Monday, October 14, 2019

Kunya Ginshiƙin Tsaron Ƙasa Da Bunƙasarta



Kunyar da ke tsakanin yara da manya ita ta wanzar da zaman siyasar shugabancin ƙasar Hausa ta fi kowace biyayya tsakanin masu mulki da moro. Da Musulunci ya zo, kunyar ta faɗaɗa tsakanin malamai da ɗalibai. Tsare wannan kunyar ya hana wanzuwar yi wa masu iko tawaye da zanga-zanga, ya toshe rigingimu irin na addini tsakanin mabiya da shugaba ko malamai. Rashin kunya ne yin sa-in-sa da shugaba ko malami.

Kunya Ginshiƙin Tsaron Ƙasa Da Bunƙasarta
 
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Harsuna da Al’adu
Tsangayar Fasaha da Ilimi
Jami’ar Tarayya Gusau

Gabatarwa
          Hausawa na cewa, lokacin abu a yi shi. Amfanin binciken ilmi ya tunkari halin da mutanen zamaninsa suke cike gadan-gadan bisa sharuɗa uku: In dai ya haska musu haske ga abubuwan da suka shige musu duhu; ko ya tunatar da su ga abin da suka manta; ko ya ba da dabarun murƙushe matsala a gama da labarinta. Irin halin da ƙasarmu take ciki na rashin tsaro, babu wani ci gaba da zai yi amo a more shi domin babu kwanciyar hankalin tunkararsa. A tunanin wannan bincike, matsalar tsaro Kurar Gardi ce,[1] ta shafi kowa da kowa, ba ta da ɗan kallo sai dai abokin a gudu tare a tsira tare. A Bahaushen tunani, tsaro gina shi ake yi tun bunƙatarsa ba ta taso ba,[2] idan buƙatarsa ta taso duk ‘yan dabarun tunkararsa za su kasance kuwwa baya ga yaƙi. A kan wannan hasashe, na zaɓo wani ginshiƙi daga cikin taskokin al’ada, wato Kunya in yi garkuwa da ita wajen gina tunanina na hangenta ɗaya daga cikin manyan makaman tsaro na gargajiyar Bahaushe kuma nagartaccen maganaɗiso na bunƙasar ƙasa da mutanenta. Ɗaukan matakan soje na magance matsalar tsaro, kwalliya ce da ba ta taɓa biyan kuɗin sabulu ba.[3] Da mun yarda da ‘Karen da duk ya yi cizo da gashinsa ake magani’, dole mu ba al’ummarmu dama su magance matsalolinmu.[4] Don haka na zaɓo kunya a matsayin karan gwajin dahi.

Dalilin Bincike
          Nijeriyarmu ta ƙarni na ashirin da ɗaya ba ta da wata matsalar da ta kai mata ko’ina kamar matsalar tsaro. Rikice-rikicen ƙabilanci da ɓangaranci da yanki da siyasa da addini sun yi muna katutu.[5] Ana cikin wannan, guguwar rikicin makiyaya da manoma ya ɓullo kamar ta fi kowacensu bala’i da haɗari.[6] Ba a ko kai tsakiyar shafukan karatunta ba sai ga bala’o’in satar mutane da garkuwa da su da saka musu kuɗin fansa.[7] Musiba ta fyaɗen yara mata da maza sun zama ruwan dare, babu yanki na ƙasar nan da ya kuɓuta.[8] Wata baƙauyar al’ada da aka fi ƙarni ɗaya da mantawa da ita ta sake sabon fasali da tsari ta mamaye mu wato tsafe-tsafe na burin tara abin duniya da mallakarta.[9] A tarihin duniyar mutane, babu ƙasar da za ta samu kanta cikin ire-iren waɗannan matsaloli face ta durƙusa. Shawo kan waɗannan matsaloli sun fi ƙarfin ‘yan doka, sun gagari wakilan tsaro, sun turmuje barazanar ƙarfin soje, an wayi gari ƙasa ta kasa zama ga hannun kowa lafiya. A kan wannan nake son mu jarraba tunanin Bahaushe na cewa, da tsohuwar zuma ake magani. Mu manta da tunanin mai rabon ganin baɗi ya gani. Mu sani, in dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Idan rashin tsaro ya yawaita dole ƙasa ta wargaje kowa ya kama gabansa kamar yadda malamin kiɗa Ibrahim Narambaɗa ke faɗa:
Jagora:        Yau mai ashararu ya kaɗe
                   :Duniya ta yi mai fashi
Yara            :Babu zama garai zaman fitina yat tayas
                   :Ya san ba a ƙwarjini ga mutanen Hausa
                   :Kowac ce shi na iyawa ga hili nan
                   :Sai ya ƙetare gidanai ba ban kwana.
Gindi          :Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
                   :Baban Dodo ba a tamma da batun banza.



Tambayoyin Bincike
          Wannan takarda tana son ta tunkari wasu muhimman tambayoyi na tsaro da yadda al’adar kunya za ta magance su. Da yi wa barazanar tsaro riga-kafi da yi masa tanadi wane ya fi amfani ga samar da nagartaccen tsaro? Da ‘da ƙyar na tsere’ da ‘da ƙyar aka kama ni’, wane ya fi amfani ga mai ba da labari? A tunanin ma’abota basira, yason rijiya ya fi gina sabuwa sauƙi da kai ga wadatattun ruwa. In haka ne kuwa, yaɓi ya fi aza tubalin sabuwar katanga samun gawurtaccen bango. Idan za mu yi amfani da dabarun al’adunmu wajen warware matsalolin tsaronmu kamar muna yason rijiyarmu ne da muka gina da hannunmu ko yaɓi ga katangarmu da ruwa ya zaizaye. Yin ko oho da kyawawan al’adunmu shi ya dabirta tunanin matasanmu, tsaron ƙasarmu ya salwance ga hannun mariƙansa. Tambaya a nan ita ce, shin a ci gaba da yadda ake tunkarar tsaron ƙasa a tsarin salon kare jini biri jini, ko a shiga salon a taɓa kiɗi a taɓa karatu? A tunanin Bahaushe, ‘rabon faɗan Sarkin Aljan ba ya da fa’ida’, domin:
                   Shi ya tarar da yara uku na faɗa
                   Ya kama ɗaya ya karya wuya(nsa)
                   Ya kama ɗaya ya ƙwaƙwale idanu(nsa)
                   Ya kama ɗaya ya jefa matacciyar rijiya
                   Ya ce: Ba don mun zo rabo ba da faɗa ya ɓaci.

          Tambayoyin wannan bincike suna son a kauce wa irin wannan rabon faɗa a yunƙurin inganta tsaro da kawar da ta’addanci. Idan al’ada ta riga ta hango irin wannan mummunan rabon faɗa me zai hana a tambaye ta dabarun da za su hana aukuwar faɗan, da dabarun kawo zaman lafiya da za su sa a manta da faɗa gaba ɗaya?

Dabarun Bincike
          A tunanin Bature, idan ba a son a yi yaƙi a tanadi kayan yaƙi (If you want aɓoid war be raedy for it)”. Dalilinsu shi ne, ba a taɓa yaƙi ba sai da abokin yaƙi, idan abokin yaƙi ya hangi an tanadi kayan yin artabo da shi na har abada dole ya mayar da takobinsa kube. Rahotannin ta’asar rashin tsaro a ƙasarmu da muke sauraro da kallo a kafafen yaɗa labarai da sadarwa su ne matakin farko na bincikena. Na ɗan kiyaye yadda suke aukuwa, sakamakon aukuwarsu, da waɗanda ke taka rawa a ciki, da yadda wakilan tsaro da na bayan fage ke sharhi a kansu. Haka kuma, na saurari jawaban wasu da ake tuhuma da waɗanda suka yi iƙirarin da hukuncin da aka yi musu. Domin kwakkwahe bayanai na harari sassan adabin baka da dama da ke da alaƙa da tsaro da dabarun inganta shi da sasanta saɓani cikin waƙoƙin baka da rubutattu da tatsuniyoyi da wasanni da karin magana da labaran gargajiya da ƙagaggun labarai. A mataki na uku, aka waiwayi wallaffun ayyuka na masana da kundayen bincike musamman na manyan digiri MA da PhD da ke da alaƙa da aikina. Daga nan sai na shiga rangadin zaƙulo rawar da kunya ta taka a al’adance cikin farfajiyar tsaro musamman wajen riga kafi ga matsalar tsaro. An yi yawo da kunya cikin sassan adabi da aka leƙa tare da auna ta cikin ayyukan ilmi da aka gayyato don nazari. ‘Yan tambayoyin da aka yi wa jama’a domin daidaita zaren tunanin binciken sun taimaka ainun wajen gina wannan aiki.

Ra’in Bincike
          Ba dole ba ne kowane bincike ya ginu a kan wani ra’i ba, amma samar masa ra’i wata kadada ce ga ƙara fito da tunani a sarari.[10] A iya tunanina a farfajiyar wannan bincike zai girku tangaram ga tunanin Bahaushe da ke cewa: “Da tsohuwar zuma ake magani”. Wannan tunanin yana tabbatar da cewa, tafiya da waiwaye tana maganin mantuwa. A koyaushe, na gaba idon na baya ne, domin abin da gaba ta hango a zaune, baya ko ta daka tsalle ba ta hango shi. Tunanin Bahaushe na haɗa kalmomin suna uku: tsohuwa, zuma, da magani, wuri ɗaya abin tunani ne. Tsufa, gabaci ne na an ga jiya, da yau, an shirya wa fuskantar gobe. Zuma, Bahaushe na yi mata kirari da “ga zaƙi ga halbi” haka nan gaskiya take a kowace matsala aka sawo su sai wani ya ji ba daɗi, wani ya ji an yi daidai susa gurbin ƙaiƙai. Kalmar magani harshen damo gare ta. Tana ɗaukar warkar da cutar gaɓɓai, ko cutar zuci, ko shawo kan wata matsalar da ta hana wa mutane miƙe ƙafafu su wala. A ra’in wannan bincike, “tsohuwar zuma” ita ce kunya, maganin da ake son ta yi shi ne, girka tubalinta a zukatan ‘ya’yanmu ta yi tasiri sosai yadda za ta hana su tunanin aikata kowane irin aikin assha wanda al’ada ta yi kadada da kunya a ciki. Idan aka ci nasarar shayar da ‘ya’yanmu tsohuwar zuma (kunya), ayyukan da ke haddasa ta za su kau a samu nagartaccen tsaro a ƙasarmu. A ko’ina kunya ta baje haja rashin kunya zai kau, kyawawan ɗabi’u su wanzu, zaman lafiya da lumana su samu.

Mece ce Kunya?
          A tsarin al’adar Bahaushe, kunya suna ne mai ɗaukar kowane jinsi a tsarin wasu karuruwan harshen Hausa. A daidaitacciyar Hausa, a kan ce: “Kunya ce” a karin harshen Zazzau da Yawuri a ce: “Kunya ne”. A tsarin jinsi namiji “ne” makunyanci; mace ita ce makunyaciya, jam’insu makunyata. A nahawun kunya tilo ce ba ta da jam’i. Duk da haka kalmar na sarrafuwa ga waɗanda aikinta ya riska a ce; namiji kunyatacce, mace kunyatacciya, jam’i kunyatattu. A nahawun Hausa kunya ba ta da launi, amma in ta yi tsanani a kan surka mata baƙin launi a ce: “baƙar kunya”. Bugu da ƙari a tsarin nahawu tana cikin sunayen da ba a gani kamar gaskiya da ƙarya; ba ta da ɗanɗano da samata; jin ta ake yi a zuci ta rufe idanu da hankalin tuwo, ta wanzar da kasala da mutuwar jiki, mutunci da ƙima su zube ga idon ‘yan kallo.[11]
          A ma’aunin al’ada, kunya wani aiki ne ko furuci ko shiga wani hali da al’ada ta zarga ta yi tir da shi ko ta kushe shi.[12] A tunanin Bahaushe, abin da ya tabbata kunya a al’adance, da yin sa ko shiga cikin halinsa, da kallon mai yin sa ko wanda ya auka cikin halinsa, da ba da labarinsa, duk kunya ce ga wanda ya san kunya. A Hausance, wanda ba makunyaci ba, ba ya iya ba da labarin kunya da kallon kunya ko makunyaci yayin da yake aikata aikin kunya. Kunya a wajen Bahaushe raɓo ne ko kaya, wanda duk ta shafa ko ya ɗauko kayan ya jawo abin tozarta da shi da zuriyarsa.
          A walwalar zamantakewa, kunya wani nau’i ne daga cikin nau’o’in tarbiyar Bahaushe. Ta ginu cikin al’ada, an sha ta a mama, a ko’ina mai ita ya je tana cikin jininsa. Hulɗarsa da abokan zamantakewa da ayyukan da yake gudanarwa da gaɓɓansa da na furuci a baka, duk suna kiyaye da kunya. Saboda, kunya wata irin aƙida ce wadda mai ita ko’ina ya shiga ko da babu mai ita, shi yana kiyaye da ita. Kai hatta shi kaɗai yake, babu wani mutum tare da shi kunya ta mamaye shi sai ya ji ta. Dubi misalin Bahaushe ya ɓarka tusa mai tsananin ƙara shi kaɗai a jeji ko zawayi ya kuɓuce masa ya fara fita tun yana tsaye, sai ya waiga ya waiwaye ko’ina cikin kunya ko da ba kowa tare da shi. Bisa wannan hasashe za a gane kunya tarbiya ce da ake koyo, a koyar, a tashi da ita a amfana, a amfanar. Ga yadda bincikena ya fuskanci tsarin karatun.

Zubi da Tsarin Kunya
           A falsafar tunanin al’ada kunya ta shafi dangantakar mutum da mutane ta fuskar zamantakewa da mu’amala. Zubi da tsarin kunyar Bahaushe ya game tarsashin kowane nau’i na zubi da tsarin mutane ta yadda babu wani ɓangare na mutane da aka baro. Zubi da tsarin kunya yana da gurabu goma sha ɗaya kamar haka:
1.     Kunya ta iyaye.
2.     Kunya ta sarakuta.
3.     Kunya ta jinsi.
4.     Kunya ta malamai.
5.     Kunya ta ɗalibai.
6.     Kunya ta manya.
7.     Kunya ta yara.
8.     Kunya ta shugaba.
9.     Kunya ta talaka,
10.  Kunya ta taro.
11.  Kunya ta ‘ya’ya.

Idan muka nazarci zubi da tsarin kunya a ƙasar Hausa za mu ga cewa wata makaranta ce babba. A fannin tarbiya muna da kunyar iyaye tsakaninsu da ‘ya’yansu, kowanne na jin kunyar wani ya riske shi cikin aikin kunya. Tarbiya kuwa a gida take farawa. Wannan zai tilasta iyaye su kasance masu natsuwa da kamun kai, ‘ya’ya su zamo masu biyayya. Yaran da ba su samu irin wannan kulawa ba, su za su kasance fanɗararru su zamo matsala ga iyayensu da al’ummarsu su kasance wata babbar ƙofa ta barazana ga tsaro. A fashin baƙin bakandamiyar Malam Muhammadu na Birnin Gwari, ya ce:

                   Su ne ɓarayi su ne ‘yan fashi
                             Su ne maneman matan duniya.[13]

          Sata da fashi da karuwanci su ne tushen ta’addanci a Nijeriya. Gabanin gurɓatar ƙasarmu, Gwamna Lugga ya tabbatar da cewa, mace na ɗaukar masakin zinari daga Sakkwato har Bida ba tare da an yi mata fashi ba.[14] A tuna, ba wani tsaro ba ne a lokacin face kyakkyawar tarbiyar iyaye ga yaransu na sanin cewa sata da fashi da karuwanci kayan kunya ne.
          A zamantakewar iyali, kunyar sarakuta ita ce babba. Surukai su ne iyaye na biyu a matakin al’adar Bahaushe. Iyaye a da suna kaffa-kaffa ga aurar da ‘ya’yansu gidan da babu kunya domin kauce wa samun zuriya maras kunya. Shuka zuri’a ta gari ita ce tushen tsaron kaya da mutunci da bunƙasar ƙasar Hausa. Idan an yi kuren wannan a tsaro, an yi kuren kyau tun ranar haihuwa. Ashe gaskiyar iyayen yarinyar da Shayaye ɗan gidan Labbo ya nema aure suka tambayi wakilinsa Kassu Zurmi ga yadda hirar ta kasance:
Iyaye:          Shin ɗa na?
Kassu:         Ɗa na tunda an ka haife shi.

          Daga cikin rawar da kunya ta taka wajen kiyaye tsaron rayuwa, mutunci da dukiya akwai kunyar jinsi. Irin wannan kunyar ce ke tsakanin mace da namiji ko da ba a taɓa sanin juna ba.[15] Kunyar da ke tsakanin budurwa da saurayi ko an yi aure an hayayyafa ba gushewa take yi ba. Haka ta haifar da tsaron mutuncin juna da kawo zaman lafiya ga ƙasa. In ba a wannan gurɓataccen zamani ba, adabinmu bai san mace na kashe mijinta ba, bale abin da ta haifa ko ta haɗa baki da ɓarayi a yi masa sata ko a sace shi ko a kashe shi. Duk tsananin kishin kishiyoyi sai dai a yi cacar baki in an matsa a yi ‘yar kokawar ɗebe raini. A yau kashe-kashe ne, da kashe ‘ya’yan juna, da cire wa miji mazakuta ko a yi masa yankan rago.[16] Me ke damuwar ƙasashenmu da ya fi wannan? Cire wa mata kunya a ido shi ne musabbabin ta’addanci a duniyar ƙasar Hausa.
          Kunyar da ke tsakanin yara da manya ita ta wanzar da zaman siyasar shugabancin ƙasar Hausa ta fi kowace biyayya tsakanin masu mulki da moro. Da Musulunci ya zo, kunyar ta faɗaɗa tsakanin malamai da ɗalibai. Tsare wannan kunyar ya hana wanzuwar yi wa masu iko tawaye da zanga-zanga, ya toshe rigingimu irin na addini tsakanin mabiya da shugaba ko malamai. Rashin kunya ne yin sa-in-sa da shugaba ko malami. Ga dukkanin abin da adabinmu ya kalato, Turawan mulkin mallaka suka kawo wannan aƙidar ƙasarmu. Yau ga shi ta zamo ɗan zane ta hana a samu tsaro, ƙasa ta kasa zuwa ko’ina. In ba mu yarda da tsohon zuma ake magani ba, babu wani Kafinol ko ƙwayar magani ta asibiti ko soje ko baƙo da zai kawo muna tsaro a yau.
          Idan babba ya yi magana, wane yaro ya ƙalubalance shi! Ko da akwai kuskure, sai dai manya su yi gyara, kuma ba gaban yaro ba, ka da a kunyata gabaci. Don haka, gabaci na da tabbacin ɗa’a da biyayya ga na baya. Kunyar gabaci ta sa ba a taɓa samun juyin mulki ba a ƙasar Hausa gabanin gurɓatacciyar duniyarmu. Rashin tsaro a yau yana da alaƙa da ƙeƙashewar idon yara suka mayar da kunya alewa, rashin kunya ya zama mazarƙwaila. Yaro na iya zagin babba, shi kuwa na baya gare shi su yi masa yadda ya yi. Mece ce matsalarmu a yau ba wannan ba?
Abubuwan da ke Haifar da Kunya a Bahaushen Tunani
          A tunanin Bahaushe, abubuwan da ke haddasa kunya su ne musabbabin rashin tsaro da ta’addanci da tauye ci gaban zamaninmu. Da za nisance su, kunya za ta girku a zukata a samu al’umma mai natsuwa da hangen nesa. Daga cikinsu akwai:
1.     Laifi
2.     Ƙarya
3.     Fuska biyu
4.     Raki
5.     Kure
6.     Tsegumi/tsince/raɗa
7.     Mantuwa
8.     Katoɓara
9.     Waskiya
10.  Bugun gaba
11.  Saɓa wa al’ada

Manyan laifuka irin su sata da maita da kwartanci da fyaɗe da kushili, laifuka ne da babu mai son a danganta shi da su. Aikata su na sa a bar gari na har abada a je wata ƙasa nesa a tuba ko a mutu. Ƙarya da Tsegumi da fuska biyu, na sa a turke mafaɗansu cikin taro domin ya kunyata ya daina. A mafi yawan lokuta bayan turke mutum wasu kan yi hijira irin ta wanda ya aikata babban laifi. Raki[17] da kure da mantuwa, al’adar kowane ɗan Adam ce, sai dai ba a son su ga nagartattun mutane. Idan suka yawaita sukan zama kayan kunya da za a yi wa mai su dariya ya ji kunya. Bugun gaba[18] shi ke haifar da katoɓara da waskiya. Ƙauracewar kunya ga mai ita ke sa shi bugun gaba a ga wautarsa a ji masa kunya. Da wuya a yi katoɓara,[19] waskiya[20] ba ta biyo baya ba.
          Bahaushe ya tanadi kunya domin ta ratsa dukkanin hanyoyin rayuwarsa ta yi msu tarnaƙi ga aikata assha. Al’ummar duk da ba ta yi tanadi ga ayyukan da mutanenta ke aikata wa ba, ba ta samun nagartaccen tsaro. Ƙarfin iko da tsananin doka ba su tsaron ƙasa a zauna lafiya in al’ada ba ta ratsa ba. Idan za a kula, rashin samun nason kunya ga wasu ƙabilu na sassan ƙasarmu shi ne musabbabin ta’addanci a ƙasarmu. Mai da karuwanci sana’a,[21] fashi da makami kasuwanci[22], damfara abin ƙawa,[23] ta’addanci abin alfahari,[24] tun shekarar samun ‘yancin kai 1960 suke cikin lalurar. Kasuwar al’adunsu na kunyatar da waɗannan miyagun halaye, ya sa duk wani aikin ta’addanci da rashin tsaro daga sassansu ƙurarsa take fara tashi. Duk al’ummar da al’adunta da adabinta ba su yi fito-na-fito da laifuka ba, tare da kunyatar da masu aikata su, da ƙaurace musu, ba ta da gambun da zai yi mata wadataccen tsaro.

Musabbabin Karya Tsaron Ƙasarmu
          Tunanin wannan bincike kunya ita ce kan takarda. Tsaron ƙasa mutane ke yin sa, rashin tsaro daga ayyuka da halayen mutane shi ke. Daga cikin abubuwan da suka rusa ginshiƙin kunya a ƙasar Hausa, suka dasa wayewar ci gaban mai ginar rijiya, suka wanzar da rashin tsaro na har abada akwai:
1.     Mulkin Mallaka.
2.     Siysa.
3.     Boko.
4.     Kutsen Baƙin Al’adu.

Cikakken Bahaushe a cikin tsarin sarautarsa ta gargajiya yana jin kunyar iko, iko na jin kunyarsa, sai ga huntu ubangijin mai riga.[25] A ko’ina suka bayyana, ta’addanci da yaƙi suna bayyana. Su suka fara wargaza sarakunanmu na gargajiya da naɗa irin nasu masu biyayya ga al’adunsu. Tuɓe sarki da naɗa shi ya zama wasan yara. Kashe sarki da tura shi gudun hijira ya zama ruwan dare. Miyagun ɗabi’unsu na shaye-shaye da suturar tsiraici da kuranye al’aura da luwaɗi da girmama shege da shegiya da damƙa iko ga ashararu, har aka wayi gari suka cutar da adabinmu da karin maganar: shege kowa ya yi. Tsarin karatun da suka zo da shi na hautsina maza da mata a kujera ɗaya ya hana wa kunya shaƙatawa a ƙasar Hausa. Jawo mata a karagar mulki wani kashin mummuƙe ne aka yi wa kunya. Yau a kafafen yaɗa labaranmu ake muzanta kunya ana yi wa matanmu ‘yan boko kirari da; “Kallabi tsakanin rawunna.” Da duk mata suka daina jin nauyin hulɗa irin ta zamantakewa da mazan da ba nasu ba, al’umma ta kunyata kuma makunyata za ta haifa. Yawaitar yara a gidajen marayunmu ya isa mu fahimci wani abu.
          Tsari irin na demokraɗiyya bai dace da irin tarbiyarmu da al’adunmu ba. Tsarin ya haifar da mata masu zaman kansu ‘yan siyasa, da kangararrun yara irin waɗanda ‘yan siyasa ke ɗaukar nauyin ba su kayan shaye-shaye su yi ta’addanci ga abokan adawa. Fashi da makamin da aka yi a Offa, Jahar Kwara shekarar (2018) da ya rutsa da rayuka (34) ya isa babban misali[26]. Bangar siyasa ta kashe kunya a zukatan matasa da jagororin hukuma. Idan matasa suka rasa kunya ƙasa ta gama rugujewa, idan masu iko ke ingiza matasa ga ta’addanci rashin tsaro ya zauna da gindinsa a ƙasa. Babu wani magani matuƙar ba kunya aka ba lokaci ta kai ziyara ba. Daga cikin kwamacalar demokraɗiyya baƙin al’adau suka shigo ƙasarmu. Waɗanda ba su gadi kunya ba aka ba su kiyon masu kunya. Shugaban mutane ya aikata wani aiki ko ya furta wata magana da kowa sai ya ji kunyarta ya share abinsa a yi dariya tare da shi. Hausawa cewa suka yi: Na gaba idon na baya; wurin da shanuwar gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta tsoma bakinta. Wa zai faɗa Sarki ya ci ɗunya?

Sakamakon Salwantar Kunya ga Tsaron Ƙasa
          Yadda gara ke cin abu kaɗan-kaɗan haka kunya ke ƙaura kaɗan-kaɗan har ta zurare ba a ankara ba, sakamakon ƙauracewar kunya ga matasanmu, da magabatanmu, ƙasarmu ta shahara fagen laifuka daban-daban, wasu ma ba a taɓa jin labarinsu a duniyar mutane ba sai a ƙasarmu.[27] Binciken wannan takarda ya harari:
1.     Yawaitar cin hanci da rashawa.
2.     Bazuwar kangararrun yara a ko’ina.
3.     Ta’addanci da aikata munanan laifuka.
4.     Zubar da mutuncin ƙasarmu a idon duniya.
5.     Hasarar nagartaccen shugabanci.

Babu ƙasar da ba ta tanada wa cin hanci da rashawa mummunan hukunci ba da zai tozarta mai aikata su. Hukuncin da aka fi yankewa na ƙoli shi ne kisa (yadda ake yi a ƙasashen Sin da Koriya). A ƙasar Hausa kuwwa ake yi wa ɓarawo. A kudancin ƙasarmu, taya ake cinna wa wuta a ƙona shi. A yau, gwamnoni da sanatoci da ‘yan majalisa da kwamishinoni nawa aka fallasa da inkwa a hannu an tasa ƙeyarsu zuwa kurkuku saboda sata kuma har yau ba a daina ba? Dukiyar ce ake ciyar da iyali, a haifi kangararrun yara. Sau nawa ake samun rahoton yaro ya kashe mahaifiyarsa ko mahaifinsa ko ƙanensa ko wansa saboda kuɗi?[28] A duniyarmu ta jiya, girma da ƙimar ƙasarmu ya zube ƙasa yaryas saboda rashin gaskiyar shugabanninmu a siyasance da hukumance. Da shugabanninmu da malamanmu na addini da jahilanmu babu wanda ya kuɓuta.[29] Kunya ta fita ido, kowa ba ya jin kunya a ce masa ɓarawo, aka wayi gari muka kasa samun nagartaccen shugaba. Komai ƙwazon shugaban da marasa kunya ke gewaye da shi, gaba da baya tasirinsa ba ya wani dogon amo.

Amon Kunya a Kadadar Adabi da Al’ada
          Kunya ba abar da za a saka wa mutane ce kai tsaye da rana tsaka ba. Cikin adabi da al’adun al’umma za a tsince ta jefi-jefi. Haka kuma, za a dinga kiyayewa da ita da huruminta har a tarbiyantu da ita. Daga cikin nason da kunya ta yi a adabi akwai karuruwan maganar da ke nuni zuwa ga irin matsayinta a al’adance irin su:
1.     Kunya muke tsoro mutuwa ta zama gado.
2.     Ɗa na barin halas don kunya.
3.     In malam bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba ya kunyar kayar da shi.
4.     Ashe kunya ba a ido kaɗai take ba.
5.     Kunyar maras kunya hasara.
6.     Ko mutuwa na jin kunyar idon mahaifa.

A cikin adabin waƙa, Alhaji Gambo mai waƙar ɓarayi ya hikayo tattaunawarsa da Sarkin Ɓarayi Nazaƙi Sakkwato, lokacin da Nazaƙi ya nuna sha’awarsa ga tuba daga sata. Ga yadda tattaunawar take:
Gambo:       Nazaƙi ka ce sata ka aje ta
                   :Don ka tcira ƙiyama ka aje ta
                   :Ko ka sake darajja ka aje ta
                   :Ko sake suna ban sani ba!
                   :In don ka tcira ƙiyama ka aje ta
                   :Koma ka yi sata in hwaɗa ma
                   :Ka cika littafinka baba
                   :Har na mawabta an ɗiga maka
                   :Har bisa bainai an rubuta

Nazaƙi:        Yac ce: Na tuba wurin Sarkin Musulmi
                   :Na tuba wajen Usmanu Gulma
                   :In nai sata an ka kammini
                   :An ka kai ni wajen Sarkin Musulmi
                   :Na gama kunya mai kalangu/ in hwaɗa ma

Gambo:       Ko baki nai bai ruhe ba
                   :Nac ce yau wace kunya za ka tsoro
                   :In ba kunyar lahira ba
                   :Don kowa suruki nai ya ishe mishi
                   :Tare da inkwa an tsare shi
                   :Anai mishi kuwwa ‘yar gaton uwa
                   :To wace kunya za shi tsoro
                   :In ba kunyar lahira ba?

          Ashe ɓarayin ‘yan bokokonmu kunyar lahira kawai ta rage gare su. Duk abubuwan da aka yi wa Nazaƙi an yi musu ba su daina fita dandali ana hira da su ba. Kaico! Sai akwai kai wuya ka ciwo.
          A fagen sake maganganun kunya irin na kotoɓara da soki-burutsu Garba Ɗanwasa Gummi ya ruwaito zancen kunya kamar haka:
Jagora:        Arne mai katoɓa da ɓarin baki
                   :Kai ka batunka ni ka ji ma kunya tai.
Gindi:          Ya sa ‘yan maza gudu ba da laɓewa ba.

          Kunya ta yi tasiri ga tarbiyar Bahaushe sosai, hatta da ɗaurin aurensa aka je tun gabanin bayyanar addinai saukakki idan an taɓa abin kunya gidan ango iyaye ba sa ba da ‘yarsu. Idan gidan amarya aka taɓa yin abin kunya, iyayen ango ba za su karɓi auren ba. An ce, wani Bahaushe na cikin kogi yana wanka bai iya ruwa ba, ya hangi surukinsa tafe ya nutse cikin ruwa har ya mutu. Ina ga surukin ya riski an koro shi ya yi sata ko ya yi shige? Idan dattijon Bahaushe ya faɗi magana aka ce ba a san da ita ba, sai zubar da hawaye saboda kunya. Yau shugabanni nawa ke shata ƙarya saman duron wurin yekuwar neman ƙuri’a a yayata a kafafen yaɗa labarai su share abin su. Idan za a tuna, saboda saɓa alƙawalin da Janar Yakubu Gowon ya yi Janar Murtala ya yi masa juyin mulki. Shi kuwa Audu Gusau yana Ministan Gowon ya zartar da jawabi a kafafen yaɗa labarai Janar Gowon ya nemi ya jaye maganar, sai ya ji nauyin a ce ya ce, ya dawo ya ce bai ce ba ya yi murabus. Me ya sa suka yi haka su dukansu ba don kauce wa tarkon kunya ba? Idan shugabanninmu haka suke a yau, wace ƙasa za ta gwada tsawo da mu?

Sakamakon Bincike
          Binciken wannan takarda da kunya ya yi bara wajen tabbatar da dugadugansa. An auna al’adar kunya da rawar da take takawa wajen tabbatar da tsaro ga ƙasa da bunƙasar da ita. Binciken ya tabbatar da cewa, matsalar tsaro ta kowa da kowa ce, domin tsaro ya shafi duk wanda ke farfajiyar da ƙasa ta kafa tutarta. Bincike ya gano abubuwa kamar haka:
1.     Ƙarfin iko, da ƙarfin soje, da barazanar wakilan tsaro, duk ba su isa su tabbatar da tsaro ba, ko su turmuje yunƙurin tarwatsa tsaro. Al’adun mutanen da aka tanada wa tsaro sun fi tasiri gare su da gina tabbataccen tsaro a zamantakewarsu.
2.     Luguden wuta, da ɓarin albarushi, da kwaninkwamin ba-ta-kashi, da artabu da ‘yan tawaye da kangararru, da ‘yan ta’adda, bai taɓa kawo zaman lafiya na har abada. Da ya yi, da mun gani a Iraƙi da Libiya da Afganistan da Kashmir, da Syria da Sudan da Nijeriya. Yadda al’amarin yake, Karen duk da ya yi cizo da gashinsa ake magani. Idan aka gina tarbiyar tsaro a zukatan mutane a ko’ina suke aƙidar al’adunsu ke tsaronsu.
3.     Duk ƙasashen da ke tinƙahon nagartaccen tsaro, ba da ƙarfin bindiga suka same shi ba, tsaro aka gina musu a zukatansu da zukatan wakilan tsaronsu.
4.     Taɓarɓarewar al’adar kunya a zukatan shugabanninmu, da rashinta ga matasanmu, da nisantarta ga talaka da moro da mai’akwai, shi ne musabbabin rashin tsaro a ƙasarmu. Ƙasar duk da kunya ke jin kunyarta ba wurin zama lafiya ba ce bale bunƙasa.
5.     Me ya sa a cikin tarihin kafuwar ƙasashenmu tun gabanin tarihi (pre-historic) ba a san fitattun ‘yan ta’adda ba, ko fitattun ɓarayi, ko fitattun kwarata, ko ƙungiyoyin asiri da na zanga-zanga ba? Al’adar kunya ta ƙi ba da sarari ga kowa a kan haka. Ta yi tir da su, kuma ta ƙi aminta a ba su masauki a kowane Bahaushen gani. Idan mun yarda gara jiya da yau, me zai hana a gayyato jiya wurin gyaran yau, tun da Hausawa cewa suka yi: “A gyara yau don gobe”.
6.     Babbar magana ita ce, lokaci ya yi na a gyara manhajar karatun boko gaba ɗaya. Al’adunmu da ɗabi’unmu da adabinmu su mamaye darussan da ake koyar da yaranmu a kowane fanni na boko. Mun gaji da haihuwa ɗiyan rana na kwashewa, iliminmu ya zamo na biyan buƙatun wasu ba mu ba. Al’adunmu sun isa tunkarar matsalolinmu da kawo muna tsaro a ƙasashenmu.

Naɗewa
          Magabata sun ce: “Sai akwai kai wuya ka ciwo”. Tunanin Bahaushe na gina kunya a zukatan yaransa cikin adabinsa da wasanninsa na gargajiya a harkokin mu’amalar cikin gida da waje, wani babban jari ne na tsaron gida da waje da mutanenta. A ganin Bahaushe, bakin wani ba ya suɗe wa hannun wani miya, kamata ya yi kowane tsuntsu a bari ya yi kukan gidansu. Ta’addanci da taɓarɓarewar tsaro da baya suka shigo ƙasar Hausa. Waɗanda suka yi dillancin kawo su da jingar dakonsu zuwa ƙasashenmu adashi aka yi da su har yanzu ba su gama zubi ba. Matuƙar muka yi wa kunya riƙon kasainar kashi sai rashin kunya ya yi muna kamun kaza kuku. Hankali shi ne turken kunya da an rasa shi kunya ba ta da wurin zama a zuciyar mutum. Shaye-shayen zamani da ke kwararowa ƙasashenmu kunya ce ake son a kuranye a zukatan matasan ƙasarmu ta rasa baya ta ruguje. Madalla da zancen Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa da ke cewa:  
                   Ga jin daɗi rayuwa samari ka bicewa,
                   Suna wasu ‘yan ƙwange-ƙwange don nuna ɓacewa,
                   Su sa takalmin da ba wuya za a karewa,
                   Su shawo tabar da hankali zai juyewa,
                             Su gigice don su samu damar ɓacinmu.
                   (Gaskiya Mugunyar Magana)


MANAZARTA
Abdullahi, J. (1970) Nagari Na Kowa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Acemoglu, D. and James, A. R. (2013) Why Nations Fail the Origins of Power, Prosperity and Poɓerty. London: Profile Books Ltd. 

Atuwo, A. A. (2009) “Ta’addanci a Idon Bahaushe: Yaɗuwarsa da Tasirinsa a Wasu Ƙagaggun Labarun Hausa”, Kundin digiri na uku (PhD), Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo. 

Birnin Gwari, M. (b.s.) Waƙar Bakandamiya. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Ltd.
Bunza, A.M. (2009) Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre.
Bunza, A.M. (2014) In Ba Ka San Gari Ba Sauran Daka: Muryar Nazari cikin Tafashen  Gambo. Cairo: Darul Muɗbu’at Publishing Company.
Bunza, A.M. (2015) “Labarin Zuciya a Tambayi Fuska: Saƙon Dariya ga Sasanta Tsaro a Farfajiyar Karatun Hausa”, takardar da aka gabatar a Sashen Hausa, Makarantun Harsunan, Kwalejin Ilmi ta Adamu Augie, Argungu.
Bunza, A.M. (2015) “Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato Abin Koyi ga Shugannin Zamaninmu”, takardar da aka gabatar da taron yini ɗaya da Centre for Intellectual Serɓices on Sokoto Caliphate ta shirya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A.M. (2015) “Zaman Lafiya ya fi Zama ɗan Sarki: Tunkarar Zaɓen 2015 a Nijeriya”. Takardar da aka gabatar a taron kyautata zaman lafiya a zaɓen da aka gudanar 2015 wanda Orphans of Huffaz Educational Foundation Birnin Kabi suka shirya.
Denham, M.D. Captain H.C. & Oudney (1826) Narratiɓe of Traɓels and Discoveries in North and Central Africa in the year 1822, 1923 and 1824. London: John Murray.
Ɗanfodiyo, U. (b.s) Wathiƙatil Ikhwani. Sokoto: Goɓernment Printers.
Lockhart, J.R.B. (1996) Clapparton in Borno. Koln: Rodiger Koppe Verlag.
Muri, A.M. (2003) “The Defence Policy of the Sokoto Caliphate 1804-1908”, PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Shehu, M. (2018) “Zaman Lafiya ya fi Zama ɗan Sarki: Tunanin Bahaushe a kan Zaman Lafiya da Sasantawa”, Kundin digiri na uku (PhD), Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Wali, M.S. (b.s.) Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana.


[1]An ce Gardi ke wasa da kura a fada sai ya lura da cewa takunkuminta ya kwance. Ya waigo ga Sarki ya ce: “Allah ya taimaki Sarki, yau kurar ta kowa ce.” Da faɗar haka, Gardi ya nemi agajin dugadugansa jama’a suka taya shi.
[2]Wannan daidai yake da tunanin Bahaushe da ke cewa: “Ba a fafe gora ranar tafiya.”
[3]Ga al’adar ɗan Adam a koyashe aka kai masa hari sai ya yi ɗaukar fansa. Mai musun haka ya dubi irin artabun da ake da ‘yan Boko Haram babu satin da ba su kai harin fansa ba. Dole a sake lale domin an ce amfanin dara a kasa.
[4]Muna da al’adar tsagaita wuta da sulhu da zaman yarjejeniya da mayar da takobi. A tunanin wannan bincike idan an ba kunya fage za a ci nasara.
[5]Bayan rikicin Kudu da Arewa, ga kangararrun Neja Delta, da ‘yan Ododuwa, ga ‘yan Biafara, ga Boko Haram ga Matsin Arewa, ga su nan dai.
[6]A Zamfara da Kaduna da Neja da Kabi abin ya fi muni. Daga shekarar 2016 - 2018 ana kirdadon a jihar Zamfara ‘yan ta’adda sun kashe fiye da mutane dubu (1000).
[7]Wannan ya tilasta wasu jihohi ƙago dokar kisa ga ‘yan samame amma duk a banza sai daɗa haɓaka yake.
[8]Abin ban haushi har jinjira ‘yar watanni uku an taɓa yi wa fyaɗe a ƙasarmu. Anya! Ba ƙarshen lokaci muke ba.
[9]A Kudancin ƙasarmu har kamfuna ke akwai da za a kai mata budare a yi musu ciki su haihu a biya su karɓe ‘ya’yan a yi tsafi (child factory). A duniyar tarihi, Nijeriya aka fara jin wannan musibar.
[10]Nagartattun bincike-binciken da aka yi a duniyar ilmi a da ba a ɗora su a kan kowane ra’i ba, kuma su na baya suka kafaɗarsu aka ji su a duniyar ilmi. Ina da fahimtar cewa, zantukan hikima na adabinmu cikin waƙoƙinmu da karuruwan magana sun cancanci a jinjina su ga ra’o’in bincikenmu. Tabbas! Kamata ya yi a kai na hannu gida kana a dawo a ɗauki na dawa.
[11]Idan kunya ta kama Bahaushe zai ce ya ji nauyi ya kasa zance, ya kasa ɗaga kai sama, duk ya rikice ya gigice.
[12]Laifukan sata da kwartanci da fyaɗe da kushili in an kama mai su za a nisance shi, a tilasta shi gudun hijira zuwa wata duniya ba ƙasar ba. Wasu tun ba a tilasta su ba za su gudu, wasu kuwa masarautar ƙasar ke sa a dasa ƙeyarsu zuwa iyakar ƙasarsu su fita ƙasar gaba ɗaya.
[13]Waƙar Bakandamiya ta Malam Muhammadu na Birnin Gwari. NNPC, Zaria.
[14]Wannan wani shahararren zance ne na Clapperton H. A dubi Denlam, Major D., Captain H. Clapperton and Dr. Oudney (1926) Narratiɓe of Traɓels and Discoɓeries in North and Central Africa in the Year 1822, 1823 and 1824. London: John Murray.
[15]Mujaddadi Ɗanfodiyo ya hikayo haɗurran haɗuwar mace da namji ta fuskar soyayyar da Allah Ya gina a cikin jikinsu a littafensa mai suna Wasiƙatul Ikhwani ya ce: Da akwai jijiyar namiji ɗaya a bangon gabas ta mace ɗaya a bangon yamma da kowannensu ya yi burin haɗuwa da ɗan uwansa saboda soyayyar da ke cikinsu. Don haka, kunyar da Hausawa suka gina tsakanin jinsin mace da namiji mai tushe ce.
[16]Jaridun ƙasar nan da dama sun zo da labarin mace da ta cire wa mijinta mazakuta don yana da budurwa. Wata matar Kwastam ta zuba masa guba ya mutu don zai yi aure. Mace ɗaya kawai aka samu ta faɗa kududdufin Legas ta mutu don likitoci sun gano ‘ya’yanta ba na mijin ba ne 10/6/2018.
[17]A dubi, Bunza, A. M. (2017) “Raki a Tunanin Bahaushe”, takardar da aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
[18]Shi ne yi wa kai kirari da kururuta kai ta kowace fuska.
[19]Katoɓara ita ce ɓaro maganar da ba ta gyaruwa. Wai an ce, Maikatoɓara koyaushe ya je fada sai an yi masa duka domin bai iya zance ba. Matarsa ta nuna damuwarta da kar ya ƙara yin zance a fada. Da ya je fada ya yi shiru da bakinsa. Fadawa suka ce: “Yau lafiya Maikatoɓara ba a ce komai ba?” Ya ce: “E, a koyaushe na yi zance Sarki ya sa a yi mini duka, yau Sarki ya doki uwarsa.”
[20]Waskiya ita ce toge maganar da aka yi kai tsaye tun ba a yi nisa ba. Dubi zancen Malamin Kiɗa:
Jagora:   Ga gidanka guda duniya
                                :Guda na Firdausi an yi
                                :Alhaji Ɗandurgu babu hwashi Aljanna kay yi
Yara:      In Allah Ya nufa
Gindi:    Alhaji Ɗandurgu taimakon Allah ag garai
                                :Na lura da duniya akwai namjin arziki.
[21]‘Yan Nijeriya da ake kamawa da laifin karuwanci a ƙasashen waje, ba Hausawa ba ne. Ba a taɓa kamo Bahausa ko ɗaya ba.
[22]Fashi da makami a Kudancin Nijeriya aka san shi kuma har gobe can ya fi yawan aukuwa. Wajajen shekarar 1980 - 1985 ya fara bayyana a Arewa. A Arewa ma za a tarar da na Kudu ne suka zo da abinsu.
[23]Damfara, ‘yan Ghana da ‘yan Kudancin Nijeriya suka zo da shi a Nijeriya ta Arewa.
[24]Daga fashi da makami aka ƙarasa gaba zuwa ta’addanci da ƙabilanci da ɓangaranci da yanki a siyasa. Bahaushe bai san da su ba, da baya aka shigo masa da su.
[25]Bature ke nan, ga shi cikin gajeren wando da ‘yar taguwa kamar ta aro amma shi ne shugaban Sarakuna masu manyan riguna. Huntu shi ne maras sutura.
[26]Akwai takaici a ce manyan ‘yan siyasar ƙasa da ake zargi da hannu cikin ta’addanci na fashi. Wannan rashin kunya har ina? Yaya ƙasa za ta ci gaba da shugabannin ta’addanci a matsayin jagora?
[27]A ƙasarmu kawai aka taɓa samun magidanta suka yi wa budurwa cikin shege ta haifi yaro, suka kashe shi aka ba karnuka naman suka cinye. Jaridar Aminya ta shekarar 2016 ta kawo rahoton abin ya faru a jihar Katsina.
[28]A garin Gusau shekarar 2016, Jaridar Aminiya ta ruwaito yaro ɗan jami’a ya kashe mahaifiyarsa da yayarsa saboda wasu ‘yan kuɗi ƙalilan.
[29]A cikin fafitikar farauto waɗanda suka ci kuɗin makamai wani tsohon gwamnan Arewa ya karɓi naira biliyan huɗu (N4bl) ya ce, ya raba wa malamai su yi addu’a. Pastor nawa ya sayi jirgin sama cikin wannan hada-hadar? Idan mutanen Allah sun yi tsamo-tsamo cikin yaudara, me za a cewa mutanen Shaiɗan?

No comments:

Post a Comment