Bisa
ga al’adar ɗaliban harshen,
ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe
tarkakken nazarin da ɗalibi zai
ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi
in yi bara da Hausa.[1]
Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[2] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai
harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu
da neman shahara a ciki. A ganina, gajeren tunanin ‘yan bayan fage ga duniyar
ilmi a koyaushe yana nuna musu, wace fa’ida ke cikin karatun harshenka na gado
da ka tashi ciki, ka balaga ciki, kuma kana rayuwa a ciki?[3]
Masu irin wannan fahintar…
Don Me Ake Karatun Hausa?
Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
Waya: 0803 431 6508
Takarda da aka
gabatar a bukukuwan makon Hausa na ɗaliban
Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato, ƙarƙashin kulawar Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Ranar Asabar 10-11-2012 a mazaunin
Jami’a na dindindin (ETF 3) a ƙarƙashin shugabancin Kwamishinan Yaɗa Labarai Malam Nasiru Ɗanladi Baƙo (Kogunan Sakkwato) da ƙarfe goma na safe.
Gabatarwa:
Bisa
ga al’adar ɗaliban harshen,
ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe
tarkakken nazarin da ɗalibi zai
ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi
in yi bara da Hausa.[4]
Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[5] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai
harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu
da neman shahara a ciki. A ganina, gajeren tunanin ‘yan bayan fage ga duniyar
ilmi a koyaushe yana nuna musu, wace fa’ida ke cikin karatun harshenka na gado
da ka tashi ciki, ka balaga ciki, kuma kana rayuwa a ciki?[6]
Masu irin wannan fahintar tunaninsu ya kasa hango musu cewa, da wane harshe
suka yi karatun da suke cin gajiyarsa?[7] Da
suka faɗo duniya, da
harshen iyayensu suka faɗo, ko
iyayensu ne suka koyar da su harshen har suka iya magana da shi? Domin daɗa
juna sani ga masu sha’arwar karatun harshensu, da masu ganin ɓeran
gida ba ya da mai, ya sa na yi tunanin wannan rubutu ga ɗaliban
karatun Hausa cikin sigar tambayar, don me ake karatun Hausa? Burina a nan shi
ne, bayanin wannan tambayar ya fito ƙarƙashin hasashen da Aƙilu Aliyu ya yi na cikin waƙarsa ta: “Hausa Mai Ban Haushi.” A
faɗarsa:[8]
Tsuntsu
kamata yai da shi ya yi kuka
Ya
irin na kakanninsa can mai nisa.
Harshen Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa:
A
wannan fasali ma, kamata ya yi in ce, mene ne harshe. Da gangan na zaɓi
wannan tsarin domin in ƙara
kusantar da Hausa a tunaninmu. A hangen masana, ba wani abu ne harshe ba, face
sadarwa da ke wakana tsakanin mutum da mutum ta fuskar magana da daidaitaccen
lafazi da aka saba da shi. Sadarwa ta fuskar magana ita ce, harshe, kuma ita ce
sunan da ake bai wa kowane harshe doron ƙasa.[9]
Dabarun sadarwa na ishara, da ƙaƙale, da rubutu, da dabarun al’ada,
ana kiransu hanyoyin sadarwa.[10]
Idan haka ta tabbata, harsunan duniya duka martabarsu ɗaya
ga masu amfani da su.
Harshen
Hausa na daga cikin manyan harsunan ‘yan zuriyar Chadi.[11]
tana daga cikin manyan harsunan da Afirka ke bugun gaba da su ga kowane misali
na martabar harshe.[12]
ta yi wa sauran harsuna babakere a Afirka ta Yamma.[13]
Ya yi wa sauran takwarorinsa fintikau cikin gida Nijeriya.[14]
Ya dakashe wa harsunan Turai kaifi cikin ƙasashen da suka yi kaka-gida (watau
Turanci da Faransanci).[15]
Ya hana wa harsunan mulkin mallaka salwantar da nahawunsa.[16]
Tasirin da addinin Musulunci bai sa Larabci ya durmuyar da kalmominsa na asali
ba.[17]
Juyin-juya-hali na masu jihadin ƙarni na goma sha tara, bai firgita
martabarsa ba ga masu shi, da masu koyonsa.[18]
Ya tilasta wa harsuna maƙwabtansa
da waɗanda suka riske shi aro cikinsa
saboda wadatattun kalmominsa da yalwatacciyar al’adarsa.[19]
Ya yi aro irin na ci gaba da wasu harsunan da zumuntar zama ya haɗa
su, ba tare da salwantar da kalmominsa na asali ba.[20] A
duniyar Afirka, shi ne harshen da ya fi kowane bazuwa, da yaɗuwa,
da karɓuwa, da sarƙuwa cikin harsuna, ba tare da zama
harshen ƙasa
a hukumance ba.[21]
Kaɗan daga cikin martabobin harshe
Hausa ke nan wanda ya sa masananmu ke cewa, mai maɗi
ke talla, mai zuma ido yake sa wa. Wannan zance nasu ya hau ƙololuwar tunanin makaɗa
Narambaɗa a faɗarsa:
Jagora: Maɗi
bai kai ga zuma ba
Yara: Kowal lasa shi ka hwaɗi
:Kwandon
wake bai kai ga
:Damen
gero ba
Jagora: Ɗan akuya ko ya yi ƙahoni
Yara: Ya san bai yi kamar rago ba
Jagora: Duw wada ɗan
sarki yaƙ
ƙasura
Yara: Kak ka raba shi da bawan sarki
Gindi: Gorarman Tudu jikan Sanda
:Maza su ji tsoron ɗan
mai Hausa
A sauƙin fahimta da koyo, Hausa ita ce
zuma, sauran harsunan Afirka maɗi ne.[22]
ta fuskar martaba da ɗaukaka,
Hausa damen gero ce takwarorinta na a Kwandon wake.[23] A
wajen yaɗuwa, da bunƙasa, a nahiyar duniyar zamaninta,
Hausa karon rago ce, mai manyan ƙahoni sauran harsunan ƙarninta bunsurai ne ɗan
ƙahonsu na
ɗara ne, bai isa karo da manyan
harsunan Turai ya kai labari ba.[24]
Mai musun wannan ya tambayi harshen
Yarbanci da Ibo da Wolof da Fulantanci
da Kanuri da Asante da Wangara da Kisuwahili zai tabbata, Hausa ce sarauniya,
sauran harsuna ‘yan galadimomi ne ba su da bambanci da bawan sarki da za a
kira, ya rugo a guje.[25] Waɗannan
hasashe-hasashenmu, ana iya kallonsu ta fuskar mamayar da Hausa ta yi wa
kafafen yaɗa labarai na
duniyar zamaninmu.[26]
Mujallun ilman Turawa, da fadakarwa, da jaridu, na duniyar ƙarni na ashirin da ɗaya
za su tabbatar da haka.[27]
Ban
so in raba bayanin Hausa da Hausawa ba a wannan ɗan
rubutun, amma bayani ya tilasta haka. Da Hausa da Hausawa abu ɗaya
ne, kamar mutum da sunansa. In aka kira sunansa shi ne, in shi ya faɗi
sunansa linzaminsa ne. Hausawa su ne tarsashin jama’ar da ke amfani da harshen
Hausa a matsayin harshen uwa, ko in ce harshen haihuwa.[28] Haka
kuma, ya kasance ga iyayensu suka gaji harshen, su kuwa iyayensu sun gada daga
iyayensu.[29]
A al’adar Bahaushe, wanda ya gaji abu iyaye da kakanni ya taki hujjar da zai faɗa
a saurare shi.[30]
Hausawa a doron ƙasa
ba ƙyalle ba
ne, idan aka nazarci nahiyoyin da suka mamaye. A gida Nijeriya, sun kafa
daulolin da babu wata al’ummar da ke da irin su yawa, da ƙarfin mulki, da tsarin shugabanci,
da fice a tarihi.[31] A
cikin Afirka ta Yamma, sun yi ale-ale a Ghana da Nijar da Mali da Togo da Benin
da Abijan da Saliyo da Borkina da Libiya da Morocco da Tunis da Masar da Sudan
da Saudi Arabiya. Cikin al’ummar da ke zaune a duniyar baƙar fata, babu wanda ya kai Bahaushe
barbazuwa a duniyar zamaninsa.[32]
A
ma’aunin ɗalibta da na
karatu, matsayin harshen Hausa da Hausawa a duniyar baƙar fata ya isa ya zama hujja da ɗalibai,
da malamai, da manzarta, da masu bincike, na kowane fannin ilmi su tunkare shi.
Burin kowane harshe shi ne, ya samu masu magana da shi.[33]
Ya mamaye nahiyar da ya tsira.[34]
Ya samu karɓuwa ga maƙwabtansa na ciki da na waje.[35]
Masu magana da shi, su fantsama a uwa duniyar zamaninsu, da harshen a
bakunansu.[36]
Idan harshe ya kai ga wannan muradi, duk wata musibar masassara, da za ta sa ya
suma, ko ya mutu, ya tsallake ta. Don haka, ko musibar yaƙi da annoba tana raga masa, bale
wani baƙon
haure da zai zo da tsakiyar rana da ƙarfin soja.[37]
Hausa ita ta yi wa kanta gwagwarmaya wanda ke karatunta gajiyarta ne zai ci, ba
neman a riƙa
ta miƙe tsaye
take ba.[38]
Tsaye aka taras da ita kamar ‘alif baƙi’ kuma tana saman harsunan zamaninta irin
yadda ‘alif ja’ ke saman kowane harafin da aka rubuta.[39] A
gai da Alhaji Muhammadu Gambo Fagada[40]
da ke cewa:
Jagora: Dole nakiya ta yi zaƙi Sanda Ummaru
:Don
da zuma aka fara yin ta
Martabar Karatun Hausa:
Karkarar
da muka fito mun ga matsayin Hausa na zama tsayayyen harshe, wadatacce ga masu
magana da shi, yalwatacce ga kalmomi, kuma sananne a duniyar zamaninsa. Ga
alama, ɗalibin nazarin
ilimin Harsuna zai ce: “Da an ce, martabar karatun harshe abin ya fi amo.” A
ganina, an gama kyau tun ranar haihuwa. Da Hausa muke rubutu a kan Hausa muke
magana. Da Hausawa da masu sha’awar karatu ko nazarin Hausa muke tattaunawa.
Don haka, gara a yi, ga wuta, ga masara, filin wuri dabon Ɗankama. Harsuna duniya ba ta fuskar
tsawonsu, ko faɗinsu, ko
nauyinsu ko kwalliyarsu, ko wayewarsu, ake kallo a kasancewarsu harshe ba.
Haka! Akan kalli wasu daga cikin waɗannan
a wasu ɓangarorin ilimin
harsuna, amma fa’idojin harshe ga ɗan
Adam, wanda zai sa a yi ɗalibtar
karatunsa suna da yawan gaske.
Irin
tazarar da ke tsakani mai karatun harshe da ɗan
kallo tankar tazarar da ke tsakanin mutumin da ke ji da kurma ne. ba a fi kurma
sutura, da zati, da taƙama,
da cika ido ba. Da an fahinci ba ya ji ya zan rabin mutum. Da wanda ba ya jin
abin da ake faɗa, da wanda ke
ji ya kasa fahinta, maƙawabtan
juna ne. idan aka kwatanta su da mai gani da makaho ba a yi kure ba. Domin da
wanda ba ya gani, da mai gani garaye-garaye,[41]
da wanda ya kasa ahuma da fahintar abubuwa da yake ganin tazararsu ba ta da
yawa. Idan aka kwatanta su, da mai hankali da mahaukaci ana iya yin muwafaƙa. Mai hankalin da ya kasa aiki
irin na masu hankali, lokacin da ake buƙatar a auna hankalinsa, a cikin wannan
rutsin, sunansu ɗaya da
mahaukaci. Dangantakar da ke tsakanin masani harshen da ake magana da shi, da
wanda bai san harshen ba, irin ta malami ce da jahili tuƙaƙƙe (watau murakkabi).[42]
Komai wayonsa, da wayewarsa, da ƙwarewarsa, ga abin da yake ganin ya ƙware a kai, idan ana magana da
harshen da bai sani ba, kamar ana ba gawa labarin sanadiyyar mutuwarta ne a
al’adance. Da me labarin ya amfane ta? Wane amfani daga cikin amfanonin maganan
mai labarin ya amfana da shi? Kwatanci masani harshe da wanda ya jahilci
harshe, irin na baƙo
ne da ɗan gari. Yaya za
ka kwanta wanda aka haifa cikin gari, ya manyanta ciki, ya san mutanen garin,
suka san shi, da wanda bai taɓa sanin
gari ba, ya wayi gari a ciki. Bai san kowa ba, kowa bai san shi ba. Bai taɓa
ganin kowa ba a garin kowa bai taɓa
ganinsa ba? Yadda yake zarar ido irin na sabon makaho. Yake waiwaye-waiwaye
irin na baƙon
ɓarawao. Haka nan wanda bai san
harshe yake ba idan ana hulɗa da
harshen a gabansa. Dubi irin damuwa, da tsarguwa, da rashin natsuwar da mace za
ta ji a babban birnin da ita kaɗai ce
mace, ko namiji zai ji a alƙaryar
da shi kaɗai ne namiji.
Kwatankwacin haka ne mutum zai samu idan ya baƙunci gari/ birnin da ba a jin harshensu,
shi kuwa, kowa ba ya jin nasa.
Tabbas!
Kintsuwar mutum, da zamansa kamili, ba ta cika, sai yana iya magana a fahince
shi, ko ana magana ya fahinta. Waɗannan
abubuwa biyu su ne tubalan da suka gina kowane harshe a duniya. Dole mai
hankali ya sake tunanin cewa, wai idan babu harshen sadarwa a duniya yaya hulɗar
rayuwa za ta kasance wa ‘yan Adam? Bayanin da za a ba wanda ya yi wannan
tambayar shi ne, ya dubi rayuwar tsuntsaye, da ƙwari, da dabbobin garinsu. Mutanen garinsu
ba su fi su yawa ba, amma wane tasiri suke da shi a garin? A koyaushe, harshe
na da alaƙa
ta ƙuƙut da hankali, da mutunci, da
martabar ɗan Adam. Ashe,
mamakin nazari ko karatun abin da mutum ba ya kasancewa cikakken mutum sai yana
da shi, wani duhu ne na ƙoli
daga cikin duffan rashin sani. Idan wani ilimi na zama wajibi da kowane ɗan
Adam, da wuya bai kasance ilmin sanin harshensa ba. Bisa ga haka, ba sai na gaya
wa ɗaliban Hausa su yi karatun Hausa
ba. Ga fili ga doki ga wurin suka mai daɗi.
Ko ba a faɗi ba ido ya san
abin da ke cika masa tumbi.
Hasken Harshen Hausa Ga Ɗalibansa:
Babu
shakka, kowane harshe haske ne ga masu magana da shi, da ɗalibansa,
da manazartansa, da malamansa. Ɗaliban
harshe na kowane zamani, na kowace ƙasa, darajarsu ɗaya,
tsawonsu kwatankwacin mashaci yake a ma’aunin nazari.[43]
Harshen Hausa wani haske ne ga ɗaliban da
ke nazarinsa a kan kowace fuska suka samu rayuwarsu ciki. Ga ɗan
abin da na hango na irin matsayin hasken harshe ga ɗaliban
nazarinta.
Ɗaliban Hausa, ku sani, Hausa kamar
farfajiyar duniya ce da ke shimfiɗe,
tattare da mutane, da ƙwari,
da dabbobi, da itace, da ƙoramu,
da tsaunuka, da rafuka, da tuddai. A cikin wannan yanayin harshe kamar rana
yake ko wata. karin harshe zai zamo taurari.[44]
Idan babu rana da wata sararin duniya ba ya zaunuwa a wala a ciki. To, ka ƙaddara faɗin
duniyar nan, yaya zai kasance, idan an cika shi da bil Adamu, kuma babu wani
harshe da ake sadarwa da shi? Ko da harshe ɗaya
kacal aka samu duniya, hasken rana ya bayyana ga mazaunanta. Yayin da ranar za
ta faɗi, wato idan harshe ya cika ya
batse, za a ga wata da taurari sun bayyana cikin dare, wannan kwatankwaci
kururuwan harshen ne. wata na nan a matsayinsa na harshe mai wakiltar rana,
domin idan harshe ya cika ya batse, ci gaban da ke aukuwa a duniyarsa na ƙara yawaita masa baƙin kalmomi sababbi, da na aro,
cikin haka, a samu tasirin wasu tsofaffin kalmomi, sai haskensa ya ɗan
dushe, ya tashi daga duniyar rana zuwa darajar wata. Taurarin da ke gewaye da
shi kuwa karuruwan haushe ne, da ke tsira bisa ga saɓanin
yanayi, da nahiya, da ci gaba, da walwala, da siyasa, da addini, da al’adr da
harshe ke haifarwa. Harshe wani dogon haske ne mai game ko’ina da ko’ina irin
na rana ga masu nazarinsa. Waɗanda ke
magana da shi idan ba su karance shi ba, ɗan
hasken da suke da shi nasa bai fice na tazarar da ke tsakanin faɗuwar
rana zuwa shigan duhu na haƙiƙa ba.
Hasken
harshen Hausa, da amfanoninsa ga ɗalibansa,
irin na maji yunwa ne da abinci. Ɗan kallo ga nazarin harshe, wanda bai ɗalibce
shi ba, mayunwata ne ga amfanonin da ke cikinsa. Misalin wanda ya ratsi harshe,
harshe bai ratse shi ba, kamar maji yunwa ne da ƙishirwa matsananciya, a yi masa wanka da
fura da ruwa masu sanyi sosai tsarkakakku, amma a hana shi lasa ko tas daga
ciki. Wankan da aka yi masa zai wadatar da shi daga matsalar yunwar da yake
ciki? Ga aikin hankali, takaici ma zai ƙara masa. Irin wannan takaici ne ke sa
wanda bai karanci harshen Hausa ba, ke mamakin masu sadaukar da kansu suna
karatun Hausa. Takaicinsa, yana Bahaushe uwa uba, amma a ce, wai bai san
harshensa ba, sai ya je ya ɗalibce
shi. Ya manta da cewa, kai ke da gonanka, amma idan ka yi shuka, sai ka ƙi yin noma da sa taki lallai sai ka
sha takaici ranar girbi. Sau nawa mutum zai manta da kayansa, waɗanda
ya ajiye da hannunsa, a ɗakinsa,
sai matarsa, ko yaronsa, ya nuna masa wurin da suke? To! Haka koyon harshenka
na farko yake a makaranta. Dalilinmu ke nan, na koyon harshenmu, domin ba a san
tabkin da ke makara da ruwa ba. Ai kamata ya yi a ce, mata ta san mijinta ko
daji ta gan shi komai taron maza tana bambanta shi.
A
ganinmu ɗaliban harshen
Hausa, haɗarin da ke cikin
rashin koyon harshenmu a matakin nazari, haka yake kamar a ce, ga ƙasa mai ɗimbin
arziki, da tsaro, amma ba ta da tsarin mulki da shugabanci. Me za ka ce wa,
sabuwar mota da aka shirya gagarumin biki da ita ba ta da kowane irin mai da za
ta sha? Yaya rayuwarka za ta ji, idan kana cikin matsananci hali na neman
agajin gaggawa, ga ka da sabuwar waya, da kuɗi
a hannu, amma babu kowane irin layi cikin wayarka, yaya za ka ji wannan
matsalar? Gabanin ka ba ni bayanin irin ƙuncin da kake ciki, fiye da wannan ƙuncin wanda bai zurfafa cikin
harshensa nag ado ba yake ciki. Dalilin ɗaliban
harshe ke nan, na cewa, kowane ilmi gare ka a duniya, ka yi ƙoƙari ka fahinci sirrin harshenka, in kana
son ka ji daɗin duniyar
zamaninka. Ma’ilmanci da bai iya sarrafa ilminsa cikin harshensa nag ado, ya
shiga cikin ɓatan ɓakatantan
domin ya zama buzuzu ga ƙarfi
babu dabara, in ji malamin kiɗa Narambaɗa:
Jagora: Banza sha’anin maras kare
Yara: sai kuwwa, sai ko wanda yak kashe
:Ya ce mishi, “Amshi rataya.”[45]
Gindi: Ya ci maza, yak wan shina shire
:Gamda’aren Sarkin Tudu Alu
Ƙumshiyar
Karatun Hausa:
Manhajar
kowane harshe daji ne ba ka da gambu. Idan za a koyi harshe, duk wata albarkar
da ke ciki, sai an yi mata fasalin kanta. A nazarin Hausa, muna da: Al’ada da
Adabi da Harshe. Waɗannan
duwatsun murhu uku, su suka sa karatun Hausa ya zama wani dodo a cikin karatun
harsunan duniya. Alal misali, a Turanci akwai Harshe da Adabi, amma babu
‘Al’ada”. A Jamusanci akwai Harshe da Adabi amma babu “Al’ada”. A wajen masu
nazarin Hausa, duk wata taska ta rayuwar Bahaushe sai an ƙwalailaice ta, domin ɗalibi
ya zamo wayayye ga sanin al’ummar da ya karanta ta kowace fuska.
Muradin
Nahawun Hausa, ba iya magana, da rubuta ta, da karanta ta ne babban muradi ba.
Muradi shi ne, a iya magana. A iya fahimtar magana. A iya fassarar magana. A
iya danganta magana da mai yin ta, da wanda/ waɗana
ake yi wa ita, da halayyar da ake yin ta, da lokacinta, da gurbinta. Buƙatarmu a adabui ita ce, ta kasance
taskar adana hikimar magabata,[46]
ta fuskar adabin baka da rubutacce, domi a waigi jiya, a tsura way au ido, a ƙyallaro gobe. A cikin al’ada ne za
mu ga yadda harshe da adabi suka narke cikin sosai, da yadda za a warware su a
yau, su zama rumbun arziki ga na gobe. Wanda ya rasa al’ada bai san wurin da ya
fito ba, ya manta da wurin da ya dosa.
Idan
haka ta samu, ɗalibin da ya
karanci Hausa ba Hausawa kawai zai amfana da karatunsa ba domin ba rayuwar
Hasawa kawai ya karanta ba. Ya san Hausa da Hausawa ciki da waje. Ya san maƙwabtan Hausawa. Ya san abokan hulɗar
Bahaushe. Ya san harshen Hausa, da harsunan da Hausawa ke da zumunta da su, da
yadda zumuntar ta kasance. Ya san rayuwar Hausawa, da al’adusu, da al’adun sa
suke so, da waɗanda ba sa so.
Ya san miyagun al’adu da al’adu na gari. Rashin samun haka a yau ya sa
ma’aikatanmu nay au suka zama, ɗaka gumi,
waje ɗari, gado kazunzumi, zani ga ƙyaya. Bayan ba sani ba, kuma ba a
san ba a sani ba, an sunsune sai da sanin ba a sani ba.
Da Me Hausa Za Ta Ciyar Da Mu Gaba?
Amfanonin
karatun harshe ga mai karatunsa bayyane suke ba sai an lalaba ba. Masu tunanin
ganin, wai harshenmu na gado bai da rawar da zai taka a cikin wayayyen zamani
irin namu, sun yi wa Hausa sanin damisar Bunu.[47]
Duk wani ci gaba da ɗan Adam
zai yi tinƙahi
da shi, na kowane zamani, da harshe aka assasa shi. Harshen ne ginshiƙin duk wani ci gaba da kowace ƙasa ke bugun gaba da shi. Babu ƙasar da ta ci gaba, ba ta da
harshen ƙasa!
Babu ƙasar da
ta bunƙasa,
ba ta amfani da harshenta ba wajen ilmantar da ‘yan ƙasarta. Idan haka yake, harshen ne
ginshiƙin
da ya tangale kowace dabara ta ciyar da ƙasa gaba. Ga abin da Narambaɗa
ke cewa ginshiƙi:
Jagora: Shigifa in babu azara
:Kuma
babu ginshiƙi
:Ai
ka san sai ta tuɗe
Yara: Me aƙ ƙarhin shigifab ba su ba.
Gindi: Abdu ƙanen mai daga
:Kan
da mu san kowa
:Kai
mun ka sani Sardauna
Da
mai halitta ya halicci halittarSa ta farko magana ya fara koyar da ita. Sai da
baki ya biyu da magana aka fara zancen sanin yadda za a yi bautar wanda ya yi
halitta. Harshe shi ne ci gaba da ya fi kowane ci gaba fice daga cikin ci gaban
ɗan Adam. Wanda ya karanci harshe
shi ne sarkin sarakuna cikin masu ilmi da basira’[48]
domin da harshe ne za a yi hulɗa ta
zamantakewa. Da harshe za a yi addini kowane irin addini ne a doron ƙasa. Da harshe ne za a yi tunanin
matsugunnin da ya fi cancanta a zauna a rayu. Da harshe za a tsara dubarun
zaman lafiya, da dokokin ƙasa,
da tsarin mulki da hukumar da za ta tsare martabar dokoki, ta hukunta waɗanda
suka saɓa mata. Ai
wannan ita ce hujjar cewa, mutum ba zai zama alƙali ba, a kowace ƙasa ta duniya, face yana sa ƙosasshen ilmin harshen da ake
zartar da shari’a da shi.[49]
Haka kuma, ba za a yi wa mutum hukunci ba, face yana fahintar harshen da ake yi
masa hukunci da shi dalla-dalla.[50] A
taƙaice,
karatun Hausa zai agaza wa wannan ƙasa tamu ga dukkaninb abin da ya shafi;
tsaro, da yaƙi,
da sulhu, da kowane tsari na gudanar da dokokin ƙasa.
Hudowar
demokraɗiyya wani
tsintuwar guru cikin suɗi ne ga
masu karatun Hausa. Nijeira ta Arewa, babu siyasar da za ta yi, ba da harshen
Hausa ba, kuma duk siyasar da ta juya wa Hausa baya tana rigayan rana faɗuwa.
Tattalin arzikin kowace ƙasa
da harshe aka gano shi, da shi ake haƙo shi, in na haƙowa ne, da harshe ake nemo shi, a
taskace shi, a amfana da shi. Yaƙe-yaƙe, da ta da zaune tsaye, da ke ci wa duniyar
ƙarni na
ashirin da ɗaya tuwo a ƙwarya, bay au aka fara su ba,
hasali ma, an yi has ashen za su faru, kuma ga su, sun wakana. Bakin duk da ya
yi has ashen faruwarsu, shi ya tanadi yadda za a magance su. Ashe ke nan, idan
aka rasa harshe, zaman lafiya ya ƙare ga al’umma. Gidajen Rediyo da
Talabijin da Jaridu na duniya da ƙasa sun isa abin ba da misali.[51]
Masana
tarihi, da walwala, da harshe, sun tabbatar da gudummuwar harshe ga bunƙasar kimiyyar da duniyar mutane ta
samu. Mafi yawan ƙasashen
da suka buwaya da kimiyya, da harshensu suke amfani. Idan sun ga wani abin buƙata cikin wani harshe, sai su
fassaro shi cikin harshensu na gado, su sa zaren tunaninsu na gado. Ai musulmi
suka fara ƙirƙiro har jirgin sama, da ilimin
lisafi, wasu ‘yan mu-muka-iya suka fassara fasahar cikin harshensi aka bar
musulunci da hamma kawai. Ƙasashen
Hindu da Bulgaria da Masar da Saudiyya da Spain da Rasha duk ta tafarkin amfani
da harshensu ne suka samu fice da ƙwarewa ga fannonin kimiyyar yau da ake
auna ci gaban kowace ƙasa
das u.[52]
Naɗewa:
Hausawa
na cewa, mugun gatarinka, ya fi sari ka ba ni. Ni a fahintata, ƙwai a baka ya fi kaza a akurki. Ƙoƙarin kai na hannu gida, shi ne dabara, da
wayo, gabanin da dawo a kama na dawa. Ala tilas, mu yarda da cewa, da dahuwam
da bandam da suya duk gashi ya fi su sanin asirin wuta. Ba kushe abin da ba ka
sani ba, za ka yi, kai dai, in ba san gari ba saurari daka. Duk da haka, a
kiyaye, da jin daka, da kukan zakara, duk shiga gari ya fi su. Tuni muna sane
da cewa, in ka ji namu da mai shi. Don haka, a kiyaye, mai hankali ba ya nunin
gudansu da hannun hagu. Mu dai taka rawa gwargwadon takenmu, domin, in da wani
ya yi rawa aka ba shi kuɗi, in
wani ya yi duka zai sha. In bayan rashin sani ya fi dare duhu, wa zai daka wa
cikinsa wuƙa
ya yi kirari? Mu dai muna tare da makaɗa
Narambaɗa:
Jagora: Da a ce ku gai da ɗan
mai taru
:Gara a ce mai taru
Yara: Kwak kashe kihinai
:Sai shi nasa goranai
Gindi: Na riƙa ka da girma Audu ƙanen mai daga
:Kan
da mu san kowa
:Kai
mun ka sani Sardauna.
MANAZARTA
Adamu, M. (1975) Hausa
Factor in West African History. Zaria: ABU Press.
Aliyu, A. Fasaha Aƙiliya. NNPC, Zaria.
Bunza, A. M. (2008) Narambaɗa. Wallafar Lagos:
IBRASH, Publishers.
Bunza, A. M. 2012: “In ba ka San Gari ba Saurari Daka:
Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo”, kammalallen bincike ba a wallafa ba.
Bangbose, A. (1977) Language
and Nation: The Language Ƙuestion in Sub-Saharan Africa. Edingburgh, Uniɓersity Press.
Crystal, D. (1970) The
First Dictionary of Lingusitics and Phonetics. London.
Fagge, U. U. (n.d.) Ire-iren
Karin Harshen Hausa na Rukuni. Benchmark Publishers, Ltd.
Jespersen, O. (1965) The
Philosophy of Grammar. New York: The Norton Library www.norton&comapany.com
Mai’aduwa, Y. A. (1982) “Harshen Hasusa a Jarida, kundin
digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Maiyama, U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar Hausawa: Nazarin
Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Mamman, M. (2012) Essays
in Hausa Grammar and Linguisitics. Zaria: ABU Press.
Musa, M. R. (1988) “Hatsin Bara: Kafofin Watsa Labarai na
Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Omar, S. (2012) “Hijirar Modibbo Kilo daga Sakkwato zuwa
Makka”, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Salilhi, Z. D. (1986) “Jaridun Hausa: Haɓakarsu da
Gudummuwarsu kan Harshe da Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar
Bayero.
Sakkwato, A. B. (2011) Ginin Jimlar Hausa: Jagora ga Mai
Nazarin Harshe.
Sani, M. A. Z. (2011) Gamayyar
Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa. Zaria: ABU Press.
Tayson, L. (2006) Critical
Theory Today: A User Friendly Guide. London: Routledge Taylor and Francis Group.
Trudgill, P. (1974) Sociolinguistics:
An Introduction. Penguine Books.
Usman, B. (2008) “Hikimar Magabata: Rayuwar Alhaji Usmaru
Nasarawa Wazirin Gwandu”, kundin digirin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yakasai, S. A. (2012) Jagoran
Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Serɓices.
‘Yar-adua, T. M. (2008) The
Syntactic and Semantic Aspect of Hausa Ƙuantifiers. Kano: Clear
Impressions, Ltd.
[1] Bangbose, A.
(1977) Language and Nation: The Language Ƙuestion
in Sub-Saharan Africa. Edingburgh, Uniɓersity
Press.
[2] Na san akwai taƙaddama tsakanin manazarta Harshe da Adabi kan cewa,
Hausa harshe ne ko ƙabila? A
wajen Hausawa, Kalmar Hausa na da ma’noni da yawa. Tana da ma’anar ‘azanci’ ga
wanda ya ƙware ga
Magana. Tana ɗaukar ma’anar ‘dabara’ wajen sarrafa abu. Tana ɗaukar ma’anar ‘habaici’ wajen gugar zana ga su nan
dai.
[3] To, idan haka ne, wace fa’ida ke cikin karatun
harshen da ba naka ba, ba na uwarka ba, ba na ubanka ba? Da wace hujja za ka
karanto harshen da ko da ka zo gidanku/ garinku ba ka da abokin labari da shi?
Waɗannan abubuwa suna nuna raunin tunanin masu rena harshensu
na gado.
[4] Bangbose, A.
(1977) Language and Nation: The Language Ƙuestion
in Sub-Saharan Africa. Edingburgh, Uniɓersity
Press.
[5] Na san akwai taƙaddama tsakanin manazarta Harshe da Adabi kan cewa,
Hausa harshe ne ko ƙabila? A
wajen Hausawa, Kalmar Hausa na da ma’noni da yawa. Tana da ma’anar ‘azanci’ ga
wanda ya ƙware ga
Magana. Tana ɗaukar ma’anar ‘dabara’ wajen sarrafa abu. Tana ɗaukar ma’anar ‘habaici’ wajen gugar zana ga su nan
dai.
[6] To, idan haka ne, wace fa’ida ke cikin karatun
harshen da ba naka ba, ba na uwarka ba, ba na ubanka ba? Da wace hujja za ka
karanto harshen da ko da ka zo gidanku/ garinku ba ka da abokin labari da shi?
Waɗannan abubuwa suna nuna raunin tunanin masu rena harshensu
na gado.
[7] Duk wani harshen da ka yi karatu da shi, in ba naka
ne na gado ba, na wani ne, to shi ko da ya raina harshensu da wane za ka yi
karatu? Don haka babu ƙasƙantaccen harshe kowane harshe, harshe ne, kuma
amfaninsu da muradinsu ɗaya ne.
[9] Domin tantance ma’anar harshe a
dubi, Crystal, D. (1970) The First Dictionary of Lingusitics and
Phonetics. London. Haka kuma akwai ƙarin bayani a
cikin, Yakasai, S. A. (2012) Jagoran
Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Serɓices. Shafi na 2.
[10] Don ƙarin bayani a dubi, Musa, M. R. (1988) “Hatsin Bara: Kafofin Watsa Labarai na
Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
[12] Don haka ne a shekarar 1979 aka yi tunanin saka Hausa
ɗaya daga cikin harsunan da za a iya magana das u a
Majalisar Dokokin Duniya (United Nation)
[13] A faɗin farfajiyar
Afirka ta Yamma Hausa ita ce fitaccen harshen da babu ƙasar da babu masu magana da ita. Wurin da ta yi
babakere shi ne, ita kaɗai ce ta yi fice a kafofin yaɗa labarai na duniyar zamaninta. Kafofin yaɗa labarai na BBC da ƁOA da Jamus da dai sauransu.
[14] A gida Nijeriya muna da kimanin harsuna fiye da 400.
Abin sha’awa, babu harshen da ya samu karɓuwa
da hukuma kamar Hausa. ‘Yan bokon da ke da digirin BA da MA da PhD na Hausa sun
fi kowane ‘yan bokon da suke karatun sauran harsunan Nijeriya a duniya.
[15] Buƙatar harsunan Turai su ne, su taushe harsunan da ba su ba, su hana su
fice a ƙasashen da
suka mallaka. Turanci da Faransanci sun kasa su sake ƙafafunsu sosai a ƙasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da Mali da Borkina
saboda hurjin kyanwa da Hausa ta yi musu.
[16] Yadda Turanci ya ci zarafin nahawun Ibo da Yaruba,
bai ci zarafin nahawun Hausa haka ba. Wataƙila saboda Hausa ba gare shi kaɗai ta dogara ga are-aren kalmomin da ba ta da su ba.
Hausa ta yi aro a Faransanci da Larabci da sauran maƙwabta harsunan ciki da waje. Tasirin nahawunta da ta
gada kaka da kakanni Turanci bai ci nasarar ruguza shi ba.
[17] A zauruka kawai ake amfani da kalmomin fannu na
Larabci a cikin koyarwar da ake yi wa ɗalibai.
Are-aren kalmomin da Hausa ta yi ga Larabci ya fi yawa a fagen addinin
Musulunci.
[18] Mujaddadi Ɗanfodiyo da mataimakansa sun yi rubuce-rubucen waƙoƙi da litattafai da yawa cikin harshen Hausa. Wannan shi ya ƙara wa Hausa ɗaukaka
a idon masu sha’awar addinin Musulunci. Fitaccen aikin Hausa da aka yi cikin
ajami a ƙarni na
goma sha tara shi ne, Markabul Awwamu, na Muhammadu Tukur.
[19] Masana ilimin harsuna na ganin saboda yalwatar
kalmomi ya sa harshen Hausa ya fi kowane harshe na yankinsa sauƙin koyo da fahimta.
[20] Baƙin kalmomi da Bahaushe ya aro na maƙwabtan harsuna da ke gewaye da shi da na baƙin haure yawa gare su. Duk da haka, wannan ba ta cuta
wa harshen ba, saboda Bahaushe ba ya aro sai ya tabbatar da babu abin cikin
harshensa. Idan kuwa ya yi aro yana Hausantar da ita ta yadda ko mai ita na
asali ba ya iya gane kalmarsa ce aka aro.
[21] Kiswahili ke bugun gaban yawan mutane masu magana da
shi domin farfajiyarsu shi kaɗai ne harshen
da aka yi wa kaciya. To! Hausa duk da yawan da take da shi da karɓuwar da ta yi, babu ƙasar da aka keɓe
ta a matsayin harshen ƙasa. Da
Nijeriya ta yi haka da Afirka gaba ɗaya
ta koma Bahausa. Wai duk ƙoƙarin ga na Hausa, na Hausawa ne ba da hannun hukuma
ba.
[22] Zaƙin maɗi da zuma ba a kwatanta su da Hausa babu harshen da
zai gwada tsawo da ita a cikin ƙarnin da muke cike a yau.
[23] Ga al’ada, wake ya fi gero tsada, amma gero ya fi
wake daraja a ma’aunin Bahaushe.
[24] A tambayi Igbo a shekarar 1987 Jami’ar Nsukka ta
tilasta a riƙa magana
da harshen Igbo a Majalisar Ƙoli ta Jami’ar (Senate). Dalilinsu shi ne, sun fahinci in ba a yi hattara
ba, Turanci zai kashe harshen Igbo gaba ɗaya.
Da baya, Yarbawa suka fara yin irin wanna tunanin.
Jagora: Duk waɗa ɗan sarki yak
kai
:Ɗan sarki aka ce mai
:Don sarki ka kira nai
:Shi sheƙo da gudu
Yara: Ai mai jirgi ka fito
:Mai gora sai wahalab banza
Gindi: Tura haushi ɗan Amadu
:Ɗan Sanda na Alƙali
[26] Hausa na da tasha a BBC da ƁOA da Jamus da Sin da Iran da Masar da Libya. Babu
wani harshe daga cikin harsunan Nijeriya da Afirka ta Yamma da ke da wani shiri
ko na sati ɗaya a shekara ne a ciki in ba Hausa ba. Ashe ko
Kiswahili da ta mamaye ƙasashe da
yawa ba ta samu wannan haske ba.
[27] Don ƙarin bayani a dubi, Salilhi, Z. D. (1986) “Jaridun
Hausa: Haɓakarsu da Gudummuwarsu kan Harshe da Al’adun Hausawa”,
kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero., da Mai’aduwa, Y. A. (1982) “Harshen
Hasusa a Jarida, kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
[28] Masana na amfani da harshen ‘uwa’ wasu su ce ‘harshen
farko’ ko ‘harshen haihuwa’ wajen tabbatar da harshen asali na mutum. Ina da
fahintar cewa da za a tsayar da ɗaya,
a ce, ‘harshen gado’ da zai fi fice.
[29] Wannan shi ne ra’ayin Mahdi Adamu
Ngaski, don ƙarin bayani
a dubi, Adamu, M. (1975) Hausa Factor in West
African History. Zaria: ABU Press.
[30] Al’adar Bahaushe ta rinjayar da uba ga gado don haka
a ganin Bahaushe harshen uba shi ne harshen haihuwa wato ‘harshen gado’ ba na
uwa ba. Ai don haka ne nike da ra’ayin a kira shi ‘harshen gado’ kawai a huta.
[31] Daulolin sun haɗa
da Gobir da Kabi da Zamfara da Zazzau da Katsina da Kano da Maraɗi wasu masana tarihi sun ce da Yawuri. Babu al’ummar
da ke da irin waɗannan dauloli a cikin al’ummomin Nijeriya da Afirka ta
Yamma.
[32] Babu wani tudu da tsibiri da kogi da rafi na cikin
farfajiyar Afirka da ba a samun Bahaushe. Kai har cikin ƙasashen Asiya Hausawa sun yi zaman yawace-yawace tun
ana zuwa aikin Haji a ƙasa, don ƙarin bayani dubi, Omar, S. (2012) “Hijirar Modibbo
Kilo daga Sakkwato zuwa Makka”, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[33] Idan ba ya da masu magana da shi, ba ya da karnan
farauta. Idan ya rasa karnan farauta ya rasa suna, harshen da ba ya da suna ba
za a ce da shi harshe ba. A ƙa’idance kowane harshe a duniya yana da suna.
[34] Daulolin da muka ambata na ƙasar Hausa duka Hausa ce harshen ƙasa gare su. Maƙwabtansu ma Hausawa sun shaƙa musu Hausa, wasu sun koma Hausawa.
[35] Idan waɗanda
aka Haifa da harshe su kaɗai ke iya magana da shi, ba ya dogon rai. A birnin
Makka, idan ka ga yadda mutanen Pakistan da Indiya da Rasha ke magana da Hausa,
ka zaci kana a Shahuci Kano. Haka ake son harshe, ya zama ana iya koyonsa cikin
sauƙi.
[36] Dr. Ɗahiru Argungu na Sashen Harsunan Turai na Zamani ya ba ni labarin cewa:
lokacin da yake karatun digirinsa na PhD a Uganda a Intarnational Islamic Uniɓersity in Uganda,a Mbale suka yi kiciɓis da mai sayar da nama tsire da balangu. Da suka
tambaya, suka tarar da Hausawan Sakkwato ne da ke zaune a can tun yaƙin duniya na (farko ko biyu?). Ni ma na taɓa tsintuwar wani Bakano a Ingila da yawon karatun allo
ya kai shi Borno daga nan sai Sudan sai Masar sai Ingila, ya share shekaru 40 a
London.
[37] Irin yadda Ingilishi ya yi wa Hausa shigan kutse a
daulolin ƙasar Hausa
bai so ya bar ta da hakin susa ba. ‘yar sa’ar da ya ci, ‘yan boko masu ido ɗaya suka rungume shi da hannu biyu suka watsar da
Hausa, da baya suka dawo da rakiyarsa dole.
[38] Harshen Hausa da al’adun Hausa sun kai wurin da
karatun Hausa ba ya iya zuwa can ko da mafarki. Tun gabanin a yi tunanin ƙaƙalo boko a duniya Bahaushe ya riga ya shiga uwa duniya da Hausa da
al’adun Hausawa. Mai koyon Hausa a yau, kansa ne yake taimaka wa, ya samu
abinci ba Hausa yake taimakawa ta samu ɗaukaka
ba. Hausa ta riga ta cira mai niya ya tashi ya bi.
[39] ‘Alif ja’ da jar tawada ake rubuta shi. ‘alif baƙi’ kuma da baƙar tawada. Don haka ne ya sa Bahaushe ya yi musu suna
da irin launin tawadar da ake rubuta su.
[40] Gambo fitacccen makaɗin sata ne, cikakken sunansa Alhaji Muhammadu Gambo Fagada. Domin samun
cikakken tarihinsa da waƙoƙinsa a dubi, Maiyama, U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar
Hausawa: Nazarin Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD, Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[41] Idan ganin mutum na yi yana ɗaukewa irin na tsohuwar fitilar hannu ana ce da irin
ganin, gani garaye-garaye. Masu tallar aya na tallar ta da cewa:
Aya ruguza aya!
Garinmu babu makaho
Sai
dai mai gani garaye-garaye.
[42] Shi jahili tuɓaɓɓe, bai sani ba, bai san bai sani ba. A yi daidai a yi
faɗa da shi, in an yi kuskure ya ba da tukuici.
[43] Tinƙahon kowane harshe a duniya shi ne yawan jama’ar da ke magana da shi. A
ilimin harsuna ta fuskar ƙwayar
sautuka da furuci da kalmomi da jimloli kowane harshe yana da su yana da yadda
ake tafiyar da su. Don haka batun fifiko bai taso ba a nan.
[44] Irin hasken wata shi ke sa a dinga ganin taurari ba
masu haske sosai ba. Haka harshe yakem idana ya ƙasura sai ya fara batsewa, ya haifar da karuruwan
harshe barkatai.
Jagora: Mai kare ka farauta
:Maras kare sai
:Ya tayas a kasha
Yara: A bar
shi nan sai haɗiyar miyo.
[46] Wannan ne dalilin da ya sa wani haziƙin ɗalibi ya yi
bincike a kan wani fitaccen rumbun adabi, ya sa wa kundinsa suna: Usman, B.
(2008) “Hikimar Magabata: Rayuwar Alhaji Usmaru Nasarawa Wazirin Gwandu”,
kundin digirin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo. A dube shi sosai, za a tabbatar da iƙirarin da muke yi.
[47] Sanin damisar Bunu shi ne sanin da ba tabbatacce da.
Bunu ya ce, ya san damisa yana ba da bayanintam ya ce, ƙarama ce, ‘yar firit, mai gashi irin na kyanwa,
yaronsa na cewa, yawwa! Baba ka gane damisa. Ya ƙara bayaninsa cewa; mai manyan ƙahoni. Yaro ya ce:’Wayyo! Baba ba ita b ace.”
[48] Duk wani ilimi da ɗan
Adam zai nema a duniya da harshe zai neme shi, da harshe za a bayar da shi.
Wannan shi nem dalilin faɗata na cewa wanda ya karanci harshe shi ne sarkin
sarakuna.
[49] Ashe gaskiyar jami’o’innu da ke tilasta waɗ alibi samun cikakken karatu a Turanci gabanin a ɗauke shi ya karanci shari’a (Law). Alƙalanci babban matsayi ne, da sai wanda ya san kansa fa
harshen ake shari’a da shi.
[50] Wannan ya nuna
dole mai hankali ya tashi tsaye ya koyi harshensa da wasu harsuna da ke kusa da
shi.
[51] Musibar da ta auku tsakanin Hutu da Tutsu da ta yi
sanadiyyar hasarar sama ga mutane miliyan ɗaya
da ake son yanzu a kwantar da ƙurar gidan Rediyon BBC ya buɗe
musu tasha ta musamman da harshensu.
[52] Dubi irin matsalar da ke ga koyon sabon harshe, wai a
cem idan mutum na son karatun digiri wajensu sai ya karanci harshensu. A
Bulgaria sai an koyi harshe. A Russia sai an koya a France sai an koya, ga su
nan dai.
No comments:
Post a Comment