Wednesday, January 2, 2019

Gurbin Sarkin Musulmi A Ganin Watan Azumi



Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin halittun da ba su ƙidayuwa ga wani bawa daga cikin bayinSa. Ya ƙago sammai ya ƙawata (ta duniyarmu) da hasken taurari domin amfaninmu. Ya ba mu rana da wata domin daidaita ibadojinmu gwargwadon savawarsu a duniyarmu. Burina a wannan ‘yar takarda shi ne, lalubo wasu matsalolin ganin watan Ramalana da irin gurbin da shari’armu ta yi wa Sarkin Musulmi na kowace ƙasa ta Musulmi a ciki. Wannan xan yunƙuri an yi shi da nufin cike wani givi daga cikin kusurwowin da Shaixan ke kutsowa ya yaudare mu ta fuskar haxin kanmu. Matsalolin da ke tattare da ganin wata a duniya…

Gurbin Sarkin Musulmi A Ganin Watan Azumi

Aliyu Muhammadu Bunza
Tsangayar Fasaha da Nazarin Musulunci
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato
Ƙibxau: mabunza@yahoo.com            
Waya: 08034316508

Takardar da aka gabatar a taron ƙasa-da-ƙasa mai take: “Ganin Wata da Haxin Kan Musulman Nijeriya: Tafarkin Ci Gaba”, ƙarƙashin kulawar Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato, Gwannatin Jihar Sakkwato, Majalisar Sarkin Musulmi da Jama’atu Nasaril Islam, Nijeriya ranar 6 – 9 ga watan Yuli, 2012 a babban Masallacin Abuja.

Gabatarwa:
Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin halittun da ba su ƙidayuwa ga wani bawa daga cikin bayinSa. Ya ƙago sammai ya ƙawata (ta duniyarmu) da hasken taurari domin amfaninmu. Ya ba mu rana da wata domin daidaita ibadojinmu gwargwadon savawarsu a duniyarmu. Burina a wannan ‘yar takarda shi ne, lalubo wasu matsalolin ganin watan Ramalana da irin gurbin da shari’armu ta yi wa Sarkin Musulmi na kowace ƙasa ta Musulmi a ciki. Wannan xan yunƙuri an yi shi da nufin cike wani givi daga cikin kusurwowin da Shaixan ke kutsowa ya yaudare mu ta fuskar haxin kanmu. Matsalolin da ke tattare da ganin wata a duniyar Musulmi ta yau suka wajabtar da sake bitar ayyukan magabata domin a ciwo kansu. Na kasa wannan takarda zuwa gida uku: Kashi na farko shi ne, goshin aiki, wanda ya ƙunshi share fagen nazari. Sashe na biyu, ya ƙunshi kayan cikin takarda wanda ya fuskanci muradinta gadan-gadan. Sashe na uku, ya yi mata marufi da sakamakon abubuwan da aka ƙyallaro a nazarin.

1.0   Rana da Wata a Ibadojin Musulmi:
Rana da wata halittun Allah ne da yake ambatar su bisa irin tsarin da muka jera su.[1] Mulkin Allah Ya game su gaba xaya domin ƙasa duka tasa ce.[2] Annabcin Muhammad (SAW) ya game duniya mafitar rana da mafaxarta.[3] Da rana muke kirdadon lokuttan sallolinmu – biyar. Da ita ake dogaro ga buxa bakin azumi kowane iri[4]. Ta fi wata girma ga hankalin tuwo, ita ce gabansa a tabbataccen nassi[5]. Da tsayuwar wata aka jingina ibadar Hajji da Zakka da Azumi[6]. Ashe ke nan, sanin gurbin waxannan halittu na nassoshin shari’a wajibi ne ga mai son ya yi ibadarsa yadda aka umurce shi ya yi.[7] Waxannan halittun sukan sava wa juna gwargwardon yadda haske da duhu ke jewaxi a duniyar mutane.[8] Ala tilas, Musulmi su nazarci yadda waxannan halittu ke sava wa juna a duniyar da suke zaune domin abin zai shafi ibadojinsu na farilla da aka farlanta musu.[9]

2.0   Wane ne Sarkin Musulmi?
Musulunci shi ne miƙa wuya ga dukkanin umurce-umurcen Allah, da nisantar hane-hanenSa, da yarda da ƙaddarorinSa da aminta da bin tsarin da Allah ya tsara.[10]  Wanda Allah Ya aiko a matsayin annabi ko manzo, shi ne sarki ga duk wanda ya yarda da saƙonsa.[11] Wanda Annabi ya aiko ya wakilta shi ga jama’arsa a kan wata matsala na wani yanki shi ne sarkinsu.[12] Idan kuma Annabi ko Manzo ya yi wafati, wanda jama’arsa suka taru suka zava ya zama Halifansa.[13] Haka sarautar Musulunci ta fara tun daga magabata ya zuwa gare mu yau na ƙarshen zamani[14].
Magabata masana shari’a sun tabbatar da sharuxxa goma sha xaya da ake buƙata ga wanda za a naxa Sarkin Musulmi.[15] Daga cikinsu sun ce biyu ba dole ba ne.[16] Ba za a yi Sarkin Musulmi biyu a ƙasa xaya ba[17]. Ba a tuve shi daga sarauta matuƙar bai kafirta ba, kafirci bayyane.[18] Yi masa xa’a dole ne matuƙar bai ci karo da kulkin nassin littafin Allah da umurnin Annabi (SAW) ba.[19] Wajibi ne a ƙasar Musulmi a sami Sarkin Musulunci mai tsare musu addininsu da hukunce-hukuncensa.[20]
A fiƙihun ganin wata, matsayin Sarkin Musulmi na fitowa da sunaye daban-daban makusanta ga aiki da gurbin da Sarkin Musulmi yake da shi a shari’a.[21] A ayyukan magabatan farko, yakan fito da sunan Imaamul A’azam, Amirul Mu’uminina, Khalifa, Waziri, Hukuuma da Masu hukunci[22].  A rubuce-rubucen waxanda suka biyo bayansu, akan sami sunaye irin su Amiiru, Haakimu, Imaamu, Sulxaanu, Alƙaadhii da dai sauransu.[23] Idan al’amarin Musulmi na haxe wuri xaya dukkanin waxannan  sukan xauki aiki irin na Sarkin Musulmi (Imaamul A’azam) ga abin da ya shafi ganin wata a Musulunci.[24]

3.0   Farfajiyar Ikon Sarkin Musulmi a Fiƙihun Ganin Wata:
A kowane vangare na addini Imaamul A’azam na da hannu a ckin ƙasarsa.[25] Khalifofin Manzo (SAW) su suka maye wannan gurbi bayan wafatin Manzo (SAW). Fitattun Khalifofinsa huxu sun yi fice a kan haka.[26] Bayan gushewarsu Banu Umayyad sai Abbasid suka hau gadon.[27] Daga wannan lokacin sarautar Imaamul A’azam ta musulman duniya gaba xaya ta raunana. Zancen tafiyar da ayyukan musulmi gaba xaya ƙarƙashin shugaba xaya na duniyar musulmi ya ci tura.[28]
Tun a wancan zamani fiƙihun ganin wata da ibadojin da suka rataya gare shi ya fita ga hannun shugaba xaya a duniya. Waxanda suka biyo baya ana ce da su Asarud Duwailat Wal Mamalik (wato sauran ‘yan dauloli ko ƙasashe) Fatimawa suka kafu a Masar, Samaniyyun a ƙasar Farisa da Asiya wanda ya haxa da Bukhaara da Samarƙandi. Ragowar Banu Umayyad suka kafa tasu daula a Andalus[29] (Spain), daga cikinsu aka sami Almuraabideen da daular Ottomon Usmaniyya (taTurkiyya). Muhammad Algaznawiyyun ya kafa daular Gazanawiyyu (Gazanawa) a ƙasar Afghanistan wadda ta mamaye Arewa maso yamma na ƙasar Indiya da cibiyarta a ƙasar Gazna.[30] Tun a wancan lokacin ibadojin da suka ta’allaƙa ga ganin wata suka daina fitowa daga Makka ko Madina ko Kufa ko Basara, kowace daula da shugaban da ke tafiyar da ita. Daga cikin daulolin akwai daular Usmaniyya[31] da aka kafa a 1492 ita ta makaro har zuwa shekarar 1924. Wannan shekara ita ce shekarar ƙarshe da daulolin Musulunci suka ruguje a duniyar Musulmi.[32]
A duniyar baƙar fata musamman a Afirka ta yamma, an kafa wasu dauloli irin su daular Sakkwato da daular Masina da daular Umar Al-Futi[33]. Waxannan daulolin kowaccensu gashin kanta take ci, duk da yake Musulunci shi ne ginshiƙin tafiyar da harkokinta[34]. A zamaninsu, babu wadda ta dogara da wata kan gudanar da al’amurranta na addini domin jagororinsu ba Imaamul A’azam ba ne ba kuma Khalifofi ba ne.[35] Bayansu an sami daulolin da suka miƙa wuya ga addinin Musulunci, wasu an ci su da yaƙi, wasu ba a ci su ba, amma kuma kowaccensu da ƙasarta da al’ummarta da sarakunanta irin su: daular Shonghai, daular Kabi, daular Borno, daular Gobir da dai sauransu.[36] Waxannan duk da sarakunansu da ƙasashensu kuma musulumai ne ‘yantattu, suna karvar umurnin ibadojinsu ga sarakunansu.
Dangantakar sarautunmu da ganin watanmu a yau yana da sarƙaƙiya. Idan za a kula, sarakunanmu na daulolinmu na gabanin jihadin ƙarni na 19 da na bayan jihadi kowanensu cikakken iko yake da shi[37]. Wani ba ya tuve wani, wani ba ya naxa wa wani sarki a ƙasarsa. Wani ba ya da alaƙa da wani.[38] Wani ba ya naxa wani sarki a ƙasarsa. Wani ba ya tuve wani sarki na ƙasar wani. Wannan shi ya sa fiƙihunmu dole ya sauya matuƙar ba mu haxe a zaman ƙasa xaya ta Musulunci ba, ƙarƙashin sarki xaya na Musulunci. Wanda duk zai hukunta  ganin watan wani Sarki a wata daula, a kan wasu jama’a ko dukkanin jama’ar dauloli mabambanta ala tilas ya tsura wa wannan matsala idon natsuwa na fiƙihun Ƙur’ani da Hadisi bisa ga zamanin da ake ciki.[39] Sarkin Musulmi a yau an hana shi damar da shari’a ta ba shi na zartar da dokokin shari’a. Ga ƙasa ta Musulmi dokoki na son rai da kafirci.[40]

4.0   Duniyarmu a Fiƙihun Ganin Watanmu:
Wajibi ne ga kowane sarki, na kowace irin al’umma, a kowace ƙasa yake, komai kwarjinin mulkinsa, da ficensa, da aminta da sunansa, ya san da cewa, matsalar ganin wata tana buƙatar sanin fiƙihun yanayin duniyar da ƙasashen duniya suka mamaye. Daminar wata nahiya a lokacin wata ke cikin raninta. Wata ƙasa sam ba ta da damina, wata ba ta san rani ba. Yayin da ake bazara wata nahiya, a wata hunturu ne. Wasu kan xauki dogon lokaci ba su ga rana a nahiyarsu ba, wasu kuwa ranar ta haddabe su da tsananin zafi. Da Allah zai azurta mu da mujaddadin ƙarshen zamani a matsayin sarkin musulmin duniya baki xaya, dole sai ya karanci wannan fiƙihun yanayi gabanin ya yanke hukuncin lokuttan ibadoji da ibadojin da suka shafi ganin wata. Dubi waxannan misalai domin ka tabbatar da hasashenmu:[41]
i.                   Lokacin da rana ke faxuwa Makka a lokacin Musulmin California ke jiran hudowarta.[42]
ii.                 Bambancin lokacin tsakanin Makka da California awa goma sha xaya ne (rabin rana xaya).[43]
iii.              Faxuwar rana a California a Makka ana haramar sallar Asuba, a Indonesia ana sallar la’asar ta gobe.[44]
iv.               Lokacin da ake sallar Subahin a Makka a Amerika-ta-Arewa (North America) ba su gama Isha’i ta jiya ba.[45]
v.                 Idan Musulmin Los Angeles suna sallar Asuba a ƙasar India da Pakistan suna magariba ko Isha’i ta wannan rana.[46]
vi.               A rana xaya akan sami bambancin kwanan wata a duniya, misali da marece sanyin la’asar (yamma) na ranar Lahadi a ƙasar Amerika shi ne ranar Litinin da asuba a Indonesia.[47]
vii.            A cikin Makka kaxai akwai bambancin awa xaya tsakanin Jidda da Damman.[48] Hararar da masana duniya suke yi wa yanayin duniyar da muke ciki ya tabbatar da duk ibadojin da muke yi ta la’akari da rana da wata ba za a iya a yi su a lokaci xaya ba. Kai ko rana xaya ba za su yi wu a duniyarmu ba. Don babu wata hukuma ko wani sarki ko wani shugaba da zai daidaita wannan yanayi ya kasance xaya, bale ya tilasta musulmi su bi tunaninsu a kan ibadojin da suka ratayu ta duban rana da wata.

5.0   Yaya Za a Dubi Wata:
A shari’a, kowane wata ana son a fita a nemo shi domin a tabbatar da tsayuwarsa. Tun lokacin Manzon Allah (SAW) Sahabbai sun kasance suna fita wajen gari duban wata.[49] Za a fita da yawa manya da yara da zarar rana ta faxi tun da sauran gajimari har zuwa vacewarsa. Wanda duk ya ci nasarar gani ya nuna wa jama’a su shaida. Ya yi tsaye wurin da ya gan shi ya kifa masa ido ya nuna.[50] Waxanda ya nuna wa, su duba sosai, su kuma dubi idon wanda ya ce ya gani, domin tabbatar da kaifin ganinsa da lafiyar idanunsa.[51] Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka biyo bayansu ba su sava ba ga yin haka, saboda haka ganin watansu ya kuvuta ga rikici.
Bisa ga ingantacciyar magana watan Musulunci kwana ashirin da tara (29) yake yi.[52] An kuma sami sahihin bayani yana yin talatin (30).[53] A wata riwaya cewa aka yi, idan aka sami gumuzun giza-gizai ko ƙura ko hayaƙi ko hadari sai a ƙaddara masa kwana talatin (30).[54] Don haka za a neme shi yamma bayan faxuwar rana a ranarsa ta ashirin da tara (29).[55] Watan Musulunci ba ya kwanaki ƙasa da ashirin da tara (29), ba ya yin sama ga talatin (30).[56] Idan aka yi haka, aka ga wata, an yi abin da shari’a ta tanada.
 A ganin wasu magabata, faxar da hadisi ya yi na: “ku ƙaddara masa”. Suka ce wata ƙofa daga cikin ƙofofin fasaha ne Manzo (SAW) ya buxa. A kan haka suka halasta duban wata da na’urori irin na kimmiyar zamani da hisabi da ilmin taurari da falaƙi.[57] Nassoshin shari’a ingantattu sun soke wannan ra’ayi domin savawar sa ga ingantacciyar aƙida da koyarwar Manzon Allah (SAW).[58] Don haka, shugaba ko hukuma ba su da ikon bin haramtaccen tafarki domin tabbatar da halastaccen aiki.[59] Gani ga ido aka ce. In ba a gan shi da ido ba, bai tsayu ba, ko da wata fasaha ko kimiyya ta tabbatar da tsayuwarsa a shari’a bai tsayu ba.[60] Idan ta ƙaryatar da rashin tsayuwarsa, ko an ce ba a iya a gan shi da ido a ranar, matuƙar an samu shaidar wani ya gan shi ko mai ido xaya ne ya sami adilan da suka shaida yadda ya shaida, wata ya tsayu a shari’a. Hisabi da na’urorin kimiyya ba su isa su ƙaryatar da ganin ido ba.[61] Da ganin ido sarki zai yi dogaro, kuma da shi zai tabbatar da tsayuwar wata ya sanar da mutanensa. A cikin Muntaƙa sharhin Muwaxxa Malik an ce:
Ibn Naafi’un ya ruwaito daga Naafi’u daga Maalik, a cikin wata alƙarya akwai wani sarki da ba ya azumi da ganin watan (mutanensa) ba ya salla da ganin watansu. Shi yana azumi da salla ta fuskar hisabi kawai (Malik) ya ce: ‘ba a koyi da shi, ba a bin sa.[62]
6.0   Me Ke Tabbatar da Tsayuwar Wata ga Sarki da Jama’arsa?
Abu na farko da ya kyautu xalibin ilmi ya sani shi ne, kowane watan Musulunci abu uku ke tabbatar da shi. Magabata sun fi mayar da ƙarfi ga watan Shawwal da Ramadan saboda ibadojin da suka rataya a kansu. Shaihu Khalil na cewa:
Watan azumi na tabbata da cikar watan Sha’aban ko da ganin mutum biyu adilai… ko taron jama’a (abin gaskatawa) su gan shi.[63]

Wannan zance na Shaihu Khalil a kan shi ne masana mazhabobi suka sha kai da komo wajen tattauna shi da tsettsefe shi. A taƙaice, abu uku ke tababtar da tsayuwar kowane wata a Musulunci kamar haka:

i.                   Cikar watan Sha’aban (wato kwana talatin (30).[64]
ii.                 Mutum biyu adilai su gan shi.[65]
iii.              Jama’a masu yawa su gan shi.[66]
Wurin da sarki zai shigo a cikin nassi na xaya sai in an sami fa’in gumma alaikum a nan, sarki ya samu ya karvi bayanin wani gari ko wata gunduma daga cikin gundumominsa da ke da lafiyyayen sararin samaniya. Idan ya sami shaida daga can sai ya zartar, in bai samu ba, sai a ƙaddara masa kwana talatin (30). Idan akwai tsaftataccen tsari yin haka zai kuranye kowace matsala ga gari ko ga ƙasa.
A wajen tantance adilai biyu ma sarki da masarauta sun shigo. Ga al’adar mutanen duniya na kowane zamani, za a sami shugabannin da suke yi wa biyayya. Idan sarki ya tabbatar da adalcin mutanen da suka ga wata, shi zai yi sanarwa ga mutanensa a kan abin da ya tabbatar.[67] Haka kuma, idan mutanen baƙi ne ba a san halinsu ba, ko daga wata ƙasa suka gan shi suka shigo ƙasarsa ko daga wani gari ko zuwa garinsa. A nan duk, sarki kaxai zai iya tantance adalcinsu da adalcin ganinsu domin ya tabbatar.[68]
Idan jama’a da yawa suka gani istifaadha an hutar da sarki da yekuwa ta tantacewa sai kowane allazi ya ja nasa aamanuu. Fiƙihun da za mu cira a nan shi ne, kowane xaya daga cikin abubuwan nan uku na tabbata ba da an je gun sarki ko shugaba ba, kuma azumi ya inganta. Da an samu tabbacin xaya azumi ya wajaba sarki ya sanar ko bai sanar ba. Sarki na iya kuren ƙidaya ya cika Sha’aban, a ga wata savanin umurninsa, kuma azumi ya tabbata bisa ga nassin, faman shahida da suumuu li ru’uuyatihi.[69] Ƙin karvar shaidar ganin watan wani (mutum xaya) ko wasu ga sarki, ba hujja ce ta rashin tabbatuwar tsayuwar wata da wajabcin azumi ga wanda ya gan shi ko waxanda suka gani ba, domin, a cikin Mawaahibul Jalil Sharhin Makhtasar Khalil Shanƙiixii ya ce, Malik ya ce:
Shin kana ganin wanda ya ga wata shi kaxai sarki na da damar ƙin karvar shaidarsa? Ya ce: ‘E yana da’. Na ce: ‘Wannan shi ne zance Malik?’ Ya ce: ‘E.’ Na ce: ‘Ko wanda ya ga wata shi kaxai yana da damar ya yi azumi idan Sarki ya yi watsi da shaidarsa?’ Ya ce: ‘E.’ Na ce: ‘To! Idan ya sha ruwa fa, zai yi kaffara ko ranko ga zancen Maliki: Na ce: ‘In ya gan shi, shi kaxai yana wajaba gare shi ya sanar da sarki a zancen Maliki?’ Ya ce: ‘E, domin wata ƙila wani ba shi ba ya gan shi tare da shi, sai a inganta shaidarsu (su biyu).’[70]

Ibn Ƙudaama cikin Almugnii ya tabbatar da:
Idan suka ba da shaidar (ganin wata) gaban sarki, sarki ya yi watsi da shaidarsu saboda jahiltar halayensu wanda duk ya san da adalcinsu ya sha ruwansa.[71]
Shaihin masanin ya ƙara da cewa:
Watsar da shaidarsu da sarki ya yi, ba wani hukunci ne ya yi a kansu ba, ya dai tsaya ne kawai domin bai san su ba, ba ya da ilmi a kansu, yana jira ya samu wani a kansu.[72]

Manyan malaman Malikiyya sun tabbatar da ingancin wannan zance a cikin Annawaadiru waz ziyaadaati alaa maa fii mudawwanati wa min ghairihaa minal ummahaatu an ce:
          Malam Muhammadu xan Rushudi ya ce:
Idan mutum ya ga watan Ramadan shi ya wajaba gare shi ya azumce shi. Idan ya sha ruwa yana mai cike da ilmin wajabcin azumi (ga wanda ya ga wata) gare shi ba tare da (wani) tawili ba, rankon (azumin nan) da kaffara sun hau kansa. Haka kuma, in ya ga watan Zulhajji shi kaxai, ya wajaba gare shi ya tsayu Arfa shi kaxai ba da kowa ba, kuma yin haka ya isar masa ga hajjinsa. Malamai na bayan magabata sun ce: “Wannan zance sahihi ne”.[73]

Waxannan nassosi sun tabbatar da cewa, sarki ba ya da hurumi na ya hana xaukar azumi ko aje azumi idan ganin wata ya tabbata. Ƙin amintar sarki ga shaidun da aka gabatar masa kai tsaye ko ta hannun wakilansa ba hujja ce ta xaukar azumi ko aje shi ba.

7.0   Matsayin Sarki ga Sanarwar Ganin Wata:
Musulunci addini ne da ya ƙarfafa biyayya da xa’a ga shugaba,[74] ya kuma haramta yi masa tawaye da wofintar da shi.[75] Nassoshin ganin wata asalinsu daga Annabi da Sabbansa da Tabi’ai aka naƙalto su, don haka nassoshin suka yawaita. Ga wasu kamar haka:
i.                   Abdullahi ibn Umar ya ruwaito cewa: Mutane sun ƙwala ido duban watan sai na gaya wa Annabi (SAW) cewa, na gan shi, sai ya yi azumi ya umurci mutane su yi azumi.[76]
ii.                 Rab’iyyun bn Hiraashin ya ruwaito daga wani mutum daga cikin Sahabban Annabi (SAW) cewa: ‘Lallai, mutane sun yi savani a ƙarshen watan Ramadana sai wani Balarabe ya zo gaban Manzon Allah cewa an ga wata jiya. Annabi (SAW) ya umurci mutane su sha ruwa.[77]
iii.              Abdullahi bn Ahmad bn Hambal ya ce: “Na tambayi babana a kan ganin wata idan mutum kaxai ya gan shi, sai ya ce: Sarki zai yi wa mutane umurni su yi azumi”…[78]
iv.               Imam bn Rushid ya ce: “Idan ta tababta a wajen sarki ganin wata da shaidar mutum biyu adilai, Sarki zai umurci mutane da yin azumi ko shan ruwa kuma ya jagoranci mutane kan haka.”[79]
v.                 Ibn Aabidiinil Hanfiyyu ya ce: “Abin da yake ma’inganci a kan waxannan duk shi ne, an rataya shi ga ra’ayin sarki in zuciyarsa ta ba shi ingancin abin da aka zo da shi na ganin wata da yawan shaidun wurinsa sai ya ba da umurni a yi azumi.[80]
vi.               Ibn Ƙayyim na cewa: “Xaga cikin shiriyar Annabi (SAW) ita ce, umurtar mutane da xaukar azumi bisa ga shaidar mutum xaya musulmi aje azumi kuwa da shaidar mutane biyu.”[81]

Waxannan nassoshi sun tabbatar da sarki ke da ikon ba da sanarwar ganin wata ga jama’arsa.[82] Sanarwar sarki ta ganin wata tare da umurnin a xauki azumi ake yin ta ko aje shi kamar yadda nassoshi suka tabbatar. Sanarwar sarki ta ba a ga wata ba, ba hujja ce ga wanda ko waxanda suka ga wata ba. Malam Xan’alƙaasim ya faxa a cikin Majmuu’aati cewa:
Daga Maliki wanda ya ga watan Ramadaana ko Shawwal shi kaxai, to ya sanar da sarki.[83]



8.0   Hukuncin Sarki Ga Shaidar Ganin Wata:
Sanarwar ganin wata ba wani sharaxi ne daga cikin sharuxan azumi ko rukuninsa ba.[84] A zance mai faxi, wasu mazhabobi ba ya daga cikin abubuwan da suke gani muhimmai ga al’amarin azumi. Ya kyautu mu tantance me ke sa a sa sarki ga sha’anin ganin wata? Wasu magabata, masana Furuu’a har babi sun keve a cikin rubuce-rubucensu mai irin wannan matsayin ko suna. Waxannan matsaloli duka an fi cin karo da su wurare biyu daga cikin abubuwa uku da ke tabbatar da tsayuwar watan azumi da muka ambata:

8.1   Mutum Xaya:
Duk da yake wasu mazhabobi sun ƙi inganta ganin mutum xaya shi kaxai a wasu zantuka. A wasu zantuka kuma an sami ingancin haka cikin mazhaba xaya, don haka buƙatar shigar sarki ta zo a nan.[85] Mai Harraashi sharhin Mukhtasar Khalil ya dubi ganin mutum xaya kamar haka:
          Wannan matsala ta kasu gida uku:
(Na farko) ganin mutum xaya (shi kaxai), ko wanda ya ji daga wanda ya gani (shi kaxai), ko wanda ya ji daga wanda ya ji wurin mutum xaya da ya gani. Mutum biyu na farko (wanda ya gani da wanda ya ji daga wanda ya gani) Azumi ya wajaba a kansu. (Azumi) ba ya wajaba ga na ukun face idan sarki ya yi hukunci (ga tabbatar shaidarsa).[86]

Zancen Kharrashi na farko mai Dasuuƙi ya tabbatar da shi a faxarsa:
Shi kan wanda ya ga wata (azumi) na wajaba a kansa yanke (saki ba ƙaidi).[87]

Ibn Rushud a cikin Bidaayaa ya tabbatar da wannan zance da faxarsa:
Ta fuskar ganin wata da ido ƙuru-ƙuru (ba shaidu ba) tabbas malamai sun haxu a kan cewa, wanda duk ya ga wata (suka yi arba da juna) shi kaxai, lallai ne ya yi azumi.[88]

Ibn Ƙudaama a cikin Almugnii ya ambaci sarki kamar haka:
Idan sarki ya yi hukunci ga ganin mutum xaya shi kaxai ya halasta (ba jayayya).[89]

A ganin watan mutum xaya, sarki na da ta cewa ga tabbatar da shi ko akasin haka. A cikin Sahihul Fiƙihus Sunna an ce, wanda ya ga wata shi kaxai idan ba a karvi shaidarsa ba yana da zavi uku:[90]
i.                   Ya xauki azumi kuma ya aje azumi da ganinsa shi kaxai.
ii.                 Ya yi azumi da ganinsa, amma kar ya sha sai tare da mutane.
iii.              Ba zai yi aiki da ganinsa ba gaba xaya.

Zance na farko ya yi canjaras da nassin aya da hadisi a kulkin baƙi.[91] Zance na biyu gavarsa ta farko ta yi daidai da zance na farko, gavarsa ta biyu mazhaba ce.[92] Zance na uku ba ya da kulkin nassi tabbataccen, an gina shi a kan wata fassara mai nisa.[93] Malam Ibn Ƙudaama ya magance matsalar da hutar da mutane zuwa wajen sarki tantancewa ya ce:
Wanda ya ga wata shi kaxai aka ƙi yarda da shaidarsa, (ya samu) ya yi azumi. Wannan magana mashahuriya ce a cikin mazhaba cewa, ko da adili ne ko fasiƙi, ya kai bayanin ga sarki, ko bai kai ba, an yarda da shaidarsa, ko ba a yarda ba, duk dai azumi ya kama shi, wannan shi ne zancen Malik da Lais da Shafi’i da A’shaabul Ra’ayi da Ibn Munzil.[94]

Idan mutum ya ga wata da kansa haƙiƙanin gani, zance na tantance shi bai taso ba komai lalacewarsa tilas ya tashi da azumi. Buƙatar tantancewa kore ƙarya, shi ko ganau yake ba jiyau ba don haka gani ya kori ji.

8.2   Adilai Biyu:
Tantance wane ne adili? Yana da wuya, kamar tantance, wane ne fasiƙi? Don haka magabata managarta ke ƙoƙarin sa sarki ko hukuma a ciki domin samun tsaftataccen hukunci da ya kuvuta ga son rai. Mai sharhin Mukhtasar Harshi ya ce:
Hukuncin tsayuwar wata ga samun shaidar adilai ga wata samun shaidar adilai da misalinsa, shi da tabbatar da tsayuwar wata, daga sarki, daidai suke, sarkin ya kasance babban sarki kamar Khalifa ko ƙaramin sarki ga gunduma duk dai maganar xaya ce.[95]

 A nan, kowane sarki na iya tantance adili biyu a kan shaidarsu ta ganin wata. A Haashiyatil Addasuuƙii alaa Sharhil Kabir an ce:
Wanda duk adilai biyu suka ba shi labarin sun ga wata ko ya ji su suna labarin ganin watansu ga wani ba shi ba, (wanda ya ji labarin) azumi ya wajaba gare shi…[96]

Wurin da gizo ke saƙa shi ne:
Da mutum biyu sun ga wata kuma ganinsu bai tabbata a wajen sarki ko hukuma ba, ba za a yi hukunci da ganin ba. Idan wasu mutum biyu suka cirato labarin daga waxancan biyun da sarki bai tabbatar ba kuma su mutanen wani gari ne daban da waxancan na farko suka ba da labari ga shaidar waxancan mutum biyu na farko. Ba ya wajaba ga mutanen garin su yi azumi. Na’am da dai an gaya wa sarki wancan ganin da aka yi, wanda aka cirato daga mutum biyu da suka gan shi, sai sarki ya yi hukunci a kan haka, to, hukuncin ya game kowa, wanda duk ya ji hukuncin ya wajaba gare shi ya yi azumi.[97]

Ashe sarki na da damar karvar shaidar waxanda suka shaida daga wasu. A sani cewa:
Babban abin da zai game gari ko ƙasa duka da azumi shi ne, hukuncin da sarki ko hukuma za ta yi ko ta zartas ko samu tabbatacciyar shaida a wurinsu wadda ba ta koruwa.[98]

Ya zo a cikin Annawaadiru cewa:
Malam Abdullahi ya ce, na ba da labari daga Ahmad bn Maisar Al’Iskandiraani cewa, shi ya ce: ‘Idan adili ya ba ka labarin cewa, wata ya tsayu bisa ga hukuncin sarki kuma shi sarki ya yi umurni da a yi azumi ko aka ciro wannan labarin daga bakin wani a gari na daban, aiki da wannan labari ya hau kanka a kan babin karvar zancem mai gaskiya ba a kan babin shaidu ba (domin shaidun sai mutum biyu).[99]

Magana a nan ita ce, shin ko sarki na da ikon watsar da shaidun adilai biyu? Ibn Ƙudaama ya faxa a cikin Almugnii cewa:
Da duk shaidu biyu suka shaidi ganin wata wajibi ne a karvi shaidarsu a wajen Abubakar.[100]

Bisa ga wannan ya ƙara da cewa:
Idan aka ba ka labarin ganin wata daga wanda zancensa ke inganta, azumi ya wajaba ko da sarki bai tabbatar ba.[101]

Wa ke tabbatar da shaida? Wa ke karvar shaida ya tantance ta? Jawabi a nan shi ne, “sarki ko hukuma”. Idan suka tantance, sanarwa na hannunsu. Su adilan biyu, in an tabbatar, in ba a tabbatar ba, azumi ya kama su, ya kuma kama duk wanda ya ji labarin ganinsu, da wanda ya yarda da su, da wanda labarin ganinsu ya girshe shi.[102]

8.3   Ganin Jama’a da Yawa:
Hausawa sun ce mutuwar taro kaka. Idan mutanen gari ko ƙasa ko gunduma da yawa sun ga wata sanarwa kawai ya hau kan sarki ko hukuma. Abin da ake nufi da ganin jamaa’atul mustafiidha jama’a masu yawa shi ne:
Kowane xaya daga cikinsu ya ba da labari da kansa cewa shi da kansa ya ga wata.[103]

8.4   Muhallin Sarki a Mazhabobi Cikin Sha’anin Ganin Wata:
Sha’anin ganin wata:
Mazhabobi makarantun ilmi ne maƙoƙarta mahimmata wajen tace nassoshin shari’a da daidaita su domin kuranye fitina da rabuwar kai ga al’umma. Ginshiƙan mazhabobi shi ne, Alƙur’ani da Hadisi, abin da duk ya sava musu ba zancensu ba ne fassara ce aka yi a kan kuskure.[104] A wajen fitattun mazhabobi huxun da suka yi fice a nan nahiyar[105] kowannensu da yadda ya dubi gurbin sarki da hukuma a bagiren ganin wata.

8.4.1 Shafi’iyya:
A tsarinsu ganin watan mutum xaya adili ya wadatar ko da baƙo ne, ya dai kasance mai hankali, baligi, xa, namiji, adili (ko da a fuska). Zai ba da shaida da faxar: Ash’hadu “na shaida”. Muhallin sarki a wajensu shi ne alƙali wanda suka ce:
Mai shaidar zai ce ‘Ash’hadu” na shaida ni na ga wata. Ba dole sai ya ce: ‘gobe azumi ne’, a shaidarsa ba. Azumi ba ya wajaba ga tarsashin mutane face sai alƙali ya ji wannan shaidar ya kuma yi hukunci da ingancinta ko ya ce: “Na tabbatar da tsayuwar wata a wurina”.[106]
Duk da haka, sun aminta da ganin mutum xaya, sun ce wajibi ne ya tashi da azumi, ko ya gaya wa alƙali ko bai gaya masa ba, ko alƙali ya karvi shaidarsa ko bai karva ba, duk dai zai tashi da azumi. Haka kuma, wajibi ne ga duk wanda ya gaskata shi ya yi azumi.
A mazhabarsu cewa suka yi:
An so tantance fitar wata da wajabtar da azumi ya zamo ga masu jagorancin jama’a wato sarki ya yi hukunci da kansa. A duk lokacin da sarki ya yi hukunci azumi ya wajaba ga mutane ko da kuwa hukuncinsa a kan mutum xaya ne ya ga wata adili.[107]

8.4.2 Malikiyya:
Ana tabbatar da ganin wata da ganin ido wanda ya kasu gida uku: Ganin adilai biyu, mutane da yawa, ganin mutum xaya wanda zai tsaya a kansa da wanda ya gaskata shi, ko sarki ya hukunta a yi kamar yadda ya gabata. A wajensu, sarki zai fito kamar haka:
Zai wadatar idan aka naƙalto labarin ganin wata daga hakimi (ko sarki) ko hukuncinsa ya tabbatar da tsayuwar wata. Idan adili xaya, ko wani wanda ba a san halinsa ba ya ga wata,  yana wajaba gare shi ya kai labari ga sarki domin ya buxe ƙofar shaida, da yawa za a sami wani da zai zo ya tabbatar da maganarsa in ya kasance adili, ko a sami shaidun jama’a in ba adili ba ne. babu sharaxin faxar “Na shaida” a wajensu.[108]


8.4.3 Hanafiyya:
Idan sama’u na garau sun ce, dole a sami shaidar jama’a da yawa. Sun ce:
Yawan jama’a ya dogara ga ra’ayin sarki ko na’ibinsa babu tilas ga samun wani adadi yankakke ga magana yardajjiya.[109]

A fahintarsu sun ce:
Babu sharaxin sa bakin sarki ko wata majalisa ta alƙalai. Idan mutum xaya da shaidarsa ke inganta ya ga watan azumi ya ba da labari ga wani wanda shaidarsa ke inganta, sai shi na biyun ya je wajen alƙali/sarki ya ba da shaida a kan shaidar na farko sarki ya samu ya yi riƙo da shaidarsa.[110]

Sun inganta cewa, wanda ya ga wata shi kaxai ya shaida wa alƙali cikin dare idan yana alƙaryarsu.

8.4.4 Hambaliyya:
        Dole a shaidar ganin watan azumi ya fito daga, mai hankali, adili ciki da waje. Adilin mace ko namiji babu rarrabewa. Xa ne ko bawa babu rarrabewa. Babu sharaxin faxar “Na shaida” ga mai ba da shaidar.
A kan sarki suka ce:
Idan sarki ya ƙi ya karvi shaidarsa saboda rashin sanin halin mai ba da shaidar (ba ya cutarwa). Ba wajibi ba ne zuwa ga alƙali ko masallaci, kamar yadda yake ba wajibi ba ne sai ya sanar da mutane.[111]

A kowace mazhaba daga cikin waxannan mazhabobi guda huxu da muka ambata sarki ba ƙyalle ba ne a ganin wata. Sarki ko hukuma na da matsayi biyu manya-manya.
i.                   Sanarwar ganin wata ga jama’a
ii.                 Hukunta a yi azumi a kan shaidar adilai biyu ko mutum xaya.
A kula, sharxanta jiran umurninsu (sarki da hukuma) bayan tsayuwar wata ta tabbata ba ta taso ba. Vata azumin da aka yi a kan sahihin ganin wata ba su da hurumi a ciki. Ƙin tabbatar da shaidar adilai biyu ga sarki ba hujjar hana a tashi da azumi ko a sha ruwa ba ce. Yalwataccen gani ga jama’a masu yawa ba ya buƙatar jiran wani bayani daga sarki. Tabbacin cikan Sha’aban kwana talatin (30) na wajabta azumi ko da sarki ko hukuma ba su sanar ba. Sanin ire-iren waxannan fassarori ne Hanabila (Hambaliyya) suka kakkave hannun sarki da hukuma cikin sha’anin ganin wata.

9.1   Gurbin Sarki ga Ganin Wata Ƙasarsa:
Kowane sarki na iyakokin ƙasa da iyakokin mulkinsa da ikonsa. Haka kuma, babu ƙasar da ba ta da maƙwabta a sassanta. Wannan fasalin zai dubi waxannan matsalolin da muka ambata kamar haka:

9.1.1 Ganin Wata Wuri Xaya a Ƙasa Zai Wadatar da Ƙasar Duka?
A fatawar Malikiyya sun ba da cewa ganin ƙasar sarki xaya zai wadatar da duniya. Ga yadda Albadarut Tamaama ya kawo shi:
Idan an gan shi a ƙasa/gari (xaya) ya wajaba ga jama’ar ƙasa dukkaninsu. Wannan ita ce mashahuriyar magana a Malikiyya.[112]

Fitattum malaman Malikiyya sun yayyafa wa hukuncin ruwa sun gyara masa zama. Ibn Abd Barr ya kawo ijma’in da ya kore wanan a Malikiyyance ya ce:
Ba za a duba ba zuwa ga abin da ke bayan ƙasar Harrasani da Indolos ba.[113]
Malam Ƙurxabii ya ce:
Idan ganin wasu ya kasance bayyane yake a wani wuri kuma wasu masu shaida (koma bayansu) shaidar mutum biyu (sun gani) azumi ya wajaba gare su. Malam Xanmajishuuna ya ce: “A’a ganin waxancan ba zai wadatar ga mutanen garin da aka gan shi ba sai fa idan an tabbatar da ganin ga babban sarki (Imaamul A’azam) a lokacin zai lizimci kowannensu. Domin ƙasa a haƙƙinsa (Imaamul A’azam) kamar ƙasa xaya ce domin tabbatar da hukuncinsa ga kowannensu”.[114]

Ana duba zuwa ga abubuwa da yawa gabanin a zartar da hukuncin wani gari ko wata ƙasa a kan wata ƙasa. Wasu masana sun ce, a dubi savanin mafitar rana da faxuwarta.[115] Wasu sun ce, a kula da nisan wuri daga gari zuwa gari.[116] Wasu har tsawon nisan da zai sa a yi sallar ƙasaru sun lave gare shi.[117] A kan haka Muslim ya zartas a kan hadisin Ibn Abbas cewa kowace alƙarya ta yi aiki da ganinta a ƙarshe an yi ijma’i kamar haka:
Marubucin littafin Azzalaali ya ce, (Ijma’in) da aka yi shi ne a duba tsakanin gari da gari idan akwai nisan kilo 2226 (dubu biyu da xari biyu da ashirin da shida), hukuncinsu xaya ga xauka da ajewa domin maxali’insu xaya.[118]
Idan ƙasar sarki ta kai haka ya kula, idan ba ta kai ba, babu savani a xauka tare a aje tare. Ganin wani gari zai wadatar da wani gari matuƙar ba su zarce tsawon da aka yi ijima’i a kai ba.[119]

9.1.2 Fita Wata Ƙasa Zuwa Wata Ƙasa da Azumi:
Faxar cewa, ikon sarki a ƙasarsa kawai yake. Ƙasarsa ma idan ta yi yawa ƙwarai ta zarce kilo mita (2226) kamar wata ƙasa ce ta daban. Wanda ya bar ƙasarsa da azumi ya yi wata ƙasa an faxa a cikin Tandhihul Ahkaami:
Wanda azumi ko shan ruwa ya riska a wata ƙasa, tilas ya yi azumi ko ya sha a ranar ko da ba xan ƙasar ba ne domin hukuncinsu ya hau kansa. Idan ya koma a ƙasarsa yana da azumi ƙasa ga (29) sai ya cika su bayan Idin garinsu/ ƙasarsu.[120]
9.1.3 Ganin Watan Sarkin Musulmi da Kansa:
Sarki shi ne uban kowa, kuma a gun sa za a kai kowace irin matsalar ganin wata. Malaman fiƙihu sun ce, ba za a yarda da ganin sarki shi kaxai ba.[121] In ya ga wata hukuncinsa xaya da wanda ya ga wata shi kaxai. Sanannen hadisin Kuraibu ya isa ya zama hujja a nan, lokacin da Ummil Falali ta aike shi Sham zuwa ga Mu’awiya sai Ibn Anas ke tambayar Kuraibu ya ce:
Na ce masa, ganin Mu’awiya da xaukar azuminsa bai ishe ka ba (zama hujja ba)? Sai na ce: “A’a (bai isa ba) haka dai ne Manzon Allah (SAW) ya umurce mu.[122]

A lura Amirul Muminina ne kuma Imaamul A’azam ya ga wata, kuma Sahabin Annabi (SAW), kuma xaya daga cikin masu rubuta wahayi (Alƙu’ani) ya ga wata, wani Sahabi ya ƙi ya aminta ya zavi tsayawa kan hadisi ga hukunci.

9.1.4 Dangantakar Sarki da Sallar Idi:
Ana iya savanin ganin wata ranar xaukar farko kuma tilas a gan shi da cikar Ramadan don a yi salla. Abin nema a nan shi ne, shin dole ne a yi salla tare da sarki? Ko dole ne a aje ganin wata idan ya sava da ganinsa sai lokacin da na sarki ya cika a yi salla? Sheikh Muhammad Salih Al-usaimin ya yi buxi ga waxannan matsaloli kamar haka:
Babu sharaxin neman iznin sarki ga sallar Idi. Muddin dai ganin wata ya tabbata ga mutanen gari (ƙasa) suka sha ruwa ba za a ce sai sun nemo iznin sarki domin gudanar da sallar Idi ba ko da sarki ya ce ba za a yi salla ba, haƙiƙa wajibi gare su, su tsayar da ita su sava masa saboda ba a yi wa duk wanda aka halitta xa’a domin a sava wa wanda ya yi halitta (Allah).[123]

 10.0 Kuren Ganin Wata:
Ba abin mamaki ba ne a yi kuren watan azumi ko Hajji ko waninsu. Idan Arfa ce aka hau a kan kuskure aka gabaci wata sarki zai sa a warware a je a hau wata gobe. idan an hau bayan ranar ta wuce ba a sake jawo ta gaba. Don haka ne A’isha (RA) a bayanin Mawaahibul Jalil ke cewa:
Da dai mutane sun yi kuren ganin wata, A’isha (RA) ta ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: Ranar sallarku (shan ruwanku) ranar da mutane ke shan ruwa. Ranar Layyarku ranar da mutane ke Layya.[124]

Wannan ita ce hujjar da wasu ke dogaro da ita su vata sallar Idi da Layyar waxanda suka ƙi bin sarki bisa ga abin da suke da shi na yaƙinin ganin wata. To! Ta tabbata abin nufi shi ne, idan an yi kuren ganin wata duk ranar da aka yi salla ita ce ranar salla domin taruwar mutane a kan kuskure a ranar bai cuta wa ibadarsu ba. Malam Bagwii ya ce, wasu masana sun fassara wannan hadisi da cewa:
Ma’anarsa shi ne, a yi azumi a sha ruwa tare da mutane da mafi girman mutane.[125]

Abin da ake nufi da kuren ganin wata shi ne, haxuwar jama’a a kan adadin kwanan wata su wayi gari a kan kuskure, ko a samun shaidar ƙarya a hau a kanta bisa kuskure, ko sarki ya yi hukuncin a kan kuskure. Waxannan duka suna cikin abubuwan da Allah Ya yi alƙawalin da ba zai kama bayi da su ba.[126] Idan azumi ne sarki zai ba da umurnin a ranka kamar yadda ya sha faruwa a Saudiyya da ƙasarmu.[127]

11.0 Ƙasar da Babu Sarkin Musulmi Yaya Za su yi?
Babu shakka, tun rushewar daular Musulmi ta ƙarshe a shekarar 1924 al’umma suka shiga cikin duhu a kan harkokin addininsu. Musulmin da ke wata ƙasar da ba ta Musulunci ba irin Nijeriya idan an bar su da shugabanninsu na asali kamar yadda aka yi wa Nijeriya[128] Sheikh bn Baz ya ce:
Xaixaikun musulmi (da aka tarwatsa ko ba su da ƙasa) sun samu su xauki azuminsu suna masu koyi da Alƙalansu/Sarakunansu su sha ruwa tare da su domin faxar Manzo (SAW): “Azuminku ranar da kuke azumi shan ruwanku ranar da kuke shan ruwa, ranar layyarku ranar da kuke layya”.[129]

A bayyanin Annawaadiru an ce:
Idan musulmi sun kasance a wurin da babu imaami sarkin musulmi (na musulunci) wanda zai jagoranci al’amarinsu cikin xaukar azumi da shan ruwa ko ya kasance tare da wanda zai iya aikata haka su dogara gare shi, wanda ya tabbatar da ganin wata da ganin kansa ko da ganin wanda ya dogara gare shi sai ya yi azuminsa a kan haka, ya sha ruwansa a kan haka….[130]

12.1 Ko Sarki Ya Samu Ya Kafa Kwamitin Ganin Wata?
Bisa ga nassoshin ayoyi da hadisai da fahintar mazhabobi da magabata masana wata nemansa ake yi. Abin da ake nema ba mutum xaya za a sa ba. Wata ana tabbacin shaidar ganinsa abin da ake buƙatar shaida, mutum xaya bai shaidun kansa. Ibadojin da suka ratayu ga ganin wata mafi yawansu wajibai ne. Abin da wajibi ba ya tsayuwa sai da shi shi ma wajibi ne. Ƙasar Musulunci ba unguwa ko gari xaya ko ƙauye ba ce. Garuruwa da yawa za su taru su yi ƙasa kuma sarki a gari xaya zai yi cibiyar mulkinsa[131] sauran wuraren da ba cibiya ba dole a sa na’iban sarki da waziransa da hakimmansa da alƙalansa. Wannan yawaitar ta wajabtar da kafa wata hukuma ko wasu jama’a na musamman da za su tsare masa wani yanki daga cikin yankunan da ke ƙarƙashinsa.[132] Ƙasarsa za ta iya kai faxin adadin tsawon da ake samun savanin vullowar rana da wata, waxannan duk dalilai ne daga cikin dalilan Musulunci da ke sa sarki naxa mashawarta da wakilai daban-daban.
Binciken da muka yi kwanakin baya ya tabbatar da samuwar kwamitocin ganin wata a ƙasashen Musulunci a ko’ina.[133] Akwai shi a cibiyar Musuluncin duniya Saudi Arabia da sauran ƙasashen Larabawa da Asiya da Turai da Afirka. Matuƙar dai mutanen da ke ciki, adilai ne, baligai, masu hankali, ‘yantattu, mazaje, masana al’amarin wata sun kasance kamar shaidar adilai ne ga ganin wata ko jama’a masu yawa. Idan dai sun yi aikinsu kamar haka:
i.                   Sun yi ido-da-ido da waxanda suka kawo shaidar cewa sun ga wata.
ii.                 Sun zaunar da su, suka tantance su tsakani da Allah.
iii.              Sun gamsu da abubuwan da suka ji da bakunan shaidunan.
iv.               Sun gamsu da mutuncin shaidun ga tantancewar da suka yi.
v.                 Su (wakilan sarki) sun gamsu da cewa lallai wata ne aka gani da ido ƙuru-ƙuru ba da shamaki ko dodon bango ba. Wato ganin ido ba na hisabi ba.

Samun waxannan abubuwan biyar ba a jin kunyar fuskantar kowane musulmi a kan kowace irin Mazhaba yake dogaro da ita ga tabbacin tsayuwar wata. Bisa ga bayanan magabata da muka tattavo can da nan, za mu ce:
i.                   Azumi ya wajaba ga waxanda suka kawo shaidar ko da Sarki ya yi watsi da shaidarsu.[134]
ii.                 Azumi ya wajaba ga ‘yan kwamitin Sarki ko da Sarki ya yi watsi da rahotonsu da suka samu ga waxanda suka tantance.[135]
iii.              Azumi ya wajaba ga wanda duk ya yarda da kwamitin ko da Sarki ya ƙi karvar rahotonsu.[136]
iv.               Azumi ya wajaba ga duk wanda ya tsinci rahoton ga bakin ‘yan kwamitin ko da Sarki ya ƙi yin sanarwa a yi azumi ko a aje azumi.[137]
v.                 Azumi ya wajaba ga duk wata ƙasa da ke kusan wannan ƙasar wadda suka haxa maxala’i xaya da ita in sun samu rahoton.[138]

Idan aka lura kowane xaya daga cikin waxannan abubuwa biyar yna da madogara daga cikin hujjojin da suka gabata na shaidar ganin watan mutum xaya ko adilai ko jama’a masu yawa.

12.2 Ko Sarki ya Samu Dangane Rahoton Kwamiti?
Ga tsarin shugabancin Musulunci Sarki shi ne wuƙa shi ne nama. Idan shari’a ta kafa wata doka a kan kowa, to, sarki na ciki kamar kowa.[139] Bisa bayanan da muka ga sun gabata, damar da sarki yake da ita na dangane kwamiti ko ya yi watsi da rahotonsu shi ne, idan ya tabbatar da cewa:
Kwamitin ya shiga wani hali daga cikin halayen da ke sa a ƙi karvar shaidar Musulmi kamar:
i.                   A same su sun yi ridda su duka (Allah Ya tsare su Ya tsare mu).[140]
ii.                 A same su cikin mariisa su duka (Allah Ya kiyaye su Ya kiyaye mu).[141]
iii.              A tabbatar da kasancewar su mahaukata (Allah Ya tsare mu) yayin da suke gudanar da aiki ko ba da rahoton.[142]
iv.               A tabbatar da ba su zauna da kowa ba, ba da rahoton ƙarya suka yi.[143]
v.                 A tabbatar sun karvi rahotonsu cikin watan Sha’aban tun Ramadan bai kama ba.[144]
vi.               A tabbatar da shaidun da suka gabatar duka babu wanda shari’a ke yarda da shi.[145]
vii.            A tabbatar da ko da sun ba da rahoton tabbacin ganin wata a ranar, lokacin da suka haƙiƙance ganin wata rana ba ta faxi ba, kuma a cikin ranar ake son tabbatar da tsayuwarsa.[146]
viii.         A tabbatar da ba da ganin ido suka ba da shaida ba, bugun ƙasa aka yi ko hisabi ko ‘yan leƙe-leƙen zamani na ilmin wuce Allah da sani.[147]
ix.               A tabbatar da game baki aka yi da su, an ba su lokacin da ake son a yi salla da lokacin da ake son a xauki azumi. Su kuwa suka game baki da shaidu a kan haka, ko suka jirkita shaidar zuwa son ransu.[148]
x.                 A tabbatar da ba a cikin ƙasarmu suka yi zaman karvar rahotonsu ba, a wata ƙasa ce can daban, ba su san shaidu ba, shaidu ba su san su ba.[149]

Idan za a yi mini uzuri waxannan abubuwa guda goma na ciro su ne, bisa ga ingantattun nassoshi da ke bayanin ganin wata da na sarrafa a wannan takarda. Kowanne daga cikinsu yana da madogara a nassi sahihi ga dokokin ganin wata a shari’ance. Idan duka abubuwan goma ko wasu daga cikinsu ko xaya daga cikinsu ya tabbata, Sarkin Musulmi na da damar dangane shaidar kwamitin amintattunsa na ganin wata, Musulmi na da haƙƙen jin dalilan da sarki ya dogara da su na dangane kwamitinsa da watsi da rahotonsu.[150]

13.0 Matsalar da Sarkin Musulmi Ke Fuskanta a Ganin Wata:
        Wannan matsala ba ta tattaunuwa sosai sai an waiwayi matsayin ƙasar da muke a shari’ance da siyasance. Bisa haƙiƙanin gaskiya, ƙasarmu ba bisa tsarin shari’a ake gudanar da ita ba.[151] Don haka, tsarin dokokinta da suka kafa sarakunanta a kan siyasar ƙasa an ka kafa su, ba a kan dokokin shari’a ba.[152] Don haka, hukuma ke riƙe da ragamar sarautunmu ita ke naxi ita ke warware (cire) su.[153] Daulolin da ke cin gashin kansu ƙarƙashin jagorancin sarakunan Musulunci suna da yawa a ƙasarmu.[154] A tsarin wannan fiƙihun matsalolin da sarkin Musulmi zai fuskanta sun haxa da:
i.                   A ƙa’idar nassin shugabanci Sarkin Musulmi shi ya kamata ya zama Amirul A’azam ko Khalifa amma akwai sarakunan Musulunci masu irin matsayinsa a ƙasa xaya. Da su sarakunan sun haxa kai sun zavi babba daga cikinsu suka mayar da al’amarin wurinsa da abin ya fi.[155]
ii.                 Matsala ta biyu kowane sarki daga cikin sarakunanmu na Musuluncin yana da ‘yancin kafa nasa ‘yan kwamitin ganin wata bisa tsarin shari’a. Haka kuma, ganin watan jama’arsa a shari’a yana wajabtar da azumi a faxin ƙasarmu da maƙwabtanta. A shari’ance, kowane sarki na da haƙƙi daga cikin haƙƙoƙin ganin wata a ƙasarsa.[156] Babu laifi sarakuna su yi cibiya wuri xaya da za a sanarwar ganin watan da ya tabbata a kowane gefe na ƙasar nan.[157]
iii.              Matsala ta biyu ita ce karkasuwar Musulmi zuwa Mazhabobi da Xariƙoƙi da Ƙungiyoyi da Nahiyoyi (Kudu da Arewa) kowannensu da irin nasa tsarin shugabanci da shugaban da yake yi wa xa’a.[158] Abin ya kankama har ƙungiyoyin ganin wata an fara samu a ƙasar nan. Abubawan da suka yi tsauri kowane vangare ya xauki nauyin dubin wata da kansa. saboda rashin gansuwa da abin da ke faruwa ga Majalisar Sarkin Musulmi.[159] A ƙarshe, sai kowane vangare ya xauki nauyin yi wa jama’arsa sanarwar ganin wata da kansa. Babu shakka a shari’ance, sarki ke da wannan damar ba kowa ba.[160] Kasawar da tsarin ya yi, shi ya haddasa wannan matsalar. Yadda za a magance wannan matsalar shi ne, a faxaxa kwamitin Majalisar Sarkin Musulmi domin samun gurabun zaunar da waxannan vangarorin a ciki.[161]
iv.               Ra’ayoyin ganin wata uku ke ga Musulmin Nijeriya. Na farko, akwai masu ra’ayin bin nassoshin magabata sau-da-ƙafa na tabbatar da ganin ido ƙuru-ƙuru. Na biyu, akwai masu ganin a bi kimiyyar zamani. Na uku, akwai masu ganin dole a bi ganin Makka musamman ga abin da ya shafi Layya. Idan majalisa ta buxe ƙofofin sauraron waxannan a kowane lokaci buƙata ta taso za a rage rarrabuwar kanun musulmi.[162]


14.0 Ganin Wata da Haxin Kan Musulmi:
Allah Ya umurce mu zama abu xaya kar mu rarraba.[163] Ya tabbatar da rarrabuwarmu na rage muna ƙarfi.[164] Manzon Allah (SAW) ya tabbatar wa al’umma taimakon Allah na nan ga haxin kansu.[165] Tsananin kishin Musulunci ya sa malamai ke tsananta a haxu a yi azumi tare, a sha ruwa tare. Duk da haka, a san haxin kai da Allah da ManzonSa ke kira shi ne, a kan littafin Allah da sunnar Manzon (SAW).[166] Littafin Allah Ya wajabtar da azumi ga ganin wata Manzo ya tabbatar da haka,[167] ƙin bin wannan umurni ba zai kai mu ga tudun-mun-tsira ba. Ga abubuwan da shari’a ta tabbatar a kan haxin kan ganin wata:
i.                   Musulman duniya sun damu da a samu haxin kan musulmi na ganin wata a duniyarmu  musamman ga abin da ya shafi Azumi da Hajji.[168] Majalisar Malamai ta Duniya a Makka[169] da Majalisar Masana Fiƙihun Duniya[170] sun ba da fatawowinsu a rubuce na tabbacin ba a tava haka ba tun zamanin Manzon Allah (SAW) ya zuwa yau shekaru fiye da dubu xaya da xari huxu. Yadda Allah Ya fitar da watansa haka nan yake son bayinSa su yi ibadarSa da ganinsa.[171]
ii.                 Da musulmi za su haxe kai ko da a Hajji ne a bi ganin watan Makka da haxin kanmu ya yi.[172] Manyan Shehunan Malaman Makka sun ba da fatawa a kan cewa, Allah da Manzonsa ba su tilasta wa musulmi bin ganin watan Makka da Madina ba ko wata ƙasa.[173] Sun tabbatar da cewa, kowa ya bi ganinsa da ya tabbatar da ingancinsa.
iii.              Domin tabbatar wa duniya haxin kanmu yana da kyau musulmin duniya su aje ganin watan Layyarsu su yi wa Arfa xa’a sai an sauko idan ganin watansu ya yi canjaras da na Makka a aikin Hajji.[174] A kan wannan musulman Nijeriya da yawa na Arewa da Kudu suka ba da goyon baya.[175] Masana duniyar musulmi ma sun ba da fatawa a kan cewa haka ba ta taso ba. Da Allah na nufin irin wannan haxin kai da Ya tabbatar da shi a littafinSa ko a bakin ManzonSa. Da ganin wata ya ce a yi koyi ba da tsayuwar Arfa ba.[176]
iv.               Ya kai xan’uwana! Da Allah na son taruwarmu a lokaci xaya, a wurin ibada xaya, a rana xaya, domin haxin kanmu, da Ya ambaci haka a littafinsa ko Ya shirya yanayin duniyarsa yadda zai dace da irin wannan tunani.[177] Yadda Ya tsara duniyarSa a lokuta mabambanta, haka Yake son a gudanar da ibadojin da Ya rataya a kan lokutan. Guji aiki da ƙila-wa-ƙala da hankalin tuwo, bi nassi shi ne tafarkin haxin kai da tsira gobe ƙiyama.

15.0 Dangatakar Makka da Sarkin Musulmi a Ganin Wata:
Makka ita ce alƙiblar kowane musulmi a duniya. Wanda duk Allah Ya xora wa jagorancin musulmi samun kyakkyawar alaƙa da ƙasar Saudiyya abin so ne gare shi. Ƙasar aka tayar da Manzo (SAW). A ƙasar aka yi masa wahayi. A ƙasar aka fara shimfixa shari’a. A ƙasar aka fara duk wani aiki da shari’a ta wajabta ko sunnanta. Dujjal ba ya shiga ƙasar.[178] Ba a cin ƙasar da yaƙi.[179] Cikin ƙasar kaxai ake Hajji da Umra. Dole duk masallaci ya fuskanci ƙasar ga sallarsa.[180] Duk da haka, babu nassin aya ko hadisi sahihi da ya wajabta koyi da ayyukan ƙasar, sai dai an wajabta koyi da littafin Allah da aka saukar a ƙasar da Manzon da aka haifa a ciki. Allah! Muna ƙara godiya.
To! Ganin watan Makka bai zama hujja ga sauran ƙasashen duniya kamar yadda ganin watan sauran ƙasashe ba ya zama hujja a kan Makka.[181] Ƙasar Yemen da take baki da hanci ga ƙasar Saudiyya kowa ganin watansa daban.[182] Idan Sarkin Musulmi ko wani talakansa ya je Makka da azuminsa a baki wanda ya xauka bisa ganin watan ƙasarsa ya aje azuminsa da Makka zai yi koyi domin hukuncin ƙasar ya hau kansa. Haka idan mutanen Saudiyya suka shigo ƙasarmu da azumin da suka xauka daga Saudiyya da ganin watan ƙasarmu za su yi aiki ga aje azumi.[183] Idan aka sami kuskuren azumin ƙasa ga ashirin da tara (29) a ranka bayan salla. Wanda kuma duk ya je da azuminsa ga baki bisa sahihin ganin watan ƙasarsu idan ya cika talatin (30) a kowace ƙasa dole ya sha ruwa domin ba a azumi talatin da xaya (31).[184]
Irin iko da damar da shari’a ta bai wa Sarkin Makka ga xaukar azumi  da ajewa irinsa ta bai wa Sarkin Musulmi na kowace irin al’umma. Yadda ba a dogara ga Makka ga lokutan salloli biyar na farilla ba, haka ba a dogara gare su ga ibadojin da aka rataya ga ganin wata ba.[185] Yadda ake iya yin kuren Arfa a sake in da tazara, haka za a iya yin kuren Idi a sake in da tazara.[186] Yadda za a iya kuren ganin wata a Makka a yi ranko haka za a iya yin sa a kowace ƙasa.[187] Ba a sharxanta wa Sarkin Musulmi bin Makka ga ganin wata ba, ba a kuma sharxanta masa tambayarsu labarin watan da za a yi ibada a ƙasarsa ba.

16.0 Yaya ya Kamata Sarkin Musulmi ya yi Sanarwa?
Magabata ba su da nassin da ya zo da kaifiyyar yadda sarki zai yi sanarwa ba ƙarara.[188] Hadisai dai sun tabbatar da shi ke da haƙƙin sanarwa. Rashin sanarwarsa ba ta wajabtar da barin xaukar azumi in wata ya tabbata.[189] Sanarwarsa ba ta wajabta a yi azumi ko a yi salla in wata bai tabbata ba. Don haka, ingancin sanarwar Sarki shi ne tabbatar da tsayuwar wata bisa haƙiƙa.
Yadda ake samun kai da komon rikice-rikicen ganin wata a Nijeriya babu wata ƙasa ta duniya da ke da shi. Masana addini sun ce, ana tilasta wa mutane doka gwargwadon abubawan da suka haddasa na fajirci.[190] Don haka, da za a sauya tsarin sanarwar ganin wata da Sarkin Musulmi ke yi, zuwa haka:
A fara buxe sanarwar da jawabin Sarki:
i.                   Sarkin Musulmi ya gabatar da babban sarkin da aka ga wata ƙasarsa.
ii.                 Sarkin da aka ga wata ƙasarsa ya gabatar da Hakimin da aka gani a garinsa.
iii.              Sarkin ko Hakimin ya gabatar da waxanda suka ga wata, a gan su, a ji muryoyinsu, a ji shaidarsu.
iv.               A gabatar da kwamitin da ya tantance su a gan su, a ji muryoyin yadda suka tantance su.
v.                 A ƙarshe, sai Sarkin Musulmi ya tabbatar wa musulmin ƙasarsa wata ya tabbata.
Idan aka bi waxannan matakai a gidajen Rediyo da Talabijin, duniya ta ji, ta gani, an yi wa rikincin ganin wata kabari a Nijeriya da yardar Allah. Duk ‘yan ƙorafe-ƙorafen da musulmin Nijeriya ke yi na rashin gamsuwa da ganin wata suna cikin waxannan matakai biyar da muka ambata. Idan aka yi haka, duk wata kafa da shaixan zai buxe wa wani ko wasu na jayyaya an toshe ta. Haka kuma, masu ganin a dogara ga na’ura da masu ganin a dogara ga wata ƙasa duk wannan shaidar ta isa ta hujjace su ba tare da an raba kan musulmi ba.

17.0 Sarkin Musulmi da Fiƙihun Ganin Watan Zamani:
A yau duk wani musulmi da ke raye ya san da cewa, ya zo zamanin da ilimi ya yawaita, fahintoci sun yawaita, kimiyya na ja-in-ja da aƙidojin addini Musulunci. Ga masana ilmin Taurari, da Falaƙai, da Hisabi, da Na’urori daban-daban, da aka sha ayyukan rayuwa da su ana dacewa. Masu kimiyya kan ayyana ranar da za a iya dacewa da ganin wata a kowace nahiya ta duniya. A bincikensu, akwai lokutan da ba za a iya ganin wata ba da ido ƙuru-ƙuru a wata nahiya, sai dai a wata, saboda dalilai na kimiyya da bincikensu ya tabbatar. A matsayin sarki na shugaban musulmi, yana da haƙƙen ya dube su da idon basira. Idan haka ne, su kuma tilas su yi wa sarki uzuri ya auna bincikensu da nassoshin shari’a, domin tabbatar da su, ko sake bitar su.
Addini bai soke ci gaban da kimiyya ta haifar ba, sai dai, ya yi mata shinge/ iyaka da nassoshin ayoyi da hadisai da ba a son a tsallake su. Mene ne laifin Sarkin Musulmi idan ya ce, a tsaya wurin da shari’a ta ce mu tsaya? Manzon Allah (SAW) ya faxa:
        Daga Raja’a xan Haiwata ya ce: 
        Lallai Annabi (SAW) ya ce: Haƙiƙa     abin da nake yi wa al’ummata tsoro shi ne gaskatar da al’amarin taurari (masu amfani da ilimin taurari).[191]

Manzon Allah ya tabbatar da cewa:
“Allah ya yi waxannan taurari domin abubuwa uku: ƙawata sama’u da jifar shaixanu da zamansu alamomin da ake gane hanyoyi (cikin dare). Wanda duk ya sauya amfani da (su) taurari a wanin waxannan abubuwa uku, ya yi kure, kuma ya tozarta ladarsa.[192]

        A ƙarshen al’amari dai mun ji yadda Manzon (SAW) ke umurtar mu da cewa:
Ku ƙaryatar da masu ilimin taurari ko da sun faxi gaskiya.[193]

        Waxannan sun tabbatar muna da cewa, ganin ido na wata shi ake nema ba hisabi ba. Wajibi ne a ƙaryata masu hisabi ko da sun yi canjaras da abin da ido ya tabbatar in ji Annabi (SAW). Babu hujjar tsayawa a saurari wata fatawa ta inganta hisabi ko kimiyya a fiƙihun ganin wata. Sarkin Musulmi na da damar kore duk wani rahoton ganin wata na hisabi ko ilimin taurari ko wata na’ura ta can daban. Idan ganin ido ya tabbata, ko masu kimiyya sun ce, ba a gani, iliminsu ne bai kai can ba, na Allah Ya wuce can, a bi Allah a sa musu ido.
        A kula, duk da ci gaban kimiyyar yau, babu ƙasar da ba ta da kwamitin ganin wata na ido. A Saudiyya Ummul Ƙura Calendar tun shekarar 1950 ta samu sauye-sauye, a 1973 aka sake gyare-gyarenta, saboda kurakurai da aka samu. A shekarar 1998, aka sake gyara a 2002 abin ya sake dagulewa fiye da na 1950-1972.
Don haka suka dawo rakiyar ilimin taurari suka tabbatar da ganin ido kawai.[194] Wata sabuwar matsalar kimiyya da za ta riski sarkin musulmi ita ce, idan rana ta kama wata gabanin faxuwar rana, gobe xin wannan rana nawa ga wata? Idan rana ta kama wata ranar 29 ga watan musulunci?[195] Waxannan matsalolin duk ya kyautu sarki ya shirya musu tun ba su zo suka sake ruxa masa mutane ba.[196]
18.0 Hanzari:
        Sarkin Musulmi na kowane zamani, na cikin kowace irin al’umma yana da alfarmar da ya kyautu muminan zamaninsa su sani. Na farko, ya kyautu a sani cewa, mutane ke ganin wata, su gaya wa wakilan sarki, ba sarki ke ganin wata ya ba su labari ba. Idan sun faxi gaskiya, sun taimaki jama’a, kuma sun sami lada. Idan suka faxi akasin gaskiya, ba zai cuta wa azumin mutanen da komai ba, ga ladarsu, da ibadarsu. Sarkin Musulmi da jama’arsa ba za su cutu da shaidar ƙarya da wani maƙaryaci zai yi a kan ganin wata ba.
        Yana da kyau musulmi su sani cewa, Manzon Allah (SAW) bai tava ganin watan azumi ba, ya ba da labarinsa. Dukkanin azumin da ya yi, gaya masa labarin an ga wata aka yi, ya aminta, ya ba da umurnin a yi azumi. Nagartattun sahabbansa huxu da suka khalifanci daular Musulunci, babu wanda ya ga watan azumi da kansa, ya ba da labarinsa. Da dole ne sai kowa ya ga wata da idonsa, da su za a fara gwada wa. Da ganin wata wata martaba ce, wa zai riga su samun ta? Babu shakka, Manzo (SAW) ya yi azumi ashirin da tara (29) fiye da yadda ya azumci talatin. Cikin waxannan azumi (29 ko 30) kowane aka doge ana yi har tashin ƙiyama ba abin damuwa ba ne, domin babu nassin da ya ce, ba a dawwama a kan xaya, ko kada a dawwama a kan xaya, ko dole a surka, a kai, a kai.
Maganin rikice-rikicen ganin watan azumi shi ne, yin tawagar mutane da yawa zuwa nemansa. Wannan shi ya taimaka wa ƙasashen Pakisatan da Indiya da Malaysia da sauran ƙasashen musulmi na Asiya. Sarkin Musulmi shi ne makwantar kowace magana ta ganin wata. Taimakon da za mu yi wa musulmi shi ne, kowane gari da ƙauye da birni su fita ayari – ayari domin neman watan azumi ranar duban farko.

Naxewa:
        Sarkin Musulmi na kowace al’umma Uba ne ga jama’arsa, babu wani sha’ani na addininta da za a aje shi gefe xaya. A shari’a, sarki ke da haƙin sanarwar ganin wata da ba da umurni a xauki azumi. Yana da damar naxa amintattunsa su tantance masa rahoton ganin wata. Yana da hurumin tabbatar da ganin wata ko da na mutum xaya ne. Duk wata Mazhaba da Xariƙa da Ƙungiya da ke zamaninsa ya shamakance ta ga duk wani al’amari na ganin wata. Dole a saurare shi, kuma a yi masa xa’a nassi ne ingantacce. A wajen mabiya kuwa, suna da tazarar da shari’a ta ba su na ganin wata tare da Sarkin Musulmin zamaninsu. Da su da Sarkin Musulmi shari’a na cewa:
i.                   Wanda ko waxanda suka tabbatar da ganin watansu sahihi ne ko da sarki bai karvi shaidarsu ba azumi wajibi ne gare su da waxanda suka yarda da ganinsu. A nan, sanarwa ce ba su da ikon yi, ko ba da umurni ga sauran jama’a, wanda ya yarda da su shari’a ba ta hana shi ga xauka ko ajewa ba.
ii.                 Sarkin Musulmi kawai, ko wakilinsa ke da ikon tabbatar da ganin watan mutum xaya, ko adilai biyu. Duk da yake, su, dole su yi, azumi ko da ya soke shaidarsu.
iii.              Ganin watan mutane da yawa ba ya buƙatar tabbatarwar Sarkin Musulmi da umuurninsa, domin abin ya zama ruwan dare.
iv.               Da gani ido ƙuru-ƙuru kawai sarki ke da dama a shari’a ya yi sanarwar tsayuwar wata. Idan abin da Sarkin Musulmi ya dogara gare shi ya sava wa nassi na ganin ido, ya hau wata fatawa ba ita ba, musulmi na da damar bin fatawar Annabinsu ga azuminsu, da sallarsu, su roƙa wa sarkinsu gafara da shiriya ga Ubangijisa.
v.                 Babu wani, ko wasu mutane, ko wata hukuma, da ke da iznin shata ranar da za a xauki azumi da aje shi, face da ganin watan ido ƙarara kuma ƙuru-ƙuru. In ba da shi aka dogara ba, sanarwar kowa abar danganewa ce a bi abin da ya tabbata ga nassin Ƙur’ani da Hadisi.
vi.               Abubuwa biyu suka hau kan Sarkin Musulmi a sha’anin ganin wata, sanarwa da umurni. Su kuma mabiya abu biyu ke kansu, Gani da shaidarwa gaban sarki. Xaukar azumi da aje shi na a kan duk wanda ko waxanda suka ga wata sahihin gani ƙuru-ƙuru da waxanda suka aminta da ganinsu.
vii.            Sarakunanmu na Nijeriya matsayinsu xaya da Sarkin Musulmi ga musulman da ke ƙarƙashinsu. In sun tabbatar da ganin wata hukuncin da suka yi ya kama duk wani musulmi da ke ƙarƙashin riƙonsu. Aza wa Sarkin Musulmi nauyin sanar da ganin wata, shi ya fi dacewa, domin tabbatar da haxin kanmu da zaman lafiyarmu da inganta jagorancin shugaban musulmi. Allah Ya haxa kanmu. Amin!                    
Manazarta:
Albaani, Muhammad Nasiruddin (1985) Irwaa’il Ghaliili fi takhariiji Ahaadisi Munaaris Assabiili, Xabaƙatis Assaaniyati, Maktabatil Islaamii.
Albaanii, Muhammad Nasiruddin, (1988) Swahiihu Sunani Attirmizii, Maktabatil Mu’aarif Riyadh.
Albaanii, Muhammad Nasiruddin, (1989) Swahiihu Sunani Abi Daawud, Maktabatil Islaami, Lebanon.
Albaanii, Muhammad Nasiruddin, (1989) Swahiihu Sunani Alnisaa’ii, Maktabatil Islaamii.
Albaaji, Alƙaadhi Abi Walid Sulaiman bn Khalf bn Sa’ad bn Ayuuba, (1999) Almuntaƙa Sharhu Muwaxxa’i, Darul Kutbul Islamiyya.
Albassaami, Abdullahi bnn Abdur Rahman, Tauhhiihul Ahkaami Min Bulugul Maraami, Juzu’i na 3.
Albukhaari, Imam Muhamamd bn Isma’iila, (1997) Swahiihu Bukhaari, Darus Salam Lin Nashra wat Taurii’i Alriyaadh.
Addasuuƙii, Shamsuddein Muhammad Arafata, Haashiyatul Dasuuƙii Alaa Sahrhil Kabir.
Alfark, Ƙadhii Abu Ya’alii Muhammad bn Husaini (1994) Ahkaamul Sulxaaniyya, Lebanon.
Algamaarii, Ahmad bn Sadiiƙ (1999) Taujiihil Auzaari li Tauhiidil Muslimiina fis Swaumi wal Ifxar, Daarun Mafaa’is
Alharshiyyu, Muhammad bn Abdullahi bn Ali (1997) Haashiyatul Harshii, Juzu’i na 3.
Al-indolosiyyu, Imam Ƙaadii Abdul Walid Muhammad bn Ahmad bn Rushud Alƙurdabiyyu (2001) Bidaayatul Mujtahidi wa Nahaayaatul Muƙtasidi
Aljaziirii, Abdulrahman (2001) Alfiƙhu Alaa Mazaahibul Arba’ati Lil Ibaadaati, Daarul Munaaraa.
Al-Maawardi, Abil Hassan Aliyu bn Muhammad bn Habiibul Basrii Albagdaadi, Ahkaamul Sulxaaniyyati wal Wilaayatil Addiniyya,
Almagribii, Alƙaadhi Allaamatu Alhassan bn Muhammad bn Sa’id, Albadarut Tamaamu Sharhi Buluugul Maraamu Min Adillatil Ahkaami,
Almakkiyyu, Muhammad Sulxan Alma’asuumii Alhujandiyyu, Halil Muslim Multazimu bit Tibaa’i Mazhabun Mu’ayyanati Minal Mazaahibil Arba’a?
Almalkanuwwii, Imam Abdul Hayyi (2000) Alfakkud Dawwaar fii Ru’uyatil Hilaali bin Nihaari, Daaru bn Hazan.
Almalkanuwwii, Imam Abdul Hayyi (2000) Alƙaulul Manshuur fii Hilaal Khairus Shuhuur, Daarul bn Hazam.
Almuhanaa, Aliyu Sulaiman (1986) Masaa’ili Imam Ahmad bi Riwaayaati Ibnihii Abdullahi.
Almuƙaddissii, Shamduddin Abdur Rahman bn Muhammad ibn Ahmad bn Ƙudaama, Almugnii li Shaikhul Kabir, Juzu’i nan 4.
Al-Osaimin, Shaikh Muhammad bn Saaleh (2010) Aljaami’ul Ahkaami: Fiƙihus Sunna, Juzu’i na 2, Daarul Al-Ghad Al-Gadeed, Egypt. Almansoura.
Alsajsataaniyyu, Abii Daawud, Masaa’ili Imam Ahmad.
Al-Usaimin, Muhammad Assalih (1996) Sallar Idi: Tambayoyi (54) da Amsoshinsu a cikin Sallar Layya da Azumi, Fassara zuwa Hausa Aliyu M. Bunza.
Assaalim, Abu Malik Kamal bn Sayyid, Sahiihu Fiƙhus Sunna wa Adillatihi wa Taudhiihul Mazaahibul A’imma, Juzu’i na 2.
Assubaƙiyyu, Aliyu bn Abdulkaafi (2000) Al’alamil Manshuuri fi Isbaatia Shuhuuri, Daaru ibn Hazam, Lebanon.
Attanwakhii, Sahanuun bn Sa’iid, (1986) Almudawwanatil Kubraa.
Bin Baaz, Abdul Aziiz bn Abdullahi, (2002) Fatawaa bn Baaz Idaaratul Buhuusul Ilmiyya wal Iftah, Riyadh.
Birnin Kabi, Umar bn Isa (2001) “Udhhiyyaati Nisbati Ahlil Nijeriyya Yauma Yaƙuumul Hujjaaji bi Arafatin.” Mujalla Raddi zuwa ga Abdurahman Jega, ba a gabatar da ita ko’ina ba.
Boxinga, Hassan S. (2001) “Savanin Ganin Wata a Tsakanin Ƙasashen Duniya da kuma Ibadun Azumi, Hajji, Sallar Idi da Yanka, Mene ne Mafita?” Muƙala da aka gabatar ga Jamaa’atul Muslimiina, Sakkwato.
Bn Aabidiina, Muahmmad Amiinu (2000) Tambihul Gaafili wal Wasnaani alal Ahkaamil Hilaali Ramadhana, Daarul ibn Hazam, Lebanon.
Bn Ƙudaama, Abii Muhammad Abdullahi bn Ahamd (1992) Almugnii, Alƙaahira.
Bn Taimiyya, Shaikhul Islam Ahmad (1995) Risaalatil Fiƙhis Swiyaami, Daarul Fikr.
Bunza, Aliyu Muhammad, Mukhtar U. (1994) Ganin watan Azumi (Laluben Haƙƙin Lamarinsa Cikin Hadisan Annabin Rahama (SAW).
Bunza, Aliyu Muhammad (2001) Haxuwar Idin Layya da Tsayuwar Arfa, wallafar Milestone Information & Publishing House, Sokoto.
Bunza, Aliyu Muhammad (2009) Me Ya Haxa Layya Da Arfa A Shari’ance” Takarda da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa na Jama’atu Izaalatil Bidi’a wa Iƙaamatis Sunnati (JIBWIS), Bauchi.
Bunza, Aliyu Muhammad (2009) Inkaarin Yanka Layya Goma ga Zil-Hajji: Nassi ko Tawili? Muƙalar da aka gabatas a taronƙara wa juna sani na ƙasa a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Dabagin Arxo, Usman bn Muhammad (2000) “Warware Matsalolin Idi da Layya Dangane da Savanin Ganin Wata Tsakanin Ƙasar Saudiyya da Nijeriya”. Mujalla ba a gabatar da ita ko’ina ba.
Xanfodiyo, Shehu Usmanu: Bayan Wujuub Al-Hijra Alal ‘i-ibaa, Khartoum University Press.
Gyalgyal, Mujtaba, Muhammad Bala (2001) “Adillati alaa Iƙaamaamati Iiidi wal Udhhiyyaati fi Yaumil Aashiri min Zulhajj wa lau lam Yaƙihul Hujjaaji bi Arfati.” Mujalla ba a gabatar da ita a ko’ina ba.
Hasshaamii, Aliyu, Wujuubir Rijuu’i ilal Kitaabi Was Sunna.
Ibn. Daƙiiƙil Al’iidi, Muhammad bn Aliyu bn Wahaab bn Muxii, (2010), Sharhu Ummadatul Ahkaami, vol. 1, Daarul Alzaujiyyu Alkhaahira.
Ibn. Taimiyya, Shaikhul Islam, Majmuu’ul Fatawaa
Isbir, Hasan Ahmad (2000) Arba’u Risaa’ili fii Hilaali Khairus Shuhuur, Daaru ibn Hazam.
Jalingo, Ibarhim Jalu Muhammad (2009) “Ru’uyatil Hilaali fil Islami wa Tahaddiyaatuha li Wahdatil Ummatil Muslimati fii Nijeeriyaa.” An gabatar da ita a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Jega, Abbas Muhammad (2001) Annaarul Mus’ara li Taharriƙil Mubtada’iina wal Mulhidiina fi Sha’ani Salaatil Idaini wa maa Yata’allaƙu bihimaa, babu wurin bugu.
Jega, Abdurrahman Isa (2001) “Mushkilatul Udhhiyya wa Taƙadiimuhaa Ƙablal Wuƙuufi bi Arfati,” Mujalla ce ba gabatar da ita ko’ina ba.
Jos, Sheikh Alhassan Sa’id (2012) “Wane ne yake da haƙƙin sanar da watan Azumin Ramadan?” Cikin, Mimbanin Sunna, JIBWIS.
Jos, Alhassan Sa’eed Adam (n.d.) An Advice to the Intelligent Scholar (A true and clear Islamic view on Moon Sighting) IBZAR, Publishing, Jos.
Kuci, Musa ibn Ibrahim, “Risaalatis Sugraa fi Bayaani Ba’adi maa Yaƙa’u fi Duluu’il Hilaali Ramadhaana”, (rubutun hannu) ba a gabatar da ita ko’ina ba.
Ƙairawaniyyu, Imam Abi Muhammad Abdullahi bn Abii Zaidi, Annawaadiru Was Ziyaadaati Alaa maa fii Mudawwanati wa Min Ghairihaa Minal Ummahaatu, Juzu’i na 2.
Mabera, Abubakar Usman (2000) “Arrabixa Bainal Hajj wal Udhhiyyaati.” Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani masallacin Ƙaraye, Titin Sarki Yahya, Sakkwato.
Mandawari, Yusuf Uba (1995) Shin Za a yi Sallar Idi Ranar da ake Arfa? W. F. Xandago S/ Titi Kano.
Rivah, Abubakar bn Usmanu (2001) “Muƙaalaati Haula Salaatil Idi Wal Udhhiyyaatu.” Ba a gabatar a ko’ina ba.
Shaikh, Salman (n.d.) “Hilaal Sighthing and Islamic Dates: Issues and Solution Inshaa Allah”, www.hilal.sighting.org/papers/salman.pdf.
Shanƙiixii, Ahmad bn Ahmad Almukhtar Aljaahinii, Mawaahibul Jaliil min Adillatil Khalil, Juzu’ i na 2.

1.  Islamic Cresent Observation Project www.icoproject.org
2.  Hilal Sighting Committee of North America www.hilalsighting.org
3.  Hilal Sighting Process in Saudi Arabia and its Implications worldwide – Salman Z. Shaikh – 2nd ICOP Conference, Amman, Jordan www.jas.org.jo/hilal
4.  Moon Calculator (Moon Calc), Dr. Monzur Ahmed www.starlight.demon.co.uk/mooncalc
5.  Moonsighting for the Month of Ramadan By Shaikh M. Ibrahim Memon, Darul Uloom Almadania, Buffalo, NY, USA www.zaytuna.org/artcledetails.asp?articleID=100








[1] Irin tsarin Alkur’ani tsari ne da ke tabbatar da cewa, littafin Allah ne wanda babu ruɗewa a cikin maganganun ayoyinsa. A koyaushe Allah na ambatar “Rana” gabanin “Wata.” Abin  nufi a nan shi ne, za a ji lafazi da Wash shamsu wal ƙamaru” ba  za a ji walƙamaru wash shamsu ba. A dubo sura ta 91 aya ta 1 – 2.
[2] Saɓanin dare da rana da littafin Allah ke ambata saɓanin dare da  rana ya tabbbatar da kasancewar  Rana da Wata bayi daga cikin bayin Alllah. Nassi ya tabbatar da su ma suna yi wa Allah bauta dubi sura ta 22 aya ta 18.
[3] Nassin littafin Allah ya tabbatar da wannan domin ya kira Makka cibiyar Alƙaryun duniya gaba ɗaya dubi sura ta 42 aya ta 7.
[4] Azumin farilla da na ranko da na taɗawwu’i  da na kaffara duk ɓacewar rana ne lokacin shan ruwa gare su. Dubi littafin Sifatus Siyami na Sheik Nasirud Diin Albani.
[5] Wannan rubutaccen zance ne ta bakin Annabi Ibrahim (AS) a faɗarsa cikin sura ta 6 aya ta 78.
[6] Alƙur’ani ya ce, aikin Hajji na sanannun watanni ne sura ta 2 aya ta 197. Zakka sai an cika watanni goma sha biyu, sura ta 2 aya ta 110. Azumi a watan Ramadhana sura ta 2 aya ta 185.
[7] Tun gabanin bayyanar agogo da kimiyyar hisabi magabata na dogara ga nassoshin hadisai wajen kirdadon ibadojinsa.
[8] A dubi Alƙur’ani sura ta 10 aya ta 6.
[9] Bisa wannan tunani na magabata suka tabbatar da ingancin  Ikhtilaaful muɗaali’i saɓanin yanayin haske da duhu da jewaɗin rana da wata ke  haifar wa a duniyar mutane.
[10] Nassoshin Alƙur’ani da Hadisi da dama sun zo da bayanan ma’anar musulmi. Don ƙarin bayani a dubi Annawawi, Hadisi Arba’uuna na Imam Nawawi.
[11] Ai don haka ne Alƙur’ani ke cewa, ku yi wa Allah ɗa’a, ku yi wa Manzonsa ɗa’a, da shugabanninku, sura ta 4 aya ta 59. Da haka tsarin shugabanci ya fara Mahalicci zuwa halittu ta bakin zaɓaɓɓen halittu.
[12] A yau, ana amfani da sunaye da yawa a ƙasashen Musulmi irin su Khalifa Sultan, Amirul Muminuna, Haakim da sauransu. A Arewacin Nijeriya muna amfani da “Sarkin Musulmi” a Borno Shehu a Gobir da sauran sassan daulolin ƙasar Hausa ana ce wa “Sarki”.
[13] An ce, sunan matsayin Abubakar shi ne “Khalifatur Rasulullahi.” A Hausa a ce “Magajin Manzon Allah.” Da haka, shugabancin musulunci ya fara bayan gushewar Annabi (SAW).
[14] Haɗuwar da sahabban Annabi (SAW) suka yi da amincewarsu ga zaɓen Sayyidina Abubakar Ibn Abi Kahaaha ya khalifanci masoya manzo bayan  wafatin manzon Allah (SAW) ita ce hujjar ma’abota sunna.
[15] Ana son  ya zamo Musulmi, Mai hankali, Namiji, Ɗa, Baligi, Lafiyayye, Mujtahidi, Mai gaba gaƙi, Mai Adalci Mai iya zartar da Hukunci, d.s haka Usaman Ɗanfodiyo ya ambace su a cikin littafinsa Bayan Wujub Al-Hijr ‘Alal-ibaadi, na Khartoum Uniɓersity, Press. Wallafar Islamic Academy, Sokoto shafi na 64.
[16] A dubi littafin da aka ambata a lamba ta 15 shafi na 64.
[17] Hadisi ya zo a kan wannan magana a faɗar Manzon Allah (SAW)
[18] A dubi littafin da aka ambata lamba ta 15 babi na 6 shafi na 61. Domin ƙara tantance tsarin sarautar musulunci a dubi Alfark, K.A.Y. (1994) Ahkaamus Sulɗaaniyya,
[19] Idan ya yi umurni da a yi abin da yake saɓo ba za a yi ba, saboda nassi cewa ya yi: “Ba a yi wa wani wanda aka halitta ɗa’a domin a saɓa wa wanda ya yi halitta.” A dubi gabatarwar littafin Al- Akhdari na Abdur Rahman Al-Akhdari.
[20] Domin ƙarin bayani a kan haka, a dubi littafin Alfark, K.A.Y (1994) Ahkaamus Sulɗaaniyya.
[21] A fiƙihun ganin wata, sarki babba ne ko ƙarami, da wanda ya aza a matsayin wakilinsa ko Alƙalinsa, ko Hakiminsa duk suna zartar da tabbacin tantance ganin wata a madadin sarki bisa ga umurninsa a ƙasarsa. In ga uzurin rashin lafiya da tsufa da tafiya da sauransu.
[22] A rubuce-rubucen farko ana zance ne tun lokacin da akwai }asashen da daulolin musulunci masu }arfi. Bayan rugujewar ‘yan sauran daulolin da suka rage a 1924 aka sauya tsari.
[23] Rubuce-Rubucen wa]anda suka biyo baya su ne wa]anda ]aliban malaman farko suka yi. Da yawa daga cikinsu an yi su bayan barbazuwar Turawa da sunan Mulkin Mallaka a }asashen da Musulunci ya kafa daulolinsa. A irinsu za a ji sunaye irinsu Sultan da Emir d.s.
[24] Ha]uwar al’amarin musulunci wuri ]aya zai kasance }ar}ashin shari’ar da jagoranci wanda suka za~a a kan }ur’ani da sunna komai fa]in }asashen ba za a sami matsalar gudanar da shikashikan addininta ba. Rashin  shari’ar ne ya jefa al’ummar musulmi cikin shugabancin Mazhabobi da [ari}o}i da }ungiyoyi idan shari’a ta kafu da ita shugaba zai yi garkuwa ya huta  jama’arsa su ha]u wuri ]aya.
[25] Kakka~e hannun Sarkin Musulmi cikin harkar siyasar }asa Turawan Mulkin Mallaka suka yi shi, ya cuta wa shugabanci. Demokara]iyya da mulkin soja suka zo suka yi babakere.
[26] Khalifofin hu]u su ne, Abubakar, Umar, Usman,da Aliyu. ‘yan rigingimun siyasa da aka samu lokacin Khalifa na uku da na hu]u ba su gurgunta martabar khalifancinsu ba.
[27] Fitinar da aka samu ga zuriyar Banu Umayyad na }arshe shi ya haifar da }ananan daulolin Fatimiyya Usmaniyya da Marwaniyya da makamantansu.
[28] Wannan shi ya haifar da gadon-na-gaje-ka a sarautun Musulunci al’amarin shugabancin Musulunci ya fa]a tarkon Shai]an. Daga nan }ofa ta bu]e tu’assibanci ga Mazhabobi da [ari}u da }ungiyoyi, shugabancin Musulunci ya rarraba. Aka wayi gari a yau sarkin Musulmi ikonsa a fada kawai yake da amo da tasirin da ake bu}ata.
[29] An ce, }asar Andalus ta yi zama }ar}ashin Musulunci fiye da shekara ]ari uku. Har yanzu tasirin musulunci bai gushe ba a sunayensu da al’adunsu.
[30] Rubuce-Rubucensu na fi}ihu da tauhidi da yawa sun shiga a }asashen Afirka ta Yamma daga Masar da Morocco. Daga cikin su akwai littafin Samar}andi
[31] Wannan daular an yi ta a Turkiyya, ita ce ake ambata da sunan “Ottomon” a littattafan masu tarihi lafazin “Ottomon” ina ganin na harshen Turkanci ne da ba su iya furta “Uth” ko “Us” na  ga~ar farko ta “Usmanu”.
[32] Daga wannan shekarar ta 1924 babu sauran kufan wata daula magabaciya a duniyar musulunci sai dai wata da ta tsira da baya.
[33] Daular Sakkwato a Jagorancin Usmanu [anfodiyo, daular Masina a }ar}ashin Seku Ahmad na Bambara da Umar Al-futi a Senegal.
[34] Ba su sami nasarar ha]ewa wuri ]aya su zama gagarumar daula ]aya ba. Cikin wannan hali ne Turawan Mulkin Mallaka suka zo da ta’addancinsu na ruguza shari’a a duk }asar da aka kafa ta. Tun a lokacin Sarauatar Musulunci ta Sakkwato ta shiga matsala ya zuwa yau.
[35] A bisa wannan tsarin, ganin watan ]aya daga cikinsu ba ya wadatar da ]aya. Haka kuma, kowane daga cikinsu na da ikon tafiyar da al’amarin ganin watansa da daularsa wannan ba laifi ba ne a shari’a sarakunan Nijeriya su kula da wannan sosai.
[36] Wa]anana daulolin har yanzu gidajensu na nan, kuma sarautunsu na nan, daulolinsu na nan raye ba su mutu ba. Sarakunansu na nan musulmi suna tafiyar da musulunci. Idan sun ga wata ba su yi laifi ba su zartar da a yi azumi ko a aje azumi a daulolinsu. A Shari’a ko da akwai Imamul A’azam ko Amirul Muminina bai isa ya soke ganin watansu ba ko ya tilasta su dakata Idi da shan ruwa matu}ar sun tabbatar da ganin wata a daulolin ri}onsu.
[37] Idan hakanan ne kuwa, a }a’idar ganin wata, su ke da ha}}i ga jama’arsu ba wani ba. Hadisin {uraibu ya isa ya zama hujja, a }asa ]aya, ri}o ]aya, amma ganin wata ya bambanta. A tuna, lokacin da aka ruwaito hadisin {uraibu shari’ar musulunci ake gudanarwa ]ari bisa ]ari. A yau fa?
[38] A irin wannan yanayi, }o}arin da ake yi na mayar da al’amarin ganin wata abu ]aya a Nijeriya domin ha]in kan musulmi ko masarautu kure ne. Ha]in kai duk shi ne, yi wa Allah da Manzonsa ]a’a in an ga wata a ]auki azumi, in an gani a sha. Wannan shi ne ha]in kan da Allah ke nufi ga bayinSa, koma bayansa ɗemuwa ce da ɓata mai jefa mai su cikin hushin mahaliccinsu (Allah Ya tsare mu).
[39] Sarkin Musulmi na da ikon ba da sanarwa sarakunan su yi azumi (su da jama’arsu) ko su aje bisa ga ganin watan da ya zartas. Ikon da ba ya da shi ne, hana su ]aukar azumi ko aje azumi bisa ga sahihin ganin watansu ko da kuwa mutum ]aya ya ga wata suka hukunta a yi azumi ta zauna.
[40] Shari’a ba ta iyakance adadin shugabannin da musulmi za su samu ba a }asar da ba ta musulunci ba. Wani shugaba ba ya da iko ga wani shugaba ga abin da shari’a ta ba kowanensu damar ya zartar.
[41] Tsarin dare da safiya da saɓanin rana da wata a duniyar mutane abu ne tabbatacce. A }asa ]aya ana samun bambanci bale a }asashen duniya. Lokacin da musulman Amerika ke gudanar da Sallar Juma’a }asar Indonesia suna shirin Sallar Azahar ranar Asabar. Abin nufi, su sun gama juma’a tun jiya ranar Juma’a domin }arin bayani a dubi lamba ta (42).
[42] A dubi sheikh, S. “Hilal Sighting and Islamic Dates: Issues and Solution inshaa’Allah”, shafi na II
[43] Dubi madogarar da aka ambata a lamba ta 42 shafi na 7.
[44] Dubi madogarar da aka ambata a lamba ta 42 shafi na 7.
[45] Dubi madogarar da aka amabata a lamba ta 42 shafi na 9.
[46] Dubi madogarar da aka amabata a lamba ta 42 shafina 9.
[47] Dubi madogarar da aka amabata a lamba ta 42 shafi na 10.
[48] Dubi madogarar da aka amabata lamba ta 42 shafi na 12.
[49] Hadisin Abdullahi bn Umar ya isa hujja a nan. Hadisin cewa ya yi:”Taraa’an naasul Hilaala fa akhbartu Rasuulallaahi (SAW) annil ra’aituhu, faswaama wa amaran naasa bi swiyaamihi” Wa]anda suka ruwaito shi su ne: Abii Dawud da Daaramii da Ibn Hibban da Darul }uduii da Baiha}ii Imam Nawawi ya inganta shi a cikin littafensa Al-Majmu’u juzu’I na 6 shafi na 276 Albaani ya inganta shi cikin littafinsa Swahiihu Sunani Abil Daawud juzu’I na 2 shafi na 55 da kuma cikin Irwaa’il Galiili juzu’I na 4 shafi na 16.
[50] Masana a kan duban jinjirin wata sun ce, kamar zinari yake da saurin ~acewa (in ji Bahaushe) don haka ake son a yi tsaye tsaf wurin da aka gan shi, ka da a ]aga wurin, a yi wa mutane kururuwa su zo su gani. Ai sunan jinjirin wata hilaali a lugar Larabaci ya samo asali ne daga ]agar da muryar da ake yi na kururuwar ku zo ku ga sabon wata ne. Ba abin mamaki ba ne idon wanda ya ga wata ya ]an ]aga ka]an ya ~ace masa gaba ]aya.
[51] Ana iya samun mutum ya ga wani abu kamar wata amma ba wata ba ne, an ce yana duban wata sai girar idonsa fara ta ranka~o a }wayar idonsa ya ce: “ga wata ya gani” Anas (RA) da ya tsufa ƙwarai aka cire ta  aka ce “ina watan?” Bai gan shi ba. Irin haka ake gudun ta auku.
[52] Sahihin hadisin Ibn Umar na cewa: “Asshahru tis’un wa ishiruuna lailatan falaa taswuumuu hatta tarauhu, fa’in gumma alaikum fakmiluu iddata salasiina.” Bukhaari ya fitar da shi a cikin littafin Azumi babin da ke cewa: izaa ra’aitumul hilaala faswuumuu a dubi Fatahul Baarii juzu’i na 4 shafi na 143 lamba ta 1909. Muslim ya ambace shi a kitaabus swiyaamu babin da yake cewa: Wujuubu Swaumi Ramadhaan li ru’uyatil hilaali, juzu’i na 2 shafi na 1081.
[53] Hadisin Abu Huraira da Bukhaari da Muslim suka fitar bisa tsarin lamba ta (52) da muka ambata wata na iya kwana talatin. Don haka, kasancewar wata na kwana 29 tsawon shekaru 100 ko 200 ko fiye ba abin zargi ba ne da zai zama dalilin rigingimu da zargin juna da ~ata wa juna ibaada a kan tawili.
[54] A dubi littafin Almagribii, H (2007) Albadarut Tamaamu sharhi Buluugul Maraami min Adillatil ahkaami, juzu’i na 2 sahfi na 171 ya kawo hadisin Bukhari na Ibn Umar da ya tabbata wata na iya 30.
[55] Khalifofi da tabi’ai sun kasance suna fita neman jinjirin wata ranar 29 gare shi. Watan musulunci ba ya 28 kuma ba ya 31. Allah shi ne mafi sani.
[56] Wanda ya ]auki azumi a kan kowane irin ganin wata, na muntum ]aya ne, ko adilai biyu, ko na jama’a, ko na hukuncin Sarkin Musulmi, idan aka ga watan Sallah yana da azumi 28 dole ya ranka ]aya. Idan ko har ya cika talatin babu labarin wata ranar 31 zai sha ruwa. Idan daga Nijeriya ka ]auki azumi da sahihin ganin wata, ka je umra aka ga wata kana da 28, sai ka sha ruwa ka ranka ]aya. Idan ka cika talatin ba a ga wata can ba, dole ka sha ruwa ɓoye, ka yi Idi tare da mutane.
[57] Matsalolin ganin wata ya sa aka tura wa majalisar fatawa ta saudiyya tambaya, mai lamba (2) kwanan wata musulunci 13/8/1392 a kan halaccin amfani na hisabi ko na’ura ko ilmin fala}i suka amsa da cewa a ha]awar malmai yin haka bai halatta ba: Wa amma maa yata’alla}a bi isbaatil ahilla bil hisaabi faƙad ajma’u A’adhaa’il hai’ati alaa adami I’itibaarihi. Wa billahil taufii}.” A dubu littafin Alhassam, A (2003) Taudhiihul Ahkaami min Bulugul maraami a kan bayanin hadisi na 541 shafi na 454.
[58] A kan wannan matsala Imam Mahdi da wasunsu sun tafi a kan cewa: “Lallai masanin taurari, idan ya san abin sanin gaske tabbatacce ya yi aiki da shi, hukuncinsa kamar wanda ya ka]aita da ganin wata ne shi ka]ai.” A dubi littafin da muka ambata a lamba ta 54 shafinsa na 171. Malam ibn Buzaizata ya ce. “Wannan bayani mazhaba ce ɓatacciya domin littafin da muka ambata lamba ta 57 shaikhul Islami Ibn Taimiyya ya fa]a cewa: “ta tabbata a sahiihiyar sunna da bayanan sahabbai cewa, ba ya halatta a yi dogaro ga hisabin taurari. Wanda ya dogara gare shi kamar shi ya ɓata cikin shari’a kuma mai bidi’a ne a cikin addini.” Shafi na 450.
[59] Hanyoyin da ake bi na zamani na ganin wata ta fuskar kimiyyar Kwamfuta ko ilmin Taurari ko Hisabi ko ilmin Fala}ai su ma suna da kurakurai irin nasu da ]an kallo bai sani ba. Amfani da su domin a tabbatar da tsayuwar wata ba tafarkin sunna ba ne idan har wata bai ganuwa da ido a lokacin da ake zaton ya tsaya’ in ba a iya ganinsa }uru-}uru bai tsaya ba ko da a kimiyance ya tabbata. Dalili kuwa Annabi (SAW) cewa ya yi Liru’uyatihi” matu}ar ido ba ya ƙyallaro shi, shari’a ba ta aza muna azuminsa ba. Idan ido ya gan shi, azumi ko sallah suna tabbata ko da kimiya ta tabbata wata  ba aya ganuwa a wata rana a duk duniya. A azumin 2009 Masana taurari sun ce wata ba ya ganuwa da ido duk duniya sai ga shi an gan shi a Libya da Marocco ilmin duk da ke mu}abala da ilmin Allah da manzonSa, ba a kafa hujja da shi wajen tabbatar da hukuncin Allah da manzonSa.
[60] Ana iya samun na’urar da za ta nuna ranar da wata zai tsaya na tsawon shekaru ]ari ko fiye. A ciki, ana iya samun kurakurai dari ba abin mamaki ba ne. Mutum ne ke }era na’urar ta basirar da aka ba shi, ba ta wahayi ba. Al}ur’ani ya gama da wannan hukunci a fa]arsa “Afalaa yatadabbaruunal }ur’aan, walau kaana miin indi ghairil laahi la wajaduu fiihi ikhtilaafan kasiiraa.” Sura ta 4 aya ta 82 duk abin da ba zancen Allah ba, samun kurakurai bilaa adadin ciki tabbas ne. Allah Ya sa mu gane.
[61] Daga cikin matsalolin ganin wata uku, ]aya kawai yake yanke, saki ba }aidi, nashin ƙasa babu kure. Sauran biyu kuwa lalura ce mai tunku]e hukuncin nassi. Abin nufi a nan shi ne, gani da ido shi ne asali. Abin da duk ya }aryatar da ganin ido }arya ne.
[62] A dubi littafin Albaaji, A (1999) Almunta}a sharhin Muwatta Malik, Tah}ii}u Muhammadu Abdul}adir Ahmad A]aa’a, juzu’I na 3 shafi na 9.
[63] A dubi littafi Shan}ii]ii, A (2005) Mawaahibul Jaliili min Adillatil Khaliili, juzu’I na 2 shafi na 5.
[64] A dubi madogara ta 63 shafi na 6.
[65] A dubi madogara ta 63 shafi na 7.
[66] A dubi madogara ta 63 shafi na 10 da Iziyya  da  Rissala da Askarii da Mudawwana duk sun tabbatar da wa]annan maganganun uku. Wa]annan maganganun uku ba mazhaba ba ce, maganganu ne game gari ga masana fi}ihun ganin wata gaba da baya. A dubi littafin da muka ambata a lamba ta 67 ba Bamalike ba ne a mazhabance, amma ya kawo wannan batu a kan sharhin hadisi na 541 shafin sa na 454.
[67] Idan mutum ]aya ya ga wata ba ya da ikon sanarwa sai dai ya gaya wa sarki, duk da yake shi azumi ya hau kansa. Haka adillai biyu, sarki ka]ai ke da ikon tantance su. Gamin mutane da yawa, da cikar wata talatin, ba ya bu}atar wata tantancewa da sanarwar sarki ga ingatacciyar fassara.
[68] A irin wannan matsalar, abin da sarki ya tabbabtar ita ce maganar kamawa, wadda ya watsar ta watsu ga hukunci amma wanda aka watsar da batunsa, in shi, ko su, suka gani, su kan dole su tashi da shi, in na ajewa ne kuwa tilas su aje, a ingantaccen zance mai inganci ko da za su jinkirta Idi su yi tare da sarki.
[69] Malamai magabata sun ce, wanda duk ya shaidi ganin wata wa]annan nassoshi na aya da hadisi sun ]aure shi, ba ya da za~i sai ]aukar azumi.
[70] A dubi madogarar da muka amabata a lamba ta 63 shafi na 10.
[71] A dubi littafin Almu}addassii, S. Almugnii juzu’i na 4 shafi na 128.
[72] A dubi madogarar da muka amabata a lamba ta 71 shafi na 128.
[73] A dubi littafin {airawaaniyya, A.M. Annawaadiru waz Ziyaadaati Ala maa lil Mudawwanati wa Gairihaa min Ummahaatu, juzu’i na 2 shafi na 4.
[74] Allah Ya yi umurni cewa. “ Ya ku wa]anda kuka yi imani, ku yi wa Allah ]a’a ku yi wa Manzon Allah ]a’a, da shubanninku.” Sura ta 4 aya ta 59 Umurnin yi wa Allah ]a’a da yi wa manzo sun zo zozo-zozo ga awon kalmominsu domin manzo duk ayyukansa babu na yarwa. Shugabanni kuwa sharaɗin yi musu ]a’a in umurninsu bai yi takin sa}a da na Allah da manzonSa ba.
[75] Wanda ya yi wa shugaban daular musulunci tawaye na zarge-zarge don a tu~e shi ko na }in bin umurninsa da ya bayar ko hana a bi umurninsa, matu}ar dai umurnin bai sa~a wa na Allah da manzonSa ba, ya aikata babban laifi dole sai tuba. Wanda duk ya yi wa shugaban musulunci tawaye ya hallatta a ya}e shi har sai ya dawo. A sahihiyar Magana bai yi ridda ba.
[76] A dubi lamba ta 49 mun ambaci mafitar hadisin da matsayinsa.
[77] Ga riyawar ya ce: “an rajulin min aswhaabin nabiyyi (SAW) annahu }adikh’talafan naasu fii aakhiri yaumi in dan Nabiyyi (SAW) la’ahallal Hilaalu amsi ashiyyan fa’amara Rasulul laahi (SAW) naasa an yufdiruu.” Imami Ahmad ya fitar da shi da Abu Daawuda. Albani ya inganta shi a cikin Swahiihu sinanin Abii Dawud, juzu’i na 2 shafi na 45.
[78] Fa}ad }aala Abdullahi bn Ahmad bn Hambali: sa’altu abii an ru’uyatil Hilaali izaa shahida alaa ru’uyatihi rajulin waahidun }aala: ya’amurul Amiirun naasa bis swiyaami fakultu li abii: fa in shahida alaa ru’uyatil hilaali rajulun waahidun fil if]aari: }aala laa hatta yakuunan rajulaini yashhadaani fa’ amma rajulun waahidun falaa.” A dubi Masaa’illil imaamu  Ahmad bi riwaayaati ibnini Abdullahi  juzu’i na 2 shafi 610-611 taha}i}u addoktor Aliyu Sulaiman Almuhamma bugu na farko (1986) da littafin Rawaa’idul muuntakhalibatul Awaali An shuyuukhul Assi}aati (Alghiikaniyaati) juzu’i na 1 shafi 401 wallafar Abi Bakr Muhammad bn Abdullahi As Shaafii (ya mutu hijira 354) Taha}i}in Dr. Marzuuk Azzaharaaniyyu bugun farko 1997 Darul Ma’amun liltaraas.
[79] Fa’izaa sabata indal imaami ru’uyatul Hilaali bi shahaadati adlaini amaran naaasa bis swiyaami awil fi]ri wa hamalan sassa alaihi. A dubi Mu}addimatil Muhadaati na Abi Waliidu Muhammad bn Ahmad bn Rushadi Alkur ]abiyu, Tacewar Dr. Muhammad Hajji bugu na farko (1988) Daarul Garabil Islmic juzu’i na 1 shafi na 251
[80] Waswswahiihu min haaszaa kullihi annahu mufawwadhu ilaa ra’ayil imaami in wa}a’a fi ƙalbihi suhhatu maa shahiduu bihi wa kasuratil shuhuudu amara bis swaumi.” Yana ciki Haashiyatu Raddul Mukhatar na Muhammad bn Amiinus shuhumi bi ibn Dabi diina bugu na biyu (1966) Darul Rikr, juzu’i na 2 shafi na 388.
[81] “Wa kaana min hadiyihi (SAW) amaran naasi bis swaumi bi shahaadatil rajulil waahidil almuslimi wa khuruujihim minhu bi shahaadati al-isnaini.” A dubi Zaadil Mi’aad fii Hadyi Khalril anaam. Juzu’i  na 2 shafi na 49 – 50.
[82] A nan duka bayanan Manzo (SAW) ya ba da a yi sanarwa bisa ga abin da jama’a suka gani na jinjirin wata. Babu wurin da aka ruwaito ya gan shi, shi da kansa. Haka kuma, ba a ruwaito an gani an gaya masa ya ƙi ya karɓa ba. Abin da jama’a suka gani shi ya tabbatar kuma ba a wayi gari abin ya zama ƙarya ba.
[83] “Wa minal Majmu’aati ƙaala ibn Alƙaasim an Maaliki: wa man ra’aa hilaala Ramadaana aw shawwaalin wahadahu  fal yu’ulimil Imaamu.” A dubi Annawaadiru waz ziyaadaati Alaa maa fil Mudawwanati Min Ghairihaa Minal Ummuhaatu, na Imam Abi Muhammad Abdullahi bn Abi Zaidil Ƙairawaniyya (ya mutu hijira 386) tacewar Muhammad Usmaani, juzu’i na 2, shafi na 4.
[84] Wanda ya ga wata da kansa ƙuru-ƙuru wa yake jiran ya sanar da shi? Sai dai ya sanar da sarki. Waɗanda suka ga wata su biyu, sai dai su sanar da sarki domin duniya ta ji. Idan kuwa duk duniyar ce ta shaida, zancen sanarwa ya ƙare. A taƙaice, sanarwar ganin wata faɗakarwa ce ga wanda bai gani ba, bai ji ba. Waɗanda suka gani, sai harama kawai.
[85] A wata fatawa Imam Malik ya ce: “Wanda ya ga wata shi kaɗai, ya sha ruwa, zai yi ranko da kaffara. Imam Abu Haniifa ya ce, zai yi ranko kawai. Wasu almajiransu manya-manya sun ce, babu ranko domin mutum ya samu ya hau Arfa shi kaɗai da ganin watansa. A dubi Annwaadiru juzu’i na 2, shafi na 4. Ire-iren waɗannan rigingimu dole a sa Sarkin Musulmi ciki domin a tabbatar da na tabbatarwa. Zance mafi rinjaye shi ne, ganin watan mutum ɗaya hujja ce a kansa ta kowace fuska (ɗaukar azumi da ajewa). Zai gabtar da kansa gaban sarki domin neman ƙarin shaidun da za a zartar da hukunci a kansa.
[86] A dubi,  Haashiiyatul Kharshi Lil Imam Muhammad bn Abdullahi Ali Alharshiyyu Almalikiyyu, alaa Mukhtasar Khalil (1997) juzu’i na 3, shafi na 8.
[87] A dubi Haashiyatil Addasuuƙi Alaa Sharhil Kabir  juzu’i na 1, shafi na 790.
[88] A dubi littafin Bidaayatul Mujtahidi wa Nahaayatul Muƙtasidi, ibn Rushudi, A. (2001) shafi na 229.
[89] A dubi Almugnii juzu’i  na 4, shafi na 125.
[90] A dubi littafin Assalim, M. Sahiihu Fiƙihus sunna wa Adillatihi wa Tandiihul Mazaahibul A’imma, juzu’i na 2, shafi na 92.
[91] Ayar da ke cewa: “fa man shahida minkumul shahara” sura ta 2 aya ta 185 “suumuu liru’uyatihi” da Bukhari ya ruwaito.
[92] Faɗar da ya yi azumi da ganinsa hadisi ne, kuma magabata sun inganta haka. Mun tattauna shi a lamba ta 85. Gaɓa ta biyu, ta yi canjaras da zancen Mazhabar Imam Abu Hanifa mun faɗe shi a lamba ta 85.
[93] Malam Albassami a cikin sharhinsa da ya yi wa Buluugul Maraami min Adillatil Ahkaam mai suna: Tandhiihul Ahkaami, juzu’i na 3 ya ce: “Sharaɗin zamantowar wata jinjiri ya bayyana a sama, mutane su gan shi. In ba a gane shi ba, ba jinjirin wata ba ne. Ba za a ce mishi jinjirin wata ba sai face ya bayyana an gan shi kamar yadda Alƙur’ani da sunna suka tabbatar.” shafi na 458 – 459. Da wannan fatawar ce, wasu suka ce wanda ya ga wata shi kaɗai ba zai yi aiki da ganinsa ba sam. Sun manta a cikin wannan nassi ya ci gaba da cewa: “Amma magana mashahuriya ita ce, wadda Mazhabar Imam Ahmad da a’imma salasa (Mazhabobi uku) suka hau. Lallai wanda ya ga wata shi kaɗai azumi ya hau kansa da dukkanin hukunce-hukuncen wata da ke rataye da shi saboda saninsa na cewa, wannan rana ce daga cikin Ramadhana.” Shafi na 459.
[94] A dubi littafinsa Almugni juzu’i na 4, shafi na 127.
[95] A dubi Haashiyatul Kharshii Alal Mukhtasar Khalil, juzu’i na 3, shafi na 7.
[96] A dubi Haashiyatul Addasuuƙii Alaa Sharhil Kabir, juzu’i na 1, shafi na 790.
[97] A dubi madogararmu ta 95, shafi na 7.
[98] A dubi madogararmu ta 96, shafi na 797.
[99] A dubi madogararmu ta 73, shafi na 6.
[100] A dubi madogararmu ta 94, shafi na 125.
[101] A dubi madogararmu ta 94, shafi na 125.
[102] A dubi madogararmu ta 94, shafi na 128.
[103] A dubi madogararmu ta 95, shafi na 796.
[104] Imaamu Malik na cewa: “Kowane mutum akwai abin karɓa a zancensa akwai na mayarwa face ma’abocin wannan kabari”. (ya nuni kabarin Annabi) (SAW). A wata faɗa ya ce: “Idan hadisi ya inganta shi ne mazhabata.” Don ƙarin bayanin tu’assubanci ga Mazhaba a dubi littafin Usmanu Ɗanfodiyo Hidaayatul Ɗullabi da littafin Shaikh Albaani Sifatus Salaatin Nabiyyi (SAW) da littafin Ali Al-khasshani, Halil Muslim? Da ayar; “wa’a’ tasimu bi hablil laahi jamii’an walaa tafarraƙuu” aya ta 103__ sura ta 3.__
[105] A nahiyarmu ta Afirka ta yamma, musamman Nijeriya da Ghana da Nijar, mun fi sanin Malikiyya da Hanafiyya fa Shafi’iyya da Hambaliyya. Akwai Zahiriyya ta ibn Hazam, a yanzu aka fara saninta da littafinsa Almuhalla lil Aasaar ya shiga hannun ɗaliban ilmi.
[106] A dubi littafin Isma’ila, M. (2001) Alfiƙhu Alaa Mazaahibul Arba’ati lil Ibaadati, shafi na 441.
[107] A dubi madogararmu ta 106 shafi na 443.
[108]  A dubi madogararmu ta 106 shafi na 442.
[109] A dubi madogararmu ta 106 shafi na 441.
[110] A dubi madogararmu ta 106 shafi na 441.
[111] A dubi madogararmu ta 106 shafi na 442
[112] A dubi, Almagribi, A. Albadaraut Tamaamu Sharhi Buluugul Maraamu Min Adillatil Ahkaami, juzu’i na 2, shafi na 169.
[113] A dubi madogararmu ta 111, shafi na 169 Ibn Abd Barr ya kawo ijima’in.
[114] A dubi madogararmu ta 111, shafi na 169.
[115] A dubi madogararmu ta 111, shafi na 169.
[116] A dubi madogararmu ta 111, shafi na 169.
[117] A dubi madogararmu ta 111, shafi na 169.
[118] A dubi madogararmu ta 93, shafi na 452 – 3.
[119] Watau tsawon kilomita 2226, a dubi A dubi madogararmu ta 93, shafi na 452.
[120] A dubi madogararmu ta 93, shafi na 452.
[121] Dalilinsu a nan shi ne, a Hadisin Kuraibu, sarki a matsayin shaidan mutum ɗaya ne dole sai an samu wanda zai tabbatar da shaidarsa su zamo su biyu. Idan haka ta samu, sai a je wajen Alƙali ko Waziri ko wani na’ibi ya karɓi shaidar sarki da abokin shaidarsa. A nan, sarki ya tashi zama sarki ya zama shaida yana buƙatar wani magabaci ya tabbatar da shaidarsa. Allah shi ne mafi sani.
[122] A dubi madogararmu ta 90, shafi na 95.
[123] A dubi Al’usaimun, M. (2010) Aljaami’ul Ahkaami: Fiƙihus Sunna, juzu’i ba 2, shafi na 16.
[124] A dubi madogararmu ta 63, shafi na 9.
[125] A dubi madogararmu ta 63, shafi na 9.
[126] Idan an yi kuren ganin wata ba abin damuwa ba ne, haka yake kamar an yi daidai, muddin ba a ganganta shi ba. Idan da tazara a sake, in babu Allah Ya yafe. Me ya yi zafi a cikin wannan?
[127] A shekarar da ta gabata Saudiyya sun yi sanarwa cewa, sun yi kuren ganin wata, har sarki ya ɗauki nauyin ciyar da mutane ga rankon da za su yi. Babban gidan jaridar Makka (Saudi Arabia) mai suna ‘Arab News’ a watan Fabrairu 11, 2000 ya taɓa ruwaito kuren ganin watan ƙasar Saudiyya.
[128] Mulkin mallakar da aka yi wa Arewacin Nijeriya na yaudara ne. An soke shari’a aka bar sarakunan da ke gudanar da ita bisa ga jagorancinsu. Daga nan aka kawo musu tsarin mulkin Yahudu da Nasara. Sarakunanmu ba su da laifi, domin an fi ƙarfinsu don haka akwai buƙatar a taimaka musu yanzu, in til in ƙwal rinin mahaukaciya. Allah Ya taimake su, Ya taimake mu. Amin!
[129] A duba a Majmuu’u Fataawaa wa Muƙaalaati Mutanawwa’atu nasa shafi na 97.
[130] A dubi madogararmu ta 83, shafi na 7.
[131] Yana da damar naɗa kwamitocin da za su sauƙaƙa masa tafiyar da ayyukansa na shari’a. Kafa kwamitin ganin wata, a ganina abin so ne, domin sarki bai shaidun kansa da kansa.
[132] A dubi madogararmu ta 18 don ƙarin bayanin hukunce-hukuncen sarautar musulunci.
[133] Domin ƙorafe-ƙorafen da masarautar Saudiyya ta yi ta samu game da kurakuran ganin wata ashekarar (1419H) sai Majalisar Ƙoli ta sarauta ta ba da umurnin a kafa kwamitin ganin wata wanda ya haɗa da:
i.                     Babban Alƙali ɗaya daga Ma’aikatar Shari’a.
ii.                   Ma’aikacin KACST/ Masana Kimiyyar Taurari.
iii.                 Ma’aikacin Imarah ɗaya (Majalisar Ƙoli ta Alƙarya).
iv.                 Mutum ɗaya da zai saudaukar da kansa.
Yanzu haka, akwai kwamiti shida kusa ga Makka, Riyadh, Ƙassim, Hail, Tabuk da Asir. Don ƙarin bayani a dubi Shaikh, S. Hilaal Sighting and Islamic Dates Issues and Solution Insha’ Allah. www.HILAL.SIGHTING.ORG/paper/salman.pdf.
[134] Aya da Hadisi sun ce, a yi azumi idan an ga wata, wanda ya gani ba shi da zaɓi sai biyar umurnin Allah da Manzo.
[135] Wanda ya karɓi rahoton ganin wata ga wanda ya gani da idonsa, tilas ya yi azumi in ya amince da ganinsa.
[136] Wanda ya yarda da adalci wanda/ waɗanda suka ga wata azumi ya wajaba garai. Haka ‘yan kwamitin da aka sa, idan ka yarda da su, suka tabbatar da ganin wata magana ta ƙare.
[137] Ai Haashiyatil Addasuuƙii ya ambaci haka a shafinsa na 795, juzu’i na 1.
[138] Wannan mashahuriyar magana ce a mazhabar Maliki da waninsu. A dubi lamba ta 111 don ƙarin bayani.
[139] Manzon Allah kaɗai ke da khusuusiyya a addinin musulunci.
[140] A sharaɗin ganin wata akwai sharaɗin kasancewa musulmi.
[141] Wanda ke cikin maye ba a karɓar shaidarsa domin ba ya bisa hankalin kansa. dubi sura ta 4 aya 43.
[142] Alƙalamin Allah ba ya a kan mai barci sai ya farka. Mahaukaci har sai hankalinsa ya dawo. Don haka, shaidar mahaukaci ɓatacciya ce.
[143] Shaidar da aka tabbatar da ƙarya ce ɓatacciya ga shari’a.
[144] Idan shaida ta gabaci aikin da ake son a yi shaida, abin ya zamo labarin ƙanzon kurege. Domin ba za ka ba da shaidar mutum ya sha giya gobe ba ka ce a yi masa haddi yau.
[145] Idan aka samu yara ne ba su balaga ba, ko ‘yan ƙwaya ne, ko mahaukata, ko makafi, ko fitattun maƙaryata a zamaninsu. Ba su jin kunyar a ce sun yi ta.
[146] Da za a ce, yau ashirin da tara Larba, sai su ba da rahoto da La’asar cewa ga wata sun gani. A nan, an riga malam masallaci. Bayan Magaribar Larba ɗin ake son gani.
[147] Ganin wata ta hisabi ko ilmin taurari ko falaƙi ya saɓa wa sahihyar aƙida ba a hukunci da shi in ji Sahabban Annabi (SAW).
[148] Duk shaidar da aka tabbatar da yaudara a ciki, ana buɗe shaidar a biɗi wani.
[149] Saɓanin maɓullar rana da wata tabbatacen abu ne a shari’a da hankalin tuwo. Idan mai ba da shaidar watan wata ƙasa, ya zama wata ƙasa da maɓullarsu ba ɗaya ba, shaida ba ta yi ba. Haka ba a ba ka aiki ka gama shi, ka je wanda bai ba ka aiki ba ka mayar masa da gami.
[150] Idan har Sarkin Musulmi zai soke rahoton da kwamitin amintattu na ganin wata suka bayar. To, tilas ya fuskanci musulmi ya gaya musu dalilin rashin karɓar rahoton ko soke rahoton. Duk wata maganar da yake ganin ba dole ba ne ya sanar da jama’a game da soke rahoton ganin wata ba , to, ba za ta isa ta hana a ɗauki azumi ko aje shi ba.
[151] Kundin tarihin mulkin ƙasarmu ya ce: “Kowace irin doka ta saɓa masa ba doka ba ce, kuma haramtacciya ce sokakka gwargwadon saɓawarta ga dokar.” A ina za mu aje wannan taɓargaza?
[152] A tausayawa sarakuna ba don son su aka yi haka ba. Martabarsu na nan, amma a fiƙihun shari’a ba su da rawanin Amiirul Muminiina ko Imaamul A’azam ko Sarkin Musulmi a Hausance. Allah Ya yi mana jagora.
[153] A shari’a ba a tuɓe sarki sai in ya yi ridda a bayyane. Wannan zancen hadisi ne. A dubi madogararmu ta 15 domin ƙarin bayani.
[154] Ikon kowannensu na nan iyakan ƙasarsa kuma in an ga wata shi ne wuƙa shi ne nama.
[155] Idan sun yi haka a kan al’amarin ganin wata, to, a sanar da Musulmi su jiya don su ja ɗamarar ba da goyon bayansu. A sani, ko an yi haka, ganin wata na nan yadda yake babu wanda ya isa ya sauya shi ga yadda shari’a ta tanaje shi.
[156] Nassoshin kowace mazhaba sun tabbatar da haka.
[157] Ban ga laifin kasancewar Cibiyar Sakkwato ba don alfarmar Mujaddadi da mataimakansa. Idan aka yi mata ƙanwa a Borno ya dace domin sahara ce a bar ganin wata ba da matsala ba.
[158] Duk da haka a sani, babu wani shugaban wata Mazhaba ko Ɗariƙa ko Ƙungiya da ya cancanta ya yi sanarwar ganin wata ga Musulmi. Sarkin Musulmi shi ke da wannan iko. A yi ɗa’a da biyayya ya fi.
[159] Irin abin da ya faru a shekarar 2011 ka da Allah Ya sake maimaita shi.
[160] Mun gabatar da hadisai bakwai a kan haka ingantattu.
[161] Yin haka zai toshe wata kafa in Allah Ya so.
[162] Domin masu ganin sai an bi Makka sun kai ga ɓata wa musulmi ibadarsu ta layya bisa ga tawili, Arfa da Layya abubuwa ne mabambanta, ɗaya ba ta haɗa ɗaya. Ba tarihinsu ɗaya ba. Ba hukuncinsu ɗaya ba. Ganin wata sahihi shi ke tabbatar da kowannensu, da an gan shi, ba a jiran ɗaya sai aikatawa kawai. Don tantance wannna al’amari a dubi: Jalingo, I. J. M. (2009) “Ru’uyatul Hilaali Fil Islaami wa Fahadiyyaatuhaa li wahadatil Ummatil Muslimati fii Nijeeriyya.” Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
[163] Ya ce: “Wa’atasimuu bi hablil laahi jami’an walaa tafarraƙuu” sura 3aya 103.
[164]  A dubi sura ta 8 aya ta 46.
[165] Manzon Allah (SAW) ya tabbatar muna da cewa, taimakon Allah na ga jama’a. Ya tabbatar muna da cewa, al’ummarsa ba ta taruwa a kan ɓata. Haƙiƙa, kyarkeci na cinye akuyar da ta ware. Wanda duk ya rabu da jama’a gwargwadon taƙi ya cire rigar musulunci ga wuyansa, dubi Wassiƙatul Ikhawni na mujaddadi Ɗanfodiyo.
[166] A dubi madogararmu ta 132 ta fayyace haɗin kai sarai.
[167] Ƙin bin wannan umuruni shi ne rashin haɗin kai ga musulmi.
[168] Wannan ba shi ba ne, haɗin kai na ga biyar littafin Allah da ManzonSa da fassarar magabatan farko.
[169] Ga fatawar nan a rataye na 1
[170] Ga fatawar nan a rataye na 2
[171] Duk sharaɗin da ba a cikin Alƙu’ani ya fito ba, ba a hadisi ba, yana buƙatar Alƙu’arni da hadisi don samun karɓuwa.
[172] Rashin samun nassin aya ko hadisi da ya tabbatar da haka, shi ke tabbatar da cewa, wannan maganar kuskure ce, da daidai ce da ta samu nassi.
[173] Majalisar Malamai ta Makka ta ba da wannan fatawa ga ta nan a rataye na 3
[174] Maɗali’inmu ba ɗai ba ne, don haka kowa ya bi ganin watansa in ji Imam Muslimu ya yi babi na musamman mai wannan suna a sahihin littafinsa.
[175] Wannan ya haifar da rarrabuwar kan ma’abota sunna a Nijeriya a shekarar 2011. An yi rubuce-rubuce da yawa a kan haka.
[176] Haba! Sau nawa malamai na gaya muna cewa ko Arfa aka hau bisa kuskuren ganin wata in an gabace ta, a sake in ta wuce Allah Ya karɓa.
[177] Yadda ya shirya duniyarSa duka, duk mai son Ya dube shi da idon rahama ya bi ta haka nan ga ganin watansa da lokutan sallarsa da sauran ibadojinsa.
[178] Hadisai sun tabbatar ba haka.
[179] Nassin Ƙur’ani ya ce: “Wa anta hillun li haazal baladi” sura ta 90 aya ta 2.
[180] Sura ta 2 aya ta 115.
[181] Dubi madogararmu ta 132.
[182] Dubi madogararmu ta 132.
[183] A dubi madogararmu ta 161.
[184] A dubi madogararmu ta 161.
[185] Tsakanin Nijeriya da Makka akwai bambancin awa biyu. Wannan ya isa ya ɓata salla da azumi da gado da shiga musulunci da dai sauran ayyukan ibada da lokaci ke da muhimmanci.
[186] A Mazhabar Malikiyya ba a sake Idi.
[187] Duk da cewa a kwamitin ganin wata na Makka akwai masana ilmin Taurari a ciki ƙa’idarsu ita ce, da ganin ido ake yin sanarwa. A dubi madogara ta 133 don ƙarin bayani.
[188]  Abin da ya zo a hadisai shi ne “fa amaran naasa” ko “amara bis swaumi”, ko “ya’amaru” ga su nan dai. Don haka ta kowace irin fuska ana sanarwa.
[189] Idan ganin ya kasance gama gari an huta.
[190] Malam mai Risala Abi Zaid Ƙirawaani ya ambaci haka a wajen biyan jingar fito gabanin a shiga jirgin ruwa. Ga ƙa’idar shari’a, sai ka fita lafiya ka biya kuɗi. Mutane suka gane da sun ƙetara lafiya ba su, ba kuɗin fito. Dole ala ƙirƙiro, sai ka biya, ka shiga, in ba a sauka lafiya ba ku duka kun yi hasara. Wannan ƙirƙira shi aka yi bayan da mutane suka gane bijirewa da gangan. Allah masani.
[191] Abd. Bn Humaid ya ruwaito shi. Ibn Asaakir ya kawo irinsa. Sheikh Suyuuɗi ya kyautata shi. Dubi Fatahul Majid Sharhu Kitabut Tauhid. Shafi na 331.
[192] Bukhari ya ruwaito shi.
[193] Fatahul Majid
[194] A dubi madogararmu ta lamba 132 shafi na 3. A faɗar masana ilmin taurari, idan aka halicci wata yana sabo, sai ya kai wani mataki na lokaci za a iya ganinsa da ido ƙuru-ƙuru. A lokacin da suke da ilmin sanin an halicci wata, amma ba ya ganuwa da ido, a shari’a ba a halicci wata ba, yana can ɓoye ga wanda ya yi shi. Sai ya bayyana an gan shi, an yi masa kururuwa. Don ƙarin bayani a dubi, Ibn Taimiyya, Shaikhul Islam Ahmad (1995) Risaalaatu fi Fiƙhis Swiyaami, Daaru Fikir, shafi na 19 a babin da yake cewa: Laa yusbitul Hilaali illa bir ru’uyati. Yana faɗar: Falaa hilaala ila mastahalla fa’izas tahallahul waahid wal isnaani falam yukhbiraa bihi falam yakun zaalikal hlaali. Falaa yusbitu bihil hukmu hatta yukhbiraa bihi. Ɗantaimiyya ya ce, wata ba wata ba ne har sai ya bayyana an gan shi da ido an ba da labarinsa an shaide shi. Watan masu ilimin Taurari daban, watan masu addini daban. Da mutum zai mutu ya bar matarsa da ciki, likita ya tabbatar da lafiyar jinjirin a cikin uwarsa da rayuwarsa sahihiya, da za su iya ganewa a ilminsu. A ilmin rabon gado, ba a ba shi gado na namiji ko mace ko ɗiya biyu ko mata-maza har sai an haife shi lafiya. Idan za a haife shi cikin minti ɗaya da aka tabbatar da lafiyarsa ya zo duniya bai yi kuka ba, ba a ba shi ruwa ya sha ba, ba ya gado don bai zo da rai ba. A nan, ba a ƙaryata likita ba, amma an bi shari’a, kai! Ko da yaron ya yi fitsari ya yi atishawa, mataccensa ya zo a shari’ance, batun gado babu shi. Haka nan hukuncin ganin watan masu Hisabi na ilmin Taurari yake. Watan da suka gani nasu ne, na ilmin da suke da shi ne irin jinjirin da likita ya gani a cikin ciki. Bai zo da rai ba, ba ya gado. Ba a ga wata ba, babu azumi ko shan ruwa, in an ga wata sai a yi ibada. Masana ilmin Taurari sun ce, na’urar da ake amfani da ita Tabaron Hangen Nesa (Telescopes) ba ta da tabbas. Mutum biyu za su iya su duba zama ɗaya, ɗaya ya gani, ɗaya bai gani ba. Haka kuma, sun ce, ana iya ganin wata kwana ɗaya kafin ya bayyana a duniya. Wannan ba wata ba ne a shari’ance. Madogararmu ta 132 ta fayyace kimiyyar sosai, ta kuma bayyana cikas na kimiyyar da ake amfani da ita. Don haka shaidar ganin wata ta wannan fuskar ba madogara ce ga Sarkin Musulmi ba, kuma ya samu ya kore ta, ya ƙi yarda da ita, bisa damar da shari’a ta ba shi na tabbatar da ganin ido. Ai wani zai ce da ido masu Telescopes ke amfani sai mu ce in babu ƙira me ya ci gawayi? Su ɗebe shi, su yi amfani da ganinsu, da shari’ar Musulunci ta aminta da shi.
[195] An tambayi Sheikh Alothaimeen fatawa a kan idan rana ta kama wata yaya kwanan watan Musulunci zai kasance? Mai tambayar na cewa:
“Idan rana ta kama wata gaba ɗaya ko ta tsare sashensa bayan faɗuwar rana, a ƙasar Saudiyya, aka kuma tabbatar da wanzuwar irin wannan yanayi a yammacin ƙasar Saudiyya. Mene ne hukuncin rana ta biyu (wato gobe) a ƙasar da rana ta kama wata? Ko wannan na daga cikin lalurorin cika wata talatin (30)? Idan watan da ke biye ya fara daga ranar (da ranar ta kama wata) fa fuskar ƙidaya ko ganin wata. Mene ne hukunci?” Mai gabatar da Tambaya shi ne, Abdul Aziz Sultan Almar’eshi. General Manager Responsible for Watching Hilal at The Department of Astronomical Research at King Abdul Aziz City for Science and Technology.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Idan Rana ta kama wata, a kowane wuri a duniya bayan faɗuwar rana, ganin sabon wata washegari ba zai yiwu ba. Wannan shi ne abin da ma’ilmanta masana suka tabbatar cewa, abin da ake kira rana ta kama wata shi ne, samun wata a tsakiyar rana da duniya (su rutse shi ga shi tsuru-tsuru). Haka kuma, sannane abu ne ga masana da jama’a cewa, jinjirin wata (sabo) ba za a gan shi ba ko ba zai tsaya ba face an neme shi bayan faɗuwar rana. In haka ne kuwa, sabon wata ba zai fara ba a daren nan da rana ta kama shi ba, bayan ta faɗi, wannan ba zai taɓa faruwa ba saboda al’adar Allah da Ya saka ta sagegemiyar (ɗawafin) rana da wata (a duniyarmu). A dubi Surat Al-An’am (6:96) da Sura Ya-Seen (36: 38 – 40) da Sura Ashshams (91: 1 – 2) wannan ayar ta nuna wata a daren da yake jinjiri yana biye da rana. Don haka, idan wata yana bin rana zai fito bayan ta fito domin ba zai kasance ga wata ya kasance tsakanin rana da duniya ba. Don haka, yaya za a iya wata ya tsallake ya kasance tsakanin rana da duniya? Bugu da ƙari, wanda duk ya nazarci motsin rana da wata zai ga, wata a koyaushe yana mara wa rana baya ne a tafiyarsa. Don haka, ana iya ganin wata a darensa na farko na tsayuwa, zai iya ya kasance mita biyu ko uku, nesa ga rana. A dare na biyu wata zai ƙara nisantar rana. A dare na uku zai ƙasa nisantar ta ƙwarai da gaske, haka zai ci gaba har zuwa tsakiyar wata. A wannan lokaci wata zai kasance a gefen rana. Tsakaninsu zai kasance kamar tsakanin gabas da yamma. Idan mutum ya ce wata zai fara a wannan dare da a ranar da rana ta kama wata bayan faɗuwar rana, haka yake kamar mutumin da ya ce wata zai kasance cikin girmansa cikakke (ƙato da shi ya cika da’irarsa da aka sani duka) a cikin daren da aka halicce shi. Ko a ce, kamar dai mutumin da zai ce, rana za ta ɓullo gabanin ta faɗi, ko ya ce, jinjiri zai fito a gan shi gabanin (mamarsa) ta haife shi. Waɗannan abubuwa duka abubuwa ne da ba su kasancewa bisa ga tsarin dokoki da al’adar da Mahallcinmu ya aza duniyarSa a kai, a irin tsarinta da muke ciki a yau. A tuna! A kan imani da ƙudurar Allah, babu shakka cewa, Allah a kan komai mai iko ne babu abin da ke buwayarSa. Yana iya Ya haɗa watannin biyu wuri ɗaya, ko Ya rarrabe su, ko Ya dushe su, ko Ya sa su kasance cikin haskensu a kowane lokaci Ya so kamar yadda Ya labarta muna a cikin Sura Al-Ƙiyam (75: 7 – 10), amma dokokin da Allah Ya tsara duniyar nan tamu da su ƙayyadaddu ne, ba sa sauyawa face sai a kan karamomi/ mu’ujizojin Annabi ko don tabbatar da karamar wani Waliyi (Amintaccen Allah). Wannan fatawar Muhammad AsSaleh Al-Othaimeen ya rubuta ta (30/1/1412 H). A dubi Mujallar Al-Da’awah ta 1725, Shawwal 1420, Saudi Arabia.
[196] Masana ilmin taurari bisa ga tafarkin sunna sun ce, khusuufin rana ba ya faruwa sai a ƙarshen watan Musulunci. Ita kuwa rana ba ta kama wata (watau khusuufil ƙamari) sai a tsakiyar watan musulunci, yayin da wata zai yi banga-banga da rana a wani gefenta na daban sai ƙasa (duniya) ta zamo tsakankaninsu. A duba cikin, Ibn Daƙiiƙil Al’iid, Muhammad bn Aliyu bn Wahab bn Muɗii (2010) Sharhu Ummatul Ahkaam, Juzu’i na 1, baabus salaatul Khusuufi, shafi na 625.

1 comment:

  1. Merkur Sbar - XN Gaming
    Merkur Sbar. Product Code: H2520090. Manufacturer: Merkur. Additional information. Categories. SBR / 메리트카지노총판 Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic 바카라 / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic 제왕 카지노 / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic / Nordic

    ReplyDelete