Maƙasudin wannan xan bincike shi ne, yi
wa wasu salailan adabi sunan da ya dace da su domin ƙara faxaxa bincike da nazari. Nazarin
ya yi ƙoƙarin
tabbatar da samuwar “Salon Bugun Gaba” cikin kowane sashe na adabin Bahaushe.
An tsara aikin cikin manyan sassa tara (9), ƙananan
sassa goma sha xaya (11). An ziyarci makaxan baka (8), marubuta waƙoƙi
huxu (4), marubuci xaya (1) domin a tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba. An
sarrafa karin magana (3), xiyan waƙar
baka goma sha uku (13), rubutattun waƙoƙi huxu (4) domin a daddagi bagiren
sosai a xebe kokanto...
Bugun Gaba
(Salon
A San Ni, A Ji Ni, A Gane Ni Ne Wane)
Aliyu
Muhammadu Bunza
Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato.
mabunza@yahoo.com Phone: 0803 431 6508
TSAKURE
Maƙasudin
wannan xan bincike shi ne, yi wa wasu salailan adabi sunan da ya dace da su
domin ƙara faxaxa bincike da nazari. Nazarin
ya yi ƙoƙarin
tabbatar da samuwar “Salon Bugun Gaba” cikin kowane sashe na adabin Bahaushe.
An tsara aikin cikin manyan sassa tara (9), ƙananan
sassa goma sha xaya (11). An ziyarci makaxan baka (8), marubuta waƙoƙi
huxu (4), marubuci xaya (1) domin a tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba. An
sarrafa karin magana (3), xiyan waƙar
baka goma sha uku (13), rubutattun waƙoƙi huxu (4) domin a daddagi bagiren
sosai a xebe kokanto. Sakamakon nazari ya tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba,
don haka aka tanada masa turaku bakwai (7) na fexe shi da tsettsefe shi. A ƙarshe, aka shawarci masana da
manazarta da xalibai da a saka shi cikin tsarin salailan da ake nazarin
salailan adabi da su da cikakken sunansa na “Bugun Gaba” (BG).
GABATARWA
Zaman marina da masana da manazarta ke yi wa sha’anin
ilimi wani babban cikas ne ga ci gabansa. Hausawa na cewa, hannu xaya ba ya
xaukar jinka. A fagen karatu dole a samu kowa da irin wurin da yake sha’awa. Za
a samu kowa da wurin da ya fi ƙwarewa.
Masana, kowa da wurin da ya yi fice, ya yi zara, ya furce tsara. Tattare da
haka, da za a sami ‘yar tazara a ziyarci fagen juna ba ƙaramar nasara za a ci ba wajen ciyar
da ilimi gaba. A nazarin Hausa, fannoni uku, Al’ada, da Adabi, da Harshe, maƙwabta ne na ƙud-da-ƙud
idan za a fahince su. Da masanan sun yi tsayin daka, sun yi wa nazarin Hausa
taron dangi, da yanzu an wuce yadda ake a yau (2011). ‘Yar gudummuwar da nake
so in bayar a nan ita ce, in yi amfani da fagen xalibta ta “Al’ada” in ƙyallaro fannin “Adabi” waƙa, in yi amfani da dabarun “Harshe”
domin fito da wata gudummuwar da nake so in amfani fagen nazarinmu da shi. A
kan wannan tunani na yi wa wannan takarda take: “Salon Bugun Gaba”.
WAIWAYE
Ina sane da cewa, masana da manazarta Hausa jiya da
yau sun yi abin a zo a gani a kan tsettefe salo da yadda ake sarrafa shi a waƙoƙin
baka da rubutattu da rubuce-rubuce da zube da wasan kwaikwayo. Jagoran kallo
salo cikin rubutattun waƙoƙi (Muhammad, 1977) ya yi garkuwa da
waƙoƙin
Aƙilu Aliyu. Wanda ya fara dubansu a
babban digirin waƙoƙin baka, (Gusau, 1986) ga waƙoƙi
fada ya yi turke. Haƙiƙa (Birniwa, 1986) ya dube su a waƙoƙin
siyasa. Bayero, (1986), ya hange su a Jigon Madahu. Bello Sa’idu, (1978), ya
ruwaito su a waƙoƙin ƙarni
na 19 da na 20. Birnin Tudu, (2002) ya nazarce su a Jigon Furu’a. Bello Bala,
(2008) Mairukubta, (2010) da Maiyama, (2008) sun kalle su a waƙoƙin
xaixaikun mawaƙa. Ayyukkan da
suka fitar da salo a matsayin babban fagen daga su ne, Xangambo, (1980) da
xalibinsa Mukhtar, (1987), a taƙaice,
haka salo ya ci gaba da yaxuwa cikin rubuce-rubucen Al’ada da Adabi da Harshe
na nazarce-nazarcen Hausa. Alhaƙiƙa, wannan yunƙuri ya cancanci a yabe shi sosai.
To! Da yake masana salo sun ce zavi ne na mai rubutu
(ko mai magana ko mai aikata wani aiki) (Mukhtar, 1988), don haka ba ya da lokacin
da za a ce, an kammala bincike a kansa. Haka kuma, ba ya da lokacin da za a
daina yi masa salo ta fuskar ƙirƙire-ƙirƙiren sunaye ta hanyoyin da za a
nazaarce shi. A ganina, ayyukkan da magabata suka gabatas, su ne xalibansu suka
faxaxa, xaliban xalibansu suka ci gaba da laguda ana sarrafa hanyoyi irin na
muryoyin xaliban Malam Zurƙe
(Imam, 1966). Ban ga laifin haka ba idan an yi shi da manufar ƙara jaddada karatu da raya shi. Duk
da haka, ai waƙa xaya ba ta gama
niƙa irin na babban gida mai babban cefane
(wato fagen nazarin Hausa). Matuƙar
an yarda babban kifi na mai babban gora ne, to lalle kuwa babban kaya suna buƙatar babban gwammo. Ina ganin lokaci
ya yi na a fara tunanin faxaxa wasu hasashe-hasashen nazari a ƙara musu tsawo, waxanda ba su da ƙafafun a yi musu, waxanda ƙafafunsa ba su tsayu ba a tsayar da
su, waxanda aka tsayar da ƙafafunsu,
a yi musu turke na mannanu in ji ƙuda
da ya faxa ƙwaryar alewa.
HUJJAR
BITAR NAZARI
Rubuce-rubucen magabatanmu na salo sun yi wa salo
adalci, sun kuma rage ƙofar
da xalibai za su iya su leƙa
su tsinto wani abu ko wasu abubuwa. Sun yi nazarin ƙwaƙƙwafi
a kan kamance da siffantawa da jinsantarwa da kambamawa da kirari da zuga da
waskiya da adon harshe da azanci da dai
makamantasu. Abin ban sha’awa, kowane xalibi ya tashi nazarin Adabi ko Al’ada
ko Harshe cikinsu yake sassaka ya kai ya komo da ‘yan dubarunsa. Cikas da na
hanga ita ce, ban ga muna yawaita ƙoƙari na faxaxa waxannan makamam salon
na magabata ba, balle mu ƙirƙiro wasu daga cikinsu ko mu ƙirƙiro
sababbi da za su ƙara
musu tsawo. Babban muradin malami ya ga xalibi ya fahince shi. Yadda zai
tabbatar da ya fahinci malam shi ne, ya yi bitar karatunsa daidai ya ƙara kansa gaba bisa ga tafarkin da
malam ya koyar da shi. Idan aka kula sosai, yawaitar mawaƙan baka da marubuta, da yawaitar
littafain zube da na wasan kwaikwayo, da jaridu da mujallu da kafafen yaxa
labarai da ake amfani da Hausa a yau abin lura ne. A auna tsawon gonan bana da
igiyar bara da wuya a yi canjaras da abinda aka samu bara domin jiya ba yau ba.
BUGUN
GABA
Ban ce ba a yi wani abu da ya yi kama da wannan ƙudurina ba. Na san an yi ayyuka da
dama a kan kirari wanda a ƙarƙashinsa ake amfani da kalmomi irin
washi, koxa kai, kambamawar zulaƙe
da dai sauransu. Kirari kandamemen fage ne, idan aka dubi Kafin Hausa, da Mode,
da Bunza, da dai makamantansu.
Ga tsarin kirari
a.
Mutum na iya wa kansa kirari
b.
Wani na iya yi masa kirari
c.
Ana yi wa wani abu/wasu abubuwa kirari
Idan aka zaburar da mutum ga abin da ya saba yi, ko ya
shahara, ko ya buwaya, ko ya ƙware,
idan kalmomin sun shiga jikinsa, sun tsima shi, su ne kirari. Idan ya furta
wasu kalmomi domin tabbatar da abinda ake gaya masa, su ma kirari ne. Idan ma wani dabba ko icce ko gari ko ƙasa ake yi wa wannan washin duk da
yake ba sa ji, ba su mayar da martani, duk dai kirari ake yi musu. Ma’anonin
kirari da masana da dama suka bayar za su hau wannan da’awar ta kiriri.
A tsarin Al’ada, “Bugun Gaba” mutum shi zai yi wa
kansa. Mutum kaxai ke bugun gaba baya ga shi babu wani. Mutum shi zai yi bugun
gaba da kansa, idan wani ya yi masa ya zama kirari. Ga irin tsarin al’adar
Bahaushe ƙunshiyar “Bugun
Gaba” za a ga:
a.
Za a yi bugun gaba da tushe (iyaye da
kakanni)
b.
Za a yi bugun gaba da asali na ƙabila
c.
Za a yi bugun gaba da buwaya na magani/
tsafi
d.
Za a yi bugun gaba da fasaha ko basira ko
hazaƙa
e.
Za a yi bugun gaba da ƙarfin jiki ko lafiyarsa
f.
Za a yi bugun gaba da duk wani abu da ake
jin an rinjayi abokin magana ko jayayya
g.
Ba a bugun gaba da duk wani abu da al’ada
ta tozartas sai fa a fagen shaguve
Asalin bugun gaba a al’da shi ne, mutum ya doki ƙirjinsa da tafin hannunsa na dama ya
furta magana ga mai son rena shi ko rena masa wayo ko asali. Idan ya doki ƙirjinsa da hannun dama ya ce:
“Ni jikan Xanfodiyo za a gwada wa karatu? Littafi ya
sha ƙarya da masu kuri da shiya!
“Ni Balaraben Makka, Buzu ke yi wa dubin hadarin kaji!
Sai dai a fi mu ƙaton
naxin hawa Geloba.”
Ire-iren waxannan ne Bahaushe ke cewa ‘bugun gaba’, da
mutum ya furta su za a ce, “Ka ji bugun gaba”. Idan Bahaushe, ya doki gabansa
da hannun hagu, galibi abinda ya gani, ko ya ji, ko ya karanta, ya ba shi
mamaki ne, ko bai yarda da shi ba.
Ga al’ada, idan mutum ya samu karvuwa ga wani abu
kamar ya samu shiga a hukuma ko wani shugaba ko fice a sana’a, idan ana furta
wannan baiwar gaban idonsa zai xauki sigar kirari. Idan shi da kansa ke faxarsu
ba da wata shigar washi ba ko alfahari ba ya zama “mamakar da kai”. Idan kuwa
ya ji ana faxarsu ya sharve maganar, ya tabbatar da su, ya yi bugun gaba.
Narambaxa ya fito da shi a sarari a waƙar,
“Ya ci maza” yana cewa:
Jagora: In
ka ga mutum
Na ‘yan noƙe-noƙe
Yara: Sarki
bai dara mai ba,
Ran da yad dara mai
Sai bugun gaba
Gindi: Ya
ci maza ya kwan shina shire
Gamda’aren Sarkin Tudu Ali.
Idan Bafade bai samu shiga ga sarki ba yake kashe
jiki. Da ya samu shiga sosai, ana yi da shi, maganganun da yake faxa na nuna da
su ake yi, da doron da yake yi da sarki, su ne bugun gaba in ji malamin kixi na
Sarkin Gobir (Narambaxa). Da fatar an fahinci wannan kalmar daxaxxiya ce cikin
harshen Bahaushe da al’adunsa.
BUGUN
GABA A MUDUN ADABI
Idan muka dubi bugun gaba da idon basira za mu fahinci
babu sassa na Adabin Bahaushe da babu ratsinsa ciki. Ga wasu misalai kaxan
cikin Karin Magana da suka shahara a bakin Bahaushe.
i.
Muna wasa ne? Bagware ya ba da magani an
sha an mutu ya ce, “A gama kuka a ba mu kuxinmu”.
ii.
Annabijo dai! An ce wa takaren Xanfulani
Alhaji.
iii.
Gwamma ke san Allah? Ta ce, “Ga gidan ga
gidan”.
Bagware da ya ba da magani aka sha aka mutu bai san
laifi ya yi wa Bahaushe ba. A wautarsa, wai maganinsa katta’u ne don haka yake
bugun gaba da cewa, “Muna wasa ne”? Da wani ya furta wannan zance a kansa da
kirari ya yi masa, amma da yake shi ya furta da kansa sai ya zama bugun gaba. A
zaton Xanfulani wanda ya je Makka sau xaya ko biyu shi ne Alhaji. Idan an je
sau barkatai dole likafa ta ci gaba daga Alhaji zuwa “Annabi”. Don haka, da aka
ce masa Alhaji, ko dai bai doki ƙirjinsa
da tafin hannunsa na dama ba, faxarsa ta cewa, “Annabijo dai Moddibo” bugun
gaba ne. Da maroƙi
ya kira shi da sunan “Annabijo”, kirari ya yi masa. Gwamma Bagwara ce, ta yi
gida kusan masallaci. Ana cikin zance da ita aka tambaye ta imaninta da faxar,
“Ke san Allah”? Ita kuwa tana bugun gaban maƙwabciyar
masallaci ce, sai ta ce, “Ga gidan ga gidan”? Wai ga gidanta ga xakin Allah, wa
ya fi ta sanin maƙwabcinta?
Gwamma bugun gaba take, a nan, babu batun
savo a wurinta.
Idan muka leƙa
cikin labarun gargajiya da barkwanci, ba a rasa abubuwan tsinta ba a ciki. An
ce, wata rana kuturu da makaho suna taxi bayan an dawo da yawon bara. Kuturu na
yi wa makaho gori da cewa, su kaxai Allah Ya ambata a littafinSa a wurin da Ya
ce, “Wal fuƙara’u wal
masakina”. Kuturu ya ce, duk malamin da ke duniyar nan, ya san da kutare ake
zance ba kowa ba. Makaho ya yi dariya domin a ganinsa ya fi kuturu hujja mai ƙarfi. Don haka da bugun gaba ya ba da
bayani, ya ce: “Mu dai da Ya ce, “Walaƙad
mannannaa alaihim”, za a yi wa kuri? Da an kula sosai amsar da makaho ya bayar
ta bugun gaba ce, domin nassi ya fito ƙuru-ƙuru da faxar an manne musu idanunsu.
Shi kuturu ina aka nuna an ƙiƙƙille yatsunsu?
Na so mu ziyarci littafin Ruwan Bagaja wurin da
aka haxa Imam da Malam Zurƙe
ƙure (maƙabala)
da sarki ya so ya ji ra’ayi Imam a kan haxuwar sad a Malam Zurƙe ga yadda Imam ya mayar da gami:
“Ina tuna jahilan yaran almajirai ne masu ja da manya.
Lalle dai ƙaramin sani ƙuƙumi
ne.” (Imam, 1966:8)
BUGUN
GABA A WƘOƘIN BAKA
A nazarin waƙa
salo ya fi shahara da jan hankali. Da wuya a nazarci waƙa a manta da salonta abin ya yi
armashi. Na fi ganin laifin xaliban nazarin waƙa
da ke kallon jiya a yau ba da idon ƙara wa jiya tsawo ba, ko a kakkave
mata ƙura . A fannin waƙa, sukan sarrafa ‘Bugun Gaba”
gwargawon iyawarsu.
MAKAXAN FADA
Makaxan fada sun yi fice ƙasar Hausa sosai domin sarakunan ƙasar Hausa suke yi wa waƙa. A tsari siyasar zama gari, ko ƙasa, ko wata gunduma, sarki ne na
farko. Wanda duk ke cikin ƙasarsa
talakansa ne. Xaya daga cikin makaxan fadar Isa, Makaxa Ibrahim Narambaxa na
cewa:
Jagora: Kak
ku gama ni da yaro
Yara: Kun
san yaro bai yi fasashata ba
Jgora: kak
ku gama ni da yaro
Yara: kun
san yaro bai yi zalaƙata
ba
Jagora: Kak
kugama ni da yaro
Yara: kun
san yaro bai yi kamab babba ba
Jagora: Ƙaryar banza, ƙaryar wofi
Wane yaro inda Narambaxa
Yara: Mai
tabarukun Sarki
Gindi: Gogarman
Tudu Jikan Sanda
Maza su ji tsoron xan
Maihausa.
Narambaxa na bugun gaba da fasaharsa da basirarsa da
daxewa cikin fagen waƙa
tare da samun yardar sarki. Waxannan abubuwa da su Narambaxa ke bugun gaba,
kuma da yake shi ke wasa kansa da kansa ya zama salon “Bugun Gaba”. Ta fuskar
buwaya a fagen waƙa
yana cewa:
Jagora: Zamfara
ba Makaxin da ka ja mini
Yara: Baya
ga Xandawo sai ko Jankixi
:Sai Xandodo Alu mai Taushi
:Amma ba makaxin gayya ba.
Gindi: Gogarman
Tudu jikan Sanda
Maza su ji tsoron xan
Maihausa.
A bayyane za a ga kamar kirari makaxa ke yi wa kansa.
A faifan nazari za a ga bugun gaba ne yake yi da zara takwarorinsa mawaƙa da ya yi a ƙasar Zamfara.
MAKAXAN MAZA
A tsarin rukuninsu makaxan noma da dambe da kokuwa da
tauri da banga da mafarauta da masunta da maƙera
duk suna shiga ciki. Ga abin da Makaxa Xan’anace ke faxa a waƙar Nadelu:
Jagora: ‘Yan
makaxa ku na nan Arewa,
:Masu leƙa xan abin kixi
:‘Yan waƙoƙi
ƙire-ƙire
:Makixa ku dai ka hassadanmu
:To mu dai ba mu hassadakku
:Hwaxa musu ko sun yi
hassadanmu
:Ga banza an nan
:Makixa sai dai ku dangana
:Wani mai roƙo
ba a …
:Ba a sake mai da kama ta Hausa
Gnidi: Kai
maza suka shakku ko can
:Kiro Nadelu kutunkun vauna
Alhaji Bawa Xan’anace yana bugun gaban cewa, idan yana
nan da ransa, ko ya mutu, ba za a yi wani maroƙi
irinsa ba a ƙasar Hausa. Da shi
ake yi wa kixa, ya furta haka, abin zai tabbata kirari. Furta abin da bakinsa,
kuma shi ne uban kixa, shi ya tabbatar da abin zaman ‘Bugun Gaba’. Wani
takwaransa Yaro Hore Makaxin noma cewa yake yi:
Jagora: Xan
nan ha’ Ƙudus
:Ha’
Kano Yaro Mani
Yara: Ba
a yi uban kixi
:Wanda yad doke min ba
:Sai dai yaro an fi mu…
:Gangunmman hira
Gindi: Kama
hakalinka kullum
:Ka sa gamba lauxi
:Za ni wurinka
:Xangarba gunguman noma
MAKAXAN JAMA’A
Masana sun saka duk wani mawaƙi da ya shahara wajen yi wa jama’a waƙa ba tare da rarrabe wani fanni da
zai rinjayar da waƙoƙinsa ba cikin wannan rukuni. Wasu na
hangen gefen da waƙoƙin suka fi yawa. Wasu na ganin gefen
da ya fi shahara a fagen waƙa.
Ga misali daga waƙar
Halohalo ta Alhaji muhammadu Shata Katsina.:
Jagora: Ba
a samo canji na ba
:Belle in huta
:Belle in ce in sarara
:Yardar Allah ta fi ta kowa
:Na’abu xan Ibrahim
:Shata ne…
Gindi: Halohalo
mai ganga ya gode
:Yaran mai ganga sun gode
Alhaji Shata ya yarda da faxar wasu masu sha’awar waƙoƙin
baka ke yi na cewa, shi ne shugaban ƙasan
mawaƙa Hausa. Ban ce, ba shi ba ne amma
nuna ya yarda da maganar, har yana bugun gaba da cewa, ba a samo “Canjinsa ba”
balle ya aje waƙa
ya zauna ya huta, ya sarara. Hangen da yake yi na wannan xaukaka har ya furta
ta a waƙe da kansa ta bakinsa ba ta bakin
yaransa ba shi ya mai da furucin “Salon Bugun Gaba”.
MAKAXAN SHA’AWA
Makaxan sha’awa galibi abinda ya burge su ko ya burge
jama’a shi suka fi yi wa waƙa.
Rukuninsu babba ne a cikin rukunan mawaƙan
baka. Ga xan abin da Mamman Gawo Filinge ke faxa, a waƙarsa ta, “Ya Allah Gyara…”
Jagora: Ku
sauran ‘yan matan Gawo
:‘Yan ƙanana ne ba manya ba
:Ko nonon ba su fara ba
Yara: Manyan
ba su fi mu fasaha ba
:In don kalamin waƙa ne
:Da Larabawa za a kara mu
:Mu da Bature sai Hindu
:Amma fa ba Tukuru ba
:A yee borki …
… … …
Yara: Mu
mun iya ba mu koya ba
Jagora: Haka
nan na
Gindi: Ya
Allah gyara
:Wahabu ka taimaki ‘yan Nijar
FANXARARRUN MAKAXA
Mawaƙan
da ke yi wa abubuwan da al’adunmu nagartattun suka zarge su nake yi wa suna da
“Fanxararrun Mawaƙa”.
Cikin wannan rukunin kixin sata da kixin caca da kixin kwartanci da karuwanci
da dai ire-iren su. Ga abin da Alhaji Gambo Fagada ke faxa:
Jagora: Kway
yi kixan sata ƙasag ga
:Bai yi wa Gambo mai kixa ba
:Ko an cira ni kixan manyan kalangai
:Ba ka sanin sunan varayi
:Kamaw wada Gambo ke faxin su.
A wata rerawa yana cewa:
Jagora: Don
koway yi kixin sata irina,
:Ko ka yi kalangai ka cira
ni,
:Ba ka sanin sata irina,
:Don ba ka hwaxin sunan
varayi.
:Kamar wada Gambo ke
hwaxinsu.
Tabbas! Babu mai musun cewa, Gambo ya
san sata, ya san varayi matacci da na raye da na xaure. Faxar haka da kansa bai
bari a faxa ba, kuma a fagen waƙa,
shi kaxai ya tabbatar da virvishin “Bugun Gaba”. Da ya ga ana son a rena
imaninsa saboda irin kixan da yake yi, sai ya ce:
Jagora: Hwaman
ya’amal mis ƙaala zarra
:Wanda yas san Ƙur’ani irina
:Duniyag ga uban wa za
shi tsoro
Ga al’ada, mai yi ba ya faxa, balle a fagen karatu da
ake son ƙanƙan
da kai. Faxarsa ta nuna cikakken masani Alƙur’ani
ne, bugun gaba ne ƙarara
a bayyane.
MAKAXAN TASHE
Binciken tarihin rayuwar wasu makaxan baka na ƙasar Hausa ya nuna waxanda ba ‘yan
gado ba, da yawa, daga waƙoƙin tashe suka fara. Ga wani zance na
mawaƙin tashe na Tungar Bella da Taƙaji, suna cewa:
Jagora: Sai
dai a hi mu
:Kalangu da kurkutu
Yara: Amma
ba a fin mu
:Daxin baki
Gindi: Yau
da borin Goje
:Kana da borin tashe
MAKAXAN GIRSHI
Zamani ya kawo mu yau da mutum ya yi tsintuwar fasaha
sai ya zama mawaƙin
girshi. Wani lokaci a ji waƙoƙin abin yabo gwanin ban sha’awa, wani
lokaci ga su nan dai. Da yawa daga cikinsu xan lokaci kaxan suke su gama
yayinsu a manta da su. Ga wani xa daga xiyan waƙar
Ganxo Ambursa, cikin waƙar
“Ba a gane manya…”
Jagora: Musa
uban kixi
:Ni ban san ka da shakka ba
: Na san wurin kixi
:Kai kan ka wuce ‘yan yara
:Ni ko wurin xumi ka san
:Na wuce ‘yan yara
:Ko manya-manya sai in sun
:Yarda mu sasanta
Gindi: Ba
a gane manya
:Sai
ci ya samu
Yaba wa Musa wajen kixa, kirari ne aka
yi wa Musa. A vangare xaya kuma, faxar ya zarce yara wajen “xumi” (magana) da
cewa ko manya sai dai a sasanta Salon “Bugun Gaba” ne.
JIRWAYIN
BUGUN GABA A RUBUTATTUN WAƘOƘI
Ana yi wa waƙoƙin baka suna da waƙoƙin
hululuwa domin kutsawar su ga al’amurran da addini ya yi hani. Rubutattun waƙoƙin
su ne, waƙoƙin masana addini da almajirai da
masoya makaranta. Yanzu, zamani ya kutsa cikinsu sosai, yadda duk ake samun
salon “Bugun Gaba” cikin waƙoƙin baka, haka ake samu a cikinsu. Ga
xan misali a kwatanta:
WAZIRIN GWANDU ALHAJI UMARU
An yi kundin digirin BA da PhD a kansa Ikara, (1982)
da Usman, (2008). Cikin waƙar
Yabon Sarkin Gwandu Yahaya, ya ce:
Na saba miƙa
shexara
Ta tsaya tsaf babu tanƙwara
Ai waƙa
ba ta gagara
Muddin na tashi fassara
Wada duk nika so ina
hwaxi rarara
(Sa
maza gudu)
Idan malami ya kai ga furta fagen da ya buwaya da
bakinsa da iƙirarin cewa, ya
wuce kure a ciki abin ya zama ‘bugun gaba’.
AƘILU ALIYU
An yi rubuce-rubuce da yawa a kan waƙoƙinsa,
fitaccen aikin da aka yi a kan waƙoƙinsa shi ne, Muhammad, (1977) kundin
PhD. A wata waƙarsa ta “Noma
tushen arziki” yana cewa:
Na dai shiga takarar waƙe
Kaina tsaye zuciya miƙe
Ba jirge na zo ba ko duƙe
Tsini ba ya zama feƙe
Ba zan zama wai ga waƙa ba.
Wannan xangon dukkaninsa bugun gaba ne xango na ƙarshe ya fito ƙuru-ƙuru
ga mai marare.
SAMBO
WALI
An yi rubuce-rubuce da yawa a kan waƙoƙinsa.
An rubuta kundayen digirin BA kusan 3 – 4 akansa. Shahararren aikin da aka yi a
kansa shi ne, Bunza, (2002). A waƙarsa
ta “Zaman Banza” yana cewa:
Idan an tabbai ka xan’uwa wat tsara ta
Wali Sambo ka tsara wagga muddin waƙa ta
Gixaxawa za ka je ki can na shiyata
Dawaman roƙon mukai Gwani don ya tsare mu
GARBA
GWANDU
An yi aikin digirin BA a kansa, Balarabe (1980), an yi
nazarce-nazarce da yawa a kan xaixaikun waƙoƙinsa. A waƙarsa ta “’Yan makaranta” yana cewa:
G. G. na Maikudu sha’iri ƙi fansa
Shi yay yi waƙar ‘yan sukul nan Hausa
SAKAMAKON
NAZARI
Muradin shi ne a fahinci bambanci kirari da bugun
gaba. Idan har kirari na da kasonsa mai tsoka cikin nazarin salailan adabi, ya
kyautu a share wa Salon Bugun Gaba, fili mai faxi. A ganina, Salon Bugun Gaba,
ya ratsa dukkan sassan Adabi da Al’ada da Harshe na Bahaushe. Da wuya a yi
nazarin wata waƙa
ta baka ko rubutacciya ba a ci karo da shi ba. Haka kuma, taskar karin magana
da salon magana da shaguve da azanci da barkwanci da tatsuniya da labarum gargajiya
duk ana samunsu a ciki. Rubuce-rubucen littattafanmu na ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo da
finafinan Hausa yana ciki tsumbul ba tsintuwar dami a kala ba ne. tabbacin
samuwarsa haka shi zai ba mu damar mu kalli kayan cikinsa kama haka:
i.
Tushe: Iyaye
da kakanni, d.s.
ii.
Asali: Harshe
da ƙabila, d.s.
iii.
Baiwa: Fasaha
da fahimta da sani, d.s.
iv.
Koyo: Ƙwarewa da gogewa da iyawa, d.s.
v.
Togiya: Hawa
da nuna wuraren da aka fi wani
vi.
Suna: Ficen
suna da zarta tsara
vii.
Turke: Za
a yi turke ga abin nan da ake zance a kansa
Da wannan xan taƙaitaccen
bayani zan ce, ya kyautu mu sanya ‘Salon Bugun Gaba’ xaya daga cikin salailan
da ake tsettsefewa wajen nazarce-nazarcenmu. Gadon fixa da na zana bakwai, na
zana su bisa ga xan binciken da na yi, da fatar za a taya ni gyare-gyare da ƙare-ƙare
da rage-rage mu daidaitu mu ciyar da harshenmu gaba.
NAXEWA
Hausawa na cewa, zama wuri xaya tsotsayi in ji ƙuda. Na yarda da faxarsu ta cewa, da
koyo akan iya. Yana da kyau masana da manazarta da mu xalibansu mu yi riƙo ga karin maganan da ke cewa, da
rashin tayi akan bar arha. Haƙiƙa in dambu ya yi yawa ba ya jin mai.
Don haka, muna da jan aiki a gabanmu na zage dantse mu ga muna bitar ayyukan
magabata, da niyyar ƙara
kyautata su da inganta su domin su kasance wandon roba daidai da kwankwason
kowane irin zamani. Na tava gabatar da wani salo kimanin shekara biyu da suka
gabata, mai suna “Ingiza Maikantu Ruwa”. Na gabatar da shi a Jami’ar Umaru Musa
‘Yaraduwa, Katsina. Na kuma aika da binciken ga masana fannin waƙa fitattu domin su taya ni
gyare-gyare, kuma an wallafa ta a mujallarsu ta HIMMA. Da fatar wannan ta shiga
sahun waccan bayan na karvi gudunmuwarku. A taƙaice
Salon Bugun Gaba shi ne:
“Furucin da wani mutum zai yi a cikin zancensa ko waƙarsa ko rubutunsa yana ƙoƙarin
fito da irin martabarsa ko ƙwazonsa.
Galibi idan fagen fasaha ne, mai bugun gaba zai yi bugun gaban da fasaharsa ne
da ya yi fice da ita. Idan fagen awon mutunci ne da sauran sassan da gidajen
shida za a yi iƙirari.”
MANAZARTA
Alƙali, A. (1989) “Cuxexeniyar Adabi:
Tasirin Adabin Baka A Kan Rubutattun Waƙoƙin Hausa Dangane da Habaici da Zambo
da Kirari da Karin Magana”, kundin digirin MA, Kano, Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (1994) Yaƙi da Rashin Tarbiya Cin
Hanci da Karvar Rashawa Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo
Wali Basakkwace, IBRASH Lagos
Bunza, A. M. (2009) Narambaxa,
IBRASH Lagos
Bunza, A. M. (2011)
“Sakkwato ce Tushen Hausa In Ji Narambaxa”, Muƙala,
Jami’ar Umar Musa, Katsina.
Birnin-Tudu, S. Y. (2002)
“Jigo da Salon Rubutattun Waƙoƙin Furu’a na Ƙarni na Ashirin”, kundin digirin PhD,
Sakkwato, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
Birniwa, H. A. (1987) “Conservatism and Dissent: A comparative study
of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Circa 1946 – 1983”,
unpublished PhD thesis, University of Sokoto.
Xangambo, A. (1980) “Hausa Wa’azi Verse from Circa 1800 – 1970: A
Critical Study of Form, Content, Language and Style”, PhD thesis, University of
London.
Xangambo, A. (2007) Xaurayar
Gadon Fexe Waƙa.
Kaduna: Amana Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa
Yanaye-yanayensu da Sigoginsu, Benchmark Publishers
Limited.
Gusau, S. M. (2009) Diwanin
Waƙoƙin Baka: Zavavvun
Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa,
Century Reseach and Publishing Limited, Kano – Nigeria.
Hiskett, M. (1975) A History of Hausa Islamic Verse, SOAS, London University.
Ikara, A. T. (1982)
“Umaru Wazirin Gwandu da Waƙoƙinsa”, kundin digirin BA, Zaria,
Jami’ar Ahmadu Bello.
Imam, A. (1966) Ruwan
Bagaja, NNPC, Zaria
Muhammad, D. (1977) “Individual Talent in the Hausa
Poetic Tradition a Study of Aƙilu
Aliyu and His Art” PhD thesis, SOAS London, University.
Omar, S. (1983) “Style
and Theme in the Poems of Mu’azu Haxejiya” MA, thesis, SOAS London University.
Sa’id, B. (1978)
“Gudummuwar Masu Jihadi kan Adabin Hausa”, kundin digirin MA, Kano, Jami’ar
Bayero.
Sa’id, B. (2002)
“Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin, A Sakkwato a Kebbi
da Zamfara”, kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Usman, B. B. (2008)
“Hikimar Magabata” kundin digirin PhD, Sakkwato, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
Yahya, A. B. (1987) “The Verse Category of Madahu with Special
Reference to Theme, Style and Background of Islamic Sources and Belief”. PhD
thesis, University of Sokoto.
Yahya, A. B. (2001) Salo
Asirin Waƙa,
FISBAS Media Services,
Kaduna.
No comments:
Post a Comment