1. Shukura ga
Allah guda masani halin kowa,
Mai ƙaddarowa ta
tabbata babu mai tsawa,
Ya mai
hukuncin da ba makara da gaggawa,
Masanin
da ilminSa ya wuce hankalin kowa,
Subhaana lil laahi tsarki na ga
Rabbani.
2. Na yo
salati ga Manzo shugaban bayi,
Ahalinsa
dukkan sahabbai ƙoƙari sun yi,
Na riƙo ga sunna ta
sadu da mu ruwan sanyi,
Mariƙa amana sahada
kun riga kun yi,
Matsayin shahidi ga nassi babu saɓani.
3. Mai rai a
ce ya mace ba al’ajab ne ba,
Mutuwar
shahada buki ne ba na wasa ba,
Ita ce
manunin aƙida ba ta yi ƙura ba,
Ita
fassara ce mutum bai tabka shirme ba,
Shaidarmu ke nan ga Awwalu namu
Albaani.
4. Ba mu
shaidi Awwal a kan ilminsa ya kai ba,
Ba mu
tsarkake ayyukansa hawa kurarra ba,
Ba mu
yanke ƙauna irinsa ba zai yi laifi ba,
Katarin
da Allahu yai masa ne abin duba,
Kalimar shahada ta zan ƙarshe ga
Albaani.
5. Ita ce
alamar kusantar Rabbu mai girma,
An zaɓi bawa cikin bayi na alfarma,
Ya samu
babban rabo na shiga sahun dama,
Ladar
karatunka ce Allah Ya saka ma,
Zance ga nassi sahihi babu ƙaulaani.
6. Awwal haƙiƙan Tabaraka ya
yi ma baiwa,
Ya sa ka
layi da muminnai suke kewa,
Ka samu
hasken da yaf fi gaban musun kowa,
Haka
Rabbu Yaƙ ƙaddaro tafiya ta gaggawa,
Mutuwar shahada rabo ce babba Albaani.
7. Ƙarshen ƙwarai muminai
abada ka alwashi,
Rahama
gado ce da babu kamar ta gun taushi,
Ta zarce
kaafur da almiski wajen ƙanshi,
Shuhadaa’u
Aljanna ke karɓa da lallashi,
Fatarmu ke nan ga Awwalu namu Albaani.
8. Masani
hadisi maƙoƙarci ga tsentseni,
Fatawarka
nassin hadisi babu saɓani,
In ga
sahihin hadishi ba shi sharani,
Da gani
da aiki zama ɗaya ne ga Albaani,
Bai faɗa ɗirkaniyar rigima ta ƙaulaani.
9. Awwal a
fannin hadisi ka yi tabarma,
Fiƙihun hadisai na
salla in gajerta ma,
Matani
da ilmul rijaalu maza na alfarma,
Isnaadu
bin taliyonsa hagunsa har dama,
Sun zauni ƙirjinka Awwalu babu saɓani.
10. Fatawar
Buhaari da Muslimu Tirmizi daidai,
Kundin
Nisa’i, Abu Dawuda zancenai,
Haka
Baihaƙi ko Muwatta mai karutu nai,
Awwal
idan ya hawo sharhinsu bakinai,
Tamkar ka ce zamaninsu guda da
Kirmaani.
11. Fatawarsa
koyaushe dai a bi maluman farko,
Masana
hadisi ga sunna masu yin sabko,
Su ne
yake kwaikwayo fatawarsu yaɗ ɗauko,
Sunansa
Mamman Awal tun fil azal farko,
Ƙaunar hadisi ya sa mu kira shi Albaani.
12. Bai yarda
yin ƙungiyar raba kan Musulmi ba,
Bai
yarda Zazzau a wa bidi’a masauki ba,
Bai
kutsa kainai siyasar tara jalli ba,
Bai
yarda yin kore gwannati na biyanai ba,
Roƙo da yin raraka faufau ga
Albaani.
13. Ɗan kasuwa ne ga
boko bai zama baya,
Bai ɗau karatu asusu ba don hawan kaya,
Komai
tulin gingiraɓai ba shi yin zarya,
Ba a
game kai da shi a yi fassarar ƙarya,
Filin wuri ne dabon Ɗankama Albaani.
14. Bai yarda
bin Mazhaba a aje hadisai ba,
Bai ɗauki ƙissa salo ga zubin karatu ba,
Bai ɗauki wasa da kaulahasan karatu ba,
Bin
malami sau ƙafa bai ɗauki wannan ba,
Sunna ake bi idan aka samu saɓani.
15. A bi taliki
sai ka ce gunki yana kuri,
A yi mai
nasiha a kan nassi ya sha bauri,
Harakar,
karatu ta zan wasan kiɗin tauri,
Kabbarbari
had da kuwwa kanka na kauri,
Alaramma na dama ga ɗan agaji hauni.
16. Ilmi a mai
she shi hajar ɗaukakar suna,
Ya zamo
jidali da cin zarafi da ƙin juna,
Haske ya
koma duhu, inwa ta zan rana,
Ustazu
in za ka adalci ga zance na,
Mabiya ga sunna a yau an sa su ruɗani.
17. An wa siyasa
hadissai don biɗan romo,
Wa’azi
ya koma kamar wasan kiɗin komo,
Mabiya
da Malam kwaɗai kowa ya dai samo,
Tsoro ya
zauna zukata ce ka kai zomo,
Taƙawa da bin gaskiya suka zan
cikin rauni.
18. Samun irin
Awwali ɗan Iro mai daga,
Da irin
su Jafar Kano bidi’a ta bar tunga,
Sunna ta
miƙe ƙafa mabiya suna farga,
Yau
jami’a ga hijabi har da sa raga,
Ƙwazonku ne kai da Jafaru Shehu Albaani.
19. Kun taimaka
raya sunna nan ƙasar Hausa,
Aka ba
matasa fahinta wadda ba nisa,
Sunna ta
tozarta ƙila-wa-ƙala ba fansa,
Tafiyarku
ta zan hasara gun mu kakkausa,
Samun shahadarku shi yak kore ruɗani.
20. Makasanka
Awwal hasara ta tuƙaƙe su,
Ba
mumini duniya da yake mutunta su,
Ranar ƙiyama Tabaraka
zai hukunta su,
Nassi na
aya ya ce wuta za a sakka su,
Shi ne hukuncin kisan kai babu saɓani.
21. Mik kai
matashi shiga fitinar kisan kanu?
‘Yan yara
daidai karatu sun sake hannu,
An
birkice hankulansu a mai da su shanu,
A saka
su hanyar ta’addanci su sa hannu,
An ɓata ƙarshen matasa dama har hauni.
22. Ƙarninmu yai
arziki da irin su Albaani,
Harakar
ibadarmu ta huta da saɓani,
Mun gane
nassi sahihi mun ga mai rauni,
Maganar
da duk ba hadisi ba ta yin shuni,
Nahawunta bai sa mu tabka musu da saɓani.
23. Babbar
hasara gare mu rashinka Albaani,
Babbar
musiba ƙasarmu kashe su Albaani,
Fitinar
da ta’ kunno kai bayan su Albaani,
Tsananin
bala’insa ba magana ta saɓani,
Yaƙi ake son ya tashi ƙasarmu mai
gauni.
24. Sa hankali
dubi Siriya yau ina saura?
Bagadada
birnin Iraqi ina batun gyara?
Afgaani
ta zan kamar akuya gaban kura,
Islamabad
mumbari aka kai harin sara,
Nijeriya kan sahu take babu saɓani.
25. Modibbo
Albaani sannu mazan sanin girma,
Masani
hukuncin zama da kiyaye alfarma,
Samun ku
ya tauye ‘yan bidi’a ganin dama,
Miƙe ƙafafu da
sokiburutsu ba dama,
Fatawar da duk ba hadisi mun aje
hauni.
26. Ita
jarabawarka Malam ka riga ka ci,
Kwanci
kushewarka ba tsoro bale ƙunci,
Samun
shahadarka ya tayar da mu barci,
Tilas faɗin gaskiya ko da akwai ɗaci,
Babin gumuzu sahihi ne a Shaukaani.
27. Ba mu ɗebe ƙauna ba Malam ba mu manta ka,
Ƙwazon karatunka dole ake mutunta ka,
Nasarar
shahadarka Awwal ta faranta ka,
Ƙaunar hadisi gamo da katar ta sakka ka,
Fatar mu Ya Rabbi gafarta wa Albaani.
28. Rigimar kisa
ba ta sa sunna ta ja baya,
Birnin
Kano an yi je ka ga mib biyo baya,
Makasa
Umar yanzu Sakkwato dole sai ɓuya,
Makasa
ga Albaani ga su Abuja kan ƙwarya,
Ƙarshen guluwi shiga babi na kaico ni!
29. Tammat
bayani na tanzanko da juyayi,
Babban
abokinka Ali na Bunza ne yay yi,
Na
tababta Awwali dai lokaci ya yi,
Zancen
adashinmu masu zubinmu duk sun yi,
Mu ke da kwasa na ƙarshe babu saɓani.
Aliyu M. Bunza
Umaru Musa
‘Yar’Adua University,
Katsina
Jumu’a 7/03/2014
Daga Katsina zuwa Sakkwato
No comments:
Post a Comment