Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta wannan waƙa
ranar 8 ga watan Ogusta, shekara ta 2019. Tana da adadin baituka arba’in da
biyu (42). Ta kasance ‘yar ƙwar huɗu.
GASKIYA A КI KI, A SO KI
1.
RoƙonKa
nikai Tabara ƙara basirata,
Ban
hikima mai yawa ta gyara fahimtata,
Sa
mini tsoronKa zuciyata Ka tsare ta,
In bi umurninKa sau da ƙaf ba saɓawa.
2.
Mai
rai duka na da lokacinai na taɓawa,
In
waƙaci ya yi babu sauran walawa,
Komai
ka gani a duniya zai ƙarewa,
Ikon Allah kaɗai ya zan mai dogewa.
3.
Halin
jama’a yana ban tsoro sosai,
Ƙarshen
lamari ka iske ya koma tausai,
Mai
shawagi ka iske ya kasa ta kainai,
Ya yi shiru babu wanda yaz zo cetawa.
4.
Gawurtaccen
azuraki dole gudun ka,
Mai
son ƙarshen ƙwarai a dole ya ƙyale ka,
Halinka
ya sa mutan ƙwarai na shakkar ka,
Ka warwatse su makirai na ta matsowa.
5.
Ramin
ƙarya ba zai yi zurfi da yawa ba,
Ko
an ga ruwa cikinsa ba za su daɗe ba,
Take
su ƙwafe ba za ka iske guɓɓa ba,
Кarshen ƙarya da masu so nata kokawa.
6.
Ba
matsiyaci kama da ƙaton mamugunci,
Mai
haɗa cuta ya je ya noƙe ya yi ƙyarci,
Mai
fatar mai akwai ya koma matsiyaci,
Sharri ƙarshensa madugu yaka murɗewa.
7.
Ka
haƙa rami cikinsa ka faɗi gigirce,
Son
girma ya zubar da girmanka taƙaice,
Yau
ga harshen maƙetaci an yi duƙunce,
Ya shiga ramin da yah haƙa sai
biznewa.
8.
Yau
ga giba da tsegumi an yi tsugunne,
‘Yan
sauraro ba batun karkaɗa kunne,
Ga
Suda ba ɗumi da hannu aka nune,
Baki ɗaure wuya ya kai ba kubcewa.
9.
Manyan
iya ƙulle-ƙulle yau ta ƙulle su,
Ga
su ga fili Huwallazi ya tona su,
Babu
kare bin damo da su har tawagarsu,
Кarshen ƙaiƙai kan masheƙiya za ya
bicewa.
10.
‘Yan
a yi sai mun gani , ku zo ga shi ku shaida,
Mai
kun-fa-ya-kunu Ya gama kuma Ya yarda,
Mai
tauhidi a dole zai dangane sanda,
Alƙwalin Jalla fil azal bai tadawa.
11.
Ga
wata ‘yar shawara aboki ta iyaye,
Kar
ka yi sharri saboda ƙarshensa hawaye,
Fuska
biyu na zubar da girma a kiyaye,
Sai an tsare gaskiya shiri ke dacewa.
12.
Gaggawa
ba ta yin kunu ba ta saba ba,
Saurin
nema ba za ya kawo samu ba,
Kushe
mutane ba zai hana su darajja ba,
Wa ya isa cewa lokaci ba ya tahowa?
13.
An
shafa ma zuma ga baki sai hauka!
Had
da kirari da ci da ƙarfi ga manyanka,
Romon
sata ya sa ka kushe gabacinka?
Ya zama wa’azi gareka ɗai ba ƙarawa.
14.
Tad
da wuya dorina da kyau a ga fuskarki,
Wai
gwanki ne ka tsegumin kyaun fuskarki,
Ya
turo raƙumi a je a ga leɓenki,
Wa ke da kamar ƙwarai cikinku ta
burgewa.
15.
Hayyanka
da ɓata ‘yan’uwa don a yaba ka,
Kaiconka
da yaudara a san ta ga fuskarka,
In
bone ya ci ka babu mai hoho kanka,
Sharrin da ka haddasa mutane ka
tunawa.
16.
Girman
kai, ji da kai musiba ce babba,
Ɗanga,
fahari, bugun gaba ba a gane ba,
Ni
nac ce, wa ka yi idan ba ni ne ba?
Кarshe bai kyau da rarahe aka ƙarewa.
17.
Wayon-a-ci,
yanzu had da kai ga jidalin ga,
Ka
gwaggeahe wuri kana ta baƙar darga,
Shaiɗan
ya dambala ka had da sayo ganga,
Gangumman Ɗan’ubayyu Malam ka kaɗawa.
18.
Girma
ya ɓaci tun da Malam ya makabce,
Gemu,
hana-ƙarya wanzamai sun kakkarce,
Ya
baza hoda idon maza ya bobboce,
Ya ce: “Jarƙaniya”, “A’uzu” muke cewa.
19.
Dole
da takaici malami da shiga ɓanna,
Malam
da kwaɗai da hasadar yankan ƙauna,
Kullum
su ke gaban sahun suɗan kwanna,
Ga rawani ya zube ana tattakawa.
20.
Kaza
‘yar tone-tone ta tone bonenta,
Ta
ruga ya biyo har ya danne ta,
Ga
zakaru na ganinta ba mai tanya ta,
Kowa ta gabansa yan nufa ba mai waigowa.
21.
Kura
sunanki ko’ina mai-a-ci-wawai,
Mun
ji awaki suna kashedi wurin karnai,
Sun
ce, “Su yi hanzari su shaida wa bisaisai”,
Ko ban fasa ƙwai ba ɗalibai na ganewa.
22.
Miƙe
tsaye Rozo-rozo ai mun gane ka,
Buzuzu
shi ya fallasa muna halinka,
Ya
ce muna, “Dole-dole ta fita iskarka”,
Shanshani ta ce, “Da kai da su ba ɗasawa”.
23.
Kasa
ke ce uwa ga ƙwari mamugunta,
Ga
Baƙi nan da Gajere ke sunka gabata,
Ke
ƙyale Jannasuri ya faɗa asunta,
Komarci ne munafuki ya ƙi tsayawa.
24.
Siffar
Jimina haƙiƙa ɗai da ta tsuntsaye,
Jemage
yay yi ɓad da sau ba tuntaye,
Shi
Aku martabarsa na nan baka ɓoye,
Hankaka, Zarɓi, Shamuwa ba ku iyawa.
25.
Kai
tashi Biri maɓannaci an gane ka,
Je
tambi Dila karo da mu ta ari hauka,
Kai
dai Gafiya aradu ko mun ƙyale ka,
‘Yan sharanin maraice ba sa ƙyalewa.
26.
Ɓera
ga saninmu ɗan hali ku ne manya,
Gafiya
sunanka yai amo har a surayya,
Kun
gama aikinku Mage ko ta tare hanya,
In ku mayas, in ku dakata babu wucewa.
27.
Na
tabbata sa ido kwaɗai yaka kawowa,
Baki
da kwaɗai a nan saleɓa ka zubowa,
Lasan
baki ga mai kwaɗai wa ka hanawa,
Modibbo ƙuda wurin kwaɗai aka shurewa.
28.
Alhudahuda
kau saninsa bai albarka ba,
Shehin
masani halama dai ba a shirya ba,
Ni
kau ga zaton da nay yi dai ba kai ne ba,
Don alfarmar sani ƙana’a taka sa wa.
29.
Shashasha
bunsuru akwai kissan kaura,
Kowa
ya sanka kai kaɗai aka barara,
Ka
ce: “Bana ka shirya wa fansarka ta bara”,
Rago ya ce: “Maraba shege ka ƙiyawa”.
30.
Ba
dai banza ba in ƙuda na bin walki,
In
ba tusa ba to akwai warin baki,
Ko
zawo ya tsure mu’anya tai tsaki,
Ba shakka don gawai ƙuda ba su biyowa.
31.
Kura
a yi hanƙuri abin daga Allah ne,
Suna
ya ɓaci ko’ina ki biya nune,
Ke
ci awaki da raguna had da mutane,
Danƙa amana gare ki ba mai farawa.
32.
Giwa
bukkar dawa karo ba ki saba ba,
Tilas
namun dawa su yarda da ke babba,
Mai
jayayya ya zaburo ban mu hana ba,
Kashinsa da hannuwansa shi zai
kwashewa.
33.
Ba
wani naman dawa da zaki ka tsoro,
Кarya
ce Cirza ke faɗa, ya fito taro,
Gwanki
da Kada da Dorina sun ɗau horo,
Sun ruga babu sallama ba su iyawa,
34.
Tsuntsun
da ya ja ruwa, ruwa za su kashe shi,
Don
iska, walƙiya da tsawa ka tare shi,
Saukan
manyan ruwa su ɓata dabararshi,
Iccen da ya shekaro sani zai mancewa.
35.
Mun
yarda haniniya Dawaki ke yin ta,
Bobbowa
Raƙumi kaɗai yai gadon ta,
Hargowa
na ga auraki ba ƙyafƙyafta,
Ka ji caransu sai gari zai wayewa.
36.
Ban
taɓa kwana da ƙin mutum a cikin rai ba,
Ni
dai bisa nau sani, idan ban manta ba,
Ban
taɓa cutar mutum saboda ƙiyayya ba,
Ba wata matsala da Zil Ulaa bai kwancewa.
37.
Wanda
ya miƙa wa Jalla kai ya zama Shago,
Ba
ya zama tunkiya a ja shi awa rago,
Don
mun ƙi aron halin kare sheƙo, rugo!
Za a haƙa min shigo-shigo ba zurmewa?
38.
Ba
mai zance da ku ya kau ba ku sauya ba,
Ba
alƙawalin da anka yo ba ku saɓa ba,
Babu
amanar da nis sani ba ku cinye ba,
Duk mai yin tin-da-tin da ku bai
morewa.
39.
Sata
da kwaɗai da raraka wayon zamba,
Son
kai, son maguɗi, a ce ba mu gane ba,
Кarya
ga tsegumi da tsince su yi kwamba,
An ce a kula ya zan jidali na ƙurewa!
40.
To
daɗa sai an jima Buwaye maci baƙi,
Katakoron
Kare-ɓuki mai ɗan baki,
Je
sannu katoɓara, gidoga a ci tsaki,
Rana ta ɓaci gaskiya za ta fitowa.
41.
Tammat
nai godiya ga Allah Makaɗaici,
Sarkin
da Ya fid da mu ga hali matsananci,
Yai
muna baiwa da gaskiya dole kwatanci,
Duk ga maƙiyanta nan suna warwatsewa.
42.
Sunana
Sha’iri Alu yaron Bunza,
Babban
birni da ke gabas ƙauyen Geza,
Geza
birnin kwalamshe mai suyan kaza,
Yanzu ina Jami’ar Gusau bisa koyarwa.
No comments:
Post a Comment