Showing posts with label WAƘOƘI. Show all posts
Showing posts with label WAƘOƘI. Show all posts

Monday, October 14, 2019

Gaskiya A Кi Ki, A So Ki

October 14, 2019 0


Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta wannan waƙa ranar 8 ga watan Ogusta, shekara ta 2019. Tana da adadin baituka arba’in da biyu (42). Ta kasance ‘yar ƙwar huɗu.

Wednesday, January 2, 2019

Mutuwa

January 02, 2019 0


Roƙo nika yi ga Wahidun mai gyarawa,
Sarkin da ya zarce masu ilmi ganewa,
Kai kay yi sama’u kay yi ƙassan zaunawa,
Kay yo Aljanna kai wuta mai ƙonarwa,
Kay yo duniya da rayuwa don zaunawa,
Kaƙ ƙaddaro lahira ga ƙarshen komawa,
Kowace rai la muhala ƙarshen ta macewa,
Tilas in ya mace ƙasa zai komawa,
Tsoron mutuwa ga masu rai bai ƙarewa,
Domin ba ta kure da ta zaka kamawa,
Ɓera bai ce wa mage sannu da hutawa,
In sun gamu hanya wa mutum sai rugawa,
Don me akuya ka ba da bai babu tsayawa?
In kura ta yi mui guda ba ta tsayawa.

Ta’aziyyar Mallam Ibrahim Awwal Albaani Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

January 02, 2019 0


1.       Shukura ga Allah guda masani halin kowa,
          Mai ƙaddarowa ta tabbata babu mai tsawa,
Ya mai hukuncin da ba makara da gaggawa,
Masanin da ilminSa ya wuce hankalin kowa,
          Subhaana lil laahi tsarki na ga Rabbani.

2.       Na yo salati ga Manzo shugaban bayi,
Ahalinsa dukkan sahabbai ƙoƙari sun yi,
Na riƙo ga sunna ta sadu da mu ruwan sanyi,
Mariƙa amana sahada kun riga kun yi,
          Matsayin shahidi ga nassi babu saɓani.

3.       Mai rai a ce ya mace ba al’ajab ne ba,
Mutuwar shahada buki ne ba na wasa ba,
Ita ce manunin aƙida ba ta yi ƙura ba,
Ita fassara ce mutum bai tabka shirme ba,
          Shaidarmu ke nan ga Awwalu namu Albaani.

Sunday, December 30, 2018

Maƙarƙashiya

December 30, 2018 0


Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ya”. Yawan baitocinta hamsin (50). An kammala ta ranar Lahadi 25/05/2014 daga Masar zuwa Katsina, an haɗa ta a Kano, Mumbayya House, BUK, ɗaki na 10. Ga dukkanin alamu kashe-kashe da zubar da jini da ta’addancin da ake son a liƙa wa musulmin Arewacin Nijeriya, maƙarƙashiya ce. Tilas, a sake zama a nazarci matsalolin da idon adalci a ɗebe bambancin addini da aƙida da siyasa da yanki da ɓangaranci. Zancen Boko Haram wata sabara ce da ake fakewa da ita a harbi barewar da ake son a kashe. Idan haka ne kuwa, ya zama dole a sake lale ‘yan dara, a hura wuta kowa ya ga rabonsa, komi taka zama ta zama.

Ganin Ido Nassi Ne Da Babu Ƙila-Wa-Ƙala

December 30, 2018 0


Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “wa” yawan baitocinta saba’in da ɗiya (71). An kammala ta ranar Larba 8/01/2014 a kan hanya tsakanin Katsina zuwa Sakkwato. Burinta kakkaɓe ƙura ga ‘yan kurakuran da suka gabata na rikicin ganin watan Ramala na shekarun 2012, 2013 da 2014. A shari’armu, yaƙinin ganin wata ya kore kowane irin tawili. Ana dogara da yaƙinin gani a kawar da maganar kowa, komai nauyinsa a sikelin zamaninsa. Idan ganin ido ƙuru-ƙuru ya tabbata zancen kalanda da kwamfuta da hisabi ba su da gurbin zama in ji Manzon Allah (SAW). Ƙaryata yaƙini domin sauraren umurnin wani ko wasu cin dugadugan Manzon Allah (SAW) ne. Fatawa da tawili da ƙiyasi da duba zuwa ga al’adar ƙasa/jama’a na siyasar shugabancinta duk ganin yaƙini ya haramtar da su. Dogara ga ganin ƙasa mai tsarki ko kirdadon ibadojin da ake gudanarwa ciki na tsayuwar Arfa da yanka ba ya da madogara ga littafin Allah da Hadisan ManzonSa (SAW). Kawar da kai ga yaƙinin ganin wata a kan kowane irin dalili saki zari kama tozo ne. Annabi (SAW) bai ɓoye komai a saƙon manzancinsa ba. Da wane dalili za ka bar umurninsa ka bi sabaninsa?

Saturday, December 29, 2018

Kifi Na Ganin ka Mai Jar Homa!

December 29, 2018 0


Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ƙe”. An gina ta da baitoci talatin da uku (33) an kammala ta Alhamis 16/01/2014 da ƙarfe 11:05 na dare a Arkilla, Wamakko jihar Sakkwato. Babban abin da ke hana wa ruwa gudu a rayuwar ‘yan Adam ita ce hassada. Jiyewa mutane, da ƙin su da ɓata su da kushe cigabansu da rena ƙwazonsu da wulakanta nasarorinsu da shafa musu kashin kaji duk hassada ke haifar da su. Ɓata lokacinka na ƙoƙarin nuna cikas ga wani ba kai ba, shi zai ba da damar a gano babban cikas da ke a ƙirjinka na hassada. Me zai hana idan ka san ba yabawa za ka yi ba, ka sa wa bakinka takunkumi? Da ka bi wannan shawara, ka huta, an huta da kai.

Laifi Tudu Ne

December 29, 2018 1


Waƙar ƙwar uku ce, babban amsa amonta “na”. Yawan baitocinta saba’in da shida (76). An kammala ta ranar 10/06/2013 a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina. Mai yawo lisafin laifukan mutane da leƙen kasawarsu da ƙoƙarin ci musu zarafi da muzanta su bai tsaya da kyau ya karanci nasa hali ba. Don haka, waƙAr take hararar abubuwan da mahasada da magabta da ‘yan sa ido da ‘yan sai-mun-gani ke ƙoƙarin kai hari ga marubucinta. A ganin Bahaushe, mutum duk ɗan tara ne. Da akwai ɗan goma, da shi ya kamata ya yi wa ‘yan tara kallon kifi na ganin ka mai jar koma (homa). Kama kanka! Wanda ke cikin ta tsaka mai wuya, ina ya ga bakin kirari?

Allah Ba Ka Da Dole

December 29, 2018 0



An tsara waƙar a tsarin ‘yar tagwai. Babban amsa amonta “wa”. An tsara ta cikin baitoci saba’in da tara (79). An kammala ta ranar Jmu’a 25/1/2013 a Sakkwato. Addu’a ce da godiya ga Allah ga irin taimakonSa ga bayinSa ga tsallake tarkon miyagun abokan zaman zamani. Godiya ga Allah wajibi ne ga kowane bawa, bale wanda Allah Ya kuɓutar da shi ga tarkon makircin abokan ƙarshen zamani “kifi ku ci ‘yan’uwanku”. Allah Ya yi muna tsari da tsarinSa. Amin!

Kaska

December 29, 2018 0



Waƙar Kaska mallama ce (ƙwar biyar). Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta hamsin da takwas (58). An kammala ta ranar Lahadi 30/6/2013, a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa Katsina. A ganin Kaska, siyasar zamani ta demokraɗiyya ita ta jefa ƙasarmu cikin musibun da take ciki a yau. Siyasar zamani ta tarwatsa saraua da masarautu. Ta gigita addini da mabiya. Ta muzanta malaman addini, da ma’aikatan hukuma. Ta ɓata wa talaka tunani. Ta sagarta matasa maza da mata. Ta danbala ‘yan kasuwa. Ta yi wa gaskiya idon marurugiya aka yi wa ma’abotanta ƙofar raggo. Da dai an koma ga tsarin da wanda ya yi halittu. Ya shirya wa halittunSa, da abu ya fi.

Kashi Ya Game An Sake Rabawa

December 29, 2018 0


Waƙar mallama ce (ƙwar biyar). Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta saba’in da uku (73). An kammala ta ranar Jumu’a 19/05/2013 a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina. Saƙonta gargaɗi ne ga ma’abota riƙo da kira zuwa ga sunnar Manzo (SAW) da su gyara zama ciyawa ta ci doki. Abubuwan da aka kora a da, a yanzu ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Idan maƙoƙo ya fito a bakin zabiya zancen waƙa da zaƙin murya ya ƙare. Ina laifin wanda ya gaya maka bakinka na wari ka nemi ruwa da asawaki ka wanke ɗoyin ya kawa! Matuƙar imani na ƙaruwa da raguwa, to, namu ya ragu. Allah Ya cece mu.

Gyara Kayanka

December 29, 2018 0


Wannan waƙar ‘yar ƙwar hudu ce. Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta ashirin da takwas (28). An kammala ta ranar Jumu’a 28-05-2013 a garin Katsina, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa. Kira take ga jama’a da su guji giba da tsegumi da yaɗa ji-ta-ji-ta da hassadar abokan zama. Ta yi wa zunɗe da raɗa da kwarmato da an-yi-an-ce da sa ido zangazanga. Matuƙar aka ba su tsoro suka guje wa wuraren shawagin ‘yan Adam, za a samu zaman lafiya.

Jiya Ba Yau Ba

December 29, 2018 0



Wanda duk ya ga jiya, ya san yau na buƙatar agajinmu. Ganin irin riƙon sakainar kashi da na yau ke yi wa al’adunmu na jiya shi ya tunzura ni rubuta wannan waƙa. Masu gani dole sai an sa su, da masu ganin ba a yi sai da su, sun yi kuskure. Hausawa sun ce, wanda ya riga ka barci dole ya riga ka tashi. Idan za a yi koyi da gabaci ba za a ci wahalar sakamakon bin son rai ba. A ganina, har gobe mazan jiya guntun igiya ne, ko kun ruɓe akwai ranarku. Matasan yau kuwa man kaza ne, in rana ta yi su narke.

Ta’aziyyar Kaftin Umaru Ɗan Suru

December 29, 2018 0


Na rubuta wannan waƙa ranar Talata 11 ga watan Disamba na shekarar 2012. Na yi ta ne a Sakkwato. A lokacin ina aiki a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato Nijeriya.

Friday, December 28, 2018

Anya Dai! Mu Taka Sannu

December 28, 2018 0


Ga alama abubuwan da magabata suka hanga bisa ga nassohin bayyanar ƙarshen zamani sun yi kere a zamaninmu. Manya da ƙananan alamomin tashin duniya sun yi wa zamaninmu dumudumu. Maƙasudin wannan waƙa jawo hankalin masu hankali a kan sake bitar waɗannan abubuwa da idon basira. Ganin irin nisan da muka yi ya sa na kira mu da muryar: Anya Dai! Mu Taka Sannu. Na rubuta ta ranar alata, 28-01-2014, 11:38pm, a Katsina.

Thursday, December 27, 2018

Malammai

December 27, 2018 1



1.                 Ni kiri Rabbana Jalla mai iko sarkin sarauta duka,
Sarkin nan da yay yo dare rana sammai da ƙassai duka,
Wanda Ya ƙaddaro rayuwa mutuwa ikonSa ce Maiduka,
Ba makawa ga bayi kiranKa buwayayye gwanin ɗaukaka,
          Mai ilmin da ya kewaye komai da saninSa yat tabbata.

2.       Nasa sani gwani fil azal yake komai ba ya ɓoye Masa,
          Babu kure bale mantuwa wane wahami ya riskan masa,
Shi yat tsara kaiNai da ilmiNai haka mun ka iske masa,
Ba ma shisshigin binciken ilminKa da istiwa’i bisa,
  Ɗan ilminmu bai kai ba, in mun ce mu yi, nan yake barkata.

3.       Don haka mumini ba ya ɗanga ba ya bugun gaban ya sani,
Taka sannu Modibbo, hayya da cewa: “wane mi yas sani”,
Allah Ya faɗa ba sani tari a cikinmu sai ƙanƙani,
Wanda ka taƙaman ya iya ƙarshe sai ya yi da na sani,
  Bil’amu yak karantar da mu masani duka bai wuce karkata.

Lokacin Abu A Yi Shi In Ana Son A San Shi

December 27, 2018 0


1.                 Mu gode Allah ɗaya mai komai
Da yay yi komai a lokacinai,
Yay yi hukunci bisa yardaTai,
     Ga lokaci wa ka karkare shi?.

2.                 Bisa yardaTai ya ƙago bayi,
Ga ƙassai ga sama’u Ya yi,
Da fasullan shekara da yay yi,
     Na lokaci ba a gurgasa shi.

3.                 Shi dai waƙaci a kiyaye shi,
In ya zo ba a tunkuɗe shi,
Mai iƙirarin ya gurgusa shi,
     Kar ku yi shakka ga ƙaryata shi.