1.
Mu gode Allah ɗaya mai komai
Da yay
yi komai a lokacinai,
Yay yi
hukunci bisa yardaTai,
Ga lokaci wa ka karkare shi?.
2.
Bisa yardaTai
ya ƙago bayi,
Ga ƙassai ga sama’u
Ya yi,
Da
fasullan shekara da yay yi,
Na lokaci ba a gurgasa shi.
3.
Shi dai waƙaci a kiyaye
shi,
In ya zo
ba a tunkuɗe shi,
Mai iƙirarin ya
gurgusa shi,
Kar ku yi shakka ga ƙaryata shi.
---------------------------
Aliyu
Muhammad Bunza
-------------------------------
1.
Mu gode Allah ɗaya mai komai
Da yay
yi komai a lokacinai,
Yay yi
hukunci bisa yardaTai,
Ga lokaci wa ka karkare shi?.
2.
Bisa yardaTai
ya ƙago bayi,
Ga ƙassai ga sama’u
Ya yi,
Da
fasullan shekara da yay yi,
Na lokaci ba a gurgasa shi.
3.
Shi dai waƙaci a kiyaye
shi,
In ya zo
ba a tunkuɗe shi,
Mai iƙirarin ya
gurgusa shi,
Kar ku yi shakka ga ƙaryata shi.
4.
Mai ƙwazon kan ya zo
ya leƙo,
Wai zai
ruga ya sa ya sheƙo,
Haba!
Idan kai yana da sanƙo,
wa zai gashi ya sutarta shi?
5.
Gaggawa ba ta
sa a girma,
Komi
nakinka in gaya ma,
In waƙaci ya yi babu
dama,
Komai shi za shi bayyana shi.
6.
Bari doro don
kana da kuɗɗi,
An shiga
mulki ana ta faɗi,
In waƙaci ya yi babu
daɗi,
Zama guda za shi toskana shi.
7.
Ilmi bai tsere
lokaci ba,
In ka
same shi zan ka tuba,
Daina
kirari kana ta ƙaba,
Ko an ce: “Wane ba awa shi”.
8.
Bil’ama ya so
ya ƙure Musa,
Ganin
karatunsa ya yi nisa,
Tabara
yab bi shi har maƙosa,
Da lokaci an ka dambala shi
9.
Da lokaci yay
yi an ka kammai
Mala’iku
an ka sa su jimai,
Bugu
guda an ka yo gaba nai,
Nahawunai an ka yamutse shi.
10.
Ga shi rugun
zaune an ka nuno,
Sunanai
an ka ce ya zano,
Yay yi
ta wayon biɗan ya gano,
Amma yak kasa rubuta shi.
11.
Kun san Ƙaruna ya yi
suna
Da
lokaci yat taho na ƙuna,
Gaban
mutane a tsakan rana,
Ƙasa ta kammai ta adana shi.
12.
In mai mulki
bai manta ba,
Bai yiwa
Fir’auna ƙwarjini ba,
Da
lokaci yay yi bai kula ba,
Cikin ruwa an ka birkice shi.
13.
Duk mai cewa ƙarfi ya zo,
Ya bar
tsoro yana ta ƙozo
In waƙaci ya yi babu
gwarzo,
Zama guda za a murƙushe shi
14.
Ku dubi tsarin
maza na farko
Da
shirye-shiryen da sun ka ɗauko,
Da
lokaci yay yi sun ka sauko,
Kamin ya biya ya kakkaɓe shi.
15.
Ɗan boko in ya sa agogo,
Kaman ya
tusgo da shi ya rugo,
Kan
ajima in ya je ya rego,
Nan waƙaci za shi ba shi haushi.
16.
A yau ina altaɗar da jaki?
Kuɗinsu da sun wuce tumaki,
A yanzu
sun zan adon musaki,
Waƙaci tilas a girmama shi
17.
Waƙaci kwas san
irin halinai,
In ya ga
ya fara isalinai,
Miƙa wuya zai yi
kar ya farmai,
Ya sa shi mala ya maƙure shi.
18.
In jiya ne kay
yi naka loto,
To bari
yau masu yi su ƙoto,
In ka ce
dole za ka gitto,
waƙaci ko za shi ba ka kashi.
19.
Shi waƙaci bai jira ga
kawo,
Kuma
take ya gama da kawo,
Bai
rigima bai faɗa da tsawa,
A hankali za shi hukunta shi.
20.
Ku dubi kyawon
abu na sabo,
Kaman a
lasa idan ka dubo,
In waƙaci yas shigo
ya tarbo,
A kai shi Juji a jikkita shi.
21.
Ƙuruciya in tana da gauni,
Da
shekaru za a sa ta rauni,
A zo
zama dole sai da, ‘wai ni’!
Tashi sai an kakkama shi.
22.
Mai karfin
hankali fasihi,
Ka iske
ya dambale wa kihi,
Shekaru
sun shige da zurhi,
Wahmi ya fara sunsuna shi,
23.
Dubi irin zaƙunon budurwa,
In waƙaci za shi ba
ta kewa,
Haurun
su zube ga gantsarwa,
Haibar fuska a tamuƙe shi.
24.
Lotto muddin
yad darkako,
Kowat
tarbe shi ba shi ƙarko,
Zama
guda zai mutuwar kasko,
A kai shi daji a turbuɗe shi.
25.
Rana haskenta
in ya ɓullo,
Hantsi
kowa yake ta kallo,
Kan
agajenin karin kumallo,
Waƙaci shi za shi rarrabe shi.
26.
Mai cewa ya iya
kwatse shi,
Mai
doron sun ƙware taɓo shi,
Mai cewa
mu ka yi kiro shi,
Waƙaci muka sa shi hukunta shi.
27.
Tambayi mai
kakkaɓi da kauɗi,
Nuna zaƙewa gwanin zumuɗi,
Leɓo kakan kwaɗai da lauɗi,
Da mucciya an ka zungure shi.
28.
Mai cewa, yanzu
ba kamata
Waƙaci ya mai da
shi ƙwatata,
Har ya
zan yanzu bai da gata,
Waƙaci ya ida kalmishe shi.
29.
Mai turo yara ƙaryata mu,
Wurin
karatu a kunyata mu,
Waƙaci yaz zo ya
faranta mu,
Yau yaran su ka ƙaryata shi.
30.
Tambayi Ɗankama goga
masu,
Uban
samaƙi mai ‘yan gasu,
Da
lokaci za shi suɗaɗa su,
Zama guda an ka ba su kashi.
31.
Kai waƙaci ka yi ba ta
kashi,
Masu
gidajen ƙarau gilashi,
Ga su ƙuyaya su yanka
kashi,
A sa ƙasa ai ta rurrufe shi.
32.
Masu hawa raƙuma dawaki,
Da dubun
kaji cikin akurki,
Yau abu
ya zan kamar mafarki,
Duk wakaci ya kacaccala shi.
33.
Manyan girma
‘yan alfarma,
Jarummai
masu ji da fama,
In waƙaci ya yi babu
dama,
Da hawaye za su kammala shi.
34.
Maganar banza
rashin azanci,
A ba ka
girma ka sa bananci,
In waƙaci ya taho da ƙunci,
Da mu da kai, wa ka tsallake shi?
35.
Da lokaci za a
shirya komai,
Da shi
ake kammalar da komai,
In ba
shi ba shiri na komai,
Domin shi za shi barkata shi.
36.
Komai waƙaci garai
sananne,
An ka
gina kansa ayyananne,
Komai
fitina ta tufananne,
Ƙyale waƙaci shi toskana shi.
37.
In ka ji an ce,
mutum da kaifi,
Komai
sai ya yi ci-da-ƙarfi,
In waƙacinai ya zo da
zafi
Zama guda za shi murƙushe shi.
38.
In an ce, wane
shi ka tashe,
Ya ɗauko lokaci gasasshe,
Waƙaci zai sa shi
dallasshe
Sai ka ji shu har an manta shi.
39.
Gwani ga ƙira da masu
noma
Da ‘yan
farauta da masu koma,
In waƙaci ya yi sai
su koma
Kaman da ɗai ba su aikata shi.
40.
Waƙaci da rabo
suna da sauri,
Komai ƙwazon rabo da
sauri,
Sai waƙaci ya yi zai
yi kuri,
A buɗe hannu a
rungume shi
41.
Ba a taɓa yaƙi da lokaci ba,
An ka yi
nasarar kara da shi ba,
Bai taɓa lattin zuwa wuri ba,
Bale a girsai a hukunta shi.
43.
Ka bar ganin
wai kana da girma,
Don haka
tilas ake raga ma,
Da
lokaci ya yi in gaya ma
Girman duk zai warwatse shi.
44.
Ina bika
madugun azanci,
Da shi
da suda uwar habarci,
Da
lokaci yat taho da ƙunci,
Tsakan faƙo sun ka yanka kashi.
45.
Dubi taɓaɓɓen ga jiɓananne,
Da shi
da wawan ga toskanne,
An ce
kawunsu tufanannen,
Yau waƙaci ya tozarta shi.
46.
Sukuntumau mai ƙullin ƙarya
Da Kakkaɓi mai bakin kurya,
TuwOnsu
yau ya koma gaya,
Da lokaci yaM muzanta shi.
47.
Komai nutse
ruwa in ji Kabawa,
Tudu ake
tarbon gaggawa,
In yan
mace ciki ya zan gawa,
Ga tunkuɓa aka dako nai shi.
48.
Mazambaci duk
ku tabbatar mai,
Yana da waƙacin da za a
kammai,
A
karanto mai a fallasa mai,
Bayan kunya a hukunta shi.
49.
Mahassadi
mantuwa ka kammai,
Rabon
mutum wa ka tunkuɗe mai?
Ubangijinai
ya ƙaddaro mai,
Waƙaci ne, wa ka tunkuɗe shi?
50.
Ka reni yaro ka
suturta shi,
Da ya ga
an fara girmama shi,
Kai zai
duban ka mutunta shi,
Hadda faɗar ba ka girmama shi.
51.
Ya za ni bari a
cutata min,
A sa ƙiyayya a ƙuntata min,
Don waƙaci ya ɗan hasko min,
Ake bukatar a daƙile shi.
52.
An hau karaga
an yi ta sara,
A
mumbari an hau ba gyara,
A
dandali kullum barara,
Wai waƙacina a turmuje shi
53.
Muƙaddami da ka
wannan sara
Yau waƙaci ya mai sai
gara
‘Yan
aikensa ka ci mai gyara,
Shi gilma rai su ƙi gaskanta shi.
54.
A lokacinsu na ɓannan suna,
Da shi
da Bagudu ɗan Maigona,
Da
Bangaje mai ƙaurin suna,
Da Ginshimi mai kan ramboshi.
55.
Ba sa tadar
sunan kowa,
Magibaci
wa zai yin kewa,
Mahassadi
mai kushe gawa,
Kaɓɓa bakaniken gilɓoshi.
56.
Mu tuba mu duka
tun ba mu zo ba,
In
jama’a ba su yafe ma ba,
Akwai
tumulli ba ƙarami ba,
A ƙulla dambe da mai tarkoshi.
57.
A lokacin da
kake dai ka yi,
Da
lokacin sakayya yay yi,
A ɗebe zancen samun sanyi,
Kama a tad’inu a bar manta shi.
58.
Duk wani mai
hankali shirarre,
Ya san
zancen ga babu kore,
Kai ko
mai hankali gajere,
Waƙaci bai fara makkasa shi.
59.
Allah roƙon na Bunza
gata,
Wurinka
ko na taho da rata,
Da
lokaci yay yi min na ƙeta,
Ka yi min ahuwa, a kunyata shi.
Aliyu
Muhammadu Bunza
Jami’ar Usmanu
Danfodiyo
Sakkwato,
Asabar 26/07/2014
Ramadan 29/1435/1A.H.
Arkilla Sakkwato
9:18pm
No comments:
Post a Comment