Wannan
waƙar ‘yar tagwai ce. Babban amsa amonta “ya”. Yawna baitocinta arba’in da
biyar (45). An kamala ta Talata, 3/7/2013, a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa,
Katsina. A irin hasashenta, babu abin da ya fi gaskiya daɗi a duniya. Tsohuwa ce da gidan kowa ana sha’awar ta, kuma duk wurin da aka
rasa ta ko aka hana ta zama ko aka ba ta tsoro wurin ya ɓaci. Farfaɗo mata da martabarta ta samu sakewa a zamaninmu shi kaɗai ne zaman lafiyarmu da kwanciyar hankalinmu. Rashin ba ta masaukin ƙwarai shi ya
lalata zamaninmu.
---------------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
--------------------------------
1.
Shukuran
ga Allah wahidun mai agaji,
Da salati gun
Manzo aminin shiriya.
2.
Na
yo yabo matuqa dukan asahabihi,
Manyan gwaraje masu
nakkasa qarya.
3.
Saqo
garan ya xan’uwa ka tsaya ka ji,
Komi mukai mu bi
gaskiya shiryayya.
4.
Ita
ce amintatta a kowane zamani,
A sahu tana gaba
ba a kai ta a baya.
5.
Launinta
ba surki fari ne ko’ina,
Riga da taggo ba
qananan kaya.
6.
Ta
girmi kowa shekaru wane mutum!
In kai musun haka
je ka tambayi qarya.
7.
Qarfinta
ya fi na xan Adam da mutantani,
Doki da zaki ta
aje musu kuyya.
8.
In
ta tsaya gantsarwa doro babu shi,
Ziqau take tankar
a soke tavarya.
9.
Muryarta
daxi ke gare ta a ko’ina,
Ga shiga jiki ta
zarce sautin kurya.
10.
Zance
na kowa bai fice ba nata ba,
Ita qunshiyar
zancenta bai da musanya.
11.
Zancen
waninta ya bar xaga maka hankali,
Bari dai ta furta
yanzu ka ji kumurya.
12.
Ba
ta Karen miski da shadda don qawa,
Mai su idan ya
rasa ta zai yi quyaya.
13.
Ba
‘yar sarauta ce ba, ba ‘yar fada ba,
Fadar da babu ta
an baro ta a baya.
14.
Carbi,
tulin rawani, gafakka, kandili,
In an rasa ta su
zan tumullin kaya.
15.
Faxi
gare ta qure ta wane xan Adam!
Wane gaban qato
taya ta amarya?
16.
Ce
babu shakka shi tsawo ko rijiya,
Qarya ka xan rame
da babu mavoya.
17.
Iccenta
shi ka fure da ‘ya’ya mai yawa,
Wane kaxanya
xorawa da magarya.
18.
Ita
ce nagartar jarumai a fagen faxa,
Ta tsere sanda
wargajewar kwanya.
19.
Manyan
mazanta a ko’ina su ke zara,
Maqiyansu dole su
vuya tun day hanya.
20.
Dokinta
dole fagen suka shi ke zagi,
Sauran a bayan
nata sui ta tavarya.
21.
Mai
son ta in ya guje ta kunyanai take,
Zangonsu bai nisa ta bar shi a hanya.
22. Mai son ta, mai
aurenta, ba ya da fargaba,
Shi ke zagin taro a kowace hanya.
23. Komai ya lalace
idan aka bincika,
Ita anka ba tsoro saboda hamayya.
24. Ita xai ta kai
maqiyinta ke kewan ta zo,
In an ka gurmatsai cikin gogaggya.
25. Ita ce watan Salla
saboda farin jinni,
Ciyo ga reta ga masu wasan vuya.
26. Akushin tuwo ce
babba ta ishi unguwa,
Don ba ta varewa ya kumbun qwarya.
27. Ita sanfara ce
babba gagari muciya,
Tuqin tuwo in ga ta ba a tukunya.
28. Allonta ba ya faso
ku tambayi Gangaram,
Alaramma ba ya musanta iccen danya.
29. Zaqinta ya zarce
zuma saqa fari,
Balle maxi da ake da ‘ya’yan xinya.
30. Ita tat tsayar da
samai qasai ba ginshiqi,
Da wata da taurari irin su Surayya.
31. Mai gaskiya bai
waiwaya in ya wuce,
Bai dube-dube irin na xaukar kaya.
32. Bai soke kai qasa
juddadun ya qi tassuwa,
Fuskarsa ba ta baqi irin na tukunya.
33. ‘Yar tsohuwa ke
samun sa’ar zamani,
Tsufanki duk bai sa jikinki mijirya.
34. Surukinki yai
sa’ar xiyar babban gida,
Ko ba a so sunansa dai Rabakaya.
35. Ba ta kira a qiya
a tsira da arziki,
Magujinta sai ya gama da wasan vuya.
36. Tsoron mijinki a
dole ne don xaukaka,
Tun bai tsaya ba ake riqe masa kaya.
37. Ki yi dariyarki da
gaske ba mai ja da ke,
Hauru farare ba baqi da wushirya.
38. An ce da ni ke
yada zango Yawuri,
A cikin garin Ngaski in ji Baraya.
39. Na gai da rini
masu kere itatuwa,
Xan goriba tilas ya gai da giginya.
40. Kushe ki yas sa
duniya tay yamutse,
UN tana ta rabon faxa da tavarya.
41. Nijeriya an bar
Arewa cikin duhu,
Ta yi cefane amma tuwo ta ci gaya.
42. Duk wanda yaq qi
batunki zai da na sani,
Domin gudun ki ka sa a faxa haxaya.
43. Muddin kina tsaye
wa mutum ya yi kangara!
Wasan kixi da rawa a qaga mashaya.
44. Fafau ba za ki faxa
ba sai ke tabbata,
Zancen da duk ba ke ba shi ne qarya.
45. Roqon da nay yi
Aliyu Bunza ga Qadirun,
Koyaushe tare da ke muke baja kaya.
Aliyu Muhammadu
Bunza,
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa
‘Yar’adua
Talata, 3/7/2013
No comments:
Post a Comment