Tunanin
Bahaushe a kan tsaro ya shafi tsaron lafiyar jiki da rayuwar da ke ɗawainiya da
ita; tsaron ƙasa da tattalin arzikinta; wadatuwar abinci da ayyukan yi ga masu
tsaro da ƙasar da ake ɗawainiyar tsarewa. Ke nan, tunanin Bahaushe na faɗar ‘tsaron kaya ya fi ban cigiya’, ya
tabbatar da kasancewar tsaro makamin farko a rayuwar ɗan Adam. A fashin baƙin
tsaro za mu ce, shi ne, samun walwala da sakewa da more wa ƙasa ga ɗan ƙasa, da
samun cikakkiyar natsuwa da za ta gargaɗi kowace irin barazana da fargaba da
tashin-tashina ga ‘yan ƙasa da baƙin da suka baƙunce ta. Samun wannan cikakken
aminci shi ne tsaro ga ƙasa.
Tsaro
A Nijeriyar Кarninmu: Lokacin Abu A Yi Shi
Aliyu Muhammad Bunza
Professor of African Culture (Hausa)
Faculty of Humanities and Education
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau
Zamfara State
Email: mabunza@yahoo.com
Tel: 0803 431 6508
Gabatarwa:
Kishin ƙasa a addinance shi ne, son
abin da Allah ke so ga bayinSa da ƙin dukkanin abin da Ya hane su. A al’adance
shi ne, son ƙasar haihuwa da ƙaunar cigabanta.
A tsarin mulkinmu yakan zamo, bin dokokin ƙasa sau da ƙafa da tsayin
dakan kare martabobinta. A cikin tsarin kishin ƙasa son ƙasa shi ne na farko, abin da duk ya biyo baya cikon sunna ne
makaho da waiwaye. A duniyar mutane, babu ƙasar da za ta samu nagartaccen tsaro
face jama’ar da ke ciki na sonta da son ‘ya’yanta da son zama a cikinta na
din-din-din. Wannan shi ne tushen tsaro, idan aka rasa shi, ba a yi komai ba an
raki baƙo ya dawo.
Mene Ne Tsaro?
Tunanin Bahaushe a kan tsaro ya shafi
tsaron lafiyar jiki da rayuwar da ke ɗawainiya da ita; tsaron ƙasa da tattalin
arzikinta; wadatuwar abinci da ayyukan yi ga masu tsaro da ƙasar da ake ɗawainiyar
tsarewa. Ke nan, tunanin Bahaushe na faɗar ‘tsaron
kaya ya fi ban cigiya’, ya tabbatar da kasancewar tsaro makamin farko a rayuwar
ɗan Adam. A fashin baƙin tsaro za mu ce, shi ne, samun walwala da sakewa da
more wa ƙasa ga ɗan ƙasa, da samun cikakkiyar natsuwa da za ta gargaɗi kowace
irin barazana da fargaba da tashin-tashina ga ‘yan ƙasa da baƙin da suka
baƙunce ta. Samun wannan cikakken aminci shi ne tsaro ga ƙasa. A duniyar ƙarninmu, babu ƙasar da ta hau wannan
mataki, domin duk ƙasar da aka ɗora kan wannan mataki za a ga kowane bakin wuta
da irin nasa hayaƙi.
Mene Ne Rashin
Tsaro?
A kowane wurin tsaro ya kasa samun
masauki, rashin tsaro ya kore shi. A duniyar ƙarninmu, babu ƙasar da ba ta yaƙi
da rashin tsaro, domin babu ƙasar da ke da cikakken tsaro na ƙarshe a duniyar
mutane. Idan muka harari ma’anar tsaro, za mu ce, rashin tsaro shi ne:
Wanzuwar yaƙe-yaƙe
da ta’addanci a ƙasa. Rugujerwar dokoki da zai ba da tazarar aikata manya da
ƙananan laifuka. Cin hanci da rashawa da ke rusa dokoki da masu zartar da su. Кarancin
abinci da mamayar yunwa a ƙasa, cututtuka da mace-mace su hauhawa. Rashin
nagartaccen ilimi ga matasa da yawaitar takkwallan magabata, dulunduniya ke
nan, makaho ya yi wa makaho jagora, gorar ta fi su gani. Tashin-tashinar
siyasa, addini, ƙabilanci, ɓangaranci, wanda ya fi annoba gaggawan rusa ƙasa.
Dawwamammen talauci da zai kore kunya da mutunci da sanin ya kamata a idon
mutane, wanda zai haifar da komai ta banjama, banjam! Fajirran masu mulki da
shaƙiyan talakawa, ya kasance, gaba kura baya sayaki. Bayyanar makwaɗaitan
shugabannin addini da makaftattun mabiya, aljanna gafara wuta salamu alaikum.
Rashin tausayi da son kai ga zukatan ‘yan ƙasa, kowa kansa kawai ya sani, wani
ba shi ba oho! Kowa ya ɗebo da zafi, bakinsa.
Waɗannan abubuwa (11) na rairayo su a
fashin baƙin tsaro domin su fito da ma’anar rashin
tsaro. Idan dai haka rashin tsaro yake, wa ke da haƙƙin rashin tsaro? Babu
wai, lokaci ya yi na a bugi garwa balbelu su tashi a samu inuwar gincirawa
hankali ya kwanta. Idan mun aminta da cewa, abubuwan nan (11) da muka lisafa su
ne rashin tsaro; idan sun kau, an samu tsaro, to za mu ce, tsaro dai a tunanin
wannan bincike a Nijeriyarmu ta yau shi ne:
Kurar Gardi:
An ce wai, a tatsuniyar Bahaushe,
Gardi ne ya je fada da kura cikin takunkuminta da igiya ya ɗaure da kwankwasonta.
Fada ta fito tana kallon yadda Gardi ke wasa da kura, ga shi ya sha layu da ɗamara
da kambuna na tsarin jikinsa a matsayin tsaro.
makaɗi na danna tambura, ‘yan kallo na sake jiki sun samu cikakken tsaro ga
kura daga Gardi. Sarki da ‘yan majalisa a sahun gaba ana kallon wasa. Halinka
da matsalar tsaro, cikin wasa da kura
da tumulli da ita, ashe takunkuminta ya kwance! Gardi bai ankara ba. Da ya ahumo,
ya ga haƙoran kura jajir a waje, sai ya ce: “A daina kiɗa tambura”, ya ja baya
ya yi tsaye zugum! Da aka ɗan yi rata, ba a ga Gardi ya ci gaba da wasa ba, sai
Sarki ya ce: “Sarkin Gardi me ake ciki?” Gardi ya ce: “Allah ya jima da ran
sarki, yau kurar ta kowa ce, domin ‘yan dubarunmu na gado sun ƙare saura ɗaya.”
Sarki ya fahimci abin da ke faruwa, amma ya ƙara tambaya: “Wace dabara ce ta
rage?” Sarkin Gardi ya ce: “Ga ta Allah ya jima da ranka”, sai ya laɓaɓa ya
sulale ya ruga abinsa, ya bar kura da igiya a kwankwaso da baki buɗe. Ala
tilas, Fada da ‘yan kallo da makaɗan Gardi suka taya shi gadon gidansu. A
ganina, cikin wannan halin shugabanninmu suka tarar da Nijeriyarmu ta yau. Sun
tarar da kowa ya gudu, yanzu suke kiran jama’a su dawo. Makaɗa Narambaɗa na
tare da ni a wurin da yake cewa:
Jagora: Yau mai ashararu ya kaɗe.
Yara: Duniya ta yi mai fashi,
:Babu zama garai, zaman
fitina yat tayas,
:Ya san ba a ƙwarjini ga
mutanen Hausa,
:Kowac ce shina iyawa ga
hilin nan,
:Sai ya ƙetare gidanai ba ban
kwana.
Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa,
:Baban
Dodo ba a tamma da batun banza.
Kasancewar tsaron ƙasa haƙƙin kowa da
kowa ne, in ya taɓarɓare ba wuri ɗaya ke da laifi ba, ya zama Kurar Gardi, in dai kowa ya ba da
gudunmuwarsa, in ko kowa ya hau dugadugansa. Ina da ra’ayin kowa ya ba da
gudunmuwarsa domin ƙasa tamu ce, ba mu da wata ƙasa ba ita ba. Bisa ga ra’ayin
Bahaushe da ke cewa: “Na gaba idon na baya”. Na so in fara duba hukuma.
Matsayin Hukuma:
Hukuma ita ce halastacciyar gwamnati
da aka kafa bisa ga tsarin dokokin yi wa ƙasa da ‘yan ƙasa hidima, da kare mutuncinsu
da rayukansu da arzikinsu. Ita ke da halastattun makamai na zuwa artabu da kare
ƙasa da zartar da hukunci da murƙushe ta’addanci da tawaye da zangazanga da
hare-haren maƙiya. Abin so a nan shi ne, dole a tanadi wadatattun masu tsare doka;
da ingantattun masu artabu; da wadatattun
makaman artabu; da amintattun masu zartar da hukunci; da natsattsun masu jewaɗin kawo mata rahoton ƙasa; da wadataccen arzikin da zai biya
su albashi da yi musu hidima.
Babbar matsalar ƙasarmu ita ce, rashin ƙwararrun wakilan tsaro da ƙarancin
makaman tanadin tsaro. Faɗin farfajiyar ƙasarmu ya yi wa tanadin tsaronmu rata,
idan an rufe kusurwar gabas, ta yamma ta buɗe, idan an rufe ta arewa, ta kudu
ta ba da tazara. Babu hukumar da za ta ci nasarar tabbatar da tsaro a ƙasarta sai
ta zage damtse wajen tabbatar da:
i.
Yaƙi da cin hanci da
satar dukiyar gwamnati ba sani ba sabo.
ii.
Zartar da hukuncin ƙasa a
kan kowa ya faɗa komai matsayinsa.
iii.
Samar da aikin yi ga ‘yan
ƙasa da kashe zaman banza mai haddasa aikin banza.
iv.
Tanadin hanyoyin samar da
wadataccen abinci mai gina jiki da ba da ƙoshin lafiya domin kare ‘yan ƙasa
daga cututtuka da ta’adin yunwa. Yin haka, rigakafi ne ga annoba.
v.
Nagartaccen ilimi ga ‘yan
ƙasa da zai sanya su kishin ƙasarsu da son jama’arta da ciyar da ita gaba.
Кasar da duk ta yi arzikin tsayar da
dugaduganta kan waɗannan abubuwa biyar, sauran matsalolin rashin tsaro za ta yi
ban kwana da su. Hukuma ba dodo ce ba, ba kuma aljana ce ba, sai waɗanda ake
jagoranta sun ba da cikakken haɗin kai, sannan zaman lafiya zai wanzu a
ƙasarsu.
Ni da Kai da Ku da
Su da Mu:
A cikin sha’anin tsaro, dole kowa ya
sa hannu domin hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Kada mu kuskura bambancin
addinimu da harshenmu da siyasarmu na nahiyoyinmu da matsayinmu da buƙatunmu su
dagula tsaron ƙasarmu, zaman lafiya ya gagare mu. Mu sa natsuwa mu duba,
sace-sace, fashi da makami, satar mutane da garkuwa da su a yi jingar fansa,
damfara, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, fyaɗe, liwaɗi da maɗigo, tsafe-tsafe da
aƙidojin ta’addanci ba sakacin gwamnati ba ne, namu ne! Sakacin gwamnati shi ne
ƙin hukunta mai laifi idan laifinsa ya tabbata. Wa ya sa ya aikata laifi? Don
me ya aikata laifin? Ruwansa! Ba gwamnati za a tambaya ba, shi za a tambaya.
Tsananin bala’in rashin tsaro a
ƙasarmu yau ya kai ma’aikatan da gwamnati ta ba amanar tsaro, wasu da hannunsu
cikin dagula tsaron. Wasau ma’aikatan gwamnati da ke cin gajiyar ta, su ke yi
wa tsaro zagon ƙasa. Akwai jagororin da ba su tsira cikin ta’asar ba. Wasu
sarakunan gargajiya da hakimai da su ake game baki a sace talakawa a kashe su.
Marasa kishi mazauna gari da zauna gari banza, su ne ‘yan rahoton ‘yan ta’adda.
‘Yan uwanmu na zaman gari da unguwa, ko na sana’a, ko ‘yan uwanmu na jini su ne
‘yan koren ‘yan ta’adda da ke kashe mu. Takkwallan ‘yan siyasarmu da wagilan
magoya bayansu, sun ɗauki ta’addanci wani sabon salon siyasa, don haka suke
amfani da ta’addanci domin kashe abokan adawa. ‘Ya’ya ke game baki da ‘yan
ta’adda a yi wa mahaifansu ta’addanci, a ci gajiya tare da su. Mata ke ƙulla wa
mazajensu makirci a kashe su, su gaji dukiya, ko a wawashe su, a raba da su.
Matsalar kishi ga matanmu ta kai matsayin ta’addanci, domin babu wata ma’ana ta
ta’addanci da kishi bai fassara ba. Ku nemi ma’anonin ta’addanci a
ƙamusoshinku, ku karanci jaridun ƙasarku da kafofin yaɗa labarai su yi muku
fashin baƙi.
Tarken Tsaron
Кasarmu A Taƙaice:
Tarkakken nazarin rashin tsaro a
ƙasarmu ya nuna Mahadi ne mai dogon zamani. Ga dukkanin bincikena, fasa
ƙwabrinsa aka yi, ba ƙasarmu aka haife shi ba, ba gadonsa muka yi ba. Ya zama
wajibi ga kowane ɗan ƙasa ya zama Kwastan
da Imigirashin a gargaɗo dukkan
rassan rashin tsaro, su bar ƙasa domin tsallakowa suka yi ba da izini suka
shigo ba. Abubuwan lura daga cikin rashin tsaro a ƙasarmu su ne:
i.
Da matasa marasa aikin yi
ake amfani wajen tayar da kowace irin fitina da aiwatar da ta’addanci.
ii.
Babu fitina ko
ta’addancin da ke faruwa a ƙasarmu face an sunsuna masa addini da ƙabilanci don
a ƙara masa amo, a daɗe ana fafatawa.
iii.
Dukkanin ta’addancin da
ke aukuwa a ƙasarmu da kuɗi ake ɗaukar nauyin masu jagorantarsa ta fuskar biyar
jinga da sayen makamai da toshiyar baki. Matuƙar babu wannan, babu ta’addancin
da zai yi awa ashirin da huɗu (24, kwana ɗaya) ba a murƙushe shi ba.
Abin Takaici:
Ga hasashen da na yi na matsalar
tsaro a ƙasarmu, ‘yan siyasa ne gaba wajen wanzar da shi. Akwai mamaki ƙwarai
mu gano cewa, dukkanin ‘yan siyasarmu sun san da rashin tsaron ƙasarmu,
musamman a nan Nijeriya ta Arewa. Manyan ‘yan takarar shugabancin ƙasarmu
kowane ya hau karagar yekuwar neman ƙuri’a zai ce: “Idan na ci nasarar cin zaɓe
zan kawar da matsalar rashin tsaro a Arewa tare da murƙushe Boko Haram.” Wannan na nuna matuƙar ba
su ke kan karagar mulki ba, ba su suka ci zaɓe ba, to, a mutu har liman a
Arewa. Waɗannan kalamai suna da harshen damo; ke nan mai faɗar zancen ya san
‘yan ta’addar, rufa su ya yi, ko da hannunsa ciki, ko yaransu ne. Matuƙar ba
shi/su aka zaɓa ba, kowa ya wuce lahira ba su damu ba. Allah ya isa! Ta tabbata
matsalar tsaron ƙasarmu da lauje cikin naɗi. Allah ya isar muna da isarsa.
Amin!
Ina Mafita?
Idan ana biye da mu da sauraro na
fahimta za a ga cewa, daga cikin hanyoyin da za a bi a samu fita cikin bala’in
ta’addanci a ƙasarmu su ne:
i.
Matasan da ake amfani da
su a sama musu aikin yi a shagaltar da su, a ko’ina suke a hana su zaman banza.
ii.
A ƙara ƙarfafa darussan
sana’o’in hannu a kowane mataki na karatu. A tilasta ɗalibai samun takardar
shahada biyu, ta karatun da suka yi, da sana’ar da suka ƙware a kai.
iii.
A yi zaman gaggawa na
ceto ilimi da manhajarsa a ƙasarmu. A tilasta darussan tarbiya, kishin ƙasa,
matsalolin cin hanci da ta’addanci a manhajar yara, su tashi da sanin muninsa a
cikin jikinsu.
iv.
A taƙaita tura yara
karatu ƙasashen da ba mu yi tarayyar al’adu da tarbiya da su ba.
Rubuce-rubucensu, da kafofin yaɗa labaransu, a ɗauki matakan ɗosane (karya) su,
kada su yi tasiri a zukatan yaranmu.
v.
A mayar da yekuwar yaƙin
neman zaɓe na ‘yan siyasa a gidajen rediyo da talabijin da jaridu domin a rage
banga da ta’addanci da kalaman ɓatanci.
Naɗewa:
A matsayin da ƙasarmu take ciki,
lokaci ya yi na a fara lura da zurfin karatu da shekarun waɗanda ke neman
manyan kujerun siyasa. Matuƙar ba nagartattun shugabanni ke akwai ba, tabbatar
da tsaro a ƙasa mawuyacin abu ne. A fara tunanin haramta siyasar tazarce a kowace kujera. Duk ƙasar da ta
yi sakaci tsaronta ya salwanta, ta gama wargajewa. Don haka, a halin da muke
ciki, mu tilasta yaranmu shiga ayyukan tsaron ƙasa da soje da ɗan sanda da
kowane nau’in aiki na tsaro. Tilasta ɗiyanmu mata karatun aikin jinya da likita
dole ne. Lokaci ya yi da za a ce muna da Jami’ar kanmu da za ta kula da
buƙatunmu.
No comments:
Post a Comment