In An Ci Moriyar Ganga A Ba Ta Tukuicin Girma: (Awon
Nauyin Butulci A Duniyar Tunanin
Bahaushe Tsakanin Adabi Da Haƙiƙa)Tunanin Bahaushe da ke cikin karin
maganar: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza”; wani sabon salon faɗa da ‘butulci’ ne
a kaikaice. Don haka, wannan binciken ya yi shimfiɗa da ma’anonin da
kalmar ‘butulci’ ke ɗauka ƙarƙashin harshe da
adabi da al’adun Bahaushe. Don tsettsefe bayani, an gayyato Ƙamusoshin Hausa
fitattu guda uku da na Turanci ɗaya. Wannan ya ba mu hasken fito da fuskoki goma na
‘butulu’ a Hausance. A duniyar Adabin Hausa, an ratsi karin magana 12,
tatsuniyoyi 2, waƙar baka 1, kirari 11, jimillar taskokin adabin 25 ke
nan a kan sikelin awon butulci. A haƙiƙanin al’amari, an
waiwayi shari’o’i guda biyar na butulci da ke gaban kotunanmu masu jiran
hukunci. A cikin kowacensu butulci ya haddasa kisan kai na gilla. A kwakkwafen
shari’un aka waiwayi yadda addinin Musulunci ya harari...
In An Ci Moriyar Ganga A Ba Ta Tukuicin Girma: (Awon
Nauyin Butulci A Duniyar Tunanin
Bahaushe Tsakanin Adabi Da Haƙiƙa)
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
mabunza@yahoo.com
0803 431 6508
Takardar da aka gabatar a babban taron ilimi na
bukukwan sati ɗaya ƙarƙashin Score
Card Committee na Jami’ar Umaru
Musa ‘Yar’adua domin jinjina wa da ban kwana na ɗebe kewar Farfesa Mu’uta Ibrahim Mataimakin Shugaban
Jami’ar mai barin gado, 2015, a Babban Ɗakin
Taro na Jami’ar, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami’ar mai karɓar ragamar mulki
Farfesa Idris Isa Funtua, 2015
TSAKURE
Tunanin Bahaushe da ke cikin karin
maganar: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza”; wani sabon salon faɗa da ‘butulci’ ne
a kaikaice. Don haka, wannan binciken ya yi shimfiɗa da ma’anonin da
kalmar ‘butulci’ ke ɗauka ƙarƙashin harshe da
adabi da al’adun Bahaushe. Don tsettsefe bayani, an gayyato Ƙamusoshin Hausa
fitattu guda uku da na Turanci ɗaya. Wannan ya ba mu hasken fito da fuskoki goma na
‘butulu’ a Hausance. A duniyar Adabin Hausa, an ratsi karin magana 12,
tatsuniyoyi 2, waƙar baka 1, kirari 11, jimillar taskokin adabin 25 ke
nan a kan sikelin awon butulci. A haƙiƙanin al’amari, an
waiwayi shari’o’i guda biyar na butulci da ke gaban kotunanmu masu jiran
hukunci. A cikin kowacensu butulci ya haddasa kisan kai na gilla. A kwakkwafen
shari’un aka waiwayi yadda addinin Musulunci ya harari butulci da butulai. A
kakkaɓen buzun bincike,
an gano sifofi 27 da kowane butulu ke iya siffantuwa da su. A ma’aunin al’ada,
cutar butulci ta fi fitattun cutuka 10 ciwo a zuciyar Bahaushe. Bincike ya ci
nasarar ƙyallaro turakun
butulci 6, wanda ya kira mashaƙatar butulci. A duniyar Bahaushe,
an waiwayi barazanar butulci wurare 10 ga ci gaban ƙasarmu; kana
aka yi daddage na musamman a kan yadda
butulci yake yi wa ilmi zagon ƙasa. A naɗe buzun karatu, an
ayyana yadda za a magance cutar butulci da dambarwarta. A sakamakon bincike, an
ƙyallaro
muhimman abubuwa 6, duk da haka, ƙololuwar cutar
butulci dai kashe wanda aka butulce wa. A ko’ina butulu yake, tare da mutuwa
suke yawo. Kowace cuta butulu ya ɓarka, a saurari wata a gaba, in bai raba
abokin adawa da ransa ba. Ba don butulci ba, da ƙasarmu ta cancanci
ta limanci duniyar zamaninmu a kan kowane fanni na rayuwar duniyar mutane.
Gabatarwa:
Tunanin Bahaushe da ke ƙunshe cikin karin
maganar: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza” kukan kurciya ne.
Zargin maciya moriya ganga ke yi, da baya su kushe ta, su jingine ta, har su
kai ga cuta mata da bakunansu bayan sai da suka dafa kafaɗarta duniyar
lokacinsu ta san da zubin tsawonsu. A
tunanin Bahaushe “ganga” ta wakilci duk wani abu da aka ci, ko ake cin
amfaninsa aka more masa. Tunanin Bahaushe na sarrafa “ganga” a karin magana shi
ne, ita ce muryar makaɗa, ba don ta ba da
makaɗa ba kowa ba ne,
don ita aka san da shi, ita ce tagomashinsa, da ita yake ci.[1]
Abin da duk ya kasance wa mutum da irin wannan matsayi, ya cancanci ya gode
masa, ya yi masa kariya iya ƙarfinsa. Bahaushe sakayawa ya yi da
cewa: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza”, ni kuwa na sauya tunanin
zuwa: “In an ci moriyar ganga, a ba ta tukuicin girma”. Da ma abin da Bahaushe
ke kira shi ne, “Kada a ci moriyar ganga da baya a ce mata koren banza”. A wata
fassara shi ne, idan an ci moriyarta a gode mata, don haka na fassara shi zuwa,
“Yaba kyauta tukuici”. Abin da duk aka ci amfaninsa ya cancanci a girmama shi,
a saka masa da kyautatawa, wannan shi ne “tukuici”. A taƙaice, muradin
Bahaushe ga wannan karin magana shi ne, yi wa “butulai” tawaye da zanga-zanga
da ature cikin ruwan sanyi. Ganin irin yadda “butulai” ke yawaita, “butulci” na
ƙara
tunzura, “butulcewa” ya zama ruwan dare, nake son in ɗora shi a faifan
nazarin al’ada mu ga yadda Bahaushe ya harare shi. Haƙiƙanin wannan
bincike a misalai na haƙiƙa da aka shaida aka ɗora shi an gayyato
sassan adabi domin su mara masa baya kawai.
Dabarun
Bincike:
Matsalar da nake son in waiwaya daɗaɗɗiya ce kuma babu
al’ummar duniya da ta kuɓuta daga gare ta.
Kimiyyar rayuwa ce da kowane ɗan Adam, na kowace ƙabila, da launi,
da addini bai kuɓuta ba. A wata
mahanga, matsala ce da ta dabaibaye halittu masu rayuwar dabbobinsu, ƙwarinsu, da
tsuntsayensu. Don haka, dabara ta farko da na bi ta ita ce, yin nazarin ƙwaƙƙwafi na ratsin
kalmar “butulci” cikin harshe da adabi da al’adun Hausawa. Mataki na biyu,
tsura wa kalmar ido da faɗin ma’anarta a
wasu harsuna na daban. A mahanga ta uku, na yi rangadin gani ga ido, da
tattaunawa da jama’a, da waɗanda abin ya shafa, da ofisoshin wakilan tsaro
‘yan-sanda, da SSS, da kotunan shari’a domin tantance shari’o’in da suka shafi
“butulci”. Na ɗan yi yunƙurin rairaye jinsi
da shekaru da halayyar aukuwar butulci ga butulai, da dangantakar su ga abin da
suka butulce wa. Wannan ta kai ni ga tantance waɗanda musibar butulai ta fi auka wa
a al’adance. A dabarun bincikena, a kowane mataki Bahaushe ne bara ga binciken
kuma babban buri a tantance sakamakon ƙarshe na butulci
ga wanda aka butulce wa da wanda ya yi butulci. Ta haka kaɗai za mu iya
fayyace sakamakon butulci ga ci gaban duniyar mutane a rayuwarsu ta haƙiƙa.
Mene
Ne Butulci?
Kalmar “butulci” fitacciya ce kuma sananniya
cikin kalmomin Hausa. Da wuya a samu harshen da ba ya da ita a kalmominsa wadda
ruhin ma’anarta ya yi kusa da na Hausa. A fassarar Reɓ. G. P. Bargery ya
harari kalmar da cewa:
Kalmar “butulci’
na da ma’anar “rashin godiya’. Namiji da macen kalmar ita ce “butulu” jam’inta
shi ne “butulai’. A Hausar Kabi, ana ce wa jakar ɗura shinkafa “butulu”.[2]
Irin kallon da Ƙamusun Hausa ya yi
wa kalmar bai butulce wa Bargery ba,
domin cewa ya yi:
Butulu suna ne na
jinsin namiji da mace, wadda jam’insa ita ce “butulai” dukkaninsu na ba da
fassara “mutum maras godiya’. Butulci kuwa yana nan a matsayinsa na “rashin
godiya”.[3]
Sanin irin makusanciyar dangantakar da
ake iya samu tsakanin harshen Larabci da Hausa na tuntuɓi masana Larabci
domin ƙarin bayani. A wajen Larabawa ma’ana ko kwatancin
kalmar “butulu/butulci” ita ce “kufrun” wato “Kafirci”.[4]
Da wannan sunan kulkin nassin Ƙur’ani ya ambace ta tun daga ƙissar Shaiɗan da Adamu har
yanzu zuwa bayin da suka biyo baya.
Duk da yake nason da harshen Larabci
ya yi cikin harshen Hausa Turanci bai samu wannan gatar ba.[5]
Amma yadda suka kalli kalmar da sunan ‘betray/betrayal”, biri ya yi kama da
mutum. A fassarar sun ce:
A doguwar fassara
“butulci” na ɗaukar ma’anar
zamba cikin aminci, rashin imani, saɓa alƙawali, tona asirin
wani abu, yaudara, zamba, ga su nan dai. Butulci na ɗaukar ma’anar nuni
ko bayyanar da wani abu da ke ɓoye; butulce wa wuta da hayaƙi ya yi shi ke
bayyanar da ita a gane wurin da take.[6]
Yunƙurin Roɗana Ma Newman a Ƙamusunsu akwai ƙarin haske; domin
cewa suka yi:
Kalmar ‘betrayal’
wadda za a zuba a jimla a matsayin ‘betray a trust’ sun fassara shi da ‘Ci
amana’. “He bretrayed his country” - “Ya ci amanar ƙasarsa”. Idan kuwa
ta sauya zuwa: ‘betray’s confidence’ ta koma, tona asiri.”[7]
Wurin da na ga fassararsu ta ɗan soma ba su ruwa
da na koma ga kalmar ‘treason’ suka fassara ta da ‘cin amanar ƙasa’ sai ma’anar
ta yi tangam da wadda suka ba ‘betrayal’. Betray ta ɗauki ‘butulci’ ya
fi fito da ita ƙuru-ƙuru, ita kuwa treason ta yi zamanta na
‘cin amanar ƙasa’, sai karatun ya fito a bayyane.
Tsettsefe
Ma’ana:
Wannan binciken gaba ɗayansa a kan
kalmar ‘butulci’ aka ɗora shi, don haka
nake ganin dole sai an yi tankaɗe da rairayar kalmar an kai ga haƙiƙanin ma’anar da
bincike zai dafi kafaɗarta ya tsayu da ƙafufunsa. A
ganina, gudummuwar Bargery tana ɗingishi domin taƙaita ma’anar
‘butulci’ ga ‘rashin godiya’ kawai bai yi wa Bahaushe susa gurbin ƙaiƙai a kan yadda
yake kallon ‘butulu’ da ‘butulci’ ba. Irin masassarar da ta kama ma’aunin Bargery
ita ta kama ta Ƙamusun Hausa. Yadda Ƙamusun
Websters
ya fuskanci kalmar akwai wuraren da suka yi canjaras da Bahaushen tunani
musamman da ya kalle ta da ma’anar ‘rashin imani’ da ‘tona asiri’ ko ‘zamba
cikin aminci’.
Waɗannan ma’anonoin duk suna iya bayyana
cikin ƙunshiyar ma’anar butulci amma ba su Bahaushe ke ce wa
“butulci’ ko “butulu” ba. A ganin
Bahaushe, butulci na da fuskoki goma da ake iya rarrabe shi da sauran miyagun
halaye:
1. Ba a samun sa sai
bayan an zauni abu zaman aminci da buƙata zuwa gare shi,
ba shi ke da buƙata ga mazauninsa ba.[8]
2. A samu cin
amfaninsa sosai da sosai har wani ba maciyi amfanin ba ya shaida.[9]
3. A ribaci amfanin,
a yi zara da shi, a yi fice na a zo a gani, wato an kai ga buƙatar kusantar shi.[10]
4. Maciyi moriyar ya
ga ya cika da wanda ya more wa, ko ya yi kusa ya cika da shi, ko ya cika har ya
ga rinjaye a kansa.[11]
5. Samun tabbacin
cikawa ko zaton rinjaye sai a fito gaba da gaba da shi, a yi kirarin ƙarfi ya kawo tsoro
ya ɗebe, ko maraƙi ya cika da
manyan shanu.[12]
6. Ba a kan kirarin
kawai za a tsaya ba, sai a yi tsaye a kushe shi, a ɓata shi, ko a
cutar da shi ta hanyar amfanin da aka samu gare shi.[13]
7. A ƙara matsa lamba a
kafirce masa a yi masa fito-na-fito irin na zanga-zanga a shuka ƙiyayya da shi.[14]
8. A yi kunnen uwar
shegu da dukkanin amfaninsa da aka ci, a mara wa masu adawa da shi baya, in an
ga ya gagara, a ci zarafinsa da zuƙuƙunsa.[15]
10. Babbar buƙata ko buri a
gusar da martabar da aka san shi da ita
ko ɗaukakar da ya yi
ko amfanar jama’a da ya yi ko baiwar da jama’a ke ganin yana da, a maye
gurbinsa da abin da ya shuka, a ga baya gare shi, a yi masa fitsari a kan
kabarinsa.[17]
Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu. Waɗannan ma’aunai goma za mu iya takura su da
faɗar:
Butulu shi ne,
maras godiya ga amfanonin da ya ci ga kowane irin abu. Mai tsananin wutar zuci
ta tukuicin sharri ga kyautar alfarma da gatar da aka yi masa. Mai tsananin son
kai da kishin zucci ga duk wani ba shi ba, sakayyarsa ga kowa ita ce, a ɗeɓe idon sani a sa
na mugunta. Zama lafiya da shi, ba a taimaka masa ya kai ga buƙatarsa ba, da ya
kai ga burinsa, babban maƙiyinsa shi ne, wanda ya dafi kafaɗarsa ya kai ga buƙatarsa. Tukuicin
da zai yi wa macecinsa na fito-na-fito da adawa da gaba da takaici da cin
zarafi da cin dugadugai na ƙurewa da ƙin ƙarawa cikin
makirci da yaudara, na ganin iyaka da ganin bayan macecinsa, shi ake cewa
“butulci”. Assha! An butulce wa: yaba kyauta tukuici.
Butulci
a Farfajiyar Karatun Adabi:
Duniyar adabi ƙawatacciya ce
gewaye da abubuwa na haƙiƙa, ƙunshe da waɗanda ba su ba,
taskace cikin ƙawataccen harshe da aka sarrafa a baka ko a rubuce ko
a aikace irin na wasan kwaikwayo da wasannin gargajiya. A cikin kowane salo na
adabi ana iya cin karo da saƙon “butulci” ko aikin ‘butulu”.
Abin sha’awa, a kowane sashe na adabi “butulu” da ‘butulci” abin kushewa ne na ƙarshe. A cikin
taskokin karin magana da kirari da shaguɓe waɗannan ‘yan misalai suna ba da haske a kan hoton ‘butulci” da ayyukan
‘butulci’.
Butulci
Cikin Karin Magana, Kirari, Salon Magana da Shaguɓe:
(i)
Sai
an ci moriyar ganga a ce mata koren banza.
(ii)
Tuwon
girma miyarsa nama.[18]
(iii)
A
ci gari da kai a ba ka kuturun bawa.[19]
(v)
Godiyar
Maye.[21]
(vi)
Godiyar
‘ya’yan kunama.[22]
(ix)
A
ja mu a kai mu an doki uwar makaho.[25]
(xi)
Mutum
ba ya nunin gidansu da hannun hagu. [27]
(xii)
Bakin
da ya ci ya gode in ba na kaza ba ne.[28]
Butulci
Cikin Tatsuniya da Labaran Gargajiya:
Yadda tatsuniyoyi da labaran gargajiya
da almara da ƙissoshi suka fito ƙuru-ƙuru ga tona asirin
butulu da butulci sassan adabi na karin magana da sauran zantukan hikima ba su
kai can ba. Mu tsura wa wannan tatsuniya ido sosai mu gani:
Tatsuniyar Yaro da
Maciji da Zarɓe da Maharbi:
Wani yaro yana cikin daji ya ji
kururuwar wasu mutane sun koro maciji suna neman su kashe shi. Da macijin ya zo
wurin yaron ya nemi ceto. Yaron ya kwanta, ya buɗe bakinsa ya ce wa maciji: “Shiga
cikin cikina, in sun wuce ka fito ka tafi abinka.’ Da suka wuce, ya ce wa
maciji: “Bawan Allah fito sun wuce”. Maciji ya ce: ‘Ina! Ni na samu wurin zama,
kayan cikinka su ne abincina har sai ka mutu.” Yaro ya dinga kukan fitan rai.
Yana cikin kuka, ya gamu da zarɓe, zarɓe ya tambaye shi abin da yake yi wa kuka, ya kwashe ya
gaya masa. Zarɓe ya ce: “Ka je ka
kwanta a rana ka buɗe baki, in ya ji
zafin rana zai turo kansa waje shan iska in cire maka shi.” Yaro ya bi umurni,
maciji na jin zafin rana ya zaro kai waje zarɓe ya cafke ya zaro shi waje, ya
wurgar. Yaro na mirmijewa ya cafke zarɓe, zarɓe ya ce wa yaron; ‘Me ke faruwa?” Yaro ya
ce: “Ai na samu naman da zan warke mikin da maciji ya yi mini. Da na sha
romonka ai sai in mirmije.” Zarɓe ya koma kuka, suna cikin taƙaddama sai ga wani
maharbi ya zo. Ya tambaye su matsala, zarɓe ya kwashe ya gaya masa. Maharbin ya
fanshi zarɓe ga hannun yaro.
Ya karɓi zarɓe ya sake: zarɓe na jin ya fita
hannun yaro ya faɗa hannun maceci,
maceci (maharbi) na sake shi, sai ya yi caraf! Da idon maharbi ɗaya ya yi sama da
ita, ya kai maharbi durƙushe da ido ɗaya kogon idon ɗaya na zubar jini.[29]
Labarin Wani
Makaho da Wani Mai Doki a Zangon Fatake:
Wani mutum ne mai tsananin tausayi ya
tarar da wani makaho shi kaɗai a zangon fatake ruwan sama na duka ba kowa. Ya je
ya ɗora makahon a kan
dokinsa ya ɗora babbar malfa a
kan makaho maganin ruwa. Suna cikin tafiya, labari ya yi labari, sai makahon ya
tambayi sunan dokin, wanda ya taimake shi ya gaya masa sunansa. Ya tambaye shi
kuɗin da ya saye shi,
da wurin da ya saya, da la’adar da aka yi, da dillalan, duk ya kwashe ya gaya
masa. Shigarsu gari ke da wuya, sai makaho ya aza kuka da ihu! Da kururuwa
cewa, ga mai ido zai ƙwace masa doki. Aka je fada, sarki ya binciki makaho,
ya kawo duk abubuwan da macecinsa ya gaya masa ya faɗa. Aka karɓe doki aka ba shi.
Aka kai makaho gidan baƙi aka sauke, mai doki kuwa aka kai shi gidan Yari
saboda laifin sata. Makaho na cikin holewa cikin dare bayan kalaci, sai ga
bayin Sarki na amana sun zo rangadin gidan.
Da shiga gida, suka riske shi yana kewar samu, yana cewa: “Na samu doki
da malfa da wurin kwanciyar sarauta a banza.” Suka koma suka ba Sarki labarin
abin da suka tsinta. Sarki ya karɓe doki ya ba mai abu, ya kori makaho daga
garinsa. [30]
Butulci
a Rayuwar Mawaƙa:
Mawaƙan baka da
rubutattu ba su tsallake farfajiyar adabi ba ta fuskar karatun “butulci” da
“butulu”. Makusanci daga cikin misalan da zai wakilci mawaƙan baka da
rubutattu shi ne wanda malamin kiɗi Narambaɗa ya ambata a cikin ‘Waƙar Ya Ci Maza” ya
ce:
Jagora: Sarki! Ka ga mutum shidda,
Yara: Babu mai zaunawa lafiya da su.
Jagora: Wanga “azuji” wanga “butulu”
Yara: Guda “ashararu’ guda “maɓannaci”
Jagora: Wanga guda “tsohon munafuki”,
Yara: Akwai wani na nan “mai ƙure mutum”
Gindi: Ya ci maza ya kwan shina shire
Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.[31]
Idan muka waiwayi abubuwan da suka
auku tsakanin yaro da maciji da zarɓe da maharbi dole mu gaskata makaɗa Narambaɗa. Babu wanda zai
zama lafiya da shi. Darasin da ke cikin labarin makaho, da mai doki, wata
babbar ishara ce ta duk wata rigar mutunci da butulu zai saka domin ya samu
wurin zama cikin mutane. Haƙiƙa, wanda duk ba a
wa butulci ba, bai san ciwon batulci ba labarin butulci yake ji. Wanda ya ɗanɗani azabar
butulcin butulu zai ci Narambaɗa gyara ya ce. “Makaɗa lalurar waƙa ce ya sa, ya
saka “azuji” na farko domin su duka shida butulu ne kakansu, azuji da ashararu
jikoki, maɓannaci kama kunne,
tshohon munafuki, tankaɗa hauɗi, mai ƙure mutum taka
kusheyinsu ne”.Yanzu bari mu waiga kan awon butulu da butulci a duniyar haƙiƙa kamar yadda
bincike ya kalato muhimman shari’o’i biyar kamar haka:
Abdulƙadir Usman S. Ɗori Alero A Garin
Kwaifa:
Wannan yaro ma’aikaci ne a Jihar Kabi
a ma’aikatar Kiwon lafiya. Yana sana’ar sayar da kayan masarufi da tufafi. Yakan
shiga ƙauyuka ya ba da bashi, in wata ya yi, ya je ya karɓo kuɗinsa ya ƙara ba da wani. A
garin Kwaifa yana da abokan ciniki da yake ba bashi, aka yi ɗiban wa’adi ba su
biya ba. Don haka, da ya je ƙauyensu suka nemi ya ba su kayan
sallah, ya nemi su biya tsohon bashin da ya ba su. Suka kasa biya, ya ƙi ya ƙara musu. Bayan
da da ya gama abin da yake a garin, ya
yi wa mai masaukinsa goma sha na arziki, sai masu bashin suka game kai da mai
masaukinsa ya gaya musu lokacin da zai bar
garin. Da ya kama hanya, suka bi shi suka kama, suka ɗaɗɗaure shi a kan
babur nasa suka sassare shi sai da ya mutu. Suka jawo fetur daga babur nasa
suka zuba masa, da shi da babur duka suka ƙona su ƙurmus! Sai bayan
‘yan kwanaki aka gano (I.D. Card) nasa da bai ƙone ba a dajin da
suka butulce masa. Yanzu haka butulan na gidan Yarin Birnin Kabi fiye da
shekara uku babu hukunci. ‘Yan’uwan mamaci sun gaji da kai da kawo kotu sun sa
ido.[32]
Alhaji Yahaya
Sa’idu Andarai da Bello Uban Dawaki Ƙwannawa:
A shekarar 2014 wani babban ma’aikaci
(Director Finance) Local Goɓernment
Commission a gwamnatin jihar Kabi, mutumin garin Andarai ta Maiyama Local Goɓt, mazaunin Sokoto
a gidajen gwamnatin jiha. Yana da yaro mai suna Bello Ubandawaki Ƙwannawa ɗan wani hakimi a
Unguwar tsohon filin jirgin sama. Ya yi wa yaron aure, ya gina masa gida, a
aurensa naira N300,000 ya ba shi na hidimar buki, yana sana’a da shi ta gidaje
da filaye. Ya ba yaron wasu kuɗi na sana’a, yaron ya kira shi cewa ya zo an sayi
fili. Gabanin ya zo, yaron ya yi hayar makasa, aka kashe shi cikin gidan yaron.
Aka gina rami tsakiyar falon yaron. Aka
saka gawa a ciki ba sallah balle wanka, aka rufe, aka nemo magina suka shafe
wurin da siminti aka saka babban kafet (darduma) na ɗaki kamar ba a yi
komai ba, aka kawo kayan kaɗe-kaɗe aka ɗora aka ci gaba da shaƙatawa. Yaron da waɗanda suka karɓi jingar kisan duk
suna gidan Yarin Sakkwato, babu labarin kowane irin hukunci.[33]
Wasu Yaran Bunza
da Maigidansu Igbo a Bunza 2014:
Kafafen
yaɗa labarai sun
ruwaito wasu yara da wani Igbo ke hulɗar cinikin magani da su na tsawon shekaru.
Yana bin su bashi sun kasa biya. Da ya zo karɓar bashi suka lallaɓe shi ya je gidan ɗaya daga cikinsu
har ɗakin uwarsa suka
riƙe
shi suka yi masa yankan rago. Suka ɗauki gawar suka kai wajen gari a wata ƙaramar hukuma suka
yar. Asirinsu ya tonu ta hanyar motar da suka ɗauka haya domin su kai gawar daji.
Wannan musibar ta auku garin Bunza, jihar Kabi. An ce shari’ar tana gaban ‘yan
sanda ana bincike kamar yadda aka saba.[34]
Lawwali Gandi da
Maƙwabcinsa 2013:
A jihar Sakkwato a ƙaramar hukumar Raɓah wani Cashier na Ƙaramar Hukumar Raɓah ya gamu da
ajalinsa ta hannun yaransa da yaran da ke koyar da ‘ya’yansa karatun Islamiyya.
Sun shiga gidansa suka kashe shi, suka banka wa gidan wuta, suka ɗauki abin da suke so
suka tafi abin su. Yanzu haka suna gidan Yarin Sakkwato jiran hukunci tun
shekarar 2014.[35]
Tsohon Shugaban
Jami’a (ƁC)
da Yaransa, 2015:
Wani tsohon mataimakin Jami’ar… ya
gamu da ajalinsa ta hannun yaran gidansa da ya riƙe ya ɗauki nauyin karatunsu
su biyu. Da suka buƙaci kuɗin da suka gani gare shi, suka bi dare suka kashe shi,
suka ɗauke motarsa da kuɗin da ke ciki. Da
bakinsu suka tabbatar da cewa, shi ya ɗauki nauyin karatunsu kuma saboda kuɗi suka kashe shi.
An yayata a kafafen yaɗa labarai an nuno
su a hannun wakilan tsaro. Zancen hukunci kuwa, shiru ka ce, an aiki bawa
garinsu.[36]
Duniyar
Butulci a Ma’aunin Siyasar Duniya:
Misalan biyar da suka gabata na haƙiƙa ne da wataƙila ina kusa da su
don haka na shaide su. Waɗansu misalai kuwa duniya
ta shaide su a zahiri, sai dai, wataƙila ba a yi
tunanin aza su a sikelin butulci ba. Gabanin mu kwakkwahe batu ya kyautu mu ƙyallaro irin
butulcin da Kampore ya yi wa Thomas Sankara. Abokan zahiri, Thomas ya jawo Kampore
ya yi masa mataimaki ya sake komai a hannunsa. A cikin wasu jawabansa yana
cewa: “Kampore will be the last man to betray me and our country.”[37]
Me ya wakana? Kampore ya kashe shi ya hau karaga. Irin kusancin Saddam Hussaini
da Tarikh Azeez ya isa misali. Masu addini irin na Tarikh a ƙasar Iraƙ ‘yan tsiraru ne,[38] amma Saddam ya yi tsaye ya yi masa mataimakin
shugaban ƙasa. A ƙarshe, ta hannunsa
aka kama Saddam aka kashe aka tarwatsa ƙasar.
Dangantakatar Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Nzegu abin misali ne.
Nzegu ta hannun Sir Ahmadu Bello ya samu ci gaba gidan soja. Da guguwar butulci
ta murɗi zuciyarsa, shi
ya je har ɗakinsa ya bindige
shi, ya mutu, ya jawo gawar ƙasa giriri har wajen gidan.[39]
Mafasa baƙin tarihi sun ce,
da Bisalla da William Sirry da Bukar Suka Dimka a ƙarƙashin General
Murtala suka samu ƙarin girma. Saboda kusanta, Bisalla da Murtala, kotun
soja ta bi duk yadda za a yi a kuɓutar da shi ga butulcin da ya wakana, an
kasa samun kafar yin haka. Yayin da za a bindige Bisalla ya furta cewa: “Yesterday
I was about to be free, but today for this boy Dimka, Allah Sarki.” Kisan gilla da
Dauda Malam Wanke ya yi wa Ba’are Mainasara butulci ne. Ku tambayi ƙarshen Wanke![40]
Kaico! Butulci ya fi sharri gaggawa, da saurin tafiya, da mayar da gami, da ɗaukar fansa, da
dogon shaƙo da sha yanzu magani yanzu. Wace cuta ta fi butulci?
Tashi tsaye ka nemi maganinta.
Butulci
a Ma’aunin Addini:
A ko’ina mutum yake yana tare da
al’adarsa. A doguwar fassara, al’ada ita ce aƙidar da mutum yake
a kai, ta hani da horo. A buɗaɗɗiyar fassara ƙangin doka ta hani
da horo da samun sakamako ita ce “addini”. Bahaushe ya rayu a tsakanin aƙidun addinai huɗu: addinin
gargajiya, addinin Yahudu, addinin Nasara da addinin Musulunci. A ƙasar Hausa addinin
Musulunci ya fi kanta da amo da rinjaye da yawa da masu aiki. Don haka, da an
ce addini a ƙasar “Musulunci” zai fara zuwa a zuciyar kowane adilin
mai bincike. Addinin Musulunci da Bahaushe ya runguma ya yi wa butulci suna da
“kufurun” wato kafirci. Na kalli abubuwan ta fuskoki kamar haka:
i. Da Allah Ya halicci
Mala’iku, da Adamu, da sauran abubuwa, ya umurci a yi wa Adamu sujuda a
matsayin tukuici ga baiwar da ya yi musu. Nassi ya ce: “Shaiɗan ya yi girman
kai ya ƙi.” Ƙin bin umurni, da takin saƙa da Mahaliccinsa,
da butulce wa ni’imar da aka yi masa Allah Ya ce: “Wa
kaana minal kaafiriina.”[41]
ii.
Halittar
Annabi Isah (AS) ta jefa Yahudawa da Nasara cikin ɗemuwa, don haka
suka ƙirƙiro aƙidar ukuntawa (doctrine
of trinity).
Raba Allah gida uku ya sa, nassin Alƙur’ani ya ce sun
kafirta. Ashe ƙoƙarin takin saƙa da Allah da sama
masa kishiya da yin fito-na-fito da iradarSa ya sa aka kira su “butulai”.[42]
iii. A hadisi an ce, wasu bayin Allah
mahaifinsu ya mallaki taguwa da ita aka ɗauki nauyin gidan duka. Da ita aka yi ɗawainiyoyin Hajji
da Umura da sama wa yara abinci. Bayan rasuwar mahaifinsu suka je da ita Hajji
za su yi hadaya da ita, suka kasa rinjayarta su kayar su yanka. Matsalar aka
kai ta gaban Manzo (SAW) ta bayyana wa Manzo irin butulcin da suke son yi mata,
bayan sun gama cin moriyarta su yanke ta. An ce, Manzo (SAW) ya umurce su da su
sake ta, kuma kada a yi murai a yanka ta har abada.[43]
iv.
A
addinance, idan ɗa ya kashe uba za
a kashe shi, a hana shi gado, saboda tsananin butulcinsa. Idan uba ya kashe ɗa, ba a kashe shi
domin nassi bai yarda akwai butulci a nan ba.[44]
v. A fagen yaƙi na kowane irin
jihadi, a kowane hali mahaifa suka shigo hannun ɗa a matsayin bayi sun ɗiyauta saki ba ƙaidi. Ɗa ba zai auri
mahaifiyarsa ba da matar mahaifinsa da wadda ta shayar da shi nono addinin
Musulunci bai yarda a butulce wa kowa ba.[45]
Ma’aunin
Tantance Butulci Ga Butulu:
Kwakkwahe bakunan waɗannan misalai da
muka gabatar kan butulci suna buƙatar a ɗora su a kan wani
ma’auni da za a tantance mai butulci. Ga ɗan abin da muka gani a kan butulu, za mu
tantance butulci da sifofi kamar haka:
ii.
A
ceto ransa, ya yi sakayya da kashe maceci.[47]
iii.
A
sanar da shi abu ya ƙulla adawar ja-in-ja da masanin da ya sanar da shi
abin, ya yi gagarumar adawa a kushe shi.[48]
v.
Idan
aka kuɓutar da shi tarko
ya shigar da wuyan macecinsa, ya tsallake, ya hau bakinsa da kirari.[50]
vi.
Idan
aka suturtar da shi, ya cire suturar mai sutura da ya ba shi, ya ƙara da nasa, ya
bar maceci tsirara, ya sa a yi masa ature da gayyan wayyo![51]
vii.
Godiyarsa
a koyaushe in ya yi ta, yaudara ce, domin tukuicin da zai bayar muninsa ya yi
muni.[52]
Babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa
bakwai da butulu ya rage. Da za a ɗora shi a kan kalmomin al’ada na hukunta
halayyar masu munanan halaye, bisa ga bitar abubuwan da suka wakana na misalan
adabi da zahiri za mu ce, butulu dai:
1. Mayaudari ne -
nisanci ba shi amana domin duk yadda ya san mutum yana yi masa aibi.
2. Maƙaryaci ne - ba a
shiga ɗaki da maganarsa.
3. Macuci ne - kiyayi
dukiyarka da irlinka.
4. Mahassadi ne - bai
taɓa ɓoye jiyewarsa ba
in ya samu tazara.
5. Munafuki ne - kada
ka yarda ka sake jikinka da shi.
6. Ɗan’ta’adda ne -
nisanci kaɗaita da shi.
7. Maras tausayi ne -
ba su taɓa haɗa hanya ɗaya da imani ba.
8. Maƙiyi ne - komi ya
yi maka shigo-shigo ba zurfi ne.
9. Mugu ne - bai taɓa yi wa sabo da
kusanci ragowa ba.
10. Annamimi ne - duk abin da kuka yi tare, ba shi
yake nufi ba.
11. Mutakabbiri ne - bai taɓa jiran lokacinsa
ba, idan ya ga an ba shi tazara.
12. Ɗan jidali ne -
babu mai zaunawa lafiya da shi.
13. Jahili ne - bai taɓa tunanin komai ya
ruɓa yana wari ba.
14. Wawa ne - mai ganin
kowa wawa a irin wayonsa na wauta.
15. Matsoraci ne - bai gaba-da-gaba sai dai sari
ka noƙe.
16. Raggo ne - bai taɓa ɗebe wa kansa
takaici ba sai ya gayyato abokan kunyata.
17. Maras haƙuri ne - bai taɓa yarda da rabon
kwaɗo ba ya hawa sama
ba.
18. Maras dangana ne - bai taɓa sake wa Allah
abin da ya rinjaye shi ba.
19. Marowaci ne - bai yarda da cewa, yaba kyauta
tukuici ba.
20. Makwaɗaici ne - ko wuta yana lasawa in bai kai
ga masƙin da ke kanta ba.
21. Maras kunya ne - bai taɓa aikin da
sakamakonsa ya kasance madalla ba.
22. Maras gaskiya ne - zantukansa da ayyukansa ba
su taɓa yin daidai da
niyyarsa ba.
23. Sakarai ne - kowa ya san halinsa, shi ko Allah
bai ba shi hankalin sanin halin kowa ba.
24. Baƙauye ne - na ƙarshe, ƙyasuwa da sabara
albarka!
25. Makiri ne - komai ya faɗa ko ya aikata, da
lauje cikin naɗi.
26. Tabanjama ne - bai taɓa kunyar kunya ba,
sai dai kunya ta kunyace shi.
27. Butulu ne - sai ya ci moriyar mutum ya ƙunduma masa
sharri.
Tirƙashi! Butulu ya
cancanci kowane irin kirari na muzantawa da tonon asiri. Me za ka ce, in na yi
masa kirari da:
·
Bunguli
shigan mai ila
·
Talallabiyar
kashi, ba a faɗi ba rai ya ɓaci
·
Mugun
maƙetari
ci baƙi
·
Tsululu
mugun zawo ana karta kana biyar ban hannu
·
Sharri
gaba aka sa ka, kowa ya sa ka baya cim mai kake yi
·
Gizago
ba ka da sabo
·
Ciwon
ciki babu nasiha
·
Cinnaka
ba ka san na gida ba
·
Hannu
na gaisuwa ƙafa na sata
·
Gatari
faɗan kusa da kusa
·
Mugun
tuwon da bai kashe yunwa ana kwalfarka maigida na mutuwa
Kowace sifa daga cikin sifofin nan 27 aka
bi a hankali a cikin adabin baka da rubutacce na Bahaushe za a fitar da hoton
butulu a ciki. Idan aka nuta cikin bincike ga abubuwan da ke bayyana na haƙiƙa, za a ci karo da
su daɓa-daɓa a fuskar butulu.
Waɗannan musibun suka
sa a Bahaushen tunani cutar butulu ta fi ta komai ciwo domin a ɗan awona:
1. Ta fi sata ciwo ga
mai dukiya.
2. Ta fi ƙarya ciwo ga mai
hankali.
3. Ta fi duka zafi a
mutunci.
4. Ta fi yaudara cin rai ga mai zuciyar taimako.
5. Ta fi ƙazafi ɓata suna ga ƙarshen
sakamakonta.
6. Ta fi munafunci ciwo ga mai imani.
7. Ta fi cin nama zafi ga kamilin mutum.
8. Ta fi zamba cikin aminci ga amintacce.
9. Da ita da mutuwa tangam suke ga misali na
zahiri.
10. Ta fi ƙaddara raɗaɗi da zogi domin ƙaddara ta kowa ce,
ita ko ta masu yaƙi da ƙaddara ce.
Mashaƙatar Butulu
Ga alama, mun bi ko’ina mun daddage
domin hana wa butulu da butulci mazauna. Duk da haka, a duniyar tunanin
Bahaushe akwai wuraren da butulci ke shaƙatawa idan an yi
la’akari da cikakkiyar ma’anarsa da aka rairaye. A kowace zamantakewa da za a ɗan jima ana
amfanin juna nan ne butulci ya fi shaƙatawa. A koyaushe
Bahaushe ya yi tunanin butulci a zamantakewa yakan hango zama irin na:
1. Mahaifa da
‘ya’yansu.
2. Ma’aurata (mace da
miji).
3. Maigida da yaronsa
(ko a sana’a ko a ilmi ko a mulki)
4. Zumunta ta jini.
5. Zaman abokai (na
soyayya).
6. Baƙo da mai
masaukinsa.
Irin kusancin da ke cikin waɗannan wuraren
zumunci shida za mu ga, akwai sakewa da imani da juna, da miƙa al’amari ba da
mugun zato ba, da yin hidima ta tsakani da Allah, da wahalar da jiki da samu da
lokaci da basira domin a amfani juna. Ba a zaton a yi wata hidima da zato irin
na ‘yan adashi ko ‘yan biki ko ‘yan ga-aiki. Duk wata amfanar juna da aka yi,
ana yi domin ta cancanta a yi ta, shi ma wanda ake yi wa, haka zai ji a ransa
idan yana da sukuni fiye da haka zai saka. To! Idan aka yi rashin sa’a ganwo ya
birkice da dami, wutar hasada da mugun zama ta ruru, wani ya fara yi wa ganga
kallon koren banza, kai tsaye Bahaushe zai ce; “An yi “butulci”, mai halin a
kira shi “butulu”. A ko’ina batulci ya bayyana, yawo ya tafi wuraren nan shida nan ne mashaƙatarsa ta al’ada
da aka saba jin zarmoɗansa. A irin
wannan kusanci an fi saurin hango rashin godiya, da cin amanar zama, da butulce
wa mafari, da cin zarafi, da rashin ragowa, da jiyewa, da tozarta mafari, da
rashin ragowa da tausayi irin ta wagilin baligi da iskan hunturu ke ratsawa,
kamar yadda makaɗa Gambo ya sifanta
kansa lokacin da yana matashi, wagili ya ce:
Jagora:San da ba ni da tsinka ban da lura
:Ban da ragowa ban da sabo
:Ba ni da imani sa’annan/ ga
raina.
Idan dai ba a ga butulci cikin waɗannan wurare shida
da aka ambata ba, a ko’ina aka gan shi zai iya ɗaukar wani suna ko sifa daga cikin
sifofi (27) sai sunan ya ɗan sha barafasa.
Idan ana neman wuta maƙera ba a same ta ba, aka ci karo da ita masaƙa aka ɗiba, duk dai
sunanta “wuta” sunan muhallin da aka same ta ne kawai ya bambanta da irin
mamakin da ta bayar.
Barazanar
Butulci Ga Cigaban Al’ummarmu A Yau:
Illolin butulci ba ga
rayuwa da dukiya kawai suka tsaya ba. Ga dukkanin alamu, abin ya ci zarafin ci
gaban zamaninmu da zamantakewarmu wanda ke buƙatar kulawarmu ta
gaggawa domin Gumi ta riga ta gamu da Anka. A dubi ‘yan waɗannan ƙorafe-ƙorafe na mai
bincike a kan rutsin butulci da ke yi wa zamantakewar Hausawa barazana a yau.
Malamai
Da Makarantu:
Yadda waɗanda suka ci moriyar ilmin zamani
na farko tun yana da guiɓinsa, ya yi musu
goma na arziki, suka sa ido makarantun na lalacewa babu kowace irin kulawa.
Yadda duniyar zamaninmu ta sa wa fitattun malaman da aka ci amfaninsu ido da
tsufa na wahalar da su ka ce, ba kafaɗarsu aka dafa aka zama abin da aka zama
ba. Wannan butulci ne ko da ba a ce wa gangar ‘koren banza’ ba, domin an sa
mata ido da tsufa da talauci su ƙarasa ta. Assha!
Tir! Haba! Malami uba ne mai siffar uwa ma ba ɗa nono.
Zaman
Karkara:
Yadda ƙauyawan da rayuwar
ƙauye
ta nagartar musu da rayuwa da tarbiya da ƙwazo, ta ba su
damar cin moriyar zama birni. Yau su da ‘ya’yansu ke kafirce wa zama ƙauye, an yi
kaka-gida birane an sauya suna an sake jiki birni ƙauyuka na zama
kangaye.[53]
Sakamakon wannan butulci kunya ta ƙaurace birane ta
sa muna ido da halinmu, zama lafiya ya gagara. Wannan butulci ne na ƙin ƙarawa.
Tsufa:
Yadda muka sa wa gabaci ido su yi yaƙi da tsufa butulci
ne babba. A kowace duniya da wayewar kai ya ratsa, tsofaffi magabata maza da
mata da suka makaro suna da ma’aikatar da ke kula da su, da yi musu hidima na
har abada, har sai lokaci ya yi halinsa. A irin fahimtarmu a sa wa tsufa ido da
gabaci, mai rabon ganin baɗi ya gani. Barin gabaci da tsufa dambe babu mai rabo
babban butulci ne.[54]
Me ya durƙusar da tattalin arzikinmu da rashin tsaro ba wannan
ba?
Zumunta:
A da, zumunta ita ce madafa ga maraya da
marashi da gajiyayye da wanda ya hau dokin ta tsaka mai wuya da kowane irin
mabuƙaci. A yau, an sa ƙafa an shure ta,
matuƙar ba ka da, ba ka da ɗan’uwa, da rashi ya riske ka in kun
fi tururuwa zuri’a kai ne ɗan’uwan kanka. In ka ji kalmomin zumunci na kai da
kawo irinsu baba, babban ƙane, taubashina da dai makamatansu mai furta su mabuƙaci ne, wanda ake
furta wa su yana kan ƙarfen Nasara. Sau nawa ake tsintar jinjirai a kai su
gidajen marayu su rayu a can, alhali suna da iyaye da dangi kowa ya sa gabansa
inda ya dosa, ba ya da wani ɗan’uwa daga matarsa sai ‘yan’uwanta. Me ya taɓarɓare muna tsaro da
taɓarɓarewar tarbiya ba
wannan ba? Sau nawa ana aikata fashi da makami da zai ci rayuwar waɗanda aka yi wa,
kuma a tarar da ‘yan’uwa cikin ta’asar? Ka ce, ɗan’uwanka abinka, su ko ‘yan’uwa su
ce, halinka shi bi ka
Abota:
Ko ba a ce uffan ba, zamanin abota da
miƙa
amana gare ta ya fara wuce wa in bai zurare ba gaba ɗaya. Irin hidima
da kusanci da ɗaukar wa rai da
danƙon
zumuncin abota na mutanen da, a yau sai dai a tsince shi cikin adabi don a
karanta a yi kewar tunanin gabaci. Sau nawa abotar soyayya ko ta siyasa ko ta
addini ko ta wasa ko ta sana’a ke haddasa kisan kai na butulci domin wani
tsohon bashi ko wata buƙatar da ake son a yi bayan aboki ya mutu? Wane butulci
ya fi haka a duniya? Ina za mu je da irin wannan tunani? Yaya za a samu cigaba
aminci bai gabaci zamantakewar abota ba? Butulcinmu ya haifar da wannan.
Taimako:
A da, a addinance da siyasance,
taimako wata babbar gada ce ta ƙarfafa danƙon zamunci da son
juna.[55]
Tsananin butulcinmu ya sa a yau, da taimako ake garkuwa a yi cuta, da zamba
cikin yarda, da 419, da kai hare-haren ƙunar baƙin wake. Da wuya
ka ji an ɓarka wata
gawurtacciyar sata ko ƙasaitacciyar damfara ga mai hannu da shuni ba da
hannun waɗanda ya taimaka ko
yake taimakawa ba. Wane butulci ya kai, sai an yi maka agaji, ka gode, an gode,
ka biyo baya da bi-ta-da-ƙulli na kashe wanda ya taimake ka, ka yi awon gaba da
dukiyar da yake agaji da ita, a bar iyalai cikin rashi biyu, an yi haihuwar
guzuma ɗa kwance uwa
kwance. Butulcinmu ya haifar da yawan marayu da naƙasassu da gwagware
da marasa galihu. Anya kuwa allonmu bai cike da rubutu ba?
Sana’o’in
Gargajiya:
Matakan da magabata suka bi na kashe
fatara da talauci da zauna-gari-banza da ci-ma-kwance da roƙo da bara da
raraka da ci da ceto da ci da addini da mutuwar zuciya ita ce ta ƙarfafa sana’o’in
gargajiya. Yau da noma da wanzanci da kamun kifi da ƙwadago da ujule da
fatauci da sauransu ga matasanmu sun zama ƙauyanci. Waɗanda aka yi
sadakin kakannninsa da iyayensu da wata sana’a ta gado sun yi watsi da ita, sun
wofintar da ita sun shiga cikin masu yi mata shaguɓe da ature.[56]
Mene ne butulci in ba haka ba? Ina ta kai mu yau, in ba sace-sace da ƙwace da ƙeƙeshewar kunya ga
idanunmu ba? Kowace al’umma ta bai wa butulu masauki sai ya yi mata butulci ci
gabanta ya dabirce.
Gaskiya:
Idan ba a manta ba, Bahaushen asali
babbar suturarsa ita ce “gaskiya”. A namu zamani, wayonmu ya muzanta ta. Ta
kasa samun wurin miƙe ƙafafu a gidajenmu da ma’aikatunmu
da masallatanmu da zamantakewarmu. Wannan ya haddasa sai gaskiya ta ceci mutum
ya hau tudun-mun-tsira ya gayyato ƙarya a yi mata
kisan mahaukacin kare. Duk al’ummar da gaskiya ta ƙaranta dole
butulci ya yawaita. Da butulci ya kafa gwannati ƙasa ta gama durƙushewa komai ƙarfin tattalin
arzikinta da ilminta da ƙarfin sojanta. Ƙasarmu ba ta da
ciwon da ya fi na butulci. Ku sa ido ku ga yadda mai gaskiya ɗaya, talaka, ya karɓe mulki ga hannun
hamshaƙan jigajigan masu abin duniya fiye da miliyan ɗari biyu. A cikin
duniyar da ake ciki yau 2014/2015 babu wanda ya kai ɗan Nijeriya sanin
amfanin gaskiya da daɗinta da ƙarfinta da
tagomashinta.[57]
Ƙasar
Amerika da Ingila da Faransa da Jamus da Rasha su ne shaiduna a kan wannan iƙirari.
Tsarin
Siyasa:
Tsarin siyasa ta demokraɗiyya a kan butulci
butulai suka ɗora shi. Tsarin ya
yi takin saƙa da duniyar tunaninmu ta gargajiya da saukakkin
addinai da ya taras na Yahudu da Nasara da Musulunci, aka aminta Allah bai san
matsalolinmu ba, muka shata wa kanmu tsarin da ya dace da tunaninmu.[58]
A koyaushe tunaninmu ƙaruwa yake yi, matsalolinmu na nunka su, tsarinmu ya
kasa yi muna susa gurbin ƙaiƙayi. Idan ba a manta ba, butulcinmu
kwatankwacin abin da ya auku tsakanin Shaiɗan da Ubangiji ne bayan an halicci Annabi
Adamu (AS). Akwai ƙasashen da ba su kai mu arziki ba a da, da suka bar wa
mai komai mai kowa dabara, yau su ke rungume da kwankwason tattalin arzikin
duniya. Ko yanzu ba mu makara ba, mu dai sallami “baba butulu” ya koma ƙauyensu. Babu wai,
hatta da wasan bori da tauri ya fi tsarin da muke a kai daidaitacciyar manufa
ta kare rayuwar jama’a da dukiyoyinsu da mutuncinsu.
Gaba
Ta Koma A Baya:
Tunanin tsantsame hannu gabaci ga
shugabancinmu a sake ragama ga matasa wata alamar taɓuwar hankali ce da
butulcin da muka yi wa gabaci ya haifar.[59]
Kushe hasashen gabaci na faɗar, komai saurin Laraba tana barin Talata ta wuce,
wauta ne. Ko hankalin tuwo ya san, da jiya, da shekaranjiya, da shekaranjiya
ban da jiya duk jiya ce gabansu. Wa zai musunta cewa, da gobe da jibi, da gata,
da citta, duk daga yau aka fara ƙidayar su? Me matashi
ya sani bayan kece raini ya shiga tsara a dama da shi komai ta banjama, banjam?
Su wane ne ‘yan ƙunar baƙin wake, mai rabon
ganin baɗi ya gani? Waye ke
kirarin ƙarfi ya kawo tsoro ya ɗebe? Wane rashin hankali ya fi
abokin yaƙi ya yi iƙirarin, “a mutu
duk har liman!” Ai Bahaushe cewa ya yi: “Abin da babba ya hango a zaune yaro ko
ya daka tsalle ba zai hango shi ba”. Don me ake cewa, “Ana barin na zaune domin
na tsaye?” Wane ne na zaune? Yaro. Wane ne na tsaye? Babba. To, wace dambala ta
kai ga barin na zaune domin na zaune? Ban ga wata basira cikin faɗar; ana barin na
tsaye domin na tsaye ba. Ƙasashen da ba su butulce wa al’adunsu ba, zancen sa wa
matasa ido da rayuwar al’ummarsu ba ta taso ba.
Nauyin
Butulci A Sikelin Ilmi Da Cigaban Ƙasa:
Ɗan abin da na rego
gabanin wannan ɗan bincike shi ne,
yadda butulci ya taka rawa wajen rusa ƙasarmu a yau. Na
so a nan, in ɗan yi tsakure a
kan dangantakar butulci da taɓarɓarewar ayyukan ci gaban ƙasa. A tunanina,
dukkan ayyukan ciyar da ƙasa gaba “ilmi” ne cibiyarsu. Idan butulci ya rasti
wurin da ake bayar da ilmi, ba zai ƙyale masu bayar da
shi ba. Idan masu bayar da shi suka shaƙi gubar hayaƙinsa za su sunsuna
wa masu karɓarsa (ɗalibai), daga nan
kuma ƙasa ta kai sin waw raa takuri sai durƙushewa.
Ƙololuwar sirrin
ilmi ita ce nagartattun kayan aiki da ƙwararrun masu
bayar da shi amintattu. Matuƙar an samu haka komai ya yi an ba
gwauro ajiyar mata. Nagartattun kayan aikin ilmi ba su kai ƙwararrun masu
bayar da shi muhimmanci ba, a ƙa’idance. Butulcin da ya shiga
cikin ilmi shi ne “Maguɗin Jarabawa”. Babu
butulcin da ya kai malamin da aka koyar, ya gane abin da aka koyar da shi, ya
karɓi takardar shaidar
ya cancanci ya koyar ko ya yi aiki a kan abin da aka koyar da shi, ya dawo yana
yaudarar al’umma yana bayar da takardun shaida ga waɗanda ba su
cancanta ba, ya saka al’umma gaba ɗaya cikin hasara. Idan butulci ya ratsi
gandun ilmi an gama da ƙasa gaba ɗaya domin:
(i)
Tattalin
arzikinta gaba ɗaya ga ilmi ya
dogara.
(ii)
Makarantun
koyar da kowane irin aiki ilmi ne jigonsu.
(iii)
Kiyon
lafiyar ƙasa ƙashin bayansa ilmi.
(iv)
Fasaha
da kimiyya da ƙere-ƙere ilmi ne tsarinsu.
(v)
Tsaron
ƙasa
da gudanar da tsare-tsarenta ilmi ke tsare da shi.
(vi)
Kowace
musiba ta shafi al’umma da ƙasa da ma’ilmanta za a fuskance ta,
idan ta buwaye su sai a sa wa mai yi ido.
Wataƙila don ganin ɗan biyan da ake yi
wa masu bayar da ilmi bai taka kara ya karya ba, ko kuma ganin garaɓasar wasu wuraren
aiki saɓanin nasu sai
butulci ya shige su. Illar da wannan butulci ya yi ƙasashenmu na da
yawa. Daga cikinsu akwai:
(i)
Taɓarɓarewar shugabanci
na gaba ɗaya daga sama har ƙasa, ka ce ba a taɓa shaƙa ƙurar allin karatun
boko ba.
(ii)
Fasahar
rubutu da karatu an yi kusan rasa ta ga waɗanda ke da shaidar ƙare karatun
firamare da gaba da firamare.
(iii)
Takardun
shaidar digiri ba su kai nauyin na makarantun sakandare ba.
(iv)
Manyan
takardun digirin MA, MPhil, PhD a yau da wuya su gwada tsawo da takardun
shaidar digiri na magabatansu.
(v)
Shaihunan
masana sun yawaita an kasa fitar da suhe wuta a kowane fanni na bincike, domin
kama da wane ba wane ba ne.
A taƙaice yau,
butulcinmu ya kai ga takardun shaidar ƙare karatu ke da
muhimmanci ba karatun ba. Kwalayen digiri nawa na ƙarya ake fasa ƙwaurinsu zuwa ƙasarmu a cutar da
mu da al’ummarmu mu sa ido? Likitocin ƙarya da lauyoyin ƙarya da
injiniyoyin ƙarya da masanan ƙarya da kwalayen
digirorin PhD na ƙarya da ke cikin ma’aikatunmu da jami’o’inmu kaɗai sun isa su durƙusar da ƙasar nan. Yayin da
mai koyo da wanda ke koyarwa duk jigonsu wanda bai koya ba, yaya za a yi a gano
abin da ake son a koya? Sa wa wannan ido ba taimakon ƙasa ba ne, tsayin
daka a tantance takardun kowane irin mai aiki ba ƙulla sharri ba ne,
kwance sharri ne, domin maganin sharrin da aka tanka/ƙulla. Butulcin da
ke a nan shi ne, waɗanda ya kamata su
yi tsaye a yi bincike, su ke ba da takardun na ƙarya. Waɗanda za a su yi
binciken takardunsu ne ake son a yi bincike. Masu ba yara takardun shaidar
karatu ba su da takardun shaida. To! Mai sahihiyar takardun shaida ya sa ido a
ci gaba da aiki da takardun ƙarya, ya yi butulci. Dole mu yi wa
kanmu adalci, in muna son adalci ya gudana ƙasarmu.
Tanade-Tanaden
Al’ada Na Kare Butulci:
Haƙiƙa babu al’ummar da
ba ta da butulu. A kowane wuri aka samu butulu dole butulci ya bayyana. A
ma’aunin bincike, da za a magance butulci gaba ɗaya da duniya ta zauna lafiya. A
irin rutsin da na ƙyallaro butulu da ire-iren musibunsa, hanyoyin da za a
bi a narka gubar ƙullun butulci a zukatan waɗanda ake butulce
wa su ne:
(i)
Mutane
su ilmantu da cewa, akwai butulu, akwai butulci, kada a yi sakaci da sanin haka
cikin kowane irin al’amari na duniya.
(ii)
A
cikin kowace hulɗa da zamantakewa
ta duniya mai hankali ya yi shirin ko ta kwana ga kutsen butulcin butulu.
(iii)
Kada
tunanin butulu da butulci ya zama sanadin barin taimako da kusantar mutane, a
dai yi taka tsantsan da sanin akwai su. Kada cutarsu ta hana a ceci wani.
(iv)
A
al’adance, komai za ka yi ka san dalilin da ya sa za ka yi shi. Dalilin ka shi
ne maganin dahin da butulu zai harba domin ba don shi aka yi ba, butulcinsa shi
zai cutar ga sakamakon da zai riska.
(v)
Masana
sun ce, yana da kyau mai wayo da hankali a koyaushe ya saɓa wa tunanin masu
ganin sun san shi ga abin da suke ganin yana iya yi ko zai yi. Idan katawar
‘yan-sa-ido ta kasa samun makarin wurin kamu ga ƙafafunka ka sha
maganin batulcinsu.
(vi)
A
gudunmuwar adibban Larabawa cewa suka yi: “Abubuwa uku korarru ne a duniya babu
su: Dodo da Hijilma da aboki na har abada (wato amini na ƙarshe)”. In an sha
wannan ɗan magani wataƙila a samu
riga-kafi.
Sakamakon
Bincike:
A rayuwar ɗan Adam, komai zai
aikata yana son ya ga sakamakonsa domin tantance shi sosai. Dalilin da ya sa na
yi wannan bincike shi ne, ɗora duniyar almara da ta zahiri domin a kyautata zaman
ta zahiri soasai, a samu ci gaba ciki. A ɗan abin da na hango a wannan bincike na
lura da cewa:
1. Butulci ya fi amo
sosai a duniyar siyasa musamman ga masu mulki da aminansu na tsaro ko tafiyar
da mulki. Butulcin da ke bayyana a nan bai taɓa barin mai mulkin kan karaga ba,
bale rayuwarsa. Idan ba a kashe su ba, sai bayan sun sauka kujera butulcin
butulai ya bayyana.
2. Butulcin da ke
aukuwa a abota ya fi na ɗa da uba da
mahaifa ko mata da miji ko mai masauki da baƙonsa muni. Abotar ƙarshen zamani tana
cike da matsalolin da sun fi gaban hankali ya yarda da aukuwar su. Butulci
tsakanin iyaye da ɗa, ɗa ne mai laifi.
Tsakanin miji da mata raba aure na maganinsa. Tsakanin baƙo da mai masaukinsa
na ɗan lokaci ne. To!
Na abota ya fi muni domin shi ake kira da ta ciki na ciki, da lauje cikin naɗi, zama da
kusurwa, zaman ‘yan marina, ba a iya saurin tantance shi sai ɗaya ya zama
sanadiyyar mutuwar ɗaya bisa ƙyashi da jiyewa.
3. Babu cigaban da
butulci ba ya rusawa domin shi ke tarwatsa haɗin kan jama’a kowa ya sa kansa
daban. Wannan ne dalilin da ya sa dokokin ƙasashen duniya
suka saka masa hukuncin kisa ga mai shi kai tsaye babu tara balle ɗauri (treason).
4. Butulci karatunsa
na tushe ƙofar taimako da agaji ga mutane. Gajiyayyu da marasa
galihu da mabuƙata da marayu dalilin tagayyararsu a duniyar zamaninmu
shi ne butulci. Wanda duk ya karanci butulci sosai da sosai yana jin tsoron ya
je taimako sai an nemi taimakon a taimako shi.
5. Butulci na sa rashin yarda da rashin natsuwa
da tsoro a zukatan jama’a. Wannan zai rarraba haɗin kai, da zarar haɗin kai ya wargaje ƙarfin jama’a ya
ragu.
6. Butulci na haifar da mummunan ƙarshe da ɓata zumunci da ɓata zuri’a gaba ɗaya domin a al’ada
cutar butulci da wuya a manta da ita a rayuwa.
7. Bala’in butulci ya fi auka wa masu hannu da
shuni da masu tausayi ga musibun da ke auka wa jama’a. Wanda duk belar ta rutsa
da shi, an ba shi tsoron sake tunanin sake jiki da abin hannunsa ga jama’a. A
koyaushe tunaninsa sau ɗaya gyaɗar makaho ke ƙonewa.
8. Bisa ƙiyasi, jinsin
mazaje sun fi mata butulci, kuma matasa sun fi yawa a ciki, haka kuma sai
hasken ilmi ya bar farfajiyar tunani ake auka wa butulci.
Naɗewa:
Ba taimako ke da ciwo ba, tukuicin
butulci ke da ciwo. Ciwon butulcin butulu na ɗan lokaci ne, don haka kada ya
rafashe ka ga taimakawa. Da ɗai butulu zai tuna da: Ba ka tunɓuke sarki ka yi
Sarki, zai tabbatar da ƙarshen ƙaiƙayi kan masheƙiya yake komawa.
Rashin tunawa da akwai ranar ƙin dillanci shi ke sa a manta da
cewa, ba a san tabkin da ke makara da ruwa ba. Karatun da ke cikin saƙon munafucin Dodo
yakan ci mai shi, shi ya tabbatar da abin da duk ka shuka shi za ka girba. Dole
mai samu ya kawar da kai ga rama cuta ga macuci ibada, domin faɗar kowa ya yi
zamba kansa ya yi wa ya share wancan nassin. Kai dai a matsayinka na mai
hankali da wayo, ka riƙa sara kana duban bakin gatari. Duban bakin gatari shi
ne, a gyara yau don gobe. Da butulci wata hajar talla ce, da sunansa ya yi
tagomashi cikin taskokin adabi da al’ada. Mai wayo a koyaushe ɓoye tunaninsa yake
sai ya ga na sauran abokan tafiya, domin ya san gaggawa ba ta kunu. Ilmin da
muke da shi na ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, shi ya sa
muna natsuwar hango komai nisan dare gari zai waye, sai gari ya waye za a fara ƙyarga sunan
ranaku, don haka butulu ka sani komai saurin Larba tana barin Talata ta wuce.
Wannan lisafin haka yake a garin kowa sai garin da baba Litinin da Talata. Bisa
ga darzajen karatun da muka yi, za mu iya taƙaita taƙaitaccen sakamakon
butulci da cewa idan za a naɗe nazarin bitar karatun sakamakon nazarin butulci a
ce:
Butulci ƙololuwar hasada ce
da wauta ta ƙiyayya da ƙyashi da son kai
suka haifar. Musibarta idan ta shafi mahaifa tana da alaƙa da taɓuwar hankali ga
mai ita. Ga masu tausayi da ba da agajin gaggawa, ganwo kan birkice da kaya. Ƙarshen sakamakonta
ga masu hali da abokai da masu mulkin da masu gida da yaransu, ta fi haifar da
ruɓushin dukiya da
rayuwa cikin ƙazantaccen artabu na rashin tausayi da nuna rashin
sani da sabo da ragowa. A zamaninmu, ba ta taɓa kai hari ba ta risga da rayuwa da
dukiya gaba ɗaya ba. Haka kuma,
taurarin butulci su ne waɗanda ake amincewa
tare da dogon zamani na zamantakewar kyautatawa.
MANAZARTA
Abraham, R. C. 1946. The Dictionary of the Hausa Language. London:
Hodder and Stoughton.
Awde, N. 2006. Hausa-English Dictionary. Longman, reprinted.
Bargery, G. P. 1933. A Hausa-English Dictionary and English Hausa Ɓocabulary. Zaria: ABU Press.
Bunza,
A. M. 2009. Narambaɗa. Lagos: Ibrash
Islamic Publication Center.
Bunza, A. M. 2014. In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen
Gambo. Cairo, Egypt: Elkods Printing House.
Bunza,
A. M. and Nofal, M. A. (ed.) 2013. Ruwan Bagaja In Perspesctiɓe: Eight
Decades of a Hausa Masterpiece in Prose 1933-2013.
Published
by Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity, Katsina and Uniɓersity
of Cairo, supported by Tertiary Education Trust Fund (TETfund) Nigeria.
Bunza, A. M., Gobir, Y. A., Sallau, B. A. (eds.) 2013. Taɓarɓarewar
Al’adun Hausawa (The Detrioration of Hausa Culture).
Published by History and Culture Bureau, Katsina State, and Umaru Musa
‘Yar’adua Uniɓersity, Katsina.
Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya. 2006. Ƙamusun Hausa. Wallafar Jami’ar Bayero Kano.
Gummi, A. M. 1979. Alƙur'ani
Maigirma Da Kuma Tarjamar Ma'anoninsa Zuwa Ga Harshen Hausa. Wurin da aka Tanada Musamman na Sarki Fahad don buga Alƙur'ani mai girma, Saudiyya.
Hubbard,
P. J. 1973. “Education under Colonial Rule: A History of Katsina College
1921-1942”, PhD Thesis, Madison: Uniɓersity
of Wisconsin.
Magaji, A. 1999. “Kunya da Mutunta Mutane a Al’ada.” cikin Hausa
Studies. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Mani,
A. 1966. Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa. Zaria: NNPC.
Mashi,
A. A. 2000. “Zama da Maɗaukin Kanwa:
Tasirin Zamananci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin digirin MA, Sashen Harsunan
Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Nduka, O. 1964. Western Education and the Nigeria Cultural
Background. Ibadan: Oɗford Uniɓersity Press.
Newman, R. M. 2003.
An English-Hausa Dictionary. Longman, reprinted.
Rimmer, E. M. 2009. Zaman Mutum
Da Sana’arsa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
The New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of English
Language: Deluɗe Encyclopedic Edition. Trident Press, International
Edition (1996).
Yahaya, I. Y. 1971/72. Tatsuniyoyi da Wasanni Juzu’i na 6.
Ibadan: Oɗford Uniɓersity Press.
[1]
Abin mamaki a nan shi ne, a
cikin Hausawa makaɗa ‘yan tsirarru ne amma ga fitattun karin maganganu da suka
shafi kayan kiɗa suna fitar da duniyar tunanin Bahaushe. Daga cikinsu akwai: Ganga ba ki
asiri; tambarin talakka cikinsa; da gangan kiɗin ganga da lauje; gyaran gangar
Azbinawa; ba gyaran-gyaran a yi mai kura ta sato ganga; shiru mai kiɗin kalangu ya faɗa rijiya; ga su nan dai. Don haka, ƙunso muhimmin saƙon Bahaushe cikin kayan kiɗan Bahaushe ba baƙo ba ne.
[4] Hira da Dr. Abdulƙadir Sani, Shugaban Sashen Larabci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto (da ya gabata) Litinin, 2015.
[5] Turanci ya zo ta fuskar ci da ƙarfi ta fuskar mulkin mallaka na indirect rule a arewacin Nijeriya
da assimilation a ƙasar Jamhuriyar Nijar wanda ya haifar
da yaƙe-yaƙe da gaba. Bugu da ƙari, ya zo da baƙon addinin Mishon da ke takin saƙa da aƙidar addinin Musulunci da ya tarar.
Waɗannan abubuwan tarihi suka rage wa
Turanci tagomashi a zukatan Hausawa ko lokacin da Turawa na kan
danniyar mulkinsu haiƙan.
[6] The
New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of English Language: Deluɗe
Encyclopedic Edition,
Tredent Press, International 1996 Edition.
[8] Dubi irin zaman da Saƙimu agolan Malam Nabakin Kogi ya yi da Malam, kuma ya zama ajalin Malam
da matansa huɗu duka. A dubi, A. Imam, Ruwan Bagaja, NNPC, 1933.
[9] Irin zaman mata da miji a daɗe ana tare ana cin arzikin miji ana
cikin daula, da ɗan abin ya ƙare ta tayar da jidali dole sai an
sake ta. In ba a yi ba ta kai kotu, wannan shi ne butulci.
[10] Yadda ɗalibi zai karɓi takarda daga hannun malaminsa. Idan
ya ga ya kai ga karɓar manyan takardun shaidar MA, MPhil, ko PhD ko ya ga ya kai
Shaihin masani ya fara raba ruwa rana da malamansa, wai ya ga ƙafafunsa sun kama ƙasa. Tir! Ai babban butulci ne a
manta da cewa, sai an yi shuka ake zancen tumu.
[11] Tarihin wani malamin kokuwa da ɗalibinsa ya isa misali. Bayan an
tabbatar masa da ƙwarewa ga kokuwa, ya gama da kowa a
garin bayan malaminsa. Aka zuga shi da turu ya ce, malamin ya zo a taka. Malam
ya ƙi, ya matsa dole sai an yi, aka taka aka kayar da ɗalibin kamar bugun ashana. A dubi, A.
M. Bunza, “Baki Abin Magana” wallafar Association of Nigerian Languages Teachers
of Nigeria.
[12] Wannan ana iya kwatanta shi da
sakayyar shugaba Jonatahan na PDP da shugaba Buhari na APC. Buhari ya gyara
Nijeriya tun ba a ko san da Jonathan ba. Ya daidaita tattalin arziki, da tsaro,
da siyasa, da kawar da zalunci. A cikin wannan gagarumin aiki Jonathan ya rayu
ya zama abin da ya zama. Yau don ya samu riƙa ƙasar na wucin gadi yake ta yin kirari
na rinjayar Buhari cikin arzikin da Buhari ya shimfiɗa. Wannan butulci ne.
[13] Kamar mutum ne ya saya raƙumi ko sa ya dinga yin ƙwadago da shi. Raƙumin ya sama masa dukiya da zai saya abinci ya rayu. Ya sama masa wata
dukiyar ya saya filin gida ya gina shi. Yana samun gida, ya ci gaba da neman kuɗi, ya tara jallin aure. Ranar da za a
yi walimar aurensa, ya yanka raƙumin a yi liyafar walimar aure da
shi. Wannan shi ne misalin wannan ɓangare na butulci.
[14] Tamkar dai yadda ɗan Adam yake, bayan Allah Ya halicce
shi an ganar da shi Mahaliccinsa. Da ya girma, ya kama tsafi da shirka, ya yi
fito-na-fito da Mahaliccinsa da ya ce ba ya gafarta wa shirka da Shi. Wannan
kafircin shirka da yake yi shi ne kafirce wa Allah da butulce maSa.
[15]
Irin yadda makaɗa Gambo Fagada yake yi wa masu gidajensa ɓarayi da shi da makaɗa
Kassu Zurmi. In an koro ɓarawo su shiga cikin ‘yan kuwa
alhali in ya ci nasara su ke shan daɗi. A wani ɗan waƙa
Kassu na cewa:
Jagora: In an samu a ishe mu
:In ku tas samu ku yi yamma
(Sakkwato)
:Sai an
dawo
Wai abin nufi shi ne:
In sun sato su zo a ci tare
In ko su aka kama su tafi Sakkwato
hursuna!
[16] A ganin mafi yawan mafasa baƙin zamantakewa wannan ita ce ƙololuwar butulci a rayuwar ɗan Adam. Wanda duk ke da hannu na
sanadiyyar kasancewarka wani abu a duniya ta kowace fuska ka kasance, a
koyaushe yana gabas kana yamma, a koyaushe kana bayan akasin tunaninsa da
manufarsa da ra’ayinsa hasadar ta kai matuƙa. Babban burinka kada sunansa ya yi
fice a kan naka.
[17] Butulu ba ya da kai sai na ɗaukar kaya. Ba ya da hankali sai na
cin tuwo. A ko’ina yake babban burinsa ganin bayan wanda ya yi wa butulci. A
bisa wannan tunanin, da duk gubar butulci ta yi turnuƙu sai ya zama sanadiyyar mutuwar wanda ya yi masa tsani.
[18] Wanda duk ya kyautata maka ka
kyautata masa fiye da yadda ya yi maka. In ka cuta masa ka yi butulci.
[21] Tukuicin cuta ga wanda ya kyautata.
Godiyar Maye ga wanda ya kyautata masa shi ne ya kama shi ya cinye.
[26] Haugen banza butulun wofi, to
madokin ya sha ke nan? Allah Ya wadaren butulu.
[27] Gidan gado ya amfani ɗa, ya sani ko bai sani ba, nunin
gidan da hagu ko cikin kure butulcewa ne.
[28] Goge baki ga ƙasa da kaza ke yi bayan ta ci abinci ya sa Bahaushe na zarginta da rashin
godiya irin ta butulu.
[29] Butulcin maciji ga yaro neman
rayuwar yaro, bayan yaro ya kuɓutar da shi daga makasa. Butulcin yaro ga zarɓe neman kashe zarɓe, bayan zarɓe ya ceto ransa daga maciji. Butulcin
zarɓe ga maharbi nakkasar da maharbi na
har abada, bayan an kuɓutar da rayuwarsa daga yaro. Wannan shi ne misalin ƙaramin butulci na cuta wa maceci. A ƙarshen wannan ƙissar, mutum aka fara yi wa butulci kuma mutum aka yi wa butulcin ƙarshe. Don haka, mutum ya fi kowace halitta ƙiyayya da butulci. Wannan ƙissar sananniya ce a tatsuniyoyin
Hausawa amma ni na karance ta a rubuce-rubucen darussan adabi na Dr. Ibrahim
Sarkin Sudan Kwantagora, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato wajajen 1999/2000.
[30] Na samu wannan ƙissar ga Alhaji Muhammadu Ɗanɗa Hamma Ali, Principal Goɓt. Technical Secondary School Farfaru
Sokoto a wata hira ta musamman wajajen 2013/2014. Wannan ƙissar ta tabbatar da kasancewar butulu maƙaryaci kuma azzalumi, makunyaci,
mayaudari. Kasancewarsa wawa ya sa aka tarar da shi yana kirarin zambar da ya yi.
A kula, butulci ba ya da bambanci tsakanin lafiyayyu da marasa lafiya domin
makaho ne aka taimaka ya yi butulci.
[32] Na bi diddigin wannan shari’ar ta
hannun abokina Dr. Ibrahim Sarkin Sudan Kwantagora, Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato shi kuwa abokin
yayan Marigayi Abdulƙadir S. Dori ne, wato Dr. Haruna Alero na Economics Dept. UDUS. Na
je ta’aziyyar Alero tare da Dr. Ibrahim da misalin ƙarfe 9:30 na dare a garin Alero. Abin lura a nan shi ne, taimakon da ya
yi wa butulai shi ya zamo sanadiyyar hasarar rayuwarsa da dukiyarsa. Wannan shi
ne ƙarshen yaudara. Idan naka butulu ya bar ka da ranka ka kwana da kariyar
bai manta ba.
[33] Yahaya Sa’idu Andarai maigidana ne a
Goɓernment
College Sokoto (Nagarta College Sokoto) yana aji biyar 1977 ina aji 3. Musibar
ta auku a garin Sakkwato ina cikin garin. Yayin da musibar ta auku yana Director Finance Local Goɓernment Serɓice Commission Kebbi State. An kashe shi ranar 15/09/2014.
Wanda ya kashe shi yaronsa ne kuma abokin sana’arsa, mai kula masa da ‘yar
sana’arsa ta filaye. Shi ya yi wa yaron aure, ya gina masa gida, a hidimar
auren naira dubu ɗari uku ya ba yaron na shagalin biki. Wannan duk ba ta sa ya
gode ba, don haka ya gayyato ƙatta ya biya su, suka kashe shi. Kisa
shi ne mataki na ƙarshe na butulci. Me kake zaton za ka
yi wa butulu bai nemi ya gama da rayuwarka ba?
[34] Ba ni cikin garin Bunza ko da abin
ya auku amma ranar na shigo garin. Matsalar ta auku a shekarar 2014. Yaron
Igbo, yana da babban chemist a garin Koko ƙaramar hukumar Koko-Besse, Jihar
Kabi. Sunan maigidansa Emeka. Yaran da ake zargi ɗaya ya tsere ɗaya an sako shi. Da wannan matsalar
da ta garin Kwaifa duk ɗaya ce, bashi ya haddasa kisan kai. A ko’ina aka ga butulci
ya haifar da kisa wani abu ake son a ɓoye kada ya bayyana a jiya, musamman
matsala irin ta bashi idan ya yi yawa kuma ya tsawaita (bad debt).
[35] Lawwali Gandi Cashier
ne a Ƙaramar Hukumar Raɓah ta jihar Sokoto. Waɗanda ake tuhuma har da maƙwabcinsa ciki. Kisan ya biyo da ƙuna irin na Abdulƙadir S. Ɗori Alero. An san ya san makasan nasa, kuma saboda
irin tsananin kusancin da suke da shi ya sa suka ƙona gidan gaba ɗaya kada a kama su butulcinsu ya bayyana
su tozarta.
[37] Yayin da ya kashe Thomas Sankara an
yayata wannan jawabi a gidan Rediyon BBC da ƁOA da CNN da Radio Faransa sosai.
Kusancin Sankara da Campore da ya kashe shi irin na Ba’are da Wanke ne a
Jamhuriyar Nijar. Ya yi wannan jawabin ne lokacin da jami’an tsaro na ciki
(SSS) suka yi masa hannunka-mai-sanda kan take-taken Campore.
[38] A ƙasar Iraƙi Yahudu da Nasara in ma akwai su ‘yan tsiraru ne. Tarikh Azeez Kirista
ne (Masihi) amma aka ba shi mataimakin shugaban ƙasar tare da sanin masu addinin
Masihi a ƙasar ba su da ko kaso ɗaya bisa ɗari na jama’ar ƙasar Iraƙi. Gabanin da a auka wa ƙasar da yaƙi, aka tilasta a yi ƙuri’a ta a je yaƙi ko kada a je tare kuma da nuna yarda da gwamnatin da ke ci. Duk faɗin majalisar Iraƙi kowa ya yarda ƙuri’ar Tarikh kaɗai ce aka samu ta nuna rashin yarda.
Da za a kai musu babban hari na farko Tarikh ya gaya wa UN/Amerika wurin da za
a yi taron majalisar ƙoli ta Iraƙi, da lokacin da za a yi, da lokacin da manyan ƙasa za su shiga ɗakin taro. Daidai lokacin jiragen yaƙin Amerika suka kai hari wurin zaton Saddam na ciki. Duk da wannan bai sa
Saddam ya fitar da shi ba ko ya ɗaure shi ko ya kashe shi. Da yake
butulu maras kunya ne, maras sanin ya kamata, wawa, maƙetaci bai ja da baya ba sai da aka kashe Saddam. Me kake zaton ka yi wa
naka butulu ku zauna lafiya? Idan butulci ya haɗa da siyasar mulki sai ya ci rayuwa
yake ƙarewa.
[39] An ce da Sir. Ahmadu Bello ya
tabbata kashe shi za a yi, ya gaya wa Nzegu cewa: “Abin da ya kawo ka gidana ba
za a ci nasararsa ba ko da kun kashe ni.” Wane takaici ne, na jan gawar
maigidanka ƙasa giriri bayan ka kashe shi? Halin butulci ke nan,
ko an mutu dafin gubar na nan ba ta gushe ba. Dubi yadda mutanen Kwaifa suka ƙona gawar maigidansu Abdulƙadir Usman S. Ɗori Alero.
[40] Wai: “Jiya kaɗan da an kuɓutar da ni, amma yau saboda wannan
yaro Dimka Allah Sarki!” A koyaushe butulu ganin yake yi in ya yi ta’adi yana
iya kuɓuta. Abada wanzan ne ba ka so ga
jikinka. Da zai samu ya kuɓuta sai ya aikata wadda ta fi wannan muni. Ku tambayi Zarɓe da ya cire wa yaro maciji.
[43] Hira da Malam Mas’udu a makarantarsa
ta zaure da ke masallacin Yarbawa Sokoto shekarar 2011.
[44] Haka fassarar nassin ƙissar yake a fassarar magabatan farko. A Saudiyya shekarar 2014 wani ya
doki ‘yarsa har ta mutu, aka yanke masa hukuncin bulala ɗari da ɗaurin shekara (biyar), dogaro a kan
ba a kashe uba saboda ɗa.
[45] A cikin babukan yaƙi na Risala da Mukhtasar
Khalil an ambaci
haka. Sheikh Ibn Ishaƙ a cikin littafinsa Sullamul
Gawaamidi Fi Ilmi Rasaa’idi ya ambaci haka, wallafar Ɗan’ige Tsamiyar Dila, Sakkwato.
[48] Irin haka ta auku tsakanin Annabi
Musa (AS) da Malam Bil’amu Ɗanba’ura. Duk ɗalibin da ya butulce wa malaminsa
sunansa Bil’amu.
[49] Wane tsuntsu maharbin da ya ceci zarɓe zai sake taimaka wa a duniya? Ai
zarɓe ya rufe ƙofar ceto.
[50] Haka makaho ya yi wa mai doki da ya
taimake shi.
[51] Butulcin da maciji ya yi wa yaro ya
yi kusan haka. Butulan Abdulƙadir S. Ɗori Alero sun fi fito da wannan maganar a fili ƙarara.
[52] Dangantakar Bello Ubandawaki da
Yahaya Sa’idu Andarai babbar hujja ce.
[53] Da yawa daga cikin fitattun
shugabannin duniya a ƙauye suka tashi suka amfana da
nagartacciyar rayuwa irin su Mammar Gaddafi da Nelson Mandela da Saddam
Hussaini da Shehu Shagari da Nnamdi Azikiwe da Yakubu Gawon da Dauda Malam
Wanke da Ba’are Mainasara da sauransu.
[54] Tilas a buɗe wata gagarumar ma’aikata da za ta
kula da gabaci in ba haka ba butulce wa gabaci ya gama da mu.
[55] Yanzu an manta da ajo da karo-karo
da ɗegiya da tukuici da kyauta da biki da
ɗauke da rance da bashi da jingina da
tugu da sauran nau’ukan taimako.
[56] A iya sanina, yau sana’ar ƙira da rini da kamun kifi da wanzanci sun shiga cikin haɗarin lokaci na yau ciwo gobe lafiya
jibi masassara.
[57] Don ƙarin bayani a dubi, M. Safana,
“Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, kundin MA, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
[58] Tsarin sarauta irin ta addininmu ta dace
da tunaninmu.
[59] Yau 2015, ƙasarmu ta fi kowace ƙasa maguɗi da cin hanci da ta’addanci
sanadiyyar miƙa ragama ga baya a manta da gaba.
Use the MyBookie promo code “MYB100” to double your first transaction of $50 or extra. You’ll claim a most bonus up to as} $1,000 in free bet credits! There’s a 10x rollover requirement connected to your sportsbook funds, and you’ll have 30 days to beat the percentages. Now that you’ve verified your private information, it’s time to make your first sportsbook deposit and start betting with MyBookie! You’ll be redirected to their cashier web page, the place find a way to|you 1xbet possibly can} choose your most well-liked cost option.
ReplyDelete