Addinin Musulunci
ya yi fiye da shekaru aru-aru da leƙo
Afirka idan aka yi la’akari da ɓullar
addinin a Makka da tarihin Hijira ta farko da ta biyu[1]. A
hasashen tarihi, daulolin ƙasar
Hausa maƙil suke da mutane a zamanin da Musulunci
ya bayyana a duniya. Tarihin yadda ya
shigo ƙasar Hausa abin kirdado ne tsakanin Daular
Borno da Daular Mali da Daulolin Larabawan Sahara da kuma ɗaiɗaikun ‘yan kasuwa…
Gurbin
Harshen Fashin Baƙi Ga
Mai Tafsiri
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Harsuna da
Al’adu
Tsangayar Fasaha
Da Ilimi
Jami’ar Tarayya
Gusau
Afrilu, 2018
Tsakure
Tafsiri shi ne fashin baƙin Alƙur’ani daga Larabci zuwa
harshen Hausa. A fagen tafsiri, harsuna biyu ake kokuwa da su: Harshen da ake
karanto kulkin baƙi
da harshen da ake fashin baƙi
da shi. Dole ne ga mai tafsiri ya naƙalci
harsunan biyu tare da sanin al’adunsu da adabinsu. Mai tafsiri ma’ana yake ƙoƙarin bayarwa, don haka
dole ya tunkari ma’anar kurum. Harshen Hausa fitaccen harshe ne a addinin
Musulunci domin Musulunci ya fi shekara dubu a ƙasar Hausa. Daɗewar
da addinin ya yi ciki wani makami ne ga mai tafsiri ya yi taka tsantsan wajen
isar da saƙo
cikin kyakkyawar Hausa, da zaɓen kalmomi, da kula da al’adun masu
karɓar
saƙo.
Takardar ta yi ɗan share fage kan Tarjamomin da aka
wallafa na Alƙur’ani
zuwa Hausa (na Kabara da Gummi da Sa’idu da wasu). La’akari da yawan Hausawa a
duniya da daulolinsu da dangoginsu da kashe-kashen karuruwan harshen Hausa,
babu dole ga mai fashin baƙi
na zaɓen
wani daga cikin karuruwan harshe ya yi ƙuƙe-na-ƙuƙe. Binciken ya gano buƙatar a samu ayyukan
magabata na Hadisi a taskace shi kamar yadda aka taskace tarjamomin. An ɗora
binciken kan fasula haɗi da naɗewa
domin warware bakin zaren matashiyar muƙalar.
Gabatarwa
Tunanin saƙon wannan bincike shi ne,
lurar da gogan fashin baƙi
(Malamin Tafsirin Alƙur’ani)
yadda zai sarrafa harshen gado da yake fashin baƙi da shi domin masu
sauraronsa su amfana da shi sosai. Hikimomi da fasahohi da ke cikin harshen
suna cikin jikin duk wani ma’aboci harshe, kuma su ne wayonsa na yin awo da ƙima ga abubuwan da ya
tunkara, da waɗanda
suke tunkararsa, da waɗanda ya gani, da waɗanda
ya ji, da waɗanda
yake karantawa, da waɗanda ake karanta masa. Waɗannan
abubuwa suka tilasta wa duk wanda zai yi fashin baƙin Alƙur’ani da harshen Hausa a
ƙasar
Hausa, kuma ga Bahaushe ko mai jin Hausa, dole ya yi hattara sosai domin
Hausawa cewa suka yi, ‘Magana zarar bunu ce, da ta fita sai gyaran zama na baya
ga walle’; wanda bai dace ba ga mai fashin baƙin nassoshin addini.
Tarihin Fashn Baƙin Nassoshin Alƙur’ani (Tafsiri)
a Ƙasar Hausa
Addinin Musulunci ya yi fiye da
shekaru aru-aru da leƙo
Afirka idan aka yi la’akari da ɓullar addinin a Makka da tarihin
Hijira ta farko da ta biyu[2]. A
hasashen tarihi, daulolin ƙasar
Hausa maƙil
suke da mutane a zamanin da Musulunci ya bayyana a duniya. Tarihin yadda ya shigo ƙasar Hausa abin kirdado
ne tsakanin Daular Borno da Daular Mali da Daulolin Larabawan Sahara da kuma ɗaiɗaikun
‘yan kasuwa[3].
Gabanin saduwar Bahaushe da cikakken Alƙur’ani wasu littattafai
na furu’a da yabon Manzo da Salatai suka fara bayyana. Can da, a watan azumi, a
kan taru a yi addu’o’i da karatun salati da waƙe-waƙen yabon Annabin rahama
(SAW) cikin Larabci. Da Alƙur’ani
ya bayyana, ba a daina ba domin a tunanin Hausawan farko Musulmi, Alƙur’ani ba ya fassaruwa da
kowane harshe na duniya in ba Larabci ba[4]. Don
haka, hidimomin watan azumi na wancan zamani ya tsaya ga ibadojin gaɓɓai,
karance-karancen ƙissoshin
yaƙe-yaƙe da tarihin fiyayyen
bayi Muhammadu (SAW). Da abin ya ƙara
haɓaka
aka fara karatun Ashafa
ta Alƙali
Iyadh da Ishiriniyya
da Alburda
da Dala’ilul Khairati[5].
Ga alama, tafsiri ya fara wakana ƙasar
Hausa wajajen ƙarni
na 16 zuwa na 17, bisa la’akari da ƙwazon
Malaman ‘Yandoto da ƙwazon
Malam Jibril bn Umar[6]. Bisa ga
wannan kirdado an fi kimanin shekara ɗari shida (600) ana
fashin baƙin
Alƙur’ani
mai tsarki a ƙasar
Hausa.
Matsayin Harshen Hausa a
Addinin Musulunci
Harshen Hausa wani gwarzo ne daga
cikin gwarajen da suka yi wa Musulunci jihadi, da babu malamin da ya yi
kamarsa. A Afirka harshen addini ne, domin kashi tis’in da bakwai (97%) ko
tis’in da takwas (98%) na Hausawa Musulmai ne[7]. Shi ne
harshen da ya fi kowane amo a duniyar baƙar fata[8]. Shi ne
harshe na 11 daga cikin ƙididdigar
harsunan duniya 7000 mafi yawan jama’a da ke magana da shi. Hausawa ne ƙabilar da ta fi kowace ƙabila tasiri a cibiyar
Musuluncin Duniya (Saudiyya) don haka harshen Hausa ya yi fice hatta cikin
hidimomin cikin Hajji harshen Hausa ne na farko a cikin harsunan Afirka da ake
yin sanarwa da shi a Jimra
(Shaiɗan
ƙarami
da Shaiɗan
babba)[9].
Bahaushe ne na farkon karɓar kyautar duniya ta sanin luggar
Larabci Shaikh Nasiru Kabara (fayyace sunayen doki ɗari)
a Masar[10].
Harshen Hausa ne harshen farko na Afirka da aka tarjama Alƙur’ani ciki a rubuce
(Shaikh Abubakar Mahmud Gummi)[11].
Bahaushe ne na farko da ya karɓi kyautar duniya na hardace Ƙur’ani kulkin baƙi da fashin baƙinsa a Larabci (Shaikh
Jafar Muhamud Adam)[12]. Sanin
wannan ga mai fashin baƙi
wata hujja ce ta daidaita masa akala na ba da muhimmanci ga harshen Hausa da
yake fashin baƙi
da shi. Ashe mai tafsiri cikin Hausa da duniyar Musulmi yake magana, dole ya yi
zaɓen
kalmomin da za a fahimce shi. Hausa na da gurbi cikin Majalisar Ƙoli da Fiƙihun Musulunci na duniya
da ke da cibiya a Jedda.
Ilimin Fashin Baƙi da Naƙalinsa
Ana amfani da kalmomi da dama domin su
ba da makusanciyar ma’ana ta fashin baƙi.
Daɗaɗɗiyar
kalmar da aka fi sani ita ce “mayau”. Mayau shi ne, wanda ake yawo da shi ko
aka aje shi domin da an samu wani wanda ba a jin harshensa kamar Balarabe da
Bature, shi yana jin harshen sai ya mayar da gami ga waɗanda
ba su ji. Kalmar fassara ta fara bunƙasa
a karatun zaure na littattafan ilmi wanda Bahaushe ke cewa “karatun sani”.
Littattafan da ake karanta masa ma’anonin nassoshinsu shi ne “fassara”. Haka
abin ya zo ga aikin boko da jarida. A wajen Alƙur’ani a can da, nan kaɗai
ake amfani da kalmar “fashin baƙi”
domin irin tatarniya da taka-tsantsan da kaffa-kaffa da tsantseni da ake wajen
fayyace maganar Allah ga bayinSa cikin wani harshe da ba da shi Allah Ya yi
magana ba, don haka ake kiransa “fashin baƙi”, kuma a koyaushe aka
gama sai mai fashin baƙin
ya ce: Allah masani, Allah Ya sa mun dace.
A fagen fashin baƙin Alƙur’ani sunan fassarar da
ake ita ce “fassarar nan take” irin wadda ake a tarukan Majalisar Ɗinkin Duniya da manyan
tarukan ilmi na ƙasa
da ƙasa.
Irin wannan fassarar ta fi komai wuya, sai gogaggu ga nahawun harsunan kuma ƙwararru ga iya magana.
Mai fashin baƙin
Alƙur’ani
ya kyautu ya kalli waɗannan salailai na fashin baƙi guda uku:
i.
Fashin baƙin ba ni in ba ka
fassara.
ii.
Fashin baƙin kalma da kalma.
iii.
Fashin baƙi mai ‘yanci.
Fashin baƙin
ba ni baƙi
in ba ka fassara shi ne wanda ake yi a tafsirin da, mai jan nassi ba nassin
gaba ɗaya
zuwa aya zai jawo ba. Zai tsakuro kowane baƙi ɗai
bayan ɗaya
goga na fashewa; misali:
Wa minas naasi man
ya ƙuulu
aamanna bil laahi.
Daga
cikin su mutune mai cewa imaanina ga abin bauta
·
Fashin baƙin kalma da kalma ya fi
sha’fuwar mai karatu shi kaɗai
a wani lokaci ko da ja masa baƙi
ake yi. Yana da siga kamar haka:
Lil Laahi mulkus samaawaati wal ardhi yakhluƙu maa yashaa’u
Lallai ga abin bauta mulkin sammai da ƙassai yana halitta abin
da ya so.
Idan an duba wannan fassarar ta fi ta farko sake jiki,
amma ma’ana ta ƙuru-ƙuru ta maƙale.
·
Fashin baƙi mai ‘yanci shi ne,
fashin baƙin
da goga zai yi tsayin daka ya saka dukkanin kalmomin da Bahaushiyar ma’ana za
ta sadu da Bahaushe. Yana da ‘yancin hararar nassin a kaikaice yadda ma’anarsa
za ta fito ƙuru-ƙuru. Misali:
Laisa ka mishlihi
shai’un wa Huwa sami’un ali mun
Bai yi kama da komai ba,
kuma ta tabbata mai ji ne da cikakken ilmi.
A wajen fashin baƙi da Hausa fasara mai
‘yanci ta fi karɓuwa da isar da saƙo sosai. Fashi baƙin da ya fi kusantar da
ma’ana shi za a zaɓa. Kamar kalmar “Waabilun” ta nassin Alƙur’ani ba za a fassara ta
ba da: “ruwan bisa”, ko “manyan ruwa”, ko “ruwa”, ko “ruwa da iska da tsawa”,
ko “ruwa ka-in-da-na-in”, duk a luga ba a fassara wa Bahaushe abin da ya sani
kuma ya yi daidai da “waabilun” na Larabci ba. A nan, mai fashin baƙi na da ‘yancin shiga
al’ada ya fassara ta da: “ruwa kama da bakin ƙwarya”. Ƙaddara idan da Turanci
kalmar ta zo, Bature zai fasara ta da: “It rains
cats and dogs”, ai ba za ka ce: “An yi ruwan
kyanwowi da karnuka ba”?
Kashedi ga Mai Fashin Baƙi
Nassin Alƙur’ani ya ce, a isar da
saƙo
kuma bai ayyana harshen da dole da shi
za a isar ba. Kulkin baƙi
ya yi gargaɗi
cewa, saƙon
da za a isar a fassara shi cikin hikima da daɗin
baki. A tsarin addininmu, fashin baƙi
ba na katoɓara
ne da soki burutsu ba. Ya kyautu mai fashin baƙi ya kula da abu uku da
za su ba shi haske ga abubuwa goma: Na farko, a harshen da yake tafsiri akwai
waɗanda
suka fi shi saninsa da fahimtarsa. Na biyu, akwai waɗanda
fahimtarsa da su zozo-zozo take. Na uku, akwai waɗanda
ke ƙasa
da shi ga fahimta. Don haka ya riƙa
magana da waɗanda
ke ƙasa
da shi sannan za su fahimce shi. Tilas wajen zaɓen
kalmomin a kula da wannan a sa masa ido sosai don a amfana a amfanar.
Abubuwa goma da waɗancan
abubuwa uku za su haifar a fafitikar fashin baƙi su ne:
1.
Kula da hankalin masu
sauraron fassararsa.
2.
Sa lura ga wayewar kansu
ga kalmomin isar da saƙo.
3.
Natsuwa da gurbin ilminsu
wajen ba su fassara.
4.
Tuni da addinin da suka
fito da wanda suke ciki dole ne.
5.
Martaba al’adunsu da ba
su yi taho-mu-gama da aƙida
ba.
6.
Lura da irin zamanin da
ake ciki wata kwalliya ce ga fassara.
7.
Kaffa-kaffa da aƙidojin waɗanda
ake yi wa tafsiri abin so ne.
8.
Ba da tazara ga
fahimtocinsu wajen fashin baƙi
salon jawo hankalinsu ne.
9.
Dole a kiyaye da
siyasarsu wajen luguden kalmomin fassara.
10. Tarihinsu
wani makami ne daga cikin makaman da mai tafsiri ya kamata ya tanada.
A kowane hali mai tafsiri ya so ya sarrafa harshe
wajen fashin baƙin
kuramen kalmomin nassoshin buwayayyen littafi in bai harari waɗannan
abubuwa da kyau ba, yana rasa ‘yan sauraro nagartattu.
Da Tsohuwar Zuma Ake
Magani
Ƙur’anin da za a yi fashin
baƙinsa
ya ce, a tambayi masana ga abin da ba a sani ba[13]. Haka
kuma, ya tabbatar da cewa, saɓanin harsunan da aka ƙaddaro mu da shi, domin
mu san kanmu ne ba don bugun gaba ba[14].
Dalilin da ya sa Allah Ya aiko manzonsa da harshe ɗaya
tattare da sanin bayinSa ba harshe ɗaya kawai suke magana da
shi ba, ita ce babbar hujjarmu ta cewa, fassara wata farfajiya ce babba cikin
addini da dole sai da ita saƙon
addini zai barbazu kamar yadda wanda ya aiko addinin Ya yi umurni. Mai tafsiri
ya sani cewa, komai za ya fassara an riga shi, shi bita ce kawai zai yi. Don
haka, ka da ya ƙirƙiro fassararsa da salon
harshensa kawai wai don ya ji harshen asali na littafin Allah.
Daga cikin masu tafsiri a Arewacin
Nijeriya yau a iya saninmu, fiye da kashi (85% - 90%) ba su koye shi tun
farkonsa har ƙarshensa
gun wani malami ba. Wasu ta hanyar zuwa sauraron tafsirin wasu, wasu a kaset na
rediyo da bidiyo, wasu daga fahimtar fassarar littattafan furu’a Iziyya, Risala, da Askari. Manya-manya daga masu
tafsiri a ƙungiyoyinmu
na Musulunci Tarjamar Ma’nonin Alƙur’ani
zuwa Hausa na Shaikh Abubakar Gummi, ya shaihuntar da su. Akwai wasu malamai da
suka yi tarjamar Alƙur’ani
zuwa Hausa cikin kyakkyawar Hausa, da ya kyautu a ce an nazarce su domin ƙarin gudunmuwa. Idan aka
yi guzuri da wasu daga cikin waɗannan za a amfana sosai.
1.
Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani zuwa Hausa na
Shaikh Nasiru Kabara.
2.
Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani zuwa Hausa na
Shaikh Abubakar Gummi.
3.
Tarjama da Tafsirin Alƙur’ani cikin Hausa na
Farfesa Bello Sa’id da wasu Indiyawa.
4.
Tarjamar Alƙur’ani zuwa Hausa na
Wani/wasu da ba suna.
5.
Sabon Tarjamar Alƙur’ani da Gyare-gyare
wanda wasu ɗaliban Ilmi suka
yi kan fassarar Shaikh Gummi.
A ɗan nawa bincike, idan mai tafsiri ya
tanadi waɗannan,
zai ƙara
samun haske sosai. Dalili kuwa za a ga wani Bakano ya yi shi, wani Basakkwace
ya yi shi, wani kuma ɗaliban ilmi ne na zamani suka soko
muryoyinsu. Duk da yake muna ganin fassarar waɗanda
suka yi wa Shaikh Abubakar Gummi gyara ba ta zauna ba, abin kamar shigar ƙadangare shantu ne, babu
laifi duk dai a karanta domin ko ɓata ƙara sanin daji ne.
Harshen Tarjama
Mai tarjama ana son ya ƙoshi da abubuwa sosai da
sosai. Harshen matanin da ake fashin baƙi, da harshen da yake miƙa saƙonsa a cikin a lugude su
sosai. Sanin nahawun harsunan kaɗai bai wadatarwa sai an naƙalci adabinsu da
al’adunsu. Kowane ɗaya aka yi wa raggon kaya daga ciki za a
ji fassarar bambarkwai ba wani nauyi a ma’ana kamar hakin da guguwa ya ɗauko.
Wanda duk ya ɗauki
ɗawainiyar
fashin baƙin
Alƙur’ani
zuwa Hausa ya kiyaye da harshen da yake fassarar kamar haka:
1.
Amfani da sanannun
kalmomi gama-gari da aka saba ji. Babu laifi a faɗi
tsohuwar kalma a gwama ta da sabuwa domin a fahimce ka kamar kalmomi: ruɓushi/hasara,
kushewa/kabari, kasanki/likkafani, rausuwa/sakin aure, kububuwa/majici,
kashindo/kayan sata, zakara/Ladan, cissawai/ragar rana, Dandu/Asibi,
gogarma/Sarki, kushili/luwaɗi.
2.
Kiraye haramtattun
kalmomi. Fashin baƙin
littafin Allah ibada ne, dole ne a yi shi cikin natsuwa da ƙanƙan-da-kai da kunya da
ladabi da biyayya. Allah ba Ya jin kunyar bayyana wa bayinSa,[15] amma
kuma Ya yabi masu jin kunya ga hulɗoɗinsu[16]. Mai
tafsiri rungume da Alƙur’ani
yake, bambancin maganar Allah da ta bayi, kamar tazarar da ke tsakanin bayi da
Allah ne[17].
Abubuwan da suka shafi al’adun kunya ana yi musu lulluɓi
kamar haka:
i.
Abin da ya shafi
tsiraici: A ce al’aura, ko farji, ko gaba, ko baya.
ii.
Abin da ya shafi hulɗa
da iyali: a ce, biyan buƙata,
ko kwanciya, ko taki, ko saduwa ko kusanta ko bi da sauransu.
3.
Kiyayewa da taƙadarun sassan adabi: Kowane
harshe na da wasu abubuwa daga cikin adabinsa da ba su dace a gayyato su wajen
fashin baƙi
ba. Duk abin da ya shafi izgili ko tsokana ko wautar da wata ƙabila ko wani mutum ko ke
iya tsirar da ƙabilanci
da rashin tsoron Allah a zuci a kiyaye da shi wajen tafsiri. A dubi waɗannan
misalai a gani:
i.
Sai na ga abin da ya ture
wa Buzu naɗi.
ii.
Muna wasa ne, Gwari
ya ba da magani an sha an mutu.
iii.
Cinike! Inyamuri
ya sha mari.
iv.
Mun goga don Allah, Ɗanfulani
a masallacin Yola.
v.
Kangali Kano ƙwaari minna, in ji Ɗanbarno
da ya sha gora a ka.
Addini na kowa ne, duk wanda ya ba da
gaskiya a kansa na iya zuwa ya saurari malami mai fashin baƙi. Idan ya koma na cin
fuska, da cin zarafin wasu, ko muzanta su, wani abu ya shiga ciki.
4.
A kiyaye sosai da yin
ingausa a fashin baƙi:
Ingausa shi ne, surka wani harshe cikin wani yayin fashin baƙi. Mun san babu makawa ga
mai fashin baƙin
Alƙur’ani
dole a ji surkin kalmomin Larabci ciki jefi-jefi amma ka da abin ya kasance daɓa-daɓa,
har sai ɗaliban sani kawai
ke fahimtarka. Idan ingausar Larabci ta yi yawa tana ɓatar
da ma’anar fassara. Haka yake wajen ingausar Turanci da bai ko kai matsayin
mustahabbi ba, ga mai tafsiri cikin Hausa. Waɗannan
abubuwa sukan bijiro wa mai tafsiri musamman idan an shiga cikin
hukunce-hukuncen shari’a na rabon gado da aure da cinikayya da aikin hajji da
zakka da sauransu. Ba dole ne sai mai fashin baƙi ya samo ma’anar kowace
kalma cikin Hausa ba, ai sunan tafsiri “fashin baƙi” abin da ake cewa
“fashi” kuwa shi ne “bayani” a lugude kalma luƙui-luƙui har sai mai harshen ya
gane abin da ake nufi.
A fuskantar nassoshin rabon gado za a ci karo da
kalmomin fannu da yawa alal misali: mas’ala, asibi ko asibci, tadakuli,
tabayuni, tawafuƙi,
da tamasuli ga su nan dai. Da mai tafsiri ya kusanci yadda magabata suka
fassara su a tafsirai da tarjamomin da suka yi wa Alƙur’ani cikin Hausa domin
samun daidaiton tarjama. Ka tuna, masu sauraronka sun sha sauraron wasu ba kai
ba.
Nahawun Tarjama
A tsarin ilmin harsuna, cikin harshe nahawu
ke bayyana. Nahawu shi ne, daidaiton kalmomi da ‘yan rakiyarsu cikin magana
tare da sassaɓawarsu
na lokuta da zamani da rarrabe jinsi da sigar yadda kalmomin za su yi tunkuɗeɗeniya
da sassaka a lafazance domin fitar da ma’ana. Mai tafsiri cikin Hausa ya san
Hausa ce yake yi kuma da masu jin harshen Hausa yake magana. Idan haka ne, ya
kula, zurfafa cikin bayanin ilimin Larabci ga abin da ya shafi nahawu da balaga
da manɗiƙi da sarfu da li’irabin
jimlolin ayoyi, a makaranta ya kamata a yi shi can cikin ɗaliban
ilimi. A dandalin tafsiri idan aka ce a yi shi, za a cinye lokaci kuma kaɗan
daga cikin masu sauraro kawai za su amfana. Nassin Alƙur’ani ba ya fassaruwa
gaya ba tare da gudunmuwar nassoshin Hadisai da biyan gurabun magabatan farko
ba. Idan aka kawo Hadisi, fashin baƙin
isnadinsa da mazajensa da taliyon ƙullin
dangantakarsu ya fi dacewa a makaranta. Idan aka tsawaita bayaninsu, wanda bai
yi karatu ba zai ji an gundurar da shi. Yawwa! A kula, domin daga cikin mafi
yawan waɗanda
ke zuwa sauraren tafsiri, waɗanda ba su ƙoshi da karatu ba sun fi
yawa.
Wannan ‘yar faɗakarwa
ko kusa ba za ta hana malamin tafsiri amfani da kalmomin fannu na nahawu ba.
Zumuntar harshen Hausa da Larabci Mahdi ne mai dogon tarihi, a wajen fassarar
za a ji kalmomin fannu sun yi kama da juna. Musamman idan aka zo a ire-iren waɗannan
wurare a kula da suna, wakilin suna, aikatau, sifa, bagiren lokaci da na zamani
da ‘yan rakiya, da miƙau
da karɓau
da sauransu. Abin nufi a nan shi ne, da a ce: “Dawuda shi ne ma’aikaci Jaluta
shi ne wanda aikin Dawuda ya riska, don haka makashin shi ne Dawuda, marigayin
shi ne Jaluta, ya tabbata haka, saboda bayyanarsa da wasalin bisa”. Cikin sauƙi za a fassara abin da
cewa: “Dawuda ya kashe Jaluta.” Bahaushe zai gane kai tsaye.
Matsayin Harshe da Al’adunsa
a Tafsiri
Daga cikin harsunan da muke da su
dubbai a zamanin Manzo (SAW) aka zaɓi Larabci aka aiko addini
da shi ta hannun Balarabe wanda ke tsakiyar birnin Larabawa masu bugun gaba da
harshensu. Cikin buwayayyen littafinmu, an nuna muna harshe wani yanki ne na
al’ada, wanda bai san al’adarsa ba, na da sauran saninsa[18]. Sanin
al’adar harshe kuwa sai wanda ya sha shi a mama, wanda duk ya sha shi a koyo ɗan
lasa ya yi ko me jin ƙwarewarsa
da ake yi[19].
Mai fashin baƙin
nassoshin Alƙur’ani
zuwa Hausa ya kiyaye da kyau ana samun kirari da karin magana da hannunka mai
sanda da bambance-bambance gajere da dogon wasali waɗanda
ke haifar da sassauyawar ma’ana. Fassara karin magana cikin karin magana zai fi
amo a karatu, haka kuma fassara al’ada cikin al’ada makusanciyarta ya fi
soyuwa. Dubi waɗannan bayanai sosai domin ƙarin bayani:
i.
Laisai khabaru kal iyaani
(Ga ni ya
kori ji.)
ii.
Yadul kaatibu amyaa’un (Tuntuɓen
alƙalami.)
iii.
Hatta yalijal jamalu fis
samil khiyaaɗ (Sai raƙumi ya shiga akurki.)
Cikin karin magana da waƙoƙin baka ake tsintuwar
daidaitattun kalmomin tsohuwar Hausa nagartacciya. A cikin buwayayyen
littafinmu wurare da yawa an yi muna hannunka mai sanda kan haɗarin
da ke cikin karin sauti da sauya harafi wajen sauya ma’anar abin maƙasudi. Ga misali:
·
A cikin Suratul Baƙara an ce, su ce: “Ƙiɗɗatun”
suka ce “Habbatun” aka zarge su da zalunci:
Idan al’ada ta ƙi kalma saboda wata ‘yar
matsalar da ta bayyana gare ta, babu laifi a guje ta ga fassarar littafi mai
tsarki.
·
Kalmar “raa’ina” ta
suratul Baƙara
ta tabbatar da haka:
Yaa
ayyuhal laziina aamanuu laa taƙuuluu
raa’ina wa ƙuuluu
inzurnaa was ma’uu wa lil kaafirrina azaabun alimun[21].
A riƙa
kulawa sosai, rashin ƙoshi
da harshen fashin baƙi
na sa a ƙosa
da tafsirin mai tafsiri.
Zaɓen
Kalmomin Fashin Baƙi
Baƙaƙe da wasula suka taru
suka yi kalma, don haka Bahaushe ke cewa, ‘Baƙi sai da wasali’. Kalmomi
sai sun yi gurguzu da ‘yan rakiya za a samun jimla mai ma’ana. Abin so ga mai
fashin baƙi
shi ne, ya tabbatar da cewa, kalmominsa sanannu ne kuma gama-gari a duniyar
Bahaushe, a kuma tabbatar da cewa ba ta kece wa al’ada da addini bante ba. Don
haka ake son mai fashin baƙi
ya nisanci:
Kalmomin
batsa.
Kalmomin
zagi.
Kalmomin
zargi.
Kalmomin
ƙabilanci.
Kalmomin
siyasar addini.
Kalmomin
izgili.
Kalmomin
katoɓara.
Kalmomin
bugun gaba.
Kalmomin
shaguɓe.
Kalmomin
rashin ladabi.
Kalmomin
tsokana.
Kalmomin
habaici mabayyana.
Kalmomin
zanga-zanga da taho-mu-gama da raddi.
Zaɓen
kalmomi wajibi ne domin littafinmu Alƙur’ani
ya karantar da mu.[22] Da
Mahaliccinmu bai tsara Alƙur’ani
cikin zaɓaɓɓun
kalmomi ba, da mun ji cike da kunnuwanmu daga maƙiyanmu. Kalmomi irinsu
Mushiriki da Kafiri da Arne da Takkwali da Shege da Ɗan’iska, da Munafuki suna
da nauyi ga al’adar Bahaushe, suna firgita shi, su hana shi tsayi ya fahimci
karatun da ake yi masa musamman idan ya gane da shi ko da su ake. Yawo da
kalmomin ba da mu ciki ba, irin su ɗan Izala, ɗan
Ɗariƙa, ɗan
Tawaye, ɗan
Gufama, ɗan
Jos, ɗan
Kaduna, Basalafe, Baƙadire,
Ba’ash’are, Bamalike, suna ɗan ƙara nisantar da mu[23]. Haɗin
kanmu a kan Alƙur’ani
da sunna tilas ne ba da yaye-yaye ba. Ban ce, a sauya wani hukunci ba, amma in
ya zama dole, mu koma ga tsohuwar Hausa da za ta ƙara haɗa
kanmu, marasa karatu su ƙara
gane karatu, to a bi, domin a sunna an ce, “Yaƙi ɗan
yaudara ne”23. Idan mai tafsiri ya iya kwanton ɓauna
a fassara babu dabbar da za ta gagare shi farautowa a ilmance. A ɗan dubi tunanina a kan
rage wa wasu kalmomi nauyi a fassara:
i.
Shirka - yi wa Allah kini/kishiya.
ii.
Mushiriki - mai hautsinawa (in ji Ɗanfodiyo) aje-aje.
iii.
Kafiri - fanɗararre/gaba
ga ƙul
yaa ayyu.
iv.
Bidi’a - yaye-yaye (in ji masu jihadi).
v.
Ɗanbidi’a
- mai yaye-yaye.
A kula, Hausawa cewa suka yi, mai laɓaɓe
ba ya ɗagar
da hannu sama. Ni dai ban ga laifin kirarin matsoraci ba, da aka ce: “Yaro kai
da uwaka uwaku”, “Ya ce: “Yadda duk ka ce, haka na ce”. Wannan shi ne tafsiri
ba mayar da raddi cikin raddi ba duk a rududduge.
Wace Hausa ce Raba
Gardama ga Mai Tafsiri?
Yanzu zan ce, su ya kawo gurbi, wato
aski ya kawo gaban goshi, ƙarshen
tika-tika-tik! Idan mai tafsiri da Hausa ya kula da waɗannan
abubuwa da muka lisafo tun da farko har ya zuwa nan ƙurewa, to, ya san Hausar
da kamata ya yi a tafsirinsa. Harshen Hausa wani harshe ne babba da Afirka babu
kamarsa sassa da yawa. Hausa na da kare-karen harshe da yawa da Hausa
daban-daban da ya kyautu mai tafsiri ya ɗan
san su irin shan rowan tsuntsaye kamar haka:
1.
Hausar Sakkwato Sakkwatanci
2.
Hausar Kano Kananci
3.
Hausar Zamfara Zamfaranci
4.
Hausar Zazzau Zazzaganci
5.
Hausar Kabi Kabanci
6.
Hausar Katsina Katsinanci
7.
Hausar Gobir Gobarci
8.
Hausar Haɗejiya
Haɗejanci
9.
Hausar Yawuri Yawuranci
10.
Hausar Arawa Arabci
11.
Hausar Gimbanawa Gibananci
12.
Hausar Gubawa Gubanci
13.
Hausar Filinge Hausar
Filinge
14.
Hausar Maraɗi
Maraɗanci
To, masu tafsirinmu sun fi ƙarfin Nijeriya domin abin
ya shiga ƙasashen
Nijar da Ghana da Benin. Don haka, a kula da daidaitacciyar Hausar da
jami’o’inmu na ƙasa
ke amfani da ita. Tarjamomin da Shehunnanmu suka yi na Alƙur’ani, da Hausar kafafen
yaɗa
labarai da ‘yan jarida ke yi, da wadda ake tsinta a rubuce-rubucen ilmi na
malamanmu na Hausa. Harshe a koyaushe bunƙasa yake da ƙara tsawo daga zamani
zuwa zamani, dole mai tafsiri ya kiyaye. Kalmomin da ba a samu cikin wani karin
harshe, ana samunsu cikin wani karin harshe, sai a je can a ara? Zaɓen
daidaitacciyar Hausa da za a yi tafsiri da ita kamar matsalar zaɓen
mazhaba ce ga ɗalibin
ilmi. Kowace mazhaba da hujjarta ta fi rinjaye, ga sahihin nassi ita ce mazhabar
ɗalibin
ilmi. Madalla da zancen Imamu Malik:
A koyaushe Hadisi ya inganta nan ne mazhabata”.
Don haka, Hausar duk da aka fi fahimta a wurin da ake
fashin baƙi
ita za a fi ba ƙarfi.
Tuni Ka Sa Marayu Kuka
Matsalar daidaitacciyar Hausa a wajen
tafsiri ba wata babba ba ce, domin marigayi Aminu Kano cewa ya yi: “Nijeriya ƙasa ɗaya
ce, amma kowa ya san gidan ubansa.” Idan har mun yarda da cewa, ‘kowane tsuntsu
kukan gidansu yake yi’ masu sauraron tafsiranku ba za su ƙosa da ku ba. Ku dubi
irin zamanin da marigayi Shaikh Nasiru Kabara da Shaikh Abubakar Gummi suka ɗauka
suna fashin baƙi;
tun cikin tsohuwar Hausa har ya zuwa yau idan an saurare su ana fahimtarsu. Shaikh
Abubakar Tureta, Basakkwce ne amma Kanawa da Zagezagi na fahimtarsa. Shaikh
Rabi’u Daura da Shaikh Jafar, Katsinawan Daura ne amma idan suna fashin baƙi babu Bahaushen da ba
zai yi na ƙadangare
ba domin ya ji an yi masa susa gurbin ƙaiƙai. Idan aka saurari
kasusuwan Shaikh Albani Zariya da Bawa Maishinkafa, za a ji babu wata matsala. Shaikh
Lawal Abubakar da Shaikh Isma’ila Idris, idan suna fashin baƙi, ka ce malaman Hausa ne
a jami’a. Shawarata ita ce, a dinga sauraron fashin baƙin marigaya a samu naƙali daga gogewarsu, mu
kuma idan mun rigaya wasu su saurare mu. Allah Ya ji ƙansu da rahamarSa.
Daidaitacciyar Hausar
Fashin Baƙi
Kowane karin harshe mai fashin baƙi ya zaɓa
za a ci karo da cewa wasu masu sauraronsa ba za su fahimce shi ba. Dole ya
kasance ya ɗan
raba ƙafa
yadda kowa zai gane manufa. Daidaitacciyar Hausar fashin baƙi ta saɓa
wa Hausar fassarar ‘yan jarida da kafafen yaɗa
labarai. Ta yi takin saƙa
da Hausar ilmi da ake gudanarwa a jami’o’i. Ba ta yi daidai da Hausar kasuwanci
ba da Hausar gama-gari. Hausa ce da ta fuskanci dabaru uku na fassara:
1.
Hausantarwa
(Transadaptation).
2.
Fashin kurman baƙi (Translation).
3.
Fassara mai ‘yanci (Free
Translation).
Waɗannan fannoni uku su ne masaƙa ga mai fashin baƙin Alƙur’ani cikin kyakkyawar
Hausa. Kalmomin da suka riga suka shiga Hausa shekaru aru-aru a bar su yadda
suke kamar kalmomin: Allah, Annabi, Mala’ika, Lauhul Mahafuzu, Alƙiyama, Hisabi, Aljanna,
Sura, Aya, Nassi, Hadisi, Matani, Isnadi, Wasiyya, Rijalu, Darasi, Fasali,
Babi, Hashiya, Tauhidi, Bidi’a, Sunnah, duk sun zama Hausantattu, a ja su haka
nan, ba matsala ba ce a ilmin fassara. A fashin baƙi matsayinsu ɗaya
da daidaiciyar Hausa.
Daidaitacciyar Hausar Tafsiri ta biyu ita ce, fashin
kurman baƙi,
wato kalmomin fannu da ke buƙatar
a baje su cikin kalmomi ga mai sauraron da ba ɗalibin
ilmi ba. Daga cikinsu akwai: Furu’a, Nisabi, Buyu’a, Mirasi, Ribaɗi,
Li’ani, Fasadi, Jazaa’i, Asibi, Haddi, Tajwidi, Li’irabi, Fidiya, Hadaya,
Ihrami, Jimra, Raja’i, Batti, Dukhuli, Aƙiiƙa, Sahur, Ifɗaari,
da ire-irensu duk suna buƙatar
a farfasa su cikin kyakkyawar Hausa.
Furu’a: Karatun sani/ibada
Nisabi: Ƙimar kuɗin
zakka
Buyuu’a: Saye da sayarwa
Mirasi: Rabon gado
Ribaɗi: Daako
Li’aani: Tsineneniya
Fasadi: Ɓarna ban ƙasa
Jazaa’i: Sakamako
Asibi: Daudu
Haddi: Zartar da doka
Tajwidi: Luguden nassi
Idan aka Hausantar da Hausantattu, aka yi fashin baƙin kurame, sai a ratsi
bayani da fassara mai ‘yanci. Ana yin haka, za a ji Hausar ta fito
tiryan-tiryan mai sauraro ya gane ma’ana nan take:
Nassi: Afa
tu’uminuuna bi ba’adil kitaabi wa takfuruuna bi ba’adi? Fa maa jazaa’u man
yaf’ala zaalika illa hizyun fil hayaatid dunyaa wa yaumal ƙiyaamati yuradduuna ilal ashaddil azaab.
Fashi: Yaya
za ku yi imani
da sashen littafi (-n Allah) ku kafirce
wa sashe? Mene ne sakamakon wanda ya aikata haka, face tozarta a rayuwar duniya a ranar ƙiyama kuwa a ɗunguza
su zuwa ga matsananciyar azaba.
Idan aka dubi wannan ɗan
ƙwazo
salailai uku da muka ambata duk sun bayyana. Kalmomi da an riga an yarda da
yadda suke an bar su haka nan, su ne aka yi rubutun tsutsa. Kuramen baƙaƙe irin su kitaabi da jazaa’u da hizyun da yuradduuna da ashaddil an yi fashinsu. Kalmomin
ba’adi da yaf’al da zaalika da hayaati da yammal da ilal, duk fassara mai ‘yanci
ta kula da su tare da ‘yan rakiyar nahawunsu kuma fassarar ba ta muzanta
nahawun ayar ba. Da duk aka kula da haka za a samu dacewa da daidaiciyar Hausa
a tafsiri.
Muhimmancin
Daidaitacciyar Hausa ga Tafsiri
Da an ce, ga harshe daidaitacce, kowa
zai yi ƙoƙari ya naƙalce shi domin a fahimce
shi. Wa ya fi kowa son a fahimce shi a duniya fiye da mai fassara littafin
Allah zuwa ga bayin Allah? Muhimman abubuwan da ya kyautu mai tafsiri ya sani
ga Hausar da yake amfani da ita su ne:
1.
Yau a Nijeriya babu
lungun da Hausawa ba su share wurin zama ba. Ga kirdado, kashi (75% - 80%) na
tafsirin azumi a Nijeriya da Hausa ake gudanar da shi. Idan Hausawan Nijeriya
za a tunkara da tafsirin dole a yi Hausa gama-gari. Mai tafsirin da Hausa ya
sani da Musulman ƙasa
gaba ɗaya yake magana.
2.
Allah Ya kai mu gaba, a
Afirka ta Yamma, tare da Sudan da Afirka ta Tsakiya (Central Africa Republic)
da Libya, tafsirin Hausawa ya kai can. Idan abu ya zama na ƙasa da ƙasa (International)
muhimmin abu ne, dole a ba shi muhimmanci ta harshen da ake isar da shi. Idan
aka gurɓata Hausa da kalma
ɗaya, yana sa ma’ana ta
salwance wa mai sauraro. Ɗauki
misalin sunan bisa/sa/raƙumi
da Musulmi ke haɗa
kuɗi a yanka a daren sallar
Azumi Hausawa na ce da shi “tonton”
ko “tittirga”
ko “rarraba”
ko “watanda”,
dole mai tafsiri ya tsaya ya yi bayani sosai a nan.
3.
Ka da a manta yau ana
sauraron Tafsiri a rediyo da Talabijin da fayafan garmaho da hanyoyin sadarwa
na duniya. Mai tafsiri da Hausa a yau, duk duniya na ganinsa tana sauraronsa.
Idan ya doge ga Hausar unguwarsu ko garinsu ko yankinsu ko ƙasarsu, bai ribantar da
masu sauraronsa a duniya ba. Da ‘yan BBC da ƁOA
da RFI da Wisal TƁ
sun doge da karin harshe ɗaya
za su samu masu sauraro? To ina suka kai mai tafsiri farin jini da yawan masu
sauraro da natsuwa?
4.
Idan Hausar tafsiri ta
kasance cikin karin harshe ɗaya
masu more mata kaɗan
ne. Idan kalmominta suka yi nauyi an takura masu sauraro. Idan ta kasance
salala babu daɗi da nagartattun
kalmomi, sai ta kashe wa masu sauraro jiki, sai su kasance wasu barci, wasu
hira, wasu shagaltuwa da wasu ayyuka na dabam. Kulawa da adabi cikin fassara
muhimmin abu ne domin adabi kunne ya girmi kaka ne kuma ma’anarsa gama-gari ce.
Sakamakon Bincike
Harshen
Hausa ya yi kimanin shekaru dubu ana fafitikar yaɗa
addinin Musulunci da shi a duniyar Afirka. Abubuwan da suka yi masa tarnaƙi a da, yanzu sun kawa.
Samun rubutun ajami da rubutun boko da kafafen yaɗa
labarai ba ‘yar ƙaramar
gudunmuwa suka yi wa fashin baƙi
Alƙur’ani
zuwa Hausa ba. Tarjamar ma’anonin Alƙur’ani
zuwa Hausa na Shaikh Abubakar Mahmud Gummi ita ce makarantar farko ta masu
tafsiri da Hausa, kowa ya zo da baya kafaɗarsa
ya dafa. Kasancewar Shaikh Gummi ya tsaftace Hausar tarjama sosai, duk wani abu
da muka ambata a nan, tarjamarsa ta kiyaye da shi, za a ga hatta da waɗanda
ke takin saƙa
da shi, suna amfani da tarjamarsa. To, haka ake fatar tafsirinmu na azumi ya
kasance a koyaushe, ba safe duk sai an roƙi mutane su dawo gobe ba.
Da an ci nasarar taskace karatun Hadissan da Malam ya yi a rubuce kamar yadda
tarjama take da mun samu ƙarin
malamai Hadisi a Afirka.
Naɗewa
Masana
furu’a sun ce: Abin da duk farilla ba ta tsayuwa sai da shi to ya zama farilla.
Duk wani malamin zaure da mai wa’azi ƙasar
Hausa da Hausa aka karantar da shi, da Hausa yake koyarwa. Na yi madalla da
ganin an nemi a yi wannan taro domin inganta harshen masu wa’azi da tafsiri.
Wanda duk aka bari baya ga harshe an bar shi baya ga karatu da karantarwa.
Harshe shi ne makamin yaɗa kowane irin addini.
MANAZARTA
Gummi, A. M. Alƙur’ani Mai Girma Da Kuma
Tarjamar Ma’anoninsa Zuwa Ga Harshen Hausa.
Bunza, A. M., Ibrahim, S. S. da
Usman, B. B. 2007. Daular Sakkwato (Fassarar
Sokoto Caliphate Na Murray Last). Lagos: IBRASH Islamic Publishin House.
Omar, S. 2017. Malamai Mata A
Daular Usmaniyya A Ƙarni Na 19 Da Na 20. Zaria: Ahmadu Bello University
Press Ltd.
Ɗanfodiyo,
U. bn. Wasiƙatul Ikhwani.
Ɗanfodiyo,
U. bn. Nurul Albab.
Ɗanfodiyo,
U. bn. Bayani Bid’is Shaiɗaniyya.
Bunza, A. M. 2017. Dabarun Bincike
A Nazarin Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa (Supported by Tetfund). Zaria:
Ahmadu Bello University Press Ltd.
_____ Littafi Mai Tsarki Dud Da AFOKIRIFA.
Lagos: The Bible Society of Nigeria.
Sa’id, B. 1973. “Gudunmuwar Masu
Jihadi Kan Afabin Hausa” kundin digiri na biyu (MA Hausa). Kano: Jami’ar
Bayero.
Bunza, A. M. da Birnin Tudu, S. Y. 2017. “Grammatical Rift and Cultural
Lacuna: Constraints on English-Hausa and Hausa-English Translation” in Journal of Capital Deɓelopmetn in Behaɓioural
Sciences, Ɓol. 5, Issue 2.
[1] Musulmin farko hijirarsa ta farko, a
Habasha suka zo cikin Afirka, hanyar Masar zuwa Habasha da Indiya daɗaɗɗiya ce da Hausa suka sani tun farkon Musulunci. A can
da nan mahajjata Hausawa ke bi. Don haka ne ake da tabbacin samun Hausa shekaru
aru-aru a Indiya. Don ƙarin
bayani a dubi littafin Sa’adiyya Omar, Mibbo Kilo wallafar ABU, Press.
[2] Musulmin farko hijirarsa ta farko, a
Habasha suka zo cikin Afirka, hanyar Masar zuwa Habasha da Indiya daɗaɗɗiya ce da Hausa suka sani tun farkon Musulunci. A can
da nan mahajjata Hausawa ke bi. Don haka ne ake da tabbacin samun Hausa shekaru
aru-aru a Indiya. Don ƙarin
bayani a dubi littafin Sa’adiyya Omar, Mibbo Kilo wallafar ABU, Press.
[3] Babu tabbacin hanya ɗaya
da addinin Musulunci ya shigo ƙasar
Hausa. Akwai hasashen da ya shigo Masar daga can Borno ta same shi sai Kano. A
wani hasashe Wangarawa 400 suka shigo da shi ta Kano. A wata majiya, ɗaiɗaikun
Buzayen da suka karɓo shi daga Saharar da Amir bn Al-As ya zo
da shi.
[4] Wannan aƙidar ta sa an daɗe
ba a samu fitattun masu tafsiri ƙasar
Hausa ba. A karatun littattafan addini Iziyya, Risala, Askari, Lawwali idan an ci karo da aya a kan ce a gewaye
ta a tsallake. Haka aka ci gaba har Allah Ya kawo mafasa baƙi.
[5] Ana karanta Ashafa domin sanin tarihin fiyayye Annabi
Muhammadu (SAW). Alburda
da Ishiriniyya su suka haifar da waƙe-waƙen
yabon Manzo (SAW) cikin harshen Hausa.
[6] ‘Yandoto ta daɗe
da tarihin Musulunci. Akwai hasashen tun zamanin tabi’ai Musulunci yake a ‘Yandoto.
An ce a nan ne wani jikan Sayyidina Aliyu ya ƙaura. Wannan tarihi fitacce ne ga masu Ƙadiriyya. Malam Jibril shi ya fara yunƙurin jihadi a ƙarni na 18 (ƙn.
18), da bai ci nasara na, Ɗanfodiyo
ya yi a ƙarni na 19 (ƙn. 19).
[7] Har gobe mutumin Arewa na mamaki a ga
Bahaushe a kuma ce ba Musulmi ba ne. Wannan ita ce ta sa Hausawa Maguzawa, sun
zaɓi zama a Maguzance da yin wani addini ba Musulunci ba.
[8] A duniyar baƙar fata Bahaushe ya fi kowace ƙabila bazuwa a ciki. Harshen Hausa babu nahiya daga
cikin nahiyoyin duniya da bai shiga ba.
[11] A yau Shaikh Jafar Adam na da shekara 11
da rasuwa. An kashe shi ranar Jumu’a yana limancin sallar asuba.
[12] Ku tambayi ma’abota ilmi ga abin da ba ku
sani ba Sura ta… aya ta…
[13] Na halicce ku daga namiji da mace, kuma
na sanya ku dangogi da ƙabila
(harshe) domin ku san juna sura ta… aya ta…
[14] A duba sura ta 2 aya ta…
[15] A dubi aya ta… sura ta…
[17] Sura ta… aya ta…
[18] A wajen manyan masanan falsafa wanda ya
koyi harshen da ba nasa ba, har ya kai matsayin Farfesa, sanin harshensa daidai
yake da ɗan shekara 7 da ya sha shi a nono.
[20] Sura ta 2 aya ta…
[22] Shaikh Albani ya tsawatar ƙwarai a kan haka a cikin muƙaddamar littafinsa Sifatis Satatin Nabiyu (SAW).
[23] Alharbu hidi’atuu.
The Ticonderoga Hotel and Casino - Tucson, AZ - T-T-Tite
ReplyDeleteWith an titanium bike impressive 2,500 square feet of gaming floor, The Ticonderoga Hotel titanium solvent trap and Casino is the apple watch stainless steel vs titanium perfect venue for those who never settle titanium price per ounce for less used ford escape titanium than