Thursday, December 27, 2018

Malammai




1.                 Ni kiri Rabbana Jalla mai iko sarkin sarauta duka,
Sarkin nan da yay yo dare rana sammai da ƙassai duka,
Wanda Ya ƙaddaro rayuwa mutuwa ikonSa ce Maiduka,
Ba makawa ga bayi kiranKa buwayayye gwanin ɗaukaka,
          Mai ilmin da ya kewaye komai da saninSa yat tabbata.

2.       Nasa sani gwani fil azal yake komai ba ya ɓoye Masa,
          Babu kure bale mantuwa wane wahami ya riskan masa,
Shi yat tsara kaiNai da ilmiNai haka mun ka iske masa,
Ba ma shisshigin binciken ilminKa da istiwa’i bisa,
  Ɗan ilminmu bai kai ba, in mun ce mu yi, nan yake barkata.

3.       Don haka mumini ba ya ɗanga ba ya bugun gaban ya sani,
Taka sannu Modibbo, hayya da cewa: “wane mi yas sani”,
Allah Ya faɗa ba sani tari a cikinmu sai ƙanƙani,
Wanda ka taƙaman ya iya ƙarshe sai ya yi da na sani,
  Bil’amu yak karantar da mu masani duka bai wuce karkata.



---------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
-------------------------------

1.                 Ni kiri Rabbana Jalla mai iko sarkin sarauta duka,
Sarkin nan da yay yo dare rana sammai da ƙassai duka,
Wanda Ya ƙaddaro rayuwa mutuwa ikonSa ce Maiduka,
Ba makawa ga bayi kiranKa buwayayye gwanin ɗaukaka,
          Mai ilmin da ya kewaye komai da saninSa yat tabbata.

2.       Nasa sani gwani fil azal yake komai ba ya ɓoye Masa,
          Babu kure bale mantuwa wane wahami ya riskan masa,
Shi yat tsara kaiNai da ilmiNai haka mun ka iske masa,
Ba ma shisshigin binciken ilminKa da istiwa’i bisa,
  Ɗan ilminmu bai kai ba, in mun ce mu yi, nan yake barkata.

3.       Don haka mumini ba ya ɗanga ba ya bugun gaban ya sani,
Taka sannu Modibbo, hayya da cewa: “wane mi yas sani”,
Allah Ya faɗa ba sani tari a cikinmu sai ƙanƙani,
Wanda ka taƙaman ya iya ƙarshe sai ya yi da na sani,
  Bil’amu yak karantar da mu masani duka bai wuce karkata.

4.       Don haka masu gori da imani sai su yi hattara sun jiya,
Shirya na ga Allah, ɓata Shaiɗan ka iza ka ko ƙiya,
Nemi tsari wajen Rabbana manta da bugun gaban na iya,
Bawa bai da ƙarfi wajen shiriyarsa a daina yin fariya,
  Babu gwani ga shaiɗan daɗai zuciya sha’awa yake sa mata.

5.       Mai neman sani don ya tara kuɗi bai san da sirrinsa ba,
Mai neman sa domin ya burge bai amfana samun sa ba,
Mai neman sa domin ya kushe waninsa ba zai muruwasa ba,
Amfani da shi don a gyara miya a yi ƙulƙule bai yi ba,
    Ya zama ci-da-ceto da son girma taƙawa a cuta mata.

6.       Yin ƙarya da shi don a san girman ƙarshensa yin raraka,
Ƙin tashi biɗa don ganin ka tara sani ka cuta maka,
Amfani da shi don a kutsa fada a samu tsabar daka,
Sa rawanin sani don ka ja tawagar jama’a su mara maka,
          Ba a taɓa yi a more ba, tambola ce kar ka faɗa mata.

7.       Muddin zuciya na karanto ma ilminka ya gunguma,
Ka ɗaure gafakka karatu ta ce, ka riga ka gama,
Ta jefa ka tarkon husuma ka zan mallamin gardama,
Kwa’ iya fassara duniya sai ka yo taka ‘yar tarjama,
     Duk fatawar da ba taka ce ba, a dole ka ce a saɓa mata.

8.       Kar ka hukunta wai ɗalibinka ba zai taso ya furce ka ba,
Ko fanni kaza, wane ba ya faɗi ban goge ƙaulinsa ba,
Ni da na yo karatu Masar lugga ba a kai ni gane ta,
Balle ni da nay yo Madina hadisai ban yi ƙamfar su ba,
          An koma kirari, shari’a tun tuni an ka saɓa mata.

9.       Masu biɗan sani don a sa su sahun masana ka sheda masu,
Shi ke mai da Uttazu gojirgo goga kwamandan musu,
Sai raba kan musulmi su lalace maƙiya su, auka musu,
To don ka zamo mallami da wace sunna ka ceta musu,
          Tauhidi ya koma sana’a, Tafsiri ya koma shata.

10.     Girman kai ka rushe sani Malam saurari ɗan nan kira,
Mai jin kai karatunsa bai tasiri duniya lahira,
Mai kurin tsananta wa bayi Shaiɗan na ganinai sara,
Malaman ga su ukku kowane na fama da ciwon mura,
          Ƙirji ya rufe babu numfashi sun kasa gane mata.

11.     Malam mai farautar kurakurran takwara ya auka masa,
Duk ilmin ya koma na cin zarafi da tu’annuti fallasa,
Ƙarshen duniya ga sani tari amma ya zan nakkasa,
Ga ni’ima ta Allah tana sauka an kasa gode Masa,
          In aka sallaɗo ‘yar azaba sai a tarar da mun jikkita.

12.     Ban tausai ga Malam idan Shaiɗan ya sa shi ɓoye sani,
Wai shi kar a gane karatu, kowa kar a ce, ya sani,
Kai ku ji ɗanga-ɗanga, a sa ka cikin haraka, ta zan ɗan zani,
Hasken Rabbana ne, ka dubi fitan rana ga tsarin yini,
   Wa ka hana ta leƙo gidna wani, in haskenta ya karkata?

13.     Cewa na fi kowa sanin abu, kun ji musabbabin hasada,
Ran da waninka yay yo fice ƙirjinka ya kwana ƙugin ciɗa,
Babu zama, tsayi, ka ji an ce, Malam wane ne kan gada,
Wai kai ba ka yarda a san wani, don kai an ka shaida a da,
          Ilmi bai da Malam da zai cewa, a wurinsa zai tabbata.

14.     Ilmin rena ilmi musiba ne abu sai ya koma faɗa,
Don an fi ka aiki da sunna kullun tsegumi sai raɗa,
Ka ga ana fahimtar samarin ilmi, sai ka kushe daɗa,
Ga nassi a kulkin hadisi kai ko sai ka sa tambaɗa,
          Wai kai dole sai an ishe ka gida fatawa take tabbata.

15.     Mai da fagen karatu sarauta shi ke kawo ka-ce-na-ce,
Sannu abin ya koma na fadanci sunna ya zan ta ɓace,
Sai hasken karatu ya lalace a wurin biɗan zaƙƙace,
Yarjejeniyar kai ga samu nan taƙawarmu duk taɓ ɓace,
          In da kwaɗai ya zauna zukata, sunna dole kauce mata.

16.     Alfaharin yawan ɗalibai da magoya baya ya zan ba’a,
Ko wata ƙungiya ko ɗariƙa, yau mun furce wannan sa’a,
Duk mu haɗe a sunna wuri ɗaya shi ya fi kyau mu zan addu’a,
Watsetwarmu ɗaiɗai haƙiƙa alama ce ta ƙarshen sa’a,
  Ka da mu bari ƙiyama ta cin muna rarrabe ce kakai kwarkwarta.

17.   Ce-mini-ce-minin malami, ke sa mabiya su watse masa,
Ƙorafe-ƙorafen ɗalibai ke sa malam a rena masa,
Ƙyashi ke kashe malami ɗalibbainai su watse masa,
Mai da wurin karatu dabar tsince abu ya zamo kwarkwasa,
          Sai taƙawa ta ƙare ga baki gaɓɓai sun ƙarba mata.

18.     Malam mai kwatancin karatunai da ma’ilmatan duniya,
Mai sukan Salaf don ganin mabiyanai na faɗan ya iya,
In ga hankali, wanda anka yi yau, bai rena aikin jiya,
Albarka ga ƙarnin gabaci, nassi yaf faɗai, mun jiya,
          Duk rigima ta sukan gabaci, sharri ce a kauce mata.

19.     Ilmi ba azanci ba ne, makarinsa a je a bauta masa,
Wayo bai karatu a je makaranta can a iske masa,
Babu salo wajen gane nassi sai an hau shi an imasa,
Wanda ya san sahihin karatu burga ba ta ruɗi nasa,
          Duk nahawun da’ifin bayani bai ruɗa shi bai firgita.

20.     Ilmi bai buƙatar shahadar kwali tambayo maluma,
Don taƙawa da ilmi gidansu guda ba sa zaman gardama,
Amfanin karatu khushu’i tsoron Rabbana mai sama,
Dole a yarda sunna ta zan jagora idan ana tarjama,
   Duk hidimar ibadar da taw wuce sunna ta zamo barkata.

21.     Ba a kiran ɓatacce da tsauri ko ya kangare ya ƙi ji,
          Sa hikima a kai, ba shi girma, Mallam ko a ce Alhaji,
Lallashi a kai har ya ankara don ya tsaya cikin masu ji,
In aka tsaurara mai ya kafurce, an sa shi mugun aji,
          Laifi na ga Uttazu shi da ya darkako shi yaf firgita.

22.     Yaushe sani ya koma asusun yin giba da yin takara,
Ɗalibban sani ba haɗin kai, an shiga ukku an takura,
Wanga ya warware, wanga na tunƙa, mabiya tara in tara,
Ko Shaiɗan idan zai yi adalci ya san akwai yaudara,
   Mai da’awa ya dabirta masu biyansa su zan cikin ƙuntata.

23.     Yaushe sani ya koma dabarar ba mu kuɗi mu gyara maka?
Masu kaba’ira su da ɗaguttai sun ba ka, ka sa baka,
Kullum ba a nan, ba a can, baki sake dole kaɗa maka,
Fassiƙƙai suna isgili, “Uttazawa mazan raraka”,
          Ƙasumbar bara ba ta sunna ce ba, ku je ku yo binkita.

24.     Malammai na sunna ƙazanta ba su bari ta riskar musu,
Ba a kwaso ƙarmamuwa a ishe su gida a miƙa musu,
Kutsawa cikin ‘yan kashe-mu-raba na sa a rena musu,
Yau su faɗa a ce, ba a yi, fatawarsu gaban su za ai musu,
          Ƙarshen lokaci al’amurra ne sun soma yin jirkita.

25.     Cewa mallami bai shiga wuta, zance ne a kan kuskure,
Me ka hanawa mallam shiga Lazza in ya ƙi gyaran kure?
Ilmi ba ya ceto ga mai gangancin isgilin kuskure,
Dole hawan siraɗi ayukkan kowa Rabbana zai ƙure,
   Wanda ya je da shirka Jahannama za a kira a miƙa mata.

26.     Rena sani da kushe ma’ilmanta ba a saba more shi ba,
Yin ƙazafi, jafa’i ga mallammai a yi hattara ‘yan daba!
Muzantar da ilmi da muminnai ba a saba ƙyale shi ba,
Ƙarshen isgili nakkasa da bala’i babu kyaun aƙiba,
    Nuhu da an ka wa shi ruwa aka sa suka mai da arna gata.

27.     Mai da sani makami na cin zarafin wasu ba dabara ba ce,
Mai da fashin baƙi zage-zage haƙiƙan hankali ya ɓace,
Sa mabiya ƙiyayya da yaƙi ba shiriya ta sunna ba ce,
Shi ke sa matasa ta’addanci don hankali ya ɓace,
   An ka mayar da su cefanen shehunnai ka ji babbar ɓata.

28.     Kaicon malamai masu raya ta’addanci cikin al’umma,
A yi huɗuba muridai su gigice su husata sai ɗunguma,
Kan ƙaramar fahinta maras tushe ƙura ta musƙe sama,
A yi gayyar muridai a ba su makamai don kashe maluma,
   An yi Kano da Zazzau da Sakkwato ba a gudu a tsere mata

29.     In Ustazu yag gane cin banza taƙawa ka kubce masa,
Ba ya mutunta sunna wajen ɗagutu idan ana ‘yanmasa,
Shi ake tuntuɓa don a buɗe wuta ga waɗanda ke ja masa,
Ai ta kashe musulmi da hannunai Uttazu an nakkasa,
   Ƙarshen ƙaiƙayi masu shiƙa za ya laƙe kamar kwarkwata.

30.     Son a sani ka sa mallami limancin masu cuta muna,
Kun raba kanmu kun sa ido sojoji na ta cuta muna,
Kun koma gidajenku in an kanmuna ba ku ceta muna,
Yanzu ƙiri-ƙiri za a bin mu ana yanka kamar raguna,
   Masu kashinmu sun ba ku jinga kun maishe mu motar shata.

31.     Mugun mallami bai da kunya bai tausai wajen danfara,
Bai shakka wajen cin amana bai ƙyama ga yin yaudara,
Muddin ya fasa ya ga masƙi ko Shaiɗan yana gagara,
Sun yi yawa ƙasashenmu shi yas sa shari’armu tag faskara,
          Ga su cikinmu kullum dasisa al’amarinmu na karkata.

32.     Shehu Mujaddadi ya kira su uban falale cikin ƙorama,
Ka ga ƙadangare in ya hau tulu kama shi sai an ƙwama,
In an ɗauko sanda, a ce a buge, biyu babu ce an gama,
In an bar shi, su ko ruwan tulu sun ɓaci, ba gardama,
     Kun ji baƙar musibar zama da miyagun malamai kwarkwata.

33.     Yaya za a gane su? Farko sun fi kare kwaɗai awwalan,
Rowa ko Juhaa, ka ji babbar siffa nan riƙe saniyan,
Son banza, afafa, kamar a yi sata, da’iman salisan,
Son daɗi a hole ana ta bushaha khaliyan rabi’un,
          Muddin sun ga samu aje sunna suka yi su saɓa mata.

34.     Komi an ka shirya da su, in dai ba su ɗau rabo babba ba,
Saurara da kyau, ba a ƙarewa ba su fara sukar sa ba,
Muddin kag ga sun kame baki to ba su gane sirrinsa ba,
Ba shi haɗe kwaɗai, ba shi jin kunya, in bai ga ƙunshinsa ba,
   Bai ƙoshi wajen ka da girma sai mabiyansa ke kunyata.

35.     Yau haka zamani yak kasance ga gaba baya ta nakkasa,
Masu kira a so Rabbana su za su taho su saɓa masa,
Su ke taimakon fajiri mai imani su cuta masa,
Ba su shiri da mai gargaɗar ɗagutu ya sa a saɓa masa,
     Sun fi da son walankeluwa maganar sunna a saɓa mata.

36.     Wai yau malamai had da ‘yan banga harakar ga ta hurhura,
A yi kuwwa ana kabbarori kan mallam yana kumbura,
Sai ai mai kirari ya hau karagar wa’azi yana banƙara,
Ga ɗan agaji baya ga alaramma a hau ana tunzura,
          Ba zancen tawali’u, ko taƙawa an fara kauce mata.

37.     Bar-ni-da-mugu in yai ruwa aka matse ɓata fuska yaki,
Maruru ga dattijo ba ya faɗin gehen da shegen yake,
Ita ƙazuwa bala’in ta ƙaiƙai susa har cikin mummuƙe,
Kun ji rutsin da Nijeriya taj jefa Arewa duk mun suƙe,
   Barno, Kano, ƙasar Yobe, Bauchi, Abuja yanzu sun jirkita.

38.     Malamman da ke agajin maƙiya ba za mu ƙyale su ba,
Cin zarafi ƙazuffa da ɓannan suna ban mu yafe su ba,
Bambancin fahimta ba zai zama hujja keta haddinmu ba,
Yanzu a ce musulmi ƙasarsa ba zai kare aƙidarsa ba,
          Dole aje aƙida nagartatta ɓanna a auka mata.

39.     Ga mu muna tumulli da jahilci malam ya ƙara muna,
Babu ƙawa ta gemu na sunna yau rawani kamar an hana,
An hana tsangaya ba karatun zaure ba batun alluna,
An harbe matasanmu an bar tsofaffi cikin ɗakuna,
          Ba mai ta da murya a ba maganarsa gari a duba mata.

40.     Mun san lokaci ya taho ƙarshe wada anka sheda muna,
Komiɓ ɓaci gyaransa na da wuya haka anka nuna muna,
Domin masu gyaran da su aka ɓata abin da yan munana,
Tun da haki ya cinye awaki yuƙa tah haɗe raguna,
          Jahillai su ja jahilai shara’a tilas a cuta mata.

41.     Roƙona Ta’ala Ya gafarce ni da ni da ku maluma,
Ba shakka musibun ga yau kowa ya shaidi sun gunguma,
Ni dai shawata mu tuba gaba ɗai ba batun gardama,
Ali na Bunza na Sallama Mallam Uttazu sai an jima,
    Rabbu Ya ba mu Ikon riƙon sunna bidi’a mu kauce mata.


Aliyu M. Bunza
Umaru Musa Yaradua University, Katsina 1:50pm
5/08/2014/ Tuesday

1 comment:

  1. But have the ability to|you probably can} play for actual cash straight from your cell browser at one of the best cell casinos online. Pick from our top actual cash casino recommendations above and begin having enjoyable. ✅DraftKings Sportsbook Illinois officially launches, in partnership with Casino Queen.🗓June 2020✅Gov. Previous analysis concludes that cell gamblers are at increased threat of growing harmful gambling habits in comparison to|compared to} land-based and different non-mobile gambling 1xbet types .

    ReplyDelete