hausa ba, da
turnuƙun hayaƙin jahiliyyar
addinan gargajiya ba su jaye a zukatan ‘yan Nijeriya ba. Tun gabanin bayyanar
boko, ajami ya daɗe da kafa daula a ƙasar Hausa. Kafaɗarsa ce boko ya
dafa ya cira ƙafafunsa sama, ba don ajami ba, da boko bai samu damar
shanya garinsa a Nijeriya ta Arewa ba.[37]
Rawar
Hausa Da Hausawa A Shimfiɗar Buzun Karatun Boko
Tarihin bayyanar karatun boko da
bazuwarsa masana sun yi abin a zo a gani a kai.[38]
Abin da nake son in lalubo a nan, irin agajin da harshen Hausa ya ba boko, aka
kai ga nasarar haihuwan ‘yan bokon da suka tabbatar da kafuwar ƙasarmu, da ƙwato ‘yancinmu, da
shimfiɗa ilmin da ake
doro da shi da sunan boko a yau. Da boko ya zo, da rubutu ya tarar da Bahaushe
a dabarar salon alamomin rubutu a tsage-tsagensa na gargajiya.[39]
Haka kuma, an tarar da Bahaushe da dabarar alƙalami da tawada da
amfani da takarda da allo da fasahar karatu duk a cikin ajamin Hausa.[40]
Wannan ce ta sa, baban boko (Bature) ya ga mun fi ƙarfin a yi muna
ikon garin-da-garin[41]
irin wanda suka yi a kudancin Nijeriya, dole aka yi muna dabarar, ku bi
Sarkinku, shi ko, shi bi mu.[42]
Da ilimin boko ya zo Arewacin Nijeriya, makarantun yaƙi da jahilcin boko
aka kafa, ba yaƙi da jahilcin ilmi ba, domin da abin mu aka gan mu.[43]
Da abu ya ƙasaita, aka kafa makarantun farko a Sakkwato[44]
da Katsina[45]
da Kano[46],
kuma da Hausa ake koyar da komai da komai[47].
A farkon lokaci, akan hana wa yaro
koyon Turanci sai ya kai makarantar tsakiya (Middle School) ko ya kai aji
biyar.[48]
Koyon karatu da rubutu da harshen Hausa dole ne, kuma da shi ake tinƙahon zama ɗan takarda.
Fannonin ilmi na Lissafi da Kimiyya da Tarihi cikin Hausa ake koyon su.[49]
Da haka ilmin Hausa ya samu ratsa zukatan ‘yan bokon farko har ya samu ƙafafun tsayi a
makarantun gaba da firamare. Ashe ba don Hausa ba, da buzun karatun boko ya
tabbata naɗaɗɗe a faɗin farfajiyar
Nijeriya ta Arewa. ‘Yan bokon da aka yaye cikin wannan tsarin, da su Nijeriya
ke bugun gaba da tinƙaho har gobe.
Karatun Hausa A
Matakan Ilmi Mai Zurfi
Duk fafitikar da Hausa ta yi na kare
martabar ilmi a Nijeriya, Turawan mulkin mallaka da ‘yan barandar su sun ƙi sake mata mara
ta zama darasin ilmi mai cin gashin kansa.[50]
Ga zatonsu, barin Hausa ta miƙe ƙafafunta a karatun
boko wata kafa ce ta koran Turanci da al’adun Nasara.[51]
Da hasken rana ya bayyana ɗaliban ilmi na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da ke
Tsangayar Fasaha ƙarƙashin darusan Turanci da Larabci da
Tarihi da Walwala da Ilmin Siyasa su suka fara neman a ba Hausa gashin kanta a
darusan ilmin jami’a. Ta haka ne Hausa ta samu shiga jerin darusa masu karɓar digirin kansu.
A lokacin da masu bitar tarihin
karatun Hausa suka yi bitar bunƙasar karatun Hausa, Jami’o’in da ake koyar da Hausa fitattu uku ne. A yau,
muna da gawurtaccen cigaban bunƙasar karatun Hausa bisa ga cewa:
i.
Muna
da Jami’o’in Tarayya takwas da ake karatun Hausa (8).[52]
iii.
Muna
da Kwalejin Ilmi na Tarayya guda (14).[54]
iv.
Muna
da Kwalejin Ilmi na Jaha (17).[55]
v.
Muna
da Manyan Makarantun Fasaha guda (7).[56]
A wannan ƙarni da muke ciki,
babu harshe daga cikin harsunan Afirka da ke da makusanciyar rabin waɗannan makaman
ilmi. A gida Nijeriya ko ba a gwada ba linzami ya fi bakin kaza.[58]
Muryoyin
Hausa A Kundayen Ƙanana Da Manyan Digirori
Ɗaliban nazarin
Hausa ba su yi wa Hausa butulci ba wajen haɗa kundayen binciken samun shaidar karatun
Hausa. Na san magabata sun yi rawar gani wajen tattaro kundayen musamman a
ayyukan da muka yi bita. Hujjata ta kawo bayanin ita ce, a yanzu, ayyukan da
aka yi bayan waɗanda suka gabata
sun kusan nunka waɗanda suka gabata.[59]
Kundayen bincike, wata fasaha ce ta tabbata wa duniya cewa, ruwa na ƙasa sai ga wanda
bai tona ba. Haka kuma, da su kowane fannin karatun ilmin boko ke laɓewa wajen auna
irin gudummuwarsa ga fannin ilminsa. Bisa ga kirdadon adadi, ɗaliban da ake
yayewa a Hausa za mu ce:
i.
Kundayen
digirin BA za su kusanci dubu biyar.
ii.
Kundayen
NCE da Difloma sun haura dubu goma.
iii.
Kundayen
digirn MA da MPhil na cikin gida muna da 300.
iv.
Kundayen
digirin PhD na cikin gida muna da 100.
Haƙiƙa, mai cewa a sake
lale bai san dara ba. Lallai cikin harsunan da muke da a duniyar baƙar fata babu mai
gwada tsawo da Hausa a kan yawan masu digirin farko da manyan digirori.[60] A
harsunan Nijeriya, Hausa ce ta ɗaya ga ƙasaita a ilmi ba
da tababa ba. Ga tsarin jadawalin manyan digirori da jami’o’in cikin gida suka
bayar domin faɗar Bahaushe na
gani ya kori ji.
Hausa
Da Malamanta: ‘Ga Wuta Ga Masara’
Bisa ga al’ada, harshen Hausa na nan
bisa tsohon alƙawali na mazhaba uku; Al’ada da Adabi da Harshe. Babu
dole ga bin kowace mazhaba, kuma ba a haramta wa kowa raba hannu ba bale taɓa-ka-lashe idan buƙatar haka ta taso.[61] A
al’adance, mazhabar da malami ya kafa alƙalamin binciken
digirinsa na ƙarshe, nan ne gijensa da ake fatar samun gudummuwarsa
mai tsoka.[62]
A yau, ko ba mu yi kirarin matsoraci ba, idan aka dubi irin yawan rundunar
karatun Hausa a duniyar ilmin boko a Nijeriya, dole a cire wa Hausa hula domin
tana da:
i.
Yawana
malamai a Kwalejin Fasaha na Jihohi.[63]
ii.
Yawan
maamai a Kwalejin Ilmi na Jihohi.[64]
iii.
Yawan
malamai a Kwalejin Ilmi na Tarayya.[65]
iv.
Yawan
malamai a Cibiyoyin Nazari.[66]
v.
Yawan
malamai a Cibiyoyin Bincike.[67]
vi.
Yawan
malamai a Jami’o’in Jihohi.[68]
vii.
Yawan
malamai a Jami’o’in Tarayya.[69]
viii.
Adadin
rundunar Hausa a farfajiyar ilmi sun kai 521.
ix.
Muna
da masu murabus ashirin (20).
Ina ƙalubalantar duk
wani harshe na Nijeriya ya zo da irin wannan taliyo, ku ga irin tazarar da za a
samu. Ganin irin wannan adadi nake ganin ya kamata a ce, in kiɗi ya sauya ko rawa
ta sauya, domin an ce, waƙa ɗaya ba ta gama niƙa balle ta kai
sahe. Wai ko lokaci bai yi ba na fara baje kolin karatun Hausa a Jami’o’in ƙasashen Afirka ta
Yamma? Sussuka ɗaka, dahuwa ɗaka abin ya yi
yawa.[70]
Kar tunani mai maɗi ke talla mai
zuma ido yake sa wa ya yaudare mu. Ban ga laifin mai zuma ya ba da ya sunsuna
wa harshen mai ciniki, domin Narambaɗa ya ce, da haka nan za a raba gardama.[71]
Masana
Hausa Da Shehunanta
Ban yi musun malamina da ya kira wasu
daga cikinsu jigajigan Hausa ba.[72] A
nawa awo, matakin masani daban, matakin shehi daban. Dalili kuwa, ba kowane
masani zai zama shehi ba, amma kowane shehi, sai da ya ratsi kogin sani.[73] A
ƙa’idar
Hukumar Kula da Ilmin Jami’a ta Ƙasa (NUC),
takardar shaidar zama halastaccen malamin Jami’a ita ce takardar shaidar samun
digirin (PhD). Bisa ga wannan kirdado
nake ganin, wanda ya samu wannan shahadar, ya cancanta a kira shi masani a
fagen da ya bibbiya ko da hazaƙarsa ba ta yi fice ƙwarai ba,
ladabinsa ya cika masa tsawo a sa shi cikin sahu.[74]
Idan tunanina ya samu karɓuwa, duk mai
digirin PhD a Hausa a ko’ina yake koyarwa ko aiki,
masanin Hausa ne, domin kowane gauta ja ne, sai in bai ji zafin rana ba. Tare
da amincewarku na so a dubi wannan jadawali sosai, a ga, me Hausa ta rasa a
farfajiyar karatu da ilmi?
Gurbin
Karatun Hausa A Talife-Talifen Ilmi Da Yekuwar Nagartar Da Shi
A wannan fagen ma rubuce-rubucen da
aka yi bita sun yi abin a zo a gani. Sanin cewa, ɓarin waina cikin zuma ba ɓarna ba ne na kasa
kawar da kai ga bagiren. Yadda kowane fannin ilmi ke bugun gaban samar da
mujallun nazari da sabunta fahimta, Hausa a kan gaba take. A kowane sashe na
koyar da Hausa a Jami’o’inmu akwai mujalla ta musamman da ke kula da wallafa
takardun ilmi da aka yi na Hausa.[75] A
Kwalejin Horar da Malamai na Tarayya[76]
da Jihohi[77]
da Makarantun Fasaha[78]
duk akwai mujallun ilmi na Hausa. Bugu a ƙari, muna da
fitattun mujallun da ba na Hausa ba, amma martabarmu ta sa suna maraba da takardun
da aka yi cikin Hausa su wallafa.[79]
Shehunan Hausa da masana Hausa da malaman Hausa da ɗaliban Hausa, ba
su da ƙamfar wuraren da za a wallafa aikace-aikacensu da
bincike-bincikensu ba.
Sanin
Asali Kan Sa Kura Cin Kanjilo
Wata babbar martaba da ke ga karatun
Hausa da ta zarce sauran harsunan Afirka gaba ɗaya ita ce, samun yalwatacen fagen
nazari. Farfagandar Turawan mulkin mallaka da ‘yan wariyar launin fata, na
kushe harsunanmu da al’adunmu da wayewarmu, ba ta ci nasara ba ga Hausawan da
suka yi boko da maƙwabtansu.[80] A
ɗan binciken da na
gudanar na ga ma’ilmantanmu da ke sassa
daban-daban na ilmi sun yi wa Hausa gawurtaccen zubin adashi a fagen ilmi.[81]
Abin ban sha’awa sai ka ga mai harshe ya yi watsi da harshensa, ba kuma Hausa
ya karanta ba, amma ya yi wa Hausa namijin ƙoƙarin da Bahaushen
da ya karanci Hausa ba zai taɓa tunanin yi ba.[82]
Dalilina na yi wa wannan fasali taken
sanin asali kan sa kura cin kanjilo shi ne, sanin irin fa’idojin da ke cikin
Hausa shi ya jawo mata farin jini. A halin da muke ciki, nazarin adabi da
harshe ga masu karatun harshen Turanci, harshen Hausa da rubuce-rubucen Hausa
ne ake sarrafawa.[83] A
fannin ilmin kimiyyar harsuna, Hausa ce zakaran gwajin dahi.[84] A
fannin Larabci, Hausa ce abar kwatance.[85]
Wajen masu karatun addinin Musulunci da Hausa da ƙasar Hausa ake dubi.[86]
Masu Tarihi da Bahaushe da ƙasar Hausa ne gijensu.[87] A
wajen masu walwala da Hausa ake walwale karatu.[88]
Masu siyasa, siyasar ƙasar Hausa ce ma’aunin ra’o’insu.[89]
Masu tsimi da tanadi, tattalin arzikin Bahaushe suke Turancewa.[90]
Masu kimiyyar kiwon lafiya da harhaɗa magunguna, Bahaushe da kansa yake
kiransu likita bokan Turai.[91]
Kai! Hatta da masu ilmin ƙera jiragen sama sun san da Bahaushe na da sirrin
gaba.[92] Me ya bambanta makamai masu linzami da halbin
kasko?[93]
Masana ilmin sarrafa ƙarafa dole su jinjina wa fasahar cin taman maƙeran Hausa.[94]
Ni dai a ganina, binciken fasahar Bahaushe a duniyar ilmin boko a halin da ake
ciki yanzu, an dai fara rage zango na mai zuwa sama da ya ta ka faifai. Ga wasu
‘yan jerin kundayen digirin PhD da Hausa ta taka
rawa a wajen karatun Hausa.
Lokacin
Abu A Yi Shi
A gaskiya, Allah Ya sama wa karatun
Hausa lokaci ta hannayen wasu na can daban da ba su gama komai da Bahaushe ba.[95]
Yau, mun kai matakin da babu wata haraka ta ilmi da harshenmu bai taka
muhimmiyar rawa ba. Babu fannin karatun da za a ambaci Hausa ya nemi ƙarin bayani. Babu
takardar shaidar ilmi da Hausa ba ta bayarwa. Waɗanne makamai za mu tanada mu
tabbatar da limancin Hausa a duniyar ilmi ta wannan ƙarni? Idan muka yi
nazari da irin duniyar da muke ciki dole a ce:
i.
Muna
da nagartacciyar ƙungiyar amintattun masana da manazata Hausa da za su
tabbatar da kasancewar Hausa cikin sahun gaba a sha’anin ilmn ƙasarmu.
ii.
Ka
da mu yarda jirgin “Shirin Game Duniya” ya bar mu a baya. Mu yi tsayin daka na
ganin ilmukan Hausa na rayuwa a duniyar yanar gizo da kafafen sadarwa na
zamani.
iii.
Dole
mu tsayar da wata tuta ta ƙwararrun masana da za su duƙufa ga fassara
gadan-gadan. Mu tunkari kimiyyar zamani da dabarun sarrafa ilmi na zamani,
Hausa ta kasance mai murya ɗaya. A fara koyar da kimiyya da Hausa a makarantun
gaba da firamare.
iv.
Darussanmu
na Hausa suna buƙatar samun damarmu na lokaci na musamman mu sake bitar
su, mu daidaita akalar karatunmu da buƙatocin duniyar
zamaninmu.[96]
v.
Taɓarɓarewar ilmi na ƙasarmu ya shafi
fannonin karatunmu. Digirorin da muke bayarwa, da rawunnan da ake naɗa wa malamanmu na
shaihintaka ba su tsira ba. Mu yi tsayin daka mu kashe wutar gidanmu da kanmu,
ka da mu yarda bakin wuta ya mutu a hannunmu.[97]
vi.
Me
zai hana mu raba wa Jami’o’inmu aiki a matakan samun babban dgirin MA da MPhil
da PhD, a dinga kula da albarkatun da ke ƙasar da Jami’ar
take kusa da su na bincike da ƙwararrun da take da su?[98]
vii.
Tilas
mu kafa asusun aikin gayya na taskace fasahohinmu na baka tun ba su salwance
ba. Mawaƙanmu na baka sun ƙare waƙoƙinsu na soma
salwanta.[99]
Marubuta sun tafi abinsu, waƙoƙinsu ba a taskace
ba.[100]
Adabinmu na baka da azanci da fasaha da sana’o’inmu na gargajiya ba mu sa musu
kai ba.[101]
Kare-karen harshenmu an bar su a barkace, aka sa wa yara da ‘yan dagaji ido
suna yi musu cin alewar kuturu. Ga su nan dai!
Sakamakon
Nazari
Harshen Hausa a duniyar ilmi yana ɗaya daga cikin
manyan harsunan Afirka da suka share fiye da ƙarni ɗaya cikin karatun
jami’a. A Nijeriya, an fara gabatar da kundin digirin BA a shekarar 1972, na MA
a shekarar 1978, na PhD a shekarar 1979. A Jami’ar Ahmadu Bello,
Zariya - Ibrahim Yaro Yahaya ya fara karɓar PhD, a shekarar 1979.
A Jami’ar Bayero, Kano – Garba Muhammad Magashi ya karɓi PhD
a shekarar 1982. A Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
- Abdullahi Bayero Yahya da Haruna Abdullahi Birniwa suka yi canjaras da PhD
a shekarar 1987. Jami’ar Ahmadu Bello ta fara ba da digirin PhD na Falsafar
Bahaushe. Jami’ar Bayero, ta fara ba da digirin PhD
kan Nahawun Hausa. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta fara
ba da digirin PhD na Adabin Hausa (Waƙa). Wannan ɗan taƙaitaccen bincike,
ya ci nasarar hango abubuwa kamar haka:
i.
A farfajiyar ilmin boko a Nijeriya, Hausa na
da sansani sittin da ɗaya (61). Tana da
sashe a jami’o’i (19); 8 na tarayya, 11 na jihohi. Ta yi mazauni a kwalejin
ilimi na Tarayya, 14 na jihohi 17, manyan kwaleji 7, cibiyoyin bincike na Tarayya
4.
ii.
A
fagen bincike da nazari, Hausa na da babban gurbi a mujallun ilmi 40. Mujallun
kanta a Jami’o’i tana da 7. A Kwalejin Ilmi na Tarayya tana da 8, na jihohi
tana da 10, tana da 2 na musamman. Manyan mujallun ƙasa da ƙasa da na Tarayya
13 suka aminta da karɓar takardun
bincike da aka rubuta cikin Hausa.
iii.
Bisa
ga wannan gagarumar nasara a yau 2014, Hausa na da shehunan malamai 30; 15 a
harshe, 11 a adabi, 4 a al’ada. Madalla da tabbata muku muna da masana masu
digirin PhD kimanin 56: A al’ada muna da 13; a adabi
27; a harshe 16. A jimlace Hausa na da manyan masana 86 da dokar duniya ta ilmi
ta aminta da zamansu halastattun malamai masu koyarwa a kowace Jami’a ta
duniya.
iv.
Harshen
Hausa ya ba da gudummuwar manyan digiri fiye da ɗari huɗu 400 a gida Nijeriya.
Digirin MA 300: Jami’ar Bayero 170; Jami’ar Ahmadu Bello 70; Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo 70. A
digirin PhD, Jami’o’in Nijeriya sun yaye masana fiye
da 70: Jami’ar Bayero 40; Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo 18;
Jami’ar Ahmadu Bello 18.
v.
Daga
cikin waɗanda suka ɗalibci Jami’o’in Nijeriya
a fannin Hausa, suka karɓi diigirin BA da
MA da PhD a fannin Hausa a gida Nijeriya
10 daga cikinsu sun sami kujerar muƙamin shehunnan
malamai. A Nijeriya mutum uku suka sami digirin fintinkau (1st
class), Aminu Lawal Auta a Jami’ar Bayero – 1983; da Ahmad Baba Tela a Jami’ar
Maiduguri – 1984; da Abdurrahman Faruk a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua – 2010.
Sa’idu Muhammad Gusau shi ya fara rubuta kundin PhD da Hausa.
vi.
Lokaci
ya yi na a sake yin wani tsaftataccen aikin da zai kundace tarihin karatun
Hausa da gudummuwarta da kafuwarta a gurabun ilmukan duniya. Abubuwa na kundaye da wallafaffun
ayyuka da yawa sun salwanta. A jami’o’inmu, babu wani tsari na tsaron ayyukan da
aka yi, bale a taskace su wuri ɗaya, su samu shiga duniyar gizo. Idan mun yi canjaras
da ku a tunani a nan, ina son ku ba ni goyon baya in faɗaɗa wannan bincike
zuwa gawurtacen littafin da zai kasance babbar taska ga masu karatu da nazarin
Hausa. Na gode ga goyon bayan da na samu, ina fatar za a ƙara. An riga an
fara, kun ko ce, wuyar aiki ba a fara ba.
vii.
An
ce, cikin ƙira ake ɗaɗi: wane harshe daga cikin harsunanmu na
Nijeriya kimanin 500 ke da ɗaya bisa ukun waɗannan abubuwa da Hausa ta ƙaddamar? Da wace
hujja ake son a gurgunta harsunanmu a tsarin ilmin ƙasarmu? Muddin
harshen Hausa kaɗai ya ci wannan
nasara a tsarin ilmin boko Nijeriya da Afirka. ‘Yan’uwana! Idan boko addini ne,
to addinin Hausawa ne. Idan ilmi ne, ƙasar Hausa ya
tsira, Hausawa suka haifi abin su dole a sake wa uwa ɗanta. Idan wata
hajar talla ce, ta ko’ina aka buɗa shagon tallarsa, Hausawa ne fatakensa.
Don haka, shafa wa arewacin Nijeriya da Bahaushe ya mamaye kashin kajin BOKO HARAM wata hasada ce da ƙiren ƙarya na hana wa
Bahaushe kai ga burinsa na tabbatar da nagartaccen jagoranci a Nijeriya.
Naɗewa
Hausa da Bahaushe da ƙasar Hausa, ba ɓoyayyun abubuwa ne
ba a duniyar ilmi jiya da yau. Harshen Hausa shi ya kai sunan Bahaushe da ƙasar Hausa duniyar
da dugadugan Bahaushe ba su taɓa takawa ba, kunnensa bai da labarinsa. Daga cikin
harsunan Afirka, babu mai martabar baje kolin tunaninsa a ɓangarorin ilmi mai
zurfi kamar Hausa. A duniyar baƙar fata, babu harshen da ke da
yawan masu digirin farko da babban digirin PhD kamar Hausa. A
tarihin karatun boko na Nijeriya, Hausa ta fi kowane harshe yawan masana da
shehunan malamai. Babu abin da ya rage wa Hausa yau, face, gaggauta tunanin
Hausantar da sassan ilmi musamman kimiyya domin yaranmu su amfana da madarar
harshenmu wajen shayar da su ilmin zamaninmu. A cikin wannan ƙarni, cikin
Harsuan Nijeriya, babu wanda ya yi amon Hausa a fagen ilmi da sadarwa da
zamantakewa da bazuwa a duniyar zamaninmu. Ɗalibai da manazarta Hausa mu kau da kai ga ɓaɓatun ‘yan sa ido,
da ‘yan a yi mu gani, da ‘yan ƙaƙa za a yi! Ga saƙon makaɗa Narambaɗa gare mu, mu
duka:
Jagora: Ku saki jikinku
Lokaci da yawa ‘ya’yana
Yara: Kowac ce, duniyag ga ta ƙare, ta basai
Jagora: Yau da sarauta da ɗaukaka da muhibba
Yara: Suna gidan Basharu na Isa
:Babu sauran motcin kowa
Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
:Baban Dodo ba a tammai da
batun banza.
MANAZARTA
Abdu,
M. (bsk) Tasirin Zuwan Turawan Mulkin Mallaka Ƙasar
Hausa. Zaria:
Institute of Education, Ahmad Bello University.
Abraham,
R. C. 1959. The Langage of the Hausa People. London: University
Press.
Adam,
S. J. M. 2013. Tarjama da Sharhin Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma (Suratul-Faatiha -
Suuratun Nisaa’i). Kano:
Ɗorayi.
Adamu,
A. U. 2005. “Hausa da Hausanci a Ƙarni Na 21: Ƙalubale da
Madosa”, Takardar da aka gabatar taron wuni guda kan wayar da kan jama’a game
da harakar fim. Kano: Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa.
Adamu,
H. R. 1973. Matsayin Arewa a Tarayyar Nijeriya.
Zaria: Gaskiya
Publishers.
Adamu,
L. D. 2009. “Boko Haram Regroups n Kano”, Daily Trust - Monday,
September 21, 2009, Shawwal 2, 1430 AH, Vol. 22; No. 61; p. 1-5.
Adamu,
M. 2010. Major Landmarks in the History of Hausaland the Eleɓenth Inaugural
Lecture, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Adeyanju,
T. K. 2014. “Understanding and Stemming the Tide of Language Endargement in Nigeria”
paper presented at the First International Conference on Endargered Languages
in Nigeria, in honour and memory of Professor M. K.
M. Galadanci. Kano: Bayero University.
Albert,
O. and Ocho, L. 1981. Education in Northern Nigeria. London: Allen and Unwin.
Alhassan,
H. 1906. “Rashin Jituwa Tsakanin Malaman Satiru da Turawan Mulkin Mallaka”, muƙalar da aka
gabatar a Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci. Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Amfani,
A. H. 2004. “The Development of Hausa From Colonial Period to Modern Day States.” Ɗunɗaye
Journal of Hausa Studies, Department of Nigerian Languages.
Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Amfani, A. H. 2011 “Four Decades of Language and Linguitic Studies
in Hausa (1960 – 2000)” in Studies in Hausa Language, Literature and Culture:
The Siɗth Hausa International Conference. CSNL, Kano: Bayero University. Pp
96 – 113.
Aminu,
N. 2002. “Adabin Hausa A Zamanin Mulkin Mallaka: Nazarin da Sharhi a kan
Ayyukan Frank Edgar” Kundin digrin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Anjorin,
A. O. 1966. “The British Occupation and Development of Northern Nigeria,
1897-1914” PhD Theisis. London: University
of London.
Ayandele, E. O. 1982. “The Missionary Factor in Northern Nigeria
1870 – 1918” in Ogbu Kalu (ed.) The History of Christianity in West Africa.
London. Pp 133 – 158.
Backwell,
H. P. 1969. The Occupation of Hausaland 1900-1914. Frankcass.
Baffa,
M. S. 1985. “Roƙo: Tradition and Change in a Hausa Theatrical Form,”
MA Thesis (Englsh). Zaria: Ahmadu Bello University.
Bakura,
A. R. 2012. “Gudummuwar Turawa Wajen Samuwa Da Ginuwar Adabin Hausa,” kundin
digirin PhD. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Baldi,
S. I. 1975. “Systematic Hausa Bibliography” MA Thesis, Duƙuesne
University.
Barnes, 1995. “Eɓangelization Where it is not wanted: colonial administrators
and missionaries in northern Nigeria during the first third of the twentieth
century” in Journal of Religion in Africa, 25. Pp 412 – 441.
Birnin
Tudu, S. Y. 1990. “Nazari kan Rubutun Ajami a Ƙasar Hausa” kundin
digirin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza,
A. M. 2003. Hausa Medicine: Its Releɓance and Development in Hausa Studies. The Second Inaugural Lecture, Usmanu Danfodiyo
University, Sokoto Published by the Central
Co-ordinating Committee for University Seminars. Sokoto:
Trans Akab Printers.
Bunza,
A. M. and Nofel, M. A. (ed.) 2014. Ruwan Bagaja In Perspesctive: Eight
Decades of a Hausa Masterpiece in Prose 1933-2013.
Published
by Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina and University
of Cairo, supported by Tertiary Education Trust Fund (TETfund) Nigeria.
Bunza,
M. U. 2000. “Christian Mission in Sokoto Proɓince, 1935-1990” PhD
Thesis. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Chamberlin,
J. 1975. “The Development of Islamic Education in Kano City Nigeria, with
Emphasis on Legal Education in the 18th and 20th
Century”, PhD Thesis. Columbia: University of
Columbia.
Charles,
O. W. J. 1911. The Making of Northern Nigeria. Mcmillan Publishers.
Crampton,
E. P. T. 1976. Cristianity in Northern Nijeriya. Zaria: Gaskiya
Coopration.
Daura,
M. D. 1983. “Bunƙasar Hausa a Nijeriya 1960-1980”, kundin digirin BA,
Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Daurawa,
I. S. B. 2009. “BOKOKO A WUTA” Matasa Ƙashin Bayan
Al’umma, Fitowar Salla. Katsina: Kamfanin Matasa Media Links Nigeria,
Ltd.
Ferguson,
D. E. 1973. “Nineteeth Century Hausaland, Being a Description by Imam Omoru of
Land, Economy and Society of his people” PhD Thesis.
Califonia: University of Califonia.
Furniss,
G. 1989. “Matsayin Karatu da Nazarin Harshen Hausa a yau” cikin Harsunan
Nijeriya viv Twenteeth Year Commorative Edition (1969-89). Kano: Centre for
the Studies of Nigerian Languages, Bayero University.
Furniss,
G. 1996. Poetry Prose and Popular Culture in Hausa.
EU:
Edinburgh.
Furniss,
G. and Jaggar, P. J. (eds.) 1988. Studies in Hausa Language and
Linguistics. London:
KPI.
Hisket,
M. 1975a. A History of Hausa Islamic Verse. London: School of
Oriental and African Studies, (SOAS).
Hubbard,
P. J. 1973. “Education under Colonial Rule: A History of Katsina College
1921-1942”, PhD Thesis, Madison: University
of Wisconsin.
Ibrahim,
I. A. 2009. “Matsayin Karatun Zamani da Aikin Gwamnati a Musulunci”.
Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani
na Jama’atu Izalatil Biɗah wa Iƙamatus Sunnah,
Reshen Katsina, a kulawar Hukumar Alhazzai.
Ikara,
B. 1975. “English as a factor in the Process of Hausa Language Modernisation: A
study of the Impact of English on the Hausa Language in Northern Nigeria”
PhD Thesis. London: University
of Leeds.
Jaggar,
P. J. 1994. The Black Smiths of Kano City. Rudiger Koppe Ɓerlag KOLN.
Joe, A. 1984. “Hausa Folk Theatre and Occupational Groups: Some Eɗamples
in Zaria - Kaduna State”, MA Thesis (English). Zaria: Ahmadu Bello University.
Jonathan, R. 2001. “Good and Bad Muslims: Islam and Indirect Rule
in Norhtern Nigeria” in International Journal of African Historical Studies
34. Pp 601 – 618.
Kani,
A. M. 1978. “Literary Activities in Hausaland in the Late 18th and
Early 19th Centuries”, MA Thesis (History). Zaria: Ahmadu Bello University.
Mahuta,
M. S. 1986. “Nazarin Harshen Hausa a Jami’o’in Nijeriya”, kundin digirin BA,
Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Maishanu,
H. M. 2006. Five Centures of Historial Writing in Hausaland and Borno 1500-2000. Ibadan: Macmillan
Nigeria Publishers.
Mani,
A. 1957. Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa. Zaria: NNPC.
Miles,
W. F. S. 1994. Hausaland Divided: Colonialism and Independence in Nigeria and
Niger. Ithaca:
Cornell University Press.
Mohyidin,
B. A. 2004. Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma Fassara da Bayani Da Fassara zuwa ga
Harshen Hausa. India:
Continental Book Centre.
Newman, P. 1996. African
Linguistic Bibliography Hausa and the Chadic Languages Family. Rudiger Koppe Ɓerlag. KOLN.
Newman,
P. 2000. The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar, New Haven: Yale University
Press.
Nuhu,
B. 2007. Mungo Park Mabuɗin Kwara:
Labarin Tafiya ta Farko da ta Ƙarshe. Zaria: NNPC.
Ƙaraye, M. 2014. “Folklore as a Ɓital Resource for
the Documentation of Endargered Languages” paper presented at the 1st
International Conference on Endangered Languages in Honour of late Professor M.
K. M. Galadanci. Kano: Bayero University.
Richard,
H. D. 1985. The Conƙuest of Northern Nigeria. London.
Robinson,
C. H. 1896. Hausaland or Fifteen Hundred Miles through the Central Sudan. London.
Salim,
B. A. 2009. “Remarks on African and European Perspectives on Hausa Studies: Linguistics, Literature and
Culture”, in Proceeding of the Second International Conference on Hausa
Studies Africa and European Perspectives (10-17th Feb, 2008).
Kano: Bayero University.
Shankar S. 2014. “Who Shall Enter Paradise? Christian Origins in
Muslim Northern Nigeria, Ca. 1890 – 1975” in New African Histories Series.
Ohio: University Press.
Swai,
B. 1985. “How the Past is Politically Inspected and Historically Produced”,
public lecture presented on 9th March, 1985. Sokoto: University
of Sokoto.
The
Bible Society of Nijeriya, Lagos. 1979. Littafi
Mai Tsarki duk da AFORIKIFA. (KO DEUTEROCANONICAL).
Tibendarana, P. K. 1983. “The Emirs and the Spread of Western
Education in northern Nigeria, 1910 – 1946” in Journal of African History,
24. 517 – 534.
Tibenderana,
P. K. 2003. Education and Cutural Change in Northern Nigeria. Kampala - Uganda:
Fountain Publishers.
Uba, C. N. 1976. “Problems of Christian Missionaries in Muslim
Emirates, 1900 – 1928” in Journal of African Studies 3. Pp 351 – 371.
Ɓatagarawa, A. G. 1986. “Tarihin Rubutun Ajami a Ƙasar Hausa”.
Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani.
Sakkwato: Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari.
Wakili,
H. 2005. Turawa a Ƙasar
Haɗeja:
Karon Haɗejiyawa
Da Turawan Mulkin Mallaka. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Westley,
D. 1986. “The Oral Tradition and the Beginning of Hausa Fiction,” PhD
Thesis, Madison: University of Wisconsin.
Yahaya,
I. Y. 1988. Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC.
Yakasai,
M. B. Ɓ.
2009. “Wai Shin Boko Haramun Ne?” Kano: Mustapha Bala Volɓo Yakasai:
08061617071/ 08086133483.
Yakubu,
M. et al 2003. “1903 Reɓisited:
Murry Last” in Colonial Conƙuest and Resistance, inside Northern
Nigeria a Century of Transformation 1903 – 2003.
Arewa
House, Zaria: Ahmadu Bello University.
Yusuf,
M. A. 2008. “Ajami: Samuwarsa da Bunƙasarsa a Ƙasar Hausa” cikin Algaita
Journal of Current Research in Hausa Studies No. 5; Vol. I. Department of
Nigerian Languages, Series. Kano: Bayero University.
[1] A kowane fanin ilmi, tarihi na da rawar da yake
takawa. Samun tarihin abu, shi zai ba da hasken ina aka fito? Me ake ciki yau?
Yaya za a fuskanci gobe? Rashin daidaita akalar tarihi ya sa ayyukan magabata
suka shiga hannun mayaudara suka mayar da su nasu da qarfi da yaji. Lokaci ya
yi na mu samu darasin da zai kula da tarihin ayyukan da aka yi a Hausa a kowane
rukunin karatun neman digiri.
[2]
Dalili kuwa Hausa a
matsayinta na harshe a Nijeriya ba ta da matsayi a hukumance, amma ta mamaye
qasa. Daga cikin harsunan Afirka ita ce ta mamaye mafi yawan kafafen yaxa
labarai na duniyar qarni na ashirin da xaya.
[3]
Da ita Turawan Mishan suka yi
garkuwa ga yaxa addininsu. Da ita aka fara koyar da boko. Dokokin hukuma da
ayyukanta da Hausa ake shirya su a Nijeriya ta Arewa tsawon mulkin mallaka zuwa
wannan qarni.
[5]
An gabatar da binciken 1975,
yau muna 2014. Wallafe-wallafen da aka samu bayan aikinsa a kan fannonin da ya
yi rubutu sun nunka na aikin nasa ninkin-ba-ninkin. Kakkave wa bincike gara
wajibi ne a fagen ilmi domin samun cigaba.
[6]
Paul Newman, African Linguistic
Bibliographies Hausa and Chadic Language Family, vol. 6, KOLN. 1996.
[7]
Paul Newman ya tattaro
ayyukan da aka wallafa da waxanda ba a wallafa ba na kundayen digiri da
takardun qara wa juna sani. Ba a kan Hausa kaxai ya tsaya ba. Ya haxa da dukkanin
harsunan iyalan Chadi na Tera da Margi da Bade da Mandara da Wula da da dai
sauransu. An buxe gaba da yawa dole a kasa rungumo wasu. Mayar da hankali a kan
ayyukan harshe kaxai shi ya rage wa aikin Newman nauyi a ilmance, kuma ya kasa
yi wa harshen Hausa babbar gayya domin ya kau da kai ga ayyukan adabi da
al’ada.
[8]
Aikin Newman an wallafa shi
1996. Daga wannan lokaci ya zuwa yau 2014, shekara 18 ke nan. Ko a fannin
harshe kaxai an samu digirin MA da M.Phil da PhD
fiye da ashirin; wallafaffun litattafai da mujallu da takardun da aka gabatar a
tarukan ilmi sun fi dubu cikin shekara goma sha takwas a duniyar ilmin harsunan
iyalan Chadi da Hausa. Doguwar tazara ga aiki wata dama ce ta sake bitarsa.
[9]
Graham L. Furniss, “Matsayin
Karatu da Nazarin Harshe Hausa a Yau”, cikin Hasunan Nijeriya, xiv Twentieth Year
(1969-89) Commemorative
Edition. Centre for the Study of Nigerian Languages, 1988/89: Shafi 1-14.
[10]
Bayan da Furniss ya gabatar
da muqalunsa biyu, ya wallafa gagarumin aiki a kan rubuce-rubucen da aka yi a
Hausa gaba xaya mai take: Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. Edinburgh: University Press, 1996. Wannan aiki ya warkar
sosai sai dai ya yi shekara 18 da yi.
[11]
Ibrahim Yaro Yahaya, Hausa A Rubuce:
Tarhin Rubuce-rubuce Cikin Hausa.
Zaria: NNPC, 1988. Asalin wannan littafin wata takarda ce da ya gabatar a
Bukukuwan Qungiyar Hausa ta Kwalejin Ilimi ta Sakkwato, a shekarar 1980.
Fa’idojin da aka hango ga takardar aka ba shi shawara ya faxaxa ta zuwa
littafi, NNPC suka yi alqawalin wallafa shi. Wannan ce ta sa a aikin ya haxa da
kundayen neman takardar shaidar NCE da Diploma na Kwalejojin Ilmi da Kimiyya.
Aikin ya tattaro iya abin da ya sawwaqa a fagen. A yau, aikin shekarunsa
ashirin da shida (26). Ayyukan da aka yi bayansa suna yin irin aikin sau biyar
ko bakwai.
[12]
Aikin Haliru Ahmad Amfani
takarda ce da aka wallafa mai taken “Four Decades of Language ans Linguistic
Studies in Hausa (1960-2000) in Studies in Hausa Language, Literature and
Culture: The Sixth Hausa International Conference, CSNL, Jami’ar Bayero,
Kano, (eds) Yalwa, L. X., Bichi, A. Y. and Sani, S. 2011. Pp. 96 – 113. Ta
qunshi ayyukan digirin MA da M.Phil da PhD da wasu wallafe-wallafen da aka yi
a kan harshe (nahawun Hausa) kaxai. Takarda ta lisafa ayyuka xari da huɗu. Ya kawo kundayen PhD
43 kundayen digirin MA 59.
[14]
A dubi Sabi’u Alhaji Garba,
“Shirye-shiryen Rediyo na Hausa: Tubalan Gina Demokraxiyya a Nijeriya” cikin
Lawal, Sa’idu da wasu. Studies in Hausa Language, Literature and Culture, the First National
Conference, CSNL, Kano:
Bayero University, 2013. Pp. 651-669; da takardar da
ya gabatar mai taken “Hausa in the Media” a taron LAN, 2011; da “Hausa Gidan
Rediyon BBC” kundin digirin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, 2010.
[15]
A dubi Umar Aliyu Bunza,
“Mujalla da Jaridun Hausa: Samuwar su da Rashin Tabbatar su daga 1986 – 2006”
kundin digirin MA, Sokoto: Usman Danfodiyo University,
2008.
[16]
Ina ganin aikin Sabi’u na
qarshe 2010 da na Umar Bunza na qarshe 2008 ko a bayansu abubuwa da yawa da ya
kamata a yi nazari sun wakana.
[17]
Ayyukan Furniss da Newman ba
su bazu a Afirka sosai ba. Da Furniss ya lura da haka ya zo ABU Press aka sake
buga shi domin ya samu shiga hannun xalibai da malamai da manazarta Hausa na
qasar Hausa. Aikin Newman bai samu wannan damar ba.
[19]
Wannan wani sabon ra’ayin
Mahdi Adamu ne da ya bayyana a takardarsa mai take, Major Landmarks
in the History of Hausaland,
The
Eleventh Inaugural Lecture. Wadda aka gabatar ranar Alhamis, 1 ga Afirilu 2010.
Sokoto: Usman
Danfodiyo University.
[20]
Wata hira da na yi da hakimai
da dagatai da iyayen qasar Argungu a shekarar 2013 – 2014, yayin da muke
qoqarin raba tallafin da gwamnatin Kabi ta yi wa waxanda ambaliyar ruwa ya
rutsa da su. Sun tabbatar mini cewa, ai shi ne dalilin Kabawa, idan ana yi musu
taken Kabi a bukukuwansu tamburan cewa suke:
Jagora: Da mi tac ci Hausa?
Jama’a: Da qarfi da yaji.
Hausa a wajensu ita ce Sakkwato.
Ita kuwa Sakkwato, asali qasar Gobir ce Fulani suka mamaye da sarautar iko
cikin qasar Gobir. Don haka suke kiran ta Hausa.
[21]
Na yi yunqurin yin fashin
baqin wannan batu a wata takardar da na gabatar mai take: “Sakkwato ce Tushen
Hausa in ji Narambaxa (Laluben Gudummuwar Mawaqa A Kan Asalin Bahaushe da
Harshensa)” Takardar da aka gabatar a taron qara wa juna sani a Tsangayar
Fasahar Xan’adam, Jami’ar Umaru Musa, ‘Yar’adua, Katsina, ranar 05-05-2011.
Dubi yadda makaxa ke karanto wannan ra’in a bakandamiyarsa:
Jagora: Yau mai ashararu ya kaxe
:Duniya
ta yi mai fashi
Yara: Babu zama garai zama magana yax xauko
:Ya san ba a qwar jini
ga mutanen Hausa
:Kowac ce yana
iyawa ga hili nan
:Sai ya qetare
gidanai ba ban kwana
Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron
giwa
:Baban
Dodo ba a tamma da batun banza.
Naramabaxa Sarkin Gobir na Isa
Amadu yake yi wa waqa. Isa kuwa mulkin Fulani ce, amma qasar Gobir ce, don haka
ake cewa sarautar - Sarkin Gobir, Isa. Mutanen Hausa ke nan suna nufin mutanen
Isa, qasarsu ce Fulani suka gwamatse don haka ta koma “Hausa” makaxa ya kira su
“mutanen Hausa”.
[22] Arawa da Gobirawa da Kyangawa da
Kabawan Kabi da al’ummomin qasar Yawuri suna kiran Sakkwato “Hausa” ko “Gabas”.
Dalilinsu na ce mata Hausa mun ambace shi lamba ta 21. Tunaninsu na kiranta
“Gabas” shi ne tana gabas gare su, kuma ta can ne Musulunci ya zo musu. Na yi zaton tunanin
haka ne ya sa Sani Aliyu Xandawo a waqarsa ta Gwamnan Sakkwato Shehu Muhammed
Kangiwa yake cewa:
Jagora: In arziki nike nema
:Ban zuwa gabas
Yara: Domin ga gabas sabuwa
Gindi: Bajini na Sarkin Kudu
:Gwamnan jihar Sakkwato
:Shehu
Kangiwa mai niyyar riqon gaskiya.
[23]
Tsabagen qabilanci ke sa
Bahaushe ganin duk wanda ba Bahaushe ba sunansa “Baubawa”, a Sakkwato a ce musu
“Damqe” saboda danqar quda (quje) da suke yi idan ya hau jikinsu ko abincinsu.
Idan mutum ya aikata wani abu na rashin fasaha da wayo, Hausawa na cewa “ba ya
da Hausa”. A wani lokaci har da ce masa, abu kamar ba Bahaushe ba? Haka kuma,
idan fasaha ta yi qoli sosai ana ce da ita Hausa. A cikin wata shahararriyar waqar
yabon Annabi (SAW) da liman Aliyu Isa ya yi bisa ga ma’aunin bakandamiyar
makaxa Narambaxa yana cewa:
…………………………………
Alfahari nikai da
shi ga irin Hausata
……………………………………
A tunaninsa waqa Hausa ce, domin ta
tattara qolin fasaha da basirar mai yin ta a harshen da yake bayar da ita.
[24]
Sanin damisar Bunu, a san abu
ba yadda yake ba. An ce, Bunu yana ba xansa labarin damisar da ya gani jeji.
Xan nasa ya san damisa sosai. Bunu ya ce: “Qarama ce, mai jikin kyanwa, mai
sauri da anniya, mai haqora masu kaifi, mai “manyan qahoni.” Sai yaro ya ce:
“A’a baba ba ita ce ba.” Ambaton qahoni ya vata duk wani kwatanci da Bunu ya
yi. Ta tabbata bai san damisa ba.
[25]
A ma’aunin ilmin da ake ba da
takardar shaidar kammala karatu, ana buqatar gabatar da kundi a matakin NCE da
BA da M.Phil da PhD. Duk wanda ya rubuta kundinsa a
kan wata fasaha ko wani tunani ko wani aiki ko wata sana’a ko wata gwagwarmaya
ko wata kimiyya ta Bahaushe, Hausa ya yi wa aiki. In za a yi adalci, Hausa ya
karanto, domin kundin wata hujja ce ta tabbatar da karatunsa ya yi. Da shi da
wanda ya karanta Hausa duk gudummuwarsu xaya ce a fannin da ya gabatar da
kundinsa.
[26]
Babu takaicin da ya kai
butulci a rayuwar Xan’adam. Yau, waxanda takardar shedar samun digirin Hausa ce
tushen arzikinsu, da na iyalansu su ke xari-xari a ce, Hausa suka karanta.
Ire-Irensu da ke Jami’o’inmu bisa qaddara suna koyarwa, su ke da ra’ayin a
koyar da Hausa cikin Turanci. Abin kunya, a tambaye su, ina wani aikin da suka
yi cikin Turanci da masu Turanci suka yaba? Babu. Ina gudummuwar da suka yi wa
Hausa da suke ci cikinta? Babu. Wa ya san da su a duniyar ilmin da suke doro?
Babu. Wannan shi Bahaushe ke cewa vatan baqatantan.
[27]
Akwai addinai na gargajiya a
kowane saqo na yankin Nijeriya, sai dai ba su da yawa. Haka kuma, ilmin addinin
Musulunci da Boko ya dushe haskensu. A taqaice, a yau, Nijeriya addinai biyu ne
manya kuma da su ake tafiyar da siyasar qasar – Musulunci da Kiristanci.
Mabiyansu sun yi yawa, sun fi ma’ilmanta, sun fi masu iko, sun fi ma’aikatan
hukuma, sun fi ‘yan siyasa, su ke hulxar diflomasiyya da qasashen waje a kan
takwarorinsu na addini.
[28]
Addinin Musulunci harshensa Larabci.
Addinin Kirista harshensa Turanci/Ingilishi. Waxannan harsuna duka Hausa
ta ci gabansu wajen addinan a fagen wa’azi da wallafe-wallafe da kafafen yaxa
labarai da hanyoyin sadarwa. Musulunci da waqe-waqen Hausa aka fara yekuwarsa.
Addinin Kirista, ‘yan Mishan da rubutun ajamin Hausa suka fara kiran magoya
baya. A yanzu, a iya samun babban Fada a addinin Kirista a Arewa da bai iya Turanci ba. Haka kuma, ana
iya samun masu wa’azin da ba su iya Larabci ba. Da me suke kira a ji su? Da
harshen Hausa.
[29]
Wangarawa suka fara lurar da Hausawa yadda za a
yi fashin baqaqen Larabci zuwa Hausa. A qasar Hausa, dukkanin littattafan
addini da Hausa ake koyar da su. Ilmukan Qur’ani da Hadisi da Nahawu da Luga da
Fiqihu da Shari’a duk ana karanto nassi da Larabci ana fashin baqinsa da Hausa.
Wannan fasahar ta agaza wa Hausa sosai wajen adana tsofaffin kalmominta da
dabarun rayuwar gargajiya. Ya kyautu a ce an fara juyar da tafsiran masana irin
su Nasiru Kabara da Abubakar Gumi da Xahiru Bauchi da Jafar Adam da Sidi
Attahiru Sakkwato da sauransu zuwa Hausar Boko da ajami.
[30]
Sheikh Nasiru Kabara ya fara
fassara hizo goma daga nan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya fassara gaba xaya.
Sheikh Nasiru Kabara ya fassara gaba xaya aka wallafa a Libya. Farfesa Bello
Sa’id da wasu Indiyawa sun yi fassara an wallafa a Indiya. Wasu malamai na Kano
da suka voye sunayensu sun fassara, an wallafa. An fara buga Juzu’i 10 na
Sheikh Jafar Adam. Wasu xalibai a Masar na tarar da su a Azhar a shekarar 2014
suna ta qoqarin fassarawa, sun yi nisa.
[31]
Sheikh Sanusi Gumbi ya fara
fassara wasu babuka na juzu’i na farko na Buhari an wallafa. Yanzu haka, mun
tattara fassarar marigayi Sheikh Abubakar Gumi ta Buhari muna neman masu
taimakawa a juyar da shi a rubuce, tuni mun fara. Jami’ar Bayero Kano, Sashen
Nazarin Addinin Musulunci, an ce sun kammala fassarar Buhari da Tirmizi
da Abu Dawuda da Ibn Maja da Muwaxxa da Baihaqi.
Sun sa xalibansu fassarawa madadin kundin BA a da ke ake yi.
[32]
An fasssara littafin Risala
da Iziyya da Ashamawi da Ta’alimu da Tuhatul
Hukkam da Qawa’idi da al-Ahlari da Ilmin Hadisi
da makamantansu.
[33]
Bayan fassarar Linjila ta
gaba xaya, akwai fassarar Tafsirin Linjila Afokirifa duk cikin Hausa.
Cikin Hausa kaxai aka yi wannan aiki a harsunan Nijeriya.
[34]
Ibrahim Yaro Yahaya, Hausa
A Rubuce, 2002, shafi na 251-254 ya
kawo littattafai xari da huɗu (104) da aka yi na addinin
Kirista cikin Hausa.
[35]
A fagen xaukaka addinin
Musulunci a duniya Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya karvi kyautar Sarki Faisal. A
vangaren Luga Sheikh Nasiru Kabara ne tauraron duniya. A fagen luguden Alqurani
da fashin baqinsa Sheikh Jafar Adam ne jagoran matasan Musulmin duniya.
[36]
Don qarin bayanin wannan, a
dubi Aliyu, S. A. “Christian Missionaries and Hausa Literature in Nigeria,
1840-1890 A Critical Evaluation”
in Kano
Studies, Vol. 1, No.1, BUK, 2000; da Ayandale,
E.A. “External
Relations with Europeans in the Nineteenth Century: Explorers, Missionaries and
Traders”, in Groundwork of
Nigerian History, 1980; da
Crampton, E. P. T. Christianity in Northern Nigeria, Gaskiya Corporation, Zaria, 1976; da kuma
Littattafan Baldi da Ibrahim Yaro Yahaya da aka yi bita duk sun zo da su da yawa.
[37]
Rubutun Ajami shi ne
tabbataccen rubutun Hausa da ya bazu a duniya. Da shi Mishan suka fara yaxa
manufofinsu. Domin qarin bayani a kan ajami a dubi, Sani Yusuf Birnin Tudu,
“Nazari kan Rubutun Ajami a Qasar Hausa” kundin digirin MA Jami’ar Usmanu Xanfodiyo,
Sakkwato, 1990.
[38]
Don qarin bayanin karatun
boko a dubi Isma’ila Tsiga, “A Century of Boko Education in Hausaland”, paper
presented at book presentation on Eight Decades of Hausa Masterpiece in Prose: Ruwan Bagaja in
Perspectives.
Katsina: Umaru Musa ‘Yar’adua University,
2014.
[39]
Don qarin bayanin samuwar
rubutun Hausa na gargajiya a dubi Aliyu M. Bunza, Rubutun Hausa:
Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa,
Lagos: Ibrash, 2002.
[40]
Don qarin bayanin rubutun
ajami a dubi, Sani Yusuf Birnin Tudu. 1990 an ambace shi a lamba ta 37.
[41]
Ikon garin-da-garin shi ne direct rule, irin wanda Turawan Mulkin Mallaka suka yi wa kudancin Nijeriya saboda
samun su cikin rashin kintsattsen shirin siyasar gudanar da mulki. A Arewacin
Nijeriya suka shimfixa mulkin indirect rule.
[42]
Wannan dabarar siyasar mulki
ita ce indirect
rule an sake wa sarakuna ragamar
shugabantar mutanensu a kan yaudara da azuzanci domin an mayar da su
jeka-na-yi-ka, sai an shirya tsari a ba su, su aiwatar.
[43]
Dabarar Turawa da qago adult education, wato “Yaqi da jahilci”, ita ce
kushe duk wani ilmi, da ba nasu ba. In dai iya rubutu da karatu ne ilmi, fiye
da qarni uku Hausawa na da shi gabanin bayyanar Turawa. A li’irabin “ilmi” da
UNESCO ta bayar, ilmi shi ne, iya rubutu da karatu, da koyar da su a kowane
harshe. Idan haka ne, cewa an kafa makarantun yaqi da jahilci a qasar Hausa cin
mutunci ne da cin amana da yaudara. Wato ilmin addinin Mishan shi ne ilmi, wani
ba shi ba jahilci ne. Rubutu da karatu da harufan Romanci da Turawa suka zo da
shi, shi ne ilmi. Rubutun Larabci da ajami da Musulunci ya zo da su jahilci ne.
Marigayi Alqali Haliru Binji ya tava qalubalantar wakilan UNESCO da aka turo a
Sakkwato bisa ga wannan hujjar da muka ambata. Da suka zo, ya rubuta takarda ga
iyalinsa cewa: “A zo da tabarmin zama da kayan rubutu maza-maza”. Ya rubuta
cikin ajami ya tura gida. Wanda aka aika ya zo da su duka. Suka tambaye shi,
iyalinsa na jin Larabci? Ya ce; “Ai da Hausar ajami na rubuta musu saqon”. Ya
ba su suka gani, ya gaya musu: “Wannan shi ne ilmi a wajenmu”.
[44]
An kafa makarantar boko ta
farko a Sakkwato a 1905.
[46] A Kano ita ce Makarantar Xanhausa.
[47]
Tabbacin wannan shi ne,
Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari Shugaban qasa a jamhuriyya ta biyu yana koyar
da ilmin qasa (Geography) ya mayar da shi waqa. Aka wallafa waqar a matsayin
littafi mai suna Waqar Nijeriya. Zaria: NNPC.
[48]
Na saurari wannan a hirar da
Shehu Gixaxawa ya yi da Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a cikin wani shiri na
gidan Talabijin na Rima, Sakkwato mai take: ‘Mazan Jiya’ wajajen shekarar
2012/2013. A bakin Shehu Shagari wannan maganar ta fito.
[49]
Abin ban sha’awa, wannan
tasirin ne ya sa hatta da Turawan da ake turowa ayyukan hukuma a Arewa suna
qoqarin koyar da fannonin aikinsu cikin Hausa. Wani Baturen Ingila masani
Safiyo (Survey) da ya zauni jahar Sakkwato a
garin Ka’oje ya buxe makarantar Safiyo ta farko a Nijeriya. Ya rubuta littafin
koyon Safiyo da Hausa ya kira shi Ilmin Safiyo.
Da shi yake koyar da duk wani ma’aikacin Safiyo da ya zo qarin ilmi a makarantar.
[50]
A xan namu tunani, Turawan
Mulkin Mallaka ba su tava kwasan kashinsu ga hannu ba, kamar yadda suka kwashe
shi a Arewacin Nijeiya da Hausawa ke da rinjaye ba. Irin hasarar da suka yi a
Satiru 1906 da yaqin Giginya - Sakkwato da Yaqin Burmi da Ningi da Kwantagora
da Yawuri da Busa ba qaramar annoba ba ce gare su. Haka kuma, sun tarar da
qasar Hausa da wayewar karatu da rubutu da tsarin shugabanci, irin nasu. Don
haka, idan suka yi sakacin ba harshen Hausa muhmmanci wata sabuwar zanga-zanga
ce suka tsira wa kansu. Tunaninsu na harshen Hausa na iya mamaye Afirka a yi
musu wani sabon tonon silili shi ya sa suka bai wa kowane lardi ya kafa jarida
da harshen lardinsa. Dabararsu ita ce, idan aka bari muka yi magana da murya
xaya, wa za su sake yaudara?
[51]
A xan binciken da na yi;
Turawa sun yi amfani da Hausawa wajen aikace-aikacen tsaronsu da leqen asiri.
Hausawa ake zuwa da su Ghana da Turai ana horar da su dabashirin tsaro da leqen
asiri. Su aka fara koya wa karatu da rubutu da Turanci. Su suka riga ‘yan
kudancin qasar samun fasahar karatu a rubutu ta ajami. Idan aka goyi bayan
Hausa, ajami zai ci nasara. Idan aka ci nasara, kamar an sake yayyafawa tutar
jihadi ruwa ne a qasar Hausa.
[52]
Jami’ar Ahmadu Bello Zariya;
Jami’ar Bayero, Kano; Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato; Jami’ar Jos; Jami’ar
Tarayya, Gusau; Jami’ar Maiduguri; Jami’ar Musulunci, Katsina; Police Academy,
Wudil.
[53]
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua,
Katsina; Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi; Jami’ar Jihar Yobe; Jami’ar Jihar
Bauchi; Jami’ar Jihar Jigawa, Kafin-Hausa; Jami’ar Jihar Oyo; Jami’ar Jihar
Kaduna, Kaduna; Jami’ar Jihar Taraba, Jalingo; Jami’ar Jihar Sakkwato,
Sakkwato; Jami’ar Jihar Adamawa, Mubi; Jami’ar Jihar Gwambe.
[54]
Federal College of Education,
Gusau; Federal College of Education, Zaria; Federal College of Education, Kano;
Federal College of Education, Katsina; Federal College of Education, Pankshin;
Federal College of Education, Kontagora; Federal College of Education, Katsina
Ala – Benue; Federal College of Education, Yamufo; Federal College of
Education, Ijanikin – Lagos; Federal College of Education, Abeokuta; Federal
College of Education, Adeyemi – Ondo; Federal College of Education (Special),
Oyo; Federal College of Education, Okene; Federal College of Education, Zuba.
[55]
Shehu Shagari College of
Education, Sokoto; Adamu Augie College of Education, Argungu; College of
Education, Maru; College of Education, Minna; College of Education, Dutsinma;
Sa’adatu Rima College of Education, Kumbotso; College of Education, Kwara;
College of Education, Ilorin; College of Education Ekere – Ekiti; College of
Education, Gumel – Jigawa; College of Education, Azare; College of Education,
Gashuwa; College of Education, Gindiri - Plateau State; College of Education,
Wakabiu – Maiduguri; College of Education, Hong –Adamawa; College of Education,
Zing - Taraba State.
[56]
Haliru Binji Polytechnic,
Sokoto; College of Preliminary Studies, Yawuri -Kebbi State ; College of Legal
and Islamic Studies, Misau; College of Islamic
and Legal Studies, Ringim; College of Legal Studies, Nguru; Bala Usman
College of Legal Studies, Daura.
[57]
Centre for Study of Nigerian
Languages and Folklore, BUK; Centre for Hausa Studies, UDUS; Oral Documentation
Unit, ABU; Center for Trans-Saharan Studies, UNIMAID.
[58]
Abin da nake son in nuna a
nan, daga qididdigar masana ilmin harsuna da tarihinsu a duniyarmu ta yau akwai
kimanin harsuna dubu shida zuwa dubu bakwai. A binciken SIL sun ce, harsunan
duniya dubu shida da xari tara da goma sha biyu ne (6,912) daga cikinsu kashi talatin,
wato dubu biyu da tas’in da biyu (2092) cikin Afirka suke. A nawa zakuxe, daga
cikin harsunan Afirka (2092) Nijeriya na da kimanin xari biyar (500) daga cikin
harsunan Nijeriya (500) Hausa ita ce kan takarda ga qasaita da bunqasa da jure
wa cutukan da ke kama harshe da murmuje wa daga kowace irin masassara. Don
qarin bayanin waxannan matsaloli a dubi, Maikuxi Qaraye, “Folklore as a
Vital Resource, for the Documentation of Endangered Languages”, paper, 2014; da
Thomas K. Adeyanju, “Understanding and Stemming the Tide of Language
Endangerment in Nigeria” paper 2014.
Sun yi hasashen martabar Hausa yadda na kalle shi a wannan batu. Harshen Hausa
ya riga ya yi allurar riga-kafin kowace iri cuta da ke kama harshe. Ya yi nisa
a ilmi. Ya mamaye kafafen yaxa labarai.
[59]
A da, muna da Jami’o’i uku
kawai. A yau 2014 Jami’o’i kawai muna da wajen ashirin (20) masu ba da digiri a
fannonin ilmin Hausa.
[60]
Daga cikin qasashen da aka yi
wa Mulkin Mallaka na Afirka, babu wadda harshenta na qasa ya yi wa ‘yan
damfaran Turai barazana kamar Hausa. Ita kaxai ta samu cin nasarar mamayar
Jami’o’i na Tarayya da Jaha da masu zaman kansu, ba a kai ruwa rana ba. Ta fi
kowane harshe manyan masana masu digirin PhD da kujerar Farfesa a Nijeriya.
[61]
Binciken babban digirin PhD na Hausa da al’ada aka fara a 1942, digirin PhD na harshe an soma shi a 1953 na adabi kuma a 1969.
Buqatar Turawan Mulkin fallasa ya sa nazarin harshe ya yawaita musamman bayan
yaqin duniya na biyu. Buqatarsu ta kasuwanci da tsaro da neman mazajen soja ga
yaqe-yaqen da duniya take ciki da yaxa addinin Mishan wuraren da suke ganin
Musulmi sun riga su ko sun mamaye ko sun kafa daula, su suka sa suke ba da
qarfi ga koyon harshe a karon farko.
[62]
Idan digiri xaya ke ga
malami, fannin da ya rubuta kundin digirin BA nan ne fagensa. Idan digirin MA
ne fannin kundinsa nan ne gijensa. Idan digirin PhD
ne vangaren kundinsa nan ne gonarsa. Wanda ba ya da digiri ko xaya, fannin da
ya fi ba da gudummuwarsa ita ce fagensa kamar irin su Malam Zarruk (Harshe),
Neil Skinner (Adabi), Abubakar Imam (Adabi).
[63]
A shekarar 2014 muna da 42.
[64]
A shekarar 2014 muna da 187.
[65]
A shekarar 2014 muna da 124.
[66]
A shekarar 2014 muna da 10.
[67]
A shekarar 2014 muna da 4.
[68]
A shekarar 2014 muna da 50.
[69]
A shekarar 2014 muna da 84.
[70]
Kasawar masana Hausa na qulla
zumuncin ilmi da Jami’o’in Afirka ya cutar da cigaban Hausa. A Masar, ana
karatun Hausa a Jami’ar Cairo da Azhar amma cikin Larabci. An ce a Jami’ar
Nijar za a fara, amma cikin Faransanci in kuwa da Hausa ne, wa ke gare su da
zai xauki xawainiyar babban digiri ga harshen da bai tava koya ba? Ya kyautu a
ce, an fara musayar malamai tsakaninmu da
Nijar da Ghana da Benin da Togo da Borkina da Gabon Da Aljeriya da Tunis
da Maroko da CAR da Habasha da sauransu. Yadda Hausa ta bazu a kafafen yaxa
labarai na duniya, ya kamata a ji ta a fagen ilmi haka.
[71]
Makaxa Narambaxa cewa ya yi:
Jagora: Maxi bai kai ga zuma ba
Yara: Kowal
lasa shi ka hwaxi
:Kwandon wake bai kai
ga damen gero ba.
Jagora: Xan akuya ko ya yi qahoni
Yara: Ya
san bai yi kamar rago ba.
Jagora: Duw wada xan sarki yaq qasura
Yara: Kak
ka raba shi da bawan Sarki.
Gindi: Gogarman Tudu jikan Sanda
:Maza su ji tsoron xan
mai Hausa.
[72]
Farfesa Abdulqadir Xangambo
ya yi takardar tunawa da gudummuwar Farfesa M. K. M. Galadanci da Farfesa I. Y.
Yahaya (Allah Ya jiqan su) ya yi mata take “Jigajigan Hausa: Gudummuwar Farfesa
M. K. M. Galadanci da Ibrahim Yaro Yahaya”, cikin ALGAITA Vol. 2.
No. 1. Nuwamba,
2002.
[73]
Tun farkon al’amari
nagartattun mutane suka assasa karatun Hausa. Masana harshen Turanci da Larabci
da Tarihi da Addini da Sojoji da ‘yan leqen asiri suka xaure mata gindi. Don
haka, tsawon qarni xaya da ta yi ana gogawa da ita a farfajiyar ilmi ba a tava
samun karatun zuqu ba daga digirin BA zuwa Farfesa ba. Gwanin ban sha’awa, ya
zuwa yau 2014, mutum uku kaxai ke da digirin fintinkau (First Class) a duniyar
qasar Hausa. Aminu Lawal Auta, BUK – 1983; da Ahmad Baba Tela, UNIMAID – 1984;
Abdurrahman Faruk, UMYUK - 2010.
[74]
A qa’idar ba da takardar
shaidar kowane mataki na karatun boko akan ce, an ba da ita ne a kan cancantar
xalibi da qwazon karatunsa da ladabinsa. Xaya duk aka rasa daga cikinsu digirin
bai zauna ba.
[75]
A Jami’o’in Tarayya da na
Jaha muna da: Harsunan Nijeriya,
CSNLF, BUK; Harshe
Sashen Harsunan Afirka da Al’adu, ABU; Xunxaye Sashen
Harsunan Nijeriya, UDUS; ALGAITA
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, BUK; HIMMA
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, UMYUK; Zauren Waqa,
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, UDUS; Kadaura, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, KASU (ba ta fito
ba).
[76]
A Kwalejin Tarayya muna da: Kwantagora
Journal of Languages and Literature.
(FCE); Journal
of Languages and Linguistics Inquiry,
School of Languages FCE, Katsina; WAZOBIA, Journal of Hausa Studies, FCE, Kano; ZUBA Journal of Hausa Studies, FCE, Zuba; OBUDU Journal of Languages
(OJOLA) FCE, Obudu; Huda-huda Journal of Languages Art and Social Sciences (JOLASS), FCE Okene; OYO Journal of
Languages and Linguistics
(OJOLAL) FCE, (Special) Oyo; KUNDI Journal
Federal College of Education, Kano.
[77]
A Kwalejojin ilmi na jihohi muna da: Minna Journal
of Languages and Literature
(MIJOLL); AMIMAI Journal
Umar Sulaiman COE, Gashuwa; GOKARAM Journal
Umar Sulaiman COE, Gashuwa; KABA Journal
Umar Sulaiman COE, Gashuwa; ZOBIAWA Journal of Department of Nigerian Languages ACE, Ondo; JAGORA
Journal of Languages Isa Kaita
College of Education Dutsinma; KONJOLLS Kwantagora Journal of
Languages and Literature,
Niger State; KANTA Journal of General Studies, Adamu Augie College of Education, Argungu - Kebbi
State; KABAI
Journal of Multidisciplinary Studies,
COE, Maru - Zamfara State; IKERE Journal of Languages,
COE, Ikere - Ekiti.
[78]
A makarantun fasaha da
kimiyya muna da: The Beam
Haliru Binji Polytechnic Sokoto; YAJAS Yauri Journal of Arts and Science, College of
Basic and Advance Studies, Yawuri, Kebbi State.
[79]
Fitattu daga cikinsu a gida
Nijeriya akwai: MALAM Journal of Language, Literature and Criticism, Department of Arabic, UDUS; XEGEL Journal of the faculty of Arts and Islamic Studies, UDUS; Studies in
Humanities, Journal of the Faculty of Arts and Social Sciences Complex, UDUS; AL-NAHDA
Journal of Islamic Heritage,
CIS, UDUS; FAIS Journal of Humanities, BUK; The Journal of
Islamic Sciences and Muslim Development, UDUS; AL-SAHWAH Islamic Journal,
Kaduna State University;
Minna
Journal of Educational Studies.;
Kusugu
Journal of Education TETFUND SUPPORTED; SARDAUNA
Journal of Multidisciplinary Studies.;
TAMBARI
Journal (COESU)
FCE, Kano.; FARFARU Journal of General Studies, COE, Sokoto.; West African Journal of Language,
Literature and Criticism
(WAJLLC), Bayero
University, Kano.
[80]
Yunqurin Bature ya kasa cin
nasarar tilastawa Hausawan qasar Hausa Turanci. Babbar riga da hula ta gagare
shi kora ga Hausawa ‘yan boko. Ya kasa cin nasarar tabbatar da wajabcin auren
mata xaya ga ‘yan boko. A kundin tarihi waxanda suka fara rubutu da Hausar boko
Durugu da Abbega da aka kai Turai cikin matsananciyar qurciya a wajajen (1850)
da Abbega ya dawo gida a wajajen 1912 ya
koma ga al’adunsa da addininsa na Musulunci Allah gagara misali, a dubi Mamadou
Di’awara, Studien zur Kulturkunde 125 Heinrich Barth et l’Afrique KOLIN, 2005, shafi na 130 - 131.
[81]
Masana a fannin Turanci sun
mutunta Hausa a rubuce-rubucen kundayensu na BA da MA da PhD. Misali a Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato, Farfesa
Bello Bada ya rubuta PhD a kan Karin Magana, Farfesa Malami Buba ya rubutu PhD
a kan Nahawun
Hausa, Farfesa
Asabe Kabir ta rubuta PhD a kan Tatsuniya. Dr. Aminu Mode ya rubuta PhD a kan Kirari,
Dr. Abubakar ya rubuta PhD a kan Nahawun Hausa. Dr. Baba Waziri ya rubuta PhD a kan Nahawun Hausa,
Dr. Ibrahim Awwal ya rubuta PhD a kan Nahawun Hausa, Dr. Kabir Madaki ya rubuta PhD a kan Nahawun Hausa.
Wannan misali a Jami’a xaya ne kawai.
[82]
Bari in jinjinawa malamin
malaman harshen Hausa a fuskar nahawu da ilmin harsuna Farfesa Thomas K.
Adeyenju da har yanzu bai iya magana da harshensa na gado ba, domin bai iya shi
ba Hausa ya iya. Su ne masanan farko da suka yi PhD
Hausa tare da Farfesa M. K. M. Galadanci, a 1967/68. Irin gudummuwar Farfesa
Mahdi Adamu ga taskace tarihi da al’adun Bahaushe dole a jinjina masa.
[83]
Aikace-aikacen kundayen
qanana da manyan digirori da takardun qara wa juna sani a fannin Turanci na
Jami’ar Bayero, Kano da Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya da Jami’ar Usmanu
Xanfodiyo, Sakkwato da sauran jami’o’in da ke tasowa a Arewacin Nijeriya Hausa
ta riga ta karve tuta. To! Shi ya sa nake ganin, lokaci ya yi na mu zauna mu
haxa kai mu zama abu xaya, a saka mana sunan da ya dace, kowa ya hau kan
mazhabarsa.
[84]
A taqaice, masu nazarin ilmin
harsuna (Linguistics) na jami’o’in arewa da kuma Hausawa da suke zuwa wasu
jami’o’in duniya da Hausa suke kundace
manyan digirorinsu.
[85]
A jami’o’in Sudan da Masar da
nan gida Nijeriya Hausawa da ke karanta Larabci sun ba da gudummuwa gagaruma a
rubuce-rubucen kundayen digirin MA da PhD wajen amfani da Hausa a matsayin
harshen gwaji. Misali Dr. Abdurrahman Adoro ya rubuta PhD a Jami’ar Undurman, Sudan kan littafin Magana Jari Ce; abokin aikinsa Dr. Mustapha M.
Yusuf ya rubuta PhD nasa a kan “Kwatancin Amsa Kaman
Larabci da na Hausa”, a Jami’ar Afriqiyya, Sudan, ga su nan dai.
[86]
Manyan masananmu a fannin
Islamic Studies irin su Farfesa Sani Zaharaddin da Farfesa Abubakar Gwandu da Farfesa
Umar Labxo da Farfesa Ahmed Moyi Gada da Farfesa Jafar Makau Qaura da Farfesa
Abdullahi Sifawa kundayen digirinsu na PhD a kan al’amurran addini da suka
wakana qasar Hausa ne, ko na malanta ko koyarwa ko rubuce-rubuce ko jihadi ko
wa’azi ga su nan dai.
[87]
Yadda ayyukan masu tarihi
suka taka rawa cikin karatun Hausa abin yabawa ne. ayyukan su Bala Usman, Farfesa
Mahdi Adamu, Dr. Garba Nadama Bello Alqali, Farfesa Tibendarana, Farfesa
Balogun, Farfesa Ahmad Baqo, Farfesa Aminu ‘Yanxaki, Farfesa Hamza Maishanu,
Farfesa Ibrahim Jumare, Dr. Lawal Gwadabe da Dr. Tsafe da Dr. Sabo Albasu da
sauransu da qasar Hausa da Hausawa suka yi bara ga ayyukan digirorinsu da
wallafe-walafensu da rubuce-rubucensu na ilmi. Fannin Tarihi wani makami ne
kawai gare su na hasko bagiren da suke son su nazarta na Bahaushe da qasar da
yake zaune ciki.
[88]
Daga cikin ‘yan ayyukan da na
ga sun yi kama da haka akwai PhD Abdullahi Sokoto a kan zangazangar
Satiru da Satirawa na 1906. An yi PhD uku a kan amfanonin Madatsar Ruwa
ta Bakalori da ke Zamfara. Akwai digirorin MA da PhD
da aka yi a kan karuwanci a qasar Hausa da magungunan gargajiyar Bahaushe da
yawa. Ban ce, sun fita da’irar fagen nazarinsu ba, amma karatun Hausa ne, domin
bisa ga Hausa da Hausawa aka kalli abubuwa, da an xebe Hausa ciki aikin ba zai
kai gayya ba. Wannan ce ta tabbatar da kasancewarsa gudummuwa ga karatun Hausa.
[89]
Masu ilmin siyasa sun yi
ayyuka masu ma’ana a kan tsarin mulkin Hausawa da siyasar demokraxiyya da
waqe-waqen siyasa da gwarajen siyasa a qasar Hausa.
[90]
Daga cikin misalan akwai PhD na Malam Alero a Sashen Economics da ya yi a kan
Adashin Bahaushe.
[91]
A ganin Bahaushe, magani duk
bokanci ne. Ba wai yadda na bayan fage ke kallon bokanci da idon addini ko idon
gargajiya ba. A tunanin Bahaushe, sana’ar bayar da magani da warkarwa ta kowace
fuska sunanta “bokanci”. Dalilinsa ke nan na cewa, likita bokan Turai, watau
bokan qasar Turawa.
[92]
Asirin “gaba” shi ne asiri da
ake yi mutum ya tashi sama kamar tsuntsu. An yi wani shahararren maharbi a
qasar Nijar a garin Jinju mai suna “Audu Gaba”. Da asiri ake yi masa kirari,
Audu Gaba a qarshen rayuwarsa ya koma Bunza da zama a unguwar Jugan Biri nan
Allah Ya yi rasuwarsa a wajajen shekarar 1968/70 ya bar baya da yawa.
[93]
Ai qabilar Haiti suna da
wannan tsafin kuma har gobe da tsafin America ke mutunta su. Don qarin bayani a dubi Aliyu M. Bunza,
“Hayaqi Fid Da Na Kogo: Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa” MA, BUK, 1990.
[94]
Don qarin bayani a kan qira a
dubi, Philip, J. Jaggar, The Blacksmiths of Kano a Study in Tradition Innovation and
Entrepreneurship in the Twentieth Century, KOLIN, 1994.
[95]
An daxe ana rubuce-rubuce
cikin Hausa tun qarni na sha takwas gabanin boko ya bayyana a Nijeriya.
[96]
Na farko dai, su yi kusa ga
juna. Na biyu, a saka darussan da suka dace da bokon qarninmu. Na uku, a riqa
sara ana duban bakin gatari.
[97]
Mu sake bitar yadda za mu
nagartar da kundayen digirorin BA da MA da PhD.
A halin yanzu, kashi ya kusa ya game, da wankiya da kasala da rashin ta cewa,
da yin halin hankaka ga ayyukan mutane a babban digiri dole a dube shi sosai.
[98]
Yana da kyau a ce, muna da
wata matsaya ta karatun MA da PhD ta yadda xalibanmu za su amfana da
mu sosai mu amfana da su. Gabanin mu yarda a rubuta kundin MA da MPhil da PhD sai mun tabbata babu irinsa a cikin kowane harshe a
kowane fannin karatu.
[99]
Yau, fitattun qungyoyin
mawaqan Fada da Maza da Ban dariya da Jama’a da Sana’a sun kau, sai dai waqoqin
a gidajen Rediyo. Har yanzu, ban da Shata ba a yi PhD a kan ko xaya ba. Wane adabi ya fi na waqoqin baka
tsofaffi ga mai karatun adabin Hausa?
[100] Marubuta waqoqin da aka assasa
karatun Hausa da nazarin waqoqinsu, irin su Aliyu Namangi da Aqilu Aliyu da
Yusuf Kantu da Na’ibi Sulaiman Wali da Alqali Bello Gixaxawa da Maikaturu da
Garba Gwandu da Wazirin Gwandu da Aliyu Xansidi da Shekara Sa’adu da Lawal
Kwantagora da Mu’azu Haxeja da Kaftin Suru da sauransu, ba su a duniya.
[101] Ya zuwa yau, kan sana’ar Wanzanci
da Kamun kifi kaxai aka yi aikin PhD, sauran ko na digirin MA ba su
samu ba. Yaya aka yi haka? Ina muka dosa? Sirrin kalmomin harshenmu na cikin
tsofaffin sana’o’inmu. Idan muka bari suka mutu mun kashe Hausa.
No comments:
Post a Comment