Sunday, December 9, 2018

Ƙunar Bakin Wake: Ƙalubalen Tsaron Ƙarninmu



The current security situation in our dear Nigeria deserves our serious attention to arrest the ongoing unpleasant happenings. In Hausa Culture, war is a necessity in unavoidable situations; against all odds, to identify enemy, is key to open up the door to the battle field. Of course, there was never a conflict-free society in human history. However, a promising leadership is an advantage for the peaceful coexistence in any community. At very moment, Nigeria is said to be fighting a battle with unidentified enemies in the name of the so-called BOKO HARAM. The military propaganda that, BOKO HARAM were defeated, can be contested with the booming suicide bombings across the country….

Ƙunar Bakin Wake: Ƙalubalen Tsaron Ƙarninmu
(Duba cikin Tunanin Bahaushe Abin da ya koro ɓera…)

Aliyu Muhammadu Bunza

Abstract:
The current security situation in our dear Nigeria deserves our serious attention to arrest the ongoing unpleasant happenings. In Hausa Culture, war is a necessity in unavoidable situations; against all odds, to identify enemy, is key to open up the door to the battle field. Of course, there was never a conflict-free society in human history. However, a promising leadership is an advantage for the peaceful coexistence in any community. At very moment, Nigeria is said to be fighting a battle with unidentified enemies in the name of the so-called BOKO HARAM. The military propaganda that, BOKO HARAM were defeated, can be contested with the booming suicide bombings across the country. Thus, this paper intends to study the historical genesis of suicide bombing in the opinion of Hausa cultural critics and the possible cultural facts/reasons behind the tragedy. In the discussion, the paper would review the circumstances behind the foreign style in episode. Who are the real actors and their sponsors (if any)? The factors behind suicide bombing in Nigerian context would be critically examined for the attention of security intelligence, the state and the general public. In the opinion of this paper, the definition of the term BOKO HARAM is still under the cloud. In this view, it is very much contestable for the national troops to claim upper hand against the unknown enemies. Persistent suicide attacks are the aftermath of the alleged defeated war that never was. A popular Hausa proverb says: what cause a rat to jump into fire must be hotter than the fire, and thus the questions raised herein are; who is the rat? What is fire? Who is chasing the rat? Why did the rat opt to jump into fire? Certainly, these questions must be addressed in good faith for the suicide bombing to be off rooted right way.

Gabatarwa
            Babu ƙasar da za ta yi wasa da abubuwan da ke yi wa rayuka da dukiyar ‘yan ƙasa barazana ta doge da zama ƙasa ɗaya al’umma ɗaya. Idan aka sa wa kowa ido ya kare kansa, ƙasa ta gama rushewa. Idan hukuma ta kasa yi wa ta’addanci taho-mu-gama, zaman lafiya ya ƙare ga ƙasa. Duk ƙasar da ta yi hannun makafi da zaman lafiya, zancen wani ci gaba bai taso mata ba. Babu shakka, babu yaƙi mafi muni irin na sari-ka-noƙe. Daga cikin sigogin sari-ka-noƙe ƙololuwarsa ita ce, ƙunar Baƙin Wake (ƙundumbala). Ƙasar duk ta yi gaba-da-gaba da ƙundumbala, zancen dangane makamai da sulhu sai dai abin da Allah Ya yi. Dabara kaɗai da ta rage ita ce, bai wa masana damar duƙufa binciken musabbabinsa da gano hanyoyin da za a rage wa belarsa barbaza bira irin ta gama gari. Zuciyar wannan ɗan bincike ita ce, ƙwalailaice musabbabin ƙundumbala, da yadda za a kawar da ita gabanin ta kawar da mu a ƙasarmu ta haihuwa.
Dabarun Bincike
            Ƙudurin wannan bincike cike yake da matsaloli masu yawa. Na farko shi ne, abu mai wuya ne a kai ga wanda ko waɗanda abin ya shafa kai tsaye. Don haka, dabarun sun tsaya ga nazarce-nazarcen ayyukan da aka yi a kan yaƙe-yaƙe da ta’addanci. An sa ido sosai ga rahotannin da ake samu ta kafafen yaɗa labarai na rediyo da talabijin da hanyoyin sadarwar zamani da jaridu da mujallu. An samu ɗan tattaunawa da ‘yan gudun hijira da musibar ta rutsa da su, da wasu da bala’in ya auku a kan idonsu. Da yake tantance labari abu ne mai wuya sosai, na ga ya dace in ɗora binciken a kan wani fitacce ra’i na Bahaushe mai cewa: “Abin da ya koro ɓera ya faɗa wuta ya fi wutar zafi”.[1] A kan wannan tunanin na gina binciken domin tantance musabbabin ƙunar Baƙin Wake a ƙasar Hausa.  
Fashin Baƙin Matsashiya
            Na ɗora matashiyar wannan takardar bisa ga sananniyar ƙissa mashahuriya a ƙasar Hausa. Abin da ya ƙara ɗaukaka ta shi ne, wani gwarzo daga cikin gwarajen adabin Hausa Alhaji Abubakar Imam[2] ya taskace ta a cikin adabinsa da taken: “Ƙunar Baƙin Wake.” Da ta shiga duniyar boko ta barbazu kamar wutar dawa. Ga ɗan taƙaitaccen tsakuren kayan cikin lamarin.
            Wai, wani ɗan sarki ne a koyaushe zai je kilisa ba ya hawan doki sai dai a kawo masa talaka ya hau ya je kilisa da shi. Idan ya hau, zai dinga yi masa ƙaimi da bulala da wulaƙanci daban-daban tsawon yini. An ce, shi kuwa Baƙin Wake, ya rantse duk ranar da hawa ya zo kansa ba za a ƙara hawan wani talaka ba. Da hawa ya zo kansa ranar Alhamis, aka ratso wajen gari wajen ‘yan juyar tukwane. Ya rirriƙe Yarima sosai, ya nufaci wuyar wuta Yarima na ihu! Jama’a na ihu! Baƙin Wake ya daka tsalle, ya yi alkafura cikin wuta su duka suka ƙone ƙurumus!.
Ƙidan Baƙin Matashiya
            Marigayi Alhaji Abubakar Imam fitaccen adiibi ne a duniyar karatun Hausa. Ayyukansa da yawa suna sunsuno ayyukan adabin Larabci domin kasancewarsa masani a fagen Larabci.[3] Tattare da haka, ba mu ji wani masani adabi da ya danganta wannan labari da adabin wata al’umma ba. Wannan ta ba ni damar yanke hukuncin cewa, wannan labari in ya auku haƙiƙa a ƙasar Hausa ya auku. Idan kuwa ƙagagge ne, Hausawa suka ƙago aibinsu bisa ga yanaye-yanayen zamantakewar ƙasar Hausa. Ga dukkanin alamu wannan labarin yana da ƙanshin bayyana bayan zuwan Musulunci ƙasar Hausa.[4] Masu bin diddigin labarun kunne ya girmi kaka suna zaton tsakanin Katsina da Gobir labarin ya tsira.[5] A nawa bincike, an ce, a ƙasar Gobir ne abin ya auku lokacin mulkin Fulani da suka riƙa gallaza wa Gobirawa, sai Baƙin Wake ya ɗauko fansa.[6]
Maƙasudi da Muradin Ƙunar Baƙin Wake:
            Babban maƙasudi ga labarin shi ne, fito da irin mulkin Fir’aunanci na cin zarafin mutane da keta haddin bil Adam da tozartar da marasa galihu. Marasa galihu sun kasa wurin gudu bale wurin ɓuya, kuma babu mataimaki. Da suka fahimci wurin da matsalarsu take, aka samu wani gwarzo daga cikinsu ya sadaukar da kansa domin ƙwato haƙƙin ‘yan’uwansa talakawa ya ba da rayuwarsa ta shiga kundin tarihin gwagwarmayarsu. Bayan da bala’in ya auku sai musibar ta yanke. Babu Baƙin Wake, babu Yarima, dole rufe kundin shari’a. Bidi’ar da Yarima ya ƙago a kansa ta ƙare, bayan wucewarsa babu wanda ya sake jarraba ta.[7] Shi kuwa Baƙin Wake sunnarsa a koyaushe aka yi haa maza haa mata, aka kasa mafita sai wasu su tuna da mazhabarsa su rama gayya da hushi. Ina son a kula da wannan sosai domin shi ne zuciyar ɗan binciken wannan takarda. Maƙasudin ƙunar Baƙin Wake da wukaƙanci gara shahada. Muradinsa kuwa haihuwa ɗaya horon gindi, gani ga wani ya isa tsoron Allah.
Diddigin Sunan ƙunar Baƙin Wake:
            Bayan da muka ji yadda tarihin Baƙin Wake yake a adabi, na so in bi silalen batu in ɗan leƙo ko kamin tarihin Baƙin Wake akwai kalma ko kalmomi masu ruhin ma’ana irin ta ƙunar Baƙin Wake? Hausawa na da kalmomi irin su ƙundumbala da accakwama da marus da alkafura da runtse ido.[8] Waɗannan kalmomi duk suna hararar ma’anar Ƙunar Baƙin Wake domin nuni suke ga kammalawar abu gaba ɗaya mai muni da ba a samu tazarar mazayawa ba, bale a mayar da iri gida.
            Ƙarƙashin inwar karin maganganun Hausawa akwai abin cewa idan aka lura da irin su:
·         Haihuwan guzuma ɗa kwance uwa kwance
·         An ɓata goma ɗai ba ta gyaru ba
·         Bisa kan uwa da wabi
·         Komi ta banjama banjam!
·         Mai rabon ganin baɗi shi gani
·         Biyan buƙata ya fi rai
Ba da daɗewa ba, bayan zuwan bindiga ƙasar Hausa, ‘yan taui sun ƙirƙiro wa bindigar toka kirari irin na ƙunar Baƙin Wake, kirarin cewa yake yi, “Ke gawa, mai ke gawa, abin da anka nuna gawa, gawa uku jere ga juna”.[9]
Waiwaye:
            Idan muka waiwayi adabin gargajiya da na zamani na kowace al’umma, ba a rasa ɓirɓishin ire-iren zantukan da ke da ruhin ƙunar Baƙin Wake ba. Tattare da sanin haka za mu ce, abubuwan da suka haifar da su, su ne yaƙe-yaƙe na siyasa da ƙabilanci da ɓangaranci da sauye-sauyen iko na gidajen ikon duniya. Me ya sa a ƙasar Hasa bayan Baƙin Wake babu wani gwarzo da ya gaje shi? Me ya hana wa Hausawa sha’awa a kan haka? Me ya sa tun zamunan yaƙe-yaƙe ba a samu salo irin na Baƙin Wake ba? Me ya sa a tsarin yaƙi na ƙasar Hausa da tsare-tsaren jihadin da aka gabatar a ƙarni na 19 duk ba a ji duniyar salon Baƙin Wake ba? Ire-iren tambayoyi suka ba ni sha’awar waiwayen tarihin Baƙin Wake da halin da ƙasarmu take ciki a yau.
Tsaro a Bahaushen Tunani:
            A al’adance, Bahaushe na cewa: Tsaron (fakon) kaya ya fi ban cigiya. A fagen magani da warkarwa yakan ce, rigakafi ya fi magani. Idan gaba da gaba ta ci tura, yakan ce, da ƙyar na tsere ya fi da ƙyar aka kama ni. Samun wadata na abinci wani makamin tsaro ne domin Bahaushe ya fahimci annurin fuska kaurin hanji. A ganin Bahaushe, samun wadatacciyar walwala shi ne alama ko su ne manyan alamomin samun tsaro da sukuni a kowane wuri. A koyaushe ake zancen tsaro Bahaushe zai so ya ga:
            Rayukan mutane sun kuɓuta ga kowace irin barazana. Lafiyarsu na da cikakken amincin da za ta amfani rayuwarsu. Tanade-tanade tattalin arzikinsu da siyasarsu da imaninsu da al’adunsu suna da cikakken lokaci na kulawa da su. Da dare da rana matsuguninsa ba ya da shakkar sakewa da shawagi a ciki. Haka kuma, yana da tabbacin duk wani abu da zai yi wa kwanciyar hankalinsa barazana an tanadi abin da zai murƙushe shi.
            Samun irin wannan yanayi a al’adance ke sa Bahaushe kafa gari.[10] Tabbacin waɗannan abubuwa su ka gina ginin ƙasa a zukata. A irin wannan hali kawai iko ke kafa doka a yi mata ɗa’a ala tilas. Irin wannan farfajiyar ce baƙi ke ta kwararowa, ‘yan gudun hijira na neman mafakar siyasa. Kowace ƙasa ta tabbata a haka ta sa wa ta’addanci takunkumi, ta yi wa ƙabilanci tarnaƙi, ta yi wa rigingimun addini kashedi, ta yi cin hanci da rashawa kabari. To, idan haka ta samu, me zai tayar da hankalin batalakke?
Alamomin Rashin Tsaro ga Ƙasa:
            Zuciyar wannan bincike, ƙunar Baƙin Wake rugujewar tsaro ke haifar da shi. A taƙaice, alamomin rashin tsaro na kowane irin zamani sun haɗa da:
1.      Ɓarkewar yaƙi domin sai tsaro ya faskara yaƙi ke ɓarkewa.
2.      Yawan hare-hare ba kai ba gindi.
3.      Zanga-zanga da tawaye da bore barkatai.
4.      Yawaitar sace-sace da fashi da samame da cire.
5.      Yawitar ƙungiyoyin ta’addanci da sunan “ƙwato ‘yanci”.
6.      Bayyanar ƙungiyoyin asiri na tsafe-tsafe.
7.      Bunƙasar ƙungiyoyin ƙabilanci da ɓangaranci da aƙidoji.
8.      Fitintinu da rigingimu irin na addini da aƙida.
9.      Kisan gilla na siyasa da ta’addancin matasan siyasa.
10.   Rarrabuwan kan matsara ƙasa su goyu bayan 1-9).
Kowane ɗaya aka duba da idon nazari daga cikin waɗannan abubuwa goma (10) yana iya tarwatsa ƙasa ya watsa ta ɗai-ɗai. Su duka, daga cikinsu, babu wanda ya kai ƙunan Baƙin Wake guba da dahi da musifa ga ƙasa. Dalilina a nan shi ne, a dubi waɗannan abubuwa d azan lisafa.
Mahara ƙunar Baƙin Wake
            A cikin mahara na zamaninmu kowane jinsu akwai. Akwai mata da maza, kuma mafi yawa matasa, maharani za a ga su kansu ne abin ya shafa, don haka suke son su je da kansu su mutu kuma su kashe su ɗebe haushi.[11] Da abu ya yi nisa suka fara sa ‘ya’yansu.[12] A wasu wurare, su sa yaran wasu da suka farauto.[13] A wani wuri su saka waɗanda suka kama.[14] A halin yanzu, an kai ana saka masu taɓuwar hankali da dabbobi.[15] A tunanin Bahaushe ciwon da ba ya da ja da baya rayuwa yake so. Masu kai hari ba sa da wani tunai illa a mutu har liman. Mu da tunaninmu bai salwance ba, dole mu yi binciken yadda za mu yi wa wannan mugun bori girka. Garayar da ake haɗawa ta kowa ya ɗebe da zafi bakinsa ba ta dace ba, da dai an saurari Sani Aliyu Ɗandawo an fahimce shi akwai abin cewa:
Jagora:             Harsashi makarinka a kwanta.
Yara:               Amma ba gaba-da-gaba ba.
            Kwantawar da yake nufi a nan ba ta miƙa musu wuya ba, a’a a sake wata dabarar yaƙarsu ba da makami ba bala’in ya yi yawa.
Wuraren Hare-Hare
            A sanin Bahaushe, ƙunar Baƙin Wake mutane biyu ta ci, da Baƙin Wake da Yarima. A salon masu zamani da wuraren bauta, da kasuwa da wuraren zirga-zirga, da wuraren shaƙatawa, da gidajen hukuma da na mutanen gari, babu wanda ya kuɓuta. Ala tilas masu kai harin abin ya shafe su, ko dai abokan aƙidarsu ko iayalansu ko masoyansu ko masu agaza musu ko masu fahimta irin tasu ga su nan dai. Wannan wata alama ce ta nuna cewa, sun rasa hankali biyu hankalin tuwo da hankalin ilmi. To, me ya jawo wannan taɓuwar hankali gare su? Gano shi kaɗai zai ceto wannan ƙasa tamu.
Sifofin Masu Hare-Haren Baƙin Wake
            Daji ya riga ya ci wuta, su ya kai gurbi, abubuwa sun rikice, komai lauje ya kama haki ne. A farko-farkon al’amari, fita suke yi irin wadda aka san kowa da ita. Daga baya suka ci gaba da sassakiya, a yi shigar burtu irin na mace cikin maza ko mace ta yi shigar maza, ko a saka sutura irin ta isa, ko sajewa da al’ummar da aka riska, ko shigan taɓaɓɓu ko na wakilan tsaro. Don haka idan dai da akwai wata sifa da aka sani, tasu a da, to yanzu, sai dai a kama mu duka a tsare. Ina son ma’abota tunani su kula da wannan sosai su san cewa, aiki ya yi wa kurege yawa. A tunanin Bahaushe, ƙwararren direba da ya hango ruwan birki sun ƙare, yana aguje, ba ya sake ba motar amana. Wasu tsofaffi da wakilan tsaro suka gano a jiya Litinin 29/2-2016 ba su kwanta mini ba.[16]
Lokutan ƙunar Baƙin Wake:
            A al’adar yaƙe-yaƙe na duniyar mutane, an fi zaton harin ƙundumbala lokacin yaƙi. Idan a fagen daga an rinjayi wasu a kan ɗau fansa a ƙundumbala. Haka kuma, don a raba wa mayaƙa hankali biyu, ana kai harin ƙundumbala a garuruwansu da dukiyoyinsu. Bugu da ƙari, bayan yaƙi a kan kan harin musamman waɗanda aka rinjaya. A ɗan nawa bincike a kan kai harin gabanin yaƙi domin a ci ƙarfi mayaƙan ko a kashe wani jigo ko jiga-jigan yaƙin domin a karya lagon yaƙin. Ga al’ada, idan aka yi wa wani tauraro na addini ko siyasa ko mulki, hukuncin kisa bisa zalunci waɗannan hare-hare za su barbazu su mamaye ƙasa kamar wutar daji. A kowane lokaci aka tsananta musu za su tsananta domin neman mafita.
Nazari ga Shekaru da ƙimar Masu ƙundumbala:
            Daga cikin hare-haren ƙundumbala da ke sukuwa a Nijeriya binciken wannan takarda ya hango wasu abubuwan kulawa kamar haka:
1.      Ba a samu dajjijo makusanci shekaru hamsin ba.
2.      Ba a tantance wata mata da ta fuskanci shekaru talatin ba.
3.      Ba a samu wani fitaccen ma’ilmanci ta kowace fuska ba.
4.      Waƙilan tsaro na ciki da waje ba su a ciki.
5.      Fitattun ‘yan siyasa da amintattun makusantansu ba su a ciki.
6.      Ma’aikatan hukuma da suka kai matakin girmamawa ba su a ciki.
Idan wannan hasashe ya tabbata, ke nan masu ƙundumbala matasa ne da ilminsu da wayonsu da hankalinsu bai kai na hango haɗarin da suke ciki ba. A tunanin Bahaushe, idan abu ya ɓata bai kamata a ce hankali ya ɓata ba. Wa ke sa su aikin? Me ke sa su yarda da ƙundumbala a matsayin fansa? Tantance wannan wani makamin sanin yadda za a fitowa matsalar ne.
Me ya Koro Ɓera da ya fi Wuta Zafi?
            Ma’aunin al’ada bai yarda da cewa, mutum na yanke wa kansa hukuncin kisa ba. Rai ɗaya ne kuma kowa na son ya more wa rayuwa da shi. Idan mai rai ya yanke wauna ga ci gaba da raywa, kuma ya ga tilas sai ya samu ‘yan rakiya a dubi alaƙarsa da ‘yan rakiyar da yake son tilasta wa rakiya. Dalilin Bahaushe na danganta wannan karin magana ga ɓera shi ne, ya karantar da mu cewa, da ƙwari da dabbobi da tsuntsaye da mutane kowa ya san abin da ke iya kashe shi. Da duk aka ga ya tunkari ajalinsa gaba-da-gaba, to da walakin goro cikin miya.
            Mu sa natsuwa mu duba idan kunama ta yi harbi za ta sauya tafiya ta riƙa yin sauri-sauri, domin ta san hukuncinta kisa. Idan mahaukacin kare ya yi cizo zai ruga, sanin da an kama shi sai lahira. Idan kura ta ɗauko dabba ta fi dabbar sauri neman maɓuya domin da masu ita sun Ankara sai dai a yi gawa biyu. A ko’ina maciji ya yi sara ɓoyewa yake cikin ciyawa ko rami, sanin cewa ɗanyen hukunci za a yi masa. Dabbobi da ƙwari ke nan, ina ga mutane masu basira da hankali, a ce su yi gaba da gaba da mutuwa? Bokonmu bai amfani al’ummarmu ba idan muka kasa binciken musabbabinsa da yadda za a magance shi. Daga cikin abubuwan da ke haddasa ƙundumbala akwai:
1.      ɗanyen hukunci
2.      Azabtarwa
3.      Wulaƙanci
4.      Zalunci
5.      Taron dangi
6.      Hararar rayuwa da dukiya
7.      Salon yaƙar ‘yan ta’adda
8.      Farfagandar ‘yan jarida
9.      Katsalandan na ƙasashen waje
10.   Tsoron hukuncin maƙiyi
11.   Siyasa
Ɗanyen Hukunci
            Gaggauta hukuntar da shugabannin adawa da tawaye da ta’addanci da addini da siyasa da ƙabilanci da hukunci mai tsanani irin na kisa shi ne tushen ƙundumbala ga magoya baya. Irin kisan da aka yi wa Muhammadu Marwa Maitatsine da Muhammadu Yusuf Maiduguri sun buɗe ƙofar ƙundumbala. An kama su da rai, ba a gabatar da su kotu ba, aka yi musu ɗanyen hukunci. Me ya haifar da ta’adanci a Libya in ba kashe Umar bn Mukhtar ba? Me ke faruwa cikinta bayan kisan Gaddafi? Wane ƙundumbala ne ba a ba a Iraƙ bayan kisan Saddam? Da Amerika ta fito fili ta ce ta kashe Usama bn Ladan an daina ƙundumbala a Afganistan? Kowane lokaci kashe shugaban jama’a a cikin fushi, ɗanyen hukunci ne kuma bai taɓa faruwa ba, face ƙundumbala ya raka shi. Babu wai, ɗanyen hukuncin da shugaban ƙasa marigayi Umar Musa ‘Yar’aduwa ya yanke na cewa a murƙushe ‘yan Boko Haram da ƙarfin soji, shi ya jefa Nijeriya halin da take ciki yanzu.[17]

Azabtarwa
            A rahotannin da ke bayyana a zahiri, azabtarwar da ake yi kamammu gababin a hukunta su wata makaranta ce, ta koyon ƙundumbala. Da duk aka samu zanga-zanga ko rigingimu musamman na addini wakilan tsaro sun ɗauki su ne wuƙa su ne nama. azabtarwa da suke yi wa kamammu idan sun tsere, ko sun kuɓuta, suke mayar da gami da ƙundumbala kowa ya mutu. Wata shekara wajajen 1982 an kamo wasu yara biyu daga Jega da tuhumarsu da sata zuwa ofishin CID Sakkwato.sun roƙa ka da a kai su saboda sun taɓa ɗanɗanar azabarsu. Aka nace sai an kai su an azabtar da su. Aka saka musu inkwa a hannu aka saka su mota tare da direba da ɗan sanda, sai da aka kawo gangaren Ƙasarawa gab da Sakkwato suka bore, suka auka wa direba, kowa da ke ciki ya mutu. Me ake zaton zai faru idan sun san wuraren da za su riski CID ko iyalansu? Dole a taka wa jami’an tsaro birki ga azabtar da waɗanda suke shiga hannunsu.
Wulaƙanci
            Wulaƙanci a fagen yaƙi ya haɗa da keta haddin bil Adam na fyaɗe da luwaɗi da tozarta iyalan abokan yaƙi da wulaƙanta addininsu. Waƙilan tsaron da ke fuskantar fagen yaƙi sun fi kowa aikata ire-iren waɗannan laifuka. Majalisar ɗinkin Duniya UN a rahotonta na bana 2016 ta tabbatar da haka a CAR da Syria da Afganistan da Iraƙ rahotannin Doron Baga da na Bama da Konduga sun taɓo babin sosai. Ga al’adan ɗan Adam, gara mutuwa da wulaƙanta shi gaban iyalansa ko cin zarafin mahaifansa. Wannan shi ke sa a bi waƙilan tsaro da ƙundumbala tare da masu rufa musu baya yaƙi ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa. A shekarar 2015, a garin Kwasara Jihar Kabi an ce, sojoji suka kama wani Bafulatani da laifin ƙin sauka babur da ya zo wurin bincike. A gaban matarsa suka saukar da shi suka mammare shi, suka ci zarafinsa sosai suka sake shi.
            Bayan ya bar su da nisa, sai ya ajiye matarsa, ya dawo wurin da sandarsa ɓoye. Ya je gun sojan yana tsaye yana taron motoci. Sai da ya tabbatar shi ne, ya kaura masa sanda a wuya nan ya faɗi matacce. Ya yi tsaye yaƙi zuwa ko’ina. Bayan ƙura ta lafa, wani soja ya harbe shi. A ƙarshe gawa biyu aka kawo Birnin-Kabi. ina za a ce yana da makaman da zai je barikin soja? Ai sai dai Allah Ya yi wasu, amma su da iyalansu sun gama mutuwa. Ire-iren haka sojojin taron dangi na UN suka yi wa mutanen Afganistan a cikin motocin sojoji ana mammaran kamammu. Kafafen yaɗa labarai na CNN da BBC da Al-Jazeera da ke sun nuna shi.
Zalunci:
            Zaluncin tsari da zaluncin waƙilan tsaro da zaluncin majiɓinta al’amuran jagorancin ƙasa na haifar da ƙundumbala. Idan mai laifi ya tabbatar ba za a yi masa adalci ba ga abin da ake zarginsa zai zaɓi mutuwa tare da abokan adawa a yi marus matuƙar yana da sukunin haka. Yaƙe-yaƙen da ke gudana a ƙasarmu musamman wanda ake ciki babban muradi shi ne kisa ba a kama a hukunta ba. Shugabannin tsaro da kansu ke ba yaransu umurni su kashe. Dubi misalin wani shugaban ‘yan sanda a zamanin mulkin PDP ya fito a kafafen yaɗa labarai yana cewa, a zaɓen da za a gudanar wurin da duk aka kashe ɗan sanda ɗaya su kashe farar hula ɗari. Idan ƙasa ta koma ƙarƙashin tsaron ‘yan ta’adda irin wannan azabtaccen ɗan sanda me zai hana ƙundumbala ta yawaita?
            A shekarar 2000 an yi tsiyar man fetur a Sokoto, ana kana ‘yan daba masu sayar da mai a kasuwar bayan fage. Sojoji ke zuwa da motocinsu, su karɓe fetur ga ɗan jagwal su je gaba su sayar, su kama mai fetur su hannunta ga ‘yan sanda. Da suka je tashar Illela Sokoto suka tarar da yara biyu ‘yan daba. Soja ya je ya karɓe galan ɗaya da jarka ɗaya yaro ya rungume shi. Da yaron ya ga za a zalunce shi ƙiri-ƙiri, sai ya bulbule galan da ke hannunsa a jikinsa da na soja, ya rungume karkar da ke cike sosai. Daga nan ya ƙwala kiran abokinsa ya ce: “Azara’ilu!” Abokin ya ce: “E”, ya ce: “Kawo ashana aljanna ta samu”. Soja ya yi ta ƙwala ihu da kuka da tsalle da ƙyar jama’ar gari suka ƙwace shi hannun yaron gabanin bayyanar Azara’ilu suka ruga a guje suka manta da motarsu da bindigoginsu. Me za ka ce idan Azara’ilu ya zo da ashana? Yaya za ta kasance idan sojojin sun karɓe fetur, sun saka motarsu, sun doshi ofishinsu? Ga alama can za a yi babbar ƙundumbala a barikin sojoji. Fiye da haka sojoji ke yi cikin rigar yaƙi da ‘yan Boko Haram a gidajensu na gado. Ta’adin sojoji da ‘yan siyasa da SSS ke haifar da ta’addancin ƙundumbala.
Taron Dangi:
            Ya kyautu a san da cewa, idan wanda ake tuhuma da laifu ya rasa mai agaji, to, kowa maƙiyinsa ne, kuma komai lauje ya kama haki ne. A tsarin yaƙi da ta’addancin da ke gudana Arewacin Nijeriya ba a taɓa yin irinsa a duniyar ƙarninmu ba. Da waƙilan tsaro da jama’ar gari duk su shiga rigar yaƙar abokan yaƙi cikin rigar hukuma dole wani abu ya faru. Bayan bambance-bambancen addini da siyasa da harshe da ɓangaranci da wakilan tsaro ke nunawa tsakaninsu da abokan yaƙi, ga kuma ƙattan gari da irin tasu manufa. Wasu kangararrun gari ne, wasu tsofaffin masu laifi ne, wasu suna da adawa da su ta bambancin aƙida da addini da siyasa da dai sauransu. Wannan ke sa a yi mahamunar ƙundumbala a gari, da yara da manya da mata da maza duk ‘yan ƙundumbala su auka wa, a mutu har liman. Dalili kuwa shi ne, sun ga ɗaga zufa waje sauro, gado kazunzumi, zani na ƙyeya. Duniya duka ta zama rana gare su, babu wurin da birbishin inwa yake. Ga ɗan bincikena, hare-haren da ake kai wa masallatai da kasuwa da sansanin ‘yan gudun hijira ba ya rasa alaƙa da wannan. A ce wai mutanen gari ke nuna gidajen waɗanda ake tuhuma da ta’addanci ana yi musu yankan rago da kisan mahaukacin kare. Yaƙar ta’addanci, ta’addanci zai haifar.
Hasarar Rayuwa da Dukiya:
            Kai farmakin bisa kan mai uwa da wabi da ake yi wa ‘yan ta’adda da ƙone-ƙonen dukiyoyinsu da gawawwakinsu wata musiba ce mai dogewa. Wanda duk ya kuɓuta cikin irin wannan rutsi babu abin da zai hana masa tunanin ƙundumbala ya ɗauko fansa, idan ba a manta ba, da aka yi musu irin wannan kwanton ɓauna a Gwoza yayyanka mutanen da suka kama suka dinga yi suna ƙona gidaje. Yaƙi ɗan yaudara ne, dole a kula da dukiya da alfarmar rayuwar mutane domin su ma waɗanda ala rinjaye su ba ƙiyayyar har abada ba ce, ta a share jini a koma was ace. A dubi idan gobara ta kama gidan tajiri dole a riƙe shi, domin idan ya ga ta doshi wurin babbar ajiyarsa sai dai a yi masrus. Idan da tunani, labarin gudun shekara da shekaru ya same ni ya isa misali. A wani gari cikin jihar Kabi da na je binciken wannan takarda na samu wani labari a irin haka a shekarar, 2015. Yaro ne mahaifinsa ya bar masa gona ɗaya kacal. Awon filayen ƙaramar hukuma ya zo kan gonar. Aka saka ta cikin awon, kuma aka ce za a biya shi ‘yan kuɗi da ba su wuce Naira dubu uku ba (N3,000). Kai tsaye, a gaban sarki ya ce: “Wallahi in na san wurin da Boko Haram suke zan gayyato su a yi ƙundumbala kowa ya mutu”. Wannan ba almara ba ce, iyakan gaskiyarsa ke nan. me za ka gani idan ya san za su ɗauke shi, su ba shi albashin da zai rayu da mamakaman da zai zo garin ɗaukar ginansu na gado?
Salon Yaƙar ‘Yan Ta’adda
            Ba ƙarfin makai, da taron dangi, da kashe abokan yaƙi, ne iya salon yaƙi ba. kasancewar a koyaushe aka naɗa jagoran yaƙi da ta’addanci babbar busharar da za a riƙa yayata wa jama’a ita ce: Jiya an kashe ɗari uku, yau an kashe ɗari huɗu, gobe za a gama da labarinsu. A tsarin labarum da ke biyowa bayan artabun da wuya a ji an ce, an kama mutane kaza suna gaban kotu ko ‘yan sanda ba. Mafi sassauci daga cikin salon shi ne, a ce: wasu sun tsere sun tsere sun yi gaba a jeji kaza ko ƙasa kaza. Ga al’dar ‘yan ƙundumbala, mutuwa shahada ce don haka ita kowannensu ke buri. Da sun ji an kashe msu fatar suke, su je su tarar da shahidin su zama shahidai gaba ɗaya. A dubi tsarin fitinar da ta auku tsakanin sojojin Burutai da ‘yan Shi’a a Kaduna. A jaridun Daily Trust da Aminiya ‘yan Shi’a sun tsaro sunayen waɗanda suka rasa rayukansu duka a matsayin shahidai. Ba na yarda da cewa shahidai ne, ko ina musun kasancewarsu shahidai. Me ya sa ba a yi amfani da kalmar tsotsayi ko ƙaddara ko hasara ko rasuwa ko wafati ko mutuwa ba? Dalili shi ne, a ɗanyanta gawagwarmaya zukatan matasa rayayyu a kuma kwaɗaita musu shiga aljanna ba da hisabi ba, don haka wallahi da sauran rina a kaba. Dole a taka wa wakilan tsaro ga kisan gilla da suke yi wa jama’a.
Farfaganda ‘yan Jaridan:
            Wasu rahotanni na kafafen yaɗa labarai suna da haɗari ga tsaron ƙasa kuma suna rayar da aikata ƙundumbala. Gabatar da hotunan gawawwaki na yara da mata da tsofaffi, da nuna irin wulaƙancin da ma’aikatan tsaro ke yi wa farar hula da yadda ake kisan gilla ga wani ko wasu, abubuwan nazari ne. na tabbata da an yayata yadda aka kashe Firimiya Tafawa Ɓalewa da Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello da Janar Murtala Ramat Muhammad da hukumomin zamanin ba sa iya kwantar da tarzomar da za ta biyo baya. Idan ko ta kwantar, ƙundumbalan da zai biyo baya zai sa a raba ƙasa ba ja-ni-in-ja ba. A farko-farkon shekarar 2015 wani hoto da ake nunawa na wasu sojoji na yi wa wasu Musulmi yankan rago ɗai bayan ɗai bisa ɗanyen hukuncin Boko Haram. Idan za a kiyaye daga lokacin harin ƙunar Baƙin Wake ya mamaye Yobe da Gwambe da Bauchi da Kano, har da Sakkwato ofishin ‘yan sanda na Marina ya sha wuta. Ban ga laifin gabatar da rahoto ga yadda aka same shi ba, duk da haka, ai Hausawa cewa suka yi wata magana sarakkuwar baki ce. A tuna ba kowane kunne ya kamata ya ji wani labari be. Me ya sa hukuma ke ɗari-ɗarin fito da adadin waɗanda aka kashe a artabu ba gudun ƙiliu ya jawo balau ba?
Katsalandan Na Ƙasashen Waje:
            Fitinun cikin gida musamman waɗanda suka yi garkuwa da addini bai kamata wani baƙo na waje ya yi masa katsalandan ba. misali idan ana ganin yaƙi da Boko Haram na addini ne ko na siyasa bai kyautu wata ƙasa ta yi ruwa ta yi tsaki a ciki ba. ɓellewar da Emeka Ojukwu ya yi daga Nijeriya ya kafa Biafara an so a ba shi launi irin na addini wanda aka sa jagoran ƙasar a zamanin Yakubu Gowon shi ya tabbatar da kasancewar yaƙin na siyasar ɓangaranci. Da Yakubu Gowon da Emeka Ojukwu duk addininsu ɗaya.
            A gaskiya, ganin irin yadda sojojin taron dangi na waje suka nakkasa Iraƙi da mutanenta, suka gigita Afganistan da ci gabanta, aka tartwatsa Libya da tattalin arzikinta, aka yamutse wa Somalia lissafi da mutanenta, halin da CAR take ciki da wanda aka saka Mali ciki na sa ‘yan ta’adda su ɗauki salon ƙunnar Baƙin Wake. Da dai za a yarda, abin aljihu na mai riga ne maganar cikin gida a bar wa ‘yan gida su fuskance ta da dole ƙunar Baƙin Wake ta lafa sosai. Da zancen ƙasashen waje ya shigo abokan faɗa ya san da an rinjaye shi, ko an kama shi, ba ko a ƙasarsu zai yi hursuna ba, ba a nan za a hukunta shi ba, ba da dokar ƙasarsu za a hukunta shi ba, in an kashe shi ba a garinsu ko ƙasarsu za a rufe shi ba, zai zaɓi zancen Ɗanƙwairo:
Jagora:  Da wulaƙanci gara shahada
            : Ga Musulmi ba illa ne ba.
Tsoron Hukuncin Maƙiyi:
            Da zarar yaƙi ya ɓarke ƙiyayya ta riga ta shiga gaba. Wanda aka akashe maƙiyi ne, wanda aka kama maƙiyi ne. Ƙasar da ake yaƙi ita ke da haƙƙin hukunta hursoninta, mashara’anta su za su hukunta abokan yaƙi. Babu yadda mutum zai yi zaton adalci daga wanda ƙiyayyarsu ta kai ga yaƙi. Babban abin la’akari sojojin da aka yi yaƙi da su, su za su hannunta hursunoni ga ‘yan sanda a rubuta abubuwan da ake tuhumarsu na laifi. Idan aka harari wannan tsarin cikin natsuwa za a ga, ashe ko ba ya daga cikin musabbaban kai harin ƙunar Baƙin Wake a barikokin soja da ‘yan sanda? A tuna, a watan Junairu 2015 da aka gabatar da kakakin PDP a kotu da tuhumarsa da hannu a kan hada-hadar kuɗin sayen makamai, bayan ya rubuta jawabinsa da ya ga kamar ga maƙiyansa zai miƙa rahotonsa sai ya ruge su a baki ya cinye. A watan Fabrairun 2016, Sambo Dasuki ya ɗaukaka ƙara zuwa West African Court  bisa ga zargin cewa, Buhari maƙiyinsa ne ba za a yi masa adalci ba. Hujjar shugaban ƙasa Buhari ita ce, suna iya amfani da belin su yi ɓatan dabo. Ashe idan haka tsarin namu yake, ya kyautu a tanadi wata kotu mai zaman kanta a wajen ƙasa domin hukunta masu laifin yaƙi da ƙasa. Irin dabarun da matasan ƙasa suka ɗauka na ƙunar Baƙin Wake, ko manya da EFCC ta yi wa diran mikiya,a ka, idan suka ga tazara suna ƙundumbala a je can a idar da shari’a.
Siyasa:
            Mantawa da siyasar ƙasa ta yi zafi sosai wani babban kure ne. waɗanda suka tabbatar da asirinsu ba ya rufuwa idan wata gwamnati ta hau kujerar mulki, suna iya ɗaukar sojojin haya na ƙunar Baƙin Wake. Dakubo Asare ya sha alwashin haddasa yaƙi irin na ƙunar Baƙin Wake da harin bomabomai a Arewa idan jam’iyyarsu PDP ba a ba ta damar ta sake hawa kujera ba.[18]  Irin take-taken ‘yan tabbatar da ƙudurin Biafrara suke yi, a ko’ina ake irin wannan yunƙurin harin ƙunar Baƙin Wake shi ne makamin farko. Matsalar da ke cikin siyasar ɓangarancin Arewa da Kudu a Nijeriya wata barazana ce. Wannan ita ta kawo salon karɓa-karɓa ga kujerar shugaban ƙasa a Nijeriya da kafa ma’aikatar kula da raba-daidai na tarayya (Federal Character Commission). Kisan gilla da Koran kare na baƙin haure da harajin ɗebe takaici da wasu jihohin Kudu suke yi wa ‘yan Arewa manuni ne ga hare-haren ƙundumbala. Abin mamaki wani gwamna daga cikin gwamnonin Nijeriya a zamanin Umar Musa ‘Yar’aduwa ya fito ɓaro-ɓaro ya ce ba ya iya kare rayuka da dukiyar ‘yan Arewa a jiharsa.[19]
            Ban ce waɗannan su kaɗai ne ba, amma idan an sa musu idon nazari za a ga biri ya yi kama da mutum. Duk da haka, ya kyautu mu hango, wai me ya sa sai yanzu salon yaƙi irin na ƙunar Baƙin Wake ya shigo ƙasashenmu. Me ya sa can a da duk waɗannan matsaloli akwai su amma ba a samu hare-haren ƙunar Baƙin Wake ba?
Zama da Maɗaukin Kanwa…
            Yaƙe-yaƙe da aka yi na duniya na ɗaya da na biyu ba su haifar da salon faɗa irin na ƙunar Baƙin Wake a Nijeriya ba. bugu da ƙari, yaƙin basasa da ƙasarmu ta shiga ciki bai haifar da irin wannan bi-ta-da-ƙulli ba tattare da sanin ya ƙunshi abubuwa da yawa. Ga ɗan gajeren bincikena, kafuwar Isra’ila a tsakiyar daular Larabawa ya fara fito da ƙunar Baƙin Wake a duniyar Afirka. Fifitar da Larabawa suka yi na ƙwato Falasɗinu da ‘yancin kansu ya kururuta yaƙin sari-ka-noƙe da sunƙuru da ƙundumbala. Fafitikar baƙaen fata na duniyar Turai na daga ciki. Gwagwarmayar ta’addanci da ke aukuwa tsakanin masu addinai Musulunci da Hindu da Kiristanci da Yahudanci wata babbar tag ace. Fina-finan da ake yaɗawa da labaran da ake barbaɗawa cikin kafafen yaɗa labarai na duniya irin su BBC da VOA da France wata mashaƙar baje kolin ta’addanci ne ga masu sha’awa da niyyar yi. Gaskiya rikice-rikicen aƙidu na Shi’a a Afganistan da Pakistan da Syria da Indiya da Masar sun samu kulawa ga matasanmu wanda muka fara ganin soman taɓi a kan kisan gillan da aka yi wa Sheikh Jafar Kano Sheikh Ɗanmaishiyya a Sokoto da Sheikh Albani a Zariya.[20]
Sakamakon Ƙunar Baƙin Wake
            A kowace ƙasa ake gudanar da ƙunar da ƙunar Baƙin Wake zancen zaman lafiya ya ƙare gar eta. Daga cikin abubuwan da za su iya haddasa cikin ƙasa akwai:
1.      Wargaza haɗin kan ƙasa, dole a raba ta kowa ya ɗauki na sa kamar dai yadda ya wakana a Pakistan da Sudan.
2.      Babu shakka, wata babbar ƙofa ce haddasa yaƙin basasa domin wuraren da ake kai hare-haren suna da barazana ga zaman lafiyar al’ummar ƙasa gaba ɗaya.
3.      Yaƙi ne mafi muni da zai hana duk wata hulɗa ta arziki a yi da ƙasa. Da duk zaman jakadanci cikin ƙasa ya faskara an gama rusa ƙasa.
4.      Wata mummunar musiba ce mai karantar da yara ta’addanci domin da su ake garkuwa, da su ake kai hari, da su ake tsare-tsaren halin. A ƙa’idance, koyar da yara ƙanana yaƙi haramun ne a dokokin yaƙi na duniya kuma laifi a al’adance.
5.      Aminci zai fita tsakanin mutane, ƙiyayya ta har abada ta stira a zukatan abokan gaba a wayi gari kowa na tsoron kowa.
6.      Idan yana aukuwa a ƙasa zancen sulhu ya ƙare. Ga al’ada, ba a taɓa samun ɗan ƙunar Baƙin Wake ya bayyana a kujerar sulhu ba. Laifi ne na ƙoli mai shi ba zai aminta ya gabatar da kansa ba domin ya san sakamakonsa. Wanda ya riga ya aikata kuwa iya riga ya mutu tare da waɗanda ya riska labarinsu ya riga ya ƙare.
Sakamakon Bincike:
            Ƙundumbalar Ƙunar Baƙin Wake matasa ta fi shafuwa, su ke kai hari, su ake garkuwa da su. A ɗan nawa bincike ga abubuwan da ake aukuwa a Nijeriya, ba ya da wata dangantaka da wani addini ɗaya. Dalili kuwa da Kirista da Musulmi da ba su kuɓuta ciki ba. Jinsin maza suka fi kai hari, mata da yara ɗaura musu ake yi a sa su ko don dole.[21] Masu shiga da kansu ko sa ɗiyansu, wulaƙancin waƙilan tsaro ya kai musu gaya suka zaɓi da su da ɗiyansu su mutu soja su gaji kangon gida.[22] Masu kai hari a wuraren bauta da matattarar jama’a haɗin guiwan waƙilan tsaro na da farar hula ya tsangwame su, suka zaɓi da su miƙa wuya gara a mutu gaba ɗaya. Hare-haren da ake kai a barikokin ‘yan sanda da soja a fara binciken waƙilan tsaro, in ba su da hannu ciki to, sun yi wani ta’addanci waɗanda suka kuɓuta suka biyo ramuwar gayya. Makaman da ake amfani da sun a kai harin Ƙunar Baƙin Wake sun fi ƙarfin mallakar talakka. Ga dukkanin alamu akwai masu ɗaukar nauyinsu domin biyan buƙatocinsu na siyasa. Dole ba a rasa hannun ƙasashen waje musamman ƙasashen da ke renon ta’addanci cikin rigar addini da masu rayar da shi domin kasuwancin makamansu. A tunanina, babu makawa halin da muke ciki face sulhu idan ba mu son ƙasa ta rabu da sunan ƙabilanci ko siyasa lisafi ya koma baya.
Shawara Ɗaukar Ɗaki:
            Idan muka yarda da Bahaushe cewa ruwa ba sa tsami banza dole mu gano me ya sa su tsami? Bisa ga ɗan sakamakon da na samu a wannan ɗan bincike ya zama dole:
1.      A samar da aiki yi ga matsa domin su ganin suke sun samu aikin yi da ta’addanci ana biyansu.
2.      Babu makawa a tsananta dokar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi. Da yaw a daga cikin masu kai harin da masu tsara musu, ba su bisa hankalin kansu, da ƙwayoyi suke aiki.
3.      Ala tilas a ƙago hukumar da za ta sake zama ta sa ido ga fina-finai da ake shigowa da su na kowace irin al’umma. Bazuwar fina-finan wata makaranta ce ta koyon ƙundumbala ga yara da matasa.
4.      Tilas ƙasarmu ta soke hulɗar jakadanci da kowace ƙasa mai rayar da ta’addanci. A daina kai yaranmu koyon komai a ciki, a kula da waɗanda suka yi karatu a can a hankali.
5.      Kula da bambance-bambancen addinai da siyasar zamantakewa da ɓangaranci da ta harshen wakilan tsaro da za a tura kwantar da kowace irin tarzoma. Da yawa daga cikin wakilan tsaro addininsu da ɓangarancinsu suke yi wa aiki ba ƙasa da dokokinta ba. Kowane irin mutum aka kama da laifi a yi masa hukunci a bayyane kowa ya ji.
6.      Dole a riƙa hukunta wakilan tsaro da ke hukunta shugabannin tawaye da bindigoginsu ba da na kotu ba. A yayata laifinsa, a faɗi hukuncinsa da aka yi masa.
Naɗewa:
            Hausawa na cewa, ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Lallai dubarun harin ƙundumbala babbar barazana ce ga tsaron kowace ƙasa a bangon duniya. Babu wani ƙarfin soje na kowace irin hukuma da zai iya murƙushe shi. Mai musu ya kalli irin taron dangin da aka yi wa Iraƙi da Afganistan da Libya da luguden wuta da ta’addancin da sojoji suke yi wa mazauna jihar Borno da Yobe duk da haka duk abin bai hana ƙundumbala haɓaka ba. Abuwan nan da ke haddasa ƙundumbala sai an fuskance su gadan-gadan an kuma yi tsayin dakan kawar da su. Matuƙar aka ce wakilan tsaronmu ba su da wadataccen ilmi na tsare doka da bin ƙa’idar yaƙi waɗanda suka yi wa ganganci ba za su daina hawa ra’ayin ta’addanci ba. Dole a yi taka tsantsan da waɗanda ake ɗauka ayyukan tsaro, ba kowane tubalen ɗan ta’adda da gogaggen ɓarawo da fitaccen mashayi da rusheshen takkwali za a ɗauka aikin tsaro ba. idan har ma’aikacin tsaro shi kansa yana buƙatar tsaro, wa zai tsare tsaro ga masu tsoron barazanat rashin tsaro? Kasawa ne hukuma ta gayyato ƙattan gari a ba su makamai da sunan banga ta yaƙar ‘yan ta’adda. Idan aka gama da ‘yan ta’adda ina za a saka ƙattan banza da aka gayyato yaƙi? A kowace irin duniya irin haka ta auku tsugune ba ta ƙare wa al’umma ba.[23] Kamar yadda murƙushe ɗan tawaye a fagen daga yake nasara, haka nan ma, tilasta shi dangane makamai a yi sulhu da shi cin nasara ne a kan shi.   






Manazarta
Abubakar, A. Nigerian Mosque Attack Raises ƙuestions Over Army Offensive’ Agencies Frannk-Press 13 August, 2015.
Bugaje, M. H.  2014. “Karin Magana Mahangar Tunani: Nazarin Lokacin Hausa”, Ph.D. Zaria: Ahmadu Bello University.
Bunza, A.M. & Muhammad A. Nofal 2013. Ruwan Bagaja in Perspectives Zaria: ABU Press.
Bunza, A.M. 2009. Naramɗa. Lagos: Ibrash.
Hisket, M. 1984. The Development of Islam in West Africa, New York.
Hisket, M. 1994. The Sword of Truth, Evanston.
Hogben, S.G. 1967. An Introduction to the History of Islamic States of/Northern Nigeria, Ibadan.
Human Rights Watch. “Nigeria Massive Destruction, Deaths from Militay Raid”, 1 May 2013.
Kamaru, J. & Cameron A 1979. Lust to Kill The Rise and Fall of Idi Amin. London: Corgi Books,
Magaji, A. 1980. “Alhaji Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa”Kundin BA, Jami’ar Bayero, Kano.
Maier, K 2000. The House Has Fallen: Nigeria in Crisis, London.
Malumfashi, I. 2009. Adabin Abubakar Imam. Sokoto: Garkuwa Media,
Salkida, A. “The Story of Nigeria’s First Suicide Bomber” Blue print magazine via Sahara reporters, http//saharareporters.com/news/page/story-nigerias-first-suicide-bomber-blueprintmagazine.
Smith, M.  2015.  Boko Haram Inside Nigeria’s Unholy War, I.B. Tauris & Co. Ltd, Sweden Scand Book AB
Zenn J. 2014. “Leadership Analysis of Boko Haram and Ansaru in Nigeria, CTC Centinel (US), February, 2014.



[1] Idan ana son a yi wa wani abu adalci ba ta fuska ɗaya kawai za a dube shi ba. A yi tankaɗe da rairaya sosai cikin haka za a ci karo da sawaba domin Bahasuhe ya ce in ga ɓarawo a dubi na mai kaya. A al’adance, maciji ya fi koro ɓera ya faɗa wuta. Maciji kuwa kashe ɓera yake yi, wai a cewar Bahaushe a jikin ɓera yake gwajin dahin da ya samo daga jikin kwaɗo. Don haka ɓera gudun tserar da rai yake yi, duk wanda ke cikin irin yanayinsa dole a yi masa uzuri.
[2] Domin samun cikakken bayanin rubuce-rubucen adabi na Abubakar Imam a dubi Ibrahim Aliyu Malumfashi, Adabin Abubakar Imam Sokoto Garkuwa Media, 2009.
[3] A dubi aikin Abdurahman Adaro, “Tubalan Larabci Cikin Adabin Ruwan Bagaja” cikin, Aliyu M. Bunza da Muhammad A Nofal ed. Ruwan Bagaja in Perspective, 2013, shafi na 259-275.
[4] Za a sunsuni haka idan aka lura da ranar da aka ce abin ya auku “Alhamis” zancen sunan ranaku addinin Musulunci ya zo da tsarin a ƙasar Hausa. Gabanin Musulunci Bahaushe na amfani da sunayen garuruwa ko wuraren da aka aka haɗuwa wata sabga. Akwai tabbacin yana da lokaci a al’adarsa, domin tabbatar da haka a dubi Hauwwa’u Bugaje, “Karin Magana a Mahangar Tunani: Nazarin Lokaci a Hausa”, Kundin Ph.D. Jami’ar ABU, 2014.
[5] Haka na samu labari ga wasu magabata a Sakkwato. Idan aka dubi sunan mai Mazhabar “Baƙin Wake” da wuya a tsallake Katsina da Gobir, musamman wajajen Sabon Birni, da Maraɗi.
[6] Wata hira da na yi da wani Bagobiri a tashar Illela a Masallacin Umar Ɗanhaɗɗabi ya ce sun cikin ƙasar Gobir ne abin ya wakana zamanin ikon Fulani. Idan haka ne kuwa, za a ce a ƙarni na sha tara ne, wataƙila wajajen riƙon Abdurarrahman Ɗanyen Kasko da Umaru mai Riggango da abubuwa suka  tsananta.
[7] A iya ɗan bincikena, shugaban ƙasar Uganda marigayi Idi Amin kawai ya jarraba irinsa ga Turawan ƙasarsa. Ya tilasta wa Turawa su ɗauke shi saman karaga suna yawon shaƙatawa da shi domin ya rama wulaƙancin da suka yi wa kakanninsu irin haka. A dubi Joseph Kaman and Andrew Cameron, Lust to Kill: The Rise and Falle of Idi Amin, pp.185.
[8] ‘Yan Shi’a na waƙa da kalmar ke bayyana a cikin taken waƙar. “Ƙundumbala za mu shiga”. Kassu Zurmi ya ambaci accakwama a waƙarsa ta Nomau Namaguya a faɗarsa.
Jagora:     Nomau Kyawon faɗa a yo accakwama
                : A kwaɓa ta baƙi ƙirin ta ƙare muku can.
Don ƙarin bayani a dubi Ahmad Magaji, “Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa”, Kundin BA, Jami’ar Bayero, Kano, 1990.
[9] Domin da an yi mata ɗuri da toka sosai idan aka harba ta, sai ta yamutse. Wanda ya harba ta yamutse shi. Abin da aka harba an gama da shi. Sai dai bayan an yi jjinya a ci gajiyar abin da ta harba in an tsira da rai. A ganin Joriki ta ƙasar Aljannare ƙaramar Hukumar Suru, Jihar Kabi na yi hira da sarkin Jirgin garin watan Janairu, 2016 a bakin kogi. Da ya gaya mini shekarunsa na ga ba su isa a ce haƙoransa sun zube kamar yadda na gan su ba. na tambaye shi, ya ce, ai yana sana’ar harbin dabbobi a da, bindiga ce ta wargaza masa baki da haƙora. Wannan ya tabbatar da kirarin da ‘yan tauri suke yi mata.
[10] Zaman lafiya shi ne gaskiya in ji Bahaushe, Malamin kiɗa Narambaɗa ya tabbatar da haka a bakandamiyarsa ya ce:
Jagora:     : Na hore ki gaskiya bari tsoron ƙarya,
                : Mai ƙarya munafuki Allah su Yaƙ ƙi,
                : Har yau ba mu ga inda an ka yi mai ƙarya ba,
Yara:       : Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi,
                : Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
Gindi:      : Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
[11] Wanda ya kawo hari a ofishin ‘yan sanda na Marina Sakkwato da kansa ya yi ƙundumbalar. Sauran sassan jikinsa da aka samu sun tabbatar da shi kaɗai ya yi abinsa.
[12] Wani magidanci da aka kama a Borno, ‘yar cikinsa ya sa. Wai a tunaninsa da sojoji su kashe shi da ‘ya’yansa gara ya tura su ƙundumbala a mutu tare.
[13] An ce a Maiduguri sun sha sace yara suna saka su cikin ƙundumbala.
[14] Yanzu haka ana zargin cewa yaran Chibok da suka kama kimanin ɗari biyu da su suke amfani wajen kai hare-haren ƙundumbala a wurare daban-daban.
[15]  A kasuwar Maiduguri wani mummunan hari da aka yi a shekarar 2014 da wani mahaukaci suka haɗa shi. An ce mahaukacin sanannen ne sosai gawarsa da aka tsinta ta tabbatar da cewa da shi suka yi amfani.
[16] A jaridar Aminiya ta ranar 29/2/2016 an nuna wakilan tsaro sun gano cewa idan matan Kanuri na takaba sukan kwance kitsonsu. Sun lura cewa, yara mata da ake turawa ƙundumbala duk kitsonsu a kwance yake. Ban yarda da wannan ba, domin ana son a danganta ƙundumbala ga Musulmi da Musulunci ne, alhali da Musulmi da Kirista du kana samunsu a ciki. To su ko waɗanda ba Kanuri ba, ba Musulmi ba, yaya za a rarrabe su? Wannan matsala dole a sake bitar ta.
[17] A wata hirada na yi da Malam Mustapha Ɗanjuma Suru ɗalibin digirin M.Sc. Statistics, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ya ba ni labarin wani ɗanyen hukuncin da aka yi a ƙauyen garin Andarai ta ƙaramar hukumar Maiyama jihar Kabi, Fabrairu 2016. Wai wani mutum ake tuhuma da yin gungume da shi da wani Bafulatani. Bafulatanin tun a jeji (daji) ‘yan banga suka kashe shi, suka ƙona shi. Shi kuwa ɗan garin sai da aka shi ƙauyensu gaban iyayensa, iyayen na roƙo a kais hi ga ‘yan sanda, shi da kansa ya ce a kai shi ga CID in an tabbatar da laifinsa a zo da shi gida a kashe shi. ‘Yan banga suka nuna masa motarsu suka ce ita za ta kai gawarsa Birnin Kabi, haka ko aka yi, nan gaban iyayensa aka yi masa kisan gilla da bindigogin farauta da makamai. Wani ɗa zai ji an yi wa mahaifinsa haka bai ɗauki fansa ba? Iren-iren waɗannan ɗanyen hukunci ke sa yaran gari su koyi ta’addanci, ‘yan uwa su yi ɗaukar fansar ƙundumbala. A al’adance, da wuya a samu cikakken mutum cikin banga. Yaya za a hukunta masu laifi ga masu laifi ’yan’uwansu ba a yi laifin da zai share laifin mai laifin ba? irin haka nawa wakilan tsaro suka yi a Borno?
[18] Shugaban ƙasar Janar Buhari a yayin yaƙin neman zaɓe ya yi kira ga gwamnatin PDP ta hukunta Dakubo Asari kan maganganun tayar da tarzoma. A lokacin a wayar hannu ake saka zantukan ta’addanci nasa kowa na ji ba a yi komai ba. To, wa zai musanta cewa ba sa rasa hannu cikin hare-haren ƙundumbala da ake kai wa Arewa domin tabbatar da burinsu na a raba ƙasa ko kowa ya mutu a ƙasa. Kasawar hukuma na kafa kwamiti na musamman a kan waɗannan manyan maganganu babban kure ne.
[19] Bayanin Gwamna Uzor Kalu na jihar Abia na wancan lokaci.
[20] Kisan Ɗanmaishiya Sakkwato an tabbatar da waɗanda suka yi shi, yanzu haka wasu daga cikinsu na tsare. An san aƙidarsu, an san ƙungiyarsu, an san irin makaman da suka yi amfani da su, su san ƙasar da ke mara musu baya. Su aka samu dumu-dumu cikin kisan Sheikh Albani jaridar Aminiya ta wallafa cikakkiyar hira da aka yi da su. Wajen kisan Sheikh Jafar da haɗin guiwarsu aka yi. Dalili kuwa shi ne, da tsarin kisan da lokacin kisan da yadda aka gudanar da kisan duk irin yadda aka gudanar da shi a ƙasashen da ke mara musu baya ne.
[21] A tsarin harin bom na zamani wanda duk aka ɗaura wa jigidar da na’ura za a dinga jan linzaminsa dole ya shiga duk wurin da aka so domin ba shi ke da ikon kansa ba.
[22] A irin ɗan binciken da na yi a kafofin yaɗa labarai da wuraren da musibun suka auku, ta’addancin da sojoji suka yi da shi da na ‘yan Boko Haram.
[23] Irin matsalolin da ƙasashen da suka faɗa musibar yaƙi ke nan. Manyan ƙasashe za su agaza musu da ‘yan ta’addan da za su yi musu yaƙi. In an ƙare yaƙi an ci nasara, in ba a ci ba ƙasashensu nag ado ba za su karɓe sub a dole su tsaya can wurin da suka yi yaƙi. Su kuwa ƙasashen da aka kai wa su, sun san wa aka kawo musu. Da haka ta’addanci zai girku cikin ƙasa a kasa zaman lafiya a ciki. Wannan ita ce matsalar da Iraƙ da Syria da Agfanistan da Somali da Mali da CAR da sauran ƙasashen da ake yaƙi ciki ke fuskanta.

No comments:

Post a Comment