An tsara waƙar a tsarin ‘yar tagwai. Babban amsa amonta “wa”. An
tsara ta cikin baitoci saba’in da tara (79). An kammala ta ranar Jmu’a
25/1/2013 a Sakkwato. Addu’a ce da godiya ga Allah ga irin taimakonSa ga
bayinSa ga tsallake tarkon miyagun abokan zaman zamani. Godiya ga Allah wajibi
ne ga kowane bawa, bale wanda Allah Ya kuɓutar da shi ga
tarkon makircin abokan ƙarshen zamani “kifi ku ci ‘yan’uwanku”. Allah Ya yi muna
tsari da tsarinSa. Amin!
-----------------------------
Aliyu Muhammad
Bunza
------------------------------
1. Ya Ahadun ya
Samadun ya Kaafi babba,
Ya Witirun Wahidun tilo ga misaltarwa.
2. Ya Alqahhaaru
ka buwaya ga mulkinKa,
Masu ganin sun buwaya su Kaka karyawa.
3. Ya Kaafi Ka
wadaci duk wani bawanKa,
In Ka ce: “Kun” Yakuunu xai za shi
zamowa.
4. Ya masani
al’amar na fai had da na voye,
Ya masani ko’ina
da babu musuntawa.
5. Ya mai ilmin
sanin qiraza da zukata,
Ka san kominsu tun gabanin furtawa.
6. Ya mai ilmin da
masu ilmi ka bixowa,
Kai ne nassi gare ka sharhi ka fitowa
7. Ya mai xaga
arzuka na bayi darajarsu,
Kai ka buwayar da mai buwaya ga
karawa.
8. Ya mai xaga
martabar quje kan giwaye,
Ko so, ko qi, da ya faxa, ba a musawa.
9. Ya mai raba
arzukan da ba mai qwacewa,
Kowa ka hana, aradu ya gama tavewa.
10. Ya mai xaga xa
cikin xiya ya zamo babba,
Yai rinjaye a kan xiyan da ka xasawa.
11. Ya ma’ishi gun
waxanda an ka ci haqqinsu,
Ka iya qwato shi ko ina aka voyewa.
12. Ya mai sakayya
kan butulcin makusanta,
Na shaidi hakan ga, na gani, sai
godewa.
13. Ya mai sa
qaiqayi ya koma ga masheqi,
Duk qwazon kakkavansa bai hana sosawa.
14. Ya mai rikitar
da makiri ga muradinsa,
Qarshen tarkonsa shi haqon zai kamawa.
15. Ya matsarin
wanda ba a so ba a qauna,
An sha sara da sassaqa ya qi macewa.
16. Ya matsarin
wanda an ka so ya yi ma savo,
Kak qaddartai da bin umurni na hanawa,
17. Ya matsarin
wanda ba a son a ji muryarsa,
Kai masa gangar maqogoro mai burgewa.
18. Ya mai son
wanda ba a son a ga ya rayu,
Masu buqatar su kau da shi na ta
macewa.
19. Ya mai
qaddarta masu giba ruxewa,
Geronsu yana batun tumu suka girbewa.
20. Ya mai dabirta
tsegumin mai qyashewa,
Yau ta hau kansa shi ake labartawa.
21. Ya mai saka wa
kowane da xabi’arsa,
Ni na shaida haqiqatan ga amincewa.
22. Ya mai bin
kowane mutum da xabi’arsa,
Kul-ba-daxe masu hanquri na ganewa.
23. Ya mahani
yaudara da cin fuskar sabo,
Kowa yac ce ya yi su bai ko morewa.
24. Ya mai saka wa
masu sakayyar cuta,
Ran da macuci ya cutu an gama cutarwa.
25. Ya masanin
masu sunsuno abu munana,
Mugun shaqensu duk hana musu fesawa.
26. Ya mai saka wa
masu yi bisa niyyarsu,
Shi ko mai tsegumi ka bar shi ga
tavewa.
27. Ya masanin
yanzu, xazu ka san shi dukansa,
Ka san jiya gobe ban da ku wa ka
gayawa.
28. Ya masanin
cutukan jiki har na qiraza,
Ba wani ciwon da zai buwai Ka ga
warkarwa.
29. Ya wanda ya
fid da Musa tarko matsananci,
Ga ‘yan-sai-mun-gani ruwa na nocewa.
30. Ya wanda ya
qaddaro Yunusa shiga kogi,
Kifi ya haxe shi yaf fito ba cutarwa.
31. Ya hasken nan
da ba duhun da ka kutsawa,
Wa tafin xan Adam ya ce zai karewa.
32. Ya farkon nan
da bai da farkon farawa,
Ya qarshen nan da bai da qarshen
qarewa.
33. Ya wanda ya yo
sama’u kana ya yo qassai,
Yay yo rana wata fitillun haskawa.
34. Ya wanda ya
qaddaro duhu yai taurari,
Don jefe shaixannun da ke linqayowa.
35. Ya kai
makashin mazan da ke karya mazaje,
Ka dai sha maqure maza sai shurewa.
36. Ya Sarkin
alqawal da ba ya tadawa,
Muddin ka yarda an gama ba fasawa.
37. Ya masanin
yaudarar ido balle baki,
Qwazon ‘yan jita-jita bai kai ga
cikawa.
38. Ya kai mai
zamani da sassauya lamurra,
Duk mai ilmin saninka shi zai ganewa.
39. Ya kai mai mai
da xan sarauta xan wasa,
Ai ta kashe mai kixi yana tattakawa.
40. Ya Faradun ya
Ahadun ya kai mabuwayi,
Ya kai Samadun Aliyu na son furtawa.
41. Nai ladabi nai
zaman biyayya ga abin ga
Amma koyaushe ni
kaxai aka kushewa.
42. Tun abu na can
duqunce har yaz zama buxe,
Duk sharrukan da an yo ban ramawa.
43. Lallai kan an
shigo ni an ci ni da zamba,
Hulxa duka kissa ce kaman ban ganewa.
44. Nay yi shiruna
ana bugu ban rama ba,
Har dai an xebe xammahan ban miqewa.
45. Ai qazafi, ai
tsince, an yi ashar sosai,
An yi ta giba da arashi babu ragawa.
46. An nuna, ai tsaki
an sha yin zunxe,
An sa ni cikin sahu ana muzantawa.
47. An tara dubu
gaban abokai an zagan,
Har a gaba na a takaran ban ramawa.
48. An leqa qauye
an ci sunana sosai,
Duk alqaryarmu ban da inuwar hutawa.
49. An dai gama
cin ido da yin yankan qauna,
Ga cin zarafin da mumini bai yafewa.
50. Wallahi irin
tu’annutin na qiyayya ne,
Cin zuququn muqarrabi babu ragawa.
51. Makirci ne da
zamba cutar kushewa,
Babbar fatar su in kalamin riddewa.
52. Tilas ne
godiya gare Ka ma ji roqo,
Kan nasarar nan da nag gani mai
xorewa.
53. Tun ba mu mace
ba gaskiya tai aikinta,
Qarya ko sai idanuwa taka zarewa.
54. Wayyo! Kaina
Alu Ilaahu ka saka min,
Can ranar nan da Alqiyama ka tsayawa.
55. Nai maka
shukura haqiqatan ka ceta min,
Ka sa na xauki hanquri bisa cutarwa.
56. Wai ko anya
akwai basira ga macuci?
Bayan ceto shi, shi ya ce zai cutarwa.
57. In har ga
hankali idanu mudu ne,
In ba shuka ina tumu za ya fitowa?
58. Na yarda da
Walga Bunza mai waqar Tashe,
Ya ce: “Qarshen ruwa Kware suka
komawa”.
59. Zaki ya ce:
“Mutum abin mamaki ne”,
Mai mamakin halinsa ya gaza ganewa.
60. Shi zai zarge
ka ko’ina zai vata ka,
In kun haxu hanya sallama zai farawa.
61. Bayan ya
nakkasa ka ya ci mutuncinka,
Zai bixi gyaran zama na baya ga
wallewa.
62. Wai wanda ka
ba wurin zama don shi yi kauje,
Shi zai jifa da shimfixarka ta
kwantawa.
63. Assha! Ustazu
wanga aikin bidi’a ne,
Qin girmama wanda ya’ aza ka ga
ganewa.
64. Don ka hau
gwangwala shaqiyyai na tavi,
Sai ka yi doro ka mance ranar saukewa?
65. Ko mun so, ko
a yarda, ko an kafirce,
Xan gaba na can gaban na baya ga
qyargawa.
66. Tambayi ragon
gidanku shaida wa Naturke,
Kunnensa yana gani qaho ke tserewa.
67. Don haka ban
rama cin mutunci da qazuffa,
Na bar su wajen Ilaahu can mai sakawa.
68. Sharri yaron
da babu qiuya ba naki,
In an aikai zama guda yaka dawowa.
69. Malam kai kak
kira shi, kab ba shi takarda,
Ya dawo ma da ambulon ka qi karvawa.
70. Kura na san
baqin jininki halitta ne,
Had dai ga mahasada macuta na qurewa.
71. Zomo wayonsa
fil azal na halitta ne,
Hatta barci yake idon ba su rufewa.
72. Shata yai
gargaxi ga taron mamugunta,
Ya ce: “Su yi hattara abin na juyowa”.
73. Ranar da ya
birkito ka san ba ka da kaico!
Domin shukar da kay yi ce kaka
girbewa.
74. Wauta ce
zahirinta illanta mutane,
Ita ce illarka in kana mai ganewa.
75. Babu musibar
da taf fi cutar da mutane,
Bayyana laifinsu ko’ina kaka zannawa.
76. Yadda ka hango
halin waxansu ka kushe su,
Kai ma haka naka wansu ke daxa
kushewa.
77. Ya Allah ya
Wahaabu ceto nika roqo,
Ga ni cikin bunguli ruwa na marawa.
78. Masu jirage
abara me kuka dubu na?
Kowammu da ya ga dorina sai zuqewa.
79. Sunana Ali xan
Muhammadu xan Bunza,
Birninmu na Shehu Jami’a nika
koyarwa.
Aliyu Muhammadu
Bunza
Jumu’a 25 ga
Junairu 2013
Sakkwato
No comments:
Post a Comment