Gobir
tsohuwar Daula ce da ta shiga gwagwarmaya da daulolin duniyar Sudaniyya. Burin
wannan bincike ƙyallaro
wasu daga cikin dalilan da suka ɗaga
Daular Gobir da Gobirawa sama ga sauran dauloli. An yi garkuwa da fitattun
ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a
wallafa ba tare da taimakon yawon rangadi da tattaunawa da dafa kafaɗar
adabin baka da rubutacce. Binciken ya gano cewa, Daular Gobir cin gashin kanta
take yi kuma Bahaushiyar Daula ce. Bugu da ƙari, ta ƙi ta aminta da tarihihin Bayajidda ya
ratsa Daularta. Dabarun yaƙin
Daular Gobir da siyasar sarautunta sun yi tasiri sosai ga daulolin Sudaniyya.
Babu Daula daga cikin daulolin Sudan…
BA
A WANE BAKIN BANZA
(Gurbin
Daular Gobir Da Gobirwa A Farfajiyar Sudaniyya)
Aliyu
Muhammadu Bunza,
Sashen
Harsuna Da Al’adu,
Tsangayar
Fasaha Da Ilimi,
Jami’ar
Tarayya Gusau,
Jihar
Zamfara.
Muƙalar da aka gabatar a Bukin Buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa
na Farko a kan Daular Gobir, wanda Tsangayar Fasaha Da Nazarin Addinin Musulunci
ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato ta shirya a Babban Ɗakin
Taro na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato, ranar 9 ga watan Yuni, 2018 da ƙarfe 10:00 na safe.
TSAKURE
Gobir
tsohuwar Daula ce da ta shiga gwagwarmaya da daulolin duniyar Sudaniyya. Burin
wannan bincike ƙyallaro
wasu daga cikin dalilan da suka ɗaga
Daular Gobir da Gobirawa sama ga sauran dauloli. An yi garkuwa da fitattun
ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a
wallafa ba tare da taimakon yawon rangadi da tattaunawa da dafa kafaɗar
adabin baka da rubutacce. Binciken ya gano cewa, Daular Gobir cin gashin kanta
take yi kuma Bahaushiyar Daula ce. Bugu da ƙari, ta ƙi ta aminta da tarihihin Bayajidda ya
ratsa Daularta. Dabarun yaƙin
Daular Gobir da siyasar sarautunta sun yi tasiri sosai ga daulolin Sudaniyya.
Babu Daula daga cikin daulolin Sudaniyya da ta yi yaƙe-yaƙen Daular Gobir. Ƙasar Gobir, Gobirawa suka sari
abarsu kuma su suka fara sarauta a ciki duk wani baƙo da ya zo ciki sai dai auratayya
ta narkar da shi ya zama Bagobiri. Binciken ya gano, rushewar Alkalawa bai rusa
masarautun Gobirawa ba da haɗin kansu.
Akwai buƙatar
samun cikakken kundin tarihin Gobirwa da al’adunsu domin a taskace shi a kundin
tarihin duniya. Gobir ta cancanci haka idan aka yi la’akari da tarihinta da ƙarfin ikonta.
Gabatarwa
Fitaccen
mutum, gawurtacce, buwayayye, maɗaukaki,
a ji mutum a ga mutum, a san mutum ya yi mutum, shi ne ‘wane’ a Bahaushen
tunani. Wane wakilin suna ne mai wakiltar wanda ya yi fice, sunansa ya yi
zarra, son kowa ƙin
wanda ya rasa. A tunanin Bahaushe, ruwa ba sa tsami banza, matuƙar an yarda da ‘zomo ba ya kamuwa
daga zaune’, wanda duk aka ga zomo rataye a kafaɗarsa
shi ne ‘wane’. Wannan shi ne hangen Bahaushe na ‘kowa ya ci zomo ya ci gudu’. A
duniyar mutane[1]
da iskoki[2],
ba yadda sunan wani ko wata ko wasu zai yi fice ya mamaye duniyar haƙiƙa da adabi, face yana da wata ɗaukaka
da ya buwaya da ita. Ma’aunin wanna takarda a sikelin ‘ba a wane bakin banza’
shi ne, ƙasar
Gobir da Gobirawa da suka ɗaukaka
sunanta a farfajiyar Sudaniyya. Tunanin wannan bincike shi ne, yaya ƙasar Gobir ta zama wance daga cikin
ƙasashen
Sudaniyya? Me ya sa za a ce wa Bagobiri ‘wane’ daga cikin dangogin zuriyar
al’umma da suka mamaye farfajiyar Sudaniyya?
Dabarun Bincike
Binciken
wannan takarda ba mai faɗi ba ne
domin dalilan da suka sanya ƙasar
Gobir da Gobirawanta suka shahara kawai ya dosa. Abu na farko da na tunkara shi
ne, tattaro adabin bakan Bahaushe domin tattaro gutsattsarin sassan adabin baka
da dama da suka kururuta ƙasar
Gobir da Gobirawanta. Mataki na biyu shi ne rubutaccen adabin da ya hau doron
burin bincikena. Na yi ƙoƙarin tattaunawa da Gobirawa da wasu
daga cikin sarakunansu ko mutanensu da ke kiyaye da tarihin ƙasarsu. Da yake wuƙa ba ta wasa kanta da kanta na ɗan
tunkari abokan zaman Gobirawa da abokan yaƙe-yaƙensu na jahiliyya domin yin tankaɗe
da rairaya. Littattafan magabata masu jihadi irin su Muhammadu Bello da Malam
Abdullahi da Wazirin Sakkwato da Abdulƙadir Almustafa sun ba da haske ga bagiren
da ake nazari. Haka kuma, akwai ayyuka da dama da su Gobirawa suka yi na tarihinsu
sun taimaka sosai. Manyan kundayen bincike na Abdullahi Rafi Augi (1982) da
Garba Nadama (1977) da Bello Alƙali
(1968) da wallafaffun ayyuka na Murray Last (1985) da su aka yi garkuwa. Na
kakkaɓe wundin wannan karatu da
tattaunawa da abokan aikina da suka rubuta ƙudurinsu na gabatar da takardun bincike na
wannan taron. Na fa’idantu sosai da wannan tattaunawar domin ita ta ba ni damar
samar wa bincikena taken da ya dace da tunanina.
Ra’in Bincike
Na
shimfiɗa zuciyar wannan
bincike bisa tunanin al’ada a kan abubuwan da adabi ke jewaɗi
da su game da Daular Gobir da Gobirawa. Tunanin mutanen Sudaniyya kan ƙasar Gobir shi ne, Gobir gidan faɗa
(yaƙi) ce. A
ko’in aka ga Bagobiri an ga wani jarumi, bahago ga abin da bai aminta ba, ɗan
tawaye ga kowane irin iko na kama karya da danniya da wariya. Bisa ga wannan
hasashe na rinjayen mutane (na bayan fage da masana masu bincike) da kuma
abokan gwagwarmayar Gobirawa da ke ganin ba haka abin yake ba. A nawa gani, Bahaushen ra’in da zan ɗora
wannan ɗan bincike shi
ne: ‘Ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba.’ Manufa ita ce, a ba bincike dama ya yanke hukuncin
abubuwan da aka tsinta a bakunan mutane. Da mai ganin ruwa na ƙasa, da mai musanta ba su a ƙasa, duk rijiya ce alƙalinsu.
Tambayoyin Bincike
Ga
alama, Augi (1982) da Nadama (1977) da Alƙali (1968) da Last (1985) da Usman (1974)
ba su rage hakin susa ba ga mai neman tarihin Gobirawa da ƙasarsu. Tattare da haka, wannan
takarda ta hango wani ɗan giɓin
da ya kyautu a ce an cike. Zance na farko shi ne, ina ne tushen kalmar ‘Gobir’?
Wane ne Bagobiri idan aka bi taliyon kalmar? Me ya kawo wa Gobirawa fice da ɗaukakar
ƙasarsu
tun gabanin bayyanar Turawa da guguwar jihadin ƙarni na sha tara (ƙn. 19)? Me ya sa har wannan ƙarni na ashirin da ɗaya
(ƙn. 21)
kamar Jangwarzo ke karagar mulki? Me ya sa Daular Gobir ta fi kowace daula
tasiri ga daulolin ƙasar
Sudaniyya? Idan bincikena ya ci nasarar yi wa waɗannan
tambayoyi shan ruwan tsuntsaye, aka fahinci saƙon, to ta tabbata: ‘Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba.’
Warware Ƙunshin Matashiya
Manufar
ba a wane bakin banza shi ne na duk wanda ya shahara akwai abin da ya taka ya
yi wa tsara fintinkau. Me ya sa Bahaushe ya ce, ‘Wane mutum in ji mutuwa!’ Bai
ce, ‘Wane mutuwa inji mutum’ ba. Domin ya san ko ba a gwada ba linzami ya fi
bakin kaza. Na yi amfani da kalmar ‘gurbi’ domin fito da matsayin Gobir da
Gobirawa a gurabun daulolin Sudaniyya. Farfajiyar Sudaniyya ita ce (Western Sudan)
a da, wadda a yau West
Africa/ sub-Saharan
Africa
za ta wakilta. Gabanin bayyanar ikon Turawa a ƙasar Hausa da ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita duk a rubuce-rubucen
Larabci da adabin baka Sudan
ko Sudaniyya
ake kiransu. A rubuce-rubucen masu jihadin ƙarni na goma sha tara (ƙn. 19) ana cewa ƙasar Biladil Suudan wanda Turawa ke
kira Western Sudan
ko Sudanic Africa.
Marigayi Makaɗa Aliyu Ɗandawo ya tabbatar da wannan kalmar
ta Sudaniyya a waƙarsa
ta Sarkin Kabin Argungu Sama’ila ɗan
Yakubu da yake cewa:
Gindi: Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
:Ila
marin rugga ɗan Yakubu sa
gurhwani.
Ƙarni tabbacin wannan akwai sarautar
Sarkin Sudan a Sakkwato (wadda ke Wurno) akwai a Kabi a Daular Kabi (wadda ke
Lailaba). A Kwantagora sarauta ce. A Yawuri an yi ta amma Kwantagora aka tura
shi. A Katsina akwai Sarkin Sudan.
Daular Gobir A Zamunan Daulolin
Sudaniyya
Daular
Gobir ba mutun tsugune ba ce a cikin daulolin Sudaniyya a tarihance da sarauce
da al’adance. Ficen ta cikin daulolin zamunanta abin kulawa ne a wannan ɗan
bincike. Tarihin Daular Gobir yana da alaƙa da rukunin daulolin da na kasa zuwa
kashi biyu: Na farko su ne daulolin Sudaniyya wajen ƙasar Hausa irin su ɗaular
Nupe (ta Nufawa) da Oyo (ta Yarbawa) da Azbin (ta Azbinawa) da Borgu (ta
Bargawa) da Borno (ta Kanuri) da Songhai (Shangawa da Dandawa da Kyangawa) da
Mali (ta Wangarawa) da Ghana (ta Asante) da Illo (ta Dandawa) da Fadan Gurma
(ta Gurmawa a Borkina Fasso). Daular Gobir ta yi zamunna ta waɗannan
daulolin kuma akwai zumuntan tarihi da al’adu da siyasar sarauta da za a samu
wuraren da suka haɗu da Gobir
jefi-jefi.
Ɓangaren daulolin Sudaniyya na biyu
su ne daulolin da farfajiyar ƙasa
ɗaya mai harshe da al’adu da siyasar
sarauta da ta zamantakewa iri ɗaya.
Daulolin da ke da wannan sun haɗa da:
Daular Kano da Daular Zamfara da Daular Kabi da Daular Katsina da Daular Zazzau
da Daular Yawuri. A talitalin tarihin daulolin ƙasar Hausa, babu labarin wani abu
‘Sokoto/Sakkwato’ sai dai Gobir. Bayan bayyanar Sakkwato a matsayin cibiyar
tsare-tsaren jihadi da ilmantarwa, aka samu Daula biyu: Daular Sakkwato da Daular
Gobir. Duk da haka, idan ana zancen harshe, da an ce Sakkwatanci, ‘Gobirci’ ake
nufi, domin cikin ƙasarsu
Sakkwato ta tsira. A tarihance da al’adance, idan ana zancen ƙasar Hausa, Gobir ce ake bayani domin
gabacinta a tarihance. Basakkwace na nufin Bagobiri domin sai an yi shuka ake
zancen tumu. Daulolin da muka ambata na farko da ba cikin farfajiyar ƙasar Hausa ba, duk abin da ya shafi
ƙasar
Hausa da Hausawa a wajensu ƙasar
Gobir da Gobirawa ake zance domin gabaci a tarihi da al’adu[3].
Tushen Kalmar Gobir
Binciken
wannan takarda da barhon al’ada ake feɗe
shi. Duk da haka, masu Tarihi da Imin Harshe da Walwala (Sociology) da
Mutuntakar ɗan Adam
(Folklore) da Kimiyyar Al’ada (Anthropology) da Kimiyyar Siyasa (Political
Science) duk a kogi ɗaya suke
su. Makaman kamun kifinsu da dabarun kamun kifinsu kawai zai sha bamban, amma
kifi iri ɗaya suke kamowa.
Wanda duk aka fi ƙwazon
keta gurbi da kurmundi dole a fi shi kamo manyan kifi ƙwangaggi. A bitar ayyukan magabata
masana Gobir da mutanenta babu silalen batu da ba su bi ba domin tantance
kalmar ‘Gobir’. Daga cikin abubuwan da suka shahara akwai:
1.
Asalin kalmar ‘Gubur’[4]
wani gari ne tsakanin Makka da Madina da suka yo hijira sunan garinsu ya bi su
daga ‘Gubur’ zuwa ‘Gobir’ wasula kawai suka sassaɓa
baƙaƙe na nan tangam! A nahawun Larabci,
harafin ‘wau’ (ﻭ)
yana kusa da wasalin rufu’a (ﻭ
) don haka ‘Gu’ a Larabci na komawa ‘Go’ a Bahaushen
lafazi domin a ajami ma ana rubuta ta (ﻏﻮﺑﺮ). Sai dai wasalin rufu’a na gaba ga
harafin ‘b’ da ya ba da ‘bur’ ya koma ‘bir’ a Hausa, nan barafasa take. Da yake
wannan Balaraben ra’ayi ne, za mu ce ƙila ana nashe wasulan kalmar ta koma ‘Gbr’
kamar yadda Masar/Misira ƙwararru
ke furta ta da rubuta ta ‘Msr’. Duk da haka, a cikin tarihi da tarihihin ƙasar Makka da Madina ina aka samu ɗuriyar
‘Gubur’? akwai kufan bayanin wannan garin a Saudiyya ta yanzu? A ina suka samu
labarin farfajiyar Ƙasar
Gobir?
2.
Ra’ayi na biyu na cewa: Kalmar
Gobir ko Gubur daga harshen Ƙibɗanci
yake. Ƙibɗawan
Masar an ce, wai, su suka haɓaka ƙasar Gobir. An ce, ‘yan kasuwa ne
da manoma suka tarar da ƙasar
cike da ma’adanin tagulla (Copper) a harshensu ‘Gubur’ ko ‘Gobir’ na nufin
‘tagulla’[5].
Ana ciro tagullar wajajen Agadez/Takedda a yi fataucinta zuwa Zaghai da Katsina
ta hannun Wangarawa. Wannan tunanin ya manta da cewa, Ƙibɗawa
yawo suka zo kuma sun tarar da wasu mutane a wurin da suka zo. Su mutanen me
suke kiran kansu? Su ke hulɗa da
tagulla ko Ƙibɗawa
da Azbinawa da Wangarawa? Me suke cewa ‘tagulla’ da harshensu? Tsakanin baƙo da ɗan
gari, wa ya cancanci a karɓi sunan
gari bakinsa? Wannan tunanin ya rage wa Gobirawa tsawo. A gafarce ni, ban yarda
da shi ba.
3.
Ra’ayi na uku na cewa: Ƙibɗawan
Masar suka sama wa babban birnin Gobir suna wato Birnin Lalle domin a harshensu
Lalle (Lenna) shi ne ‘Gobir’ a Hausa Lalle.[6]
Idan haka ne kuwa, an taras da Gobirawa da sunansu da sunan ƙasarsu, domin da ciyayi/ciyawar
lalle aka taras da su, ba zuwa aka yi da it aba. In ‘Gobir’ na nufin lalle, me
ya sa ba a ce birnin Gobir ba ake ce Birnin Lalle? Ko da Ƙibɗawan
suka zo da lalle, wa suka taras a wurin? Wannan ra’ayi na jin kunyar ɗaliban
ilimi ainun. Lallai dai abin ƙawar
duniya ne, Gobir da abinta aka gane ta. Wannan ra’ayi ya ƙarantar da Gobir.
4.
Ra’ayi na huɗu
na cewa: Shahararren masani tarihi kuma ɗan
yawon buɗe ido (ko leƙen asiri) mai suna Ibn Batuta a
tsakiyar ƙarni
na goma sha huɗu (ƙn, 14) da ya ratso ƙasar Azbin ya ce, ya tarar da wata ƙasa wai ita ‘Kubar’[7].
Wannan hasashen ya nuna Azbin daban Gobir daban, kuma sun yi zamuna ɗaya.
Wa ya rigayi wani? Bayanin bai kakkaɓe
ƙurar ba.
Kalmar ‘Kubar’ matuƙar
haka ya rubuta ta to, ta saɓa wa
‘Goboru’ da ‘Gubur’ ko kusa ba ta yi kusa da ‘Lalle’ ba. Ga wa ya ji wannan
kalmar ta ‘Kubur’ ga Azbinawa (domin ƙasar Azbin ya ratso, bai ce ya ratso ƙasar Gobir ba)? Rashin samun haƙiƙanin ina ya karɓo
kalmar ya sa ba za a shiga ɗaki da
maganar ba. Idan za a yi adalci, za a ce Ibn Batuta baƙon Gobirawa ne, domin ko da iska ya
zo ya tarar da Kaba na rawa.
Tankaɗe Da Rairayar Kalmar Gobir
A tunanin al’ada,
mai ɗaki shi ya san wurin
da ɗakinsa ke tarara.
Masana adabi suka ƙara da cewa, ko mai baibaya ya san wurin da ya taushe
matararar ruwa. Daga cikin abubuwan da ya kyautu a tsettsefe a riwayoyin kalmar
‘Gobir’ su ne:
1.
Akwai
batun cewa Larabcin daga ‘Gubur’ yake sunan wani gari tsakanin Makka da Madina.
Wannan tunain na da ƙanshin addini da jawo ɗaukakar Larabawa a idon Musulmin
Afirka. Da yawan al’ummomin Afirka suna laɓewa gare shi domin samun karɓuwa da fice. Gobir
ba ta buƙatar wannan, don babu daular da ta yi mata mulkin mallaka
kuma da addini aka tarar da ita.
2.
Ra’ayin
cewa daga harshen Ƙibɗawa ne na kalmar tagulla da lalle ya kasa fito da
harshen asali na waɗanda ake kira
Gobirawa. Ya manta da ɗan Adam ba ya
walwala ba da harshe ba, kuma masu tunani sun ce an tarar da wasu a ƙasar. Dole a zargi
ƙabilanci
da wariyar fata a cikin ra’ayin.
3.
Idan muka nazarci kalmomin duka: ‘Gubur’
da ‘Gobir’ da ‘Kubar’ duk gaɓoɓi biyu-biyu gare su. Tushen kalmomin kuwa daga ‘Gub’
da ‘Gob’ da ‘Kub’ ne, a ginin kalmomin Hausa sun hau tsarin cikakkiyar gaɓa mai ‘baƙi da wasali da baƙi’ (BWB). Masu
riwayar ba su ko ambaci Hausa daga tushen sunan ba. Bugu da ƙari, a tsarin gaɓoɓin kalmomin Hausa,
dukkan kalmomin da rufaffiyar gaɓa suke a ƙarshe, ‘bur’ da
‘bir’ da ‘bar’. Idan za mu ɗora wannan hasashe kan tasarifin kalmomin Hausa na
saka kalmar ‘ba’ a farkon sunan ƙabila da ‘wa’ a ƙarshen sunan, za
mu samu:
Gubur Bagubur - Bagobiri
Bagubura - Bagobira
Guburrawa - Gobirawa
Gobir Bagobir(i) - Bagobiri
Bagobir(a) - Bagobira
Gobir(awa) - Gobirawa
Kubar Bakubar - Bagobiri
Bakubar - Bagobira
Kubar - Gobirawa
Wataƙila ra’ayin
‘Gobir’ ya fi hawa mizanin Bahaushen ma’auni na lafazin kalmomin. A nawa
tunani, irin ɗaukakar da Gobir
ta yi ba daga waje sunanta ya fito ba, daga cikinsu ne suka ƙago abin su da aka
ga sun yi fice, kowa ya tofa albarkacin bakinsa.
Sake Duban Kalmar Gobir A Farfajiyar Al’ada
Masu ruwaito
asalin Gobir da Gobirawa sun baro wani ɗan giɓi na ‘harshe’. Zancen Larabawan Makka da
Madina da Ƙibɗawan Misira da Larabawan Yemen da Turkawan Daular
Ottoman ya kasa samun tasiri ga harshen Gobirawa na tun fil azal. Har yanzu ba
mu ji ɗuriyar waɗannan harsuna ba
ko a cikin tsohuwar Hausar ƙasar Gobir da wasu daga cikin
karuruwan harshenta. Ba Azbinawa ba ne, duk da zamantakewar su da al’adunsu d
harsunansu daban. Don wani abu baƙo kawai da muka
samu daga cikin fadar masarautar Gobir a bukukuwansu na salla, daga cikin masu
barka da salla za a fara gabatar da masu yi wa sarakunan Gobir kirari ɗaya bayan ɗaya daga sarki na
farko har ya zuwa mai ci. Bayan sun gama, sai wasu mutane biyu su zo, su yi
magana da baƙon harshe, ɗaya na fassara da Hausa. Wannan salon suna
kiransa Warkarci[8]. Gabatar da masu
yi wa sarakunan Gobir take da Hausa shi ne hujjar cewa, harshen Daular Gobir da
mutanenta Hausa ce. Samun wani/wasu baƙin harsuna a
Daular Gobir ba abin mamaki ba ne idan aka lura da daɗewarta da ƙarfinta da faɗinta da al’ummomin
da ke maƙwabtaka da ita da masu ziyararta da waɗanda ta ci da yaƙoƙinta. In dai Warkaru ba harshen Azbin ba ne da aka ce can
Daular Gobir ta fara zama, to ina zaton surkullen zantawa da iskoki ne na
sirrin ƙasa a siyasance.
A tsarin al’adar
garuruwan ƙasar Hausa, sunayensu ba su rasa alaƙa da mutanensu ko
yanayin ƙasar ko garin ko albarkatun ƙasar ko tsirrai ko
itace ko ma’adanan da ake samu ko gulabe da tsaunuka da dabbobi da ƙwari da ke wurin.
Mu tsura wa ƙasar Gobir ido sosai mu dubi waɗannan misalai:
1.
Sabon
Birni: Ya nuna an baro
tsohon birni
2.
Birnin
Lalle: Birni ne da ke da
ciyawar lalle
3.
Unguwar
Lalle: Unguwa ce da aka samo
sunan daga lalle
4.
Kalgo: Daga tsiron Kalgo
5.
Kwaren
Gamba: Saboda hakin Gamba
Aiki na kan masana
da manazarta da mu ɗalibai mu sake
nazarin mazaunin Gobirawa na farko domin mu nazarci yanayin wurin. Haka kuma,
mu ɗan yi yunƙurin gano su
Gobirawan farko da aka tarar yaya suke kiran kansu? Ko da ma sunanta ‘Goobir’
masu sauraron suna da ba ‘yan asali ba ke furta ta daban-daban? Anya ba wajen
rubuta ta ne ake samun matsala ba daga ajamin sunan ko rubutun Turawan farko?
Me zai hana mu sake bitar waɗannan ‘yan hasashe-hasashe mu ga ko akwai abin cewa:
1.
Gobarau: Masallacin
Gobarau na Katsina ficen da ya yi duniyar tarihin Sudaniyya kuma da wannan suna
‘Gobarau’. Daɗewar Musulunci a
Daular Gobir da shiga da ficen baƙi cikinta abin
duba ne. Wannan na buƙatar a dubi tarihin Gobarau da kafuwar Daular Gobir. A
sake duba wasalin /u/ da harafin /w/ ‘yan tagwaye ne, daga nannage n /u/ aka
samu /w/, don haka Turawa ke ce da harafin ‘double
u’
wai ‘u’ gida biyu. Ke nan da ‘raw’ da ‘rau’ Hasan da Husaini ne. Gobirawa –
Gobarau – Gobarawa.
2.
Goriba/Goruba: Farfajiyar Azbin
da Kabi da Katsina da Gobir marayar icen ‘Goriba’ ce. Yanayin ƙasar na yi wa icen
daidai. Idan da tabbacin itacen Goruba bargaja a wuraren zamansu na farko ƙila a ce daga
‘Goriba’ a sami ‘Goribu’ – Goribau – Goribawa – Gobirawa.
3.
Gobara: A mahangar
al’ada, mutum/wani abu na tashi da sunan asali a tsakiyar rayuwa a ƙaga masa wani suna
ga abin da aka shaida gare shi. A al’adance, rinjayar da wuta za ta yi wa
mahashinta sai ya nemo agaji a taimake shi a kashe ta, shi ake ce wa ‘gobara’.
Wutar gobara wani yaƙi ne da gudan gari dole ya tashi-tsaye. Ga al’ada,
idan Ƙudahi ko Jan-Kiyashi ko Sunge ko Cinnaka suka yi
tururuwa da yawa suka fito rami, akan ce sun yi ‘gobara’. Bagobiri ga yaƙi, ‘gobara’ ne,
duk ƙasar da suka kai wa hari sai mazajenta sun nemi agajin
dugadugansu. Idan aka kai musu hari, ƙwai da ƙwarƙwatansu ke fitowa,
a mutum har liman.
Ƙoƙarin laƙa wa Gobir sunan
da ba na harshen kakanninta ba rage mata lamba ne, a sake lale. Anya! Ƙoƙarce-ƙoƙarcen danganta
asalin Gobirawa da wasu baƙin ƙabilu irin su Ƙibɗawa da Turkawa da
Fir’auna babu hasada a ciki? Kada a manta yaƙi kashi biyu yake,
yaƙin
takobi da na alƙalami.
Daular Gobir da Gobirawa a Farfajiyar Daulolin
Sudaniyya
Daular Gobir a fuskokin daulolin
Sudaniyya kamar madubi take kuma ita ce daular da ta samu suna ɗaya gawurtacce da
duniyar Sudaniyya ta yi canjaras a kansa. Ga ɗan misali da za mu ga irin nauyin
Gobir cikin adabinmu:
1. Kano: Jalla
babbar Hausa, gari ba Kano ba dajin Allah, ko
Kano ba gari ba
dajin Allah. Duk da wannan kirari na yawan ƙasarta, Ɗantanoma mawaƙin Sarkin Kabi
Sama ya ce:
Jagora: An ce ba a wa Kano takakaka
:Sama ya tattake ta
:Don mun zo Kano da
dambun masu
:Ba mu samo gaba
ba.
2. Katsina: Bukkar
kara
3. Kabi/Argungu: Birnin kara da gambun ƙarfe
Na
Kanta ba ku da raggo
4. Sakkwato: Birnin Shehu, ta Bello mai da ƙasari zuma
5. Yawuri: In
ka san Yawuri ka san geshe?
6. Zamfara: Zurfin ciki / Gusau ta Sambo Dandin
Hausa
7. Zazzau:
A taƙaitace, a tsarin
kowace daula, kowace ƙasa akwai take da kirari. A can da, da kiɗa da rawa ake yin
taken da arashi da kirari ana yi wa abokan hamayya habaici. Da aka ci gaba ne
aka bai wa sojoji da ‘yan sanda busa bigala da atisayen
barazanan tuna baya. Wanda duk kakanninsa ba su kare ɗiyaucinsu ba, ba
ya da wani taken da zai gaya wa duniyar zamaninsa. Daular Gobir a nan ta ci
zarar sauran dauloli takarorinta. Da an ambaci Gobir da yaƙi za a yi mata
kirari
·
Gobir
ta Bawa gidan faɗa.
·
Gobir
ta Bawa kowa Sarki.
An ce, rawar
atisayen dakaru Gobir a fagen daga shi ne[9]:
:Ƙashin gwuiwan kura
:Ba lasan karnai ba
:A ba manya fili
:Ba don Allah na ba
:Ina mutuwa tayyi! Ina mutuwa
tayyi!
:Ta sheƙo ga ‘ya’ya
(tsoho)
Zaruntakar Gobirawa ta yi kusa da ta
Larabawa in ba ta yi daidai ba. An ce, Khalid bn Walid in sun je fagen jihadi
sukan gaya wa abokan karawa cewa: “Ga waɗanda ke buƙatar
mutuwa fiye da yadda suke son rayuwarku”.[10]
Tirƙashi,
maganin maƙi gudu ban kashi!
Mazakutar Gobirawa a kowane fagen nuna
bajinta suka shiga sai sun yi fice kuma da jarumtaka ake rarrabe Bagobirin asali
da Bagobirin rantsuwa. Dubi yadda makaɗa Ɗan’anace ke wasa wani
Bagobiri a fagen dambe:
Jagora: Yaƙi sabon Bagobiri
:Mai kayan faɗa
:In nig ga mutum da jan ido
:Tsoro nai nikai
Makaɗa Narambaɗa Tubali, makaɗin Daular Sakkwato
da ya yi wa Sarkin Gobir Salihu waƙa ga gindin da ya ɗora ta a kai:
Gindi: Ya buwai maza Salihu
:Ko yanzu a bar wargi
:Ba su ima Ɗan’inna
:Halin Ummaru na yay yi
Jagora: Kai a Ummaru yau
Yara: Kai a ɗan Adata Jangwarzo
Jagora: Batun da kas sani na
:Shi na za ni tusa ma
:Da gabas da yamma
Yara: Shawai bai zan done ga kowa ba
Jagora: Nan ƙasag ga kog gwada
wargi
Yara: Ummaru ya bi sai
Abin mamaki, hatta a fagen siyasar
zamani za a yabi Bagobiri sai an tuzgo da famar yaƙi da suka gada
daga kakanni. Sani Aliyu Ɗandawo da ya yi wa Gwamna Attahiru Bafarawa waƙa ga gindin da ya ɗora ta:
Jagora: Dogo bari in ma kiɗin nan na yaƙi
:Attahiru ya yi kokuwa ya yi
kaye.
Wani makaɗin fadar Sabon
Birni ya fito da ficen Gobirawa cikin waƙarsa kamar haka:
Jagora: Gobirawa kun sha kunun baƙar zuciya
Yara: Nan gidan duniya babu in da ba a san
ku ba.
A masarautar
Gobir, da duk wurin da Bagobiri yake a duniya, yana bugun gaba da Sarki Malam
Bawa wanda aka fi sani da Jangwarzo. Daga cikin malaman zamaninsa wani malami
ya rubuta waƙar yabon Bawa Jangwarzo (1790) yana cewa:
Ba da razana kigon tama
Ɗan Alasan mai
tambari
Ba da razana ƙyauren gari
Bawa kai na Magajin Gari
……………………………
Ba batun yaƙi munka zo ba
Gaisuwar mutuwa munka zo
Da batun yaƙi munka zo
Wurno ba ta yini ko ta kwan
Shiki da dole tawayen gari
Ƙanƙanan kajinmu na
Wa ɗan Gudale wa ɗan Tubali
Manya-manyan kajinka na
Kar ka tam musu sai ran buki
Wannan waƙar rubutacciya ce
bisa ga tsarin gwauruwar waƙa (‘yar ƙwar ɗaya) kuma
kwamacala ba da tsayayyen amsa amo ba. Duk yabon da aka yi wa Sarki Malam Bawa
Jangwarzo kan yaƙi ne da fama.
Kar Ta San Kar
A da, gabanin bayyanar hasken
saukakkin addinai, ƙarfin kowace daula ya danganta ga irin ƙarfin sojanta da
tanadinta na tsaro. Gobir da Gobirawa sun yi sunan yaƙi ainun, sai dai
abin kula shi ne, mayaƙi ba dole kowane karo shi ke yin nasara ba. Yadda
Hausawa ke cewa, ‘Ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare’, ba a san
gwarzo ga yaƙi ba sai an ci shi ya mayar da fansa ko ya ci nasara
ko ya sake faɗuwa. Ga al’adar
Gobirawa, cin su da yaƙi ba abin bugun gaba ba ne, domin su da yaƙi tobasai ne ƙuƙe-na-ƙuƙe sai abokin yaƙi ya gaji ya mayar
da yaƙin wasa.[11]
Daular Gobir ta kara da Katsina ta ci an
ci ta. Ta kara da Kano da Zazzau da Zamfarawa ta ci an ci ta. Ta shigo Borno da
Rano da Haɗijiya yaƙin zube ba ni ƙwarya. Ita da
Daular Sakkwato takobi bai taɓa kwana kube ba. Ta yi arangama da Azbinawa har suka
sauya mazauninsu suka dawo wurin da suke yanzu. Da Adar da Zabarma ba ta bari
suka huta ba sai da ta ɓatar musu da
lisafi. Gobir ta taya Daular Nupe ta ci zarra. Ta darzaza Oyo dole Yarbawa suka
zaɓi tobasantaka.
Tattare da tsananin tsaron Bargawa, Gobir ba ta bar su ba sai da aka ƙwama ta girgiza
su. Daular Songhai ta Askiya sun kauru da juna, Fulanin da ke Fadan Gurma
(Gurmawa) sai da Gobir ta firgita su. Daular Mali ta Wangarawa, Gobir na da
tarihin yaƙi da su na bisa kan mai uwa da wabi. Babu wata daula
daga cikin daulolin Sudaniyya da ba ta san da Gobir da Gobirawa ba a fagen
luguden takubba da ruwan masu ba. Waɗannan yaƙe-yaƙe da babu wata
daula daga cikin daulolin Sudaniyya da ta yi kama da irinsu. Kuma ta tsayu da ƙafafunta, su suka
bai wa Gobir da Gobirawa fitaccen suna da babu mai irinsa.[12]
Fice da dabarun yaƙin Gobir ya sa
suka dinga sassauya cibiyoyin daular mulkinsu. Daga cikin cibiyoyin da aka yi akwai,
Birnin Lalle da Tsibiri da Sabon Birni da Alkalawa da Birnin Magale da wani
gari kusa da Gidan Rumji na cikin Jamhuriyyar Nijar, an ce kangonsa na nan.[13]
Wannan dawara da kai da kawo ya ba Gobirawa damar barbazuwa cikin duniyar
Sudaniyya, har ya kasance babu wata daula daga cikin daulolin Sudaniyya da babu
Bagobiri a ciki. Abin ban sha’awa, ba a san su ‘yan gudun hijira ba, sai dai a
ce, ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, duk cikin shirin yaƙi ne. A cikin
kowace daula Gobirawa suka shiga baƙunci an san kar ta
san kar.
Hasken Gobir Da Gobirawa A Masarautun Ƙasar
Hausa
Bayan da yaƙe-yaƙen jihadi suka
lafa, Bature ya yi ɗan zamaninsa ya
wuce. Ƙasa ta koma hannun masu abu, kowa ya koma ƙasa da aiki ƙoƙarin gina abin da
aka rusa da farfaɗo da abubuwan da
suka salwanta. Kowace daula masarautunta suka himmatu da abin da suka himmatu a
kansa. Tasirin yaƙe-yaƙen da Gobirawa suka yi, da dabarun
tsaronsu da tattalin arziki da siyasar mulki ta ci gaba da naso manyan daulolin
ƙasar
Hausa. Bazuwar Gobirawa da kafuwar garuruwansu da tsabbacewarsu nesa ga waɗanda ba su yarda
da su ba ya haifar da wani sabon salon a tsarin sarautun daulolinmu.[14]
Rushewar Alkalawa da gugwar jihadi da
ta raba masarautar Gobir kashi biyu Sarkin Gobir na Sabon Birni (da ya miƙa wuya) da Sarkin
Gobir na Tsibiri (da ya zaɓi ‘yanci).[15]
Garuruwan Gobirawa, mutanensu suna nan tangam kamar komai bai faru ba. Don
haka, dole aka bar su da sunansu da sarautunsu. Dubi waɗannan sarautun don
tabbatarwa:
i.
Sarkin
Gobir Na Isa
ii.
Sarkin
Gobir Na Gwadabawa
iii.
Sarkin
Gobir Na Goronyo
iv.
Sarkin
Gobir Na Kalgo (Ƙasar Gwandu)
v.
Sarkin
Gobir Na Bunguɗu
vi.
Sarkin
Gobir Na Lailaba (Ƙasar Kabi)
vii.
Sarkin
Gobir Na Kwantagora
viii.
Sarkin
Gobir Na Yawuri (a Kwantagora)
Waɗannan sarautu ba ƙanana ba ne a ƙasashen da suke.
Abin ban sha’awa duk wani ɗan sarautar Sakkwato da Kabi da Gwandu zai so a ba shi
sarautar Sarkin Gobir domin wani matakin ci gaba a tsarin masarautunsu.[16]
Abin nufi a nan shi ne:
i.
Mai
sarautar sarkin Gobir Na Isa, sarautar Sarkin Musulmi yake jira.[17]
ii.
Mai
sarautar Sarkin Gobir Na Gwadabawa, sarautar Sarkin Musulmi yake jira. Sarakuna
biyu da suka fito daga can suka yi sarautar Sarkin Musulmi.[18]
iii.
Mai
sarautar Sarkin Gobir Na Kalgo, shi ake ba Sarkin Gwandu in ta faɗi. Mafi yawan
sarakunan Gwandu sai da suka yi Sarkin Gobir Na Kalgo.[19]
iv.
Sarakunan
Kabi uku suka yi sarautar Sarkin Gobir Na Lailaba kuma duk sun yi Sarkin Kabin
Argungu.[20]
Gobir Fitilar Addinan Farfajiyar Sudaniyya
Tsayin dakan da Gobir ta yi na ƙin miƙa wuya ga mulkin
gadon-na-gajeka da sunan addini ya sa wasu na bayan fage ke yi mata kallon
Maguzanci.[21]
Ko shakka babu, Gobir ta yi fice a kan addinan gargajiya na bori da camfi da
‘yan tsafe-tsafen kare kai da kaya.[22]
Mantuwar da ake yi ita ce, waɗannan abubuwa sun wanzu tun gabanin saukakkin addinai
a Sudaniyya. Babu al’ummar da ba Bamuguza ba gabanin saukakkin addinai. Don
haka, kowace al’umma da irin nata bori da tsafe-tsafe.[23]
Gobir ta shahara a nan, domin ga al’ada komai Gobirawa suka tunkara gadan-gadan
suke ba su san ido ga kifi ido ga bado ba. Hidimar Iskoki na bori daga Masar da
Morocco da Tunis da Alges da Libya suka kwararo Gobir ba Gobir ta ƙago su ba.[24]
Kasancewar Daular Gobir daɗaɗɗiya ta yi fice da zarra cikin sha’anin bori a
Sudaniyya.[25]
Saukakkin addinai na Nasara da na
Musulunci a Gobir suka fara yada zango. Gabanin jihadi babu daular da ta fi
Daular Gobir malamai a farfajiyar Sudaniyya. Masu jihadi manya daga cikinsu
suna da malamai Gobirawa kuma wasunsu ƙasar Gobir suka yi
karatu.[26]
Mujaddadi ya tabbar da akwai malamai masanan gaske Ƙasar Gobir kuma
Gobirawa. An ce, Mujaddadi na matashi ya je fadar Gobir ya yi wa malamansu
nasiha, suka yi masa tambaya ɗaya, suka ba shi shekara ɗaya, ya je ya yi
karatu ya gano bayaninta, ya dawo ya faɗa.[27]
Ya yawace ƙasa gaba ɗaya ya rasa bayani. Yadda al’amarin yake
shi ne, akwai wani bawan Allah mata-maza a Birnin Alkalawa san da yake mace
sunansa Sahura, lokacin da yake
namji sunansa Ummaru, ya rasu a mulkin
Sarkin Gobir Babaji. Ga tambayar da malaman Gobirawa suka yi masa:
Da yana mace Sahura ya yi aure ya haifi ‘ya’ya biyu, aka gane
mata-maza ne aka sake shi. Ya je ya yi shigan maza Ummaru ya auri mata suka
haifi ‘ya’ya uku. Aka gane shi, aka sake shi. Ya je ya yi mafarkin maniyinsa ya
ɗiga a farjinsa ya
haifi ɗa ɗaya. Sai ɗiyansa su shida
suka taru/rayu. Ya rasu ya bar dukiya mai yawa, yaya za a raba musu gado?
Abin ban sha’awa, Sarkin Gobir Babari
ya tura masana daga Alkalawa zuwa Tunis da Tarabulus da Misra domin tuntuɓa.[28]
Wa zai musanta kasancewar masu wannan tambayar fitattun masana na ƙin ƙarawa? Me ya sa
suka yi tambaya ga fannin gado? Ashe tuni Gobirawa ke da hulɗa da duniyar ilmin
Musulunci tun ba a taɓa mafalkin jihadi ƙasar Hausa ba. Danƙari! Lallai Gobir
mai hannu duka dama ce. Duk wani mai ƙoƙarin kushe Daular
Gobir ko Gobirawa ta fuskar addini bai san ‘Ba a
wane bakin banza ba’. Gaya masa ya sa
himma, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. A iya sanin Gobirawa
Daularsu ta Musulunci ce, kuma Musulmi ne Sarkinsu gaba da baya, kurakurai kuwa
ba hujja ce ta kore addini ga wanda ya miƙa wuya ba.[29]
Da Mujaddadi ya dawo ya ba su gari kan tambayar da suka yi masa, suka yi masa
fashin baƙinta dalla-dalla.[30] A
tuna ba tambayar ƙure ba ce, ba ta raini ba, domin abin ya wakana a haƙiƙa ba ƙire ba ne.[31]
Sakamakon Bincike
Idan Bahaushe ya ce, ‘Ba a wane bakin banza’, a bi shi a
hankali a ga wane ne wanen da yake zance a kai? Da duk suna ya yi fice, akwai
wata ɗaukaka tare da
shi. Gobirawa sun samu ɗaukaka mai yawa a
farfajiyar Sudaniyya; an yi zamanin da ba wasu sai su, kuma ba sa magana a kaɗa kai. Jihadin ƙarni na goma sha
tara ya tarwatsa babbar cibiyarsu Alkalawa. Mulkin Turawan Ingila ya zo ya sake
girgiza su. Duk wannan bai goge sunan Gobir ba, bai rage wa Gobirawa tsawo ba
saboda irin salon zamantakewarsu na a share jini a koma wasa. Ga ɗan hasashen da
wannan takarda ta leƙo:
1.
Babu
daular da ta yi faɗi da yawa da ƙasaita a daulolin
Sudaniyya irin Daular Gobir.
2.
Gobirawa
tantagaryar Hausawa ne duk wani yunƙuri na samo musu
suna a wajen daularsu, a bi shi a hankali ba a rasa bi-ta-da-ƙulli a ciki.
3.
Ci
gaban dukkanin ƙasar Sudaniyya Gobir ne tushensa ta fuskar siyasa da
tsaro da addini da wayewa domin ita ta fara yi wa baƙin Sudaniyya
masauki. Sarrafa bindiga da murƙushe juyin mulki da tsaro, gare su
aka koya.[32]
4.
Gobir
na buƙatar sabon bincike don a inganta tarihinta, a daidaita
shi ya shiga cikin sahun fitattun daulolin duiya da ake darussansu a tarihin
duniya. Wannan na buƙatar gidauniya ta musamman mai ofishi a masarautun
Gobir.[33]
5.
Ga
dukkanin abubuwan da suka bayyana Gobir ba ta aminta da tarihin Bayajidda ba.
6.
Na
fihimci cewa babu wai, Gobirawa su suka kawo dabarun yaƙi a farfajiyar
Sudaniyya, kamar yaƙin
taron dangi
da Turawa ke bugun gaba da shi; da salon a mutu
har liman
wanda Larabawa ke bugun gaba da shi; da sasasantawa
ta fuskar auratayya
wanda Fulani suka ara daga gare su. Don tabbatar da wannan iƙirari, Saular
Sakkwato ta kasha wa Daular Gobir mutane ɗari (100) da ta turo su taimaki Sarki Sama
na Daular Kabi yaƙi (da su Fulani). Aka kashe su a ganin Natsini, Gobir
ta sake turo wasu nan da nan ƙarƙashin Ɗangaladima Ali,
suka kuma ci nasarar yaƙin (Bagaye, 2018).
Naɗewa
Ban ce na ce komai ba, amma na san waɗanda suka ce wani
abu, na ce wani abu a kan maganganunsu. Tattara tarihin al’umma ba aikin
rukunin masana ɗaya ba ne, taron
dangi ake yi masa. Wanda ke tsinkayar Gobir da nisa, dubin tsoro ya yi mata.
Wanda ke kallonta kusa, bai yi mata duban natsuwa ba. Wanda ke jin ka-ce-na-ce
a kanta, bai fahimce ta ba, sai ya yi nutso cikin ayyukan da aka yi a kanta na
ilmi. Rubuce-rubucen da aka yi kan Gobir cikin Faransanci da Ingilishi da
Larabci ba su shiga sosai a makarantun ilmi na addini da boko ba.[34]
Abin ban sha’awa, ga Gobirawa da suturarsu da tsagarsu ta gado da sunayen
kakanninsu har yanzu ba su wofintar da su ba. Daulolin da Gobir ta ci yaƙi ba su taɓa tunanin mai da
gami ba, waɗanda suka ci
galaba a kanta har gobe ba su son a yi zancen fansa, kaico!
Jagora: Ashe
kura ko ta yi kwance
:Ko an yanke ba ta
motsi
:Ɗan akuya bai ƙetararta
:Yana aza kura
lahiya take
:Ba shi isa kusa ba
shi yarda
MANAZARTA
AbdulMalik,
M. (1966) Zuwan Turawa a Nijeriya ta
Arewa. Zaria: NNPC.
Adamu,
M. (1978) Hausa Factor in West African
History. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Alƙali, B. (1968)
“Hausa Community in Crisis Kebbi in the 19th Century” MA thesis,
Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity.
Augi,
A. (1979) “Migration of the Gobirawa: A Reconsideration”, Paper Presented at
Postgraduate Seminar Department of History, Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity.
Augi,
A. R. (1984) “The Gobir Factor in the Social and Political History of the Rima
Basin” (c. 1650 to 1808), PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bellio Uniɓersity Ɓol. I.
Boyd,
J. (1982) “The Contribution of Nana Asma’u Fodio to the Jihadist Moɓement of
Shehu Usman Dan Fodio from 1820-1865”, MPhil thesis. London: Polytechnic of
North London.
Bunza,
A. M. (2009) Narambaɗa. Lagos: Ibrash.
Bunza,
A. M. (2017) Dabarun Bincike A Nazarin
Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Gagare, B. (1982) Ƙarshen
Daular Alƙalawa. Lagos: Ma’aikatar Al’adun Gargajiya Ta
Tarayya.
Gatawa,
M. (1995) “Migration, Settlement and Integration: The Tuareg of Sabon Birni
Local Goɓernment Area”, BA Project, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniersity.
Gobir,
A. S. H. (1982) Kunne Ya Girmi
Kaka Ingantaccen Tarihin Hausa. Presented to Alhaji Shehu Aliyu Shagari
The President of the Federal Republic of Nigeria on the Commemorating the First
Presidential Ɓisit to Sabon
Birni on Monday 26th July 1982. By Sarkin Gobir Alhaji Muhammadu
Bawa.
Gobir,
H. and Boyd, J. (1981) “Salla in Sabon Birni in Gobir Customs and Tradition” in
Zaruma Cultural Magazine, Sokoto.
Hama,
B. (1967) Histoire du Gobir at de Sokoto.
Niamey.
Hamdan,
S. & King, N. (1975) Ibn Batuta in
Black Africa. London.
Hisket,
M. (1975) History of Hausa Islamic Ɓerse.
London.
Last,
M. (1985) “The Early Kingdoms of the Nigerian Saɓanna”in, J.F.A. Ajayi &
Micheal Crowder, Ɓol. One.
Maniya,
M. S. (2009) Tarihin Sahabban Shehu.
Sokoto: Al-Ameen Printing.
Meeek
C. K. (1971) The Northern Tribes of
Nigeria. London: Clarke, Doble and Brendon Ltd.
Miles,
W. F. S. (1994) Hausaland Diɓided
Colonialism and Independence in Nigeria and Niger. Cornell: Uniɓersity
Press.
Nadama,
G. (1977) “The Rise and Collapse of a Hausa State: A Social and Political
History of Zamfara”, PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity.
Richardson,
J. Traɓels in the Great Desert of Sahara
in the years 1845 and 1846, London: Ɓol. 11.
Sami,
S. Traditional Titles in Northern Nigeria.
Smaldone,
J. P. (1977) Warfare in the
Sokoto Caliphate Historical and Social Perspeɓiɓes. Cambridge: Uniɓersity Press.
Tarihin Daular
Gobir
Tremearne,
M. A. J. N. (1914) The Ban of Bori Demons
and Demon-Dance in West and North Africa. London: Health Cranton and Ouseley,
Ltd.
Usman,
Y. B. (1974) The Transformation of
Katsina. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Waɗanda Aka Tattauna Da Su
1.
Professor
Murray Last, Uniɓersity College, London.
2.
Malam
Yakubu Bagaye, BA, (Protocol) Sakataren Hulɗa da Jama’a na Masarautar Kabi.
3.
Dr.
Yakubu Aliyu Gobir, PhD, Dept. of Nig. Lang. UDUS.
4.
Dr.
Aliyu Uba, PhD, Federal College of Education, Ondo.
5.
Malal
Sayyadi Ruma, MA, Goɓernment House, Katsina.
6.
Malam
Bature Dunkushi, (Teacher) Malamin Makaranta/ Ɗan Sarauta.
7.
Malam
Idris Geza, (Teacher) Malamin Makaranta/ Ɗan Sarautar Geza,
(Jikan Sarkin Shiko Manu).
8.
Professor
Babajo, Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity, Katsina.
9.
Malam
Umaru Ango, Gidan Tarihin, Sakkwato.
[1] Shahara a duniyar mutane kamar
Zulqarnaini da Qaruna da Namarudu.
[2] Daga cikin Iskoki akwai Ifritu da
Dandanguna, uban Aljan da Hajon Ruwa.
[3] Daular Gobir tana gaban Kabi da
Katsina ta riga dauloli da yawa wayewar kai a duniya.
[4] A dubi Augi, Migration of Gobirawa:
A Reconsideration, paper ABU Zaria, 1979.
[5] A dubi Last, The Early Kingdoms of
the Nigerian Savanna, cikin J.F.A. Ajayi and M.
Crowder, History of West Africa, shafi na 11.
[6] Ra’ayin Murray Last ne da na
tattauna da shi ranar Talata, July 3, 2018 ta kibxau ya turo mini da saqon a
rubuce.
[8] A dubi Gobir, H. da Boyd, J. “Salla
in Sabon Birni in Gobir Customs and Tradition”, in Zaruma Magazine, 1981 shafi na 26.
[9] Cikin waqe-waqen yaran qasar Gobir
na dandali.
[11] Da suka ga an buwaye su Katsina
suka ce a mazaya a mayar da iri gida. Cikin daulolin qasar Hausa kowace na
wasan tobasantaka da Gobir kan yaqi.
[12] A al’adance ko raki Bagobiri ya yi
a kan ce assha! Baka gada ba ko ka vata iri.
[14] A ko’ina suka yi gari suna son a
naxa musu Sarkinsu. A tsakiyar wata qasa za ka ga an ce Sarkin Gobir wane.
[15] Hatta da su na Sabon Birni na miqa
wuya suka yi ga Fulani ba ana dai zaman ‘yan marina.
[16] Ya kasance wata al’ada cewa gabanin
ka yi babbar Sarauta an so a ce ka yi Sarkin Gobir a wuraren.
[17] Sarkin Gobir Amadu da Narambaxa ya
yi wa kixa, ya yi takarar Sarkin Musulmi tare da Sarkin Musulmi Abubakar na III
bayan rasuwar Hassan Xan Mu’azu.
[18] A Gwadabawa an yi Sarkin Gobir
bakwai, biyu daga ciki suka yi Sarkin Musulmi wato Sarkin Musulmi Muhammadu
Maiturare (1915-1924) da Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari (1924-1931). An yi
Sarkin Gobir Ahmadu (1924-1928), Sarkin Gobir Muhammadu Adiyya (1929-1931),
Sarkin Gobir Abdurahman Jatau (1931-1968), Sarkin Gobir Muhammadu Bello (1968-1974),
Sarkin Gobir Muhammadu Zayyana (1974-2013), Sarkin Gobir Lawal Muhammadu
Zayyana (2014-yau).
[19] Sarkin Gwandu Haruna da Sarkin
Gwandu Jakolo duk sun yi Sarautar Sarkin Gobir Na Kalgo.
[20] Muhammadun Sama da Sarkin Kabi
Muhammadu Mera duk sun yi Sarautar Sarkin Gobir.
[21] A Sakkwato da Bafulatani ya ga
Bagobiri sai ya ce: “Jikan Inna uwar bori.”
[22] Babu wata daula da ta kuvuta ga
haka, Mujaddadi ya ambaci waxannan al’adu cikin Nurul Albabi da Wasiiqatul
Ikhwani da Bayaanil
Bidi’as Shaixaniyya.
[23] Zuru akwai Magiro, Fulani na da
nasu, Yawurawa na da, ga su nan dai.
[24] A sabon binciken tsarin sunayen
Iskoki da yadda ake yi musu hidima daga qasashen Larabawa suka shigo qasar
Hausa. Musulunci ya yi naso ciki sosai.
[25] Da Argugu da Gobir da Zamfara da
Katsina bori ya bazu sosai da qyar Musulunci ya ci nasara a kansa.
[26] Mujaddadi Xanfodiyo a gidan
Sarautar Gobir ya yi karantarwa.
[27] A lokacin sun ga ya yi musu qarami
ga shiga sha’anin manyan malamai.
[29] Ba a kafirta mai salla domin aikata
savo.
[30] A cewar su: xiya da ya haifa yana
mace a ba su rabon mata, xiyan da ya haifa yana namiji a ba su rabon maza,
wanda ya haifa da kansa a ba shi rabon mace da namiji.
[31] Abin ya faru don haka ba son su
qure shi suke yi ba, so dai ake a gaya masa ya taka sannu da karatu.
[32] Gobir ta tava Sarki Kututturu,
Sarkin ya mutu suka qi su faxa don kar yaqi ya ci su. Aka ci gaba da yaqi ba
Sarki sai Kututturu.
[33] Sashen Tarihi da Masarautar Gobir
su kula.
[34] Siyasar da ke tsakanin Daular
Sakkwato da ta Gobir ba ya rasa hannu a ciki.
Yallabai ina son na dauki wannan binciken na kara fadadda shi kasancewa ta Marubuciyar harshen adabin Hausa ina neman izinin ka.... Ramlat Abdul Rahman Manga
ReplyDelete