A
iya sanina, wannan ɗan
bincike sabo ne, saboda rashin samun wani da ya gabace shi a fagen nazarin
Hausa. Duk da haka, abin da aka gina bincike a kansa “kuka” ya girmi duk wani
mai bincike da zai yi bincike a kansa. Tunanin kowane mai tunani, ba zai fice
da’irar al’adarsa da adabinsa da aka gina cikin harshen da yake rayuwa da shi.
Sanin haka ya sa na gayyato ƙwararrun
mawaƙan Hausa
(20) [14 na baka, 6 marubuta], na sarrafa ɗiyan
waƙoƙinsu (34). Cikin wannan fafitikar,
na yi garkuwa da karin magana (3), kirari (1), ƙagaggen labari (1), waƙoƙin dandali (3) domin daidaita akalar
bincike. Bisa hasken waɗannan
kayan aiki (62) aka ci nasarar gano…
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
Waya: 0803 431
6508
Takardar da aka
gabatar a taron ƙara wa juna sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina, ranar Laraba 6 ga watan Maris, 2013 ƙarƙashin
jagorancin Farfesa Sabr Salama da ƙarfe 10 na safe a
dandalin taron tsangayar fasaha.
Tsakure
A
iya sanina, wannan ɗan
bincike sabo ne, saboda rashin samun wani da ya gabace shi a fagen nazarin
Hausa. Duk da haka, abin da aka gina bincike a kansa “kuka” ya girmi duk wani
mai bincike da zai yi bincike a kansa. Tunanin kowane mai tunani, ba zai fice
da’irar al’adarsa da adabinsa da aka gina cikin harshen da yake rayuwa da shi.
Sanin haka ya sa na gayyato ƙwararrun
mawaƙan Hausa
(20) [14 na baka, 6 marubuta], na sarrafa ɗiyan
waƙoƙinsu (34). Cikin wannan fafitikar,
na yi garkuwa da karin magana (3), kirari (1), ƙagaggen labari (1), waƙoƙin dandali (3) domin daidaita akalar
bincike. Bisa hasken waɗannan
kayan aiki (62) aka ci nasarar gano ma’anar kuka, da mafarin kuka, da yadda ake
kuka, da lafuzan Bahaushen kuka. Binciken ya tabbatar da samuwar nau’o’in kukan
Bahaushe (12). Daga cikin waɗannan
nau’o’i na kuka guda (7) Bahaushe bai yi tarayyarsu da kowace halitta ba, guda
(5) suka yi canjaras da kukan dabbobi da ƙwarin ƙasar Hausa. Haƙiƙa, babu wani bincike na falsafa ko rayuwar
mutane da za ya taɓa cin nasara, in
ba a lalubo adabinsu na baka ba. Don haka, kafa hujja da adabinmu, dole ne ga
mai nazari a kan rayuwarmu. Buƙatar
wannan bincike shi ne, sama wa ire-iren waɗannan
tunane-tunane da ayyuka da falfasar rayuwa bagire mai cin gashin kansa cikin
manhajar koyar da Hausa a matakin karatu mai zurfi. To! Ga ku nan ga “kuka”
amma kada ku yi “kuka”.
Gabatarwa
Walwala ta burin
zuciyar ɗan Adam tsakanin
abubuwa biyu take dawara: farin ciki da baƙin ciki.[1]
Idan abin farin ciki ya ratsi zuciya, fuskarsa za ta nuna, ta sake sosai, ta yi
ƙyalli,
daga nan murmushi da dariya su ziyarce ta.[2]
Idan baƙin
ciki ya ratsa ta, sai ta yi baƙi,
ta turnuƙe,
idanu su yi jajir, su cika da galla, idan ya tsananta hawaye su jiƙe fuska, murya ta ba da labarin
abin da ake ciki. Don haka, da dariya da kuka, sun cancanci a yi bincike kansu
domin babu rayuwar da ba su ziyartar zuciyarta. Ɗan binciken da na gabatar kan “dariya” ya
haddasa daɗa juna sani
tsakaninmu ɗalibbai, wanda
shi ya ba ni tunanin, bayan an yi dariya a ɗan
taɓa kuka ko da ba da hawaye ba ne.
Don haka, na bar taken takardar buɗe
domin samun damar ɗora kuka a
ma’aunan adabi da al’ada a ga irin nauyinsa. Muradina shi ne, yi wa kuka kallon
ciniki, domin in samu damar rairaye shi sarai a matakin nazarin al’ada. Babu
halittar da ba ta kuka, babu halittar da ta fi gaban kuka, babu halittar da
abin kuka ba ya riskuwa ko ta riske shi.
Hanzari
Gabanin
in duƙufa da
matashiyarmu, na so in gabatar da ɗan
hanzarina a kan abin da zan yi nazari a kai. Na yi ƙoƙari iya yadda nake yi, har yanzu ban ci
karo da aikin da wani ya yi a kan ‘kuka’ ba. Ban ci karo da wani littafin da ya
keɓe wa kuka wani babi, ko fasali, ko
sakin layi, ko wasu sheɗaru ba.
Ban ci karo da wata muƙala
ko hira da aka yi kan kuka ba. A gidajen Rediyo da Talabajin ban taɓa
jin wani shiri da aka yi kan kuka ba. Ni dai a iya bincikena, ban samu ba, amma
na san, ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba.[3]
Hausawa sun ce, ‘komi ya ɓace maza
ka biɗo shi’, na tabbata ba za a rasa
wani aiki kan kuka ba, sai dai raunin da nake da shi na zama ɗalibi,
ban samu yin kiciɓis da shi ba.
A
wajena, wannan ɗan yunƙuri da zan yi jifa cikin duhu ne,
wataƙila abin
na nesa, ni ne ban samu kai gare shi ba. A duniyar bincike, idan bincike ya
kasance haka, ba za a ɗora shi
bisa wani ra’i ba, domin rashin samun kulawar magabata a kansa. Ban ce, ni ne
na farko a wannan bagire ba, kuma ban yi zaton ina iya gano abin da magabata ba
su gano ba. Wane ni! Kwaɗayin da
nake da shi, shi ne, in yi wa bagiren kwasan karan mahaukaciya, masu hankali da
basira su taya ni naɗa gammo
da kinkintsa karan da zan kwasa, da miƙe mini igiyar da zan ɗaure
su sosai, ka da bayan na ɗaura, su
kasa ɗaukuwa, ko bayan na ɗora
a ka, su kwance, ko su wargaje. Idan an fahince ni, ina fatar a sawo ni gaba
domin malamin kiɗi Narambaɗa
cewa ya yi:
Jagora: Taro na tambaye ku
:Shin
kowag ga wuta
Yara: An ka ce: “A ɗebo”
wa ka zuwa?
:Wanda
yag gani ka zuwa
:Kowas
shaida shi ka shan rana
:In
bai je ba, yai batun banza
:Ko
can yanzu shi batun banza
:Daɗin
hwaɗi garai
Gindi: Ya ci maza, yak wan shina shire
:Gamda’aren
Sarkin Tudu Alu
Ma’anar
kuka:
Masana marubuta ƙamushoshin harsuna ba su manta da
“kuka” ba a wajen bayyana kalmomin harsuna. Bisa ga uzurin da na gabatar, ya
kyautu mu fara lalubo ma’anar da suka bai wa kuka, domin mu ga yadda za mu
gwada tsawon ma’anoninsu. A wajen Turawa, “kuka” na da ma’anoni fiye da goma
sha shida domin a wajensu kuka shi ne:
Ɗaga murya a kan wani furuci, a yi iƙirarinsa a bayyane kamar wurin
talla. Haka kuma, sassauta muryar mai roƙon taimko ko alfarma, ko abin da zai shafi
rai kai tsaye a zubar da hawaye, ko a yi wani kira na neman ceto tare da
furucin nuna ƙunci
da kaico ko game fuska da zubar da hawaye da dai wasu sigogin kira da za su
nuna buƙata
cikin matsuwa. (Fassarar marubuci).[4]
A hangen G. P.
Bargery (1993: 632) ya kalli kuka a Hausance da:
Ɗagar da murya ta wanda ke cikin ƙunci ta nuna kaico, ko muryoyin
tsuntsaye ko kokawan da gurɓataccen
ciki ke yi ko muryar dabbobi.[5]
Roɗana
Ma da Newman (2003: 59) sun kalli kuka da faɗar:
Yin
hawaye, ko labarin ya sa na yi hawaye, ko ƙwala ihu! Ko ƙwala kuka ko yin kururuwar neman
taimako. A nan, za a yi amfani da ya fashe da kuka ko ya ɓarke
da kuka.
Ƙamusun Hausa na Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano (2006: 251) ya ba da fassarorin goma sha uku na
kuka kamar haka:
Kuka
ko koke-koke, ƙara
ko wani sauti tare da fid da hawaye saboda ɓacin
rai. Waɗannan sun haɗa
da:
i.
Lalura, kai kuka wurin shugaba.
ii.
Ƙara,
ma’aika suna kuka da shugabansu.
iii.
Matsala, ba kukana ba uwar kishiya
ta mutu.
iv.
Rurin dabba ko dirin tsuntsu.
v.
Ƙarar
ciki saboda hargitsewa ko ɓaci.
vi.
Kukan amarya, kukan da take yi
ranar ɗauka ko kamu.
vii.
Kukan jirigi, busan da jirgin ƙasa ke yi in ya zo tasha.
viii.
Kukan kura, ƙuru ko ƙundunbala.
ix.
Kukan kurciya, ishara ko
hannunka-mai-sanda.
x.
Kukan mujiya, yin kyauta – saurayi
ya yi wa budurwa.
xi.
Kukan kasa, sautin da mutum yake
fitarwa idan yana gyaran murya musamman idan goro ya ƙware shi.
xii.
Kukan zuci, wato damuwa ba tare da
bayyana ba.
xiii.
Kukan tsirinya, watau nishin da
mutum yake yi domin ya tsira daga wani horo.
Ɗauraya:
Fassarar da masu
Turanci suka ba kuka yalwatacciya ce sosai, ba su raga wa kuka hakin susa ba a
fassararsa ta kusa da nesa, ta al’ada da ta fannu. Sun bayyana dalilin kuka a
Baturiyar al’ada, amma ba mu ji yadda Bature ke kuka ba, da ire-iren sautuka ko
kalmomin da Bature ke furtawa idan yana kuka ba. Da na lalubo fitattun ƙamusoshin Hausa, an warkar da ni
sosai, musamman na zamaninmu na Jami’ar Bayero, sai dai kash! Ko su ba su
fayyace Bahaushen kuka ba, sun yi wa abin shafi-mu-lera, ban ci karo da kalma
ko ɗaya da za a iya rarrabe Bahaushen
kuka da waninsa ba. Yunƙure-yunƙuren masu ƙamus duk za a iya ɗauraye
shi gida biyar:
i.
Kuka abu ne da ke zuwa lokacin da
rai ya ɓaci
ii.
Kuka ana iya gane shi ta murya mai
ban tausayi
iii.
Ana iya tantance kuka ta fuskar
bayyanar hawaye
iv.
Kalmar kuka na ɗaukar
kalmomi barkatai a harshe
v.
Cikin al’amarin kuka akwai ɗagar
da murya
Waɗannan
abubuwa biyar da muka ɗauraye
ma’anonin kuka da ƙamusoshi
suka bayar, suna bayani ne a kan kuka na kowane mutum, na kowane harshe, na
kowane launi, na kowace nahiya. Ban yi musun haka ba, amma a al’adar Bahaushe,
akwai kalmomin da za a iya rarrabe kuwwa, da roƙo, da kuka, da ɓacin
rai na takaici. Irin haka ne nake son in samu a ƙamus, sai na ga ba su ba abin muhimmanci
ba.
Kuka
A Aikaice:
Ma’anonin kuka da
suka gabata sun bayyana yadda za a iya kirdadon muryar kuka da rarrabe ta da
sauran muryoyi. A wannan fasali ina son in kalli yadda al’adar Bahaushe ke
kallon kuka a aikace. A wajen Bahaushe, kuka na haƙiƙa zubar da hawaye
ke sa a haƙiƙance shi. Bayan haka, ana murzar
idanu da hannun dama, wani lokaci a sa hannaye biyu duka. A wasu halaye, hannun
da mai kuka ke sarrafa ayyukansa da shi zai share hawayen (wato in Bahago ne da
hagu, in Badame ne da dama). Bugu da ƙari, idan takaicin
kuka ya ci rai za a ga an haɗa da cizon yatsa da girgiza kai ana jujjuya shi daga
nan sai bori (in ɗan bori ne).
Narambaɗa ya yi nuni a kan
haka:
Jagora: Ku dangin farin ciki
:Kui ta zaman
farin ciki
:Su dangin baƙin ciki
:Sai murzar ido
sukai
:Sai cizon yatsu
Yara: Dori
suna kazarkazar
:Amma yanzu sun
gaza
:Duk ya sa ƙafafuwa
:Ya tattake su
Gindi: Kai
bajinin Namoda
:Gagara gago na
Zagi
:Iya gaba na Abdu
A nan, Narambaɗa ya ambaci murzar
ido da cizon yatsu bayan ya gabatar da baƙin cikin da ke
tare da mai su.
Ba dole sai an ce sun yi kuka ba, Bahaushen da Hausarsa ta ji gishiri ya san
kuka ake yi. Makaɗa Gambo ya ambaci
kuka da irin wannan sigar a taken Sani na Zauro, da Muhammadu Inuwa Ɗanmaɗacci a karon
battar da suka yi da Tsoho Tudu. Ga ɗaya daga cikin riwayar:
Jagora: Bawa dut yai jan idanu
:Nag ga shina
murzar idanu
:Nag ga hawaye na zuba
mai[7]
Kuka a duniyar dabbobi da tsuntsaye:
A
ma’aunin Bahaushe, duk wata halitta da ke da baki tana da fuska biyu a al’ada.
Idan tana sadarwa ta fuskar ɗagar da
sautinta, ‘yar uwarta ta ji ta, za a ce; “tana kuka”. Wannan sadarwar ita ce
kuka. Idan kuwa ba ta yi, ana aron magana a sa mata baki musamman a fagen karin
magana da waƙoƙi da tatsuniya.[8]
Rukunin dabbobi
sautukan da ke fita a bakunansu ana yi musu sunan gama gari “kuka”. Duk da
haka, ana rarrabe kukan dabbobi daban-daban ta fuskar sunayen da ake yi musu a
Hausance. Ga ɗan misali:
Ya yi wuta gida
bakwai da nufinai sarki,
Ya ko sa
maruruwa ciki ga sarƙoƙi,
Can shika danne
kafiri Shi buga mai kulki,
Hargowa
shi kai ciki nata tamkal jaki,
Har abada yana ciki nata ba a fissai
ba.
Jagora: Dawaki na suka sun kwan haniniya
:Bari gobe ta
zan ta banza
:Mai tsere musu
nag ga ya zo
Gindi: Ɗan Malam ci ƙwallo sarkin gudu
:Na
yarda da ɗan Hilinge
●
Kare: Ana cewa kukansa “Habshi”.
Malam Muhammadu Sambo Wali[11]
ya ambace shi a waƙarsa
ta Zaman Banza yana cewa:
Kirayo min ɗan
mu’abba mai babban baki,
Kamad dai habshin kare yana buɗab
baki,
Yabon wani yaka
so, yabon Muhammadu nika ɗoki,
Yabon wani bai
yi ka roƙi
Allahu maroƙi,
Ka nemi ijaba garai ka bar son
damunmu.
Jagora: Raƙumin siyasa shi bai iya haraka ba,
:Zalab-zalab ba ƙwauro wai za a biɗan
jikka,
:Bari Raƙumin siyasa sirdi muka labta mai,
:Mu bar shi can
cikin rana shi’ yi ta bololloƙai.
Gindi: Ba a gane manya
:Sai ci
ya samu
Da
yawa, idan ayarin raƙuma
ya ratso gari za a ji yara na waƙa da faɗar:
:Raƙumi-raƙumi zololo
:Ga kunama nan
baya gare ka
:Raƙumi shina kuka bobobo!
● Tumaki/
Awaki: Waɗannan dabbobi
Bahaushe ya fi hulɗa da su fiye da
kowace dabba, amma kukansu ba ya da wani suna face kuka. Awaki ana rarrabe sautinsu
da lafazin “mee!” Malam Bala Maigumbe Bunza[13] a
cikin waƙar,
“Damben Bala da ɗan Argungu
Gumel”, ya fayyace kukan awaki da cewa:
Jagora: Na’ iske baba Ɗankalmalo ɗaka
:Yac ce ur! Da ƙya! Da Mee! Kowa shi ɗaga
:Nac ce: Ba
“Burguma ba ce,
:Ba Kyalla ba ce
:Ai ɗan
ke na Bala yaj ja hitina.”
:Don kwak kashe
mutum duka shi ka hwaɗi.
Ga al’ada, ana korar kaza ko tantabara da
sauran tsuntsaye da lafazin “ur!” Ta sigar yadda suke fiffikawa su tashi. Idan
suna ɓanna a gargaɗe
su da “Ƙya!”
Akuya kuwa ana kiranta idan za a ba ta abinci da irin kukan da take yi, “mee!”
Bisa wannan fahinta, kukan awaki shi ne, “mee!”
●
Kura: Ita dabbar dawa ce da ta fi
amo sosai cikin adabin Bahaushe, wataƙila, saboda ita kaɗai
ce yake kamowa ya kiyata a gida.[14] Ana
yi wa kukan kura suna “Muui!” Wasalin ‘u’ za a ja shi da ƙarfi da tsawo domin idan aka ce
‘mui’ ana nufin an yi shiru da baki an
kasa ta cewa. Wannan a fili yake a karin maganan da ke cewa: “Muui! Kukan
kura.” Da karin maganan da ke cewa: Kamun kurar kurma, kurma kuka, kura kuka.”
Wato muimuiniyar da kowannensu ke yi da sautinsa, shi ne Bahaushe ya fassara da
kuka.
Idan muka dubi ɓangaren
kuka na biyu na tsuntsaye, Hausawa na ce ma mafi yawansu ‘kyarkyara’. Hausawa
na cewa kukan zabbi ‘ƙyarkyara’
kukan kaji kuwa ‘cara’. Carar kaji yara na fassara ta da ƙaƙarako. Wasannin da yara ke yi daren salla
za a ji suna waƙa:
Ƙaƙarako! Gobe sallah!
A yanke manya!
A bar ƙanana!
Sauran ƙananan alhaki irin su ƙwaƙwaƙwa kukan da suke yi ake yi musu suna da
shi.[15]
Kulɓa kuwa a ganin Bahaushe, ƙyace take yi “ƙt!”[16]
Ga su nan dai. A ganin Bahaushe, kukan dabbobi da tsuntsaye na da sunayensu
gwargadon yadda sautin kukan ya kai ga kunnen Bahaushe.
Fassarar
kukan dabbobi da tsuntsaye:
Zamantakewar
Bahaushe da dabbobi, da tsuntsaye, da ƙwari, ta ba shi damar sarrafa ma’anonin
koke-kokensu, da motsinsu, da ma’anoni daban-daban. Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya fara hange waɗannan
al’adu a cikin rubuce-rubucen na tauhidi. Ya ambaci wannan matsala a littafinsa
Nurul Albabi[17]
da Wasiƙatul Ikhwani[18]
da Najamul Ikhwaani[19].
A al’adar Bahaushe, idan mujiya ta yi kuka, wai, mutuwa take kira don haka ake
amsa mata da: “Ki ci kanki.” Idan zaki ya yi kuka, duk wurin da gara take za ta
zube ƙasa. Wataƙila wannan ne dalilin Maidaji Sabon
Birni[20]
na cewa:
Jagora: Zamanin Jangwarzo
Yara: Kura ba ta sauran kuka
:Gara
ba ta sauran saƙa
Haka Bahaushe ke ganin, a koyaushe
kurciya ke kan bishiya/ice idan tana kuka wani saƙo ne take sadarwa ga mutanen da ke wurin.[21]
Don haka ne ake da Karin maganan ‘Kukan kurciya jawabi ne’. A wasu lokuta, akan
ƙara karin
maganan da cewa: ‘Sai mai sani ka ganewa, sai mai hankali da mai lura’. Masani
shi ne, wanda ya san ma’anar kukan. Mai hankali shi ne, wanda ya kiyaye lokacin
da take kuka da abubuwan da suka faru ko ke faruwa a lokacin. Mai lura shi ne,
wanda zai iya ba da fassarar da za ta yi canjaras da abin da kurciya ke faɗa.[22]
Haka Hausawa ke cewa, haniniyar doki labarin abubuwan da ke tattare ga uban
gidansa ne yake bayarwa.[23]
Kukan kaji kuwa, maraba suke da ketowar alfijiri, kukansu na farko labarin
tsakar dare suke bayarwa.[24] A
taƙaice, a
wajen Bahaushe, kukan dabbobi da tsuntsaye saƙo ne ga jinsunansu, ko ga jama’ar da suke
tare da su. Gaskiyar Kassu Zurmi da ke cewa, kare ɗan
‘dokad/sandal dare’, ya ce in ya ga ɓarayi
sun shigo gida haushinsa faɗar yake
yi:
Jagora: ga su, ga su, ga su!
:
ga su, ga su, ga su!
:
ga su, ga su, ga su!
Bahaushe ya
camfi kukan baƙin
kare kamar yadda Bala Ganɗo ya
fassara shi da:
Jagora: Kukan baƙin kare
:Ko
can ba shi da amfani
:Duk
in day ay yi kuka
:Tsiya
shika jawowa
Gindi: Ba a gane manya
:Sai ci ya samu
Kukan
Bil Adama (mutane):
Maƙasudin wannan bincike shi ne, auna
kuka a Bahaushen ma’auni. Kukan bil Adama shi ne haƙiƙanin kuka, kuma shi ne kukan da nake son
in dira a kansa sosai domin a tantance na Bahaushe da waninsa. Idan muka
waiwaya ga fassarar da ƙamusoshi
suka bayar game da kuka, zamu iya tsakaita ma’anar kuka a Hausance da cewa:
Kuka
shi ne, kumburar murya ko shaƙewar
ta, da ɗaukaka ta,
saboda wani abin baƙin
ciki ko akasinsa, da ya ratsi zuciya, tare da zubar da hawaye, da ketowar gumi
a jiki, musamman a goshi, da fitar da majina tare da mutuwar jiki na gaba ɗaya.
Idan ana tsaye aka kai zaune, ko ana zaune aka kai kwance, ko ana tsaye aka
ruga a guje, kukan ya fi tsananta. Idan buƙata ce ga rayuwa, ko buri, ko fata, ko roƙo, ba sai an ga hawaye ko an fita
hayyaci ba.
Haƙiƙanin gaskiya Bahaushen kuka zai hau kan
wannan fassarar gadan-gadan, musamman idan aka danganta kuka ga sosuwar rayuwa
ta ƙunci aka
dubi waɗannan karuruwan
magana:
●
Wanda ya ce, bai iya kuka ba, uwar
shi ce ba ta mutu ba.
● Ba
kukana ba, uwar kishiya ta mutu.
●
A doke ni a hana ni kuka?
A wajen
Bahaushe, kuka na da dalili, don haka ne kowane kuka ke da suna. Wannan zai
bayyana sosai idan muka lalubo ma’anar karin maganar: “Mai neman kuka an jefe
shi da kashin awaki.” Yana son ya yi, babu mafari, dole ya ƙunshe kukan, har sai da aka yi masa
rauni da kashin awaki, ya buɗe baki da
dalili. Haka ɗabi’ar yara
take, irin ta awaki, hatta da abin da ke amfaninsu ake yi musu kuka za su yi.
Wannan ce ta sa Bahaushe ke da karin magana: “Dattijo ba shi kukan aski, sai
dai shi ce wurin ga bai ji ruwa ba.”[25]
Idan dai kuka ya yi kuka, ga ido za a iya fayyace shi. Irin ƙimar da ke ga ido ga kuka ya sa
Bahaushe ke cewa: “Mai zurfin ido tun da wuri yake fara kuka”, domin kogin idon
ke hana bayyanar hawaye da wuri. Idan babu hawaye ga kuka, Bahaushe na ganin da
walakin, idan aka nazarci faɗarsa:
“Kukan uwar Musa, shekara tara babu hawaye.” Makaɗa
Ɗan’anace[26]
ya gargaɗi mata da su
daina irin wannan kukan a waƙar
Nadelu da yake cewa:
Jagora:
Sai su aza muna kukan
Yara: Da ba hawaye ko tsito
…
… …
Gindi: Maza na tsoron maƙi garaje ɗan
Garba.
Muryar
Kuka a al’adance:
Yadda
Bahaushe ke tantance kuka, haka yake tantance muryarsa. Wata rana, muryar ta
kaurara, wani lokaci ta yi ƙara,
wani lokaci ta yi ziza, ga ta na dai. Waɗannan
dalilai ke sa a ji Bahaushe na cewa:
·
Ya fasa kuka
·
Ya raara kuka
·
Ya ɓarke
da kuka
·
Ya dinga zubar hawaye
·
Sun cika gida da kuka
·
Suka faɗi
suna kuka
Waɗannan
lafuza da makamantansu sun danganta da yadda muryar kukan ta shiga kunnen
Bahaushe ko dalilin da ya haddasa kukan. Lokacin da Gambo[27]
ya tayar da tubar Nazaƙi[28]
ga yadda ya ce:
Jagora: Yai wani tsalle yac cira sama
:Yaf hwasa
kuka yay yi yaya
:Yac ce: “Tuba ta tashi Gambo
:Mallami da zagin doka ga kainai
:Ya baza hoda ya yi gazal
:Ba ta batun salla akai ba.”
Da yake kukar a
husance aka yi ta, rai ya ɓaci ƙwarai, takaici ya ratse shi girshi,
dole ya fashe da kuka, irin na wani ɗan
dambe da Shago[29]
ya yi wa cin kwaɗai Ɗan’anace ya ce:
Jagora: Yay yi zaune yaf hwasa kuka
:Tsoho ba ya sa iyali kuka
Kukan da aka yi
girshi, da ƙarfi,
fasa shi aka yi, ko ɓarkewa da
shi aka yi. Idan kuwa ƙarar
sautinsa ta kai ta komo, ya zama kamar guɗa,
mai ba da labarinsa bai ji tausan jin sa ba, ya zama irin abin nan da Hausawa
ke cewa, kukan ɗan wani goge.
Haka ma yadda dakarun Jautullu Askarawan Kabi[30]
ke rawan atisayen cin Fulanin Sakkwato na Dandin Mahe[31]
da yaƙi suna
cewa:
Jagora:
Jautullu ɗan
gari na
Yara: Amma maza da hwama
Jagora: Jakadiya hito ki yi guɗa
Yara: Ki rwarwa kuka
Ga al’ada, idan
mayaƙa sun
dawo da yaƙi,
Jakadiya za ta tarbe su da guɗa. To
yau, an ci su da yaƙi.
Yadda duk za ta ɗagar da murya a
guɗa, haka za ta ɗagar
da murya ta rara kuka kamar mai rera waƙa. Haka aka yi cikin kirarin ɗaya
daga cikin taurarin Garba Ɗanwasa
Gumi mai kiɗan tauri.[32]
Tauraron ya ce, ya sare mijin Kande wurin faɗa
daji, da aka zo da shi asibiti matar ta ji, ta rugo, ga yadda ya ce:
Tauraro:
Jikinsa ko’ina bandeji
:Ga
ta da tsohon ciki tana ƙyallowa
:Nas
sare kanta
:Nas
sare shi
:Kaduna
nay yi hursuna waɗannan bayi
Haka dai
muryoyin kuka ke hawa da sauka, gwargwadon abin da ya sa kuka, ko abin da ake
yi wa kuka. Idan Bahaushe ya ji muryar kuka da irin waɗannan
ma’annai yake ambaton su.
Lafazin
kuka:
Idan an ji ƙarar muryar kuka akwai lafuzan da
ke fita ga mai kukan, waɗanda za
su sa a tantance Bahaushen kuka ne. Idan Bahaushe ya yi lafuzan tausayawa na
neman agaji da taimako ko da hawaye bai rako su ba, zai ce: “Wa ke kuka?” ko
“Ina ne ake kuka?” ko “Ana kuka a can.” Ga kaɗan
daga cikin lafuzan:
·
Wayyo!
·
Wayyo Allah!
·
Wai ni kaina!
·
Ihm!
·
Wayyo ni!
·
Yoyoyo!
·
Boni yoyo!
Bari mu waiwayi
waɗannan abubuwa cikin taskar adabi
kamar yadda masana taskar suka adana su. Marigayi Sheikh Nasiru Kabara[33] a
cikin waƙarsa
ta begen Annabi Muhammadu (SAW) da tsananin soyayyar ya ƙona zuciyarsa ya ce:
Begen
Muhammadu ya cika mini zuciya
Ya
ƙone
sassan zuciya wayyo niya!
Da zuciyar ta ƙone, zafin da zogin da raɗaɗi
suka game, sai ya furta Bahaushen lafazin kuka “wayyo!” A cikin waƙar ‘Cuta ba mutuwa ba.’ Aƙilu Aliyu[34],
ya yi irin wannan lafazin da cewa:
Harira ko ita wannan,
Kaico!
Uwar ‘ya’yan nan,
Nawa
Aminu Sulaiman,
Mariya
Muhammadun nan,
Sanda
ta je duba ni.
Ganin
masoyi kwance,
Ƙafafuwa goggoce,
Ta
kasa bakin zance,
Ta
dinga kuka ƙarce,
Faɗi
take wayyo ni!
A cikin tsananin
soyayya, duk abin da ya faru na sosa wa Bahaushe rai, za a ji lafazin wayyo!
Idan ma wuya aka sha, za a ji da lafazin za a nuna kuka. Dubi waɗannan
baitoci na bayanin ayar motsin rai a cikin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin
Rubutun Hausa. (Bunza, 2005):
Tamkar
dai ka ce: Haba! Kayya! Yawwa!
Wayyo!
Baba na bari ban ƙarawa.
Amali Subugu[35]
ya ciro irin wannan lafazi ga bakin raggo, da ya ƙi zuwa, aiki, yunwa ta sallama masa. Da ya
kasa ba ta masauki, shegen cewa yake yi:
Jagora:
Wayyo Allah! Wayyo Annabi!
Yara: Wayyo yunwa!
Wayyo
yunwa!
:Ko
jimin za ki yi
Gindi: Zahin rana bai tauye ka ba
:Sabon
Goje Isa Mai Kware
Bahaushe ko
lafazin kukan wani zai ba wani labari, da kalmar “Wayyo!” yake bayarwa domin ta
fi fice, an fi gane ta, ta fi bayyana me ake nufi. Namata mai zari[36]
da yake ba da labarin matsalar auren mace mai goyo cewa yake:
Jagora: Aure da mai goyo fitina na
Yara: Na auri goyo ban ƙarawa
Jagora:
Da nay yi niyyan in bi uwatai
Yara: Yad ɗora
kuka: ‘wayyo! wayyo!’
Gindi: Kashe wuta in an ka hasa ta
:Sarkin
maƙera Jaɓɓo
na Yarma
A nan, yaro ba
wani kukan ɓacin rai yake yi
ba, amma aka ruwaito lafazin wayyo! A cikin kukan mata maras hawaye, Ɗan’anace ya ruwaito kalmar “Wai ni
Allah!” kamar haka:
Jagora: Kukan da ba hawaye ko tsito
:Sad
da duk mun ka taɓa
:Suna
hwaɗin: ‘Wai ni Allah!’
Gindi: Maza na tsoron karo da Ado ɗan
Garba
Daga cikin
lafuzan Bahaushen kuka akwai ‘Kaico!’ A ƙa’idar Bahaushe, wanda musiba ta sama yana
kuka da ‘kaico!’ Haka ma, idan musiba ta samu wani, masoya na yi masa kuka da ‘kaico!’
Ba zan musanta cewa, wani lokaci kalmar ‘kaico’ na kasancewa kwatsewa ko
tsawatawa ko kayya! Ga abin da ake gudun ya faɗa
ga rayuwa. Ga abin da Garba Ɗanwasa
Gumi ke cewa:
Jagora: Kaico!
abin da nat tuna
:Garba
ina kuka!
:Makiyayan
ƙasag ga
:Su
na nika wa kuka
Gindi: Ya sa ‘yan maza gudu
:Ba
da laɓewa ba
:Zirnaƙo na Garba
:Kai
mai ɗamarar fama
Garba na yi wa
makiyaya kuka da ‘kaico!’ A hangen musibar da za su shiga idan suka shiga
gonakin Gumawa (mutanen garin Gumi). Da irin wannan lafazi ne mahaifiyar Alhaji
Gambo Fagada mai waƙar
ɓarayi, ke yi masa kuka kamar yadda
ya ruwaito cewa, idan ya dawo da waƙar ɓarayi,
sai ta ce:
Jagora: Sai ta ce mini: “Yaro kaico kanka!
:Mai
riƙa kura
kowane na
:Ba
shi gudun zahin haƙora”
:Sai
in yi awa ni ban sani ba
:Nan
ko na gane nuhinta
:Wai
ita nuhinta
:Kukan
da takai min kodayaushe
:Tun
da ina waƙar
ɓarayi
:Ai
ba wuce ɗauri za ni yi ba
:Sai
in Allah ya kiyaye
Idan waɗannan
lafuza suka bayyana an gama kuka ga fassarar Bahaushe. Idan ana kule ke nan, ga
fassara, Bahaushe kuka ya kasu rukuni-rukuni kamar yadda dariya ta karkasu
barkatai.[37]
Rabe-raben
kuka:
Bisa ga abubuwan
da aka nazarta na dalilan kuka da mafarinsa, masana al’ada na ganin kuka ya
karkasu kamar haka:
i.
Kukan mutuwa
ii.
Kukan ceto
iii.
Kukan takaici
iv.
Kukan magana
v.
Kukan tsoro
vi.
Kukan daɗi
vii.
Kukan sana’a
viii.
Kukan biki
ix.
Kukan ƙauna
x.
Kukan ibada
xi.
Kukan mafarki
xii.
Kukan ƙarya
Kukan
mutuwa:
A
al’adar Hausa, tun gabanin bayyanar Musulunci akwai kukan mutuwa. An fi yi wa
baligi kukan musamman waɗanda suka
mutu ba su yi aure ba, ko waɗanda suka
mutu da ƙurciyar
aure ana tsakar haihuwa. Haka kuma, shugabanni idan sun mutu ana kuka. Ga
al’ada, mata ke kukan da ɗagar da
murya. Haka kuma, duk wadda ba gidansu aka yi mutuwar ba, ba za ta fara kuka
ba, sai an yi kusa da gidan mamaci. Wani lokaci, idan suna da yawa har shawara
ake yi: Ina ya kamata a fara kuka? Maza sai dai zubar da hawaye[38]
kawai kamar yadda Gambo ke cewa:
Jagora: In ishe tsohi na hawaye
:In ishe mata sun yi yakkwat!
Jagora: Na yi kuka
:Na yi baƙin ciki
Yara: Na tuna Allah ɗai
ka isa mai
Gindi: Ya wuce raini
:Ba a yi mai shi
:Ahmadu jikan Bello sadauki
Kukan
takaici:
Wani
abu ne rai ya ƙallafa
wa kansa bai samu ba, kuma yana ganin dole ya same shi, irin kukan da Sani na
Zauro da Gambo ke cewa:
Jagora: In yak koro bai cika ba
:Sai
ka cimma hawaye na zuba mai
Kukan
ceto:
Kuka
ne da ake yi domin neman kuɓuta daga
laifin da aka yi, ko buƙatar
wani ya zo ya cece ka ga halin da aka shiga. Alhaji Umaru Nasarawa Wazirin
Gwandu[41]
ya fito da wannan kukan cikin waƙar Yabon Sarkin Gwandu Yahaya yana cewa:
Wayon
a ci, an yi ka ƙi
yi,
Wada
yag ga buge shi za ka yi,
Yac
ce: “Wayyo! Uban Jada mi niy yi?”
Malam Sulaiman Ɗunɗaye[42]
mawaƙin NPN ya
yi irin wannan kukan da ya shiga PRP bisa kuskure yana cewa:
Wayyo! Allah na tuba da shiga PRP
shirka,
Allah
na tuba gare ka
Abada
kai ne …
Amshi: ‘Yan santsi kun zama yawa
Da
ma ba ma ƙaunarku
Mu
mun koma NPN
Kukan
magana:
Kuka
a wajen Hausawa yakan ɗauki
ma’anar magana idan aka dubi kukan dabbobi da tsuntsaye da yara ƙanana. Mata na iya rarrabe kukan
jinjiri na yunwa, da na ciwon ciki, da na son ya yi barci, da kukan banza.
Masana kimiyya sun ce, a riƙa
barin yara su yi kuka sosai domin yana ƙara buɗa
musu basira.[43]
Ke nan, hana su kuka na mayar da su daƙiƙai mamugunta.
Kukan
tsoro:
Wannan
shi ne kukan da mutum ke yi kan tsoron wani abu da yake jin tsoro, ko ake jin
tsoro. Idan tsoro ya kama mutum ko ƙwala ihu! Ya yi, ana fassara shi da kuka.
Hali Rayya,[44]
ya yi irin wannan kuka a waƙarsa
ta “Wanakiri Dodon Kwanya”, yana bayyana tsoronsa ga halin duniya, ya ce:
Jagora: Wayyo
duniya! ‘Yal baya
:Kwab bi ta taki bai kai
wajje
Makaɗa
Amali Subugu ya yi irin wannan raki lokacin da ya tuna mutuwa zai yi, a yi
hisabi, yana cewa:
Jagora: In hairan kakai!
:Ishe hairan kakai!
:In sharran kakai!
:Ishe sharran kakai!
:Wayyo! Raina!
Yara: Baƙon duniya
Gindi: Zahin rana bai tauye ka ba,
:Sabon Goje Isa Mai Kware
Kukan
daɗi:
Wannan
shi ne kukan da masoya za su yi idan sun daɗe
ba a ga juna ba. Har an ɗebe zaton
a sake saduwa, sai aka haɗu. Irin
haka da an rungume juna sai kuka. A wasu lokuta, Hausawa na ce da shi
kukan-isa-barka, ko kukan murna. A nan, kukan da mata ke yi wa maza idan sun kaɗaita
yana shiga ciki in ji makaɗa Bawa Ɗan’anace:
Jagora: Sa ad duk mun ka taɓa
:Suna hwaɗin,
“Wai ni Allah!”
Gindi: Maza na tsoron karo da Ado ɗan
Garba
Kukan
sana’a
An
ce, a can da, ƙasar
Hausa akwai waɗanda sana’arsu
kawai idan aka yi wa wanda bai da ‘yan uwa da yawa mutuwa, su je su yi kuka a
biya su.[45]
Mutanen kukan ne sana’arsu, su bi unguwa su cika da kuka, dole kowa ya saki
abin da yake ya zo. Zama ɗaya a
tara jama’a irin na ‘yan gida masu ‘yan uwa da yawa.
Kukan
biki:
Yadda
duk mata ke adashin kuɗi haka
suka yin bukin kuka. Wadda duk ta yi rashi za a taru, a jajanta mata, a cika
gida da kuka, ta taso tana rabon ruwa da za a wanke fuska, tana ban haƙuri, tana gewayawa, ta ga yawan
masoya ‘yan biki. Idan aka ƙare,
tana kule da duk rawar da ‘yan biki suka taka. Idan abin kuka ya same su, za ta
je, ta yi wa kowa gwargwadon yadda aka yi mata. Ai shi ne Hausawa ke cewa,
gayyan wayyo! Wadda duk ta hau bori, idan ta samu rasuwa sai an hau mata bori.
Karin maganan da ke cewa, “Ba kukana ba, uwar kishiya ta mutu” hujja ce ta
tabbatar da samuwar ‘kukan biki’.
Kukan
ƙauna:
Ya
yi kama da kukan daɗi, amma
shi ga masoya kaɗai ya taƙaita musamman ma’aurata. Kukan ƙauna shi ne, kukan da amarya ke yi
idan aka rufe ta, za a kai gidan miji. Masana al’ada wasu na ganin kukan na
nuna ƙauna ga
iyaye ne da abokai cewa, za a rabu da su. Wasu na ganin, ai kukan na nuna ƙauna ne ga mijin na irin abubuwan
da ya ɓatar gabanin a
kai ta gidansa. Wani makaɗin biki
Abdu Ɗangishirin
Kiɗi[46]
yana da wannan fahintar a waƙarsa
ta biki da yake cewa:
Jagora: Munahukan duniya mata
:A
kai ku aure kuna kuka
:Ku
samu ɗan ɗa
kuna tawai
Ke
nan, aure ne da miji, da ribar da za a samu a auren ake yi wa kuka. Aƙilu Aliyu ya yi irin wannan kuka ga
Alhazzai ya nuna ƙaunarsa
gare su da burin/ fatar zuwa aikin Haji. A waƙar “Aikin Haji ya Wuce Wasa” yana kukan ƙauna kamar haka:
Hajiya
da Alhaji mumini,
Ki
tuna da ni ka tuna da ni,
Jirginku
ne da yake ɗirin!
Tashinsa
ya rikitar da ni,
Wayyo! Ina ma dai da ni?
Kukan
ibada:
Wannan
shi ne kukan da ya keɓanta ga
addini. Mujaddadi Ɗanfodiyo
ya faɗa cewa, a daina dukan yara idan
suna kuka lokacin kaciya, domin kukan nasu ibada ne akwai lada sosai.[47]
Haka ma, kukan da malamai masu wa’azi ɗan
turmi ke sa musu sauraro ibada ne gare su. Idan an kai ga ayoyin da suka ce a
yi kuka da yawa,[48]
sukan tsaya su daina wa’azi, su ce, “Kowa ya yi kuka sai ya gaji”, sannan a ci
gaba da karatu. Malamin shi zai fara ɓarkewa
da kuka, kuma shi zai fara dainawa. Haka kuma, ingantattun nassoshi sun zo da
wuraren da Manzo (SAW) ya yi kuka.[49]
Haka kuma, sahihin nassi ya tabbatar da wanda ya tuna gamonsa da Allah shi kaɗai
ya zubar da hawaye, Allah zai share masa hawayensa.[50]
Idan kuka ya tabbata a kan nassi ya zama na ibada. An ce, a wata shekara,
Sheikh Abdurrahman Sudaisi na jagorantar sallar Isha’i a Harami nassoshin da
yake ja suka sa shi kuka. Wani Bafulatani da aka gama ya tambayi wani mutum da
ke kusa da shi a sahu ya ce:
Me
ya samu modibbo na kuka haka? Ko sun kai ga kwagirinsa ne? Mutumin ya ce, “A’a
ba haka ba ne.” Ya sake tambaya, “Ko an yi masa mutuwa ne?” Mutumin ya ce: “Ba
mutuwa aka yi masa ba.” Ɗanfulani
ya ce: “To, mene ne dalilin kukansa?” Mutumin ya ce: “Tsoron Allah kawai ne ya
ratsi zuciyarsa.” Ɗanfulani
ya ce; “Assa! Ni kan ba ni son irin wonga imani.”
A wajen Sudaisi,
kukan na ibada ne. A wajen Ɗanfulani
yana ganin akwai kukan rashi idan aka sace wa mutum guzurinsa. Haka kuma, akwai
kukan mutuwa. Ɗanfulani
ya ambaci waɗanda ya sani, da
aka wuce saninsa ya roƙi
Allah tsari da shi faɗa cikin
kukan ibada.
Kukan
mafarki:
Duk wani abin da
gaɓɓai ke iya aikatawa a farke, ana iya
aikata su a mafarki. Ba abin mamaki ba ne, a ga yaro yana mafarkin kuka, kuma
yana kukan, alhali ga shi a kan gado yana bacci. Hatta da manya wani lokaci
takan rutsa da su irin haka. A duk ire-iren waɗannan
halin za a ce, mafarkin kuka aka yi, kuma kukan sunansa “Kukan mafarki”. Ina
ganin irin wannan kukan ne Buzu ya yi lokacin da wasu ƙwararrun ɓarayi
suka sace masa dukiya yana barci. Suka yi masa shaƙen abin da zai sa ya yi barci mai
nauyi. Yana cikin barcin suka aske masa kansa. Da ya farka, ya lalubi jaka ba
komai an sace. Ya ɗora hannu a kai
zai rara kuka da ƙwala
ihu! Da ya ji kan ba gashi, sai ya ce: “Mts! Ba ni ne ba, mafarki ne, bari in
bari.” Ya yi haka har sau uku, ya kwanta ya ci gaba da barcinsa, sai da ya gaji
da barci ya farka ya lalabi alaikum ya yi kukan gaskiya.
Kukan
ƙarya:
Abin da duk ake
yi na gaskiya ana samun na ƙarya
a ciki. Hausawa na cewa, irin kukan da karuwai ke yi wa ƙattansu na banza, idan za a yi
tafiya na ƙarya
ne. Haka ma, kukan da bazaura ke yi wa maneminta idan ana taɗi
na ƙarya ne.
Sani Ɗanbolɗo[51]
ya tabbatar da wannan a waƙarsa
ta ‘Zaura’, yana cewa:
Jagora: Haw wani kuka taka ƙaƙa ma na kunya
:Tana cewa, wai inna tana
cewa: “Ihm!”
Ki yi aure nan ni ga
danginki, “Ihm!”
Duk kukka da za
a yi don a kuɓuta daga tarkon
wani, ko a sa zuciyar wani ta karaya a kai ga abin da ake so, da mai yi, da
wanda ake yi wa duk sun san kukan ƙarya ne.[52]
Sakamakon
nazari:
Kuka
abu ne da kowace al’umma na da shi, kuma dalilin yin sa, da yadda ake yin sa,
ya kusan ya zama iri ɗaya.
Bahaushe ya kasa kuka zuwa gida biyu: na tsuntsaye da dabbobi, da kuma ba bil
Adam. Haka kuma, na bil Adam ma an fuskanci lafuzan da ake amfani da su wajen
kuka Hausantacce. Da Bahaushe ya ji shi, zai iya rarrabe shi da sauran na harsuna.
Idan dai wannan ita ce muƙala
ta farko da ta taɓi al’amarin kuka
a Hausance, za mu iya cewa, an ɗan rage
zango in ji mai zuwa sama ya taki fai-fai. Haka kuma, a ko’ina za a ba da
ma’anar kuka za a kula da yanayi, da ɓacin
rayuwa, mai sa hawaye, da nishi, da irin halin da zuciyar mai kuka take ciki
gabanin kuka ya riske ta, ko ta riski abin kuka. Ta haka za a fassara ma’anar
kukan da mai kuka ke kokewa.
A
al’adar Bahaushe, idan kuka ya haɗa
da faɗuwa ƙasa, a yi birgima irin na jaki, nan ne
bori ke shiga. Idan kukan zuban hawaye ne kawai yana shiga cikin kowanne daga
cikin rabe-raben goma sha biyu da muka ƙididdige. A wajen Hausawa, kuka na da
fa’idoji da yawa musamman na wartsake zuciya idan ta gunɗe,
ka da ƙuncin
da take ciki ya haifar da makanta ko mutuwa.[53]
Haka kuma, a wajen yara, masana al’ada sun ce, yana ƙara buɗe
wa yara basira. Idan aka tsura wa rabe-raben kuka idon nazari, za a ga mata su
ke limancin al’amarin kuka a ƙasar
Hausa.[54]
Wannan ne dalilin wasu masana al’ada suka ce, mata sun fi maza tsawon rayuwa.[55] A
ɓangaren dabbobi da tsuntsaye, kuka
harshen sadarwa ne tsakaninsu, kuma Bahaushe na rarrabe shi ta fuskar ba
kowannensu sunan da fassarar da al’ada ke yi masa.[56]
Kuka aiki ne na musamman da ba ya haɗuwa
da wani aiki in ba gudu ba.[57]
Ga alama, mai kuka ba sai ya fita hayyacinsa ko hankalinsa ba. Da yawa, ana
cikin kuka wani abu kan bijiro a aje a fuskance shi, musamman idan zai haifar
da sabon kuka ga mai kukan ko ga jama’a.
Naɗewa:
Kuka
wani aiki ne da ya shagaltar da, baki, da idanu, da tunanin mai yin sa. Don
haka ba ya haɗuwa da duk wani
aikin da ake son taimakon waɗannan
abubuwa uku. Idan dariya ta shiga cikin kuka, za ta rinjayi kukan, sai kukan ya
koma dariya. Don haka ne yara ke yi wa mai kuka da dariya waƙa.[58]
Idan magana ta bajiro ana kuka, dole a dakatar da kukan. Idan aka ci gaba da
kuka ana magana, kukan ya zama wasa ko wani abu ya shiga ga hankalin mai kukan.[59]
Kuka wata babbar taska ce da masana al’ada da adabi da harshe ke adana
abubuwan da suke sarrafawa su amfani mutane da su. Kuka da hawaye gama gari ne
ga dukkanin halittu musamman bil Adam.[60]
Kuka na ɗaukaka murya da
sauti mutane da dabbobi da tsuntsaye sun yi tarayya da shi. Duk da haka,
Bahaushen kuka ana rarrabe shi ta fuskar, sunansa, da muryarsa, da lafazinsa wani
lokaci da mafarinsa. A gaskiya, babu wani sashe daga cikin sassan nazarin
adabin Hausa da bai bayar da gudummuwarsa ga al’amarin kuka ba. Idan haka ne
kuwa, ya kyautu a ce, an keɓe wa kuka
wani ɓangare daga cikin ɓangarorin
nazarin al’ada da za a riƙa
kulawa da su ga masu nazarin Hausa. Wannan shi ne, muradina na yi wannan ɗan
bincike a kan kuka.
MANAZARTA
Balarabe,
M. M. 2004: “Rayuwar Marigayi Muhammadu Amali Sububu da Waƙoƙinsa”, kundin
digirin BA, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bargery,
G. P. 1934: A Hausa-Englishi Dictionary
and English-Hausa Ɓocabulary. Zaria: ABU Press.
Birniwa,
H. A. 1987: “Conserɓatism
and Dissent: A Comparatiɓe Study
of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Ɓerse
from ca 1946 to 1863”, PhD thesis, Uniɓersity
of Sokoto.
Bunza,
A. M. 2006: Yaƙi da
Rashin Tarbiya Cin Hanci Da Karɓar Rashawa, Cikin Waƙoƙin
Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace. Lagos: IBRASH, Publishers.
Bunza,
A. M. 2009: Narambaɗa. Wallafar Lagos:
IBRASH, Publishers.
Bunza,
A. M. 2012: “Lalurar Kiɗa a Bakin Makaɗa” muƙala, Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza,
A. M. 2012: “In ba ka San Gari ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafasasshen
Gambo”, kammalallen bincike ba a wallafa ba.
Bunza,
A. M. 2012: “Kura a Ma’aunin Adabin Hausa.” Muƙalar, Katsina:
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.
CSNL,
BUK. 2006: Ƙamusun Hausa.
1996: The New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of
the English Language.
Deluɗe Encyclopedic
Edition.
Ɗanfodiyo, S. U. (n.d) Wasiƙatul Ikhwaani. Bugun Sakkwato
Ɗanfodiyo, S. U. (n.d) Bayanil Bidi’is Shaiɗaniyya. Bugun Sakkwato
Ɗanfodiyo, S. U. (n.d) Ihyaa’us Sunna wa Ikhma’lil Bidi’a. Bugun Sakkwato
Ɗangambo, A. 2007: Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kaduna: Amana
Publishers.
Furniss,
G. 1996: Poetry, Prose and Popular
Culture in Hausa. Edingburgh: Uniɓersity Press.
Gusau,
S. M. 2008: Waƙoƙin
Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Benchmark
Publishers, Kano.
Imam,
A. 1933: Ruwan Bagaja. Zariya: NNPC
Mahe,
A 1984: “Alhaji Ɗan’anace da Waƙoƙinsa”, kundin
digirin BA, Jami’ar Sakkwato.
Maiyama,
U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar Hausawa: Nazarin Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji
Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Muhammad,
D. 1977: “Indiɓidual Talent in
Hausa Poetic Tradition: A Case of Aƙilu and His Art”,
PhD, London: SOAS.
Nawawi,
Y. Z. (n.d.) Riyaadus Swalihiina.
Newman,
R, 2003: An English-Hausa Dictionary.
Longman.
NNPC,
Fasaha Aƙiliya. Zaria: NNPC
Paden,
J. N. 1986: Ahmadu Bello Sardauna of
Sokoto: Ɓalues and Leadership in Nigeria, Zaria: Huda-huda
Publishers.
Umar,
M. B. 1984: “Symbolism in Oral Peotry: A Study of Symbolical Indices of Social
Status in Hausa Court Songs.” MA thesis, Zaria: ABU
Usman,
B. B. 2008: “Hikimar Magabata: Nazarin Rayuwa da Waƙoƙin Alhaji Umaru
Nasarawa Wazirin Gwandu.” Kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Usman,
B. B. 2008: “Kiɗan Zari na Ta Da
Maƙera”,
muƙala,
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
Uthaimin,
M. S. (n.d.) Mishkilaatus Shabbaabi.
Yahaya,
D. H. 1991: “Alhaji Musa Ɗanƙwairo, Makaɗin Fada ko na
Jama’a?’ kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
[1] Farin ciki shi ne duk wani abu da
ke jawo wa mai shi amfani ko tunkuɗe masa cuta ko kare masa musiba. Baƙin ciki shi ne, akasin farin ciki.
Zuciyar kowace halitta tana tsakanin waɗannan abubuwa biyu.
[3] A ɓangarenmu
Hausa, ban ga wani aikin NCE ko BA ko MPhil ko MA ko PhD a kan kuka ba. Haka
kuma banga wani rubutaccen aikin da ya taɓo kukan Bahaushe ba.
[4] The
New International Webster’s Comprehensiɓe
Dictionary of the English Language,
Deluɗe Encyclopedic Edition 1996; cry,
cried, crying: To utter loudly or shout out eɗclaim.
To proclaim loudly and publically adɓertise loudly goods or serɓices. Archaic to beg or implore: I cry for mercy. To
affect (one) in some specified way by weeping: to cry oneself to sleep. To
speak, call or appeal loudly, shout, yell. To utter sounds of grief and
lamentation, weep, sob. To weep or shed tears inoudibly. To make characteristic
calls: said of animals. Page, 311.
[5] A dubi, Reɓ G.
P. Bergery, A Hausa English Dictionary
And English Hausa Ɓocabulary: crying, lamentation, a plait, the notes of a bird,
the cry of an animal, rumblings in the abdomen page, 632.
Jagora: Ke
kyafilfita ta baya ga tsuntsaye
:Sai ta yini kuka kana ta
koma gida
:Ta wanke shi da hannu
Gindi: Ginshiƙi ɗan Jeka
:Ni na sani da ɗai bai yi sake ba
:Na taho murna da Muhamman
na Rwahi
:Ya tabbata sarki
Tattatre da mutuntarwar da aka yi, an fito da
Bahaushen aiki na kuka aka ce: “Ta wanke shi da hannu”.
Jagora: Bawa duy yai jan idanu
:Nag ga yana taunan haƙora
:Nag ga hawaye na zuba mai
Riwayoyin na Gambo sukan sassaɓa
daga wani wuri zuwa wani wuri. A nan, mun ƙaru da cewa wasu lokuta akan tauni haƙora gabanin kuka in ba a samu taunan yatsu ba.
[8] A tsarin nazarin adabi ana ce da wannan dabarar salon
mutuntarwa. Don ƙarin
bayani a dubi, Dangambo, A. (1982) Gadon Feɗe
Waƙa, da Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa duk muƙalu ne a Jami’ar Bayero, Kano. A tsarin karin magana
akwai; Biyan buƙata ya fi
rai in ji ƙuda, Ana
shaggu ƙasa in ji
raƙumi da ya taki kunama, Shegen
ko motsi ba a yi? Kunama da ta harbi kasko. Ga sun an dai.
[9] Liman Aliyu Isa shi ne limamin garin Isa a zamanin
mulkin Sarkin Gobir Amadu, wanda Makaɗa
Narambaɗa ya yi wa waƙoƙi da yawa. Ya yi masa bakandamiya mai take: Gwarzon Shamaki na Malam
Toron Giwa, Baban Dodo ba a Tamma da Batun Banza. Wannan bakandamiyar Liman
Aliyu Isa ya sauya zuwa begen Annabi Muhammadu (SAW) ya yi mata take:
Daɗa na ƙare lawwali
Bari in yo sani.
Waƙarsa ta
“Tuna mutuwa” ita ce “Lawwali” ta begen Annabi (SAW) ita ce “Saani” wato ta
biyu. Don ƙarin
bayani a dubi Bunza, A.M (1985) “Tasirin muulunci cikin Rubutattun waƙoƙin Hausa”, kundin digirin BA da Bunza, A. M. (2009) Narambaɗa, IBRASH, Lagos.
[10] An haifi Ibrahim Maidangwale Narambaɗa a cikin garin Tubali, ƙaramar Hukumar Shinkafi, don samun cikakken tarihinsa
a dubi, Al- Hassan, Bello Sodangi Yaro (1979) “Narambaɗa da Waƙoƙinsa,” kundin digirin BA, ABU, Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa (Yanaye-yanayesu da
Sigoginsu) Benchmark Publishers.
[11] Malam Muhamadu Sambo Wali, shahararren sha’iri ne a
Sakkwato, don samun cikakken bayanin rayuwarsa a dubi, Sanka Attahir Umar
(1983) “Alhaji Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa da Waƙoƙinsa,” kundin digirin BA, Jami’ar Sakkwato da Bunza, A.M. (2006) Yaƙi da Rashin Tarbiya Cin Hanci da Karɓar Rashawa, cikin Waƙoƙin Alhaji
Muhammadu Sambo Wali Basakkwace,
IBRASH, Lagos.
[12] Bala Ganɗo
Ambursa na daga cikin matasan mawaƙa masu azanci. Ya yi waƙoƙi masu sauraruwa da yawa, ya yi waƙar ɓannan ruwa da
waƙar shaye-shaye “A sha ruwa” da
waƙar mai shari’a Ambursa da waƙar “Ba a Gane Manya sai Ci ya Samu” da dai sauransu.
Ina godiya ga Malam Umaru Aliyu Bunza, na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Sakkwato, wanda ya fara sada ni da waƙoƙin Bala Ganɗo mai buga turaye.
[13] Malam Bala Mai Gumbe fitaccen fasihi ne garin Bunza,
ya yi waƙoƙin masu sauraruwa da yawa. Haziƙi ne na ƙarshe kuma kafinta ne mai azanci yana da tsayi da zati
sosai, baƙi ne mai
auki sosai. A lokacinsa ba a samu namijin da ya fi shi zati da tsayi da cika
irin na mazaje ba. A halin da nake wannan nazari yana raye. Haifaffen Bunza ne,
sunan unguwarsu Kwadarko.
[15] Wasu su ce da ita, agwagawa saboda kukan da take yi
na gwa-gwa-gwa! Wasu su ce, ƙwa-ƙwa-ƙwa! A wani ɓangare
na Gwandu ana ce mata “kuti”.
[16] Wai abin da ya sa take ƙyaci ƙt! Takaicin ba ta da wurin kwana ne. Don haka, a damina idan an yi ruwa
ta kama ƙyaci ƙt! Wai in ji Bahaushe, cewa take yi: “Gobe ɗaki zan gina ƙt!”
[17] Jama’atu Nasril Islam ta taɓa fassara shi zuwa Hausa ɗauke da sunan Malam Modibbo ( ) Dr. Mansur Ibrahim na
Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ya yi masa sharhi mai suna:
[18] Wazirin Sakkwato Alhaji Junaidu an ce, ya taɓa nuna shakku ga kasancewar littafin Mujaddadi Ɗanfodiyo. Duk dai yadda ya kasance kusan ƙunshiyarsa ɗaya
da Nurul Albabi da Tamyilzul Ahlil Sunna da sauran
littaffan Mujaddadi da irin tauhidin da suka ƙunsa. A faɗarsa,
wai, wani Shehu Usmanu Bahaushe ya rubuta shi. To! Duk dai yadda yake, tsarin
hukunce-hukuncen da ke ciki daidai suke da irin aƙida da tauhidin Shehu Usmanu Bafulatani. In har
hasashen ya tabbata, kasancewarsu daga mabanbantan harsuna bai cuta wa imaninsu
ba.
[19] Yana daga cikin ayyukan Mujaddadi da suka yi suna.
Masana irin su, Last, da M. M Khani da Bologun da Biɓar sun ambace shi.
[20] Maidaji Sabon Birni makaɗin fadar Sabon Birni ne, don ƙarin bayani a dubi Gusau, S. M. da aka ambata a lamba
ta (8).
[21] Ai shi ya sa muke da karin maganam ‘Kukan kurciya
jawabi ne.’ Da yawa mawaƙan Hausa
na ambaton kurciya a matsayin abokin hirarsu. A waƙar Mamman Gawo Filinge da Sa’idu Faru da makaɗa Ɗanba’u sun ruwaito haka a waƙoƙinsu.
[22] Waɗannan
fassare-fassare ne Mujaddadi Ɗanfodiyo ya zarga a cikin littafinsa Nurul Albabi da Siraajul
Ikhwani. Ya nuna yin su bokanci ne, bokanci kuwa kishiyar gaskiya ne.
[23] Ƙwararrun bokayen ƙasar Hausa
na fassara haniniyar doki. Ga al’ada dawaki daga gidan sarauta sai mawadata ke
iya kiyonsu. Haka kuma, dabba ce mai shu’umci a kan sha’anin Iskoki. An ce,
wata rana dokin wani sarki cikin ƙasar Kabi, a garin Dukushi ya yi haniniya, sai wani doki
na basaraken ƙasar
Gwandu ya karɓa masa. An yi daidai wani boka na wurin sai ya ce:
Doki ɗaya cewa ya yi: ‘cikin daɗi ya tashi, cikin daɗi zai ƙare.’ Ɗaya kuwa cewa ya yi: ‘Cikin daɗi ya tashi cikin wuya yake ƙarewa.’ Haka ko aka yi, domin sarkin mai doki na farko
a kan gadon sarauta ya mutu, ɗaya kuwa tuɓe shi aka yi. Hira da wani Ɗangaladima makusancin su, wajajen shekarar 1975.
[24] Yadda Bahaushe ke raba dare shi ne, kukan kaza na
farko da kukan kaza na biyu. Da an ji na biyu ana tunkarar ketowar alfijiri.
[25] A wani lokacin a ce; sai dai ya ce: ‘Ku sa ruwa don
Allah!’ Danƙari! An
riga an gama kuka baba.
[26] Cikakken sunansa Muhamamdu Bawa Ɗan’anace ‘Yartsakuwa a ƙarƙashin riƙon Gandi
jihar Sakkwato. Asali makaɗin noma ne da
baya ya koma kiɗan dambe. Ya yi waƙoƙin noma da dambe da yawa masu sauraruwa. Waƙar da ya yi wa Shagon Mafara ita ta fi fice. Don ƙarin bayanin rayuwarsa da waƙoƙinsa a dubi Mahe, Abubakar (1984) ‘Alhaji Ɗan’anace da Waƙoƙinsa’, kundin digirin BA, Jami’ar Sakkwato.
[27] Cikakken sunansa Alhaji Muhammadu Gambo Fagada Babba
ta ƙaramar Hukumar Maiyama. Don ƙarin bayanin rayuwarsa da waƙoƙinsa a dubi, Maiyama, U. H. (2008) ‘Sata a Zamantakewar Hausawa:
Nazarin Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhamamdu Gambo Fagada’, kundin digirin PhD, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato, da Bunza, A. M. (2012) In Ba Ka
San Gari ba Saurari Daka: Muryar Nazari cikin Tafashen Gambo, kammalallen
bincike, ba a wallafa ba.
[28] Nazaƙi fitaccen ɓarawo ne a Sakkwato, saboda shahararsa aka naɗa shi sarkin ɓarayi
amma a bayan fage can cikin abokan aikinsa. Ya tuba ya rasu 1999, yana aiki a
kasuwar Sakkwato, da baya ya koma aikin SUDA, Sokoto.
[29] Muhammadu Shago mutumin ‘Yarkahoji ne ta yamma ga
garin Rini, shi ne zakaran makaɗa Ɗan’anace. Ya tuba da dambe a garin Tambuwal. Ya kama
sana’ar dillancin dabbobi har ƙashen rayuwarsa.
[30] Jantullu gunduma ce daga cikin gundumomin Argungu.
Arawa ke sarautar garin. Arawa asalinsu, suna da dangantaka da Larabawan asali
da Kanuri (Barebari). Su suka ci Dandin Mahe yaƙi.
[31] Dandin Mahe sarautarsu ita ce Dikko, kuma ƙarƙashin gundumar Sakkwato suke. An ce, Dikkon Dandin Mahe a yaƙin Jantullu aka kashe shi.
[32] Garba Ɗanwasa Mutumin garin Gumi ne, ya yi fice a waƙoƙin tauri cikin taurarinsa akwai Ɗankurjan da Mamman Dogo da Bala Ƙonanne. Gabanin ya rasu, ya dangane kiɗa ya tuba. Yanzu yaronsa ya ɗauki turaye yana bitar waƙoƙin uban.
[33] Sheikh Nasiru Kabara fitaccen Shehin Masani ne a ƙasar Hausa. Shi ne shugaban ɗarikun Sufayen Ƙadiriyya a Afirka ta Yamma. Ya yi rubuce-rubuce da
yawa cikin Larabci da Hausa. Daga cikin almajiransa akwai Sheikh Abubakar
Mahmud Gumi. Ya wallafa Tarjamar
Ma’anonin Alƙur’ani da
Hausa. wanda ƙasar Libya suka wallafa.
[34] Aƙilu Aliyu asali mutumen Jega ne, an haife shi a Birnin Ƙaurar Laila (unguwa ce a Jega). Zakara ne a waƙoƙin NEPU, ya yi koyarwa a Kano da Maiduguri. An wallafa manyan ayyuka
biyu na ayyukansa, na farko Muhammad, D. (1979) ‘Indiɓidual Talent in Hausa Poetic Tradition: A Study of Aƙilu’s Art, PhD thesis, London da NNPC, Fasaha Aƙiliya. Ya yi
wannan waƙa lokacin
da Kiyari ya buge shi da mota a Maiduguri.
[35] Amali Subugu, makaɗin
noma ne a ƙasar
Zamfara. Ya yi waƙoƙi da yawa masu sauraruwa. Akwai waƙar Aikau, da waƙar Isa Mai Kware.
[36] Malam Bello Bala Usman ya fara fito da ayyukan Namata
mai zari a sarari: Usman, B. B. 2008: Kiɗan
Zari na Ta Da Maƙera, muƙala, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
[38] Yanzu al’adar kukan mutuwa ta ragu ko da a ƙauyukan da al’adu suka yi wa kanta. Tabbas! Tasirin
bazuwar Musulunci ne ya haifar da haka.
[39]Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ‘yan ta’addan
Kiristocin soja suka kashe shi a juyin mulkin shekarar 1966 ƙarƙashin jagorancin Nzegu. Don ƙarin bayani a dubi Paden, J. 1986, Sir Ahmadu Bello Sardauna of Sokoto,
Zariya: Huda-huda Publishers.
[41] Don samun cikakken bayaninsa a dubi, Usman B. B.
(2008) “Hikimar Magabata: Nazarin Rayuwa da Waƙoƙin Alhaji Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu da Waƙoƙinsa.” Kundin digirin PhD, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
[42] Asali mawaƙin PRP ne ya koma NPN yana waƙoƙin siyasa masu amshi. Don samun cikakken bayani a dubi, Birniwa, H. A.
(1987) “Conserɓatism and Dissent: A Comparatiɓe Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Ɓerse from ca 1946 to 1863”, PhD thesis, Uniɓersity of Sokoto.
[43] An yi wannan bayanin sosai a wata jaridar Aminiya ta
watan 8 ko 9 shekara 2012. Na karanta shi, na manta da kwanan watan jaridar haƙiƙa.
[44] Ba fitaccen mawaƙi ba ne a ƙasar Hausa. Ya yi rayuwarsa garuruwan Sakkwato
musamman ƙasar Gada.
Fitacciyar waƙarsa ita
ce, ‘Wanakiri Dodon Kwanya.’
[45] Ina godiya musamman ga Dr. Muhammadu Aminu Mode na Sashen
Harsunan Turai na Zamani da Ilimin Harsuna, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Shi ya ba ni wannan bayani na
tarar da gaskiyarsa a Bayanil Bidi’is
Shaiɗaniyya na Mujaddadi Ɗanfodiyo.
[46] Abdullahi Ɗangishirin Kiɗi
ya gaji mahaifinsa Dogo Sarkin Kiɗin
Bunza. Yana daga cikin makaɗan marigayi
Walga mai Waƙa Bunza (
Walga Maituru ya rasu a Satumba 2012), kuma Walga ya sa masa sunan Ɗangishirin Kiɗi.
Abdullahi dogo ne, mai doguwar fuska, mai sake fuska da ba’a da son mutane.
Yana raye yanzu haka da nake gudanar da wannan bincike.
[48] A dubi Suratul Tauba,
sura ta 9 aya ta 82.
[49] A dubi littafin Imam Nawawi, Riyaadhus Swaalihiina.
[50] Nassin hadisi ya ambaci haka. A dubi littafin Mushkilaatus Shababi. na Ibn Uthaimin.
[51] Sani Ɗanbolɗo mutumin Warama ne bakin ruwa can ƙasar Nasarawa Bulƙullu cikin ƙasar Zamfara. Asalinsa makaɗin cin tama ne na maƙera da noma. Ya yi waƙoƙi da yawa daga cikinsu akwai Waƙar Zaura, Ciran Rogo, Rage Sata Tsohuwa, Karen Teburi,
Sarkin Fawan Bakura, Waƙar CG,
Zambo ga Gero Zartu da dai sauransu.
[52] Duk kukan da ba a gina shi a kan gadon feɗe kuka goma sha ɗaya
ba, to yana cikin na goma sha biyu.
[53] Hausawa sun tabbar da sunu na sa a mutu, a dubi Ruwan Bagaja. na Abubakar Imam a kan
mutuwar mahaifin Saƙimu. Haka
suna sa a makanta. Haka ya auku ga Annabi Yakuba a kan ɓacewar da Yusuf ya yi, a dubi Suratul Yusuf sura ta 11 aya ta 86.
[54] Jerin rabe-raben kuka goma sha biyu, kowane za a ga
mata sun fi yawa a ciki. Haka abin yake a duniyar baƙar fata, a zaman makoki, mata ke jagoranci ‘yan
koke-koken da ake na al’ada.
[55] Wai a fassararsu saboda yawan kukan da mata ke yi ba
su da ƙunci a
rayuwarsu da yawa, saboda haka sunu ba ya cin su kai tsaye kamar yadda yake yi
wa maza cin kwaɗai.
[56] A dabbobi da tsuntsunye akwai kukan daɗi da magana da kukan mutuwa da kukan tsoro da kukan ƙauna da kukan ceto, sauran nau’o’in shida ne ban
tabbatar ba.
[57] Hausawa na cewa ba a haɗa gudu da susar baya domin da hannu da baya ne ke gudu don haka ba za
su yi aiki biyu a zama ɗaya ba. Haka kuma yake, ana iya gudu ana kuka, amma
babu wani aiki da za a iya haɗawa da kukan
gaskiya. Don da an haɗa su, kuka ya lalace. Sai wani jiƙo.
[59] Wata rana wani yaro ɗan maƙwabcina
mai suna ‘Nura’ yana kuka yayansa yana matsa masa da kira. Da ya ga yayan ya
san kuka yake yi, kuma ya matsa da kiransa, sai ya ce wa yayan: “Halama ba ka
da hankali? Ba ka ga kuka nake ba?”
[60] An ce shamuwa idan tana kuka tana fitar da hawaye. Ni
na ga haka, da wasu magabatanmu suka kama ta. Haka kuma, jaki idan yana shan
labun rake hawaye na zubo masa saboda tsananin daɗin da yake ji.
No comments:
Post a Comment