Showing posts with label WAƘOƘI. Show all posts
Showing posts with label WAƘOƘI. Show all posts

Monday, October 14, 2019

Gaskiya A Кi Ki, A So Ki

October 14, 2019 0
Gaskiya A Кi Ki, A So Ki
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta wannan waƙa ranar 8 ga watan Ogusta, shekara ta 2019. Tana da adadin baituka arba’in da biyu (42). Ta kasance ‘yar ƙwar huɗ...

Wednesday, January 2, 2019

Mutuwa

January 02, 2019 0
Mutuwa
Roƙo nika yi ga Wahidun mai gyarawa, Sarkin da ya zarce masu ilmi ganewa, Kai kay yi sama’u kay yi ƙassan zaunawa, Kay yo Aljanna kai wuta mai ƙonarwa, Kay yo duniya da rayuwa don zaunawa, Kaƙ ƙaddaro lahira ga ƙarshen komawa, Kowace rai la muhala ƙarshen ta macewa, Tilas in ya mace ƙasa zai komawa, Tsoron mutuwa ga masu rai bai ƙarewa, Domin ba ta kure da ta zaka kamawa, Ɓera bai ce wa mage sannu da hutawa, In sun gamu hanya wa mutum sai...

Ta’aziyyar Mallam Ibrahim Awwal Albaani Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

January 02, 2019 0
Ta’aziyyar Mallam Ibrahim Awwal Albaani Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza
1.       Shukura ga Allah guda masani halin kowa,           Mai ƙaddarowa ta tabbata babu mai tsawa, Ya mai hukuncin da ba makara da gaggawa, Masanin da ilminSa ya wuce hankalin kowa,           Subhaana lil laahi tsarki na ga Rabbani. 2.       Na yo salati ga Manzo shugaban bayi, Ahalinsa dukkan...

Sunday, December 30, 2018

Maƙarƙashiya

December 30, 2018 0
Maƙarƙashiya
Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ya”. Yawan baitocinta hamsin (50). An kammala ta ranar Lahadi 25/05/2014 daga Masar zuwa Katsina, an haɗa ta a Kano, Mumbayya House, BUK, ɗaki na 10. Ga dukkanin alamu kashe-kashe da zubar da jini da ta’addancin da ake son a liƙa wa musulmin Arewacin Nijeriya, maƙarƙashiya ce. Tilas, a sake zama a nazarci matsalolin da idon adalci a ɗebe bambancin addini da aƙida da siyasa da yanki da ɓangaranci. Zancen Boko...

Ganin Ido Nassi Ne Da Babu Ƙila-Wa-Ƙala

December 30, 2018 0
Ganin Ido Nassi Ne Da Babu Ƙila-Wa-Ƙala
Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “wa” yawan baitocinta saba’in da ɗiya (71). An kammala ta ranar Larba 8/01/2014 a kan hanya tsakanin Katsina zuwa Sakkwato. Burinta kakkaɓe ƙura ga ‘yan kurakuran da suka gabata na rikicin ganin watan Ramala na shekarun 2012, 2013 da 2014. A shari’armu, yaƙinin ganin wata ya kore kowane irin tawili. Ana dogara da yaƙinin gani a kawar da maganar kowa, komai nauyinsa a sikelin zamaninsa. Idan ganin ido ƙuru-ƙuru ya...