Asalin
Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta na asali ƙabilanci.
A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa
bayi, don haka a ƙasarsu
aka fara yaga wasiƙar
Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa, a shiga
rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn Saba’
suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da musibar
Karbala abin kula ne.
Kakkaɓan
Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar Labɗo
Aliyu
Muhammad Bunza
Professor
of African Culture (Hausa)
Faculty of
Humanities and Education
Department
of Languages and Cultures
Federal University
Gusau
Zamfara
State
Email: mabunza@yahoo.com
Tel: 0803 431 6508
Gabatarwa:
Kasancewar addinin Musulunci na ƙashe daga cikin saukakkin addinai na
Allah, dole ya ci karo da wasu matsaloli na har abada. Dalilan da suka haddasa
haka kuwa su ne; mai saukar da addinai (Allah) Shi Ya saukar da shi a ƙarshe, kuma Ya ce ya rufe addinai da shi.
Na biyu, Musulunci ya riski addinan gargajiya masu ƙarfi da suka mamaye duniyar zamaninsu, irin su Farisa,
Rum, Indiya, Makka, Sin, da duniyar baƙar
fata. Tarkacen addinan ba su da littafe daga Allah, Musulunci ya ambace su da
sunayen uku: Majusawa, Mushurikai,
ko Kafirai. Masu saukakkin addinai idan suka bijire
suna iya ɗaukar
biyu daga cikin sunayen uku, wato ko dai Mushurikanci ko Kafirci. Ga alama, ta
wannan hanyar Yahudu da Nasara suka kutso cikin Musulunci a makirce, suka
haddasa ƙungiyoyi da aƙidoji da ɗariƙu
da ke tarwatsa kan Musulmai da nisanta su ga sahihin tafarki. A tunanin wannan
tattaunawa, ‘Ƙungiyar Shi’a’ na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da aka shaƙa wa wannan guba.
Mece
Ce Shi’a? Wane Ne Ɗan
Shi’a?
Bai kamata a ari bakin mutum a ci masa albasa
ba, don haka, waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ɗaya daga cikin manyan Shehunan Shi’awa Muhammad bn
An-Nu’man (Al-Mufeed) ya ce Shi’awa su ne:
Mabiya
Ali (RTA) da suka yi masa mubayi’a, suka yarda da Khalifancinsa bayan Manzon
Allah (SAW) kai tsaye babu wasuɗa tsakaninsa da
Annabi (SAW); kuma suka ƙi khalifancin duk waɗanda
suka gabace shi ga gadon Khalifanci, tare da imanin cewa; Ali (RTA) ya bi khalifofin
da suka gabace shi a bayyane ba tare da biyayya ga cancantar khalifancinsu ba.[1]
A wannan riwayar ta babban shaihin Shi’a,
za mu ce, ɗan
Shi’a shi ne:
i.
Wanda
bai yarda da khalifancin Sayyidina Abubakar, Umar da Usman (RTA) ba.
ii.
Wanda
bai yarda da duk wani shugaba na Musulunci ba in ba ta hannun Ali (RTA) ya biyo
ba.
iii.
Wannan
aƙidar ita ce “Shi’a” wanda ya yi imani da
ita shi ne “ɗan Shi’a”.
Tarihin
Shi’a A Musulunce:
Masana tarihin Musulunci sun daɗa juna sani a kan tarihin Shi’a, musamman
a kan madugun tafiyarta. Abdullahi bn Saba’ Bayahude shi ya assasa Shi’a, kuma
malaman Shi’a sun ce, shi ya fara sunsuno Khalifanci Ali (RTA) da
takale-takalen yi masa mubayi’a (tun gabanin su Abubakar, Umar da Usman (RTA).
Abdullahi bn Saba’ shi ya fara cewa, Ali (RTA) Allah ne. A lokacin da yana
addinin Yahudu shi ne ya fara cewa Yusha’ bn Nuh Allah ne. Ali (RTA) ya hukunta
shi da kisa[2]
a kan gagarumin kafircinsa na ce wa Ali (RTA) Allah. A taƙaice, za mu ce, tarihin Shi’a shi ne:
Ƙungiyar da
Yahudawa suka assasa a cikin addinin Musulunci a makirce, da sunan goyon bayan
wani gwarzo daga cikin gwarazan Musulunci Ali (RTA). Hukunta Abdullah bn Saba’
da kisa da Ali (RTA) ya yi, ya tabbatar da barrantar Ali (RTA) da dukkanin
Sahabbansa a kan wannan aƙida.
Bazuwar
Shi’a A Duniyar Musulunci:
Asalin Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta
na asali ƙabilanci.
A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa bayi, don haka a ƙasarsu aka fara yaga wasiƙar Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa,
a shiga rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn
Saba’ suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da
musibar Karbala abin kula ne. Tun a wancan lokaci jama’arsu suke hijira ƙasashen daban-daban, yau ana samunsu a
Jordan, Syria, Yemen, Iran, Iraƙ, Baharain, Pakistan, India, Lebanon, Kuwait,
Afghanistan, da Afirka musamman Nijeriya ta Arewa). A Nijeriya ta Arewa, sun fi
mamaye Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi, Sokoto, da ‘yan ƙwarori a Kabi da Zamfara.[3]
Fuskokin
Shi’a A Nijeriya Ta Arewa:
A tarihance, Shi’a ta yi amfani da wasu
manyan fuskoki da za su sa a kalle ta da idon basira. Shi’a ta mamayi matasan Arewa
ta fuskar boko bayan juyin-juya halin Iran na 1979. ‘Yan boko suka riƙa tallarta da sunan Musulunci da jihadi.
Daga nan, jaridu da mujallun Iran, musamman Mahjuba,
Echo of Islam, Digest,
d.s. ana raba su kyauta ana turo wa yara ‘yan makaranta kyauta. Wannan dasisar
ta ci Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai (MSS). Da haka wasu suka samu damar
zuwa Iran karatu, aka buɗa Sashen Hausa a gidan Rediyon Ƙum. Wannan ta buɗe wata fuska ta tarukan wa’azi da laccoci
wanda ya haifar da fassara wasu mujallu da littattafan Shi’a cikin harshen
Hausa. Daga cikin littattafan da suka yaudari matasa akwai Shi’a da Aƙidojinta
na wani mutumin Ghana
wanda ya zaman sanadiyayr buɗa Masallacin Jumu’a na Shi’a na Legas. Na biyu, shi ne
littafin Muhimman
Fatawowi a kan Muhimman Matsaloli
na Muhammadu Isa Talata Mafara, wanda ya nuna Shi’a Mazhaba ce daga cikin
Mazhabobin Musulunci. Wannan littafi shi ne yaudara ta ƙarshe da aka yi wa ‘yan boko Musulmi da matasan
Sakkwato, kuma shi ne sanadin ɗaure wa zagin Sahabban Annabi (SAW) gindi a Sakkwato
da Kabi da Zamfara (Allah Ya kiyaye mu).[4]
Dasisar
Laɓewa
Ga Jihadi Da Yaƙi
Da Yahudu Da Nasara:
Shi’a ta bayyana a Nijeriya bayan da
tsarin mulkin Turawan Ingila na Kafirci ya kafa tuta a Nijeriya. Yaƙin da Khumaini ya yi a 1979 da ‘yan
barandar Amurka, har aka tumɓuke gwamnatin Shaa, ya zama wani furen kallo ga
matasan Arewa, aka mayar da hoton Khumaini wani Dala’ilul Khairati a gidaje, da motoci, da gaban riga da rawunna. Masu
wannan alamomi su ne mujahidai, akasinsu a ce musu magoya bayan Yahudu da
Nasara. Hulɗar
ta ƙasaita har ta kai ‘yan Nijeriya zuwa Iran
domin bukin ranar jihadinsu. Daga cikin waɗanda suka halarci bukin akwai: Ibrahim
Yakubu El-Zakzaky, Bashir Aliyu Umar, Ibrahim Bello, Abubakar Jibril, Abubakar
Tureta, Muhamamdu Isa Talata Mafara, Turi Hamza Lawal, Husaini Abubakar, Nuhu
Yahya, Yakubu Yahya, Mannir Lawal Rimi, Nuhu Rimi.[5] A
lokacin an ɗauka
Khumaini da Kafirai yake yaƙi,
don haka, dole a manta da duk wani bambancin Shi’a da Sunna a mara masa baya. A
cikin wannan tafiyar, abu biyu suka faru masu razana Musulmi daga bakin Jagoran
tafiyar Ayatullah Khumaini:
1.
Na
farko, da aka kai masa ziyara, ya ji sunan Abubakar Jibril da Abubakar Tureta,
ya ce, a gaya musu su gaggauta sauya sunan zuwa wani (domin ba su da sunan ƙwari).[6]
Tun lokacin, Abubakar Jibril da Abubakar Tureta, suka gaya wa abokan tafiya, ba
ta da sauran gyara, mai neman beli ya mari uwar alƙali. Anya Musulmin ƙwari na ƙyamar
Abubakar?
2.
Na
biyu, a shekarar da Khumaini ya karvi gayyatar Musulman Afirka ta Kudu. Da aka
tarbe shi a filin jirgi, a jawabinsa na babban baƙo ya buɗa da cewa:
Idan na samu
nasarar shiga Makka da Madina a matsayin mai cin su da yaƙi. Abu na farko
da zan yi shi ne, in tone gumaka biyu da ke raɓe
ga kabarin Manzo (SAW) Abubakar da Umar, ya tsine musu.
Tun a filin jirgi aka rabu dutse hannun
riga. Musuluman Afirka ta Kudu suka ce ba su da rumfar da za a zagi Sahabban
Annabi (SAW) a ƙasarsu.
Makirce-makircen
Rusa Musulunci A Arewa:
Bayyanar gwagwarmayar Shi’a a Nijeriya ta
Arewa daga 1979-2019, yau kimanin shekara arba’in (40) za mu fahimci waɗannan abubuwa:
1.
Cikin
dasisa Shi’a ta kame matasan Arewa maza da mata aka dinga amfani da su wajen
rusa Musulunci da Musulmai domin a idar da ayyukan da Turawan Ingila da ƙungiyoyin leƙen asiri ba su idar ba. Yaya muke ciki a yau? Me ya
raba mu da Chechnya da Karbala da Afghanistan da Iraƙ
da Libya? An mayar da tashintashina addini, mutuwa ciki shahada. Ina sauran zaman
lafiya?
2.
A
shekakarar 1979-1980 Shi’a ta fara sunsuna wa matasanmu Boko Haram da
zanga-zanga. Matasanmu haziƙai
suka fice daga makarantu wasu suka yayyaga takardun kammala karatunsu.
Zanga-zangar Shi’a ta farko a Sakkawato aka yi ta a shekarar 1979. Tun wancan
lokaci aka yaudari matasanmu aka saka su fitina har ya zuwa yau. Wasu sun mutu
a kaso/kurkuku, waɗanda suka fito sun zama ƙwararrun ‘yan ta’adda. Har yanzu ba ta
sauya ba.
3.
An
dasa wa matasa mummunar tarbiyya ta ta’addanci na kisan kai a wuraren bauta da
wuraren gudanar da karatu. Mun shaidi wannan a Kano kan kisan Shaikh Jafar, da
Sakkwato, kisan Malam Umar ɗan Maishiya, da Kaduna, kisan Shaikh
Albani. Wane malami ya yi tasirin Shaikh Jafar a Kano? A Kaduna, wa ya kai
Shaikh Albani matasa? A Sakkwato, wace da’awa ta fi ta Umar ɗan
Maishiya razana Shi’a? Duk wani masanin da za a fahimci Shi’a a karatunsa a
ilmance, ba za su bar shi ba.[8]
4.
Daga
cikin manyan dasisar Shi’a akwai rusa karatun zaure/soro/allo. Shi’a ba ta zo
da karatu ba. Lacca da karatun mujallu da farfagandar siyasar duniya ta zo da
su. Galibin jagororinsu ba su iya karatu ba, balle su san darajarsa da ƙimarsa. Matasan da aka jawo ta fuskar
laccoci, laccocin ne makarantarsu ta farko. Da wannan dasisar, nagartattun
makarantunmu na ilmi suka durƙushe.
Dalili kuwa shi ne, matasa na wajen gudanar da zanga-zanga, manyan malamai na
tsufa suna mutuwa; majiya ƙarfi
na wajen ƙwadago da kasuwanci da aikin gwamnati. An
yi ɓatan ɓakatantan ba a ga tsuntsu ba a ga tarko.
Allah Ya isa!
5.
Daga
cikin dalilan yaƙar Turawan mulkin mallaka a Nijeriya ta
Arewa akwai tsoron gurɓata tarbiyar mata. A kowace ƙasa aka cire wa mata kunya, babu sauran
zaman lafiya. Ƙasar da duk shegu suke da rinjaye, da ita
da maƙabarta zozo-zozo suke. Tsarin salon ilmin
Bature na cakuɗa maza da mata wuri ɗaya,
ya rusa kunya a idon matanmu. A tsarin Shi’a, wannan ba komai ba ne. Budare da
matan aure ke jerin gwanon zanga-zanga da bukin maulidi, da lacca da kallon
finafinai da fita daga garin da ake zuwa wani gari na daban na tsawon kwanaki
ba tare da kulawa da wane ne muharrami, wane ne ba shi ba? Cikin wannan
yaudarar aka tallata musu auren mutu’a,[9]
aka mutu gaba ɗaya. Matashi da matashiyar da ta saba da
auren mutu’a ba ƙaramin kira ke sa su waiwayo ba.
6.
Bisa
kyakkyawan zato, ba shauƙin
wa’azi kawai ya juyar da hankulan matasanmu suka fantsama cikin wannan fitina
ba. A kwana rawan atisaye, a yi tafiyar fanfalaƙi mai tsawo, a ɗauki
makami a kashe mai salla, dole da lauje cikin naɗi.
Babu wai, an sa matasa shan miyagun ƙwayoyi,
wanda yake wani tsari ne na musamman da duniyar yau ta shirya domin rusa
Nijeriya ta Arewa, wadda ake jin ita ce ta ɗaya
a duniyar addinin Musulunci.[10]
Babbar
Magana:
Ina kyautata zaton kashi 75% a cikin 100%
daga cikin masu da’awar aƙidar
Shi’a a Nijeriya ta Arewa da cewa ba su san Shi’a ba ta yarda da Alƙur’ani ba; ba ta yarda da Manzon Wahayi
Jibril (AS) ba; ba ta yarda da wanda aka yi wa wahayin ba (Manzon Allah SAW).
Wannan makircin na ilmi ne kuma a ɓoye yake cikin littattafan manyan shehunan Shi’a na
duniya. Shehin Shi’a Abdullahi Shubbar ya ce: “Ƙur’anin da aka saukar wa Annabi (SAW) ya fi wanda ke a
hannunmu a yau. Na hannunmu akwai maguɗi a ciki…”[11]
Don haka, Shehunsu Al-Kalbi ya ce: “Ƙur’anin
da Jibirilu ya saukar ga Annabi (SAW) ayoyinsa dubu goma sha bakwai ne
(17,000).”[12]
Shi’awa sun tabbatar da cewa ba ga Annabi Muhammad (SAW) aka aiko Mala’ika
Jibril (AS) ba, ga Ali (RTA) aka turo shi da wahayi, ya yi kure, ya kai ga
Annabi Muhammad (SAW). Don haka, a tafsirinsu Tafseer Al-Ƙur’an na Shaikh Jabir bn Yazeed bin Al-Haarith Al-Ja’fi
Al-Kufi (ya rasu 127AH) suka kafirtar da Sahabban Annabi (SAW).[13]
Idan Alƙur’aninmu ba cikakke ba ne, Manzonmu ba
shi aka nufa da wahayi ba, kure Mala’ika Jibril (AS) ya yi, Sahabban Annabinmu
(RTA) riddaddu ne ko kafirai, ina sauran Musulunci a bangon ƙasa? Gudun leƙo waɗannan abubuwa, Shi’a ta fito da dasisar ba kowa ya
kamata ya yi karatu ba, muradi dai shiga Aljanna, don haka, a bar wa Shehunnai
karatu, muridai su bi ido rufe ba tambaya. Anya! Shi’a ba wani addini ba ne?
Ina
Mafita?
Matsalar da muke ciki a yau, ba ta muƙabala ba ce, ba ta faɗa ba ce, ba ta sa-in-sa da Shi’awa ba ce.
Ruwa sun kawo a wuya, aiki ya yi wa kurege yawa. Ya kamata a ce, mun mayar da
hankalinmu ga muhimman abubuwa da suka haɗa da:
1.
Bin
hanyoyin farfaɗo da nagaratar karatun allo da rayar da
karatun zaure da faɗaɗa shi. Gabanin yaranmu su buɗe
ido da komai, su tashi da aƙidarmu
a ilmance.[14]
2.
Mu
inganta makarantun Islamiyya tare da gwama su da nagartaccen karatun boko,
yaranmu su tashi wayayyi, yadda duniya duk ta juya suna kallon ta sara.
3.
Mu
yayyafa wa wutar ƙungiyanci da ɗariƙanci da mazhabanci da ɓangaranci
ruwa. Mu riƙa sara muna duban bakin gatari, yadda
fahimtarmu take, da kowa haka take, da an daɗe
da cigaba. Mu dai sa hikima ko ba a yarda da mu ba, mu samu ladar wa’azi.
4.
Yadda
ƙasarmu take ciki yanzu, babban makami ga ahlil
Sunnah, da malaman
sunnah, shi ne a rage kwaɗayi, da son abin duniya ido rufe. A ƙaurace wa fadanci da bambaɗanci
cikin da’awa. A nisanci miyagun kalamai da tonon silili da amayo kalmomi masu
haƙorin cizo ga saɓanin
da bai taka kara ya karya ba.
5.
Masu
da’awar sunnah dole su cire rowa a zukatansu. Wajibi ne a nisanci makabtattar
hasada. Tilas a yi jifa da son girma da biɗar
a sani da bugun gaba da zaƙewa.
Zaman jiran afafa (banza) da zakka da sadaka, ba na ‘yan sunna ba ne. Dole mu
tanadi wasu hanyoyin da za mu ƙarfafa
ma’abota sunna ka da bidi’a da shirka su farauto su ba da saninsu ba.
Naɗewa:
Akwai buƙatar
mu sani cewa da’awar Shi’a a Arewa ta sa mun yi hasarar matasa a ma’aikatun
tsaro da likitoci da injiniyoyi da ‘yan jarida da fannonin aikin hukuma da
dama. Wajibi ne mu ƙarfafa yaranmu su
shiga ayyukan tsaron ƙasarmu
gadan-gadan. Ba mu da ƙasa
bayanta, ba mu kore kowa a ciki daga cikin ‘ya’yanta, ba wanda ya isa ya kore mu.
Saboda haka, tashi tsaye mu kare ta da karatunmu da makamanmu wajibi ne. Lokacin
abu a yi shi, ka da mu ja baya ga zaɓen shekarar 2019, ka
da mu yarda a saye ‘yancinmu zaman lafiya ya gagare mu. Mu zavi mai ƙaunarmu,
mai ƙaunar ƙasarmu,
mai kare mutuncinmu da na ƙasarmu.
Ka da mu yarda a yi amfani da mu a yi maguɗi ko a tada fitina.
Ku tuna, fitina ba ta taɓa rutsawa da manya ko
‘ya’yansu ba, sai dai mu talakawa. A karantarwar Musulunci, babu fitinar da ke
da sahihin nassi.
[1]
Shaikh Al-Mufeed, Awaa’il al Muƙaalat fee
Almadhaahib al-Mukhtaarah, shafi na 35.
[2]
Ahasan bn Musa An-Nubukhti, Firaƙ
As-Shee’ah, shafi na 50.
[3]
Suraj, A. D. “Historical Deɓelopment of Shi’ah, Its Activities and Implication
to Muslims in Northern-West Nigeria”, PhD Thesis, 2012, p. 96-97.
[4]
Marubucin wannan littafi yana raye, kuma ya gabatar da shi ga Shaikh Abubakar
Mahmud Gummi domin ya yi masa ta’aliƙi, marigayi ya ƙi, ya kuma yi
masa nasiha. Ya san haɗarin
da ke ciki, kuma har yanzu bai musanta abin da alƙalaminsa ya
tabbatar ba. Na samu wannan bayani daga Mal. Aminu Salihu Gummi, lokacin da na
kai wa marigayi ziyara a gidansa na tarar da littafin na Muhammadu Isa Talata
Mafara ajiye kan teburin Shaikh Gummi. Wannan littafin ya mamayi ‘yan boko da
yawa suka shiga Shi’a, wasu suka ba ta goyon baya. Shiga sahun masu zagin
Sahabbai da goyon bayan masu yi, duk abu ɗaya
ne mai hukunci ɗaya.
Allah Ya kiyashe mu. Amin.
[5]
Duba lamba ta 3, shafi na 97.
[6]
Shaikh Abubakar Jibril ya yi wannan bayani a huɗubar
Masallacin Farfaru wajajen shekarar 1990. Shaikh Abubakar Tureta ya tabbatar da
zancen a Masallacin Bello a Sokoto (1990?).
[7]
An turo wannan littafi a ɗakin
karatu na CIS, UDUS, 1988, na fassara shi zuwa Hausa, ban samu wallafa shi ba.
[8]
Idan aka lura, waɗannan
shaihunai da aka kashe bas a tu’assibanci da taƙalidanci ga
kowace ƙungiya
ko ɗariƙa. Zunzurutun
karatunsu ake tsoro ya samu karɓuwa
a samu kafa gwamnatin da Shi’a ba za ta samu sakewa ba. Allah Ya isa!
[9]
Game da auren mutu’a, Imam Khumaini ya faɗa
a littafinsa Tahrir al Wasiilah,
(shafi na 112). Ya halatta a yi auren ɗanɗana
(mutu’a) tare da mace mazinaciya, amma a ƙi shi a zuci,
musamman idan an shaidi fitacciyar karuwa ce. Idan mutum ya yi auren mutu’a da
ita ya gaya mata ta daina zina. Hmn! Hausawa sun ce ba ta mutu ba ta ɓalgace.
[10]
A rahoton BBC na shekarar 2015 an ce Nijeriya ta fi kowace ƙasa a duniya ga
rungumar Musulunci gadan-gadan ta tsayar da shi a aikace. A Nijeriyar ma a
Arewa aka ce, abin ya tabbata. Don haka, maƙiya suka biyo mu
da dasisar safarar ƙwayoyi
ana haukata matasanmu. A halin da ake ciki, Kano da Katsina da Sokoto da Kaduna
nan ake jinge Tramol da Babba Juji (Cocaine), da Tabar Wui-wui. Ana bai wa
‘ya’yanmu da sunan zikiri da wuridi da jihadi a ƙwazon aiki da ƙarfin jiki, daga
nan sai a haukace.
[11]
Almaazandiri, Mir’at Al-Uƙool fee Sharh
Akhbaar Ar-Rasool, Juzu’i na 13, Shafi na 525.
[12]
Usool Al-Kaaf, Juzu’i na 2, Shafi na
826.
[13]
Abdulrahman bn Sa’ad bn Ali, Doctrines of
the Twelɓe Shiite (Enƙuiry and Response), p. 33.
[14]
Abin kunya ne Musulmi suna kallo ana ba
kalmar ‘Almajiri’ fassarar son kai ta cin zarafi da cin irlin Musulmi da
Musulunci. Dole mu tashi tsaye mu ga yadda za mu magance matsalolinmu da kanmu.
No comments:
Post a Comment