Sassan adabinmu na baka ba ƙaramar rawa suka taka ba wajen daidaita muna akalar rayuwa a kowane ƙarni muka samu kanmu. Lallai, ba don jiya ba, da yau ta
yi masassara. Yunƙurin kyautata rayuwar yau kuwa, gobe ce ake yi wa
shimfiɗar maraba. Sarrafa karin
maganar “Sabo Turken Wawa” ya zama akalar jan zaren tunanin wannan littafi ya
dace. Abin da aka saba da shi an san shi. Abin da aka sani dole an zaune shi.
Abin da aka zauna, ya zama abokin rakiya sai a sake jiki, a miƙa wuya gare shi, har ya zama raƙumin makaho, kai ka gani ba ni ka gani ba. A ganina, burin littafin shi ne,
a riƙa…
Da Wasa Ake Gaya Wa Wawa Gaskiya
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
Jahar Katsina, Nijeriya
Bitar littafan SABO TURKEN WAWA na Halimatu AhmadUmar Bunza wanda aka gabatar a bukin ƙaddamar da littafin ranar 1 ga Watan Junairu 2014 a
babban ɗakin taro na Tsangayar Sarkin
Musulmi Muhammadu Macciɗo, Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Ambasadar Shehu Wurno da ƙarfe goma na safe
Da suna Allah mai rahama mai jinƙai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Muhammadu ɗan Abdullahi (SAW) da iyalansa da sahabansa da waɗanda suka yi koyi da su ya zuwa ranar sakamako.
Gabatarwa:
Sassan adabinmu na baka ba ƙaramar rawa suka taka ba wajen daidaita muna akalar rayuwa a kowane ƙarni muka samu kanmu. Lallai, ba don jiya ba, da yau ta
yi masassara. Yunƙurin kyautata rayuwar yau kuwa, gobe ce ake yi wa
shimfiɗar maraba. Sarrafa karin
maganar “Sabo Turken Wawa” ya zama akalar jan zaren tunanin wannan littafi ya
dace. Abin da aka saba da shi an san shi. Abin da aka sani dole an zaune shi.
Abin da aka zauna, ya zama abokin rakiya sai a sake jiki, a miƙa wuya gare shi, har ya zama raƙumin makaho, kai ka gani ba ni ka gani ba. A ganina, burin littafin shi ne,
a riƙa sara ana daban bakin gatari, domin a hangen
zabiyar tashe cewa ta yi:
Jagora: Bari
wanka da tutu don a ga iska,
Yara: Hadari
yamma ba ruwa ke da shi ba.
Bita:
An tsara littafin Sabon Turken Wawa cikin
shafuka ɗari da arba’in da shida (146).
Goshin aikin aka tsettsefe shi da shafuka ashirin da shida (26). Bayan shafin
farko na sunan littafin. Shafin da ya bi masa aka sadaukar da aikin wurin da ya
dace domin babu mai nunin gidansu da hannun hagu. An yi nagartacciyar godiya ga
kagunan da aka sha madarar karatu. Daga nan aka samu tofa albarkar masana
addini Sheikh Kabiru Haruna Gombe, da share fagen nazari daga Farfesa Salihu
Bala Aljannare, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya kakkaɓe wundin karatun domin abin aljihu na mai riga ne.
Saboda cikon sunan makaho da waiwaya marubuciyar ta ƙara wata gabatawa ta daban. Yin haka, bai zama sabon salo ba, shiƙa da daddare in ji kaza, domin malammamu cewa suka yi,
mai sanda ke da fasalin bugu.
Ainihin ƙunshiyar littafin an zuba ta
cikin babuka goma sha biyu. Waɗannan babuka su suka ba da shafi ɗari da ashirin (120) na aikin. A hangen bita, na kasa su
zuwa gida uku: Gida na farko babi na ɗaya da biyu, su ne goshin aikin. Babi na ɗaya ya taɓo tarbiya ta addini da al’ada. A ƙarshe, aka yi kwakkwahe da kunya domin ta zama madubi da ma’auni ga babukan
da za su rako su. Babi na biyu ya kalli wayewa da wauta a idon masu ganin sun
waye, ya kuma tabbatar da wautar wayayyin zamaninmu.
Kashi na biyu ya ƙunshi babuka shida (babi na 3-7). Waɗannan babukan su suka yi wa aikin susa gurbin ƙaiƙayi. An taɓo sadarwar zamani da irin bi-ta-da-ƙullin da ke ciki. An kalli tauraron ɗan Adam da idon tarbiya. An ƙyallaro yanar gizo da hankalin tuwo da na addini. An waiwayi zaman banza da
sunan majalisa da holewa ta mahangar tabaran Alhaji Muhammadu Sambo Wali
Sakkwato, da ya ce:
Ga jin daɗin rayuwa samari ka bicewa,
Suna wasu ‘yan ƙwange-ƙwange don nuna ɓacewa,
Su sa takalmin da ba wuya za a karewa,
Su shawo tabar da hankali zai juyewa,
Su
gigice don su samu damar ɓacinmu.
(Waƙar Zaman Ɓanza).
Rukuni na uku ya ƙunshi (babi na 8-12). A nan aka fito da sakamakon wayewa ga suturar mata da
maza da kuma yankan ciki da ya yi wa matan wayayyi ma’aikatansu da waɗanda ke zaune gidajensu. Ga irin abubuwan da suka haddasu,
aka naɗe karatun da faɗakarwa ga waɗanda abin ya shafa da kuma hukumar da ke kula da su, an
dai gaji an dawo ga hasashen Alhaji Muhammadu Gambo Fagada da ke cewa:
Jagora: Wai ga maciji a ɗora biyas shayi da sanda,
: To
ga ɓarayi, shi mib biɗi mai waƙar ɓarayi?
Nazari:
Ga al’adar Bahaushe, idan aka ce sabo turken wawa,
abin da zai bijiro ga tunanin Bahaushe na gidi shi ne, abin da aka saba da shi
a koyaushe shi za a riƙa tunawa. Yadda aka san shi
jiya, za a ga ko yau, yana nan ba sauyawa. Daɗin da aka sha jiya, gobe ana sa ran a sha irinsa ko
wanda ya fi shi. Yadda duk ake ɗaure dabbobi a turke, su mai da turke wurin zama na sakewa da jin daɗi, haka ɗan Adam yake ga abin da ya saba. Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa ya
kakkaɓe muna ƙura ga ma’anar kalmar “Sabo” yana cewa:
Na saba miƙa sheɗara
Ta tsaya tsaf babu tanƙwara
Ai waƙa ba ta gagara
Muddin na tashi fassara
Wada
duk nika so ina faɗi rarara.
(Waƙar Yabon Sarkin Gwandu Yahya)
Don haka, sabo sanin abu ne na haƙiƙa domin Hausawa cewa suka yi,
ido wa ka raina? Ya ce: “wanda na saba gani koyaushe”. Bisa ga wannan riwayar
magabata ke cewa, sabo da ci kwaɗai yake sa wa. Idan aka naƙalci abu sosai su ce, hannu ya
iya jiki ya saba. Dalili da haka ne suke ganin sanin asali kan sa kura
cin kanjilo (ƙonannen kashin shanu). Don me muke ganin, ɗan gafiya ko bai yi sata ba yana dogon aro? Don ya
saba da ganin banza koyaushe a gidansu. Ashe gaskiyar Bamaguje da ya shiga
birni bai ga rumbu da masussuki da ya saba gani ba ya ce, “Ana zaman ƙarya”. Tattara hankali wuri guda da ƙuƙewa ga ginan ɓera da gafiya da yanyawa da tsari da damo, ba dare ba
rana, ya sa makaɗa Maitandu Shinkafi ke yi wa
wani gwarzo take da:
Jagora: Tsohon tabuda tsohon sallatau
Yara: Uban na Nababa ya saba da gina,
Jagora: Na mai kiɗi kwana suya yakai,
Yara: Kitsen burgu hak ya kamma shi gabanai na naso.
Gindi: Ya fito ma kusa Hausance
: Nababa ya saba da
gina.
Ga al’adarmu, idan aka saba da abu, ba a gajiya da shi, in ji malamin kiɗi Narambaɗa:
Jagora: Uban Yari uban malami
Yara: Kowag gaji bai saba ba
Gindi: Koma shirin daga
: Gwarzon bahago ɗan Iro.
Idan ana biye da zaren tunanina, za a ga, an fi son
a saba da abin ƙwarai mai amfanin mai sabo ko jama’arsa. Idan abin
da aka saba da shi, ba na kirki ba ne, ba a son a mayar da shi turke. Irin
wannan turke shi Hausawa ke ce wa, turke mai caɓo (taɓo) marigayi Alƙali Bello Giɗaɗawa ya tabbatar da:
Idan dabba tana sauri ga turke,
Da amfanin da tas san za ta iske.
(Bargon
Hikima)
Marubuciyarmu ta hango turken da caɓo, don haka take ganin wawa kawai zai saba da shi.
Wane ne Wawa?
Duk da yake an yi ƙoƙarin a fayayce wawa sosai a littafin, ba zai hana a
ƙara wa Borno dawaki ba. Wawa shi ne, wanda bai san
ciwo kansa ba, bai san abin da ke cutar da shi ba, bale mai amfaninsa. Wawa shi
ne, mai kallon mutane cikin wauta a ma’aunin wayonsa na wauta. Wawa ya fi
mahaukaci ban haushi, da ban takaici, ga ayyukkansa, da lafuzzansa, da
tunaninsa. A harshen Hausa, wawa ya fi kowane nau’i na mutane sunaye barkatai
masu fito da sifarsa da ɗabi’unsa da ayyukansa.
Bayan sunansa na yanka “wawa”, shi ne solo, samɓalto, satoto, hauge, sangalaɓe, shashasha, sususu, sakarai, bi-nan, dabba’uuna,
haure, leɓo, saleɓo, hangaham, santoɓilo, talallaɓiya, hoce, gabu, raƙumi, dambalalle, jiɓananne, makananne, ga su nan dai. Da wawa da
mahaukaci da jahili, kakansu ɗaya, iyayensu mata ne suka fito gidaje daban-daban. Rayuwar da yaranmu suke
a kai yanzu ta yi canjaras da faɗar wani makaɗi Zari da ke cewa:
Jagora: Ina nika samun mahaukacin yaro wawa?
Yara: Ya tankwahe wando ya sa ƙafa ramin kura.
Duk wani abu da ya shafi wauta a wajen Bahaushe
abin zargi ne, abin kushewa ne, haraka ce ta komawa baya. Bahaushe bai tanada
wa wawa wani gurbi ba a gurbin rayuwa, face na tir! Da assha! Da kayya! Da
wayyo! Yaro ba ya son magaji wawa. Mace ba ta son miji wawa. Talakka ba ya son
sarki wawa. Sarki ba ya son talakka wawa. Makaɗa Sa’idu Faru cewa ya yi:
Jagora: Wawa bai san gacte ba
:
Don an ce za a ba shi sarki
Yara : Hay yag gama da tuntuɓe.
Gindi: Ya riƙa da gaskiya Muhammadun
Muhammadu
:
Karsanin gidan mai saje shirinka ya yi kyau.
Makaɗa Narambaɗa ya yi shakundun da cewa:
Jagora: Gidan ga mutum huɗu ba su sarauta
Yaro : Da samɓalto da satootoo
:
Shi wanga na ukku ƙazami,
: Na
cikon na huɗunsu hawaa’i.
Gindin: Shiri bajinin Mamuda
:
Abu na Namoda tsayayye.
Wautar Yau a Hankalin Jiya
Hankalin jiya shi ne, tsararren tunani na girmama
gabaci, da riƙon amana, da tsayar da gaskiya, da sanin ya kamata
na kariyar mutuncin mutum, da gidansu, da zuriyarsa, da garinsu, da al’ummarsa.
Hankalin jiya shi ne, kamalar mutum ta aiki da magana, a ji mutum, a ga mutum,
a yarda da mutum. Hankalin jiya, wayonsa gudun kunya, da adawa da ita, da ɗiyanta, da kowane bagire aka san mazauninta ne na
dindindin da na wucin gadi. Hankalin jiya, ba ya shan iska wuri ɗaya da ƙarya, kuma bai taɓa aminta su ƙulla zumunta ba, ko da ta
hanya ce mai gamin zumuntar dole. Hankalin jiya, ba ya da kasala, bai yarda kwaɗai ba, ba su abota da rowa, ba unguwarsu ɗaya da zaman banza ba, har ya ƙaura, ba su ga-maciji da yawon dandi. Zanannen sunansa ladabi, laƙabinsa biyayya, don haka ake yi masa kirari da nagari na
kowa mugu ko sai uwar da ta haife shi. Mutanen jiya sun saba da ɗansu sosai, suka wayi gari a yau, cikin wasu ‘ya’ya
na daban, da babu nagari ga iccen kabari. Allah Ya shiryar da mu.
Wayon yau shi ne, ado da ƙarya babba da yaro. Yaudara samun sa’a. Amana ta koma ganina. Gabaci ya
koma wasan yara. Nagarta ta koma kasala. Kamun kai, ya zama ƙauyanci. Sanin ya kamata ya zama wauta. Biyayya ga gabaci
sunansa gidadanci. Tarbiyantar da yara da ladabtar da su ya zama dabbanci.
Tsare mata a gidajen aure, da kare mutuncinsu, tsohon yayi ne, da tauye musu haƙƙi. Ba su damar gwada tsawo da ƙatta, da zaɓen abokin hulɗa, da tanada musu ma’aikatun renon shaggun da suka
haifa, shi ne cigaba, da ‘yancinsu, a wayon ƙarshen zamaninmu. Tun gabanin Musulunci al’adunmu ba su yarda da hautsinan ƙato da ƙatanya ba, bale yau da rana
tsaka a yi muna sakiyar da babu ruwa. Sa’idu Faru ya tababtar da cewa, ko wurin
buki a tsarin Bahaushe mata da maza zaman ‘yan marina suke yi a faɗarsa:
Jagora: Dogon sarki yana da kyawo
:
Ranar da an ka je daba
Yara : Ya yi
kyau da riguna
Jagora: Shi wanga ɗan gajere
Yara : Ku a
je shi gun rabon dawo
Jagora: Shi kai ma wanga dunƙule
Yara : Shi
kai ma wanga dunƙule
Jagora: Matuƙar wurin akwai mata
Yara : Hat
tuman gadi shikai
Gindi: Ya riƙa da gaskiya Muhamamdun
Muhammadu
:
Karsanin gidan mai saje
:
Shirinka ya yi kyau.
Me Ake Ciki Yau?
Ko kusa ,
hankalin tuwo ba zai yarda da kushe ci gaban mai ginan rijiya da muke ciki a
namu ƙarni ba. Mai hankali duk ya nace ga karatun
jaridunmu, da sauraren kafafen yaɗa labaranmu, da tauraron ɗan Adam da ke shawagi da hotuna da labaran duniyarmu, da wayar hannu da ta
zama lalura gare mu, zai tabbatar da ba ta mutu ba ta ɓalgace. Mai wayo zai gano cewa, an tashi bisa ƙasa an koma a kan daɓe. Mai hankali duk ya san, da lauje cikin naɗi. Duk wani mai bincike zai gano, da walakin goro
cikin miya. Masana sun tabbata an ƙi cin biri an ci dila. Duk mai
hankalin tuwo zai gano ko bayan tiya akwai wata caca. Matsalolin tarbiya da
suka yi muna turnaƙu a yau, na mugun maƙwabci ne, ba ka da mata ana haihuwan ɗiya da kamar ka.
Daga cikin ribatarmu da Nasara suka yi cikin rigar
waɗannan na’urori akwai: koya wa
yaranmu ƙazantattar tarbiyarsu ta neman abin duniya ido
rufe, da bugun gaba da uwa, don a ɗaure wa zina gindi. An koya wa yaranmu fashi da makami, da fashi da muƙami, da tabanjamanci da ɗan kamanci, da kwartanci da aƙidar kowa ya ɗebo da zafi bakinsa. Kyawawan
al’adunmu na aure da haihuwa da mutuwa, an durmuyar da su. Tsarkakakkiyar aƙidarmu ta addininmu a ko’ina an yi mata raɓo, an saka mu cikin ɗemuwar da ta fi dogon suma haɗari. A cikin masalatanmu da maƙaabartunmu da makarantunmu muryoyin wayoyinmu ke cashe kiɗe-kiɗen arna da waƙe-waƙensu na gumakansu da
shaye-shayensu. An mayar da Alƙur’ani da Hadisai da nassoshin
shari’a busan sheshe a wayoyin hannu da sunan kishin addini. Mun manta da
al’adunmu, waɗanda aka ara muna, mun kasa
iyawa. Na tababta waɗannan abubuwa ne Halimatu ke
yi wa shaguɓe da: “Sabo Turken Wawa”.
Muradin taronmu a yau, gano irin illolin da suka
haifar. Da iyaye da hukuma da masana su tashi haiƙan faɗa da su. Ka da a aminta da
kitsen rogo. A rege yaudarar ƙawalwalniya (ruwan faƙo). A fahinci katawar Nasara ta zamani. A lura, kama da
wane ba wane ba ne.
A da, cikin shege abin kunya ne, a yau, ya samu karin magana shege kowa ya
Yi. A da, an ce, gaskiya ka faɗa ba sanda ba. A yau, mun
ce, faɗa da faskiya tsaro ne. Magabata sun ce, namu namu ne, mu
kuwa mun ce, in ka ji namu da mai shi. Addu’ar magabata a koyaushe ita ce,
Allah da Ya ba ka raƙumi ya ba ni Zakara. Mu ko cewa muka yi, Allah da Ya ba
ka raƙumi Ya ba mu wuƙa zakaran ya ci Ubansa. Duk waɗannan musibun da makanantansu cuɗanyarmu da waɗannan na’urorin ya haddasa muna su.
Ina Mafita:
Hausawa sun ce, duk wurin da aka hau
ice nan ake sauka. Tabbasa! Karen da duk ya yi cizo da gashinsa ake magani.
Masu jihadin ƙarni na goma sha tara Mujaddadi Ɗanfodiyo da mataimakansa sun ji muna wannan tsoro tun bai
bayyana ba Uryanan (tsirara). Babu mafita face:
(i)
Girmama namu
al’adu kamar yadda suke girmama nasu. Kowa ya yi doro da al’adun gidansu.
(ii)
Yin garkuwa da
addininmu ga duk wani baƙon abu da zai shigo mu.
(iii)
Daina koyi da
su a kan kowane irin sha’ani, dama kare jini biri jini aka rabu a goshin ƙarni na
ashirin. In babu ƙira me ya ci gawai?
(iv)
Haramta wa
rubuce-rubucensu da wasanni leƙa makarantun da muke koyar da yaranmu tarbiyarmu.
(v)
Fito da wani
sabon salon yekuwar yaƙar rubuce-rubucensu da wasanninsu da suka yi kanta a
zukatan matasanmu kamar irin yadda muka taru a yau.
(vi)
Samar da
Hukumma ta musamman da za ta fuskanci yaƙi da rashin tarbiya da hana baƙin al’adu yin shigan kutse
a ƙasashenmu.
(vii)
Ƙirƙiro darusa a kowane mataki na karatu da za su yi arangama
da waɗannan abubuwa har sai mun ga baya gare su.
Ana cikin Gina ga wutsiya:
Sabon tsarin da ake son a tilasta a
kanmu matsayin addini, wata dabara ce ta
yi muna kwanton ɓauna. Cikin tsarin ake son a tilasta mu watsi da
al’adunmu kyaawawa da addininmu ya halarta muna. Idan ba ku manta ba, da demokradiyya
aka koya wa matan arewa karuwanci. Da ita aka haramta wa musulmi arewa da kudu
kullin matansu. Da ita, aka laɓe aka soke muna shari’ar
mahaliccinmu. Da ita, aka laɓe a yau (2013/2014) aka
haddasa yaƙi a arewancin ƙasar nan da ba a taɓa yin irinsa
mai muni ba ga tarihin ƙasar nan. Gare ta aka laɓe, aka ƙirkiro muna sunan da ba mu sani ba, ana yi muna kisan kyashi dare da rana.
An tozartar da shugabanninmu. An hana muna ‘yancin addininnin da al’adunmu. An
tarwatsa muna tattalin arziki. An mayar da mu saniyar wane cikin ƙasarmu. An yi
amfani da addini da ƙabilanci da ɓangaranci an raba ƙasarmu, an sa
himmar gamawa da mu gadan-gadan. Mun kasa taɓuka komai har sai da Allah Ya kawo rundunarSa ta rusa rundunar zalunci, duk
da haka ba a daina kashe mu ba. Idan ba mu sa wa jikinmu gishiri ba, a zaɓen 2015 tun ba a raba akwatunan zaɓe ba, za a
rautsar da shugaban ƙasa, ya ƙarƙare regowar da guguwar BOKO HARAM da aka ƙirƙiro muna ba ta ida ba.
Wallahi! Sai mun ɗebe bambance-bambancen siyasar ta kowane fati, mun
rungumi fatinmu mai suna, Addininmu, Al’adunmu, Yankinmu da ‘Yancinmu. Wanda
duk ya karɓa wannan kira, shi ne namu ko
da bante ko guntun wando ya baƙunce mu. Wanda ya ce ba haka
ba, ba namu ba ne, komai kaurin alkibbarsa da tsawon gemunsa. Idan tabbatar da
tutar Biafara ya faskara. Kashe Sir Ahmadu Bello kwalliya ta kasa biyan kuɗin sabula. Yunƙurin Gadion Orkah, ya zama kuwa baya ga yaƙi. Almarar BOKO HARAM ba ta biyan buƙatu kudurin 2015 da yardar
Allah. Marubuta, ga sabon fage nan na rubutu da ya fi fina-finai da na’urorin
zamani zama annoba ga arewarmu da ƙasarmu.
Naɗewa
A gai da Halimatu, a girgiza mata da ƙwazonta da hasashenta. A gai da babanmu, kuma shugabanmu,
mai Martaba Sarkin Musulmi ga yin tsayin daka ga jagorantarmu. Mu yi godiya ta
musamman ga mai girma gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Dr. Aliyu Magatakarda
Wamakko ga gagaruman ayyukansa biyu da ya yi wa takwarorinsa fintinkau a
demokraɗiyar zamaninmu: Na farko, kare
martabar Cibiyar Musulunci, Sakkwato na hana matarsa tallar kitso da beje da
sunan First Lady. Allah Ya biya shi. Na biyu, yin fito-na-fito, da
tawaye, ga ƙarya da munafucci da zurmuguɗɗu da kisisiniya ba tsoro ba ja da baya. A bisa
wannan, Allah Ya yi masa jagora mu karɓe goriba ga hannun kuturu. Masu sauraro malamin kiɗa na kiran ku da:
Jagora: Na hore ki gaskiya bari
tsoron Ƙarya
Yara: Mai Ƙarya munafiki Allah su yaƙ ƙi
Jagora: Har yau ba mu ga in da
: An ka yi mai ƙarya ba
Yara: Amma ita gaskiya
: Gani da mutane tay yi
Gindi: Gwarzon shamati na Malam
taron giwa
: Baban Dado ba a tamma da batun banza.
Na gode
Manazarta
Banza, A.M. 2013 ‘Darussan
Daular Sakkwato ga Musulman Nijeriya
na hijirar 1435 AH”. Takardar da aka gabatar a Joint
Youth Islamic Organazation, Zamfara
Satate, J.B. Yakubu Secretariat, (Nuwamba, 4.)
Bunza, A.M. 2013 “Ido Mudu Ne:
Ko Bai Ci Ba Ya San Abin Da Ke
Cika Masa Tumbi,” Takardar da aka gabatar don
walimar Samun muƙamin Farfesa ga Farfesa Aminu
Abubakar Illela, a Illela L.G Secretariat (Dec. 14,).
Bunza 2013 “Muhimmancin Hijira
A Kwanan Watan Musulunci”,
Takardar da aka gabatar ga Ƙungiyar Ɗalibai Musulumai ta Najeriya, Jahar Kabi, a masaukin Shugaban Ƙasa, BK. Dec, 19th.
Bunza, A.M. 2013 “Gurbin Ilimi
ga Haɗin kai da Cigaban Al’umma”,
takarda da aka gabatar a Zauro Development
Association (ZADA) Disamba, 27.
Bunza, A.M, 2013 “Promotable
Promotion Promotes Progressive
Professionalism”. Beingtext of paper presented at
special Fishing Festival Organized in honour of Justice Faruku Hassan Bunza as High Court
Judge, Kebbi State, April, 28th.
No comments:
Post a Comment