Roƙo nika yi ga Wahidun mai gyarawa,
Sarkin da ya zarce masu ilmi ganewa,
Kai kay yi sama’u kay yi ƙassan zaunawa,
Kay yo Aljanna kai wuta mai ƙonarwa,
Kay yo duniya da rayuwa don zaunawa,
Kaƙ ƙaddaro lahira ga ƙarshen komawa,
Kowace rai la muhala ƙarshen ta macewa,
Tilas in ya mace ƙasa zai komawa,
Tsoron mutuwa ga masu rai bai ƙarewa,
Domin ba ta kure da ta zaka kamawa,
Ɓera bai ce wa mage sannu da hutawa,
In sun gamu hanya wa mutum sai rugawa,
Don me akuya ka ba da bai babu tsayawa?
In kura ta yi mui guda ba ta tsayawa.
Don me zaki ka watse taron Gardawa?
Ƙato ko sun yi su dubu ba su tsayawa?
Don me zakara idan yana son carawa,
Yaj ji muzuru yana wurin bai motsawa?
Me ke sa ɗan Adam gudun ba waigawa,
Kayansa su faɗi bai tsayawa ɗaukawa?
In ka ga ango gudane ba sassautawa,
Ya wuce matarsa ba kula ba waigawa.
Ta leƙo ya gane ta ne yaka zuƙewa.
Wai ɗammaninsa ko yana iya
tserewa.
In ka ji ana ku gurgusa an ƙi ɗagawa,
In ta zo kan ka ce kwabo sai darewa,
Ba a kirari ta ba da fili na sakewa,
Shago da uban kiɗinsa yau ko
motsawa
Da tauri na hana ta kamu da bugewa,
Ɗankurja da Daƙƙwahe suna iya tserewa.
Ba ta tayawa da ta taho ba fasawa
Muddin ta sauka an gama sai shurewa.
Ba ta kure gun da tan nufa sai dacewa,
In ta damƙa aradu ba a kuɓucewa.
Mai jinya kwance ko ruwa ba ya haɗawa,
Ta ɗauke majinyacinsa mai iya
rugawa,
Wa ka iyawa? Ina maza masu gwadawa?
Mata sun hau dugadugai babu tsayawa,
In ka ishe ‘yan rawa kiɗi na cashewa,
Daɗi aka ji ganin kamar ba a
macewa,
In ta dako rida mai kiɗin take dahewa,
Masu rawa sai batun gudu babu tsayawa.
Tsuntsu a sama’u ta buga sai faɗowa,
Kifi a cikin tsakar ruwa sai tasowa,
Ke mai sa tagumi zugum babu muɗawa,
Mai sa murya ta kumbure sai sheƙewa.
Ba ki bugawa a mirmije don tserawa,
Kun fa yakuninki babu mai iya jurewa,
Mai sababin balbalin bala’in ruɗarwa,
Mai tashin tashinan da zai hana cashewa.
Ya ke makasan maza da ke saba kashewa!
Ke ka kashi ɗan Adam ruwanai yaka sawa.
Ya mai izo ƙaddara idan za ta isowa
Sai ta yi barazana ki kwakkwahe sheɗawa.
Ya takwarar duniya ga ɗauka da ajewa.
Sai ta ɗauka ki maƙure sai shurewa.
Yayin da ta yunƙura da niya na ajewa.
Sai ki yi tarbon da ba maraba da kushewa.
Mai sa mutukabbari da ɗanga rikicewa,
Mai ladabi babu rangwame babu ragawa.
Muminnai malamai sarakai fadawa,
Rumbace ne zama guda sai rugewa.
Masu faɗar sun buwaya su taka murjewa
In ta buga rida ko guda bai tserewa.
Ta iske ƙaddara ta ce, “Ga mu tahowa”.
Sai ke kutsa mu samu daman leƙowa.
Ta ce ‘yar tsohuwa halinki da ruɗarwa,
Ke ka ta’adinki laɓo ni aka
shafawa.
Ciwo yac ce wa ƙaddara. “Me kika cewa”?
Ku ka ta’adi musabbabi ni aka cewa.
Anka kira lafiya wurin sasantawa,
Tak kiri mutuwa da ƙaddara tattaunawa.
Laifinku guda gare ni shi za ni tunawa,
Shuka nika yi ku ƙwazzabe ta ga tonewa.
Malam Boko da Likkitoci ka tahowa,
Don tanyo na zama ku ce ba su tsayawa.
Kun saba tarar da ni riƙis ba shiryawa,
Kamin in farga kun gama sai biznewa.
Ciwo ya ce wa lafiya wa ka iyawa?
Mu da ka yin shekaru ana fafatawa.
In adadi zai wakana mu za a rutsewa,
Rai ya ji tsoro ya suɗaɗa sai tserewa.
Ƙarshen taron baran-baran ba kintsawa,
An kasa hukunta inda laifi ka fitowa,
Laifin mutuwa baƙin jini aka farawa,
Ga mugun rai da ƙeta ba sassastawa,
Ke ko laifinki ƙaddara son kutsawa,
Girshi ki faɗo wa rayuwa ba kintsawa.
Ciwo laifinka magani ba shi iyawa,
Ba ka da ranar shiga da loto na ficewa.
Ai zargin lafiya da tsoro da laɓewa.
Ciwo ƙarami ta gangara tai ta cirawa.
Ke ko mutuwa zamanki ƙarshen ƙarewa.
Ba wani mai rai da ke biɗan ki ga ganawa.
Yara da manya maza da mata kokawa.
Mai ta’aziyya da masu tanzonko haba wa!
Mai marsiyya da alƙalam shika zanawa.
Ga ta muna yi ga Rabbana muka roƙawa,
Roƙonai gafara da jinƙai ƙarawa,
Tammat Ali Bunza ne na birnin Kyangawa,
Babbar fadama da ƙaramomin hutawa.
Aliyu
Muhamamdu Bunza
Sashen
Koyar da Harsuna Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa
Katsina.
Talata 11/3/2014
Sakkwato
No comments:
Post a Comment