Monday, October 14, 2019

Muhimmancin Haɗin Kai Ga Duban Watan Ramalana




Umurnin da Manzo (SAW) ya ba Bilal na ya yi sanarwa ga ganin watan da aka shaida masa wata hujja ce ta tabbatar da hukuma ke da ikon sanarwa na ganin wata.  Waɗanda suka zo wa Sayyidina Umar bakinsu buɗe ranar da yake azumi da jama’arsa a matsayinsa na Sarkin Musulmi, ya tambaye su, suka ce wata suka gani, wata hujja ce da ta kore jiran sanarwa ga Muminai idan sun yi ido huɗu da wata. Matsalar da ke rarraba muna kai a nan ita ce, samun sanarwa na ganin watan wani wuri ko wata ƙasa daga fitattun gidajen rediyon BBC da VOA da RFI France da DW Germany da CNN da makamantansu.
Muhimmancin Haɗin Kai Ga Duban Watan Ramalana 
Aliyu Muhammadu Ɗan’indo Bunza
Tsangayar Fasaha Da Ilmi
Sashen Harsuna Da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau
Sha’aban 1439AH/Alhamis 10 ga Mayu 2018

Gabatarwa
A kowane irin al’amari Musulmi suka haɗa kansu za su ga bambanci da rarraba. Addininmu gaba ɗayansa na haɗin kai ne, kuma haɗin kai yake koyarwa ga dukkanin hidimomin ibadojinmu.  Matsalar rarrabuwar kanu da saɓanin fahimta da ja-in-ja da ke aukuwa cikinmu a farkon watan Ramalan da farkon watan Shawwal ba ta gushe ba a kowace shekara. Ƙasashen duniya irinsu Saudiyya da Masar da Sudan da Turkiyya da Iraƙi da Libiya da Marocco da ƙasashen Asiya da Gabas Mai Nisa duk sun shiga cikin ire-iren saɓani na ganin wata kuma har suka daidaita kanunsu ba su rarrabu ba.

Shimfiɗa
          Matsalar tantance ranar ɗaukar azumi da aje shi dogon tarihi gare ta a ƙasar Hausa. A Kano da ta hudo kai, Majalisar Sarkin Kano ta kafa kwamitin ku je ku gani, ku faɗa a sanar. A Sakkwato, aka yi mata taron dangi da kwamitin tantance ganin wata na ‘yan mun ji, mun gani. A Kabi abin ya zama tankar gamgami a kowace masarauta a ranar duban farko don haka aka fi jin ɗuriyarsa a gefensu saboda taron dangi. A Borno, yanayin sararin samaniyarsu ya ba su damar ribantar ganinsa fiye da kowace nahiya ta Arewa. A sassan Musulmanmu na Kudu da yanayinsu ba ya da sarari irin namu suka raba ƙafa uku, tsakanin Kalanda da Majalisar Sarkin Musulmi da Saudiyya. Maƙwabtan ƙasashe da Musulminmu ba su da rinjaye a hukumance irin Nijar da Benin da Borkina Faso da Ghana da Chadi da Cameron ba su fuskantar irin matsalolinmu, domin ganinsu ya zama ruwan dare da gani da ajewa ba ya da matsala domin labari ya bazu ko’ina. Da yawa sukan  riga mu gani, amma bisa ga rashin sani mun ƙi ɗauka da ganinsu. Gaskiyar lamari, a Afirka ta Yamma Nijeriya kaɗai ke da ra’ayin ƙuƙe-na-ƙuƙe da gardandami tsakanin Hukuma da Mabiya. Wannan matsalar ganin wata tana daga cikin matsalolin da suke yi wa haɗin kan Musulmi barazana a Nijeriya.
Fiƙihun Matsalar
          Matsalar ganin wata a halin da ake ciki a Nijeriya ba ta karatu ba ce, ta siyasar fashin baƙi ce da neman goyon baya. Can da muna da murya ɗaya daga Majalisar Sarkin Musulmi wadda ita ce ta fi cancanta da kusanta ga Sunnah. Wasu ‘yan kurakurai da ba su fi ƙarfin a gyara su ba da wasu yara da suka ari rigar malanta suka kururuta su domin biyan buƙatocinsu da Majalisa ba ta ahumo ba, su suka dagule mata tsari. Daga nan, aka rabu gida biyar: Majalisar Sarkin Musulmi, Majalisar ɗaiɗaikun Sarakuna, Mabiya Sufanci, Mabiya Ƙungiyoyi, Mabiya aƙidoji fararru, uwa uba da wasu ƙungiyoyi da aka kafa da sunan kyautata ganin wata. A sahihin nassi, Hukumar Musulunci ke da nauyin sanarwa na ɗauka da aje azumi. Idan an rasa hukumar dole abin ya koma ga waɗanda Musulmi suka ɗora wa nauyin jagorantar al’amurransu. Idan an rasa haka, hukuncin bayyane yake ga kowa. Wurin da gizo ke saƙa shi ne, da wa Hukumar Musulunci ko Jagoran Musulmi zai dogara gabanin a sanar da ganin wata? Shin Hukuma lisafinta za ta bi ko lisafin mutane ko haɗa biyu za ta yi? Tsakanin lissafi da gani da ido, kalanda, da kimiyyar zamani, wane ya samu cikakken goyon bayan hukuncin da Manzon Allah (SAW) ya yanke?

Daidaitar Lissafinmu daHaɗin Kanmu
          A al’adar Musulman duniya, babu al’ummar da ba ta tanadi nata lissafin kwanan wata ba. A hukumance, a nan Nijeriya Majalisar Sarkin Musulmi ta naɗa gagarumin kwamiti a kan haka. A kowane wata kwamitin kan aika a dubi wata ya kuma sake tura sakamakon bincikensa. Sarakunan ɗaiɗaikun garuruwa da ƙasashe da ɗaiɗaikun malamai da ɗaliban ilmi na nasu ƙoƙari. Wurin da matsalar take shi ne, da yawa akan hangi kurakurai ga ƙidan da hukuma ke yi da na ɗaiɗaikun  garuruwa/ƙasashe ko al’umma. Hukuma ta sha tsaye a kan nata lisafi domin a ganinta, ganin jama’a ne take tattarowa kowane wata. Wannan ya haddasa matsala biyu, sai a taras da ranar duban fari na jama’a ya saɓa wa na hukuma. Idan duban farin na jama’a Litinin ne na hukuma Lahadi, sai hukuma ta ba sarakunanta umurni da ranar da take a kai ta kuma haramta wa duk wani mai biyayya gare ta duban wata ranar Litinin. Idan an gan shi Litinin, Lahadi ta zama farilla ga hukuma da nata jama’a. waɗanda suka gan shi Litinin su ji tsoron yi wa Allah yaji ga abin da ya sanar da su ƙarara babu wasiɗa.
          Yadda za a samun haɗin kanmu a nan shi ne, idan ana ganin saɓani irin wannan a tsaya tsaka. Tabbas, a iya saninmu, Nijeriya ba ta taɓa samun saɓani da hukuma da ya zarce kwana ɗaya ba. A aminta da lissafin biyu (na hukuma da na masu jayayya) a ɗauki kowanensu duban farko, a kira kowa da kowa ya fito a duba. In an gan shi an huta, in ba a gani ba, a fita gobe. Wannan matsalar ba ta yi takin saƙa da kowane nassi na Alƙur’ani da Sunnah ba, kuma ba a samu sahihin nassin da ya haramta ta ba. Duk wata magana da ta ƙi ta, tana buƙatar sahihin nassi.

Kimiyyar Ƙarninmu ga Haɗin Kan Ganin Watanmu
          Kulkin nassi cewa ya yi:
Nassi:         Suumuu li ru’uyatihi wa afɗiruu li ru’uyatihi, fa in gumma alaikum faƙ diruu.

Tarjama:     Ku yi azumi da ganin sa(wata) ku sha ruwa da ganin sa(wata) in an turnuƙe muku sama’u gani ya faskara ku ƙaddarta masa taliyon lissafinku.

A yau, matsalar wannan hadisi muke ciki tsakanin ‘gani’ na ido da na ‘ƙaddartawa”. Masu fashin baƙi na farko masana salaf sun rinjayar da “ganin ido” ƙuru-ƙuru ba da wata dabara ko walankeluwa ba. Masanan zamani nagartattu ma’abota sunna wasu na ganin tun da kimiyya ilimi ne da ake iya dogaro da shi ga harkokin rayuwa, sawwara wata na’ura da za ta kaurara shi a gan shi yana jinjiri ko ta kururuta ganin ido ya hango abin da idon ƙwaƙwalwar tuwo ba ya hangowa ba laifi ba ne. nau’i na biyu na kimiyyar ita ce, wasu ƙwararru da suka karanci wata da manzilolinsa wasu sun je har a wurinsa a raye ba da musu ba. A cikin bincikensu suna da ilmin sanin ranar da za a haife shi (ya fito na yarda da shi) bin umurninsu tun ba a gan shi ba, ba laifi ba ne a zahirin bincike. Cikin wannan rugumutsi maganar kalanda da kwamfuta da kusufin rana da wata suka yi ta kai da kawo, ana daɗa juna sani. Shawo kan waɗannan matsaloli kamar magance kashi 97% cikin matsalolin haɗin kan ganin wata a Nijeriya ne.
          Mafita da samun haɗin kai a nan ita ce, a bari shari’a ta yi magana, kuma a fifita abin da ta fifita. A fara gabatar da abubuwan da ta gabatar, kuma duk abin da ba shi ta gabatar a farko ba, babu wani abu da zai limanci abin da ta limantar, bale ya goge shi, ko ya raunana shi, ko ya ba da zaɓi tsakanin biyun. A daidaitaccen fiƙihun addinin Musulunci, “gani da ido” ya kore komai. Duk abin da ya ƙaryata shi ƙarya ne. Idan wata ya fito ido ya kasa ganinsa, bai fita ba. Duk abin da zai gan shi ba ta hanyar ido ba, bai zama sunna ga masu koyi da sunna ba. Ba a tilasta wani ilmi da ba na lalura ga shari’a ba, a kan lalurar shari’a.

Hanyoyin Sadarwarmu ga Haɗin Kan Ganin Watanmu
          Umurnin da Manzo (SAW) ya ba Bilal na ya yi sanarwa ga ganin watan da aka shaida masa wata hujja ce ta tabbatar da hukuma ke da ikon sanarwa na ganin wata.  Waɗanda suka zo wa Sayyidina Umar bakinsu buɗe ranar da yake azumi da jama’arsa a matsayinsa na Sarkin Musulmi, ya tambaye su, suka ce wata suka gani, wata hujja ce da ta kore jiran sanarwa ga Muminai idan sun yi ido huɗu da wata. Matsalar da ke rarraba muna kai a nan ita ce, samun sanarwa na ganin watan wani wuri ko wata ƙasa daga fitattun gidajen rediyon BBC da ƁOA da RFI France da DW Germany da CNN da makamantansu. Waɗannan abubuwa suna barazana ga haɗin kanmu musamman idan an ce an gan shi cikin ƙasarmu ko maƙwabta da mu ko waɗanda nisansu da mu bai kai kilo mita (2226) dubu biyu da ɗari biyu da ashirin da shida ba, domin a haɗuwar malamai maɗali’insu ɗaya. Wata sabuwar matsala ita ce kafafen sadarwar zamani mai cike da yaɗa labaran da ba su da tabbas da gidajen rediyo masu zaman kansu, da gidajen rediyon siyasa da wasu mutane ko ƙungoyoyi da suka gaji da hukuma suka zama masu zaman kansu a addinance.
          Yadda za a shawo wannan matsala yana da sauƙi. Na farko, hukuma ta saka siyasa cikin tunkarar matsalar ta nemi goyon bayan sassa na Muminai. A bar ƙofa buɗe ta sauraron shedar kowa a ba da wadataccen lokaci da za a ƙure ƙorafin mai ƙorafi. A saka sarakuna da ma’aikatan tsaro, da ƙungiyoyin Musulmi ba tare da son zuciya ba, su zama wasiɗa da babban Kwamitin Sarkin Musulmi wanda shi ke da ikon yi wa Muminai sanarwa. Sanarwa sai ta yi yawa kawuna ka rarrabuwa, in ta zama ɗaya muradi ya biya. Allah Ya sa an fahimce ni.

Ganin Ido da Matsalolin da ke Tattare da shi ga Haɗin Kai
          Tul fil azal tunanin Sunna a kan ido ya dogara. Da baya abubuwan da ke haddasuwa suka haddasu aka shiga zarge-zargen wasu masu iƙirarin sun gan shi da ido. A irin zamaninmu saka kwamitin da zai tantance waɗanda za su ba da shaidar ganin wata ba laifi ba ne bisa ga doguwar fassarar wani hadisi da Manzo (SAW) da ya nemi tabbacin Musuluncin wanda ya kawo masa shaidu. Ayar da ke cewa:
Fa man shahida minkumul shahara fal ya sumhu…
(Sura ta 2 aya 185).

Wannan nassi babu tawilin da zai sa Mumini ya yi ido da ido da wata a jinkintar da shi musamman idan mun yi duba zuwa ga salsalar nassin gani da ido, da Allah ke bai wa Annabi Musa (AS) labarin cewa bayan ya baro mutanensa sun koma bautar ɗan maraƙi Musa bai yo kokanton labarin da Allah Ya ba shi ba, amma da ya dawo ya ga abin ƙuru-ƙuru me ya faru?
Nassi:         Wa lamma raja’a Musaa ilaa ƙaunihii gadhabaanaa asifaa ƙaala bi’isa maa khalaftumuuni min ba’adii. A’ajiltum amra rabbikum wa alƙal arwaaha wa akhaza bi ra’asi akhiihi yajurruhu ilaihi…

Tarjama:     Kuma lokacin da Musa ya koma zuwa ga mutanensa, yana mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: ‘Tir da abin da kuka yi mini wakilci a bayana! Shin kun nemi gaggawar umurnin Ubangijinku ne? Kuma ya jefar da allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan’uwansa yana jan sa zuwa gare shi.
(Sura ta 7 aya ta 150)
Fassarar Abubakar Mahmud Gummi.

          Ai lokacin da Allah Ya ba shi labari bai yi jifa da Allunan ba, don me da ya gan su ƙiri-ƙiri ya watsar da su? Ɗan’adam ke nan, ya ga abu da idonsa ka ce ya bari shi, ko ka ƙaryata shi, ba ka nemi ya saurare ka ba. Yadda za mu magance wannan matsalar kada ta raba muna kanu shi ne, duk wani mataki da za mu ɗauka kada mu yarda ya yi takin saƙa da waɗanda suka gani ƙuru-ƙuru, a dakatar da kowane uzuri a bi waɗanda suka gani. Duk wani tunani da bai mara wa sahihin gani da ido ba, a jingine shi.

Gurbin Sarkin Musulmi ga Haɗin Kan Ganin Wata
          Allah Ya yi umurni a yi masa ɗa’a, a yi wa Manzo ɗa’a da waɗanda aka jiɓintar da al’amurranmu a kansu. Abubuwa uku ke wajabtar da ɗaukar azumi kuma bi-da-bi suke a fiƙihunsu. Ganin ido ƙarara, umurnin Sarkin Musulmi da cikan Sha’aban kwana talatin. Sarki na da ikon tabbatar da shedu da soke shedu bisa ga ilmin da yake da shi na kansa ga masu ba da sheda. Yana da damar kafa wata ma’aikata ko kwamitin da zai taya shi aikin ganin wata. Matsalar da ake ciki a nan ita ce, shin Sarkin Musulmi na da ikon soke rahoton da ma’aikata ko kwamitin da ya ba alhakin kula da ganin wata a ƙashin kansa bayan sun tantance sun tabbata an gani ko ba a gani ba? Ga alama Sarki ba ya da wannan iko, domin nassi ya tabbatar da cewa in sarki kaɗai ya ga watan azumi ba da kowa ba, azumi a kansa zai tsaya, sauran jama’a su shiga sha’aninsu sai an samu tunfayar sharaɗin da shari’a ta bayar.

Shawarorin Haɗin Kai a Ganin Wata
          Babu nassi sahihi da ya tilasta kyakkyawar harda da tilawa ko sanin ilmin Hadisi ko wata takardar shaidar kammala karatu ko tazkiyya daga wani ko wasu mutane gabanin a karɓi shaidar mutum na ganin wata. Abin sani a nassi kawai shi ne wanda ya gani ya tunkari sarkinsa ko hukumarsa ko shugabansa ya nuna masa ko su tafi tare da wani a gani, sauran bincike-bincike a bar wa Sarki da Majalisarsa. A tunanina ga wannan takarda akwai buƙata babba ta gaggawa ga gwamnatin Sakkwato na:
1.     Ta fito da wani sashe daga cikin sassan ma’aikatar kula da lamurran addini da zai kula da ganin wata. Ya zama yana mai taimaka wa Sarkin Musulmi ga ɗawainiyar da Allah Ya ɗora masa.
2.     A matakin gaggawa, Musulminmu na kowane ɓangare su kafa ƙaƙƙarfan kwamiti a kowace Ƙaramar Hukuma da zai agaza wa Sarkin Musulmi ga ganin wata.
3.     A sa kwamitin da zai ɗauki nauyin karɓar rahoton ganin wata daga Muminai tun daga faɗuwar rana har ketowar alfijiri ko safiya, domin a wasu shekaru da suka gabata 1975/76 bayan sallar Azahar labarin ganin wata daga Sarkin Musulmi ya sadu da garin Bunza, aka umurci kowa ya yi kamun baki.
4.     A yi taka-tsantsan duk wani wanda ba almajiri ba, komai kusantarsa ga fada ko gwamnati, komai iya daɗin bakinsa da ladabinsa kar ya yi wa matsalar karatu shigar kutse na tozarta karatu da ma’abotansa.
5.     A yi wa shugabanci ɗa’a, a daina cin zarafi da fuska na shugabanni ko da an ga kurakuransu. A sa hikima wajen gyara musu domin samin haɗin kanmu. Su kuwa shugabanni su sani Allah da ManzonSa suna gaba gare su don haka ƙin jiransu idan suka yi ɗemuwa ko suka sa nawa ga karɓa kiran Allah da Manzo (SAW) ba tawaye ba ne, umurnin Allah ne na:
Wa saari’uu ila magfiritin min rabbikum wa jannaatin arduhaa…

Naɗewa
          A ko’ina Musulmi yake a duniya ya sani cewa babu nahiyar da babu Musulmi. Musulmin duniya duka sun yarda da azumi, kuma sun yarda a watan Ramalana ake gudanar da shi gabanin ketowar alfijiri zuwa faɗuwar rana. Allahu Akbar! Sai ga shi yanayin duniya ba ɗaya ba ne. Lokacin da muke sahur da buɗin baki, ba lokutan ake yi ba a Saudiyya da sauran ƙasashe. Wata duniya suna azumi ba su taɓa ganin rana ba, sai dai su yi kirdado. Wata duniyar rana katar take ba ta faɗuwa na tsawon watanni haka nan suke azuminsu. Ranar Jumu’a gare mu a wasu ranar Lahadi ce. Yaya za a yi, a yi azumi iri ɗaya a duniya? Wannan ta sa dole mu sassabto da ra’ayoyinmu mu nemi yardar Allah, rarrabuwa azaba ce, saɓani musiba ce, daɗa juna sani ba ya buƙatar raba masallatai. 


MANAZARTA
Alfark, Ƙadhii Abu Ya’alii Muhammad bn. Husaini (1994) Ahkaamul Sulɗaniyya. Lebanon.
Alkanawiyyu, Imam Abdul Hayyi (2000) Alfiƙhud Diwaari fi Ru’uyatil Hilaali Binnahaari, Lebanon: Daaru Ibn Hazam.
Al-Maawardi, Abil Hassan Aliyu bn Muhammad bn. Habiibul Basrii Albagdaadi, Ahkaamul Surɗaniyyati Wal Wilaayatil Addiniyya.
Almalkanuwwi, Imam Abdul Hayyi (2000) Alƙaulul Manshur Fil Hilaali Khairus Shuhuur, Daarul bn. Hazam.
Bunza, Aliyu Muhammadu (2001) Haɗuwar Idin Layya Da Tsayuwar Arfa. Sokoto: Milestone Information and Publishing House.
Bunza, Aliyu Muhammadu (2009) “Inkarin Yanka Layya Goma ga Zil-Hajji: Nassi Ko Tawili?” Takarda, Zaria: Ahmadu Bello University.
Bunza, Aliyu Muhammadu (2009) “Me ya Haɗa Layya da Arafa a Shari’ance?” Takarda, Bauchi: Jama’atil Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatis Sunna, Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa.
Bunza, Aliyu Muhammadu (2012) “Gurbin Sarkin Musulmi a Ganin Watan Azumi”, takardar da aka gabatar a taron ƙasa-da-ƙasa mai taken: Ganin Wata da Haɗin Kan Musulman Nijeriya: Tafarkin Ci Gaba, Ƙarƙashin Kulawar Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto da Gwamnatin Jihar Sokoto da Majalisar Sarkin Musulmi da Jama’atu Nasaril Islam, Babban Masallacin Abuja.
Bunza, Aliyu Muhammadu da Bunza, Mukhtar Umar (1994) Ganin Watan Azumi: Laluben Haƙiƙanin Lamarinsa Cikin Hadissan Annabin Rahama, Sokoto: Sidi Umar Press.
Gummi, Abubakar Mahmud (n.d.) Alƙur’ani Mai Girma Da Kuma Tarjamar Ma’anoninsa Zuwa Harshen Hausa. Maɗaba’ar Buga Alƙur’ani Mai Girma Na Saudiyya.
Ibn Abdulazeez, Muhammad Amin bn. Umar (2000) Risaalaati Tanbihul Gaafili Wal Waswani Alaa Alkaa-il Hilaalil Ramadaana Lebanon: Daaru Ibn Hazam.
Ibn Taimiyya, Shaikhul Islam Ahmad (1995) Risaalatil Fiƙhis Swiyaami. Daarul Fikr.
Mandawari, Yusuf Uba (1995) Shin Za a Yi Sallar Idi Ranar da ake Arfa? Kano:  W. F. Ɗandago.
Memon, Sheikh M. Ibrahim (n.d.) Moon sighting for the Month of Ramadan. Darul Uloom Almadina, Buffalo N Y, USA www.zaytuna.org/articledetails.asp?articleID=100 
Sheikh Salman (n.d.) Hilal Sighting and Islamic Dates: Issues and Solution Inshaa Allah. www.hilal.sighting.org/papers/salman.pdf.

No comments:

Post a Comment