Showing posts with label PAPERS. Show all posts
Showing posts with label PAPERS. Show all posts

Tuesday, August 16, 2022

Ba A Wane Bakin Banza: Gurbin Daular Gobir Da Gobirawa A Farfajiyar Sudaniyya

August 16, 2022 0
Ba A Wane Bakin Banza: Gurbin Daular Gobir Da Gobirawa A Farfajiyar Sudaniyya
Gobir tsohuwar Daula ce da ta shiga gwagwarmaya da daulolin duniyar Sudaniyya. Burin wannan bincike ƙyallaro wasu daga cikin dalilan da suka ɗaga Daular Gobir da Gobirawa sama ga sauran dauloli. An yi garkuwa da fitattun ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba tare da taimakon yawon rangadi da tattaunawa da dafa kafaɗar adabin baka da rubutacce. Binciken ya gano cewa, Daular Gobir cin gashin kanta take yi kuma Bahaushiyar Daula ce. Bugu da ƙari,...

Wednesday, September 29, 2021

Ɗiyan Sarauta A Tafashen Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo

September 29, 2021 0
Ɗiyan Sarauta A Tafashen Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun na daga cikin fitattun makaɗan fada da suka makaro a ƙasar Hausa. Binciken wannan takarda ya ɗora shi a cikin rukunin makaɗan sarauta bisa taliyon salsalar waƙoƙin gidansu da ya gada, ya ɗora a kai. Binciken takarda ya tsaya a kan jigon “zambo”, ko a cikin jigon ya taƙaita ga “zambon ɗiyan sarauta”. An saurari waƙoƙin Ɗanƙwairo da yawa na sarauta, an karanta wasu da aka taskace, an yi amfani da mataimaka...

Tuesday, September 22, 2020

Zamfarawa a Diwanin Narambaɗa

September 22, 2020 0
Zamfarawa a Diwanin Narambaɗa
 Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa mai taken: Zamfara Kingdom: Social and Political Transformation from 14th Centuary to Date. Organized by Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, 25th – 28th February, 2020, at Usmanu Danfodiyo University Auditorium, Sok...

Monday, October 14, 2019

Tsaro A Nijeriyar Кarninmu: Lokacin Abu A Yi Shi

October 14, 2019 0
Tsaro A Nijeriyar Кarninmu: Lokacin Abu A Yi Shi
Tunanin Bahaushe a kan tsaro ya shafi tsaron lafiyar jiki da rayuwar da ke ɗawainiya da ita; tsaron ƙasa da tattalin arzikinta; wadatuwar abinci da ayyukan yi ga masu tsaro da ƙasar da ake ɗawainiyar tsarewa. Ke nan, tunanin Bahaushe na faɗar ‘tsaron kaya ya fi ban cigiya’, ya tabbatar da kasancewar tsaro makamin farko a rayuwar ɗan Adam. A fashin baƙin tsaro za mu ce, shi ne, samun walwala da sakewa da more wa ƙasa ga ɗan ƙasa, da samun cikakkiyar...

Folklore And Economic Security In Nigeria: (Alhaji Gambo Fagada a Radical Whistle Blower in Financial Crimes and Economic Genocide Matters)

October 14, 2019 0
Folklore And Economic Security In Nigeria:  (Alhaji Gambo Fagada a Radical Whistle Blower in Financial Crimes and Economic Genocide Matters)
Gambo was born in Fagada Babba, Mayyama Local Government, Kebbi State, Nigeria. His real date of birth is still under the cloud, but he claimed to be Seventy years old (70) as at 2002/2003. He died in the year 2016. By his oral testimony, he might be between 85/86 years old by the year 2018/2019 respectively. His pen name is Alhaji Muhammadu Gambo Mai Waqar Varayi. He was an accidental singer as he did not learn the art of singing from any singer of...

Wane Ne Narambaxa? Ibrahim Narambaxa Buhari Maidangwale Abdulkadir Tubali (1890-1963)

October 14, 2019 0
Wane Ne Narambaxa?  Ibrahim Narambaxa Buhari Maidangwale Abdulkadir Tubali (1890-1963)
‘Narambaɗa’ laƙabi ne da ake yi masa ga karyar farautarsa da ya yi wa suna Rambaɗa. An haife shi a garin Tubali shekarar 1890. Sunansa na yanka Ibrahimu, sunan mahaifinsa Buhari Maidangwale, sunan kakansa Abdulƙadir, sunan mahaifiyarsa Riba.[1] Sunan kakarsa mace Binta. Mahaifinsa Babarbare ne daga ƙasar Nijar, mahaifiyarsa mutunniyar Badarawa ce gidan Sarkin Makaɗa Ɗangwamna. Don haka, Naramba...

Kakkaɓan Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar Labɗo

October 14, 2019 0
Kakkaɓan Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar Labɗo
Asalin Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta na asali ƙabilanci. A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa bayi, don haka a ƙasarsu aka fara yaga wasiƙar Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa, a shiga rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn Saba’ suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da musibar Karbala abin kula n...

Wurin Da Babu Ƙasa Nan Ake Gardamar Kokuwa (Sharhin Littafin: Da ‘Yan Nijeriya da Buhun Gero Wa Ya Fi Yawa?)

October 14, 2019 0
Wurin Da Babu Ƙasa Nan Ake Gardamar Kokuwa  (Sharhin Littafin: Da ‘Yan Nijeriya da Buhun Gero Wa Ya Fi Yawa?)
Hausawa na cewa: “Komi ya ɓace maza ka biɗo shi”. Babban tunaninsu a kan haka shi ne, wuyar aiki ba a fara ba. A kowane lokaci mutane ke jayayya ana buƙatar raba gardama. Idan sa-in-sa ya yawaita, gaskiya ce ba ta bayyana ba. Da ta leƙo, ita ce raba gardama. Labarin masu yunƙurin fayyace da buhun gero da ‘yan Nijeriya wa ya fi yawa, ya bice duniyar kafafen yaɗa labarai na BBC da ƁOA da RFI da jaridun ƙasa da kafafen yaɗa labarai na jihohi. Da masoyansu,...

Ruwa Na Ƙasa Sai Ga Wanda Bai Tona Ba (Hisabin Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas Azare)

October 14, 2019 0
Ruwa Na Ƙasa Sai Ga Wanda Bai Tona Ba  (Hisabin Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas Azare)
Tun fil azal karambanin leƙo abin da ya faku Bahaushe na kiransa duba. A wata fassara idan ta shafi amfanin da wuri ana ce masa “arwa”. Bayyanar Musulunci da wasu malamai suka durmuya ciki, a zauna, a harɗe, a share ƙasa, a goge, ya sa ake yi masa suna da “Bugun ƙasa”. A waƙar da muke nazari Alhaji Shata ya yi amfani da “duba”. Ta kowace fuska aka yi karambanin gano gobe, ta carbi ce, ko ta taurari, ko ta bugun ƙasa, ko ta hisabi ko ta duban motsin...

Kunya Ginshiƙin Tsaron Ƙasa Da Bunƙasarta

October 14, 2019 0
Kunya Ginshiƙin Tsaron Ƙasa Da Bunƙasarta
Kunyar da ke tsakanin yara da manya ita ta wanzar da zaman siyasar shugabancin ƙasar Hausa ta fi kowace biyayya tsakanin masu mulki da moro. Da Musulunci ya zo, kunyar ta faɗaɗa tsakanin malamai da ɗalibai. Tsare wannan kunyar ya hana wanzuwar yi wa masu iko tawaye da zanga-zanga, ya toshe rigingimu irin na addini tsakanin mabiya da shugaba ko malamai. Rashin kunya ne yin sa-in-sa da shugaba ko malam...

Gurbin Harshen Fashin Baƙi Ga Mai Tafsiri

October 14, 2019 1
Gurbin Harshen Fashin Baƙi Ga Mai Tafsiri
Addinin Musulunci ya yi fiye da shekaru aru-aru da leƙo Afirka idan aka yi la’akari da ɓullar addinin a Makka da tarihin Hijira ta farko da ta biyu[1]. A hasashen tarihi, daulolin ƙasar Hausa maƙil suke da mutane a zamanin da Musulunci ya bayyana a duniya.  Tarihin yadda ya shigo ƙasar Hausa abin kirdado ne tsakanin Daular Borno da Daular Mali da Daulolin Larabawan Sahara da kuma ɗaiɗaikun ‘yan kasuw...

Thursday, January 10, 2019

Don Me Ake Karatun Hausa?

January 10, 2019 0
Don Me Ake Karatun Hausa?
Bisa ga al’adar ɗaliban harshen, ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe tarkakken nazarin da ɗalibi zai ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi in yi bara da Hausa.[1] Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[2] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu da neman shahara a ciki. A ganina,...

Kuka A Faifan Nazari: Laluben Diddigin Bahaushen Kuka Da Ƙunshiyar Lafazinsa

January 10, 2019 0
Kuka A Faifan Nazari: Laluben Diddigin Bahaushen Kuka Da Ƙunshiyar Lafazinsa
A iya sanina, wannan ɗan bincike sabo ne, saboda rashin samun wani da ya gabace shi a fagen nazarin Hausa. Duk da haka, abin da aka gina bincike a kansa “kuka” ya girmi duk wani mai bincike da zai yi bincike a kansa. Tunanin kowane mai tunani, ba zai fice da’irar al’adarsa da adabinsa da aka gina cikin harshen da yake rayuwa da shi. Sanin haka ya sa na gayyato ƙwararrun mawaƙan Hausa (20) [14 na baka, 6 marubuta], na sarrafa ɗiyan waƙoƙinsu (34). Cikin...

Linguistic Spaces In Hausa Trado-Medical Antiquities: A Neglected Aspect In Hausa Anthropological Linguistics

January 10, 2019 1
Linguistic Spaces In Hausa Trado-Medical Antiquities:  A Neglected Aspect In Hausa Anthropological Linguistics
 This paper is an attempt to peep at a forgotten and neglected aspect of Hausa linguistics in the name of Anthropological Linguistics. It is a study which sets out to provide an overview of the subject under review as suggested by the paper’s title: “Linguistic spaces in Hausa trado-medical antiquities”. The data are gathered from primary and secondary sources specifically during field work and several contacts with selected Hausa practitioners....

Hyperbole As The Peak Of Stylistic Adornment In Hausa Oral Songs

January 10, 2019 0
Hyperbole As The Peak Of Stylistic Adornment In Hausa Oral Songs
The study area of this paper is hyperbole in Hausa oral songs. In contemporary Hausa studies, it is named Kambamar Zulaƙe (exaggeration or overstatement). In the study of the style under review, it is discovered that the literal and technical meaning of hyperbole is far beyond exaggeration or overstatement. It is a popular style, deeply rooted in all the categories of Hausa oral songs. It traces in the most prominent styles in Hausa oral songs and its...

Wednesday, January 9, 2019

Bitar Karatun Hausa A Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙrn. 21): (Wurin Da Babu Ƙasa Ake Gardamar Kokuwa)

January 09, 2019 0
Bitar Karatun Hausa A Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙrn. 21): (Wurin Da Babu Ƙasa Ake Gardamar Kokuwa)
The paper is a historical review of Hausa studies in Nigerian academia. In the struggle, relevant related literatures were critically examined to justify the dare need of an updated progress report. In this study, an advanced Hausa study is the desired target to conjugate Hausa on the rating scale of Nigerian academic standard. Similarly, tertiary institutions, Universities and research centers handling Hausa academic Activities are the umbilical cord...

From Zinder To Hausaland: (The Traces of Zinder Hausa-Muslim Scholars and Scholarship in Hausaland)

January 09, 2019 0
From Zinder To Hausaland: (The Traces of Zinder Hausa-Muslim Scholars and Scholarship in Hausaland)
Migration is a universal culture across human history. The culture of migration is unavoidable in human history from time immemorial (evolution of mankind) to date. By definition, human migration is the movement by people from one place to another with the intention of settling, permanently or temporarily in a new location (Wikipedia). The said movement could be external, which is often over long distances or internal within a short range within the...

Wednesday, January 2, 2019

The Zarma Factor In The Kingdom Of Kanta

January 02, 2019 0
The Zarma Factor In The Kingdom Of Kanta
 Cultural relationship among African societies in sub-Saharan Africa is as old as the land itself. Brutal colonial policy on African cultures and traditions couple with wicked approach to the African ancient boundaries dealt a great blow to African history and development. Powerful kingdoms and chiefdoms were dismantled and dismembered into districts, regions and provinces. This resulted in a very sever cultural and linguistic endangerments in...

Wane Ne 'Dan Ta’adda?sava

January 02, 2019 0
 Gajeren tunanin da ke ga ɗan Adam shi ya sa Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan, mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya saɓa mata. Wannan dalili ne ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke yi, a koyaushe gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a nan shi ne , ƙoƙarin dangantawa wata al’umma da ke wata...