Waƙar Kaska mallama ce (ƙwar biyar). Babban amsa amonta “ba”. Yawan
baitocinta hamsin da takwas (58). An kammala ta ranar Lahadi 30/6/2013, a
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa Katsina. A ganin Kaska, siyasar zamani ta demokraɗiyya
ita ta jefa ƙasarmu
cikin musibun da take ciki a yau. Siyasar zamani ta tarwatsa saraua da
masarautu. Ta gigita addini da mabiya. Ta muzanta malaman addini, da ma’aikatan
hukuma. Ta ɓata wa talaka tunani. Ta sagarta matasa maza da
mata. Ta danbala ‘yan kasuwa. Ta yi wa gaskiya idon marurugiya aka yi wa
ma’abotanta ƙofar
raggo. Da dai an koma ga tsarin da wanda ya yi halittu. Ya shirya wa
halittunSa, da abu ya fi.
---------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
-----------------------------
1.
Roqo
nikai a wurinka ya mai jinqai,
Sarkin da bai zance waninsa shi tassai,
Mai ja da kai Allah ina kaico mai,
Domin Jahannama za ta mai sai qosai,
Qumumus! Takai masa ba da jin tausai ba.
2.
Na
yo salati ga Xaha manzon qarshe,
Wannan da bai zance ya zan yassashe,
Mai ja da Annabi (SAW) zai zamo busasshe,
Tsarin da duk ya kafa ya zan rusasshe,
Haka za a nakkasa ba da morewa ba.
3.
Tabban
Sahabbai sun aza mu ga turba,
Masana maqoqarta, mazajen tuba,
Mariqa amana ba da cin zarafi ba,
Tsarin da kun ka bi wa mutum bai kai ba,
Sai dai kwatanci ba da zozozo ba.
4.
Ga
gaskiya yau mun gane ta a fili,
An lulluve qarya da qaton kwali,
Ta yo qawan jan hankalin mai hali,
Ta jitta doro kanta ba xan kwali,
Mai hankali ba zai aminta shiga ba.
5.
Kaska
baqin qwaron da ba na yabo ba,
Mai shan jini ta lave kamar ba ta sha ba,
Maganar ta qoshi a duniya bai zo ba,
Ga jikin da duk ta maqale ku yi duba,
Tambo takai ga qumburi ga qaba.
6.
Kaska
bala’i ce ku tambayi jaki,
Ya ce wa masu musu su je ga dawaki,
In babu su a gidanku je ga tumaki,
Ga matsematsi taka gallazawa awaki,
Matsiyaciya ba ta bar su lelawa ba.
7.
Kai
xan Adam in ban da son a sana ma,
Kayan qasa ta gaza ka ce, a aza ma,
Tsauni ya kasa aza su domin girma,
Ka tarbo qoqon kai ka ce: “A sakam ma”,
Wauta da jahilcinka ba qarami ba.
8.
Matsalar
siyasa babba gyaran qarya,
Kunya ta qaura ido ya koma gaya,
Zance xari tisi’in a bar su a baya,
An barkace tara sai guda aka kaya,
Shi ma ba za a cika shi kakkakkaf ba.
9.
Ita
gaskiya an ce ta je ta yi barci,
An vassuwa mata hankali da azanci,
In an ka gan ta a kama yin fadanci,
In tai Haxejanci a kama Kananci,
Haka za a ci gaba ba da sauyawa ba.
10.
Babba
da yaro kowane tarkoshi,
Maqoqo har ya rankavo ga maqoshi,
In sun ka taka duron suna qissoshi,
Sai an sake musu kai su sa qusoshi,
Ba su gaji jin kunya da jin tausai ba.
11.
Faufau
ba ka ji ba ka ga alkawali ba,
Zancen tsayi a cika shi bai taso ba,
Duk mai tuna musu shi ba za su kirai ba,
Mai son a daidaita ba su riqai ba,
In yai kira ba za a saurara ba.
12.
Ita
dai amana kun ga yadda ta komo,
Maciyanta kowane ya yi qaton ganmo,
Kaji da zabbi kodayaushe a romo,
Shi ko talakka shi je farautar zomo,
Haqqinsa ya salwanta bai ahumo ba.
13.
Maciya
amana yanzu su ne kowa,
Su ke faxar magana ta taushe ta kowa,
Mai ja da su take su mai sai gawa,
Sun zamto kaskar shan jinin talakawa,
Bautar da moro ba a kan sharaxi ba.
14.
Cutar
da tai wa talakka mai sai wawa,
Ya zamo katafashe gidan wani wawa,
A mayar da shi bawa a nai masa tsawa,
Ya bar gida ‘ya yara sun shiga kewa,
Ya kama banga ba cin tauri ba.
15.
Ta
tura malammai cikin fadanci,
Mabiyansu anka saka a mugun qunci,
Aka sa su dinga faxa akan ganganci,
Aka rarraba su saboda kai ga abinci,
Aka ba su tawilin da ba daidai ba.
16.
Wa’azin
ya koma duk a kan qissoshi,
Nassi sahihi anka sa garwashi,
Mai binciken su da gaskiya suka haushi,
A wurin hukuma sun ka yo alwashi,
Ba za su sava shirin da an ka biya ba.
17.
An
mai da addini kwatancin kura,
Mai son shiga ciki ya ga ba ta da gyara,
Ulama’u baki buxe don cin gara,
Juhala’u na ta faxa da suka sara,
Wani can ba zai hango faxa ya shigo ba.
18.
Babban
tukuicin malamai motoci,
Umura kujerar Hajji ba Sufanci,
An yada zancen qungiya na bananci,
Mai ba da kuxxi coci ko masallaci,
Shi ne uban tafiyan da ba a sakai ba.
19.
Kaskar
siyasa ta laqe masarauta,
Ta sa sarakai yanzu ba su da gata,
An mai da su hoto cikin mahukunta,
Sai an faxa su faxa, ya amshin Shata,
Tamkar qasar ba su ka mulkin nan ba.
20.
Ta
gadi mai da gidan sarauta tsoho,
A fitar da wansu a sa waxansu su daho,
A naxo waxanga wajen gidan ga a jeho,
Kuma ga sarautu barkatai an maho,
Ga uban qasa bai san sarakai nai ba.
21.
Ta
sa sarakai yin shiru ba su so ba,
Wani kau da kai ai ba na son rai na ba,
Tilas ta sa a yi ba cikin yarda ba,
Don xan tasha bai san akwai wani xa ba,
Balle sarauta wadda bai gada ba.
22.
Laifin
sarauta mamaya mai faxi,
Ga shiga siyasa ta yi tsaga da faxi,
Da rabon muqamai don xiya su ji daxi,
An bar talakka da xansa babu mashexi,
An takura masa ba da yai laifi ba.
23.
Shis
sa siyasa zai gane ta matseri,
Ta fitar da shi qangin mari da masari,
Ga hukunta kowa bai kula da mafari,
Gayya garaje gagara ga sauri,
A gwada wa nina-wane gai bai kai can ba.
24.
A
wajen sibil sibis abin ba dama,
Ba ta bar qwararre ko guda ba da girma,
In ba ka pati babu mai kama ma,
In ka qi miqa wuya a sa a diram ma,
A yi ma ritaya ba da shiryawa ba.
25.
Haraka
da takkwallai hasara tsintsa,
A riqe qahonin nagge don su yi tatsa,
Wai su da baki za su ce su yi tsutsa,
Sun mai da mu bayin siyasa tsintsa,
Ilmi ga pati ba lalura ne ba.
26.
Aiki
na likkita anka ba mai Maikurya,
Xan daudu su ka Pirinsipal ka ji qarya,
An ba direba akawu ya haye kaya,
Sarkin tasha Senitan da babu hamayya,
Nazaqi zai cif-joji ba da wuya ba.
27.
An
sa wa ‘yan banga tufafin sarki,
Maganar tsaro ta yamutse ga musauki,
Domin mashaya an ka kai ga mataki,
An ba muzuru shugaba na akurki,
Zakara ba zai cara na morewa ba.
28.
Yau
ga matasa sun zamo muna kaya,
Qarfi da yaji sun zamo ‘yan qarya,
In za a yin kamfen a kai su mashaya,
Su taho cikin taro suna ta tavarya,
Wallahi mun shiga ukku ba qarami ba.
29.
Sherin
siyasa ya kashe muna mata,
Qattan gwagware sun zamo ‘yan mata,
Suka vata tarbiyar qananan mata,
Yau maxigo ke tashe gun ‘yan mata,
Wallahi an cuce mu ba qarami ba.
30.
Kushili
ga manya ba a cewa komai,
‘Yan yara dole a tanada musu kanfai,
Wai don ku san Allah ana son rammai,
Qato shi hau qato ana tava mai,
Aure su qulla ba cikin voyo ba.
31.
Rashawa
da hanci su ka haddasa komai,
Ita ko siyasa ta qware ga batunai,
Shi maguxi cuta da zamba gidanai,
Waqancin siyasa nan ake koyo nai,
Gambo mijin Kulu yaf faxa ba ni ba.
32.
Yau
kashiya shi ne muqamin girma,
Ma’ajin kuxi kowa yake roqa ma,
Aiki a Finance
yanzu shi ne girma,
Babbar kujera yanzu ba alfarma,
In ba kuxi aka zo ana ritta ba.
33.
Waqincin
siyasa ba na ilimi ne ba,
Babbar takarda ba abin so ce ba,
Dokta da Furofesa ku bar wani qaba,
In an ka sa ku cikinta ko ba ku so ba,
Rikixe ku za a yi ba da kun ahumo ba.
34.
Iliminmu
in kun lura ba ya da qarfi,
Da Firamare har jama’a mai zurfi,
An tura malanta kware mai zurfi,
Sai wanda yar rasa mai gida mai qarfi,
Ya shigo da niyya ba ta dogewa ba.
35.
Don
an ga albashinmu ba shi da kauri,
Aikinmu bai da zama bale hansari,
Kuma ci gabanmu haqiqa ba ya da sauri,
Haka an ka bar mu cikin kware mai tsauri,
Kowa ya san shi ba zai kwaxan ya shigo ba
36.
‘Yan
kusuwa ta sa su dogon barci,
Sun faxa ramin gungumen komarci,
Ta karya jaarin babu ko na abinci,
An qulle shago an shigo fadanci,
Ba a samu sa’ar kwangilar qarya ba.
37.
Riba
tas saka ma waxansu don son banza,
In kwangila ta buwaya in ji Yahuza,
Miliyan biyar kan shidda don son banza,
Kwas shuka rogo ba ya tono gwaza,
Qarshe karewa ba na xorewa ba.
38.
Dottive
sun yi zugum irin na makoki,
Ta sa su sa-in-sa da ‘yan jikoki,
Duk unguwa yau baba babu aboki,
Wai don siyasa ne ya xauki mataki,
Gaba da ‘yan patin da bai xauka ba.
39.
Ta
vata ‘yan bokon da ke makaranta,
Ita jarrabawa can wajen mahukunta,
Sata akai a gaba uban makaranta,
In ya qi yanzu a je da shi maqabarta,
Banza ta sha shi ba za a ceta mai ba.
40.
Harakar
tsaro hannun agogo a baya,
Polis da soja ka bincike kan hanya,
In sun tare ka ka mai da hannu baya,
In ka qiya tilas ka sauke kaya,
A yi binciken da ba za shi amfani ba.
41.
An
sa qabilanci zukatan kowa,
Kowa qabilatai yake wa kewa,
In ba ka jin harshensa zai maka tsawa,
Komi kake so ba a yin gaggawa,
Don bai ji kai magana da harshenai ba.
42.
Haka
tas saka mu cikin giyar vangarci,
Da arewa, ‘yan kudu yanzu babu kusanci,
Gaba da yaqin vangare yai kauci,
Mulkin qasa ya vaci don ganganci,
Xaana-mu-xaana ba siyasa ce ba.
43.
Daga
vangaranci sai bixan tutoci,
Kamin a kai ga zama kiran Senitoci,
Kamin su zo kafinta yai rabtoci,
Na wurin zama da wurin aje motoci,
Na rabon qasa harakar ga ba qarama ba.
44.
Daga
nan a fara gudunmuwar sojoji,
A mayar da hafsoshinmu masinjoji,
Mu haxe tasha sunanmu fasinjoji,
Huskar samari ga zubin tamoji,
Sababin siyasa ba da tsohewa ba.
45.
An
zo ga addinanmu an rikita mu,
Aka zavi wansu ana ta fifita su,
Mabiyansu ai ta shirin zuguguta su,
A haxa su yaqi don a dabirta su,
A yi cefane da jininsu ko ba su so ba.
46.
Qarshen
siyasa ya zamo tanzanko,
Domin hasarar tata ba ta da ranko,
Fitina jidali gardama aka sabko,
A kashe qasa qarshen bala’i narko,
Hijira ta tabbata ba da shiryawa ba.
47.
Wane
ci gaba taz zo da shi ku gaya min?
Don na ga ‘yan pati suna ta matsa min,
Manyan varayi nag a sun qyacce min ,
Matuqar talakka ina faxa shi jiya min,
Ba za shi sa kai nai cikin rikici ba.
48.
Mai
farfagandar ci gaban hanyoyi,
Wa anka wa su ban da ku lauyoyi?
Don ku ka wa mota zubin tayoyi,
An bar talakka da qetaran kunyoyi,
Tamkar kurege ba da hutawa ba.
49.
Wane
tasku yaf fi barin qaga ga Nasara?
Ya kashe ya kwasa bai raga muna saura,
An bar talaka sara a bakin kura,
In ta ji yunwa an aje mata gara,
Zance na ci gaba kun ga bai taso ba.
50.
An
kwashe arzukkanmu an kai ganga,
An sa jirage sun jide su a tunga,
An bar mu nan sake “fau!” Ya bakin waga,
Hatta cikin bukkar Fulani rugga,
Ba a bar su zaune, zama na morewa ba.
51.
Hanya
ta sadarwa idan aka luro,
Don farfagandar kansu ce suka tsaro,
An bar talakka cikin bala’in sauro,
Shan Inna sun yi mitin da ciwon doro,
A gidan talakkawanmu ba manya ba.
52.
Mu
kula qasashe masu yin ta mu leqo,
Tilas talakka da ke cikinta shi sheqo,
Duk mai tsawon daraja a sa shi shi duqo,
Su masu mulkin kowane kai sanqo,
Don cin amana ba na shekarru ba.
53.
A
qasar Masar ta kakkashe talakawa,
Saura kaxan a mayar da Siriya gawa,
Afgani ga birni fayau ba kowa,
Nijeriya tamkar bala’in tsawa,
Gawar Musulmi ba muhimmi ce ba.
54.
Mu
dai siyasa gun mu ba ta da girma,
Domin musibobinta ba su da dama,
A kashe a xaure babu mai kama ma,
In ba ka yin mai ci kare ka gwada ma,
Hanyar fita birninku ba da jaka ba.
55.
Manyan
sarakai ta zubar musu girma,
Malam da Liman sun naxe tabarma,
‘Yan kasuwa, attajirai sun suma,
Kai kan talakka muqabira taka cimma,
Ba ta bar sibil saban da irlinai ba.
56.
Qarshenta
‘ya’yan nata ke jin daxi,
Babba da yaro ba su kunyar kauxi,
Manyan gidaje ga kujerin lauxi,
Manyan birane ko’ina da mashixi,
Na shirin fasadi ba batun tuba ba.
57.
Malam
da Ustaz sai a bi ni da gyara,
Givin da ke ciki kar a bar shi tsirara,
A cike shi kar a saka shi kwadon shara,
Na tabbata babin ga na rage saura,
Koyo nake ban kai ga gogewa ba.
58.
Na
gode Allah wanda yai kakana,
Wannan da yai reno wajen tsohona,
Suka zavi suna kaf-da-kaf ga halina,
Suka sa Aliyu tubarrukan a wurina,
Allah Ka sa haka yaf fi ba don ni ba.
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa
‘Yar’adua, Katsina
Lahadi, 30/06/2013
No comments:
Post a Comment