Friday, December 28, 2018

Gaskiya: A Tunanin Bahaushen Karin Magana



Tunanin Bahaushe na faɗar: “Lokacin abu a yi shi,” wata babbar makaranta ce mai fannonin karatu da yawa. Ga al’adar ɗan Adam, kowa na son gaskiya, don haka dukkanin fafutukar ɗan Adam a duniya, gaskiya yake yi wa ita. Ma’anar gaskiya a kowace al’umma bai saɓa ba. Ɗan yunƙurin da nake son in yi shi ne, leƙo inwar gaskiya cikin wani ɗan sashen adabin baka wato “Karin Magana”. Kayan cikin tunanin Bahaushen Karin Magana suna da dangantaka ta ƙuƙut da al’adarsa da tunaninsa a duniyar zamaninsa. Ganin irin halin da ƙasarmu take ciki, na ƙoƙarin

--------------------------------------
Daga
Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
mabunza@yahoo.com 08034316508
------------------------------------------------
Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ƙarƙashin kulawar Dr. Umar Aliyu Bunza wanda shugaban Sashe Farfesa Abdulhamid Ɗantunbishi ke jagoranta, Alhamis 9 ga Satumba, 2015 da misalin ƙarfe 10:00 na safe a babban ɗakin taron Tsangayar Fasaha da Nazarin addinin Musulunci.
Gabatarwa
Tunanin Bahaushe na faɗar: “Lokacin abu a yi shi,” wata babbar makaranta ce mai fannonin karatu da yawa. Ga al’adar ɗan Adam, kowa na son gaskiya, don haka dukkanin fafutukar ɗan Adam a duniya, gaskiya yake yi wa ita. Ma’anar gaskiya a kowace al’umma bai saɓa ba. Ɗan yunƙurin da nake son in yi shi ne, leƙo inwar gaskiya cikin wani ɗan sashen adabin baka wato “Karin Magana”. Kayan cikin tunanin Bahaushen Karin Magana suna da dangantaka ta ƙuƙut da al’adarsa da tunaninsa a duniyar zamaninsa. Ganin irin halin da ƙasarmu take ciki, na ƙoƙarin yi wa gaskiya babban masaukin alfarma, ya ba ni sha’awar in ɗan ambaci gudunmuwar Hausawa na ƙara wa Borno dawaki a kan goyon bayan gaskiya. Ba zan yi mamakin a ce, wannan takarda ta yi canjaras da wani aiki irinta ba, domin gaskiya sananniyar aba ce, mai farin jini, da jan hankalin ma’abota hankali. Duk da haka, ni dai, a iya ɗan bincikena, ban kai ga wani aiki da suka yi zozo-zozo ba.
Warware Taken Takarda
Babu wani sashe na rayuwar Bahaushe da Gaskiya ba ta yi naso ba. Na zaɓi in kalli karin magana domin kasancewar karin magana wata fitacciyar duniyar adabi da ta mamaye duniyar masu magana da harshe. Tunanin da ke cikin karin magana na masu harshen ne, domin su suka ƙagi karrruwan maganganunsu. Yadda karin maganan Bahaushe ke kallon gaskiya shi ne gaskiyar yadda Bahaushe ke kallon gaskiya a duniyar tunaninsa. Na taƙaita faɗin bagiren bincike a kan Bahaushen karin magana domin a kowane harshe akwai karuruwan maganganu da suke yi wa gaskiya kirari da godiya. Kasancewar karin magana ƙololuwar tunanin masu magana da harshen, idan aka nazarci “gaskiya” a ciki an kai matuƙa ga tunanin masu harshe a kan yadda suke kallon gaskiya. Abubuwan da za a tattauna a cikin wannan ‘yar takarda tantagaryar tsabagen Bahaushe tunani ne na kowane Bahaushe, a kowace nahiya yake ciki a duniyar ƙasar Hausa, wannan tunanin ya wakilce shi.
Ma’anar Gaskiya
A tsarin nahawu “gaskiya” suna ne. Daga cikin rukunin sunaye yana daga cikin sunayen da ba a gani. A wata fassara sunan na ɗaukar “nake yi” wato a ce: “Gaskiya nake yi”. A koyaushe za a fassara gaskiya, dole a yi la’akari da abu biyu: furuci da aiki. A tunanin Bahaushe gaskiyar furuci ita ce:
A darkako zance yadda aka ji shi cikin ruhin kalmomin da aka ji shi ba tare da an sauya su ba, ko a sassaɓa musu muhalli ga yadda suka sauka ba. A tabbata ba a ƙara komai ba, ba a rage komai ba, ba a kururuta ko giɗaɗa komai ba, kuma ba a rage nauyin sassakan kalmomi ba, kuma ba a ƙara musu nauyi ba. Zancen, da an furta shi, mai shi zai ce: “Haka na faɗa”,  wanda aka yi gabansa ya ce: “Haka na ji shi”. Idan ta tabbata haka, wannan shi ake ce wa, “gaskiya magana” yadda aka ji ta, haka aka faɗe ta.

A tunanin Bahaushe, ba baki kaɗai ke da haƙƙin gaskata gaskiya ba. A ayukka ma ana iya rarrabe na gaksiya da akasinta. Aikin gaskiya shi ne:
Aikata abu yadda aka shata a aikata shi. Aikin da aka aikata, ya yi canjaras da tunanin al’adar rayuwa da aƙidarta ba ragi ba ƙari. A aikata aikin da gaskiya, a kan gaskiya, bisa gaskiya, ba tare da yin takin saƙa da kowane irin ma’aunni na gaskiya ba.

Waɗannan fassarori na gaskiya ƙunshe suke cikin tunanin Bahaushe na faɗar: “In za ka faɗi, faɗi gaskiya”. A nan, gaskiyar magana ta fito. A fassarar gaskiyar aiki kuwa, za mu harari: “A daɗe ana yi sai gaskiya”. A daɗe ana me? Ana aikata wani aiki ba ja da baya, ba tsoro, ba razana bale tsangwama sai gaskiya? Da furucin da aka furta, da aikin da aka aikata na gaskiya, duka sunansu “gaskiya” bisa ga zurfin tunanin Bahaushe na raɗa mata suna “Gaskiya sunanta gaskiya”.
Jinsi Gaskiya:
Ga ɗan tunanina na ɗalibin al’ada, na so in kalli a tsarin nahawun Hausa gaskiya wane jinsi take? Me za a ce a kan jinsin a al’adance? A ƙa’idar zumuntan suna da lamirinsa, gaskiya mace ne. Dalilina na faɗar haka shi ne, ga al’adar zantukan yau da kullum, akan ji Bahaushe na faɗar:
Gaskiya ta yi halinta.
Gaskiya mugunyar magana
Gaskiyar faɗa harsashe
Gaskiya nagartar namiji.
Faɗin gaskiya ya fi mugunyar salla.
Daidaiton shigan lamirin jinsin mace na ta da –r wata hujja ce ta tabbatar da jinsin mace ga gaskiya. Yarda da ba Bahaushe ya yi na kasancewar gaskiya “magana” wata hujja ce ta zamowar gaskiya mace. Idan mun daidaita a kan kasancewar gaskiya “mace” a al’adance, tana da martabobi goma sha ɗaya:
1.                  Mace ke haihuwa matuƙar ana haihuwa gaskiya ba ta ƙarewa.
2.                  A awon shekaru mata sun fi maza makara, tabbacin gaskiya ita ce ƙarshen kowane al’amari.
3.                  A kowace al’umma, mace ake nemi ba ita ke nema ba. Wa gaskiya ke nema? Kowa nemanta yake.
4.                  Mata sun fi maza fice da haiba idan sun tsatsanta a matsayin mutane. Haka gaskiya take ko’ina.
5.                  Mata su aka fi sani da kyau irin na fuska da jiki. A koyaushe gaskiya ba ta da muni ga Bahaushe.
6.                  Mata sun fi cin adon kintsi da tsari mai jan hankali. Gaskiya da adonta aka gan ta, don haka ba ta neman wani ado.
7.                  Mata sun fi maza zaƙin murya da yauƙin tafiya. Muryar gaskiya rarara ce.
8.                  Mata sun fi maza haƙuri idan aka dubi kishi da haihuwa. Mai gaskiya kan dafa dutse.
9.                  Mata ke haƙa tarkon kama mutum. Tarkon gaskiya ƙarya ba ta taɓa tsallake shi ba.
10.              Mata ake nema ba su ke neman maza ba. Kowa gaskiya yake nema domin a ce masa mai gaskiya.
Irin tunanin Bahaushe ga mata na yau soyayya, gobe ƙiyayya, shi ke ga gaskiya a kirarin, da ake yi mata na: “Gaskiya a ƙi ki a so ki”. An yarda mace na tsufa ta kai munzalin da za a tabbata haka, amma ita gaskiya ta fi da haka, dalilinsa ke nan na ce mata: “Gaskiya ba ta tsufa”.
Fitattun Sofifin Gaskiya:
Kasancewar gaskiya suna, ba dole sai an gan ta da ido ba domin ɓoyayyen suna ce. Tattare da haka, sifoffinta da halayenta da karuruwan magana suka fuskanta abin duba ne ga kowane masoyinta. A hangen Bahaushe, gaskiya aba ce da ta tattaro abubuwa kamar haka:
Farin jini:       A ko’ina gaskiya da masoyinta yake/suke za a tarar da su
masu farin jini ga mutane. Ashe babu laifin karin maganan da ke cewa: “Gaskiya ina laifinki”? Farin jini shi ne kuɓutar illar abu ga masu kallonsa saboda tsananin son da suke yi masa.
Haƙuri: A koyaushe, gaskiya da mutanenta, an shaide su da haƙuri domin
sun san kul ba daɗe, kome nisan dare gari zai waye; don haka, a daɗe ana yi sai gaskiya.
Wayo: Ba a taɓa samun ma’aboci gaskiya wawa ba, sai dai ma’auri
ƙarya ya ga wautarsa na biya wa gaskiya sadaki mai tsada. Kafirce wa ƙawace-ƙawacen ƙyalƙyali da gaskiya ta yi dole ne, domin ita ba ta neman ado ko zaƙin muryar zabiya.

Ƙwazo: A al’adance, raggo abin kushewa ne don haka, ragganci ba ya
daga cikin sifofin gaskiya. A ganin Bahaushe, mai gaskiya shi ne managarci don haka yake cewa: “Gaskiya nagartar namiji”. Idan an ci karo da ita baibai ta gwaƙe abokin adawa ya ce: “Gaskiya dokin ƙarfe”.
Kunya: Gaskiya kunya gare ta, don haka kowa ke sha’awar hulɗa da ita.
Idan an zaune ta, zantukan ladabi da kunya za su riƙa fita a baki domin maganar gaskiya baki ba shi rawa. Idan aka rasa ta, babu wani abu da zai maye gurbinta na kare kunya. Tunanin Bahaushe ke nan na cewa: “Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi”.
Cika Ido: Mai gaskiya komai ƙarancin zatin jikinsa a idon waɗanda suka
san shi da ita ya fi toron giwa cika ido a dokar daji. Komai ƙarancin shekarun mai gaksiya Bahaushe bai ɗauke shi yaro ba saboda cewa yake yi: “Yaro da gaskiya abin tsoro ne”. Idan gabaci ya zure mata ta yi halinta akan ce: “Gaskiya ba ta da kaɗan”.
Basira: A kowace irin al’umma ma’abota basira ake ba tsaron gaskiya.
Duba zuwa ga manzanni da annabawa da mala’iku wani dogon karatu ne. A tsakaninmu ‘yan Adam, ma’abota basira daga cikinmu ke kula muna da tsare-tsare dokokinmu da zartar da hukunce-hukuncenmu. A koyaushe gaskiya ta bayyana, ƙin ba da kai bori ya hau rashin basira ne domin an ce: “Da ƙin gaskiya sai ɓata”.
Kyawo: A ji abu, a ga abu, a tabbatar da abu ya yi abu, sai gaskiya. A
lafazance da aikace, Bahaushe bai taɓa kwatanta gaskiya da muni ba. A koyaushe a wajensa fara ce fes! Mun kuwa san cewa ya yi: “Komi ya yi fari yana kyau in ban da kurkunu”. Komai munin magana a bagiren da aka furta ta ko munin aiki a wurin da aka aikata shi, in dai a kan gaskiya yake zancen muni bai taso ba, sai dai a ga manya suna na ƙadangare suna cewa: “Ka ji farar gaskiya”. Ɗanƙari! Wato gaskiyar da ke ciki ta kore komai sai dai a biyo da gyaran fuskar faɗar: “Gaskiya ciwo gare ta”.
Tsufa: A ma’aunin ɗan Adam na addini da al’ada da cigaban zamani,
tsufa ga rayuwa wata martaba ce, domin an ga jiya, an ga yau. A tunanin Bahaushe, gaskiya ba ta tsufa irin ta mutane, a koyaushe aka lalubo ta za a same ta sabuwa garas kamar yanzu aka yi ta. Maganar gaskiya ba ta tsufa, aikin gaskiya ba ya tsufa. Haƙiƙa, Hausawa sun dace a faɗarsu na cewa: “Gaskiya ba ta tsufa”.
Magani: Bahaushe ya ɗauki gaskiya wata babbar magani ga cutukan
zukata da na gaɓɓai da rigakafi da waibuwa. A hangensa shi kansa magani sunansa “gaskiya”. Ko’ina mabuƙaci yake yawo da wata buƙata maganinta yake nema ya rabu da ita ko ya shawo kanta ko ya rage ta ko ya yi mata barazana. Bahaushe na ganin, gaskiya ita ce ganmon ɗaukar dukkanin waɗannan buƙatoci. A fagen artabo da marasa gaskiya, gaskiya ‘yar tauri ce ta haƙiƙa domin Bahaushe ya yanke hukunci cewa: “Ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi”.
Fitattun Halayenta:
Hali a nan, ina son in ce, abin da za a iya gani ƙuru-ƙuru a kan wanda ta shafa ko wurin da ta bayyana ko aikin da ta ƙarasar. A kadadar adabi, babu abin da ya samu babbar shaidar ƙwarai kamar gaskiya. Wannan shi ya sa babu wani bayanin da zai iya kewaye dukkanin halayenta, sai dai a ɗan kwatanta gwargwadon abubuwan da aka tuna. Mu tsura wa waɗannan halaye ido mu nazarce su a ma’aunin gaskiya mu gani:
1.                  Bahaushe ya ce: “Idan ka ji shuru lafiya ce, gaskiya ta bayyana, idan ta ɗaga ko ita ake neman dole a ji muryoyi na tashi.
2.                  Idan ka ga ana gudu, ta bayyana ko wurinta za a je neman agaji. Ban ga laifin Rarara ba da ya ce: “Masu gudu su gudu”!     
3.                  Hausawa na cewa, “Labarin zuciya a tambayi fuska”. Idan an yi canjaras da gaskiya, za a ga fuska na haske da dariya ko murmushi, tamkar kurma na cikin mota ya tsinkayi matarsa.
4.                  Idan an tarar da fuskoki gintse cikin ƙura, wataƙila an zartar da ita ga wanda ya saɓa mata. Haka kuma, idan lokacinta ya yi dole a gintse, Bahaushe ya ce: “Gaskiya mai ɗaci”.
5.                  Kuka akasin dariya ne, amma kuma gaskiya yake rakowa a ko’ina aka ji shi. Idan ta bayyana tana sa kuka ga wanda ta ratsa. Haka kuma, da kuka ake neman zartas da ita ga wanda aka yaudara.
6.                  Bahaushe ya ce: “In ka ga barci da dogon hansari gaskiya aka taka ta ba da damar a kwanta a huta a yi barci”. Wanda ya rasa ta zancen barci sai abin da hali ya yi.
7.                  Ga al’ada, idan aka kasa barci gaskiya aka kwance wa bante. Wanda ke matse neman gaskiya ko ya saɓa mata, bai ga idon barci ba.
8.                  A ko’ina aka tarar da ana faɗa, kowane ɓangare ita yake da’awar yana da, don haka yake tsayin daka sai ta tabbata, an tabbatar masa da ita.
9.                  Ma’abota basira sun ce: “Gaskiya ta tsayar da hukuma”, a ko’ina aka ga kotu don ƙwato gaskiya da tabbatar da gaskiya aka kafa ta. Wanda duk ya kai ƙara ita yake son a ba shi. Wanda duk aka kai ƙara ana zarginsa da rashinta.
10.              Makarantun da ‘yan Adam ke yi na kowace irin aƙida da fahimta da fasaha, gaskiya ce ake son a gano a ciki.
11.              Ba a taɓa samun zaman lafiya ba face sai da gaskiya. A ko’ina gaskiya ta ƙi kai ziyara zaman lafiya ya ƙare.
12.              Rigingimu da tashin hankulkula da zub da jinainai tushensu rashin gaskiya. Mai musu ya tambayi waɗanda ke ƙarƙashin inwar gaskiya.
13.              Magabata sun ce: “In ka ga lafiya a tsufa tun a ƙuruciya aka bauta wa gaskiya”. Idan aka ga tsufa cikin wuya ba a ba gaskiya haƙƙinta cikin ƙuruciya ba.
14.              A ko’ina tsoro ya yawaita banga-banga aka yi da gaskiya, in an yi taho-mu-gama da ita, dole tsoro ya yi ban kwana da ƙirji.
15.              Gwarzo a ko’ina yake gaskiya ya rako sau da ƙafa.
16.              Masana da maɗaukakan duniya kafaɗar gaskiya suka dafa suka yi zara aka gan su, aka ji su, aka yarda da su, suka samu karɓuwa.
17.              In suna ya dashe, ba a jin ɗuriyar mai shi a ko’ina, da wuya in ba dugadugan gaskiya aka ci ba.
Nahawun Sunan Gaskiya:
A nazarin nahawun sunan gaskiya babban abin kulawa shi ne faɗar Bahaushe na: “Gaskiya sunanta gaskiya”. Sunan gaskiya kaɗaitacce ne a farfajiyar tunanin Bahaushe. A tsarin daidaitaccen nahawun Bahaushe gaskiya ba ta da jam’i, tilonta ta “gaskiya”, jam’in ta ‘gaskiya’, ba a taɓa jin “gaskiyoyi” ba. Dalili kuwa ita kaɗai ce, ta ishi kanta, da kanta, ba ta da na biyu, ba ta da mai kama da ita. Abu in dai ya kasance ita, in ko ya kasance akasinta. Na yarda da karuwa da ta ga noman ɗan koli ta ce “Abu kamar da gaske”, wai, domin ta san ba gaskiyar ba ce. Abin ban sha’awa ɗofanenta da ake yi wa kalmar koyaushe gaba yake idan aka nazarci:
Gaskatawa
Gaskacewa
Gaskanta
Gaskatacce
Gaskatacciya
Gaskatattu
Magaskanta.
A wata mahanga, a cikin tsarin sunayen itace da tsirrai na ƙasar Hausa, tare da ƙwari da dabbobi da tsuntsaye babu mai suna “gaskiya”. Da na lura cikin wannan tunanin, sai na ga akwai ice mai suna “ƙarya”. Dalili kuwa shi ne, a tsarin nahawu gaskiya ta fi ƙarfin duk wani abu da ba ɗan Adam ba. A iya sanina, babu wata halitta mai sunanta.
Gaskiya A Duniyar Dabbobi:
Wannan aikin a kan karuruwan maganganun gaskiya aka tsara su. Duk da haka, na yi aron hannu domin fashin baƙin ma’anonin wani labari da gidan Rediyon Rima ya taɓa gabatarwa a shirinsu na kacici-kacici. Labarin na cewa:
Wai mene ne dalilin akuya na a ko’ina ta ga mota ta ruga a guje? Shi kuwa kare me mota ta yi masa da ya gan ta ya ruga aguje yana bin ta da haushi? Akwai mamaki jaki komai odar da mota ke yi masa, ba ya ta da kansa, bale ya ɗaga wurin da yake. Mafasa baƙin suka ce: “kowanensu na kan gaskiyarsa. Ita dai akuya, rashin gaskiya ta yi, ta shiga ba ta biya ba. Kare kuwa, ya biya kuɗinsa, ba a ba shi canji ba, don haka yake bin gaskiyarsa”. Jaki (DPO’n) hanya, gaskiya ta yi masa yawa; ya biya ba a ɗauke shi ba, ba a ba shi kuɗinsa ba. Don me zai yi wa maras gaskiya gudu shi da gaskiyarsa? Ashe sunan wannan labari a farfajiyar karin magana: “Gaskiya ka faɗa ba sanda ba”.

Akuya ta tabbatar da maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi. A fahimtar kare, gaskiya ka faɗa ba sanda ba, ko an fi shi gudu ba zai daina bi ba, sai an biya shi. A tunanin jaki, ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi. Jaki gaskiya ya taka, to, ƙasa ta gudu ta je ina?
Tasirin Karin Maganganun Gaskiya ga Dimokraɗiyyar Ƙasarmu:
Da gangan na kawo wannan ɗan fasali domin mu riƙa daidaita karatunmu da halin da muke ciki na rayuwa. Demokraɗiyya wani ruwan dare ne a duniyar mutanen ƙarninmu. A ƙasarmu, gaskiya ta tarar da ƙarya ta tara miyagun makamai fiye da goma sha biyar (15) wanda take ganin kowane ɗaya daga ciki ya ishe ta yaƙar gaskiya. Daga cikin makaman akwai:

Kuɗi:              Na cikin gida da ƙadarori da na waje. Su ne ƙuri’a in ba su,
ba ci.
Mulki: Ita ta kafa daula ita ke da masarauta. Mai sanda ke da fasalin
bugu.
Yawa: A ko’ina ta hanga ta yi wa gaskiya rata mai yawa. Ba ta
zaton kowace matsala.
Maguɗi:          Da shi ta kafa daula kuma ta shirya shi matuƙa.
Banga: Bayan wakilan tsaro na yi mata kore ga ‘yan ta’adda da ta
yaye bila adadin.
Addini:           Cikin yaudara ta kutso da shi domin in dama ta ƙiya a koma
hagu.
Ƙabilanci:       Aka raba hankalin ‘yan ƙasa da sunan ƙabilu domin samun
damar ribantarsu.
Ɓangaranci:    Aka raba ƙasa kudu da arewa bisa cin amana.
Zumunci:        Ƙarya ta yi tsaye ta ɓata zumuncin masu gaskiya domin ta
hana su zama su fahimci bambance-bambancensu.
Tsoro/Barazana: An ba gaskiya tsoro da ƙarfin iko, an yi mata barazana
da wakilan tsaro, ta dai yi tsaye ta ƙi ta sake suna ta ce: “Gaskiya sunanta gaskiya”.
Tsafe-Tsafe:   Ƙarya ta haifar da ƙungiyoyin asiri barkatai ta fito da ƙarfin
tsafi ta fargagi gaskiya. Ina! Gaskiya ta yi tsayin daka ta tabbatar da mai gaskiya yana tare da Allah.
Ƙarya: Ta gaji da sari-ka-roƙe, ta fito ta soki gaskiya da rashin
takardun shaidar karatu. Ta kushe gaskiya da cewa ta tsufa. Ta zarge ta da hamɓare wata daula irin ta. Ta aza mata laifin zanga-zanga. Duk aka ƙare ta bisa doron karin maganan “kowa ya yi cinikin ƙarya ya yi biyan gaskiya”.
Waɗannan abubuwa kaɗan ne daga cikin zagon ƙasa da taron dangi da ƙarya ta yi gangami domin a yi wa gaskiya ature. In ban da gaskiya dokin ƙarfe ce, wa ke karɓe mulki ga mai mulki ba tare da ya kafa mulki irin mulkin mai mulki ba? Duk da kasancewar tsafi gaskiyar mai shi, ya tsaya ga mai shi, ya bar gaskiya tama. A tarihin demokraɗiyyar Afirka, gaskiya ba ta taɓa ba mutane mamaki ba kamar yadda ta bayyana a zaɓen shekarar 2015 a Nijeriya. Sakamakon zaɓen ya sabunta wa ‘yan ƙasa tunani, da dama suka dawo da rakiyar fahimtar mai sanda ke da fasalin bugu. Zancen cewa: “Gaskiya ta gama aiki”, a Nijeriya an ƙaryata shi. In ba gaskiya, babu abin da ke haɗa kan mutane mabambanta addini da aƙida da al’adu wuri ɗaya, a fuskanci abu ɗaya a yi tsaye a kansa, a tabbatar da shi, sai mai kushe ta ya ji kamar mafarki yake.
Baje Kolin Gaskiya A Ƙunshiyar Karin Magana:
Tunanin wannan takardar ya tattara ga irin yadda Bahaushen tunani ke kallon gaskiya a ƙunshiyar karin maganganunsa. Bayan an yawata da karuruwan maganganun a wurare daban-daban na baje kolin gaskiya, na ga ya dace a tattaro su gaba ɗaya a ɗora su kan zango-zango na gaskiya da suka baje koli.
Suna:
Bahaushe bai taɓa bai wa kowane irin abu sunan gaskiya ba. Sunanta ɗaya ne, ita kaɗai ke da shi, da shi aka san ta, baya da jam’i ba ya ninkuwa don haka yake da:
1.                  Gaskiya sunanta gaskiya
2.                  Gaskiya da gaskiya ake gaishe ta.

Lafazinta:
Sanin cewa, ga lafazi ake fara kirdadon gano gaskiya Bahaushe ya fi bai wa maganganun gaskiya muhimmanci. Sanin haka ya sa wasu sassa daga karuruwan maganganun ke cewa:
1.                 In za ka faɗi, faɗi gaskiya
2.                 Maganar gaskiya a yi ta da wando
3.                 Maganar gaskiya harshe ba ya rawa
4.                 Faɗin gaskiya sai namiji.
Muhallinta A Harshe Da Kunne Da Zuciya:
Idan aka furta gaskiya a tunanin Bahaushe mafaɗinta gwarzo ne domin ya yaƙi harshensa. A kunne za a fara jin irin nauyinta, zuciya ta ba da labarin launinta, ɗanɗanonta, raɗaɗinta, ga su nan dai:
1.                 Gaskiya mugunyar magana
2.                 Gaskiya mai ɗaci
3.                 Abu da ciwo kamar gaskiya
4.                 Farar gaskiya
5.                 Baƙar gaskiya (ba a cika faɗar haka ba)
6.                 Gaskiya mai ciwo
7.                 Faɗin gaskiya ya fi mugunyar salla
8.                 Gaskiya mai daɗi
Zatinta da Ƙarfinta:
Duk da yake gaskiya a nahawu ɓoyayyen suna ne, Bahaushe na ba ta zati da ruhi irin na mai rai domin ita ke riƙe da kafaɗun masu rayuwa. Duk wani ƙwazo da mazakuta da dabara sai da gaskiya ake yin sa. Harari waɗannan karuruwan magana da idon basira:
1.                 Gaskiya dokin ƙarhe
2.                 Gaskiya mai nauyi
3.                 Gaskiya ka faɗa ba sanda ba.
4.                 Gaskiya ta yi halinta.
Dangantakarta Da Mutane:
Daga cikin karuruwan maganganun da suka baje wa gaskiya koli akwai waɗanda da kallonsu suna da alaƙa da maƙagan su domin kowane irin adabi masu shi suka ƙago shi. Dubi waɗannan sosai:
1.                 Gaskiya a ƙi ki, a so ki.
2.                 Da ƙin gaskiya sai ɓata
3.                 Ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.
4.                 Na ɗaure mene ne gaskiyar maza? Ya ce: “Gaskiyar maza a sake su”.
5.                 Mai son gaskiya ka faɗa maka gaskiya.
6.                 Tsafi gaskiyar mai shi.
7.                 Gemu babu gaskiya ko na bunsuru ya fi shi.
8.                 Kowa ya ƙi gaskiya rabo nasa ƙunya.
9.                 Da ƙarya ta raba ka da mutum gara gaskiya ta raba ku.
10.             Gaskiya mazan tsaye taka so.

Dangantakarta Da Akasinta:
Wasu karuruwan maganganun Bahaushe raba ƙafa suke yi, ido ga kifi, ido ga bado. Bayan sun karɓi baƙuncin gaskiya suka karɓo uzurinta na ƙin ƙulla abota da ƙarya. Karuruwan maganganun da suka yi wannan hasashe sun haɗa da:
1.                 Gaskiya mai korar ƙarya
2.                 Abu kamar gaskiya karuwa ta ga noman ɗan koli
3.                 Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi
4.                 Gaskiya ba ta neman ado ko zaƙin muryar zabiya
5.                 A daɗe ana yi sai gaskiya.
6.                 Gaskiya ina laifinki?
7.                 Ba gaskiya awo a ɗaki


Hana Rantsuwa:
A cikin kowane irin al’amari na ilmi, ba za a rufe ƙofar abu ba gaba ɗaya. Dalilin da ya sa ake raga tazara domin ɗan Adam ɗan tara ne bai cika goma ba. Tattare da irin ƙimar da ke ga gaskiya a kowane al’amari ana ɗan samun wasu karuruwan maganan da suka ɗan zarge ta da yawan haƙuri da rashin wayo irin na yaudara. A ganina, waɗannan su ne hana rantsuwa da cewa, gaskiya ba ta taɓa samun zargi ga kowa ba. Ga hana rantsuwa.
1.       Faɗa da gaskiya tsoro ne.
2.       Ba gaskiya ba ce ga shari’a kai dai a samo sa’a.
Takin Saƙar Zamaninmu da Ƙunshiyar Karuruwan Maganan Gaskiya:
Adabi ƙawataccen asirin gudanar da tsarin rayuwa ne da aka gada kaka da kakani. Yadda gaskiya ta samu baje koli a karin maganan Bahaushe, bai kyautu a ce, akwai zamanin da za a yi mata barazana ba. Taskar adabinmu ta tababtar da gaskiya dadaddiyar abu ce a ƙasarmu. Babu shakka, mun gaji gaskiya ga magabatanmu. Lallai tun gabanin saduwa da kowace al’umma da addini da aƙida da wayewa Bahaushe yake da gaskiya. Ga irin ƙunshiyar karuruwan maganganunmu na gaskiya da wuya a sami wata al’umma a farfajiyar duniyar yankinmu da za su gwada tsawo da mu a kan tafiyar da gaskiya da yarda da ita. Idan haka ne, yaya aka yi yau an wayi gari:
1.                 A hulɗoɗin zamantakewarmu gaskiya ta yi ɓatan dabo?
2.                 A al’amarin gudanar da siyasar mulkinmu an ƙi ba gaskiya kujera ko ɗaya? An bar a tana shawagi, wai dole in ta gaji ta san wurin da dare ya yi mata?
3.                 Wurin masu addini da gaskiya take a rubuce, yau shafin ya ɓata cikin shafuka, wanda ya ce, zai binciko shi, a barkace masa tunani?
4.                 Manyan da, da su ke ƙwato wa gaskiya haƙƙinta, a yau wajensu ake karatun dabirta gaskiya?
5.                 Tsarin ilminmu da aka kafa bisa gaskiya, yau har ɗalibi ya karɓi takardar shaidar sauke karatu ba su taɓa kuren hanyar haɗuwa da gaskiya ba?
6.                 Me ya sa masu gaskiya a yau suka kasance ‘yan tsiraru, ƙauyawa, marayu, marasa galihu, talakawa, wawaye, toshon yayi ko tsohon alkawali?
Wanda duk ya san irin gurbin da ke ga gaskiya cikin adabinmu musamman cikin karuruwan maganganunmu, tilas, ya girka tagumi a kan halin da Bahaushe yake ciki a yau. Abin ban mamaki, babu wanda ya taɓa jarraba gaskiya a kowane al’amari ya kasa samun biyan buƙata. Babu wanda zai zargi gaskiya da wani muni a taɓa masa. Babu mai ganin laifinta ba a ga laifinsa ba. Babu mai takin saƙa da ita, ya cika muna ido da zuciya. Ba mu taɓa jin ɗan kokuwan da ya yi ƙarfinta ba wajen mugun kaye. Cikin ‘yan dambe, ba a samu mai maƙetacin bugu ba irin nata. Ma’abota sharo sun san sandarta ta fi ta kowa tsawo da nagartaccen ƙarfi da nauyi ga haƙarƙari. Wai a ce, duk da sanin waɗannan abubuwa, gaskiya ta tsawwala cikinmu, idan ta tunkaro mu, mu yi malle, idan ta riske mu, mu yi na bushiya, idan ta lalabo mu, mu zama kunkuru, sai ta ɗaga mu fitar da ƙafafu da hannuwa.
Ga alama, abubuwan da suka sa muka rafashe ga riƙon gaskiya irin yadda magabata suka tabbatar a karuruwan maganganunsu ina ganin akwai:
Kwaɗayi:    Hausawa sun ce: “Shi ne mabuɗin wahala”. Ga mu nan a
cikinta. Yaushe za mu fita? Sai mun sallami tsohon nan kwaɗayi.
Son kai:      Hausawa sun ce: “Mai sa son banza”. Yau son banza ya kai
mu ga aikin banza da maganganun banza. Me ke sa ma’aikatan hukuma rashin gaskiya? Son kai ke sa sata.
Son girma: Hausawa sun ce: “Mai kashe girma, yau ga girman nan
gingiraɓai ta kasa tayar da kanta bale a dafi kafaɗarta a tashi.
Rashin mutunci: Mutuncinmu ga kowa shi ne abin duniya da muka tara,
wanda bai tara ba, ba kowa ba ne. A ƙarshe, ga mu mutane waɗanda ba mutane ba na shugabantar mu. Dole gaskiya ta gudu.
Sakamakon Nazari:
A kowane zamani, adabin mutane na tasiri a kan rayuwarsu. Idan ana son a daidaita abubuwan da suka lalace a cikinsu, a harari adabinsu cikin natsuwa a ga yadda za a ceta musu da shi. Na tabbata ban yi son kai ba, idan na ce, duba cikin karuruwan maganganun Hausawa da suka fuskanci gaskiya wata shaida ce ta cewa, Bahaushe gaskiya gwaggonsa ce domin ya gaje ta, kuma ya sha ta a nono. Idan aka yi duba cikin manyan sarakunan Hausa tun na gargajiya ya zuwa yau, za a tabbatar da haka. Ashe gaskiyar Shawith Smith da ya rubuto ta’aziyyar Sarkin Gwandu Yahya cikin jimla ɗaya da cewa “Ƙur’ani don gaskiya ake tsoron ka”. Tirƙashi! Ba Muhammadu Buhari kawai ne sojan da ya riƙi Nijeriya ba. Idan lokacin da, yana soja, bindiga ake tsoro, yanzu da ya sa farin kaya, me ake tsoro? A ɗan nawa tunani, gaskiyar Buhari ake tsoro ba sunansa ba, ba muƙaminsa ba, ba tsawonsa ba, ba addininsa ba, ta harshensa ba, ba ƙabilarsa ba, ba jam’iyyar siyasarsa ba. Wannan kaɗai wata madogara ce ta cewa, adabinmu ya yi tasiri ga magabatanmu domin Muhammadu Buhari ya tabbatar da haka. A wannan ɗan bincike na lura da abubuwa kamar haka:
Gaskiya buwayayyiya ce tun a sunanta da sifarta da halayenta. Babu shakka, ta ci ragon sunanta domin babu wanda aka haifa a duniya da ba ya son a danganta shi da ita. Babu mai rai da ke son a zarge shi da rashin ta. Wanda duk ba ya da ita tsoron kowa yake yi. Wanda ya riƙe ta ya wuce tsoro, dole a tsorace shi. Dalilin da ya sa ake tsoron gaskiya da masu ita a yau, domin marasa gaskiya sun yawaita, aikin rashin gaskiya ya mamaye duniya. Gaskiya ta fi mulki ƙarfi, ta fi hukuma iko, ta fi ilmi farin jini, ta fi lafiya amfanin mai ita, ta fi wayo da hankali kare martabar suna, ta fi dukiya ɗaukaka suna, ta fi kyauta tagomashi. Domin tabbatar da ita ake yaƙi, ganin ta ke sa aje makamai, ɗammahar ta ke sa a yi sulhu. A kan kowace irin tahiya gaskiya ita ce godabe. Idan an yi ɗemuwa ita aka baro, idan an kai ga zango an yi dace da ita. Na dai yarda da tunanin Bahaushe, gaskiya ina laifinki?.

Malamaina da abokanin aikina da ɗalibanmu (in da su) ina son in yi ‘yar tambaya. Wai wane laifi gaskiya ta yi wa ilmin boko na rashin sama mata darasi mai cin gashin kansa a kowane fannin ilmi mai suna “gaskiya”? A ɗan nawa gani, in kowa zai manta da haka, bai kamata ɗan Nijeriya ya manta ba, musamman idan aka dubi takardarmu ta kuɗi naira ashirin da shugaban ƙasarmu na 2015. Don haka na ba da shawara mu fara tunanin ƙago darasi mai take “Gaskiya”.

Naɗewa:
Ba don da Bahaushe ya ce lokacin abu a yi shi ba, da na ce, a bar kaza cikin gashinta. Sanin sai da ruwan ciki akan jawo na rijiya na tuna da tafiya da waiwaya tana maganin mantuwa. A tunanin magabatanmu in abu ya ɓata bai kamata hankali ya ɓata ba don haka suke ganin, in raƙuminka ya ɓata babu laifi ko cikin akurki (-n kaji) a rega domin ɗebe kokanto. Gaskiyar magana ita ce, ana dare ga dara ya yi, sai aka ci nasara ana cikin gina ga wutsiya. Tattare da sanin cewa, aiki ya yi wa kurege yawa, amma dai aikin Magaji ba ya hana na Magajiya. Ban yarda da cewa, wanda ya yi nisa ba ya jin kira ba, sai dai idan mai kira bai ɗaga murya ba, ko iska bai buga gefen wanda ake kira ba, ko wanda ake kira bai san kiransa ake ba, ko kuma ba ya ɗammahan a kira shi. A cikin halin da ƙasarmu ta shiga har mun fara zaman dako a aza ranar zaman makoki. Da malamai da bokaye da likitoci kowa ya yi abin da ya sani, aka sa wa mai yi ido. Buwayayye, zama ɗaya ya aiko buwayayyiyar baiwarSa “Gaskiya” marasanta suka ce, “In ba ku yi ba mu wuri”! Tabbas, sanin wurin bugu shi ne ƙira. In ka ji riƙa mini kayana, Hausawa sun ce: “Ba zawo ya koro mai kayan ba”. Wanda duk ya ga duhun dare, ba a ɗaure shi ya kucce ba. Haƙiƙa, wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokuwa. Aradu! Gaskiya ta san a ko’ina ƙarya ta ɓoye kayanta, ku tambayi Malam Muhamamdu Gambo Fagada ku ji:

Jagora: Kaicon na kai na!
          : Halin duniya na ba ni tsoro!
          : Wai ga maciji ana ta/.
          : Biyas shayi da sanda!
          : Wai ga ɓarayi
          : To, mib biɗi mai waƙar ɓarayi?
Amsa ita ce: Rashin gaskiya.
  
        GASKIYA MUNA GAISHE KI.


Manazarta

Aliyu, M.S. (1980) “Sharotcomings in Hausa Society as Seen by
Representative. Hausa Islamic Poets from Ca 1950 to Ca 1982” M.A. Thesis, Knao: Bayero University.

Bunza, A.M. (1996). “Gaskiya Ina Laifinki? Tsokacin Diddigin
Musabbabin Karyewar Arzikin Nijeriya Cikin Waƙar “Gaskiya Mugunyar Magana” ta Alhaji muhammadu Sambo Wali Basakkwace” Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Bunza, A.M. (2000). A Daɗe Ana Yi Sai Gaskiya: Laluben Gurbin
Gaskiya Cikin Adabin Hausa,” Mukala: Sokoto: Jami’ar usmanu Ɗanfodiyo.

Burji, B.S. (1997). Gaskiya Nagartar Namiji, Kaduna: Baraka Press.

Dangambo, A. (1984). Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga
Rayuwar Hausawa, Kano: triumph Publishing Co.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa,
Edinburgh: University Press.

Muhammed, I. (1996). “Gaskiya Da Raha A Cikin Littafin Ruwan
Bagaja, Sharhin Ciki da waje” Kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.

Muktar, D. (1983). In Za Ka Faɗi Faɗi Gaskiya, Zari’a: Huda-Huda
Publishing Company.

Mustapha, S. (2003). “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”. Kundin
MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Skinner, N. (1971). Realism and Fantasy in Hausa Literature, in MAN.

Umar, M.B. (1987). Dangantakar Adabin Baka Da Al’adun Gargajiya, Na
Hausawa, Kano: Triumph.
 
 




No comments:

Post a Comment