Gajeren tunanin da ke ga ɗan Adam shi ya sa
Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan,
mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya saɓa mata. Wannan dalili ne
ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke yi, a koyaushe
gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a
nan shi ne , ƙoƙarin dangantawa wata al’umma da ke
wata nahiya mai riƙe
da wani addini alhakin ringingimun da ke wakana a duniyar zamaninsu. Yau, babu,
ɓata
gari sai Musulmi. Babu ɗan
ta’adda sai Musulmi. Bab...
Wane Ne Ɗan
Ta’adda?
Aliyu
Muhammadu Bunza
Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato
Waya:
08034316508
Takardar
da aka gabatar a matsayin babban baƙo
mai jawabi a taro na musamman na haɗaɗɗiyar Ƙungiyar
Musulmi MSSN, NACOMYO, FOMWAN, MSO, IMAN, WOMEN IN DA’AWA da MCAN, na Jahar
Sakkwato. Ranar Litinin 14th Rabi’ul Awwal 1433 A.H. daidai da
6-2-2012 a babban ɗakin
taro na FOMWAN, Sakkwato ƙarƙashin Jagorancin Mal. Muhammadu Bello
Ɗanmallam Shugaban Jama’atul Muslimin,
Sakkwato.
GABATARWA:
Gajeren
tunanin da ke ga ɗan
Adam shi ya sa Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan,
mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya saɓa mata. Wannan dalili ne
ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke yi, a koyaushe
gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a
nan shi ne , ƙoƙarin dangantawa wata al’umma da ke
wata nahiya mai riƙe
da wani addini alhakin ringingimun da ke wakana a duniyar zamaninsu. Yau, babu,
ɓata
gari sai Musulmi. Babu ɗan
ta’adda sai Musulmi. Babu ɗan
ra’ayin riƙau sai Musulmi,
don haka, a ƙasar nan sai
Musulmi suka kasance marayu a kundin tsarin mulkin ƙasar da suka rinjayi kowane addini da
ke cikinta. A kan haka nake son in ɗan ce wani abu a kan, wane ne ɗan ta’adda?
TA’ADDANCI:
Ta’addanci
kalmar Larabci ce mai nufin shisshigi, da wuce gona da iri, da kece wa doka
bante ta fuskar tsumbula cikin hane-hanenta a yi kane-kane ba tare da nuna wata
damuwa ba. A fassarar ƙasashen
Turai, ta keɓanta
ta’addanci ga Musulmi masu ƙwazon
neman haƙƙinsu da aka haramta musu,
ko masu kare kansu da irin makaman da ake kai musu hari, ko masu ƙoƙarin
tabbatar da dokokin addininsu a mu’amalolinsu. Idan wasu da ba Musulmi ba suka ɗauki wannan mataki, akan
yi musu suna ‘yan gwagwarmaya ko ‘yan neman ‘yanci ko marasa rinajaye ko abokan
hamayya ko ‘yan sari-ka-noƙe.
Cikin dabara da yaudara, yau, a kafafen yaɗa labarai na cikin ƙasa da na waje duk da irin waɗannan fassarori suke
amfani na shafa wa Musulmi da Musulunci kashin kaji.
Da
za a tambayi wanda aka laƙaba
wa suna “ɗan
ta’adda” mene ne “ta’addanci”? Ba zai saɓa wa fassarar da addini ko harshe ya
tanada ba. Idan aka tambaye shi aikin da yake yi, ko ya san ta’addanci ne? Ba
zai yarda ba. Dalili kuwa shi ne, shi, yana ƙoƙarin kare kansa ne ga irin farmakin
da ake kai masa, ko yana ƙoƙarin ramuwar gayya ne ga ta’addancin
da aka yi masa da sunan tsaro ko neman zaman lafiya. Don haka, a ganinsa wanda
ya kai masa farmaki shi ne “adda” shi da ke kariya shi ne “ɗanta” don haka wane ne ɗan ta’adda?
Ga
dukkanin alamu, ana amfani da kalmar ne a yau domin a ɗebe tausayin waɗansu mutane da ake son a
halaka ga zukatan jama’a. Ana amfani da kalmar ga mutanen da suka ƙi miƙa
wuya borin Turawa ya hau kansu. Ana liƙa
kalmar ga jama’ar da ke ganin kasawar Demokraɗiyya ga kare haƙƙin ɗan Adam. Ana danna ta ga
waɗanda
ke ganin rashin ingancin dokar ta yi takin saƙa
da dokokin Allah (SWT). Ana sarkafa ta ga mutanen da suka ƙi kafirce wa al’adunsu don na wasu.
Ana kururuwa da kalmar ga masu ra’ayin cewa, dokokin Allah ba su tsufa. Ana
tabbatar da kalmar ga wanda ya yi ramuwar gayya da hushi. Ana sarrafa kalmar ga
wanda ke ganin in an ɗebi
na dahuwa yana iya ɗibar
na gashi ga ban maƙiyansa.
Ana taliyon kalmar ga waɗanda
ke ganin cewa, da wulaƙanci
gara shahada. A wasu lokuta, an fi saka ta ga waɗanda suka ƙi yarda a yi musu dodorido da makamai
a tarwatsa musu fahinta.
Idan
muka sa idon natsuwa sosai muka duba, za mu ga cewa, a duniyarmu ta yau za mu
ga akwai:
i.
‘Yan
fafitikar neman ‘yancin kai daga duniyar Turawa da mamayarsu irin su Nelson Mandela
da ya yi kusan share rabin ƙarni
a gidan Yari, da mutanen Namibiya, da Zimbabuwe, amma ba a yi masu suna da
ta’addaci ba.
ii.
Masu
fito na fito da gwamnatin da ke ci a ƙasarsu.
Cikin fafitakarsu sun kashe talakawa da sarakuna da waƙilan hukuma irinsu Saro Wiwa na ƙabilar Igonni, amma ba a kira shi da
sunan ba.
iii.
Akwai
‘yan gani-kashenin siyasa da suka kai fagen kashe talakawa da masu mulki. A ƙasar nan, an sami waɗanda suka kashe Ministan
Shari’a bisa ga irin aƙidarsu
ta siyasa ba a kira su da sunan ba.
iɓ.
Muna
da ‘yan bangar kare gonakin gado da suka fito da sunan Samarin Nija Delta, sun
kashe ‘yan gida, sun kashe baƙi,
sun talauta ƙasa, sun kashe
sojoji da ‘yan sanda bila adadin, amma sai tukuici aka yi musu da albashi mai
tsoka ga kowane ƙato marashi aikin yi aka kuma buɗe musu ma’aikata tasu ta
kansu, wai su ba ‘yan ta’adda ba ne! ‘Yan kare gundumarsu ta gado ne.
WANE
NE ƊAN TA’ADDA?
Masana addini sun aminta da tashin
duniya kuma nassoshi sun inganta a kan cewa, lallai ranar Jumu’a za a sallame
mu da aiki. Bincike ya nuna Jumu’ar ba ta da Assabar, sai dai sanin wace rana
ce? An ɓoye
muna. Duk da haka, daga cikin manyan-manyan alamominta akwai bayyanar
ta’addanci a doron ƙasa.
Fassarar ta’addanci a littattafan Shari’a yana banga-banga da fassarar Turawan
mulkin kama-karya da ‘yan barandansu ‘yan bokon ƙarshen
zamani. Mutanen da ke walawa da cin gajiyar ganimar duniya, da shan jinin moro,
da tursasa wa marasa galihu, da maƙure
mai ɗan
ƙarfi, suna ganin duk abin da ke hana
su miƙe ƙafafunsu,
su baje kolinsu shi ne “ta’addanci”. Ban ga laifinsu ba, domin ƙolin tunaninsu daga duniya sai Abuja.
Idan
ana biye da zaren tunanina, ta’addanci suna ne ƙirƙirarre na wannan ƙarni da ƙarya ke son ta yi garkuwa da shi ta
yaƙi gaskiya. Tantance ɗan ta’adda a irin
fassarar ‘yan bokon zamani yana da wuya saboda yaudarar da aka saka a ciki. Da
dai za a tsaya a kalli kalmar da irin yanayinta da za a yi mata fassarar adalci
a ce:
“Yin amfani da ƙarfi
domin a turmuje mai ɗan
ƙarfi, tare da bin kowace dabara ta
rashin tausayi da keta haƙƙin
bil Adam domin kai ga wata manufa da ake son a tilasta mutane su bi ta. Ɗan ta’adda shi ne, wanda ya fara
takara, ya yi amfani da makamansa domin ya kai ga manufarsa. Ɗan ta’adda ba ya buƙatar zaman lafiya matuƙar ba a tsarinsa ba, kuma duk wurin
da ya kafa tsarinsa da ta’addanci zai yi amfani ya rusa masu adawa da shi ya
kare waɗanda
suka bi.”
GANI
YA KORI JI:
Na ƙirƙiro wannan ma’anar ta’addanci bayan
na nazarci fassarorin da ‘yan boko ke ɗora ta’addaci a kai. A ganina, ba a iya
gane ɗan
ta’adda idan ba a bi silalen tarihi ba. A tsarin malaman usulu komai
yana kan hukuncinsa matuƙar
ba Shiri’a ta zo ta ɗora
masa wani hukunci ba. Don haka, ƙasashen
duniya duka lafiya lau suke zaune gabanin rigingimun ƙasashen yamma ya sunsune su. Tarihi
ya tabbatar da cewa, ƙasashen
Turai suka fara haihuwar ta’addanci suka rene shi, sai da ya zama samari
sadauki suka aike shi sauran ƙasashen
duniya don a san shi, ya san su. Wannan hasashen nawa, ana iya kallonsa da
tubarau na tarihin duniya kaɗan
daga ciki akwai:
i.
Yaƙe-yaƙen
da Turawan mulkin mallaka suka kai a ƙasashen
Larabawa da Asiyawa da Afirka. Yaƙe-yaƙe ne na mamayar mutane a tilasta su,
su bi dokar ƙasar da ba tasu
ba. Su bi addinin da ba nasu ba. Su yarda da shugabanci da ba nasu ba. Su
rungumi al’adun da ba nasu ba. Su rusa tsarin dokokinsu su bi waɗanda aka zo musu da ƙarfin soja, so da ƙi. Wanda ya miƙa wuya ya zama bawa, wanda ya ƙi ba da kai bori ya hau a kashe shi.
Wane ta’addanci ya fi wannan a tarihin bil Adam?
ii.
Mutanen
da aka kashe, da waɗanda
aka rataye, da waɗanda
aka ƙona, da waɗanda aka sa cikin sahu,
aka yi musu kisan takaici a ƙasar
Libiya zamanin mulkin mallaka wa zai iya ƙididdige
su? Haka aka yi wa Bagadaza sama ga Musulmi dubu ɗari biyu (200,000) aka kashe, aka ƙona litattafansu, wasu aka saka teku sai
da ruwanta ya gurɓace
halittun ciki suka mutu. Ƙasar
Najad da Masar da Sudan duk sun ɗanɗani irin wannan ƙasaƙanci.
Idan tarihi na da gurbi a bayanin ta’addanci, a fassarar ma’anar wannan, a ba
masu aikin sunan da ya dace da su mu ji. Ai in maye ya manta mai ɗa ba ya manta ba.
iii.
Mu
waiwayi haɗaɗɗiyar daular Tanganyika an
yi wa mata da yara da jinjirai da tsofaffi kisan kiyashi har sai da suka ari
hauka domin su kakkaɓe
wa tabarma kunya ƙura.
Turawan mulkin mallaka sun kashe su har sai da suka gaji suka ajiye makamai
domin su raga irin da za su taya su noma gonanki kakanninsu da iyayensu da aka
kashe. Shahararru daga cikin yaƙe-yaƙen akwai Maji-maji da Mawo-mawo. Haka
aka yi wa daulolin Bantu, aka karkashe ƙabilun
Zulu aka kashe musu shuwagabanni Mzilikazi da Musheshe da Zwagendaba. Tsananin
musibar bala’in kisan kai da ƙabilun
Zulu ba su taɓa
jin labari ba, balle su gani, shi ya sa suka kira zamanin Turawa Mfacane
ma’ana; “zamanin bala’i da waba’i”. Kaico! Wai duk an yi wannan da nufin wayar
da kan ƙauyawa in ji ‘yan mun waye.
iɓ.
Idan
muka waiwayi baya a nan cikin gida, laifin me daular Musulunci ta Sakkwato da
Mujaddadi Ɗanfodiyo ya assasa
ta yi? A yaƙin Giginya ba a
iya ƙididdige shahidai. Aka je Burmi, aka
yi kamar ba a yi wani abu a Giginya ba. Aka je Haɗeja aka yi kan mai uwa da wabi, fiye
da mutum dubu goma sha biyar suka yi shahada. Ba a bar Satirawa baya ba, a 1906
su dubu goma aka ƙona
cikin garinsu maza da mata yara da manya. Duk da tsananin wannan ta’asa, wai su
ne ‘yan ta’adda. Haka kuma, an ƙone
garin Raha da Bahindi da Kwantagora wai don a tauna tsakuwa a ba aya tsoro
kawai. To! Tsakanin mai abu da marashi da ya zo da makamin yin ƙwace, wane ne ɗan ta’adda? Idan aka samu
accakwama wa ya aikata ta’addanci?
Waɗannan musibu duka ba ‘yan
gida suka jawo su ba. Baƙin
haure da ke ganin, a ba manya fili ba don Allah ne ba. Wanda ya ƙi ba manya fili a ture shi ya faɗi a kashe, wanda ya ba da
fili a bautar da shi na har abada. Wai, waɗannan kashe-kashe da babu tarihin da zai
iya ƙididdige su an yi su ne da nufin
neman wurin zama, da baje kolin sana’a, da kafa mulkin kama karya, da yaɗa addinin Yahudu da
Nasara, da hana a ga tauraron kowa in ba nasu ba. A ganinka na ma’aboci hankali
da wayo, wane suna ya fi dacewa da waɗannan mutane? Wa ya fara ta da zaune tsaye
a duniyar bil Adam? Da wace hujja bunsuru zai hana wa akuya shan ƙasari?
NASON
MIYAR JIYA GA SABON AKUSHI
Ɗan tsakuren da muka yi muke son mu
daddage shi ga abubuwan da ke faruwa a duniyar ƙarninmu.
Ga al’ada, kazar da aka yanka idan ta tashi cikin ɗaukar rai ta fi ban tsoro
da firigirtawa da ban mamaki ga wanda ya yanka ta. Idan dai yana buƙatar cin namanta, idan ya kama ta ya
danne, zai yi mata dannan takaici. Idan ya ga babu makawa sai ya sake yanka,
zai yi mata yankan takaici sai ya raba kai da wuya. Irin haka ne yake faruwa a
wannan ƙarni namu. A da, Turawan mulkin
mallaka sun yi zaton sun gama da kowa. Don haka suka share wa jikokinsu wuri su
zo su ci karensu ba babbaka. Da baya suka hango an yanka ta tashi, don haka
jikokinsu na yau ke son su yi amfani da dabarun jiya domin su taushe kazar da
kakanninsu suka yanke shekaranjiya.
Takaicin
Yahudu da Nasara ga Musulmi na gado ne. Zama tare, da karatu tare, da
auratayya, da maƙwabtaka,
da boko, da demokraɗiyya,
da buɗe
ofisoshin jekadance, ba zai karkare shi ba. Bunƙasar
addinin Musulunci ke ba su tsoro. Yawaitar malamai ke tayar musu da hankali. Ɗaukakar ƙasar da Musulunci ke shugabanci wani
abin takaici ne a wajensu ko da kuwa bisa tsarinsu ya ɗora ƙasarsa. Yawaitar Musulmi a doron ƙasa ya fi gobarar gemu tashin hankali
a wajensu. Don haka, duk hasarar da za su yi ta ganin an magance waɗannan abubuwa dole a bi
ta, ba tare da ja da baya.
Na
tabbata za ku gaskata ni, idan kuka tuna da Musulmi sama da dubu ɗari biyu tare da
shugabansu Saddam Hussaini da aka kashe a ƙasar
Iraƙi. Wa zai iya ƙididdige Musulmin da aka kashe a
daular Musulunci ta Taliban, a ƙasar
Afganistan? Dubi yadda aka rugurguza Musulmai da dukiyoyinsa a ƙasar Libiya? Aka sake biyo Musulman
Egypt da baƙar yadiya don sun
ce, a sa shari’a a tsarinsu na yanzu. Syria na cikin hayaƙi, an yi jinga da wasu mataulata su
tayar da irin wannan fitinar a Saudi Arabia. Babu wata ƙasa da Musulmi za su yunƙuro da farfaɗo da addininsu face an yi
musu taron dangi na ƙarfin
soje an tarwatsa ƙasarsu,
ko sun miƙa wuya ba a bari
sai an ga baya ga shugabanninsu da malamansu da matansansu.
Abin
ban haushi, hatta a fegen tsaron mutuncin ɗan Adam ba a ba mutane sarari ba. Ghana ta
ƙi yarda da halasta kushili (luwaɗi) an jaye tallafin da
ake ba ta. Zimbabuwe ta hukunta ɗan liwaɗi da ɗaurin gidan Yari, mai laifin ya ɗaukaka ƙara wata ƙasa ba tasa ba, Amurka ta tilasta a
sake shi, kuma an sake shi tare da biyansa diyya, ba tare da an biya wanda ya
yi wa luwaɗi
diyya ba. Nijeriya ta ƙi
sa wa dokar halasta luwaɗi
da maɗigo
hannu an ce, ta gyara dokarta ko a ɗebe ta cikin ƙasashe amintattu. Hausawa na cewa,
sare-saren hauka zubar da yawu. Da jaye tallafi, sai a batse ƙasa, daga nan, sai a sa mata
takunkumi, daga nan, sai kai mata sojojin tsaro, daga tsaro, sai tsokana, daga
nan sai farmaki, don kare ra’ayin mutane ashirin a kashe mutum dubu ashirin.
Wane suna ya fi cancanta da wannan salon Yahudu da Nasara na mamayar duniyar ƙarni na ashirin da ɗaya?
NIJERIYA
INA AKA DOSA?
Ga
alama ba a yi ƙasar da ta fi ƙasarmu zaman lafiya ba a faɗin duniyar jiya, mun yi
suna ga kwnaciyar hankali, da lumana a nahiyar Afirka, yau abin na son ya sauya
zani. A tarihi, al’ummar da ta fara wanzar da zaman lafiya a wannan ƙasar ita ce Musulmar al’ummar da aka
riska da tsarin dokokinta na shari’a daidaitacciya. Ganin haka, Turawa suka ƙago muna mulkin “Shiga gaba in bi ka”
(Indirect rule). A Kudu, aka ƙaga
musu “Biyo ni a baya” (Direct rule). Dalilinsu a nan shi ne, sun tarar da
Musulmi da tsarin da ba za a iya cire shi a kawo wanda ya fi shi ba, don haka
dole a sa su gaba a bi su baya da baƙar
yadiya. A Kudu, an tarar da su kara zube, dole aka yi musu jagora. Yaƙar daular Musulunci ta Sakkwato da
aka yi da irin raddi mai gauni da suka sha a Sakkwato da Burmi da Haɗeja da Kwantagora da
Satiru ya sa suke son sai sun mayar da raddi ko da bayan shekara dubu ne. Hanya
mafi sauƙi a yau ita ce, a liƙa musu sunan ta’addanci a yaƙe su da shi, a kashe musu matasa da
malamai sabon mulkin mallaka ya sake bayyana a Arewa. Ba daga waje aka yaƙe mu ba daga cikinmu aka yaƙe mu.
ZUBI
DA TSARIN MUSULMIN NIJERIYA
Musulunci
da ya shigo Nijeriya ba da yaƙe-yaƙe ko tsangwama ya zo ba, balle a ce,
mun gaji abinmu. Wayewar Turai ta zo da faɗa, da yaƙi,
da bauta, da zanga-zanga, don haka, fitina da tashin hankali a ko’ina ka gan
shi baƙo ne cikin Musuluncin ɗan Nijeriya, ba a ba shi
masauki ba balle ya shimfiɗa
buzun zama.
A
tarihance, Mazhabar Malikiyya ta fara ziyararmu, aƙidar Shi’a ta shigo ba ta samu karɓuwa ba ta rushe. Daga nan
sai aƙidar Asha’ira ta biyo baya. Ƙadiryya ta zo, ba ta yawaita ƙwarai ba, Tijjaniyya ta zo ta karɓi tuta. Ana cikin wannan
fafitikar Shi’a ta sake hudo kai da sabon salon na Mahajuba da Echo
of Islam ana cikin wannan yanayi ƙungiyoyi
irinsu Izala da Jama’atu suka ƙasura.
Waɗannan
ƙungiyoyin suka haifar da samarin
Salafiyya masu ra’ayin ana iya yin tantagaryar addini irin wanda Manzo (SAW) ya
yi, ba tare da an yi taƙalidanci
da kowace mazhaba ko ɗariƙa ko ƙungiya
ba. A yau, daga cikin waɗannan
kashe-kashen wanda duk aka tsokana, aka hana masa ‘yancin addininsa, aka kashe
masa malamai ko iyali ko mabiya, idan ya yi yunƙurin
mayar da martani sai a sa masa sabon suna “Boko Haram”. Haɗarin da muke ciki shi ne,
matuƙar ana son ɗebe tausayinka a zukatan
Musulmin Nijeriya, a yi ma kisan gilla ko a yi ma ɗaurin rai-da-rai sai a ce
maka ɗan
“Boko Haram”. Shi ko wanda ba Musulmi ba da ya kai wa Masallatai da Coci hari,
wane suna za a ba shi?
SUNA
A FAGEN CIN ZARAFI
Idan ana son a gane a ina ta’addanci ya
fito? Sai an bi tarihin yadda ake raɗa wa ɗaiɗaikun ƙungiyoyin
Musulmin Nijeriya suna. A tarihi, magoya bayan ƙungiya
ko mazhaba ba su ke ƙaga
mata suna ba. Sunan na fitowa ne daga bakunan ‘yan adawa ko ‘yan jarida ko
jahilai. Da wannan suna za a laɓe
a yi ta kashe Musulmi har sai an ƙare
mu gaba ɗaya
bi-da-bi (Allah Ya kiyaye). Dga cikin misalan da zan bayar a nan sun haɗa da:
a.
Magoya
bayan karantarwar Muhammad ibn AbdulWahab ‘yan Naƙshabandiyya
suka sa musu Wahabiyawa. Ba su taɓa kiran kansu da sunan ba.
b.
‘Yan
Mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya da Hambaliyya da Hanafiyya da Zahiriyya, duk
ba malaman da suka assasa mazhabar suka sa sunan ba. Malaman fahintocinsu suka
fitar cikin gundarin nassi, ɗalibansu
suka rungumi fahintar aka sa musu suna da fahintar malamansu.
c.
Shehu
Abdulƙadir Jelani da Shehu Tijjani ba su
suka sa wa ɗariƙunsu suna ba. Abokan adawa da
almajiransu suka sa sunan.
d.
Muhammadu
Marwa bai san da sunan “Maitatsine” ba ‘yan jarida da abokan hamayya suka sa
sunan daga faɗar
da yake yi “Allah Ya tsine wa maƙaryaci”.
e.
‘Yan
ƙalaƙato
ba su suka sa wa kansu sunan ba, daga faɗarsu ne na cewa “In an gabato aya babu
sauran ƙala ƙato”.
A nan, suna tsoratar da masu kawo nassoshin litattafai su gitta a kan nassin Alƙur’ani.
f.
‘Yan
zando da Ƙur’aniyyun duk
suna ne da aka liƙa
wa masu fahintar ba tare da saninsu ba, kuma galibi ba su yarda da sunan ba.
BOKO
HARAM
Wannan
ita ce ƙololuwar maganar da ake ciki a
duniyarmu ta yau. Marigayi Malam Muhammadu Yusuf (Allah ya gafarta masa) bai
kira da’awarsa suna Boko Haram ba, ɗalibansa ba su kira ta da wannan suna ba.
Ni ina ganin ‘yan boko da boko ya zama wa dole, addini ya zama musu lalura, da
su da ‘yan jaridar da ke son a turara hayaƙin
rashin jituwa tsakaninsu da jama’a ke yi musu wannan suna. Gabanin a ci
zarafinsu da wannan suna, ana ce da su “Ahalil Sunnah” kawai. Da baya
wasu ‘yan adawa suke kiran su da Yusifiyya. Da suka yi wa aƙidojin boko na Yahudanci da Nasaranci
hari gadan-gadan wanda ya tilasta wasu daga cikin masu da’awar barin aiki cikin
gwamnati saboda gani babu wata hujja sahihiya da za a iya a tunkari Allah da
ita idan an je gabanSa da Demokraɗiyya ko Gwannatin Tarayya suka yi murabus
don ganin kansu. Ba a taɓa
samun wurin da suka tilasta wani ya bar aikin gwamnati ba, ko ya bar boko, sai
wanda ya gansu da hujjojinsu ya ɗauki fahintarsu. Duk da haka, ‘yan boko da
‘yan korensu suka bi su da suna Boko Haram.
A
gaskiyar lamari, idan aka ce, al’amari boko gaba ɗaya halas ne an ci gyaran Alƙur’ani da wanda aka aiko da shi. Tun
farko a dubi Tsarin Mulki, a dubi Dimukraɗiyya, a dubi fitar mata ‘yansanda, mata
kwastan da soja da sauran ma’aikatan tsaro mata. A dubi mata masu aikin jinya
da likita. A dubi cin hanci da rashawa. A dubi shugabancin mace da alƙalancinta, da dai sauransu. Me za a
ce da su? Halas ko Haram? Me sunan wanda ya ba su suna ɗaya daga cikin sunayen da
muka faɗa?
Idan haka ne kuwa, ya zama tilas Musulmin Nijeriya su gaggauta zama su kalli
wannan matsalar da idon adalci domin samun hanyar da za a samu zaman lafiya da
juna. Wannan matsalar karatu ce ba ta amfani da ƙarfin
bindiga ana kashe mutane ba.
IDAN
BABU ƘIRA ME YA CI GAWAYI?
Haƙiƙa
hatta da masu mulkin ƙasa
sun aminta da cewa tsaron ƙasa
ya salwance. Akwai mamaki a ji shugaba da kansa ya yi iƙirarin cewa, akwai ‘yan ta’adda har a
cikin gidansa kuma ya ayyana sunan waɗanda yake ce wa ‘yan ta’adda a bayyane.
Wannan abin nazari ne sosai domin a gano ina ne salka ke tsatsa? Ana cikin
wannan ruɗun
wani ɗan
siyasa ke cewa: “Kodayake ba dukkanin Musulmi ne ‘yan ta’adda ba, amma dukkanin
‘yan ta’adda Musulmi ne.” Ko kusa ire-iren waɗannan lafuzza ba su dace ga ɗan siyasa ba, kowane irin
addini yake biya. Ba a shugabanci da rashin ƙauna
kuma ba a yin sa da rashin amincewa juna.
A
tarihin Nijeriya, ba yau aka fara nuna wa Musulmi da Musulunci rashin gatanci
ba. Matsalar Malam Muhammadu Marwa da aka yi amfani da ƙarfin soja ba a san adadin Musulmin
da aka kashe a Kano ba. Aka sake yin irinta Bulunkutu a Maiduguri. Aka ƙara yin ta a ‘Yan’awaki a Kano. Idan
an ce waɗannan
an tsokane su sun rama ko suna da makamai, to su na Darus Salam na jihar
Neja wa suka tsokana? Wane makami aka kama gare su? Da wace hujja hukuma ta
tozarta su? An yi wa ‘yan Izala irin wannan cin zarafi da mutunci tun
farko-farkon fitowarsu a ko’ina. ‘Yan Tijjaniyya ba su kuɓuta ga muzgunawar hukuma
ba a Sakkwato da Ƙaurar
Namoda da Gusau da Mungadi da Jega ga su nan dai. Wane makami aka kama gare su?
Babu
shakka, waɗannan
fitinu da rigingimu akwai masu tayar da su? Dole a wasu wurare a samu rahoton ƙarya, irin wanda Amerika ta yi amfani
da shi ta rusa Iraƙi
da Taliban a Afganistan. A wasu lokuta kuwa, a samu wakilan tsaro ke tsokanar
tsuliyar dodo don sun ga bakin wuta a hannunsu yake. Ba zan musunta a samu
siyasa a ciki ba, domin ɗan
siyasa na iya shiga kowane rango na biyan buƙatarsa.
Haka kuma, akwai laifin Musulmi su kansu na rashin haɗin kai, da kuma adawar da
ke tsakaninsu sun yi ƙawance
da hukuma domin a musgunawa abokan saɓanin fahintarsu. Ƙarancin Ilimi ga masu biya da son
shugabanci ga masu wa’azi wani makamin jawo wa Musulmi fitina ne tsakaninsu har
hukuma ta shigo ta yi musu kan mai uwa da wabi.
DA
LAUJE CIKIN NAƊI
Duk wani kewaye-kewaye da za a yi na a
goga wa Musulmi kashin kaji ga rigingimu da ke aukuwa a yau ba zai ci nasara ba
domin:
i.
An
samu hannun waɗanda
ba Musulmi ba tsamo-tsamo a cikin ƙone-ƙonen wurin ibadojin Kirista. To! A
nan, me za a ce ga wanda ba Musulmi ba cikin kayan Musulmi ya aikata ta’addanci
domin a ce Musulmi ne suka yi?
ii.
Ire-iren
makaman da ake sarrafawa sun fi ƙarfin
a ce, wasu ‘yan ɗaiɗaikun mutane ne ke da
hannu. Wanda ke cikin talauci, ina zai sami kuɗin sayen makamin da zai saya masa
abincin shekara goma?
iii.
Rahotannin
da kafofin yaɗa
labarai ke yawaita ambato na makaman da ake kamawa, musamman waɗanda aka sa shari’arsu a
Ingila (yanzu) da waɗanda
aka kama Ghana da Borno da makamantansu ba a bayyana masu su ba balle a san
dabarun da za a ɗauka
na zaman lafiya.
ME
YA KAI MU A WANNAN HALI?
Wannan
shi ne zuciyar abin da nake son in yi hasashe a ɗan bayanina. Yau mun shiga halin da
kowa na buƙatar zaman lafiya.
Don haka wasu ƙasashe na son su
samu damar shigowa cikinmu ƙasarmu
ta shiga wani hali. Babban abin da ya kawo mu a wannan hali shi ne:
i.
Kisan
gillan da wakilan tsaro ke yi wa shugabannin addini da masu addini a bayyane ba
tare da an je kotu ba an tantance maras gaskiya. Ta yaya almajirai da muridai
da mabiya da surukai da ‘yan’uwa da Musulmi za su yafe wa wanda ko waɗanda suka yi wa
magabatansu kisan gilla na wulaƙanci
da tozartaswa? Aikin hukuma ne ta lalabo waɗanda suka yi wannan aiki ta barranta kanta
da aikin ta kai su kotu a hukunta su, a san ba da yawun hukuma suke kashe
mutane ba. Idan hukuma ba ta ɗauki
matakan hukunta masu laifi ba, kamar tana koya wa waɗanda aka zalunta
ta’addanci ne. Kisan gillan da aka yi wa Malam Jafar a Kano da Muhammadu Yusuf
a Maiduguri da Ɗanmaishiyya
a Sakkwato (Allah ya gafarta musu), sun isa su zama abin misali a kan haka.
Hukuma ta yi shiru kamar an aiki bawa garinsu. Me ake zato ga ‘yan’uwan
mamatan?
ii.
Rinjayar
da aka yi wa wani addini cikin ma’aikatan tsaron ƙasa
ya sa a koyaushe ake samun ire-iren waɗannan matsaloli. Wakilan tsaro wasu na
amfani da su wajen kare addininsu. Don haka, addinin da duk aka fi yawa a cikin
wakilan tsaron a koyaushe shi ne mai laifi, shi ake kawo ƙararsa a koyaushe, har sai an sa mai
kai an cuta masa da sunan rahoton ƙarya.
Wannan haƙƙin hukuma ne ta yi
adalci a kan tsarin ɗaukar
ma’aiktanta.
iii.
Wakilcin
galihu da alfarma da danniya na zaɓen shugabannin siyasa na ɗaya daga cikin mafarin
yin haka. Da za a samu ‘yan siyasa ko da rubabi-rubabi ne waɗanda suka san addininsu
da ƙasarsu da al’adunsu dole a yi wankin ɗa kanoma mashaya a kan
kowace matsala da ta shafi ‘yan ƙasa.
Matuƙar masarautu da ƙungiyoyin sa kai da jam’iyyun siyasa
ke da babbar murya a zaɓen
shugabannimu, muna da aiki baya, an bar kyau tun ranar haihuwa.
iɓ.
Rinjayar
da aƙidoji da dokokin wani addini a ƙasar da aka ce ta gamin gambiza ce,
shi ke haifar da ta’addanci. Idan ƙasar
gamin gambiza ce, to tsarinta gaba ɗaya ya zama gamin gambiza ba irin kashin
dankali ba manya-manya su taushe ƙanana.
A ce, kowane shugaba ya hau da tsarin addininsa za a yi aiki ko ba a faɗa a rubuce ba, a aikace
an tabbatar. Waɗannan
abubuwan ke sa masu kishin addnin da ba irin na shugaba ba, su ga gara komi ta
banjama banjam! Da za a ɗora
Nijeriya da tsarinta a kan sikelin addinin Musulunci ko Kiristanci ko makaho ya
laluba ya san an ƙwari
wani addini. Ƙin gyara wannan
shi ke sa waɗanda
ake shugabanta su kasa haƙurin
walaƙanci, su da ƙasarsu a mayar da su bayi. Dole
wannan ya haifar da saɓani
a ƙasa hukuma ta fassara shi da sunan
“ta’addanci.”
ɓ.
Burin
wasu marasa kishin ƙasa
da addini da sanin ya kamata na a raba ƙasar
nan, su ci moriyar arzikin ɓangarensu.
Wasu na ganin kamar da arzikin da ke yankinsu ne aka gina Nijeriya. Bayan an
fifita su ga rabon arziki wanda yake kure ne. Aka buɗe musu ma’aikatun tarayya
na kansu cikin kuskure. Aka yanka musu albashin zauna-gari-banza mai tsoka ga
matasansu marasa ilimi da aikin yi. Wataƙila
ganin irin tsoronsu da ake ji, da reno na musamman da suke samu daga cikin
gajiyar arzikin tarayya, wanda babu wani yanki na ƙasar nan da ya taɓa samun irin wannan gata, shi ya sa suke
burin a dai raba ƙasa,
a yanka musu tasu ƙasa,
su gargaɗi
baƙin haure daga yankunansu. Da yake ba
addinin Musulunci suke yi ba, ba ‘yan ta’adda ba ne, samarin neman ‘yanci ne.
ɓi.
Burin
da wasu maƙiya Nijeriya ke yi
na ta sake shiga yaƙin
basasa domin su samu shigowa ciki su tarwatsa jama’arta da tattalin arzikinta
ya kyautu a Harare shi. Tuni sun barbaza a kafafen yaɗa labarai na duniya cewa,
a shekarar 2015 Nijeriya za ta barkace ta warwatse ta rarraba. Yanzu kuma sun
gurgusa shi zuwa shekarar 2030 bayan an gama da mu duka. Da suka ga hasashensu
ya ƙarato, abubuwan da suke son su
wakana, ba su wakana ba. Waɗanda
ake zaton su fito su yi aikin, wasu sun mutu, wasu sun kasa, wasu ba a yi da
su, wasu an gane su, wasu sun ji tsoro sun tuba, daga nan sai bakin zaren
hasashen lisafinsu ya ɓata
suka fito da sabon salon na yaƙi
da ta’addanci a jiohohin Arewa da maƙiyansu
suke.
ɓii.
Cin
hanci da rashawa da handama da babakere da shugabanni ke yi ya taka rawar gani
na fitinun da ke wakana a yau. Yau arzikin ƙasa
duka na masu mulki ne, wanda ba ya da mulki sai dai ya mutu. An mayar da matasa
‘yan ta’adda, an ba su makamai da tsaro domin su aikata abubuwan da ƙungiyoyin siyasarsu ke so. An mayar
da malamai maroƙa.
Sarakai sun zamo fadawa. An mayar da maza mata, mata sun koma maza. An cusa
yunwa cikin talakawa, an ba masu arziki tsaro. An mayar da managarta lalatattu,
lalatattu an mayar da su bayi. Waɗannan abubuwa duka cin hanci da rashawa ya
haifar da su. Don haka, yau an kai mutane bango ko ba su bin kowane irin addini
za su yi fito-na-fito da hukuma da ‘yan barandarta ko da za su yi hasarar
rayukansu. Idan aka ƙi
duban tashin hankali da ke aukuwa a Nijeriya ta wannan fuska an cuci ‘yan
Nijeriya. Yaya za a ilmantar da matasa su rasa aikin yi, a hana su shiga wani hali?
Ta yaya za a bar matasa babu ilimi babu abinci a hana su ƙunar Baƙin
Wake ga kai ka muradinsu? Yaya za a tura talaka a bango, ba arziki, ba lafiya,
babu abinci, babu matsagunni, babu tsaro, babu kulawa, babu kare haƙƙi, ba a sa ranar gyara
ba, ya fito da gora don ya gyara a ce masa Boko Haram? Idan aka bi wannan
fassarar wane ne ba ɗan
Boko Haram ba a Nijeriya?
ɓiii. Ina
daga cikin masu ra’ayin cewa, babu Boko Haram. Wani samfarin yaƙi da Musulunci ne aka ƙirƙiro
bayan da aka ƙirƙiro ciyon ƙanjamau na rage yawan jama’a a duniya
musamman na Musulmi da suka ƙi
yarda da ƙayyaje iyali na ba
gaira ba saba. An ƙirƙiro Boko Haram ne, domin a tabbatar
da an kawar da duk wani mai kishin addini da buƙatar
ci gabansa. Martanin da ake zargin ‘yan Boko Haram suna kai an fara gano ba ma
Musulmi ne ke kai shi ba. Waɗanda
ke magana da yawun Boko Haram an gano ‘yan jeka-na-yi-ka ne da ake son a laɓe gare su a kashe
Musulmi. Zargin da ake yi musu na haranta Boko an gano mafi yawansu ‘yan boko
ne, wasu ‘ya’yansu na boko ga su nan dai. Ala tilas Musulmi su yi zama na
musamman a kowace jiha cikin ƙasar
nan a fuskanci wannan al’amari tun ba a ƙare
mu cikin guguwar siyasa ba. Ba za mu yarda wani ya liƙa muna sunan da ba namu ba don ya
kashe mu ya raya jama’arsa.
SAKAMAKON
BINCIKE:
A
fahintata hukuma da kafafen yaɗa
labarai na cikin gida da na waje ba su taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen samar
musu zaman lafiya da lumana ba. A ɓangaren ma’akatan hukuma wasu ƙabilarsu suke yi wa aiki. Wasu
addininsu suke yi wa aiki. Wasu yankinsu suke yi wa aiki. Wasu ƙungiyoyinsu suke yi wa aiki. Wasu son
ransu suke yi wa aiki. Wasu aljihunsu suke yi wa aiki. Wasu siyasarsu suke yi
wa aiki. Waɗannan
su suka taru suka yi ma’aikatan tsaro da farar hula da masu gudanar da mulkin ƙasarmu. Ta yaya za a samu zaman
lafiya da haɗin
kai alhali kowa da fuskar da ya kalla irin zaman ‘yan marina? Yaya za a yi
wanda ke da ƙiyayya da wani
addini a tura shi da makami ya kwantar da tarzomar ma’abota addinin da yake ƙiyayya, bai yi wa addininsa aiki ba?
Yaya za a tura ɗan
PDP sulhun auren ɗan
CPC a ci nasara? A kan wannan tunani nake cewa:
i.
Idan
dai da’awar hukuma da ‘yan jarida na danganta musibun da ke aukuwa a Nijeriya
ta yau ga Musulmi wai Boko Haram! To, ai a Kudu can boko ya yanke cibi me ya sa
ba a samu hare-harensu a can ba?
ii.
Idan
dai tabbas ne manufar Boko Haram a daina boko, yaya aka yi ba su kai hari a
makarantun boko da ake haihuwar ‘yan boko ba?
iii.
Kai!
Hankalin tuwo ya isa ya yi hukunci manufa ita ce, ana son tarwatsa mu, a rage
muna ƙarfi, a rage muna yawa gabanin a
zauna teburin raba ƙasa
da wasu ke da’awar a yi. Idan haka ne kuwa, ya kamata mu kama kanmu tun dare
bai yi ba.
iɓ.
Masu
hangen nesa na ganin, da halastar da Luwaɗi da Maɗigo aka fara taya wa mahukuntar ƙasarmu. Da suka ƙi tayawa aka ƙago Boko Haram.
ɓ.
‘Yancin
mata na ƙarya da haranta auren mace ƙasa ga shekara 18 da tilasta wa mata
boko da tilasta shugabancin mace da tabbatar da gado ga shege kaɗan ne daga cikin abubuwa
da aka so a yi amfani da su a murƙushe
mu. Da abin ya ci tura aka ba mu suna na dabam.
MAFITA:
Ga
zatona ko ban faɗa
ba muna iya kirdadon mafita da kanmu. Ina ganin Ƙungiyar
Izala ta fara yada muna fitila. Idan muka yi koyi da tsarinta za mu gane ina
ta’addanci yake. Mu taru mu duka kamar yadda Mazhabobinmu ba su hana mu salla
wuri ɗaya
ba, ba su hana mu son juna ba da yi wa juna ɗa’a da fatar alheri. Da yardar Allah ƙungiyoyinmu da ɗariƙoƙinmu
ba za su hana mu zama abu ɗaya
ba mu tunkari abin da ke tunkararmu. Duniya ba a taɓa samun wurin da ma’abota
addini suka samu fahinta iri ɗaya
ba, amma kuma su zama abu ɗaya
a muryoyinsu da manufofinsu. Maganin wannan kawai gaggauta taro na dukkanin
wanda abin ya shafa a yi zama na musamman na ganin an kai ƙarshen kowace irin fitina da sunan
addini a Nijeriya. Ku tuna, a Kaduna ga zanga-zangar tsadar man fetur Musulmi
da Kirista aka haɗe
kai wuri ɗaya,
Kirista ke gadin Musulmi idan lokacin salla ya yi, sai sun ƙare salla a ci gaba. To! Da aka yi
haka ai ba a ji rahoton ‘yan Boko Haram ko jami’an tsaro sun kashe kowa ba.
Wasu jahohi da ba a yi haka ba, yaya aka yi? Ban ga laifin shugaba ba idan ya
ce cikin jami’an tsaro da wakilan hukuma Boko Haram suke, mun ko ga alama a
Kaduna. Madalla da wannan haske. A hasashen shugabanmu Bobo Haram gamin
gimbizar Musulmi ne da Kiristan Nijeriya su ne ma’aikatan ƙasa. To! In haka ne don me a jihohin
Musulmi kawai ake kai hari da jami’an tsaro ana kashe Musulmai?
NAƊEWA:
Shugabannin addinin da Sarakuna su daina
suɓul
da baka idan aka aikata wani ta’addanci aka jingina ga jama’arsu. Tabbas!
Abubuwan da ke aukuwa a Nijeriya a yau na ta’addanci ba Musulmi ke aikata su
ba. Yayatawar da ‘yan jarida ke yi na alhakin wasu ayyukkan ta’addanci ga wasu
mutane bai isa a yi aiki da shi a kama kashe mutane ana tsare su ba, domin babu
dasisar da maƙiya ba su yi wa
Musulunci. Tursasa Musulmi da ake sa wakilan tsaro da ba Musulmi ba na yi wani ƙaramin ta’addanci ne mai sa ƙiliu ta tono balau!
No comments:
Post a Comment