Wanda
duk ya ga jiya, ya san yau na buƙatar agajinmu. Ganin irin riƙon sakainar kashi da na yau
ke yi wa al’adunmu na jiya shi ya tunzura ni rubuta wannan waƙa. Masu gani
dole sai an sa su, da masu ganin ba a yi sai da su, sun yi kuskure. Hausawa sun
ce, wanda ya riga ka barci dole ya riga ka tashi. Idan za a yi koyi da gabaci
ba za a ci wahalar sakamakon bin son rai ba. A ganina, har gobe mazan jiya
guntun igiya ne, ko kun ruɓe akwai ranarku. Matasan
yau kuwa man kaza ne, in rana ta yi su narke.
--------------------------------------
Aliyu
Muhammad Bunza
--------------------------------------
1.
Da sunan Allah
guda Tabara abin bauta,
Mafifici
ka buwai Buwai ga buwayarwa.
2.
Salati ga
manzonKa ka umurce mu dukkanmu,
Biyayya
muka yi gare Ka babu musantarwa.
3.
Bahaushe na ce
wa zamani babbar riga,
Idan waƙaci ya yi sa ta shi ne wayewa.
4.
A nau ra’ayi
hankali ka sa a saye riga,
Ga fuskarta ake ganin alamar dacewa.
5.
Irin manyan
riguna na da ɗirka-ɗirka,
Wadatattu masu kyau da ƙarfi da daɗewa.
6.
A da rigar taƙama ga kowa a
wadace,
Ya zam mai kunya a ko’ina za ya tsayawa.
7.
A san ka da
kunya a ko’ina wata sutura ce,
Gwanin ban sha’awa da walƙiya mai burgewa.
8.
Maras kunya ko
cikin gidansu abin ƙi ne,
Abokin hulɗa cikin gari za ya rasawa.
9.
Da an gan ka da
shi, akan kira ka a ja kunne,
A ce, hayya! Da kanka in kana son morewa.
10.
Rashin kunya ƙetare ƙafafun
magabata,
Anai musu kallon na da, da ba su da ganewa.
11.
A da in babba
yana ɗumi ba mai tari,
Ya ƙare jawabi ana shiru ba a muɗawa.
12.
Da ya ce a yi,
nan da nan da sauri a gama shi,
Da ya ce a bari, zama guda ba a daɗawa.
13.
Idan ya ce
kayya! Ko ƙafa ba a ɗagawa,
Bale ya yi ƙyacci zama guda aka rugawa.
14.
Da ya yi harar
guda ana gane nufinsa,
A ce
masa na tuba, na bari, ban ƙarawa.
15.
Idan yai nune,
gaban ya ce, an ruga can,
Da
girgiza kainai zama akai ba motsawa.
16.
Ba za ka ji an
ja ba, in ya ce ya lamunce,
Idan ya
kaɗa kai, a dole ne aka fasawa.
17.
Da ya ja layi,
aradu ba mai gitta shi,
Da yai
wafaati cikin wasiyya aka sa wa.
18.
Idan ya raba
gardama, a dole a shashance,
Da ya
riski ana faɗa ido yaka ƙwalawa.
19.
Abokan damben
da kokuwa za su yi zungum!
Faɗa ya mutu, ba gunagunin zan ramawa.
20.
A cacar baki
shiru yakai bai ɗaga baki,
Da jin
zarmoɗansa bakuna na kullewa.
21.
Idan ya yi rabo
kashin gabanka kake kwasa,
Batun zaɓe, tsallake kashi, ko farawa.
22.
Idan an ga shi
zaune, za a je can a ishe shi,
Anai
masa barka da yamma sannu da hutawa.
23.
Da safe idan an
ga ya fito tarbon hantsi,
A je a
yi kwal lafiya da barka da fitowa.
24.
Idan aka hango
ya ɗauko kaya bisa kansa,
Tara
masa kanu a kai ya zaɓi na ɗorawa.
25.
Lalura duka
babba ba ya roƙon a taya shi,
Gabaci
aka wa da gaske ko bai godewa.
26.
Faɗin sunanai ƙiri-ƙiri cin fuska ne,
Bale laƙabi wa mutum ya
ce zai furtawa?
27.
Kiran sa akai
“baba” ko’ina aka tar da shi,
Gabaci yab ba shi zamani bai ƙwacewa.
28.
Zama mai hali
zama da ilmi duka oho!
Da an ga
samanai da hurhura sai duƙawa.
29.
Talakka ya
zamto walau da mulki duka daidai,
Gabaci
aka wa da shekarunsa na tsohewa.
30.
A rauni uban
mai kuɗi ya ce za shi gara shi?
Dugaduggainai
ka agajinsa ga ɓoyewa.
31.
A yau me yas
samu zamaninmu na ƙarninmu?
Gabaci
an sa shi tagumi bai da sakewa?
32.
Yana kallo an
aje shi gefe an manta,
Kaman
jiya ba ta agaza wa yau ba ga tasowa.
33.
Idan ba jiya
yau da wa ake labarinta?
Haƙiƙan ita tay yi
yau da gobe ga tsarawa.
34.
Idan ba jiya,
babu gobe, jibi a bar zance,
Bale
citta, da gata, shekaran jiya, ƙarawa.
35.
Da yanzu, da in
an jima, da ɗazu, batun yau ne,
Idan ba
jiya, lisafinsu yau, ba shi fitowa.
36.
Ashe wanda ya
rayu yau, daren jiya yar rayu,
Na gobe
daren rayuwarsa yau, jiya zai cewa.
37.
Tunanin jiya,
in na yau ya ce, ba ya kula shi,
Ya ɗirku cikin ɗemuwa da wauta da ɓacewa.
38.
Fasahar jiya,
in na yau ya ce zai ture ta,
Dabarar
yau ko da tagumi taka ƙarewa.
39.
A wayonmu na
yau, a sa matasa gaba ɗungum!
Tunaninmu
saboda shekarunsu na tasawa.
40.
Ina suka taso?
A hannuwan wa suka rayu?
Dashen asali dag gare shi reshe ka tsirowa.
41.
Idan tushen ya
ruɓe batun rassa ba su,
Da ganye
da fure da ‘yan ɗiya ba tartsowa.
42.
Da me ɗan yau zai gwada wa ɗan jiya wayewa?
Tuwon
jiya aka zazafe na yau sai lecewa.
43.
A ba kurma
rediyo da me yaka saurare?
Makaho
ya yi bidiyo da me zai kallawa.
44.
A sa ɗan yau madugu mazan jiya na zaune,
Idan
hanyar ta yi turunƙu wa aka sa wa?
45.
Dabarun yaro
fagen faɗa ai ta karawa,
A
nakkasa ƙarfi a sha wuya har shurewa.
46.
Mazan jiya
makasar faɗa suke dinga faɗaɗe,
Bugu ɗaya, in dai a faɗi, in ko rugawa.
47.
Da an faɗi fagen faɗa batun ya kai ƙarshe,
Idan an
ruga da an tsaya ba a daɗawa.
48.
Matashi lotto
gare shi mai rata babba,
Dare
duka burinsa gobe zai daɗa holewa.
49.
Mazan jiya
kwana da zullumin yau ko gobe,
Da sun
sara gatarinsu ɗai suka dubawa.
50.
Mazan jiya ko
sun yi kuskure don jama’a ne,
Na yau
don son ransu ne da burin burgewa.
51.
Na da, in an ƙaryata su sai
zub da hawaye,
Su
kwashi kawaici jiɓi ya dinga tararowa.
52.
A yau, ƙarya an aje ta
wayo da ƙwarewa,
A shaara
ta a soka rantsuwar ƙin ƙarawa.
53.
Ɓarawo kunya ka sa ya ƙaura ya salwance,
Ya bar
al’ummarsa rayuwatai da macewa.
54.
Ɓarayin yau su ka mai kiɗi su ka maroƙa,
A
kunyata kunya ta kunyace da kuranyewa.
55.
Ɗiya matan da saboda tsabar kunyarsu,
Ɗiyansu na farin uwar miji ke goyawa.
56.
Mazajen jiya don
riƙon amana da nagarta,
Rikazin ƙasa kwag gino
shi bai fara taɓawa.
57.
A yau aljifai
ake ta yanka masalatai,
Cikin
coci a tungune shi bai iya sheƙawa.
58.
Da duk an ka
sake wa yara-yara amanarmu,
Gidaje
da abin hawansu ɗai suka gyarawa.
59.
Ku dubi matasan
da sun ka ja ragama yanzu,
Ido rufe
sata ƙiri-ƙiri ba ɓoyewa.
60.
Su kwaso ƙazanta su kai a
coci, masallatai,
A sa
limamai da malamai muzancewa.
61.
A sa su halin
karnuka da manyan kuraye,
Da su
aka cuta da addu’ar sasantawa.
62.
Mazajen da, ba
a ba su mulki su yi daru,
Su kai
ga iyalai da ‘yan uwa ai ta hayewa.
63.
Kanawa ka faɗin aradu mun ga Alu Babba,
Yana
sarki layya bai da ragon yankawa.
64.
Abu Mai Raɓa na Bello Sakkwato mulkinsa,
Talakkawanai
ka layya bai da na yankawa.
65.
Halan kun manta
da Murtala jiya yar rayu?
Da yan
mutu ƙosai akai gidansu na saidawa.
66.
Gawon ya yi riƙon ƙasa yana yaro
ringis!
Da yai raran dukiya Odiji ya turawa.
67.
A tsarinmu na
yau ina kuɗi za su yi rara?
Da Nazaƙi da Annaboro
su ka fasaltawa.
68.
Tunanin jiya
bai barin na yau kwana sosai,
Jini ka
hawa zullumin abin da ka tasowa.
69.
Idan jiya ta
gyaru, yau tana da abin cewa,
Idan yau
ta barkace na gobe ka kokawa.
70.
Sanin jiya yas
sa na yau ka kuka don gobe,
Hawaye
su ƙwafe ganin ido na ta ragewa.
71.
Matasa in ban
da ku batun cigaba ba shi,
Ku
girmama na gabanku in kuna son morewa.
72.
Rawar kai na
ganin muna da ilmi da takardu,
Mu ce wa
gabacinmu ba sani ba sabawa.
73.
Na baya yana
baya ko kwaranga yat taka,
Mazan
gaba a gigirce sun riga shi ga hangawa.
74.
Idan an ce baba
an gama an kai ƙarshe,
Da an ce
ɗan ɗa uba ake fara kulawa.
75.
Fa tammat Allah
Ka ba mu ladar tsarin ga,
Aliyu
Muhammad na Bunza ne mai ratsarawa.
Aliyu
Muhamamdu Bunza
Sashen
Koyar da Harsuna Nijeriya
Jami’ar
Umaru Musa ‘Yar’aduwa
Katsina.
Lahadi 12/01/2014
Arkilla, Wamakko L.G. Sakkwato
No comments:
Post a Comment