Tun fil azal
karambanin leƙo abin da ya faku Bahaushe na kiransa
duba. A wata fassara idan ta shafi amfanin da wuri ana ce masa “arwa”. Bayyanar
Musulunci da wasu malamai suka durmuya ciki, a zauna, a harɗe, a share ƙasa, a
goge, ya sa ake yi masa suna da “Bugun ƙasa”. A
waƙar da muke nazari Alhaji Shata ya yi
amfani da “duba”. Ta kowace fuska aka yi karambanin gano gobe, ta carbi ce, ko ta
taurari, ko ta bugun ƙasa, ko
ta hisabi ko ta duban motsin wasu tsuntsaye da dabbobi, sunansa “duba”.
Ruwa Na Ƙasa
Sai Ga Wanda Bai Tona Ba
(Hisabin Waƙar
Malam Babba na Ƙofar Gabas Azare)
Daga
Aliyu Muhammadu
Buna
Gabatarwa
A watan Ogusta 1998 na gabatar da wata
takarda a kan wannan waƙa
na yi mata take: Malam ko Wani Babban Dodo: (Siddabarun Shiga da Fitar Mara Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas). A wannan
karo zan sake bitar karatun in kakkaɓe wa buzun karatun ƙura tare da faɗaɗa
bayani fa ƙyallaro
wasu sababbin abubuwa da ke muhimmanci ga mawaƙan da wanda aka yi waƙar da jigon waƙar. Binciken wannan
takarda zai tattara hankalinsa ɗungurungun kan ƙunshiyar waƙar ciki da waje.
Dabarun Bincike
Gabanin assasa wannan binciken na saurari
waƙar
daga bakin maƙaginta.
Bayan da na saurara na juya ta zuwa Hausar Boko. Na sake tuntuɓar
matanonin wasu waƙoƙin Shata da Sa’idu
Muhammad Gusau ya tattaro. Na ɗan jahilci tsakanin matanin da nake
da shi da wanda Sa’idu Gusau ya tattaro da waɗanda
ke a rediyo da garmaho akwai bambanci. Na yi ɗan
ƙoƙarin cike givin
tare da amfani abubuwan da na saurara kai tsaye daga Shata. Littattafai da
kundayen bincike da muƙalu
da aka yi kan Shata sun taimaka sosai ga wannan aiki. Tattaunawa da masu
sha’awar Shata da waƙoƙinsa ya ƙara mini kuzari. A iya
bincikena ba a taɓa wani aiki a kan wannan waƙa ba ta kowace fuska, don
haka akwai damar a sake faɗaɗa
shi bias ga wanda na yi a baya.
Ra’in Bincike
Kasancewar waƙa an gina ta a kan wani
ilmi mai cin gashin kansa wato “Hisabi” ba ya buƙatar wani dogon ƙidan baƙi. Ra’o’in al’ada da yawa
na daidaita da tunanin wannan waƙa
amma na ga ya dace a ce lokaci ya yin a mu kai na hannun gida kamin mu dawo mu
kama na dawa. Tunanin Bahaushe da aka gina cikin adabinsa ra’i ne da duniyar
tunanin Bahaushe (Hausa World View) ta haƙiƙance zamansa karatu. Bisa
wannan zubi, na ɗora bincikena a kan ra’in Bahaushe mai
cewa: “Sau nawa ake nema wuta a maƙera
a gan ta a maƙera?
A tunanin Bahaushe muddin an yi bincike ba a rasa gano wani abu ba.
Fashin Baƙin Matashiya
A tunanin wannan takarda gundarin waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas shimfiɗaɗɗiyar
ƙasa
ce da kowa ke samanta. Wanda yake da dabarar haƙar rijiya kaɗai
zai san wurin da za a gina a samu ruwa. Gundarin waƙar kamar hamada ne, sai
an shiga hisabinta za a tabbatar da cewa ruwa na ƙasa. Binciken zai kalli
waƙar
a tunanin masu hisabi. Hisabi shi ne, biyar diddigin abu ta fuskar lissafin
yadda yake da yadda yake faruwa da yadda yake sassauyawa da yadda maƙurarsa yake da karatun da
za a gano cikin lissafinsa. A kan haka, ko Shata da ya waƙar da Malam Babba na Ƙofar Gabas da aka yi wa
ita sai sun zo an nuna musu lissafin da waƙar ta ƙunsa. A tunanin wannan
bincike, hikimar hisabin da ke ƙunshe
a waƙar
ya fi waƙar
armashi da burgewa.
Duba a Ƙasar Hausa
Kowace al’umma da irin nata salon duba
da ta gada kaka da kannin. A ƙasar
Hausa bugun duba Mahdi ne mai dogon zamani. Tun gabanin saukakkin addinai a ƙasar Hausa, Bahaushe na
lisafin abubuwa da ke tare da shi ya ɗora camfe-camfensa na
duba a kansu. Daga cikinsu akwai:
1.
A laɓaɓa
gindin bishiya a daka ihu ko a doke ta tsuntsayen da ke kanta kowane waje suka
dosa nan ne sa’a take.
2.
A buɗe
akurkin kaji a je gefensa a tsaye a lura da wane wuri mafi yawansu za su bi.
Wurin da suke rinjaya nan ne sa’a take.
3.
Idan an ga yara na wasar
gudane-gudane da harbe-harbe akwai zaton yaƙi ya faru a shekarar.
4.
Idan an fito kasuwa aka
ci karo da makaho babu kanta a ranar wahalar banza za a yi. Idan kuturu da
kurma aka haɗu da su nasara ta
samu.
Waɗannan da makamantansu duk hanyoyi
duba ne na camfe-camfe, amma hannyoyin duba na ahƙiƙa waɗanda
suka yi canjaras da hisabi sun haɗa da:
1.
Lissafin kasa fasulan
shekara zuwa gida huɗu
Rani, Damina, Bazara da Hunturu.
2.
Lissafin gano kwanakin
fari da Malka ga manoma.
3.
Ƙididdigar
gano kwanakin shuka da kwanakin dashe da kwanakin shuka, da hatsi da mabunƙura ƙasa.
4.
Gano watannin ciki da ƙirdadon ranar haife shi.
5.
Rarrabe sawun ƙafar mutane da wurin da
suka dosa da rarrabe mai kaya, da wanda ke aguje, da mai tafiya, da na ƙato da matsakaici.
Waɗannan
abubuwa su suka haifar da bokanci da duba da siddabaru da sihiri a ƙasar Hausa. An yi ayyuka
da dama a kansu da yadda ake aiwatar da su Lewis, (1988) Last, (1998), Bunza,
(1988) Adamu, (1990) Handloff Safana (1982).
Duba a Adabin Hausa
Tun fil azal karambanin leƙo abin da ya faku
Bahaushe na kiransa duba. A wata fassara idan ta shafi amfanin da wuri ana ce
masa “arwa”. Bayyanar Musulunci da wasu malamai suka durmuya ciki, a zauna, a
harɗe,
a share ƙasa,
a goge, ya sa ake yi masa suna da “Bugun ƙasa”. A waƙar da muke nazari Alhaji
Shata ya yi amfani da “duba”. Ta kowace fuska aka yi karambanin gano gobe, ta
carbi ce, ko ta taurari, ko ta bugun ƙasa,
ko ta hisabi ko ta duban motsin wasu tsuntsaye da dabbobi, sunansa “duba”. Duk
mai wannan safarar sunansa ɗan Duba/Ɗanduba ko Malamin Duba
(idan har ya laɓe ga addini).
Adabin Bahaushe ya tabbatar da samuwar
duba da irin kallon da Bahaushe ke yi wa masu shi jiya da yau. A karin magana
muna da:
ü Ƙarya ƙasa malamin duba ya gano
ranar mutuwarsa.
ü Sai
Allah da Malaman gari.
A ƙagaggun
labarai muna da wani labari haka:
Wata
mata ce ragonta ya ɓata ta
je wurin mai duba, ya duba mata. A dinga zane yana sharewa. Yanzu ya ce: cikin
wata biyu, ya sake ya ce: “Ba za ta ci nasara a kanki ba (wato kishiya)”. Ya
sake ya buga ya ce: “Ba zai sake mugun abu da kika ce ba (wato maji)”. Ya ƙare
‘yan buge-bugensa duk bai ji matsar ta ƙara
masa ƙarfi ko ta nisa ba. Ya sake dabara ya ce:
“Boyar Allah me ke tafe da ke haka mai rikitarwa”? Matar ta ce: “Ragona ne ya ɓace ko aka sace”. Ya ce: “Haba!
Gaske dai nake ganin ƙaho, da
farin buzu da baƙi, an gamu, a gano
shi”.
A mahangar waƙoƙin baka “duba” bai ci
karo da kyakkyawan masauki ba. Makaɗa Narambaɗa
na kashe wani ɗan
adawa wanda yake yi wa waƙa
da cewa:
Jagora: Dub bayin Isa sun sake
Yara: Saura
mai bugun ƙasa
Jagora: Bayin Isa sun sake
Yara: Saura
mai bugun ƙasa
Gindi: Riƙa
aiki da gaskiya
: Komai
naka ya yi kyau
: Gardaye
na Garkuwa.
Marubuta waƙoƙin Hausa da addinin
Musulunci ya assasa ba su kalli duba da idon soyayya ba domin suna ganin wata
tsohuwar hanyar ɓat ace. Ga yadda Wazirin Gwandu Malam
Umaru ya ambace su cikin Waƙar
Yabon Sarkin Gwandu Yahya:
Malamman Tsibbu mu kukai?
Wane wankin alluna kukai?
Mai share ƙasa
ya swad da kai
Ko kai yada ba ka son ya kai,
shi ya kai
(Sa maza gudu).
Ɗan bugun ƙasa shi ne: “mai share ƙasa ya swad da kai”
Waziri ya ambace su da lafazin ƙyama
zuwa ga aikinsu. Takwaransa Alhaji Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa
ya ambaci ‘yan bugun ƙasa
cikin ƙattan
gari a faɗarsa:
Da ɗan Daudu da ‘yar Daudu sa’an nan ‘yan bori
Sa’an nan ƙattan
ga masu dubin taurari
Da mai arwa shi bayyanar da
jaki da makori
Da bokaye masu tanadin kamun ƙwari
(Zaman Banza:
bt.65).
Masu duba da taurari Shata ya ambace
su a waƙarsa
don ya nemi a bayyana masa ina suka dosa? Masu “arwa” su ne ‘yan bugun ƙasa. Kaftin Umaru Ɗa Suru a “Waƙar Masu Tsafi da ‘Yan
Bori” ya waiwaye duba na bugun ƙasa
da hisabi wanda ba haramtacce ba kamar haka:
To yanzu zan bahasi da mai
iske bokaye,
Mai ba da goro a ƙwaƙwalo
mai abin ɓoye.
Ƙwanƙwanto
ba shi da ƙa’ida duk ku zan lura,
Boka da wanda ka
iske boka ku saurara.
Mai fid da alƙalami
idan za ka fiddawa,
Na so ka san daga
Jumu’a ba a furcewa.
Don fid da alƙalamin
hisabi abi yin a,
Amma a zarta da
bincike ya zamo ɓanna.
Komi Tabaraka Ya rufe ba a buɗi nai,
Mai tone-tone daɗai kwamarci ka cizo nai
(Masu
Tsafi da ‘Yan Bori bt. 45-49).
A ganin Kaftin neman sanin abubuwan da
Allah Ya ɓoye
ga mutum shisshigi ne kuma tone-tone ne. bugun ƙasa kamar tone-tonen ƙasa ne domin gao me ke
cikinta. Duk mai tone-tonen ramu sai sun yi arangama da kumarci.
Shata da Malam Babba Na Ƙofar Gabas
Waƙa ce Alhaji Muhammad
Lawal Shata Katsina ya tsara domin yabo da kiran kasuwa ga Malam Babba Na Ƙofar Gabas Azare. An
haifi Shata Unguwar Sanyinna cikin garin Musawa shekarar 1923 a shekarar
mutuwar Shanu Sheme, (2006:43) sunan mahaifinsa Alhaji Ibrahim Yaro, sunan
mahaifiyarsa Lariya. Tushensa daga ƙasar
Sanyinna ta Sakkwato, tsakanin garin Goshe da Buwaɗe.
Ya rasu a ranar Jumu’a 18/6/1999 an rufe shi a garin Daura. Haɗuwarsu
da Malam Babba Na Ƙofar
Gabas a waƙa
Shata cewa ya yi shi ya tarar da Malam kan buƙatocinsa. A nawa tunani
Malam ne ya nemi waƙar
ko ta hanyar yi wa Shata babbar kyauta ko saƙo ko ta hanyar kore.
Malam Babba Na Ƙofar
Gabas Azare, sunansa Muhammadu Beji, ya rasu ranar 19th July, 2018
yana da shekara 88. Asalinsa daga Katsina yake, sunan mahaifinsa Waziri Abba.
Wazirin Katagum.
Waƙar Malam Babba Na Ƙofar Gabas
A tunaninmu na ɗaliban
al’ada wannan waƙa
tana cikin fsalin da muke cewa: “Adabin Magani” manya da ƙananan jigogin waƙar duka adabin magani
suka tunkara. An tsara waƙar
kan abubuwa kamar haka:
i.
Yabon shahararren malamin
bugun ƙasa.
ii.
Tabbatar da gogewarsa da ƙwarewarsa.
iii.
Yi masa kore ko talla ga
sana’arsa.
Zubi da Tsarin Waƙar
Shata ya samu wani matsayi a dniyar
adabin waƙa
Bahaushiya saboda ficensa da tsarin yadda yake gudanar da bayarwa da amshin waƙoƙinsa aka samu wani karin
magana wai shi: “Yan amshin Shata”. An fahimci ‘yan amshinsa ba ‘yan amshi iya
ba ne, ba ‘yan faɗi-mu-faɗa
ba ne, ba ‘yan karɓa-karɓa
ba ne, su ‘yan luguden gindin waƙa
ne da tsayi a kansa ba ragi ba ƙari
ƙuƙe-na-ƙuƙe. Waƙar da muke a kai gindinta
shi ne:
: Malam Babba na Ƙofar Gabas
Jigo
a taƙaice
-
Gabatar da gindin waƙa
-
Zuwan Shata ga Malam
Babba
-
Siffar Malam Babba
-
Mabuƙata Wajen Malam Babba
-
Tattaunawar Shata da
Malam Babba
-
Yadda Malam Babba ya yi
haɗin ƙasa
-
Yadda Malam haife ɗiyan
ƙasa
-
Faɗar
sakamakon haife ɗiyan
ƙasa
-
Haɗuwar
matar Shata da Malam Babba
-
Aikin haɗin
ƙasa
da aka yi mata
-
Sakamakon da aka ba ta
-
Kira zuwa ga jama’a su je
ga Malam
Waƙar Malam Babba a Sikelin
Hisabi
Aikin da zan yi wa wannan waƙar shi ne, in Harare ta a
kan sikelin hisabi ba na bugun ƙasa
ba. Malam Babba masanni ramli ne, don haka ɗan
bugun ƙasa
ne. Ni kuwa zan kalli shiga da titan adadin gidan ɗaya
(wato 1-10) cikin waƙar
gaba ɗaya.
Ga yadda tsari adadin gidan ɗaya yake a hisabin Hausa, Boko, da
Larabci.
ü Yawan
Adadi: 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10
ü Gidan
Cika: 2 4 6 8 10
ü Gidan
Mara: 1 3 5 7 9
ü Ƙarancin Cika: 2
ü Maƙurar Cika: 10
ü Ƙarancin Mara: 1
ü Ƙarancin Mara 9
ü Kimiyyar
da ke ƙunshe
a adadin gidan ɗaya
i.
Gidan cika adadi biyar ne
ii.
Gidan mara adadi biyar ne
iii.
Jimillar adadin gidan
cika (26)
iv.
Jimillar adadin mara (25)
v.
Kulkin bugun kulaken
gidan ɗaya (2)
Kimiyyar Hisabi
(i)
Dukkanin adadin gidan
cika aka doke shi da ɗan
uwansa cika za a samu.
(ii)
Dukkanin adadin gidan
mara aka doke shi da ɗan
uwansa mara za a samu.
(iii)
Kowane adadi na gidan
cika ko mara aka doke su cika za a samu kai tsaye.
(iv)
Idan aka haɗa
adadin adadin gidajen cika da mara gaba ɗaya
mara za a samu 26 + 25 = 51
(v)
Idan aka lissafa adadin ƙarancin cika da maƙurarta da mara za a samu
cika 2 + 10 + 1 + 9 = 22
Waɗannan adadai su ake kai da kawo da su
a hisabi da bugun ƙasa.
Adadin cika adadin nasara ne, adadin mara adadin kuɓuta
da fice ne da buwaya. A tunanin Bahaushe mutum duk ɗan
tara ne bai cika goma ba. Abin nufi a nan shi ne, tun da, da cikin wata tara
ake haihuwa ko bakwai to kowane ɗan Adam na duniya mara ne bai cika
har ya batse ba. Na yarda da faɗar Alhaji Aƙilu Aliyu Birnin Ƙaurar Lallai Jega da ya
je gasar waƙoƙi a Argungu ya buɗe
da cewa:
Jama’a taro ku saurara
In na yi da kyau ku ce: “ƙara”
In na yi kure ku ce: “Gyara”
Tilas ga mutum a sam mara
Ba zai cika har ya
batse ba.
Ƙididdigar Sunan Maƙagi Waƙa da Wanda aka yi wa
Ina son mu kalli cikakken sunayensu da
suka shahara da su, mu lissafa gaɓovin
kalmomin sunayen tare da fayyace baƙi
da wasula da suka cuɗanya da juna wajen haɗa
sunayen. Sai mun hisabance sunayen zakarun waƙar gabanin mu shiga waƙar ita kanta. A nan za mu
yi hisabin duba da kanka buga da kanka bisa yadda ake rubuta su a rubutun Boko.
To, bismilla an haɗa malamai faɗa:
Ta kowace fuska za a kira sunan Shata
da sunan ƙuruciya
ko sunan mahaifinsa ko da mahaifiyarsa ko da unguwarsu ko da garinsu na zama
dukkaninsu: gaɓovin
kalmomi tara (9) za a samu.
(i)
Gaɓovin
kalmomin tara (9) ne ba saɓawa
(ii)
Wasulan kalmomin sunan
tara (9) ba saɓawa
(iii)
Harafin kawai ke saɓawa
tsakanin 11-13
Saɓanin da aka samu a lamba ta (iii) ba
matsala ba ce, na (ii) zai rufe shi domin tsakanin baƙi da wasali idan an yi
gaggaƙa
wasali zai rinjaya domin shi ke jan baƙi
ba baƙi
ke jansa ba, don haka ne masana ke cewa: “Baƙi sai da wasali” ba su:
Wasali sai da baƙi
baƙi,
idan haka ne kuwa zancen Malam Babba a kan Shata da ke cewa:
Jagora : Ya ce mini: Kai makaɗi mai kiɗi
: Sha
shagalinka cikin duniya
: Duk
ba abin da zai tammaka
: Gidan
tara kake”
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Gidan tara (9) ita ce maƙurar mara babu ɗan
Adam da zai wuce ta don haka Shata yana matakin ƙoli sai dai a sa ido
kawai.
Ga alama cikin wannan ɗirkaniya
mota cikin randa Malam Babba na Ƙofar
Gabas ya fi Shata yin canjaras da gidan tara. A wajen masu bugun ƙasa za su ce: Lallai
malamin ya cancanci zama Shehin bugun ƙasa
kuma Shata ya yi daidai a faɗarsa da ke cewa:
Jagora: Wannan malami da dubi shike
: Ni
ko baba da waƙa
nike
Hisabin Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas
A ƙididdigar hisabin ƙunshiyar waƙa muna iya kasa ta gida
tara a warwarar jigo idan aka haɗa da rufe waƙa ta kai goma. A ƙididdigar Zubin waƙar za a kasafa ta kamar
haka:
(i)
Ziyarar Shata ga Malam
(ii)
Kayan aikin Malam
(iii)
Malam da mabuƙata a azure
(iv)
Tattaunawar Shata da
Malam
(v)
Yadda Malam ya yi haɗin
ƙasa
(vi)
Haife ɗiyan
ƙasa
da aka haɗa
(vii)
Faɗar
sakamakon bugun ƙasar
da aka yi
(viii) Matar
Shata da Malam
(ix)
Aikin bugun ƙasa da aka yi mata
(x)
Kammala waƙa da yi wa Malam talla
i.
A gabatarwar waƙa gindin waƙa Shata ya fara furtawa
bisa al’adar rera waƙa.
Gindin waƙar
na da kalmomi biyar (5). Adadin biyar adadine na mara ta tsakiya don haka
gindin matsakaici ne ita ma waƙar
matsakaiciya ce, ba ta cikin na baya. Gaɓovin
kalmomin tara (9) ne tuƙewar
adadin mara. Wannan ya ba mawaƙin
damar zaɓen ƙwangaggun kalmomi da suka
da ce da karin waƙarsa
har aka kamala babu gaza da salwantar kari bale saɓanin
ɗauka da aje ɗiyan
waƙa.
ii.
Ziyarar da Shata ya kai
wa Malam ɗiyan waƙa uku (3) ya furt amashi
biyu aka yi musu. Idan aka haɗa
su an samu marar biyar (5) wadda ita ce matsakaiciyar mara.
iii.
Kiyasin aikin Malam
diwanin baraza ne na ‘yan duba. Ya harɗe
a kan buzu, ga yashin kanka jeli gabansa, ya sha naɗi
irin na a ji Malam a ga Malam ga ƙatuwar
carbi ta biɗan tuwa. Kayan
aikin uku (3) ne aka sarrafa cikin ɗiyan
waƙa
huɗu (4) amshi huɗu
(4) idan aka tara su an samu goma sha uku (13) a hisabanci ana cikin marar mari
gidan uku (3) domin da abin da ya hau kan goma ake aikin Malam Maikaturu
Sakkwato na cewa:
“Naɗi da sanda da riƙon
kambili,
Ba
sharaɗi ne ba biɗan tuwo na.
iv.
Mabuƙatan da ke zauren Malam
wata babbar talla ce da koran fage. Mabuƙatan da Shata ya lissafo
uku ne, samari, da dattawa, da mata, gidan uku ne nan aka furta su cikin ɗiyan
waƙa
huɗu (4) idan aka narka su
an shiga adadin gidan bakwai wanda mataki babba ne a gidan mara daga shi sai
matakin ƙarshe
tara (9).
v.
Tattaunawar Shata da
Malam ba ta yi tsawo ba, Shata magana uku ya yi, Malam ɗaya.
Yawan kalmomi da aka zuba zance (23) masu gaɓovi
(51).
vi.
Adadin ɗiyan
waƙar
haɗin ƙasa (3) ne adadin
kalmomin (25) kalmomin haɗin
farko su ne:
vii.
Wajen faɗar
sakamakon bugun ƙasa
ɗiyan waƙar (3) ne masu adadin
kalmomi (21).
viii.
Da matar Shata ta je
ganawa da Malam adadin ɗiyan
waƙar
biyar (5) ne.
ix.
Aikin da aka yi mata na
bugun ƙasa
adadin ɗiyan waƙar (3) adadin haɗi
(5).
x.
Kammalawa na da ɗiyan
waƙa
(3) kalmomi (29).
Hisabin Duban da aka yi
wa Shata
Da Shata ya je gidan Malam ba tsorace
ya je ba. Ya kiyaye da abubuwan da suka gudana sosai domin a waƙa ya nuna har yadda Malam
ke yi da hannu da abubuwan da ya zana duka. Shata na cewa:
Jagora: Ya fid da uku ya ɗauko shida
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Jagora: Sannan ya ɗauke huɗu ya ɗauke tara
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Daga cikin adadan da Shata ya ambata a
nan za a ga akwai: 3, 6, 4, 9
ü Uku
fid da ta aka yi aka ɗauke
shida su biyu za su ba da tara (9).
ü Huɗu
ɗauko ta aka yi, aka ɗauke
tara za su ba da (13).
ü Tara
a haɗa da goma sha uku
za a samu ashirin da biyu (22).
ü Waɗanda
Shata ya ce aka ɗauke
su ne 6, 4, da 9 jimillarsu 19.
ü Idan
aka cire 19 cikin adadin 22 za a rage 3 kawai.
A wajen masu duba da masana al’da marar uku hatsabibiya
ce. A tunanin ɗan
Adam Bahaushe ita ce ke da:
(i)
Na shiga uku (shiga
hatsari ke nan)duk wani abin hani ko laifi aka kai adadinta babu uzuri. Da Bahaushe
ya ce: An yi ba ɗaya
ba, ba biyu ba. To! Ba zai ce: “ba uku ba”, don da an yi uku ba za a ƙyale ba. Ashe gaskiyar
Makaɗa Narambaɗa
da ya ce:
Jagora: Kai maana an ce maka bari
: Ka
sake an ce maka tsaya
Yara: Kai magana ka san ba a son ta
: Ka
ƙi bari wazzan mahaukaci
Gindi: Ya ci maza yak wan shin a shiri
: Gwamda’aren
Sarkin Tudu Alu
Bayan da Malam Babba ya ga Shata gidan
tara (9) aka sake haife ɗiyan ƙasa aka ga (3) dole ne
Malam in ji Shata:
Jagora: Yai gum da ni yana al’ajab
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Idan aka haɗa
gida 9 da 3 za a samu 12 cika. Idan adadin uku ya bugi adadin 9 za a samu 27.
Idan aka haɗa
27 da 12 za a samu 39. Dole Malam yai al’ajab domin ta kowace fuska aka bugi ƙasa Shata gidan 9 yake.
Adadin 39 da adadin gidan ɗaya ake zance. Adadin gidan ɗaya
a cikin 39 shi ne 9.
Shirin Malamin Duba a
Bakin Aiki
Duba aikin barazana ne da bugun gaba
da wayo. A riwayar Shata ya tarar da Malam cikin manyan kaya da naɗi
da carbi da ƙasa
gabansa ya harɗe
a buzu shirin aiki:
Jagora: Ya zauna harɗe da buzu nasa
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Jagora: Sannan ga ƙasa
gaba nai haka
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Jagora: Ya sha naɗi na Ƙofar
Gabas
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Wannan saƙon (jigon) cikin ɗiyan
waƙa
(3) yara sun yi amshi (3). An gina saƙon
cikin kalmomi 18 amshi kalmomi 15 jimilla 33 adadin mara 3 ya fita.
Mabuƙata Wajen Malaman Duba
Malaman duba kowa nasu ne. Akwai mata
da maza da samari da dattawa. Abin da ya bayyana a ƙasar Hausa mata sun fi
hulɗa
da su. Buƙatun
maza mafi yawan ma neman rinjaye ne da sa’a da ɗaukaka.
Mata kuwa haihuwa da zama da kishiya da mallake miji ya dame su. Me ya sa a
wajen duba wa Shata zugum! Malam ya yi yana al’ajab, amma a wajen matar Shata:
Jagora: Ya narke ya ƙyalƙyace
da dariya
: Ya
ce mata ɗa na
nan namiji
Gindi: Malam Babba na Ƙofar
Gabas
Sakamakon Bincike
A wajenmu ɗaliban
al’ada waƙar
Malam Babba Na Ƙofar
Gabas ta yi wa duba/bugun ƙasa
adalci/ ta ƙyallaro
muhimman abubuwan da bugun ƙasa
ya ƙunsa.
Shata da kansa ya tabbatar da haɗuran da ke tattare ga bugun ƙasa na shisshigin ƙyallaro gaibi da keɓanta
da mata da ba na mutum ba. Daga cikin abubuwan da wannan bincike ya gano akwai:
1.
Adadin mara ya yi fice da
yawa a hisabin waƙar.
2.
Idan aka sarrafa sunayen
Shata guda bakwai gaɓovinsa
tara ne, haka ma wasulansu da harufansu. Ashe Malam ya yi canjaras da cewa
Shata gidan tara yake.
3.
Malam Babba shi kansa a ƙididdiga gidan tara yake.
4.
Gindin waƙar ma gaɓovin
kalmominsa tara.
5.
Zubin kalmomin kowace waƙa ta baka ko rubutacciya
dole su hau hisabin giinin kalmomi gaɓovinsu,
baƙaƙensu, da wasulansu domin
ta samu rerawa a matsayin waƙa.
6.
Ga ɗan
abin da na gano wannan waƙar
kore ce da talla Shata ke yi wa Malam. Malam Babba ya yi zama a Kano mutanensa
duk su ne mutanen Shata. Babban maigidan Malam Ɗankabo, shi ma Shata
haka.
Naɗewa
Wannan bincike wani wasa ƙwaƙwalwa ne mai nuna wa ɗaliban
ilmi kowane allazi da nasa amanu. Ban ce na ce komai ba amma na san an ƙara wa adabin magani wata
‘yar gudunmuwa ta ƙara
shi gaba. A bisa gaskiyar babu bambanci tsakanin waƙar sha ruwa da ta Abu
‘Yanmama da Gagara Badau da Malam Babba Na Ƙofar Gabas a kulkin
nassoshin shari’a da al’ada. Tattare da raunin Imani da lalacewar zamani
Bahaushe bai yarda da cewa duba aiki ne nigari ba. Malamin duba komai shahararsa
ba ya cika wa Musulmin kirki ido. Muna nan tare da Alhaji Umaru Nasarawa
Wazirin Gwandu a fadarsa:
Wanda bai wuce ya yi kwana
ba,
Bai wuce ya mance abi nai ba,
Wanda bai Sana ma rabo nai
bai,
Yaushe za shi gano
min nawa?
MANAZARTA
Abbas, S.A. (2001) “Ethanomathetics
of Hausa Socio-Cultural Environment: In Search of Viable
Mathematics” Pedagology” PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Adakawa, H.B. Hisabi ta Hanya Mai
Sauƙi,
Kano.
Adamu, A.T. (1990) “Siddabaru a Ƙasar Hausa Yadda Yake da
kuma Yadda ake Gudanar da shi”, kundin MA, Kano: ami’ar Bayero.
Adamu, A.T. (2000) Tarihin Bugun Ƙasa a Ƙasar Hausa, kundin PhD,
Kano: Jami’ar Bayero.
Adamu, R. (1991) “Malam ko Wani Dodo:
Bayanin Rayuwa da Ayyukan Sarkin Bori Sule”, Kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Alhassan, H. (1994) “Hisabi da
Malamansa a Ƙasar
Hausa (1960-1994) takarda”, Sokoto: CLS, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Alhassan, H. (1994) “Yadda ake Hisabi
Ƙasar
Hausa” takarda, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A.A. (1988) “Malam ko Wani
Dodo? Siddabarun Shiga da Fitan Mara Cikin Hisabin Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas” takardar da
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A.M. (1997) “Ɗankore Sourcerar
Apperentice in Sokoto” paper presented at West African Seminar, Department of
Anthropology, London: University College London.
Bunza, A.M. (1999) “Ibrahim Yaro
Yahaya a Mizanin Hisabi”, takardar da abayar a Sashen Harsunan Nijeriya, Kano:
Jami’ar Bayero.
Bunza, A.M. (2003) Hausa Medicine
Its Relevance
and Development
in Hausa Studies, The Second Inaugural Lecture,
Usman Ɗanfodiyo
Sokoto; Lagos: IBRASH Publishers.
Bunza, A.M. (2018) “Mathematical
Heritage in Hausa Number System A proposal for Teaching Mathematics using
Nigerian Languages”, paper presented at University Seminar Series, Federal University
Gusau.
Gusau, S.M. (2018) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na
Uku Matanonin Wasu Waƙoƙin Mamman Shata
Katsina, Kano: Century Research and Publishing
Ltd.
Gwandu, M.A. (nd) “Kitabul Hisaab Wal Asaraari”.
Gwandu, M.A. Hisabi A Sauƙaƙe,
Zariya.
Handloff, R. (1982) Prayers,
Amulates and Charms: Health and Social Control” African Studies Review,
25:185-94.
Lewis, W. (1988) Hausa Medicine:
Illnesses and Well-being in a West African Culture, Durham: Duke University
Press.
Line, J. (1985) Discoɓer
Numerology Understanding and Using the Power of Number.
Aƙuarian/Thorsons
and Imprint of Harper Collins Publishers, London.
Oyebade, F.O., Francis O.A. Kammelu
N.C. (eds.) (2014) The Counting System of Some Dialects of Igbo, Hausa and
Yorua, Ibadan: Master Print Publishers.
Ƙanƙara, A.I. (2013) Mahdi
Mai Dogon Zamani Shata da Kundin Waƙoƙinsa,
Kaduna: Lapson Production.
Sa’id, B. (1977) “Ilmin Taurari a Waƙoƙin Masu Jihadi”, cikin Nigerian
Languages Vol. Vviii,
CSNL, Kano: Jami’ar Bayero.
Sheme da Wasu (2006) Shata Ikon
Allah, Kaduna: Informat Publishers.
Shirley, L. (1977) “Culture and
Mathematics: A theme for Mathematics Education”, in ABACUS 24 (1):
81-88.
No comments:
Post a Comment