Wannan
waƙar ‘yar ƙwar hudu ce. Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta ashirin da
takwas (28). An kammala ta ranar Jumu’a 28-05-2013 a garin Katsina, Jami’ar
Umaru Musa ‘Yar’aduwa. Kira take ga jama’a da su guji giba da tsegumi da yaɗa ji-ta-ji-ta da hassadar abokan zama. Ta yi wa zunɗe da raɗa da kwarmato da an-yi-an-ce da sa ido zangazanga. Matuƙar aka ba su
tsoro suka guje wa wuraren shawagin ‘yan Adam, za a samu zaman lafiya.
------------------------------
Aliyu Muhammad
Bunza
------------------------------
1.
Gode
Allahu sarki gwanin jinqai,
Wanda yay yo samai yai qassai shi xai,
Kwanaki shidda yak kammale daidai,
Bai nemi ceto da tanyo ga kowa ba.
2.
Qarin
salati ga manzonKa na nay yi,
Wanda ke ida saqon da duk Kay yi,
Shugaban Annabawa da mu bayi,
Duk wanda yab bi ba za shi quna ba.
3.
Kwas
san sahabbanka ya san mazan daga,
Wa mutum nan, su koro a yo tunga,
In sun dakako faxa ba batun raga,
Ba su yarda tsoro ya koro su daga ba.
4.
Mai
batun vata kowa kiro min shi,
Farko faxa mai abin nan da ban haushi,
Turin faxa juddadun babu lallashi,
Kowa ya zaune ka bai sha da daxi ba.
5.
Lafi
tudu ne faxa mai shi sassato,
Sai ka haye naka ka mai da shi loto,
Sannan ka hango na saura da yai reto,
Tamkar halin naka bai zan sananne ba.
6.
Kai
xan rahoto taho nan ka sha hira,
Girmanka duk ya tuxe babu ko saura,
Wai ban da kai kway yi komi akwai gyara,
Aikinka tallan kure ba da gyara ba.
7.
Kawunka
mai kwarmato na ji ya qaura,
Matarsa tsince da fuska kamar kura,
Yawon gidaje da xaki awa vera,
Iya bilkiri varka tusa cikin kwalba.
8.
Kai
mai faxin ka jiya inda wa kaj ji?
Tambo shi bushe ku tonai ya zan qurji,
Yaro da kai ga hava ta yi tamoji,
Don tsegumi ba tunanin kushewa ba.
9.
Wa
da an ka ce naf faxi ka ji ganganci,
Wa da naj jiya naf faxi ka yi saunanci,
Wawa ka yawo da zancen tamusanci,
Kowa garai yaj ji ba a san da kowa ba.
10.
Mai
kakkavin mun jiya kama bakinka,
Kai mai faxar mun gani mun fahince ka,
Wautarka tas sa mutane ka tsoronka,
Bakinka na qaiqayi bai ruwaito ba.
11.
Mai
qyaface ke lavave da hannunshi,
Zunxe da leve ake yi a vultso shi,
Ko gunxe levva da baki a turo shi,
Wai kar ya furta, a ce bai yi daidai ba.
12.
Tsaki
da qyacci abin nan a dube su,
Ni dai sanina takaici ka kawo su,
Shi ne dalilin mutane na tsoronsu,
Mai yin su qarshensa ba zai yi haske ba.
13.
“Sai
mun gani” ka ji mugun hali babba,
‘Yan sa ido kun yi suna wajen zamba,
Bisa qaddara kun ka faxa cikin giba,
Ramenku zurfi garai ba gajere ne ba.
14.
Mai
yin yabo kana qarshe ya yo suka,
In ka yi suka yabo ba shi fis she ka,
Wab ba ka ikon hisabi ga hannunka?
Ka vata aikinka ba ko guda xai ba.
15.
Mai
zaqunon wane nau ne ku shede ni,
Sannan ya kawo bayaninsa mai muni,
Duk tsegumi ne da giba ta zamani,
‘Yan an-yi-an-ce ku gyara a zan duba.
16.
Iya
murmushe buxe fuska a tarbe mu,
Mun ba da bai sai a koma ga gwalonmu,
Kullum a ratse gida don a gaishe mu,
Amma mutuncimu ba a bar shi ko xai ba.
17.
Don
me aboki ka zunxen abokinsa?
Mai hasada xai ka kushe masoyinsa,
Duk mai kalamai na cutar amininsa,
Wa za ya zauna da shi bai wahalsai ba?
18.
Mai
kwarmato ya fi kowa ido buxe,
Qanshin gari masu yawo wuya zauxe,
Don xai a sauraro zance a babbauxe,
Ya game gari take ba ko da shela ba.
19.
Kai
mai faxin ba a yi sai da ni wawa,
Ai ko kana raye ko ka zamo gawa,
Iya yi akai babu kai babu mai tsawa,
Don lokaci bai yi wannan da kowa ba.
20.
Maqetaci
kaico! Bai gane komi ba,
Mugun nuhi ya hana ma zama babba,
Bisa qaddara ga ka kullum cikin giba,
Ka san kushewarka ba za ta haske ba.
21.
Bari
jitta doro da samu kana rowa,
Wai ka ga jallinka ya fara tofowa,
Wannan da yab ba ka shi za ka dubowa,
Bai ce ka canye shi ba ka ‘yamma kowa ba.
22.
Mai
ji da kainai shina ba ni mamaki,
Mai koxa kainai ka wa kansa ga-aiki,
Don me tsakaninku aikinku bai auki?
Gonanku koyaushe ba a qare maimai ba.
23.
Raggo
rashin tavukawa ka cutar ka,
Kullum zugum zaune ka vata qarfinka,
Mata da ‘yan yara sun rena wayonka,
Cewa sukai, “baba bai qulla komai ba.”
24.
Wawa
rashin hankali yaj jivince shi,
Maganar da duk yay yi sai ta burunshe shi,
Maganar mutum kullu yaumin ta qware shi?
Wayonsa guivinsa bai kai ga koko ba.
25.
Raunin
basira ka cutar da xan qauye,
Ga zuciya miqe kullum awa saye,
Muzance kullun da huska kamar maye,
Don xai a ce wane bai xauki wargi ba.
26.
Bari taqama don a ce wane ya waye,
An kwalhe gemu hava ta bi ta kwaye,
Neman a ce ka qware ka zamo gaye,
Tsufa ta riske ka ba ka shirya komi ba.
27.
Duk
wanda yaf faxa tarkon kwaxan mulki,
Son zuciyatai yake maisuwa gunki,
Sai jewaxi ko’ina ce kakai maiki,
Koyaushe kukansa ba a ba shi girma ba.
28.
Tammat
Alu Bunza nan zai taqaitawa,
Ba arashi ne ba kai mai misaltawa,
Halinmu xai ne nike xan kwatantawa,
Yada nag gani ban yi qari ga ko xai ba.
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa
‘Yar’adua, Katsina
Jumu’a, 28/05/2013
No comments:
Post a Comment