This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue...
Showing posts with label HAUSA. Show all posts
Showing posts with label HAUSA. Show all posts
Tuesday, November 15, 2022
Tuesday, August 16, 2022
Ba A Wane Bakin Banza: Gurbin Daular Gobir Da Gobirawa A Farfajiyar Sudaniyya
Abu-Ubaida Sani
August 16, 2022
0

Gobir tsohuwar Daula ce da ta shiga gwagwarmaya da daulolin duniyar Sudaniyya. Burin wannan bincike ƙyallaro wasu daga cikin dalilan da suka ɗaga Daular Gobir da Gobirawa sama ga sauran dauloli. An yi garkuwa da fitattun ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba tare da taimakon yawon rangadi da tattaunawa da dafa kafaɗar adabin baka da rubutacce. Binciken ya gano cewa, Daular Gobir cin gashin kanta take yi kuma Bahaushiyar Daula ce. Bugu da ƙari,...
Wednesday, September 29, 2021
Ɗiyan Sarauta A Tafashen Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Abu-Ubaida Sani
September 29, 2021
0

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun na daga cikin fitattun makaɗan fada da suka makaro a ƙasar Hausa. Binciken wannan takarda ya ɗora shi a cikin rukunin makaɗan sarauta bisa taliyon salsalar waƙoƙin gidansu da ya gada, ya ɗora a kai. Binciken takarda ya tsaya a kan jigon “zambo”, ko a cikin jigon ya taƙaita ga “zambon ɗiyan sarauta”. An saurari waƙoƙin Ɗanƙwairo da yawa na sarauta, an karanta wasu da aka taskace, an yi amfani da mataimaka...
Tuesday, September 22, 2020
Zamfarawa a Diwanin Narambaɗa
Abu-Ubaida Sani
September 22, 2020
0

Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa mai taken: Zamfara Kingdom: Social and Political Transformation from 14th Centuary to Date. Organized by Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, 25th – 28th February, 2020, at Usmanu Danfodiyo University Auditorium, Sok...
Monday, October 14, 2019
Hausa Da Hausawa A Duniyar Кarni Na Ashirin Da Ɗaya (Amsa Kiran Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) Ga Ranar Hausa Ta Duniya – Litinin 26 Ogusta, 2019)
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Mutanen da ke magana da “Hausa” a matsayin harshen
gado uwa da uba, kaka da kakanni su ne ‘Hausawa’.
Samun tussan asalinsu na tun fil azal a garuruwan da Hausawa suka kafa, wata
hujja ce ta zama Bahaushe. “Bahaushe” tilo ne na mai magana da Hausa a matsayin
harshen gado, “Hausawa” jam’i ne na “Bahaushe”. A binciken magabatanmu,
‘Bahaushe’ shi n...
Tags
# HAUSA
Continue Reading
Gaskiya A Кi Ki, A So Ki
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta wannan waƙa
ranar 8 ga watan Ogusta, shekara ta 2019. Tana da adadin baituka arba’in da
biyu (42). Ta kasance ‘yar ƙwar huɗ...
Tsaro A Nijeriyar Кarninmu: Lokacin Abu A Yi Shi
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Tunanin
Bahaushe a kan tsaro ya shafi tsaron lafiyar jiki da rayuwar da ke ɗawainiya da
ita; tsaron ƙasa da tattalin arzikinta; wadatuwar abinci da ayyukan yi ga masu
tsaro da ƙasar da ake ɗawainiyar tsarewa. Ke nan, tunanin Bahaushe na faɗar ‘tsaron kaya ya fi ban cigiya’, ya
tabbatar da kasancewar tsaro makamin farko a rayuwar ɗan Adam. A fashin baƙin
tsaro za mu ce, shi ne, samun walwala da sakewa da more wa ƙasa ga ɗan ƙasa, da
samun cikakkiyar...
Wane Ne Narambaxa? Ibrahim Narambaxa Buhari Maidangwale Abdulkadir Tubali (1890-1963)
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
‘Narambaɗa’ laƙabi ne
da ake yi masa ga karyar farautarsa da ya yi wa suna Rambaɗa. An haife shi a garin Tubali
shekarar 1890. Sunansa na yanka Ibrahimu, sunan mahaifinsa Buhari Maidangwale,
sunan kakansa Abdulƙadir, sunan
mahaifiyarsa Riba.[1]
Sunan kakarsa mace Binta. Mahaifinsa Babarbare ne daga ƙasar
Nijar, mahaifiyarsa mutunniyar Badarawa ce gidan Sarkin Makaɗa Ɗangwamna.
Don haka, Naramba...
Kakkaɓan Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar Labɗo
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Asalin
Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta na asali ƙabilanci.
A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa
bayi, don haka a ƙasarsu
aka fara yaga wasiƙar
Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa, a shiga
rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn Saba’
suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da musibar
Karbala abin kula n...
Wurin Da Babu Ƙasa Nan Ake Gardamar Kokuwa (Sharhin Littafin: Da ‘Yan Nijeriya da Buhun Gero Wa Ya Fi Yawa?)
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Hausawa
na cewa: “Komi ya ɓace maza ka biɗo
shi”. Babban tunaninsu a kan haka shi ne, wuyar aiki ba a fara ba. A kowane
lokaci mutane ke jayayya ana buƙatar raba gardama. Idan sa-in-sa ya
yawaita, gaskiya ce ba ta bayyana ba. Da ta leƙo, ita ce raba
gardama. Labarin masu yunƙurin fayyace da buhun gero da ‘yan
Nijeriya wa ya fi yawa, ya bice duniyar kafafen yaɗa
labarai na BBC da ƁOA da RFI da jaridun ƙasa da kafafen
yaɗa
labarai na jihohi. Da masoyansu,...
Ruwa Na Ƙasa Sai Ga Wanda Bai Tona Ba (Hisabin Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas Azare)
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Tun fil azal
karambanin leƙo abin da ya faku Bahaushe na kiransa
duba. A wata fassara idan ta shafi amfanin da wuri ana ce masa “arwa”. Bayyanar
Musulunci da wasu malamai suka durmuya ciki, a zauna, a harɗe, a share ƙasa, a
goge, ya sa ake yi masa suna da “Bugun ƙasa”. A
waƙar da muke nazari Alhaji Shata ya yi
amfani da “duba”. Ta kowace fuska aka yi karambanin gano gobe, ta carbi ce, ko ta
taurari, ko ta bugun ƙasa, ko
ta hisabi ko ta duban motsin...
Kunya Ginshiƙin Tsaron Ƙasa Da Bunƙasarta
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Kunyar
da ke tsakanin yara da manya ita ta wanzar da zaman siyasar
shugabancin ƙasar
Hausa ta fi kowace biyayya tsakanin masu mulki da moro. Da Musulunci ya zo, kunyar ta faɗaɗa
tsakanin malamai da ɗalibai.
Tsare wannan kunyar ya hana wanzuwar yi wa masu iko tawaye da zanga-zanga, ya
toshe rigingimu irin na addini tsakanin mabiya da shugaba ko malamai. Rashin
kunya ne yin sa-in-sa da shugaba ko malam...
Muhimmancin Haɗin Kai Ga Duban Watan Ramalana
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
0
Umurnin
da Manzo (SAW) ya ba Bilal na ya yi sanarwa ga ganin watan da aka shaida masa
wata hujja ce ta tabbatar da hukuma ke da ikon sanarwa na ganin wata. Waɗanda suka zo wa Sayyidina
Umar bakinsu buɗe ranar da yake azumi da jama’arsa a matsayinsa
na Sarkin Musulmi, ya tambaye su, suka ce wata suka gani, wata hujja ce da ta
kore jiran sanarwa ga Muminai idan sun yi ido huɗu
da wata. Matsalar da ke rarraba muna kai a nan ita ce, samun sanarwa...
Tags
# HAUSA
Continue Reading
Gurbin Harshen Fashin Baƙi Ga Mai Tafsiri
Abu-Ubaida Sani
October 14, 2019
1
Addinin Musulunci
ya yi fiye da shekaru aru-aru da leƙo
Afirka idan aka yi la’akari da ɓullar
addinin a Makka da tarihin Hijira ta farko da ta biyu[1]. A
hasashen tarihi, daulolin ƙasar
Hausa maƙil suke da mutane a zamanin da Musulunci
ya bayyana a duniya. Tarihin yadda ya
shigo ƙasar Hausa abin kirdado ne tsakanin Daular
Borno da Daular Mali da Daulolin Larabawan Sahara da kuma ɗaiɗaikun ‘yan kasuw...
Thursday, January 10, 2019
Don Me Ake Karatun Hausa?
Abu-Ubaida Sani
January 10, 2019
0
Bisa
ga al’adar ɗaliban harshen,
ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe
tarkakken nazarin da ɗalibi zai
ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi
in yi bara da Hausa.[1]
Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[2] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai
harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu
da neman shahara a ciki. A ganina,...
Kuka A Faifan Nazari: Laluben Diddigin Bahaushen Kuka Da Ƙunshiyar Lafazinsa
Abu-Ubaida Sani
January 10, 2019
0
A
iya sanina, wannan ɗan
bincike sabo ne, saboda rashin samun wani da ya gabace shi a fagen nazarin
Hausa. Duk da haka, abin da aka gina bincike a kansa “kuka” ya girmi duk wani
mai bincike da zai yi bincike a kansa. Tunanin kowane mai tunani, ba zai fice
da’irar al’adarsa da adabinsa da aka gina cikin harshen da yake rayuwa da shi.
Sanin haka ya sa na gayyato ƙwararrun
mawaƙan Hausa
(20) [14 na baka, 6 marubuta], na sarrafa ɗiyan
waƙoƙinsu (34). Cikin...
Wednesday, January 9, 2019
Bitar Karatun Hausa A Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙrn. 21): (Wurin Da Babu Ƙasa Ake Gardamar Kokuwa)
Abu-Ubaida Sani
January 09, 2019
0
The paper is a historical review of Hausa studies in Nigerian
academia. In the struggle, relevant related literatures were critically examined
to justify the dare need of an updated progress report. In this study, an advanced
Hausa study is the desired target to conjugate Hausa on the rating scale of
Nigerian academic standard. Similarly, tertiary institutions, Universities and
research centers handling Hausa academic Activities are the umbilical cord...
Wednesday, January 2, 2019
Wane Ne 'Dan Ta’adda?sava
Abu-Ubaida Sani
January 02, 2019
0
Gajeren tunanin da ke ga ɗan Adam shi ya sa
Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan,
mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya saɓa mata. Wannan dalili ne
ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke yi, a koyaushe
gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a
nan shi ne , ƙoƙarin dangantawa wata al’umma da ke
wata...
Bugun Gaba (Salon A San Ni, A Ji Ni, A Gane Ni Ne Wane)
Abu-Ubaida Sani
January 02, 2019
0
Maƙasudin wannan xan bincike shi ne, yi
wa wasu salailan adabi sunan da ya dace da su domin ƙara faxaxa bincike da nazari. Nazarin
ya yi ƙoƙarin
tabbatar da samuwar “Salon Bugun Gaba” cikin kowane sashe na adabin Bahaushe.
An tsara aikin cikin manyan sassa tara (9), ƙananan
sassa goma sha xaya (11). An ziyarci makaxan baka (8), marubuta waƙoƙi
huxu (4), marubuci xaya (1) domin a tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba. An
sarrafa karin magana (3), xiyan...
Gurbin Sarkin Musulmi A Ganin Watan Azumi
Abu-Ubaida Sani
January 02, 2019
1
Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin halittun da ba
su ƙidayuwa ga wani bawa daga cikin bayinSa. Ya ƙago
sammai ya ƙawata (ta duniyarmu) da hasken taurari domin
amfaninmu. Ya ba mu rana da wata domin daidaita ibadojinmu gwargwadon savawarsu
a duniyarmu. Burina a wannan ‘yar takarda shi ne, lalubo wasu matsalolin ganin
watan Ramalana da irin gurbin da shari’armu ta yi wa Sarkin Musulmi na kowace ƙasa
ta Musulmi a ciki. Wannan xan yunƙuri an yi shi...