Monday, October 14, 2019

Wane Ne Narambaxa? Ibrahim Narambaxa Buhari Maidangwale Abdulkadir Tubali (1890-1963)



‘Narambaɗa’ laƙabi ne da ake yi masa ga karyar farautarsa da ya yi wa suna Rambaɗa. An haife shi a garin Tubali shekarar 1890. Sunansa na yanka Ibrahimu, sunan mahaifinsa Buhari Maidangwale, sunan kakansa Abdulƙadir, sunan mahaifiyarsa Riba.[1] Sunan kakarsa mace Binta. Mahaifinsa Babarbare ne daga ƙasar Nijar, mahaifiyarsa mutunniyar Badarawa ce gidan Sarkin Makaɗa Ɗangwamna. Don haka, Narambaɗa
Wane Ne Narambaxa?
Ibrahim Narambaxa Buhari Maidangwale Abdulqadir Tubali (1890-1963)


Aliyu Muhammadu Bunza
Tsangayar Fasaha da Ilmi,
Sashen Harsuna da Al’adu,
Jami’ar Tarayya Gusau

ABSTACT
“Who is Narambaɗa?” is the title of the paper under review. To give the title fair treatment, the Hausa proverb, ‘Kamar Kumbo kamar kayanta’ (Like father, like son) was employed in the analysis of the study. A cultural study of the available secondary sources (published and unpublished) on the life and history of Ibrahim Narambaɗa necessitates further investigations to ascertain the historical origin, life, death and contributions of the great singer. The result obtained during the field work were critically examined through his popular songs to justify the relevance of his poetic opinions in the study of his auto-biography. Thus, (51) verses were selected from his (40) popular songs to demonstrate who is Narambaɗa in the world of Hausa oral songs. Furthermore, the paper raised twelve research questions and were correctly handled by Narambaɗa in the philosophy of his songs. Certainly, Narambaɗa’s name rings a bell in the history of Hausa court music in Nigeria and beyond. Ibrahim Narambaɗa Buhari Maindangwale Abdulƙadir Tubali was born in Tubali in the year 1890, died in 1963 at the age of 73. The fact that death is inevitable and so his contributions to be forgotten. Indeed, it was in his poetic opinion that potential singers remain alive forever.



TSAKURE
Na yi wa takardata take: “Wane ne Narambaɗa” domin share fage masu ayyukansa da masu son su san shi. A binciken an yi amfani da ra’in kamar Kumbo kamar kayanta domin a fito da hoton Narambaɗa cikin waƙoƙinsa. Domin kai ga nasarar bincike. An gabatar da rangadi, garin Tubali da masarautar da ya yi wa waƙoƙi. An tattauna da su, da iyalansa, da abokansa da masana waƙoƙinsa da halayensa. An yi ƙoƙarin kwatanta abubawan da aka samo da shahararrun waƙoƙinsa. Don haka, an leƙo fitattun waƙoƙin Narambaɗa (40) aka tsinto ɗiyan waƙoƙi (51) aka ɗora nazarinsu a fasula (16). Taken takardar an ɗora shi a kan tambayoyi (12) waɗanda ake haƙiƙanin cewa binciken ya fito da amsoshin su. Binciken ya gabatar da shaharar Narambaɗa a fagen waƙoƙin Sarauta kuma har ya bar duniya sai dai a ce kaico! Kama da wane ba wane ba ne. An ci nasarar fito da sakamakon bincike (5) da shawarwari (5) domin taskace ayyukan Narambaɗa. An haifi Ibrahim Narambaɗa Buhari Maidangwale Abdulƙadir a Tubali ƙasar Shinkafi jihar Zamfara 1890 ya rasu 1963 yana ɗan shekara 73, a yau shekarar 2019, yana da shekara 56 da rasuwa. Allah Ya gafarta masa. Amin!


Gabatarwa
Da wuya a faɗi wani abu sabo a kan makaɗa Narambaɗa da magabata ba su hango ba.[2] Duk da haka, ba a rasa tsintuwar dami a kala ba. Maƙasudin wannan ɗan bincike shi ne tattaro gutsattsarin labarai da bayanai da suka shafi Narambaɗa domin a tace fitaccen batu da zai fito da haƙiƙanin hoton Narambaɗa a duniyar adabin Hausa. Babban buri shi ne, fayyace taƙaitaccen tarihinsa da fasaharsa da halayensa da gurbinsa a duniyar mawaƙan baka na Hausa.  Nazarin zai yi madogara da yadda waƙoƙin Narambaɗa ke bayyana wane ne Narambaɗa ga waɗanda suka san shi da waɗanda ba su san shi ba. Shaharar Narambaɗa a duniyar ƙasar Hausa ta fi ta ƙasar Isa da Sarkin Gobir da yake yi wa waƙa. Waƙar Ɗanhilinge hujja ce:
Jagora:        Sarkin Gobir na da doki irin
                   :Irin dokin ga da yay yi suna
Yara:          Ga talitta komiy yi suna
                   :Mutane na shagalin ganinai

Dabarun Bincike
          Binciken da na yi a kan makaɗa Narambaɗa na tsawon shekaru 5-10 ya ba ni damar fahimtar wane ne makaɗa Narambaɗa? Kundin digirin farko da ya fara leƙo Narambaɗa shi ne Udu (1972). Haka kuma, Bello (1979) ya ƙyallaro rayuwar makaɗa Narambaɗa da waƙoƙinsa. Babban aikin PhD na Sada (1982) ba a kammala shi ba a SOAS, Jami’ar Ingila (ɗalibin ya rasu). Gusau (1987) ya juya jerin wasu waƙoƙinsa. Bunza (1998) ya yi yunƙuri irin na wannan takarda ya taƙaita su ga falsafar waƙoƙinsa. Shinkafi (1998) ya Harari shahararrun waƙoƙinsa. Matsakaicin aiki da aka yi kan Narambaɗa shi ne Bunza (2009) a matsayin wallafaffen littafi kan rayuwar makaɗa Narambaɗa da waƙoƙinsa. Ratsa waɗannan ayyuka ya ba ni ƙarfin guiwar shiga mataki na biyu na bincikena. Na tattauna da abokansa da ɗiyarsa Hajo da mutanen garinsu Tubali da mutanen unguwarsu da waɗanda suka san shi suka nazarci waƙoƙinsa a Zamfara da kewayenta.[3] Hannayena sun kai ga ayyuka da dama da aka yi a kan Narambaɗa jiya da yau. Na samu kai ga dukkanin shahararrun waƙoƙinsa da suka bayyana a gidajen rediyo da na garmaho da bakunan wasu haziƙai masu sha’awar waƙoƙinsa. Bayan na yi kakaci cikin waƙoƙinsa sosai sai na shiga hira da tattaunawa da waɗanda suka san shi a raye suka yi hulɗa da shi, suka zaune shi, suka san wani sirri daga cikin sirrin waƙoƙinsa.[4] Wannan ya ba ni damar tunanin cewa, lallai ina iya fitowa da kyakkyawan tarihin Narambaɗa da halayensa bisa ga luguden waƙoƙin da ya zuba a rayuwarsa. Shirin shiga ruwa tun tudu ake kimtsa shi domin makaɗa Narambaɗa ya ce:
Jagora:        Ah ji wanda bai san hanya
                    :Ya yi sabko amma fa ya ɓace ya dawo
Yara:           Ila da yat tahi bai ɗora tambayan kowa ba
Gindi:          Ginshimin Haliru uban zagi na Malam Isa
                    :Gagarau jikan Shehu Iro toron giwa

Ra’in Bincike
          Ina ɗaya daga cikin ɗaliban da ke da ra’ayin cewa, a fagen ilmi, lokaci ya yi ga kowane tsuntsu ya yi kukan gidansu. Matuƙar muna tsayi a yi kare jini biri jini mu ƙwato ‘yancin kanmu mu tabbatar da ƙasarmu ta gado bisa ga dokokin da suka dace da al’adunmu, dole ilminmu na cin gajiyar duniyarmu ya rausaya amon gangarmu ta gado.[5] Ban ce, a yi watsi da ra’o’in bincike na Turai ba, amma da wace hujja za mu dunƙule namu idan suna isar da saƙo daidai da tunaninmu?[6] Na ɗora wannan bincike a kan tunanin Bahaushe da ke cewa: “Kamar Kumbo kamar kayanta”.[7] Idan aka sa natsuwa aka dubi tarkacen Kumbo da kyau, za a gano ina ta fito? Ina za ta? Ina kayanta na asali? Ina waɗanda ta saya? Ina waɗanda aka ara mata? Wane labari tarkacenta za su bayar na halayenta? Babu shakka, kayan da Narambaɗa ya taskace cikin manyan waƙoƙinsa sun isa su fito da cikakken hotonsa.
          Gudummuwar Narambaɗa da ta ƙarfafa ra’inmu ita ce:
Jagora:        Ɗan bajini shi ka zama bajimi
Yara:           Yai bobakali yai tozo
                    :Ɗan akuya na kallo.
Gindi:          Na riƙa ka da girma Abdu ƙanen mai daga.

Tambayoyin Bincike
          Irin wannan bincike yana buƙatar a daidaita akalarsa ga manyan turakun da ake son a ɗaure shi. Babbar tambaya a nan ita ce, yaya al’umma ke kallon makaɗa Narambaɗa da yadda shi yake kallon kansa? Wane gurbi yake ciki daga cikin gurabun mawaƙan Hausa? Yaya shahararsa take a cikin shahararrun mawaƙan Hausa? Me ya bambanta shi da sauran mawaƙa a cikin sana’ar waƙa? Waɗanne ne shahararrun waƙoƙinsa? Wace ce bakandamiyarsu? Wane sirri ke cikin waƙoƙinsa na ratsa zukatan masu sauraro? In an samu dacewa da fashin baƙin waɗannan tambayoyi sai mu ce, komai ya yi an ba gwauro ajiyar mata. Waɗannan tambayoyi da na tsara bayaninsu makaɗa Narambaɗa ya ce:

Jagora:        Taro na tambaye ku
                    :Shin kowag ga wuta
Yara:           An ka ce a ɗebo, wa ka zuwa?
                    :Wanda yag gani ka zuwa
                    :Kowas shaida shi ka shan rana
                    :In bai tai ba yai batun banza
                    :Ko can dauri shi batun banza
                    :Daɗin hwaɗi garai
Gindi:          Ya ci maza yak wan shi na shire
                   :Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.

Wane Ne Narambaɗa?
          ‘Narambaɗa’ laƙabi ne da ake yi masa ga karyar farautarsa da ya yi wa suna Rambaɗa. An haife shi a garin Tubali shekarar 1890. Sunansa na yanka Ibrahimu, sunan mahaifinsa Buhari Maidangwale, sunan kakansa Abdulƙadir, sunan mahaifiyarsa Riba.[8] Sunan kakarsa mace Binta. Mahaifinsa Babarbare ne daga ƙasar Nijar, mahaifiyarsa mutunniyar Badarawa ce gidan Sarkin Makaɗa Ɗangwamna. Don haka, Narambaɗa karen makaɗa ne bai gaji kiɗi ga uba ba, ga uwa ya gada.[9] Ya rasu a 1963, a yau Satumba, 2019, Narambaɗa na da shekara 56 da rasuwa. Ya rasu yana ɗan shekara 73 bisa ga riwayarsa mai cewa:
Jagora:        Na bar ƙarya ko ina kiɗi
                   :Na wuce ƙarya ko ina kiɗi
Nai sittin saba’in nika hwaɗa
                    :Mai saba’in yai ƙarya
Yara:           Ana ta zunɗe nai
                    :Ko yaran da ag garai
                    :Duk warwatse mishi sukai
                    :Shina yawo shi ɗai ɓaro-ɓaro
Gindi:          Ya ci maza ya kwan shina shiri
                    :Uban zakara dodo na Ummaru

          Ga alama an yi wannan waƙar wajejen shekarar 1960 da wasu ‘yan watanni, ya rasu a 1963. Tana daga cikin waƙoƙin ƙarshe-ƙarshen rayuwarsa.

Gurbin Narambaɗa Cikin Gurabun Makaɗan Hausa
          Masana adabin waƙa sun karkasa makaɗa da mawaƙan Hausa gurbi-gurbi bisa ga tubalin waƙoƙin da suke yi da waɗanda aka fi saninsu da su.[10] Waƙoƙin Narambaɗa sun taɓo gurabun rukunin mawaƙan baka da dama. A tarihi, waƙoƙin maza ya fara yi, da na noma da kokuwa. Ya shiga cikin waƙoƙin sha’awa idan aka kalli waƙar Dokin Iska Ɗanhilinge. Mawaƙin jama’a ne idan aka waiwayi waƙoƙin Alhaji Ɗandurgu Magatakarda da sauransu. Fitaccen mawaƙin yaƙi ne bisa ga lura da waƙar Sarkin Kware da Ɗankulodo.[11] Ya leƙo cikin mawaƙan raha da ban-dariya idan aka harari waƙar Sarkin Munafukai da idon basira. Bisa ga hukuncin da ya yanke wa kansa, shi mawaƙin Sarauta ne a faɗarsa cikin Waƙar Gogarman Tudu:
Jagora:        Kak ku haɗa ni da yaro
Yara:           Kun san yaro bai yi fasahata ba
Jagora:        Kak ku haɗa ni da yaro
Yara:           Kun san yaro bai yi zalaƙata ba
Jagora:        Ƙaryar banza ƙaryar wohi
:Wane yaro inda Narambaɗa
Jagora:        Mai tabarukun Sarki
Gindi:          Gogarman Tudu jikan Sanda
                   Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.

Ya fito ƙarara cewa shi makaɗin sarauta ne mai tabarukun Sarki, wato wanda Sarkinsa ya sa wa albarka, ya cire kayan da ke jikinsa ya ba Narambaɗa ya saka.[12] Wane Sarki ne ya yi masa haka? Uban gidansa Sarkin Gobir na Isa Amadu. Narambaɗa ya tabbatar da wannnan hasashe a bakandamiyarsa da yake cewa:
Jagora:        In an ce Isa ba ka jin an ce wani Sarki
Jagora/Yara: Ni ko duk Hausa ba ka jin waƙa bayan tau
Gindi:          Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
                   Baban Dodo ba a tammai da batun banza.

          Narambaɗa makaɗin fada ne, mawaƙin sarauta, duk waƙarsa da ba ta sarauta ba, ba ta gwada tsawo da ta sarauta domin ya fi sanin sarauta da komai. Babban uban gidan Narambaɗa shi ne Sarkin Gobir Amadu, wani ba shi ba ɗan rakiya ne a tafiyar Narambaɗa. Wannan hukunci Narambaɗa ya tabbatar da shi a Bakandamiyarsa, inda yake cewa:                
Jagora:        Kul na so kiɗi gidanka nikai can yaf fi
Jagora:        Na Magajin Gari na Jekada Audu
Yara:           Ga gidan sarki ban zuwa
:Gidan wani mai ‘yar garka
Gindi:          Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
                   Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
         
Tirƙashi! Ashe duk wata garka in ba ta sarki ba ce ƙarama ce.

Narambaɗa A Bakin Narambaɗa
          Magabata na cewa, mutum ya fi kowa sanin kansa, don haka da dahuwa da suya da banda duk gashi ya fi su sanin asirin wuta. Buƙatata a nan, in ɗan waiwayi wasu ɗiyan waƙoƙi da makaɗa Narambaɗa ya ambaci sunansa da kansa mu ji yaya yake kallon kansa a sana’arsa ta waƙa. A ɗan binciken da na yi, makaɗa Narambaɗa ya ambaci sunansa “Narambaɗa” sau shida a cikin waƙoƙi biyar mabambanta waɗanda ke karantar da mu game da rayuwarsa da yanayinta.
          Na farko, dai ya baƙunci fadar Zazzau a zamanin Sarki Ja’afaru ya ba Zagezagi labarin wane ne Narambaɗa? Ga abin da yake cewa:
Jagora:        Narambaɗa na malamin kiɗi    
Yara:           In ka ce “maraba”
:Mui ta kiɗi har mu kwan bakwai
Gindi:          Ɗan Isyaku Makaye
                   :Jafaru mai halin mazan jiya
                    :Zauna da lahiya

          Duk da kasancewar Narambaɗa magori wasa kanka da kanka, babu wani daga cikin makaɗa ko mai nazarin waƙa ko mai sha’awar nazarin waƙoƙin Hausa da zai saurari Narambaɗa ya kasa ce masa “Malam” a fagen waƙa. Tun gabanin Narambaɗa ya kira kansa da sunan haka nan manyan mawaƙan Hausa ke yi masa suna.[13]
          Na biyu, kasancewarsa malamin kiɗa, karatun da ya zuba a cikin waƙoƙinsa suna nan tare da sunansa har abada ba za su ɓata ba. Abin mamaki, manyan malamai sun bar duniya da shekaru aru-aru amma ga littattafansu nan suna waƙiltarsu ka ce suna raye ba su mutu ba. Allahu Akbar! Ashe shi ya sa Narambaɗa ya gaya wa fadawan masarautar Isa cewa:
Jagora:        Fadawa ku bugan in buge ku,
          :         Mui ta hwaɗanmu gidan duniya
Yara:           Kun san ba a hwaɗa lahira
Jagora:        Ko can ku ka zuwa lahira
Yara:           Narambaɗa ba ya zuwa lahira
                    :Ko ya zo ɗauke mai a kai
Gindi:          To ya matsafa Sadauki na Audu
                    :Baban Isa baban Buwai
                   :In donna ka gama lahiya.

          Bayan ya nuna makaɗin fada ne kuma abokin mazauna fada ne. A karatun Narambaɗa, gawurtaccen makaɗi malami ne da ba ya mutuwa. Masarauta da sarakai da fada da fadawa na mutuwa a daina jin labarinsu gaba ɗaya, amma mawaƙin da ya shahara irin sa ba ya mutuwa. Kai! Ko an ga ya mutu, mutuwa ta haƙiƙa dawowa yake yi domin a koyaushe aka tuna hikimominsa an rera su ko ba a rera ba, ya dawo duniya.[14] Yau mutane nawa ke tuna Sarkin Gobir Amadu da fadawansa da sarautarsa? Tirƙashi! Ga duniya ta haɗe ko’ina ana nazarin waƙoƙin Narambaɗa da hikimominsa. Babu wai, Sarkin Gobir Amadu da fadawansa da Narambaɗa sun tafi lahira amma Narambaɗa ya dawo.
          Na uku, yayin da ya ziyarci fadar Kwatarkwashi zamanin Sarki Alu sunansa Narambaɗa ya fito ƙarara a cikin mabuɗin ɗan waƙarsa da yake cewa:
Jagora:        Uban kiɗi Narambaɗa
                   :Yau ga ni ga Kwatarkwashi
Gindi:          Yai halin mazan jiya
                   :Ɗan Sanda mai Kwatarkwashi

          Ga alama, wannan ɗan waƙa ya nuna cewa Narambaɗa zuwansa na farko ne Kwatarkwashi. A lokacin da Narambaɗa ke cikin zamaninsa, babu wani makaɗi da ke gabansa a fagen kiɗi, shi ne uban mawaƙan zamaninsa. Ko kusa ba yana nufin shi ne uban ƙungiyarsa ta kiɗi ba, a’a ha, abin nufi shi ne, a cikin sana’ar Bahaushen kiɗi shi ne uba. Masarautu da yawa na fatar ganin Narambaɗa fadarsu ya taya su hira, a Kwatarkwashi an sha neman ya zo, bai je ba, sai mulkin Sarki Alu/Aliyu.[15] Duk da kasancewar Narambaɗa makaɗin fadar Isa, masarautu da yawa na gayyatarsa saboda shaharar fasaharsa a waƙoƙin fada.
          Na huɗu, a fadar Ƙaurar Namoda da ya je murnar naɗin sarautar Sarki Abubakar, ya haɗa sunansa na yanka Ibrahim da Narambaɗa wuri ɗaya yana cewa:
Jagora:        Iro Narambaɗa na zaka murna
                    :In kwan biyu in ga Abubakar
Yara:           Daɗa kau na san abu ya yi
                    :Shiri bajimin Mamuda
                    :Abu na Namoda shirarre

          Haƙiƙa na yarda da zancen Sarkin Zazzau Jafaru da ke cewa: “abu biyu ba sa armashi sai da makaɗa, sarauta da aure”. Wannan ɗan waƙa ya ƙara jaddada cewa, Narambaɗa fitaccen shahararre ne a ƙasar Zamfara, waƙar fada ba ta armashi in ba shi a wuri. Lallai a fagen waƙar fada Narambaɗa ne shugaba wani ba shi ba yaro ne a Zamfara, zancen nashi ƙasa ne babu kure:
Jagora:        Wane yaro inda Narambaɗa
Yara:           Mai tabarukun sarki
Gindi:          Gogarman Tudu jikan Sanda
                   :Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa

          Na shida, makaɗa Narambaɗa ya kira kansa babban kare a waƙar: “Ya hana wargi na Malam…” Yana cewa:
Jagora:        Narambaɗa babban kare na
                    :Sa’ad da nai rida
Yara:           Ban kashe laƙai-laƙai ba
                    :Ina ɓata fata
Gindi:          Ya hana wargi na Malam
          Babban kare, wato babban mawaƙi da in ya yi zambo zai muzanta mutum sosai sai an san shi ko’ina.
          Waɗannan su ne wurare shida da Narambaɗa ya kawo sunansa da kansa. An samu wuri ɗaya da ‘yan amshi suka ambaci sunansa cikin wata waƙar ga-ni-ga-ka tsakaninsa da yaransa da suke cewa:[16]
Jagora:        Da mai hashin wuta
                    :Da mai kashin wuta
                    :Da mai rabon hwaɗa
                    :Da mai haɗin hwaɗa
                    :Su duk huɗu sun taru sun game
                    :Ba mu samu guda wanda yah hi ba
Yara:           Narambaɗa komo ga gaskiya
                    :Mai kashin wuta ya fi mai hashi
                    :Mai rabon hwaɗa ya fi mai gami
                    :Ni kan ga irin wadda nag gani
                    :Ka san jimina ta hi zarvi
                    :Babban guru ko tai masassara.

Dangantakar Narambaɗa Da Makaɗan Zamfara
           Narambaɗa karen makaɗa ne don haka wasar zumunci ke tsakaninsa da sauran takwarorin sana’arsa.[17] Ba a samu wurin da ya yi faɗa ko mummunan zambo da cin fuska ko cin mutuncin wani makaɗi ba. Ya tabbatar da kyakkyawar zamantakewa a faɗarsa:
Jagora:        Zamfara ba makaɗin da ka ja mani
                    :Baya ga Jankiɗi sai ko Ɗandawo
Yara:           Sai Ɗandodo Alu mai taushi
                    :Amma ba makaɗin gayya ba

Gindi:          Gogarman Tudu jikan Sanda
                    :Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa

          Wannan waskiyar da ya yi ta toge fitattun makaɗa a Zamfarar zamaninsa, ta tabbatar da soyayya tsakaninsu.[18] Ya ƙara wannan ƙullin zumunci a Bakandamiya da yake cewa:
Jagora:        Na jiya Jankiɗi
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Na jiya Zamau
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Na jiya Gurso
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Na jiya Akwara
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Na jiya Ɗandawo
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Na jiya Nagaya
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Dodo malamin waƙa Ƙundumi Magajin Ɗanɓaidu
Yara:           Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora:        Kullun jin nikai azanci na hudo min
Jagora:        In wani ya hi ni martaba ni kau na hi wani
                   … … … … … … … … … … … … …
Gindi:          Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
                    : Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

          Waɗannan jigajigan makaɗa bakwai da ya ambata: Jankiɗi, Zamau, Gurso, Akwara, Ɗandawo, Nagaya, Dodo Malamim Waƙa Kundumi Magajin Ɗanɓaidu a duniyar ƙasar Zamfara, wani ba su ba, ba fitacce ba ne a waƙar fada. A duk ɗan bincikena ban ci karo da wani ɗan waƙa daga cikin waƙoƙin Narambaɗa da aka kushe su ko tsokane su ko yi musu habaici ba. Haka su ma ba su taɓa yi wa Narambaɗa ko shaguɓe ba. Hasali ma babu wani mawaƙi daga cikin mawaƙan Zamfarar zamaninsa da ya kawo sunayen waɗannan makaɗa gaba ɗaya ba sai makaɗa Narambaɗa. Bai yi bugun gaban cewa ya fi ko ɗaya daga cikinsu ba kamar yadda bai nuna wanda ya fi shi ba a cikinsu. Wannan ya tabbatar da kasancewar Narambaɗa cikakken wayayye wanda ya san siyasar zamantakewa.

Hoton Narambaɗa A Duniyar Sana’o’in Da Suka Ratse Shi
          Tunanin kamar Kumbo kamar kayanta ya sa ake farauto ayyuka ko sana’o’in da mutum ya naƙalta a cikin tunaninsa da fasahohinsa. Narambaɗa ya gaji noma kuma manomi ne, ya gaji kokuwa kuma ya yi ta. Farauta da kamun kifi ya iya su, tarihin Narambaɗa ba ya kammala idan ba a ambace su ba. Idan muka yi duba cikin fasahohinsa sun yi naso ciki sosai yadda wanda duk ya san sana’o’in ya ci karo da su cikin waƙoƙinsa ya san Narambaɗa ba ɗan haye ba ne a ciki ɗan asali ne don ya buɗe ido ciki sosai. Yadda ya kwatanta mai gona da mai ga noma ya isa misali:
Yara:           Mai ga noma bai yi ƙwazon mai gona ba.
Gindi:          (Bakandamiya)

          Ga abin da yake faɗa a kan farauta babu kare a hannu aikin banza:
Jagora:        Mai kare ka farauta
Yara:           Maras kare na ta bugun haki
Jagora:        Ya tayas a kashe
Yara:           A bar shi nan sai haɗiyar miyau
Gindi:          Jikan Mamman Tukur maza ba mata ba ne,
                   :Ɗan namajin duniya a gaishe ka Guraguri
         
A wata waƙar yana cewa:
Jagora:        Banza sha ramin maras kare
Yara:           Sai kuwwa sai ko wanda yak kasa
                    :Ya ce masa: “Amshi rataya”
Gindi:          Ya ci maza ya kwan shina shire
                    :Gamda’are Sarkin Tudu Alu

          Da ya zo ga kokuwa da ya gada daga mahaifinsa Maidangwale kuma shi ya yi ta sai ya buɗe da faɗar:
Jagora:        Bamin kokuwa bai iya ba
                    :Shi aka shammata kodayaushe
Yara:           Ga wata kokuwa an wuce da shi
                    :Karsanai kakkaɓe mishi ƙasa
Gindi:          Ibrahimu na Guraguri
                    :Mai Shinkahi bajimin zagi
                    :Mu dai Allah Ya bar muna kaya.

          Sanin “bami” da “shammatar kokuwa” da “karsa” sai ɗan kokuwa da masaninta. Dubi irin haƙurin da Narambaɗa ke ba Sarkin Kiyawa Abubakar inda yake cewa:
Jagora:        Ƙaryar banza sukai Alu
Yara:           Yaro ko ga kokuwa
                    :Ya san mai kasai
Gindi:          Kai bajimin Namoda
                    :Gagara Gago na Zagi
                    :Iya gaba na Modi
                    :Baban Yarin Ƙaura

          Mun san cewa, ido ko bai ci ba ya san abin da ke cika masa tumbi. Duk da haka, a fagen dambe da kokuwa da sharo ƙwararre kaɗai ke iya rarrabe buwayayye tun ba a kara ba. Irin fadamar da ta yi male-male a Tubali da noma da kamun kifi da ake ciki sun ratsi tunanin Narambaɗa sosai. Kasancewarsa masuncin gaske ya kwatanta sarautar gari da sarautar ruwa yana cewa:
Jagora:        Da aka ce ku gaida ɗan mai taru
                    :Gara a ce mai taru
Yara:           Kwak kashe kifi nai
                    :Sai ya nasa gora nai
Gindi :         Na yaba ka da girma Abdu ƙanen mai daga
:Kan da mu san kowa, kai munka sani Sardauna

          Waɗannan shaharrun karin magana ne da sarkawa suka keɓanta da su. Bugu da ƙari, ambatar “taru” da “nasa kifi gora ba saka shi ba” ya ƙara tabbatar muna da cewa makaɗa Narambaɗa basarke ne ɗan sarkawa. Mai tababa ya dubi shawarar da ya ba Alƙali Abu:
Jagora:        In ka ishe gulbi ya cike
                    :Ko ba kowa ko ka iya
Yara:           Koma ka tsaya ganga ka kwan
Gindi:          Ya ɗau girma ya san yabo
                    :Mu zo mu ga Alƙali Abu.

          Tabbas ko ba a yi fashin baƙi ba sarkawa kaɗai suka san da:
Jagora:        Mai masaki ba shi gasa da mai jirgi
                    :In dai ruwa sui ruwa
Yara:           Mai masaki ba shi fis she ka
                    :Amma mai jirgi yana kai ka wajje.
Gindi:          Alƙali shiri nai da kyawo
                    :Shi yai zaune daidai-wa-daidai

          Narambaɗa masanin tudu da rahi ne da karkarar da Bahaushe ke shaƙatawa a ciki. Fitaccen ɗan wasa ne gaba da baya. Mawaƙin da ya yi irin wannan rayuwa dole ya yi ƙoshin kalmomi da dabarar sarrafa su yadda zai burge masu saurarensa.

Wutar Makaranta
          Zamanin da aka haifi su Narambaɗa ba a san boko ba, suna dottiɓensu boko ya baƙunci ƙasar Hausa. Babban inuwar da suka taras ita ce makarantar allo wanda duk bai amfanu da ilminta ba jahili ne. Malam mai Salati Limamin Tubali abokin Narambaɗa ya tabbatar mini cewa Ibrahim Narambaɗa almajiri ne sosai, ya sauke Alƙur’ani ya ratsi littattafan furu’a har zuwa Risala.[19] Haƙiƙa biri ya yi kama da mutum domin irin kayan da Kumbo ta ɗauko sun tabbata nata domin sun yi kama da ita. Waƙar Alƙali Abu hujja ce babba a faɗarsa:
Jagora:        An wa wani Alƙalin ƙasa
                    :Da babu sani taw walwale
                    :Bai san amma ba bai san sabbi ba
Yara:           Shi sai shi tsare “min” “nun guda”
                    :Can gaba kau “raa” “baa guje”
Jagora:        Iyakar sanin an nan
Gindi:          Ya ɗau girma ya san yabo
                    :Mu zo mu ga Alƙali Abu

          A cikin darzajen Bakandamiya ya yi hannunka mai sanda ga wutar makarantar da ta ratsi shi, yana cewa:
Jagora:        Shi ko makaɗi
Yara:           Ya gyara turu daidai an nan
Jagora:        Ni kau kun gane ni na dahe turuna
Yara:           Sai zuba waƙa nikai kama da ta Alfa Zazi
Gindi:           Gwauron Shamaki na Malam toron giwa
                    :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

          Alfa Zazi Madihin Annabi (SAW) ne, shi kuwa Ibrahim Narambaɗa Madihin Sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa ne, lallai Narambaɗa ba bisa jahilci yake zuba waƙa ba, domin ya san:
Jagora:        Duk ɗan malamin da yaƙ ƙi batun Allah
                    :Yak kaɗe baƙi
Yara:           To! Allah Shi na watse kaya nai
Jagora:        Shi kama yawo
Yara:           Yan nan gidan har ya zan kango
Gindi:          Gagarau mu buge Kangara Ali ‘Yandoto
                    :Ba ya son wargi, ba a kai mai batun banza

          A wajen waƙar Alƙali Abu, baƙaƙen da aka yi lugude na min nun guda raa baa guje magana ce babba daga “min rabbi”… Babu wanda zai fahimci muhimmancin Alfa Zazi in ba Ishiriniyarsa ya ratsa ba.[20] Zancen “kaɗe baƙi” da zaman gida “kango” kalmomin fannu ne sai wanda ya zauni buzun karatu soai. Kaɗe baƙi shi ne taushe sani a yi biris da shi. Kangon gida a zaure ana nufin gidan da babu almajiri, ya zama mataccen gida ke nan.

Kamar Kumbo Kamar Kayanta
          Maganganun da mutum ke furtawa hoto ne na rayuwarsa ta fuskar ɗabi’unsa da abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so. A cikin fuskokin waƙoƙin Narambaɗa abubuwan da za a karanto halayensa tsaf da ko shi bai isa ya musanta su ba.[21] Daga cikin halayen kowa ya shaidi Ibrahim Narambaɗa da su akwai son gaskiya da tsayawa a kanta. Wannan ce ke ba shi damar koɗa gaskiya a cikin jigon yabo na waƙoƙinsa. Fitattu daga ciki akwai:
Jagora:        Na hore ki gaskiya bari tsoron ƙarya
Yara:           Mai ƙarya munahuki Allah su yaƙ ƙi
                    :Har yau ba mu ga in da an ka yi mai ƙarya
                    :Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi

          A koyaushe, mai son gaskiya ba ya da maƙiyi sai maƙaryaci da ƙarya. Babban zambo ga Narambaɗa shi ne ya yi shaidun mutum da ƙarya. Tanadin da Bahaushe ke yi wa maƙaryaci na a turke shi,[22] yana daga cikin manyan ɗiyan waƙoƙinsa:
Jagora:        Taro na tambaye ku
                    :Shin ko wag ga wuta
                    :An ka ce a ɗebo wa ka zuwa?
Yara:           Wanda yag gani ka zuwa
                    :Ko was shadi shi ka shan rana
                    :In bai tai ba yai batun banza
                    :Ko can yanzu shi batun banza
                    :Daɗin hwaɗi garai.
Gindi:          Ya ci maza yak wan shi na shire
                    :Gamda’aren Sarkin Tudu Bala.

          Da an ce mutum ma’aboci gaskiya ne za a taras ɗabi’unsa na masu gaskiya ne. Duk da kasancewar Narambaɗa makaɗi ba ya zama inuwa ɗaya da dottijon banza maɓannaci, watau mazinaci. Daga cikin manyan miyagun kalamai da zai yi wa mutum shi ne ya jefe shi da kula wa matan da ba halalinsa ba. Ya fito da wannan jigo cikin waƙar, “Koma Shirin Daga…”
Jagora:        Dut ɗan Sarkin da kag ga ya lalace
                    :Ya shiga was an bori
                    :Ba shi da niyyar Sarki
                   … … … … … … … … … … …
Jagora:        Katakoro zakara, Katakoro zakara


Yara:           Katakoro zakaran ‘Yaɗɗamna[23]
                    :Koma shirin Daga
                    :Gwauron Bahago ɗan Iro.

          Narambaɗa ya zargi wani Ɗangaladima da irin halin yana faɗar:
Jagora/Yara: Yana shewa mata shi ka kira
Gindi:          Ya ci maza ya kwan shi na shiri
                    :Uban zakara Dodo na Amadu.

          Ɗabi’un son gaskiya da dage wa kanta ya sa wasu mutane na ganin Narambaɗa hutsu mai taurin kai buwai shiri domin ba ya son magana biyu a rayuwarsa. Halinsa da na Sardaunan Isa sun yi canjaras ga faɗarsa:
Jagora:        Dut Sarkin da kas sani
                    :Basaraken da kas sani
                    :Amadu ya hi shi ƙane shiryayye
Yara:           Babu batun banza kuba sakewa
                    :Kuma in yai tsaye ba mai kausai[24]
Gindi:          Na riƙa ka da girma
                    :Audu ƙanen mai daga
                    :Kan da mu san kowa
                    :Kai mun ka sani Sardauna.

          Tattare da haka, duk wanda ya kusanci Narambaɗa ya san shi da haƙuri da kau da kai ga ƙananan kurakurai da manya ga abokan hulɗa. Da uban gidansa Sarkin Gobir Amadu ya ɗan kuskure shi a taron da ba a sanar da shi ba, cewa ya yi:
Jagora:        Wani taro da an ka zo
                    :Ni ban zo ba ka yi dottaku
                    :Ina gidanmu labari yak kai min

Yara:           Ga dottiɓe zaune gun hanya kak kawo
                    :Kac ce Siddi Sa su gun mota haƙ Ƙaura
                    :Daƙ Ƙaura ka kai su Morikki da gaggawa
                    :Sarkin Ɓurmi na hwaɗin ka daɗe kai ƙarƙo
                    :To rannan kay yi taka
                    :Kay yi ta mai ɗan ƙarhi.

Waƙoƙin Narambaɗa A Duniyar Adabin Hausa
          Ga binciken da na yi, waƙoƙin Narambaɗa da ke hannunmu a yau ‘yan kaɗan ne ƙwarai. Waƙoƙin da ya yi da ba su samu shiga garmaho da gidan rediyo ba sun fi yawa.[25] An ce tsakanin Tudu Alu da Sarkin Gobir Amadu ya yi musu waƙoƙin da za su kai ɗari. Ina kyautata zaton waƙoƙin da ya yi sun kai tsakanin 500-1000 haɗa da na kokuwa na noma da na farauta da na gayya. A taƙaice, za mu karkasa waƙoƙinsa kamar haka:
i.                   Waƙoƙinsa na Sarauta sun fi yawa.[26]
ii.                 Bakandamiyarsa ita ce Gwarzon Shamaki.[27]
iii.              Waƙarsa da ta fi tsawo Bakandamiya.[28]
iv.               Gajeruwar waƙarsa ita ce waƙar ga-ni-ga-ka.[29]
v.                 Waƙoƙinsa sun shiga kowane lungu ƙasar Hausa.
vi.               Kafafen yaɗa labarai na gida da wajen sun taimaka wajen barbaza waƙoƙinsa.
vii.            Waƙoƙinsa da suka ɓata sun zarce na hannu yawa.

Narambaɗa AFasahar Waƙa
          Narambaɗa ba kai kaɗai gayya ne ba a wajen fasahar waƙa, yana da ‘yan amshi ƙwararru masu murya ɗaya.[30] Idan yana zuba waƙa ba a iya rarrabe muryoyin yaransa domin sun shige wa juna a ɗauka tare a aje tare. ‘Yan amshinsa ba irin ‘yan amshin Shata ba ne, su ‘yan faɗi-in-faɗi ne da amshi-iyas.[31] A fagen waƙa Narambaɗa ne jagora, amma da muhawara ta shiga dole ne ya ba su gari, domin sai an zauna da su a gida an yi tin-da-tin a kan kowace waƙa, da duk ya saɓa ko wahami ya ja shi ba za a bi shi ba, yaro zai shafi taushi a rausaya rawa sai ya dawo ga bagiren da yara suka tabbatar.[32] Wannan ja-in-ja sau biyu ta auku a shahararrun waƙoƙinsa cikin waƙar:
Jagora:        Da a ce ku gai da ɗan mai taru
          Ya ce:

Jagora:        Da a ce ku gai da ɗan mai gona

          Yara suka koma ga gindin asali na gida.
Yara:           Ginshiƙin Haliru uban zagi na Malam Isa
                    :Gagarau jikan Shehu Iro toron giwa

          Ya ce:
Jagora:        Ginshimin Haliru uban zagi na Malam Isa
                    :Gogaran jikan Shehu Iro mai Shanawa.

          Suka tilasta shi komawa ga “toron giwa”
          Yana daga cikin zalaƙar Narambaɗa in ya yi waƙa ba ya maimaita salonta na rerawa da sarrafa kayan cikinta na azanci. An shede shi cewa ko ya maimaita ɗan waƙa sai ya yi ƙaƙale na sassauya shi. Ga ɗan misali a duba:
Jagora:        Ɗan Sarki da yay yi doro
                    :Har yay yi ɗan ƙusumbi
                    :Abu dai duƙui-duƙui[33]
Yara:           Hwauhwau ba ka jin an naɗai Sarki
Jagora:        Ɗan Sarkin da yay yi doro
                    :Har yay yi ɗan ƙusumbi
                    :Abu dai cumui-cumui[34]
Yara:           Hwauhwau ba ka jin an naɗai Sarki
Jagora:        Ga su can ƙasaisanmu
Yara:           Irinsu ba su ƙulla komai ba
Gindi:          Gagarau mai buge Kangara Ali ‘Yandoto
                    :Ba ya son wargi ba a kai mai batun banza

Fasahar Narambaɗa Ga Matarkan Bayan Fage
          Masu sauraron adabi da ba masu nazarin adabi a ilmance ba su na yi wa suna “matarka bayan fage”. Da yawa za a taras, sun san waƙoƙin ciki da waje, kuma da kowane masani waƙa suna jayayya a kan ƙunshiyar waƙar da suka sani a saurare su amma ba manazarta waƙa ne ba a ilmance. Shaharar Narambaɗa ta sa su sha’awar sauraronsa har suke yanke hukuncin cewa:
1.     Waƙoƙin Narambaɗa kamar karatu ne, ba don kiɗi ba, ko a masallaci a rera su.
2.     Ba a taɓa tsintuwar zagi tsirara ko wata yasasshiyar magana ta assha ba a waƙoƙinsa.
3.     Giyar waƙa ba ta taɓa jan Narambaɗa ya yi izgili ko zantukan ɓatanci ba.
4.     A cikin waƙoƙinsa ba za a tsinci sunan mutum kai tsaye da sunan zambo ba. A nawa bincike, sunan mutum uku kawai suka taɓa bijirowa, Zangai, Yaɗɗamna da Magatakarda, kai hatta da su sakaye aka yi.[35]
5.     A cikin waƙoƙin da ya ƙware na Sarauta bai taɓa cin fuska ko cin zarafin wani Sarki ko ɗan Sarauta ba, sai dai hannunka-mai-sanda.
6.     Narambaɗa ya riski zamanin siyasar Nijeriya ta Jamhuriyyar farko amma bai taɓa yi wa siyasa ko ɗan siyasa waƙa ba.[36]
7.     Sarkin Gobir Amadu ne uban gidan Narambaɗa har Narambaɗa ya bar duniya ba su rabu ba kuma bai taɓa yin wata waƙa da ta fi ta uban gidansa tsaruwa da shiga jiki da azanci ba.[37]

Wuyar Aiki Ba A Fara ba
          An haifi Narambaɗa a Tubali an rufe shi a Tubali. Akwai maganganu barkatai kan mutuwarsa amma a haƙiƙanin gaskiya gajeruwar jinya ya yi.[38] Hirarsa ta ƙarshe ya yi ta a Shinkafi lokacin da Sarkin Kudu Macciɗo ya kai ziyara a can. Bayan rasuwarsa yaransa sun yi bibiyar wasu shahararrun waƙoƙinsa ba su yi tsawon rayuwa ba suka wuce. ‘Yarsa Hajo ita ta  makaro daga cikin zuriyarsa ita ta rasu 2017/18. Narambaɗa ya mutu da buri biyu a zuciya: Na farko, burin zuwa aikin Haji, Allah bai nufa ba. Allahu Akbar! Wani bawan Allah Ya sa an yi masa aikin bayan mutuwarsa. Na biyu, ya yi niyyar ya tuba da kiɗi ya koma makaranta, Allah bai ƙaddara ba. Ƙuduri na farko ya furta shi a Ƙaurar Namoda gidan Ɗandurgu.
Jagora:        Ba kuɗɗi nif fi so ba
                    :Na fi buƙatar a ji
Yara:           Ka hau Arfa da shi
Gindi:          Alhaji Ɗandurgu taimakon Allah ag garai  
                :Na lura da duniya akwai namijin arziki

          Burin tuba da waƙa ya ambace shi a Isa cikin waƙar Sardaunan Isa:
Jagora:        Fatata ka yi Sarki Isa
                    :In yi ma waƙa kowa shi jiya
                    :Yan nan in yadda kiɗi in tuba[39]
Yara:           Na riƙa ka da girma Audu ƙane mai daga
                    :Kan da mu san kowa, kai munka sani Sardauna

Faɗuwa Ga Ƙwallo Gwaninta
          Bahaushen na da ra’in da ke cewa: mutum duk ɗan tara ne bai cika goma ba. Ai don haka ne Bahaushe ke cewa: ana wata haka in ji gwanin rawa da ya faɗi. Akwai ‘yan wurare da dama da wahami kan ja Narambaɗa ya yi kure ko ya rage givi amma masu sauraro ba su hango ba, ko sun hango sai su yi masa fassarar wani sabon salo shiƙa da daddare in ji kaza. Bari mu fara da Bakandamya da yake cewa:
Jagora:        A yini ruwa a kwan ruwa kwaɗɗo sai lela
Yara:           Shi burgu na cikin rima wahala ta cimmai

          Wannan Bakandamiya ce, wanda ake yabo shi ne Sarkin Gobir Amadu waɗanda ake kushewa su ne ‘yan adawarsa. To! Mai lela cikin ruwa shi ne Sarkin Gobir waɗanda wahala ta cimma su ne ‘yan adawa. A nan, za mu ce Sarkin Gobir ne “kwaɗɗo”? Babu laifi don an cewa ‘yan adawa burgu “gafiya”. Ambaton gwarzon Sarki da sunan “kwaɗo” kuskure ne, domin “kwaɗo” a al’adar mawaƙan Hausa zambo ake yi da shi. Ai shi da kansa Narambaɗa ya yi wa wani zambo da “kwaɗo” yana cewa:
Jagora:        Kwaɗɗon gada ab bikin tabki
Yara:           Bana yai kuka hay ya rame
                    :Jiya na ga shi bai zan kowa ba
Gindi:          Bai ɗau wargi ba na Jekada
                    :Na Majikira baban ‘yan kwana

          Bugu da ƙari, a cikin gabatarwar Bakandamiya yana cewa:
Jagora:        Wanda yaz zaka kallo ya karkaɗe kunnenai
Yara:           Ga makandamiya za ni yi cikin manyan waƙoƙi

          Ga al’ada, mai kallo idanu zai buɗe ƙwala-ƙwala, mai sauraro zai karkaɗe kunne. Babu shakka wahami ya ja makaɗa da ya cewa ɗan kallo: “ya karkaɗe kunnenai”.
          A waƙar “Niƙatau” Santsi ya sake jan tunanin makaɗa da yake cewa:
Jagora:        Mu ci tuwo cikin nama
                    :Mu sha hura cikin nono
                    :Mi talakka yas samu
Yara:           Sai dai shi ci ɗan wake
Gindi:          Niƙatau bajinin Macciɗo
                    :Daɗinka halin girma
                    :Ya tada gidan Dandiɓa
                    :Ya ta da gidan Masu

          Ba a cin tuwo cikin nama sai dai a ci tuwo da nama. Haka kuma, ba a shan fura cikin nono sai dai a sha hura da nono. Ai a waƙar Magajin Shinkafi da irin wannan batu ya tuzgo cewa ya yi:
Jagora:        Mai kamak ka Ibrahim ka ga
                    :Ya sha hura da nono ƙundum!
                    :Ya ci tuwo da nama ga sutura
                    :Ga shi had da doki da ɗamre
Yara:           Da yab biye mutanen zamani
                    :Sun ka kai shi hanyaɓ ɓanna
                    :Ga yaggiyar ruwa sunka kai shi
Jagora:        (Yau) Ga shi nan da ragga tinjim!
Yara:           Dole sai biɗan rumbace
Gindi:          Madogara na Malam Iro
                    :Uban Bawa mai gida Shinkafi

          A nan, ina ganin babu wani batu na cewa ‘yancin mawaƙi ne da sarrafa magana yadda ya so, a a ha kure ne, kuma kowa bai wuce ya yi shi ba.
          Irin gogaggen mawaƙi kamar Narambaɗa da ake ganin waƙarsa karatu ce, za a so a ji duk wata magana ya ɓantalo ya yi mata warki daidai da kwankwasonta. Ga wata magana da nake hangen tana da givin da ba a cike ba.
Jagora:        Ka ga kashi biyu na da wuyak kwasa
Yara:           Shi wane kashi huɗu yak kwasa (ɗ2)
Jagora:        Shi ka yi ma rowa, ya yi ma sharri
Yara:           Sannan ya yi ƙaunar matarka
Jagora:        Amma wani wajje na ƙwarai na
Yara:           Yana da tsaron maganar Sarki
                    :Kuma ba shi hwaɗa sai an ja shi
Gindi:          Ɗibgau bajinin Sarkin Yaƙi
                    :Gwarzon bahago ɗan Ibrahim

          Na rawaye waɗannan ɗiyan waƙa ban ga kashi huɗu ba, na dai ga: rowa, sharri, ƙaunar matarka, uku ke nan. A wajen kirkinsa an ce: tsaron maganar Sarki, ba ya faɗa sai an ja shi, wasu kashi biyu ke nan ko an haɗe su sai su koma biyar in an raba su da 3 da 2. Ba a cika givi ba ke nan, hikima ba ta fito ba.

Sakamakon Bincike
          Narambaɗa makaɗi ne da fasaharsa ke shiga zukatan mutane ta kowace fuska. Shi kaɗai ya kai matsayin ya burge na bayan fage, ya gigita Sarakuna, ya ba makaɗa ‘yan uwansa mamaki. Babu wani makaɗi da ya shahara a ƙasar Hausa face yana jin daɗin waƙoƙin Narambaɗa kuma su yi naso a cikin fasaharsa. Don haka binciken da na yi game da rayuwar Narambaɗa da shahararsa da gawurtarsa a fagen waƙa na gano cewa, mawaƙi a wannan zamani ba ya gawurta ya buwaya wajen fasaha face:
i.                   Yana da ilmi mai zurfi na addinin Musulunci ko ya kusanci malamai sosai da sosai.
ii.                 Ya kasance wani fitacce daga cikin manya-manyan sana’o’in gargajiya na Hausa ko ya gada ko ɗan haye ne amma ya ƙware.
iii.              Ya zamo mai kyakkyawar hulɗa da mutane wanda ya san mutane ciki da waje musamman abubuwan da suke ƙauna da akasinsu.
iv.               Ya zauni ƙauye sosai tare da sanin adabin gargajiya matuƙa.
v.                 Na dai fahimci Narambaɗa gajere ne ƙato sosai dottijo ga shekaru  da hali, amma yaransa matasa ne daga muryoyinsu. Narambaɗa ƙauye ya tashi amma ya fi ƙarfin ƙauye da wayo da hankali da karatu. Mai hangen nesa ne da sanin ya kamata idan aka lura da fasahar zambonsa cikin waƙoƙinsa. Tabbas! Mai kamun kai ne da kunya da mutunta mutuncin mutane. Na yarda da cewa kamar Kumbo kamar Kayanta.

Shawarwari
          Yau shekarar da muke ciki 2019 Makaɗa Narambaɗa ya shekara 56 da rasuwa. Babban abin da za a tuna har yanzu ba a yi wani aikin babban digirin MA, Mphil, ko PhD a kansa ba. Haka kuma har yanzu ba a samo hotonsa ba. Yaransa masu yi masa amshi da zuriyarsa da Sarakunan da ya yi wa waƙoƙi duk sun ƙare. Ina son in yi amfani da wannan damar in ce:
1.     Jami’ar Bayero, Kano tare da taimakon wannan Cibiya a sake tattaro waƙoƙin Narambaɗa a taskace su.
2.     A gaggauta buga takardun da aka tace na wannan taron.
3.     A samu wata kujera ta musamman da za a samo wa kuɗin bincike a yi mata suna NARAMBAƊA.
4.     Ina ba da shawarar Jami’ar Bayero, Kano da Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria da Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato da Jami’ar Tarayya ta Gusau ɗayansu ya ba makaɗa Narambaɗa digirin girmamawa (PhD) na Falsafa ko Adabin Baka.
5.     Ina roƙo kowace Jami’a da ake nazarin Hausa a ƙirƙiro darasi na musamman mai suna NARAMBAƊA.

Naɗewa
          A fagen zambo da arashi Buda Ɗantanoma[40] ya zarce tsara. A fagen kiɗin maza Ɗan’anace ne limami.[41] Idan ana zancen waƙoƙin tauri Kassu Zurmi ne basarake.[42] A waƙoƙin baje koli ga jama’a tsakanin Shata[43] da Ɗanƙwairo[44] ake jayayya. A zuga Sarki, a gigita fada da masarauta sai Aliyu Ɗandawo.[45] A kiɗin sata ba a yi kama da Gambo mijin Kulu ba.[46] A waƙoƙin ɓurɓushin zuciya da sha’awarta  Haruna Oji da Ɗanmatawalle sun san Ɗanmaraya malami ne.[47] A ƙasar Hausa, babu masarautar da ba ta da shahararren makaɗi na a ji makaɗi, a ga makaɗi, amma a bagiren kiɗin sarauta, a zuguguta sarki, a cicciɓa fada, a kumbura fadawanta, a yi wa masarautun fada da ‘ya’yan sarauta furjin kyanwa da an mabaci malamin kiɗi Narambaɗa karatu ya kai sin-wau-raa-takuri, babu sauran zance maƙoƙo ya fito a bakin zabiya.
Jagora:        A yini kiɗi a kwan kiɗi ba zancen banza
Yara:           A azo tubalin yabo a yi zambo daidai
Jagora:        Kalmomi suna fita harshe rarara
Yara:           ‘Yan kallo su yo kari ko ba su shiryo ba
Jagora:        Waƙa babu izgili shagwaɓa ko batsa
Yara:           Tamkar Busari da Malam Alfa Zazi
Jagora:        Ka ji waƙa kama da ilhama sun zan ɗai
Yara:           Sai ɗan Tubali Narambaɗa ba ƙarya ba

Gindi:          Gwarzon Shamakin mawaƙan rumbun Hausa
                    :Ibrahimu babu shakka ba a cimma ba

Jagora:        Wa Ɗandada wa Alu nan wane Gurso
Yara:           Wane Jankiɗi da Zamau mai ɗan Kotso
Jagora:        Ɗebe batun Nagaya ko Akwara yat taso
Yara:           Ko Shata da shi da Kurna yayan Ƙwairo
Jagora:        Ba su kama da Iro mai murya ratata

Gindi:          Gwarzon Shamakin mawaƙan rumbun Hausa
                   :Ibrahimu babu shakka ba a cimma ba.
Yara:           Makaɗan ganguma dama da kalangun mata
Jagora:        ‘Yan goge da tsirkiya molo sun ɓuya
Yara:           Iro da ya fito fage ba zancen ƙwarya
Jagora:        Masu zari gudu sukai tun bai kawo ba

Gindi:          Gwarzon Shamakin mawaƙan rumbun Hausa
                    :Ibrahimu babu shakka ba a cimma ba.
(Aliyu Bunza, Jumu’a 26/07/2019)
MANAZARTA
Aliyu, M. S. (1980) “Ahmadu Ɗanmatawalle” Kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero Kano.
Auta, A. L. (1986) “Gudunmuwar Waƙoƙin Makaɗan Baka Dangane da Adana Tarihi” Kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Bello, G. (1976) “Yabo, zuga da zambo a Waƙoƙin Sarauta” Harsunan Nijeriya 6:21-34.
Bello, S. (1979) “Narambaɗa da Waƙoƙinsa”, Kundin digirin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Bunza, A. M. (1998) “Naƙalin Diddigin Jirwayin Rayuwar Narambaɗa Cikin Falsafar Luguden Kalmomin Waƙoƙinsa”, Takarda Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A. M. (2009) Narambaɗa. Lagos: IBRASH Publications.
Bunza, A. M. (2014) In ba ka San Gari ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: ELKODS Printing House.
Burton, S. H. (1954) The Critisms of Poetry London: Longman.
Daba, H. A. (1973) “Ɗanmaraya mai Kuntugi da Waƙoƙinsa”, Kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Dalhatu, M. (1977) “Individual Talent in Hausa Poetic Tradition: A Study if Aƙilu Aliyu and His Art” PhD Thesis, London: SOAS, University of London.
Dawaki, A. M. (1974) “Alhaji Ɗanƙwairo Maradun: Rayuwarsa da Waƙoƙinsa” Kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗangambo, A. (1973) “Shata da Waƙoƙinsa” Kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗanjuma, M. S. (1982) “Rabe-Raben Waƙoƙin Hausa da Tasirinsu ga Rayuwa a Ƙasar Hausa”, Kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Furnis, G. (1996) Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. Ibadan: University Press.
Gusau, M. S. (1987) “Jerin Wasu Waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa Tubali”, Kano: Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: FISBAS Media.
Gusau, S. M. (2002) Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi. Kaduna: Baraka Publishers.
Haliru, A. (1982) “Aliyu Ɗandawo da Waƙoƙinsa”, Kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.
Ibrahim, M. S. (1983) Kowa Ya Sha Kiɗa. Zaria: Longman, Nigeria.
Magaji, A. (1980) “Nazari a kan Rayuwa da Waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi” Kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Mahe, A. (1984) “Alhaji Ɗan’anace da Waƙoƙinsa”, Kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.
Muhammed, I. (1977) “Waƙoƙin Maza na Ɗan’anace”, Kundin digirin BA Kano: Jami’ar Bayero.
Mungafi, B. G. (1985) “Waƙar Gagara Ƙarya Sadauki ta Marigayi Buda Ɗantanoma”, Kundin digirin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Mukhtar, I. (1984) “Nahawun Waƙa: Yanaye-yanayensa da Sigoginsa cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa”, Kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Rasmussen, D. (1975) Poetry and Truth. Paris: Monton.
Shinkafi, S. I. (1998) “Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali (1975-1960)” Kundin digirin BA Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sulaima, I. I. (1983) “Waƙoƙin Ɓarayi”, Kundin digirin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Udu, A. (1972) “Comparism of Narambaɗa and Aliyu Ɗandawo”, BA thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Umar, M. B. (1985) Ɗanmaraya Jos, Ibadan: University Press.
Zagga, U. (1980) “Jankiɗi da Waƙoƙinsa” Kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Zurmi, M. A. (1986) “Rayuwar Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa”, Kundin BA, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.


[1] Laƙabin farko da ake yi wa Ibrahim gabanin Narambaɗa shi ne, Iron Riba ko ko na Riba. “Riba” ne laƙabin mahaifiyarsa.
[2] Duk da kasancewar ba a yi babban aikin PhD a kan Narambaɗa ba amma an yi kundayen BA  da NCE da muƙalu da yawa. Marigayi Sani Y. Sada Katsina ya fara PhD a kansa har aikin ya yi nisa amma ba a kammala ba. Sa’idu Muhammadu Gusau ya wallafa waƙoƙin Narambaɗa da dama a diwaninsa na waƙoƙin bakan Hausa.
[3] Na samu tattaunawa da Alhaji Ɗanyadoto Shinkafi  da Malam Ibrahim Shinkafi yaron Mr. Wilson mahayi Ɗanhilinge da Hajo ‘yar   Narambaɗa da ɗiyar ‘ɗan amshinsa Mai’sa’a da ,Malam mai Salati abokin Narambaɗa.
[4] Masana sirrin waƙoƙin Narambaɗa da na sani su ne Alhaji Ɗanyadodo Shinkafi ya hardace mafi yawan waƙoƙin Narambaɗa. Bugu da ƙari, shi ne mai masaukin Narambaɗa duk lokacin da ya je Shinkafi. Malam Mai Salati ya fi kowa sanin sirrin waƙoƙin da fashin baƙinsu.
[5] Idan muka ce babu ranar da za mu fara saka namu tunani ke nan muna cikin mulkin mallaka a ilmance, wanda shi ne mafi haɗari dole mu fita cikin wannan ƙangi. Me ke cikin ra’o’in ilmi da babu cikin tunanin magabatanmu?
[6] Tunanin kowace al’umma yana nan cikin karuruwan maganganunta da zantukansu na hikima da waƙe-waƙensu. Da wace hujja za mu ilmantar da yaranmu da tunanin wasu?
[7] Masana sun tabbatar da cewa karin magana maganganun magabata ne da aka tsara bisa ga abubuwan da aka sani na dogon zamani kuma aka haƙiƙance kasancewarsu dahir. Ba a samu takin saƙa cikin saƙonsu da abubuwan da ke wakana na haƙiƙa ba. Masana sun ce babu wani abu da ke ƙarƙashin gizagizai da karin magana bai taɓo ba. Ina daga cikin masu ganin karin magana a matsayin ra’o’in magabata da suka cancanci a ɗora bincike a kansu.
[8] Laƙabin farko da ake yi wa Ibrahim gabanin Narambaɗa shi ne, Iron Riba ko ko na Riba. “Riba” ne laƙabin mahaifiyarsa.
[9] Sa’idu Muhammad Gusau ya faɗa a cikin littafinsa Makaɗa da Mawaƙan Hausa cewa, ga nahaifiyarsa ya gaji kotson kiɗi da ta gado ga mahaifinta. Mahaifinta bai samu ɗa namiji ba, don haka aka kwaso kaya zuwa ga jika.
[10] Akwai makaɗan Sarauta, Makaɗan Maza, Makaɗan Jama’a, Makaɗan Yaƙi, Makaɗan Sha’awa, Makaɗan Ban Dariya, Makaɗan Sata, Makaɗan  Gayya, ga su nan dai.
[11] Sarkin Gobir na Isa mai ci yanzu (2019) ya tabbatar mini da cewa waƙar Sarkin Kware: “Hawo da shirin yaƙi amali marinjayi” ta yaƙi ce: Waƙar Sarki Ɗankulodo, “Na Yari mai halin Tcagarana” ta yaƙi ce.
[12] Na samu wannan bayani daga Marigayi Alhaji Ɗanyadodo Shinkafi, 2008.
[13] Malam Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir a taron ƙaddamar da littafin Narambaɗa, 2008 a Arewa House Kaduna ya ce, ya taɓa riskar Alhaji Mamman Shata na sauraron Narambaɗa ya ce masa: “A a makaɗa har da ku kuna sauraron waƙar wani”? Shata ya ce “Ai wannan ba makaɗi ba ne malami ne”.
[14] A koyaushe kafafen yaɗa labarai na iya shaƙatawa da Narambaɗa amma ba mu taɓa jin an ce, a shaƙata da jawabin Sarki wane ba. Turawa sun ce, in ba ka son sunanka ya ɓata: “plant a tree, father a child, or author a book your name will neɓer be forgotten”.
[15] Sarki Aliyu a zamninsa ne Narambaɗa ya fara zuwa Kwatarkwashi domin har faɗa yake yi da cewa:
Jagora:           Wasu sun so ni ban taho ba nan
Jagora/Yara: Da an ka ce Alu as Sarkin ga na taho
Gindi:            Yai halin mazan jiya
                                :Ɗan Sanda mai kwatarkwashi
[16] Wannan waƙar an ce a ƙauyen Tubali aka yi ta yayin da Narambaɗa ya je bikon matarsa da ta yi yaji, Sarkin Gobir ya tura masa damman abinci babu adadi, wasu sun ce “dubu”. Ga bakin Alhaji Ɗanyadodo na karvi waƙar na rubuta.
[17] Karen Makaɗa kamar tobashin makaɗa ne, in sun yi kiɗi suka samo kuɗi, ya zo ya karɓe.
[18] Wannan togiyar ita ce waskiya domin makaɗan da aka toge su ne Zamfara, in babu su, babu kiɗi Zamfara.
[19] A zamaninsu Narambaɗa ana ƙyarga gari ashirin (20) ba a samu almajirin da ya kai ga Risala ba a karatun sani. Ashe ko a zaure, Narambaɗa ya kai malam.
[20] Wanda duk ya ratsi Ishiriniyya a wannan lokaci ya kai duk inda malami ke kai wa a ƙasar Hausa. Karatun Ishiriniyya ya haifar da mawaƙa da yawa a ƙasar Hausa.
[21] Kowace waƙa mawaƙi ya ƙaga za a samu nason rayuwarsa kaca-kaca a ciki sai ga wanda bai san shi ba.
[22] A cikin waƙar “Koma Shirin Daga….” ya ce:
Jagora:   Maganar nan da wane yai mini
Yara:      Sai na hwaɗe ta amma sai jama’a ta taru
Gindi:    Koma shirin Daga
                :Gwarzon Bahago ɗan Iro
Jagjora:  In ƙarya gare shi ta ƙara    
                :Ya kai  ga mayanki ƙauna
               
A nan an fito da turke maƙaryaci ƙarara.
[23] ‘Yaɗɗamna ita ce karuwar farko a garin Isa.
[24] “Ba mai kausai” mai kafan kai ke nan.
[25] An ce, an yi daga da Narambaɗa sosai kafin ya yarda gidan Rediyo su ɗauki waƙoƙinsa. Dole sai da aka je da mota har Isa aka ɗauki muryoyinsu. An ce, da aka ɗauki waƙarsa, aka sa ya ji, nan take jikinsa ya kwashi mazari kamar ya ruga a guje don bai taɓa sanin ana haka nan ba. Direban da ya kai su wajen Narambaɗa sai da ya  roƙi gafara ga Narambaɗa don ya ga tashin hankali ainun. Sannu-sannu har ya saba.
[26] Waƙoƙin Sarauta su suka sa aka ji shi aka ji shahararsa.
[27] Ya faɗa da kansa cewa:
Jagora:   Ga makandamiya za ni yi
                :Cikin manyan waƙoƙi
[28] An ce har ya mutu bai gama ta ba. Hira da Alhaji Ɗanyadodo Shinkafi.
[29] Ita kaɗai ce waƙar da Narambaɗa ya yi ta nan take.
[30] A tsarin ‘yan amshinsa waɗanda suka fi ƙwarewa da su aka fita yawon waƙa wajen ƙasar Isa da Zamfara.  Waɗanda ba su ba, su ake bari gida ana gagarawa har murya ta bi ragwai.
[31] A luguden amshin faɗi-in-faɗi da duk makaɗa ya aje za su yi kwakwahe irin yadda ke gudana a bakandamiya.
[32] An ce turu ɗaya ke gare su, kuma Umaru Maisa’a ke kula da shi.
[33] Duƙui-duƙui ga alama mai ƙaramin jiki ne gajere.
[34] Cumui-cumui ga alama mai babban jiki da faɗi.
[35] Zangai wani masahayi ne da shaye-shaye suka haukata, shi ne na farko a garin Isa. Yaɗɗamna karuwa ce, Magatakarda kuwa, shi ne Magatakardar Sarkin Ɗankulodo  na Maraɗi, an ce ba su shiri da Sarkinsa don haka aka gayyato makaɗa Narambaɗa.  Ya ambace su kamar haka:
Jagora:   Zangai kai ni ka so
Yara:      Ba ni son maƙwabcin Zangai
                (Sardauna Kangaren Magajin Rwahi)
Jagora:   Magatakarda da Bunsuruna
Yara:      Dan a sayo shi na kai ma kura
                (Ciwon Cikin Maza Ɗankuloda)
[36] Waƙar da aka yi wa NPC da sunan Narambaɗa ba Narambaɗa ya yi ta ba Umaru Maisa’a ya yi ta.
[37] Wannan shi ya nuna Narambaɗa bai da kamar Sarkin Gobir. Da ya je fadar Ƙaura ya yi wa Sarkin Kiyawa Abubakar waƙa da ya ga ta ɗan soma zurewa ya ce:
Jagora:   Da sanin dattaku da girma
:Da tsaron aikin ga na zamani
                :In dai ba ka koma Isa ba
Yara:      Mai Ƙaura babu awa shi
[38] Sai a dubi ka-ce-na-cen a cikin Bunza, A. M. Narambaɗa IBRASH, (2009: 30-31).
[39] Na samu wannan baitin/ɗan waƙa ga bakin Marigayi Alhaji Ɗanyadodo  Shinkafi. Ba ya cikin ɗan waƙar da ake rera wa a rediyo.
[40] Makaɗin Sarki Sama Argungu ne, shi ne ya yi wa Sarakunan Hausa zambo matuƙa.
[41] Don ƙarin bayani a kan Ɗan’anace a dubi, Mahe, A. 1985 “Ɗan’anace da Waƙoƙinsa”, Kundin digirin BA, Jami’ar Sakkwato.
[42] Don ƙarin bayani game da Kassu Zurmi a dubi, Magaji, A. (2017) “Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa”.
[43] Don ƙarin bayani a kan Aliyu Ɗandawo a dubi Haliru, H. (1982) Aliyu Ɗandawo da Waƙoƙinsa.
[44] Don ƙarin bayani a kan Shata a dubi Sheme, da wasu (2006) Shata Ikon Allah.
[45] Don ƙarin bayani a kan Gambo a dubi Bunza, A. M. In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo.
[46] Don ƙarin bayani a dubi…
[47] Ana samun cikakken bayanin Ahmadu Ɗanmatawalle cikin Aliyu, M. S. (1980) Ahmadu Ɗanmatawalle, Kundin BA, Jami’ar Bayero, Kano. Bayani kan Ɗanmaraya Jos, a dubi Daba, H. A. (1973) Ɗanmaraya Mai Kuntugi da Waƙoƙinsa, Kundin BA, Jami’ar Bayero, Kano.

No comments:

Post a Comment