Saturday, December 29, 2018

Ta’aziyyar Kaftin Umaru Ɗan Suru



Na rubuta wannan waƙa ranar Talata 11 ga watan Disamba na shekarar 2012. Na yi ta ne a Sakkwato. A lokacin ina aiki a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato Nijeriya.
                                     ----------------------------------------------
DAGA
ALIYU MUHAMMAD BUNZA
---------------------------------------------
  1)      Mu ce, ƙalu lillah wa inna illaihi,
                   Raju’i dole na.

2)      Dukan mai rai ƙarshensa
                   Kwancin kushewa, ce haka ko’ina.

3)      Idan aka sance rai jiki,
                   Ya zamo gawa daɗa sai gina.

4)      A wanke jiki a suturce gawa,
                   A kai ramensa a jingina.

5)      A bar mu muna ‘yan kokekoken
                   Rashi daga nan kuma sai ina?

6)      Mu ɗuru cikin kewar da,
                   Ba ta gushewa, rai baƙonmu na.

7)      Ziyara an ka izo mu nan duniya,
                   Mu gama ta mu dangana.

8)      Da tsufa ko yarantaka,
                   Lokacin kowa an ayyana.

9)      Da ya cika al’amarin,
                   Zaman duniya ya ƙare ko’ina.

10)    Ina Arƙilla gida waya,
                   Ta ishe mini saƙon girshi na.

11)    Haruna na Maikwari ke,
                   Gaya min abin nan sai da na jingina.

12)    Ya ce “Saƙo yaz zo garai,
                   Da Abuja rashin babanmu na”.

13)    Fasihi baban Hafsa,
                   Dogo na kulwa abin kaunanmu na.

14)    Imamin Kulwa wajen siyasa,
                   Fulani sun ce “Gonga na”.

15)    Gwanin fara’a wasa da yin dariya,
                   An san haka ko’ina.

16)    Ma’ilmantan farko ƙasar Kulwa,
                   ‘Yan boko babanku na.

17)    Mazan tsaye gun yaƙi,
                   Gidan soja Ummaru ka kai ko’ina.

18)    Ga kishin Kulwa irinka samun sa,
                   Tilas sai an sunsuna.

19)    Fice da hazaƙa ɗaukaka Suru,
                   Ko maƙiya sun jinjina,

20)    Sanin jama’a da riƙonsu,
                   Ba kissa mun shede shi halinka na.

21)    Ga jagorancin Suru,
                    Hatta Jagwadawa yaranka na.

22)    Waɗanda ke ta da gaba,
                   A yau Suru duk sanadin ƙwazonka na.

23)    Hawan mota, ƙaton gida,
                   Kamfanin mai duk renonka na.

24)    Shiga babban ofis, galila da shadda,
                   Manyan riguna.

25)    A ta da gaba a yi rangaji,
                   Wa mutum nan! Ɗalibbanka na.

26)    Ana kakak girbi ga gandunka,
                   Ga wa’adi ya ayyana.

27)    Ka ce, “Sai mun haɗu gobe,
                   Ranar ƙiyama can gun Rabbana.”

28)    Mafifici, mai ƙaddarawa, Gwani,
                   Bawa dai naka na.

29)    Ga alƙawalinKa da kay yi,
                   In babu shirka ceto Naka na.

30)    Kana yafe manya, ƙananan,
                   Zunubbai alƙawalinka na.

31)    Haƙiƙa kowa kat tsure lahira,
                   Bai tsira ko’ina.

32)    Idan ka gafarce shi,
                   Ya tsira ko ya zan Ƙuddaru na.

33)    Buƙatar sha’irran ƙasar Hausa,
                   Shi nika son in bayyana.

34)    Muna roƙon jinƙai ka sa rangwame,
                   Kaftin babanmu na.

35)    Ka sa rahamarka ta lulluɓe,
                   Duk kurakuransa na ko’ina.


36)    Ka ƙaddarce shi ya sha,
                   Ruwan kausara ko da ‘yan tsito na.

37)    Ka yafe mai zunubansa,
                   Ka san su sosai in da ya munana.

38)    Ka sa jinya ta zamanto,
                   Kaffara gunai ya mai ko’ina.

39)    Ka sa shi cikin Firdausi,
                   Ko baki-baki a kai shi a dosana.

40)    Baƙutata dogo ya miƙe,
                   Ƙafarsa cikinta ya jingina.

41)    Ya sha raɓar Firdausi,
                   Sanƙonsa duk ya yi gashi ko’ina.

42)    Cikin ni’imar Aljanna,
                   Hatta da ‘yan karɓinsa ka dunguna.

43)    Da ɗalibbanka na Suru,
                   Ɓi Bello, Gurdumu, duk yaransa na.

44)    Ina roƙa muku gafara,
                   Yanzu tanzankon duka namu na.

45)    Haƙiƙan sha’irran ƙasar Gwandu,
                   Mun shiga ɗakin fursuna.

46)    Siyasar Kulwa shirinta zai wargaje,
                   Ƙarshenta jina-jina.

47)    Haɗin kan Surawa ga dubanmu,
                   Yanzu abin nan taugo na.


48)    Tsaya wa talakka a ƙwato haƙƙinsa,
                   Ba a barinsa a muzguna.

49)    A yau ya ƙare Kulwa,
                   Domin kama da su Kaftin ƙila na.

50)    A ja waƙa tamkar ana shan ruwa,
                   Ɗan Kulwa halinka na.

51)    A gargaɗi kalmomi su dace,
                   Cikin ɗango sai sun nuna.

52)    Su darkako su tsaya ga baiti,
                   Karinsu ya dace ko’ina.

53)    A sa murya ka ji ta yi daɗi,
                   A tsunduma manyan koguna.

54)    Haƙiƙan ko Shata ya saurari,
                   Ummaru sai ya jinjina.

55)    Narambaɗa ya san an yi,
                   Mai rambaɗar baiti ga takarduna.

56)    Su Alfazazi da suna raye,
                   Za su cire maka hulluna.

57)    Da kai har su yau,
                   Kun wuce gafara ta ishe muku ko’ina.

58)    Kurakuranka muna du’a’i,
                   Ya gafarta muku Rabbana.

59)    Fulani don ƙaunarka sun bar faɗa,
                   Sun dangane sanduna.


60)    Kabawa sun yafe hakin “Maro”
                   Nagge ta cinye burgu na.

61)    Manoma sun yafe harawa,
                   A tura bisashe ko’ina.

62)    Masunta sun bar dala,
                   Don kar su cuci ƙananan kifuna.

63)    Maƙera ka sake ɗorawa,
                   Cin tama a yi ko gonanka na.

64)    A samu ƙarafa masu ƙarfin,
                   Da za a yi manyan kwasuna.

65)    A wa yunwa kabari a bizne ta,
                   Kulwa, a huta ko’ina.

66)    Ina ta’aziyya gun Jagwadeji,
                   Ɗauki Balarabe ɗanka na.

67)    Ina Malam Musa garin Suru,
                   Yaƙin baiti namu na.

68)    Kiro mini Gaarus in yana nan,
                   Da Ɗan’iya duk saƙonku na.

69)    Da Malami Jaɓɓi na Bunza,
                   Sannan da Hircin Koko ku zo mana.

70)    Ku iske Ɗanmasanin garin Jega,
                   Gun waƙa babanmu na.

71)    A tsaro baitocin du’ai,
                   Ga Kaftin domin Rabbana.


72)    Fa tammat na gode wa Allah,
                   Da zan cika tsarin baituna.

73)    Aliyu na Bunza haƙiƙa,
                   Allahu mai karɓan roƙonka na.


No comments:

Post a Comment