Hausawa
na cewa: “Komi ya ɓace maza ka biɗo
shi”. Babban tunaninsu a kan haka shi ne, wuyar aiki ba a fara ba. A kowane
lokaci mutane ke jayayya ana buƙatar raba gardama. Idan sa-in-sa ya
yawaita, gaskiya ce ba ta bayyana ba. Da ta leƙo, ita ce raba
gardama. Labarin masu yunƙurin fayyace da buhun gero da ‘yan
Nijeriya wa ya fi yawa, ya bice duniyar kafafen yaɗa
labarai na BBC da ƁOA da RFI da jaridun ƙasa da kafafen
yaɗa
labarai na jihohi. Da masoyansu, da masu mamakinsu, da masu musunsu, da masu
adawa, dole su yarda da cewa, wannan al’amari ya gawurta kuma ya yi tasiri ga
duniyar lokacinmu. Ganin irin ƙwazon matasan da suka assasa wannan
batu, suka ba lokacinsu, da tunaninsu, na ganin sai sun kuranye yanar da ke
ciki, ya san a yi wa wannan takarda taken: Wurin da babu ƙasa nan ake
gardamar kokuwa”. Yanzu sai a biyo mu a ji ina salka ka tsatsa.
Wurin
Da Babu Ƙasa
Nan Ake Gardamar Kokuwa
(Sharhin
Littafin: Da ‘Yan Nijeriya da Buhun Gero Wa Ya Fi Yawa?)
Aliyu
Muhammadu Bunza
Tunanin Na Bayan Fage
Wani da ji zancen ƙidayar buhun gero
zai ce, marasa aikin yi ne. masu wannan tunanin sun manta da cewa lissafi rabin
ilmi ne kuma babban aiki ne. a ganin wasu, wai, zauna gari banza ne da suka
rasa ta yi. Assha! Ai zauna gari banza ba ya tunanin komai sai tunanin banza.
Wanda duk tunaninsa ya doshi sanin ƙididdigar mutanen ƙasarsu da
abincinsu babu ɗan kishin ƙasar da ke
gabansa. A ganin wasu, marasa karatu ne ke son su sami wata dama ta sake jiki.
Ina! Ai daga cikinsu akwai masu karatun addini da na boko, don haka da gafaka
da digiri duk ba su jin tsoron a yi taho-mu-gama da shi. A nawa hasashe,
matasan da suka haɗa wannan muhawara cikakkun ‘yan
kishin ƙasa
ne, gogaggu, wayayyi, managarta da ke son a kan kowane al’amari a riƙa sara ana duban
bakin gatari.
Tunanin Ɗaliban Ilimi
A namu tunani, ruwa ba sa tsami banza.
Yunanin mutane abin sauraro ne da girmamawa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Idan muka
faɗaɗa
darasin da rashin tayi a kan bar arha, za mu fahimci ana tsintuwar guru cikin
suɗi
ba abin mamaki ba ne a yi tsintuwar dami a kala. Babu wai, da rashin kira Karen
bebe ke ɓata. Fahimtarmu ta cewa, rashin
sani ya fi dare duhu ita ta ba mu damar gano rashin sani ke sa Karen gwauro yi
wa gwauruwa/bazawara haushi (barazana). A taƙaice, tunanin waɗannan
matasa wata babbar makaranta ce da buɗa ƙofar kowane irin
tunani. Daga cikin abubuwan da ya kyautu mu hango akwai:
1.
Me
ya sa suka yi tunanin yawan ‘yan Nijeriya?
2.
Me
ya sa buhun gero kawai ya zo a tunaninsu?
3.
Me
suke son su nuna wa ‘yan Nijeriya da wannan tunani?
4.
Me
ya sa wannan tunani bai zo musu a mulkin soja ba?
5.
Me
ya sa sai a wannan gwamnati suka fito da wannan ra’ayi?
6.
Don
me ba su bar tunaninsu tsakaninsu ba sai da suka yayata?
7.
Mene
ne dalilinsu na yin wannan muhawara?
Duk
wani ɗalibi
irinmu ya tsura wa waɗannan tambayoyi
idon nazari sai tabbaatr da cewa, Turancin direba sai fasinja. A namu tunani
matasan sun yi amfani da buhun gero a matsayin sabara, wadda Bahaushe ya ce sai
an laɓe
gare ta a harbi barewa. Ina barewar take? Ku bi ni a sannu.
Gero a Bahaushen Tunani
Gero na da wata martaba ga Bahaushe
wadda babu wani nau’i daga cikin nau’in tsaba/hatsi, mabunƙura ƙasa, ‘ya’yan
itace, da ganyen da ya kai shi. Ga alama gero shi ne abincin farko da Bahaushe
ya fara fahimta da sanin yadda ake sarrafa shi. Kaɗan
daga cikin tunanin Bahaushe a kan gero sun haɗa
da:
1.
Gero
ne limamin ƙida cikin zuriyar tsaba/hatsi a Bahaushen
lissafi a kan ce: gero da dawa, gero da maiwa, gero da masara, da sauransu,
amma ba a limanta gero a ce: “dawa da gro” a al’adance.
2.
Daga
cikin dangogin tsaba/hatsi gero kaɗai ke da martabar a gasa shi a ci yana ɗanye
da sunan tumu, in ya bushe a gasa a ci da sunan babbaka, a tafasa shi haka nan
da kayan haɗi a ci da sunan rummace/rumbaye, a saka
shi a baka gayansa a ci da sunan mummuƙe.
Ashe gero ya buwaya, ya cancanci a yi masa karatun kansa.
3.
Daga
cikin sunayen Bahaushen gero kawai ake yi wa Bahaushen suna laƙabi da shi, ba tare da wani madanganci ba,
za ka ji sunan mutum “Gero” amma babu “Nagero” ko “Maigero”.
4.
A
ɓangaren sauran hatsi: Maidawa, Namaiwa, Mainasara,
Maishinkafa da sauransu, ɗaukar gero a idon Bahaushe ta tun fil azal
ce ba ta girshi ba.
5.
A
tsayin cimakar Bahaushe, da fura da kunu da ɓula
da zaɓu da kafa da dambu da rumbace/rumbaye da daƙuwa da tukkuɗi
gero ne maganaɗison haɗinsu.
Ba don ge ba da an tasarin more wa daɗinsa.
6.
A
Bahaushiyar al’ada, da damen gero ake toshin aure da kai kayan haihuwa, wanda
duk aka kai ba shi ba rashin sa ya haifar da haka.
Na
tabbata Narambaɗa bisa gaɓa
ya sara a fadarsa da ke cewa:
Jagora: Maɗi
bai kai ga zuma ba
Yara: Kowal lasa shi ka hwaɗi
Kwandon wake bai kai
ga damen gero ba
Jagora: Ai ɗan
akuya ko ya yi ƙahoni,
Yara: Ya san bai yi kamar rago ba
Jagora: Duk wada ɗan
Sarki yaƙ
ƙasura
Yara: Kak ka raba shi da bawan Sarki
Gogarman Tudu jikan Sanda
Maza su ji tsoron ɗan
mai Hausa.
Ashe tunanin matasanmu a kan gero ba
bidi’a suka yi ba, sun dai yi cikon sunna makaho da waiwaya.
Kwatanta ‘Yan Nijeriya da Yawan Buhun Gero
Wanda duk ke da tarihin yawaitar bil
Adam a doron ƙasa
ya san akwai buƙatar
ana sara ana duban bakin gatari. Kamata ya yi abincinmu ya fi mu yawa ba. Halin
da muke ciki yanzu mun fi abincinmu yawa, wanda ya haifar da hauhawan
farashinsa da ragaitar marasa abinci su kutsa cikin aikata miyagun ayyuka da ƙazantattun
laifuka.Tunani makaɗa Ɗangiwa da Ɗanƙwairo ya
tabbatar da wannan hasashe:
Jagora: Ashe likkita ba shi maganin yunwa
Yara: Wanga magani sai a biɗo
hura
Gindi: Cikin duniya ba abin da yak kai ga faro-faro
Ɗangwairo na
cewa:
Jagora: A samu na shan dawo
Yara: Ka a ragaice
Bi da kayan hwaɗa
maigida Ali
Ali ɗan
Iro bai ɗauki raini ba.
Hikimar Buhun Gero a Tunanin Littafin
A tunaninmu buhun gero ba ya ƙidayuwa kai
tsaye a samu haƙiƙanin abin domin
saninmu na ƙwarorin
gero ƙanana
ne adadin da ke cika buhu ba su da iyaka. Wanda duk ya ce zai ƙidaya su ya ɓaro
jan aiki. Da wuya a samu ƙaton da zai ɗora
buhun gero a kansa shi kaɗai dole sai an
aza shi. Ba a san namjin da ke rabin yini da buhun gero a kansa ba. Duk wanda
aka ɗora
masa shi a ka sai an taru za a taya shi saukewa. To kwatanta wannan da yawan
‘yan Nijeriya da buƙatocinsu
da ke kan mutum ɗaya kacal tsawon shekaru huɗu.
Wazirin Gwandu Alhaji Umaru ya ce a dinga tanya wa wanda kaya suka rinjaya:
Kwaɗ
ɗauki
kaya sun fi ƙarfi
nai ga kai
Yaf fara hanya tabbata masa
ba shi kai
Tafiya kaɗanna
shi kai shi ɗaura takai-takai
Indai ya yas in ko su faɗi
shi haushi
(Waziri Umar: Waƙar)
Karatun Kiɗan Buhun Gero
Mazajen da shiga wannan aiki su bakwai
ne domin su dace da ranakun mako. Binciken ya ɗauke
su kwanaki ɗari biyar (105), kusan wata uku da
‘yan kwanaki (kwana biyar) a kan ƙidan farilla, idan bai cika farilla
ba wata uku da kwana takwas. Yawan adadinsu su bakwai ya nuna muna kashin baƙi sai taro,
hannu ɗaya
ba ya ɗaukar
jinƙa.
Idan aka ga cikas ga abin taro a bar zargin mutum ɗaya
matsala kurar gardi ce. Idan za a yi wata uku na ƙidar buhun gero,
to wata ko shekara nawa za a ɗauka na tantance
matsalar da ke ga kowane kwano ko sa’i ko tiya? Kwatanta wannan da matsalolin ƙasarmu da mutanenta
da jihohinta da yankunanta da ƙabilunta da addinanta da al’adunta
kuma duk a ce mutum ɗaya ne limaminta. Yaya za a yi ya
kauce wa rafkanuwa? Saƙon Narambaɗa
shi ne:
Jagora: Kowac ce shina iyawa ga hili nan
Yara: Sai ya ƙetare gudanai ba
ban kwana
Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
Baban Dodo ba a tamma da
batun banza.
Me Ya Sa ba a Yi Tunanin Ƙidan
Buhun Gero a Mulkin Soja?
Hausawa cewa suka yi dama da damun
dawo in babu dama ana dama shi gaya. Mulkin soja tuƙin tsaye ne
aikin mutum ɗaya. Talaka ba ya da wata walwala
ta zaman tunanin me ya kamata ya yi? Me ya kamata a yi wa ƙasa? Don haka,
ko da akwai wannan tunani ba zai yi tasiri ba domin ‘yan ƙasa na tsakanin
bakin bindiga da kurkuku da gudun fanfaƙe. Mulkin
dimokraɗiyya
ke da walwala da sakewa da ba talakka damar taka rawa har da wuce gona da iri.
Don haka idan aka samu dama irin ta dimokraɗiyya
a yi amfani da ita yadda za a more mata, ba yadda za a wargaza ta gaba ta koma
baya. Masu jagorancin dimokraɗiyya ga saƙon malamin kiɗa:
Jagora: Abin sarauta abin rabo ne
Yara: In an samai a ba mutane
Amma shi wanda bai sani ba
Sai ya ci shi ɗai
ya ɗaura
gyashi
Ya zavi
gwalo ya wa mutane
Sai ya wuce kamar ruwan faƙo
Gindi: Tattaki maza ɗan
Sanda na Iro
Gamda’are Salau mazan ƙwarai.
Me Ya Sa Sai a Wannan Gwamnati Karatun ya
Tusgo
A tunanina, gwamnatin da ke ci yanzu
ta karvi
mulki ga wata gwamnati irinta. Duk lokacin da aka ba da mulki cikin lumana ba
da juyin mulki ba, ba da zanga-zanga ba, wanda ya miƙa mulkin zai
tsura wa mai karɓar mulkin ido sosai ya ga irin
rawar da zai taka. Don haka, tsakanin wanda ya noma gero da wanda ya sussuke
shi da wanda ya ɗura shi a buhu da wanda ya zube shi
a ƙasa
ya ƙyarga
shi ƙwara-ƙwara wa ya fi
saninsa? Yadda kowanensu ke da masaniya kan matsalolin jama’arta, ƙwazon kowace ya
danganta ga irin adalcinta. Yawan ‘yan Nijeriya ya kai miliyan ɗari
biyu (200,000.000) buƙatocinsu ya nunka haka. Dole a ce,
abin da yawa inji mutuwa da ta shiga kasuwa.
Hikimar Yayata Karatun Ƙidan
Gero
Babu shakka ba bil Adama kawai Allah
Ya halitta a duniya ba, akwai dabbobi da ƙwari da tsuntsaye
da Iskoki, da Mala’iku duk ba su gagari Allah mulki ba domin buwayarSa da
iyawarSa. Duk wani wanda ba Allah ba zai iya da mutane ba komai ƙwarewarsa da
ilminsa da soyayyar da ake yi masa. Buhun gero da aka haɗe
ƙwarori
miliyan barkatai a ciki aka ɗinke wuri ɗaya
ba magana suke yi ba, ba su da wata buƙata, ba a yi musu wani alƙawali ba, ba su
da bambancin yanki da jiha da jinsi da addini da harshe. Da tsuntsaye ne ko
dabbobi ko ƙwari
ko kiyafu aka tara wuri ɗaya dole sai an
nemi agajin tattaro su da haɗe su wuri ɗaya
su zauna lafiya. To, ina ga mutane? A haɗe
mutane gaba ɗaya, a mallake su lamui lafiya sai
Allah. A koyaushe, a kowace ƙasa, a kowane mulki, akwai mutane
shida da ba sa barin a zauna lafiya inji Narambaɗa:
Jagora: Sarki Ka ga mutum shidda
Yara: Babu mai zannawa lafiya da su
Jagora: Wanga azuji wanda butulu
Yara: Guda asheraru guda maɓannaci
Jagora: Wanga guda tsohin munahuki
Yara: Akwai wani na nan mai ƙure mutum
Gindi: Ya ci maza yak wan shina shire
Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
Me Ya Haifar da Wannan Mahawara?
Babu abin da ya haifar da wannan
muhawara face muna cikin ƙasar da kowa ya iya, kuma ba a
yarda da kowa ya iya ba. Ƙasa ce da masoya ke makaftar
soyayya, maƙiya
ke makaftar ƙiyayya.
Babu abin da za a yi wa mutane face hannunka-mai-sanda ko za su ahumo su
waiwayo a koma tsaka-tsaka. Yawanmu na ƙaruwa,
matsalolinmu na daɗuwa, fitinu da rigingimu na daɗa
wanzuwa da barbazuwa. Da za mu yi wa kanmu adalci mu zauna mu riƙa tunanin irin
halin da ƙasarmu
take ciki, da dabarun tunkararsu da zai amfane mu.
Raba Gardama
Ma’aikatanmu talatin da bakwai da suka
yi kwana ɗari da biyar suna ƙidayan buhun
gero sun samu ƙwara
miliyan goma sha ɗaya da dubu ɗari
tara da saba’in da tara da ɗari takwas da
sittin da takwas (11,979,868). A ma’auna buhu kashi uku yake kamar haka:
1.
Mudu
ɗaya na ciyar da mutum 3 ci ɗaya
kacal.
2.
Buhu
ɗaya na ciyar da mutum 210 ci ɗaya
kacal.
3.
Mutum
ɗaya na buƙatar
mudu ɗaya a yini ci 3 kacal.
4.
Buhu
ɗaya na ciyar da mutum 70 a yini ci 3 kacal.
5.
Yawan
‘yan Nijeriya 200,000,000 a raba da 70 = 2,857,142.857.
6.
‘Yan
Nijeriya na cin buhun gero 952,380,9524 ci ɗaya
a wuni.
7.
‘Yan
Nijeriya na cin buhun gero 2,957,142,857.
Sakamakon Bincike
Muddin ta tabbata yawan ‘yan Nijeriya
ya kai miliyan ɗari biyu (200,000,000) dole hukuma
ta zage damtse wajen inganta noma ta fuskar tallafa wa manoma, inganta
ma’aikatun gona, da faɗaɗa
bincike a kan sha;anin noma. Gina makarantu da ma’aikatu da gidaje da kamfuna a
rayayyen wurin nom aba ci gaba ba ne komawa baya ne. Da za a kawo sharaɗin
zama manomi ga duk wanda zai yi takarar shugaban ƙasa da gwamna da
majalisun tarayya da an taimaka. Babu shakka ‘yan Nijeriya sun fi buhun gero
yawa don haka suna buƙatar gero mai yawa domin su rayu.
Naɗewa
Ta tabbata ƙwarorin gero
11,979,868 aka samu a buhun da aka ƙyarga. Masana noma sun tabbatar da
cewa, damin gero biyar ke buhu. Matsakaicin manomi na noma dame saba’in wanda
zai ba da buhu goma sha huɗu. A cikin
kowane dame ana samun ƙwarori 2,395,973,6. Manomi ɗaya
mai noma dami (70) buhu (14) buhunsa ɗaya na
ciyar da mutum 210 nomansa gaba ɗaya zai ciyar da
mutum 2,940. Madalla da muhawarar matasa da ta buɗa
mana kafar sanin ƙasarmu
da shugabanninta da yadda za a iya wadatar da ita da kyan tsari (hurar gero)
bisa ga riwayar Muhammadu Sani Ɗanbalɗo
da ke cewa:
Jagora: Kun san layun tsari gare ni,
Mi al layun tsarinka Mamman?
Dunƙullan dawo gami
da nono,
Ko was sha su ba shi jin
kasala
In ko an yi gardama a dama
Gindi: Rabbana Allah Ka taimake mu
Mu samu fitar kai cikin
tukunya.
No comments:
Post a Comment