Ƙoshin lafiya
shi ne makamin farauto kowane irin amfani a rayuwa. Wadataccen hankali shi ne
maganaɗisun zamantakewa. Ilmi wani
babban gamji ne na hutawar masu lafiya da hankali, domin more abubuwan da
lafiya da hankali suka kalato. Haƙiƙa, biri ya
yi kama da mutum, a tarihin farfajiyar ƙasar Illela,
ba a taɓa taro na nuna farin ciki a
kan samun ƙoshin lafiyar mutanen Illela ba. Ko shakka babu,
ba mu taɓa taruwa a Illela ba domin
bukin kasancewarmu masu hankali. Cikin…….
---------------------------------------------------
DAGA
ALIYU MUHAMMAD BUNZA
Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar
Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina.
--------------------------------------------------------
Takardar da aka gabatar a buki na
musamman domin karrama Farfesa Aminu Abubakar da Alhaji Bello Isah
Ambarura da Sanusi Umar Illela da Jama’ar Ƙaramar
Hukumar Illela, Jahar Sakkwato suka shirya ranar Asabar, 14 ga
Disamba, 2013 a farfajiyar Ƙaramar Hukumar Illela.
Gabatarwa
Ƙoshin lafiya
shi ne makamin farauto kowane irin amfani a rayuwa. Wadataccen hankali shi ne
maganaɗisun zamantakewa. Ilmi wani
babban gamji ne na hutawar masu lafiya da hankali, domin more abubuwan da
lafiya da hankali suka kalato. Haƙiƙa, biri ya
yi kama da mutum, a tarihin farfajiyar ƙasar Illela,
ba a taɓa taro na nuna farin ciki a
kan samun ƙoshin lafiyar mutanen Illela ba. Ko shakka babu,
ba mu taɓa taruwa a Illela ba domin
bukin kasancewarmu masu hankali. Cikin ikon Allah, a yau, ga mu hallare domin
bayyana wa duniya wata ɗaukaka da
Allah Ya bai wa ‘yan’uwanmu ta ilimi da ɗaukakar da
suka samu sanadiyyarsa. Ashe ban yi kure ba, idan na ce, ƙoshin
lafiyarmu ya yi muna akala zuwa halartar wannan taro. Hankalinmu ya nuna muna irin
muhimmancinsa. Don haka, ku bari in faɗi da babbar
murya cewa, da lafiya da hankali talakawa ne, ilmi ne uban ƙasa domin
shi kowa ya tabbatar da lafiyarsa da hankalinsa da basirarsa. A gai da iyayen ƙasar Illela,
Allah Ya yi muku jagora.
Mene ne Ilmi?
A Hausance,
“Ilmi” baƙuwar kalma ce mai ƙoƙarin yi wa
kalmar “sani” tawaye. A fayyace abu ta fuskar ƙwanƙwance
amfanoninsa, da ƙididdige illolinsa, da ƙyallaro
dambarwarsa, da sarrafa fuskokinsa, da yin kane-kane cikin zarafinsa, masaninsa
ya zamo hannu ya iya jiki ya saba, ko an daka cikin turmi da su cikin masu
fita. Wannan shi ne taƙaitaccen li’irabin sani a wajenmu ɗalibai. Idan ba ku manta ba, mukan ji magabata
na cewa, sanin wurin bugu shi ne ƙira. Sanin
asali kan sa kura cin kanjilo (ƙonannen kashin shanu).
Dillalin wada shi ya san kuɗin jariri.
Rashin sani ya fi dare duhu. Ban sani ba ta raba ka da kowa. Sanin
halin direba sai fasinja. Ƙaramin sani ƙuƙumi ne. Ke
nan, “sani” shi ne fahimtar abu na ƙin ƙarawa har a
zama malaminsa. Wannan ita ce fatar duniyar ƙarninmu (ƙarni na 21),
kuma kowace ƙasa ta kasa biya wa mutanenta wannan buƙata durƙusasshiyar ƙasa ce.
Masana na cewa, daga cikin ma’anonin
sani (ilmi) akwai aiki da shi. A ga ya bayyana ga mai bayar da shi. A ga
nasonsa ga mai karɓarsa. A ga
tasirinsa ga wurin da ake aikata shi. A ji samatarsa ga zantukan al’ummar da ya
wanzu. A ga haskensa ga fuskokinsu. Yadda za a tabbata waɗannan batutuwa shi ne, bai wa ma’abota sani
gabaci ga abin da suka sani. Idan aka yi haka, an yi wa sani adalci. Ma’abota
ilmi na duniya (UN da UNESCO) sun yi canjaras a kan sakaɗa fasahar karatu da rubutu cikin shikashikan
ilmi. Don haka, ga musulman Nijeriya ilmin boko ba komai ba ne face cikon sunna
makaho da waiwaya, domin ko kafin a haifi uwar mai sabulu balbela tana da
farinta.
Ƙalubalen
Ilmi a Ƙarni na 21
Kowace
nahiya ta duniya da irin ƙalubalen da suke fuskanta na ilmi. Da Turai da
Asiya da Ƙasashen Larabawa da Afirka duk ƙarancin kuɗi na yi wa ci gaban ilminsu barazana. Akwai
matsalar kayan aiki, idan aka dubi yadda ilmi ke bunƙasa.
Wadatattun malamai ƙwararru wata babbar matsala ce. Yalwataccen
muhallin bayar da shi da karɓarsa shi ke
hana ruwa gudu ga bunƙasarsa. Rashin aikin yi ga waɗanda suka sauke karatu na hana wa mai niyyar
shiga miƙa wuya bori ya hau. Yawaitar manyan makarantu da
Jami’o’i masu zaman kansu a duniyar ƙarni na 21
ya yi wa ilmi babban cikas na rage masa daraja da gwaɓi da kauri da inganci da kwarjini da ɗaukaka ga idon na bayan fage. Bai wa samun
takardun shaida muhimmanci shi ya haifar da maguɗin
jarrabawa, samun takardar shaidar zur, digirorin girshi da digirorin gado, ga
su nan dai. Waɗannan
matsalolin ruwan dare ne a duniyar zamaninmu.
Tattare da waɗannan matsalolin ilmin ƙarninmu da
ya fuskanci duniyar zamaninmu gadan-gadan idan muka dubi fannonin fasaha da
kiyon lafiya da ƙere-ƙere da
tattalin arziki da sufuri da kimiyyar noma da gine-gine da sadarwa da dai
sauransu. Abin baƙin ciki, an bar Afirka da ilmin takarda na
rubutun jarrabawa, Turai da Asiya suka ɗauki alƙalamin
sarrafawa. Ina tsoron in ce, an bar mu da karatun Aku, domin ina jin har yanzu
babu ƙasar da ake ƙera keke
abin a zo a gani a nahiyarmu. Gwanjon tsumma na bura-bura da akirka su ne
kangararrun matasanmu ke ƙawa da su, wai su gayu. Taɓa jikin motoci da babura su ne masu halinmu ke
taƙama
da su ana doro wai an take. Magungunansu na gargajiya yau su ne namu na zamani.
Kaɗe-kaɗensu
da bushe-bushensu da waƙoƙinsu da
raye-rayensu yau su muka ara muka yafa muka watsar da namu. Harshensu shi ne
ma’aunin gane ma’ilmanci a cikinmu. Tsarin siyasarsu ta aljanna ta mai ƙarfi ce sai
in ba a yi shigan shanu ba, yau ita ce addininmu. Masarautunmu na asali mun
tozarta su. Yau shugabanninsu su ne shugabannin duniya, namu masu yi musu gadi
ne. Rayuwarsu ita ce rayuwa, wadda ba ita ba dabbanci ce. Addininsu shi ne
addini, kininsa sunansa ta’addanci. Kaico! To, ina amfanin ilminmu na asali da
na ƙaddara
muke hura hanci da shi a yau?
Hangen waɗannan matsaloli muka shirya wannan gagarumin
buki na nuna farin cikinmu ga samun kujerar Shaihin Masani Aminu Abubakar, na
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, da Magatakardan Dindindin,
Alhaji Bello Isah Ambarura, da Mataimakin mai kula da Taskar Tarayya ta aikin ƙasa, Alhaji
Sanusi Umar Illela. Da na jinjina takardun waɗannan
managarta sai na ga, bai kamata mu yanke ƙauna ba, in
da rai da rabo. Fatarmu ita ce, Farfesa Aminu ya fito da wani sabon salon da
zai bai wa ‘yan bokon Illela ƙarfin guiwan burin kai ga
irin matsayinsa. Alhaji Bello Isah da ya riga ya kai sin-wau-ra-takuri a cikin
ofis ya sama wa matasan Illela gurabun aikin more wa karatunsu da suka yi.
Alhaji Sanusi Umar ya mara musu baya a tabbata Illelawa ba su yi karatun Aku
ba, bale a bar su a baya ga garaɓasar
kimiyyar ƙarni na 21. Ku sani haihuwa hutawa ce, kuma
samun ɗa nagari nagartacce irinku a
irin wannan zamani shi ake ce wa tsintuwar guru cikin suɗi.
Lokacin Abu a yi shi
A duniyarmu ta yau, boko ne makamin yaƙi. Boko ne
hajar kasawa a kasuwa. Boko ne noman rani da damina. Boko ne sarauta, kuma shi
ne siyasa. Don haka, babu makawa gare mu face buɗe
gaba (ƙirji) ga kibiyar da ba ta kure. Wajibi ne ga
hukuma ta kyautata makarantun Firamare yara su samu tushe nagartacce ga
ilminsu. A inganta makarantun gaba ga Firamare da ƙwararrun
malamai da kayan aiki. A fito da wata dabara ta bai wa ɗaliban digiri tallafi daga ƙananan
hukumomi. Masu hannu da shuni su fara kafa gidauniya ta musamman domin agaza wa
haziƙan ɗalibai su
samu manyan digirori. A tilasta wa manyan ma’aikatan kowane gari sa hannunsu tsamo-tsamo
ga tafiyar da makarantun da ke ƙarƙashin riƙonsu ko
gundumarsu. A sake tunanin yadda za a kyautata wa malamai albashi da rayuwarsu
domin sai in an yi shuka ake zancen tumu. Idan aka fito da tsarin tabbata wa
duk wani ɗalibin da ya kammala karatu
da nasara sama masa aikin yi, tsaron ƙasarmu da
tarbiyyarmu za su inganta. A haramta kowane ofishin siyasa ga duk wanda ba ya
da takardun shaidar ya ci jarrabawar da ya sauke. Da dai za a keɓe kujerar Shugaban ƙaramar
hukuma da kujerar Majalisa ta kowane mataki ga masu digiri kawai, da za mu
tabbata hutawa ka alewa man gyaɗa ka tuyar ƙosai.
A fahimtata, taɓarɓarewar
tarbiyyar yaranmu rashin tsaftataccen ilmi ya haddasa shi. Rashin tsaro da
ta’addanci kuwa, talaucin da ke cizon matasa da rashin aikin yi ya ba su damar
shiga Jami’ar Aljanna gafara wuta salamu alaikum (ƙundumbala).
Matsalar da wannan ƙasa tamu take ciki a yanzu babban makamin
fuskantar masu son su yi wa kaburburan kakanninmu fitsari da tsaye shi ne ilmin
boko. Mu yi tsayin daka, mu yi shi ido buɗe, muna sara
muna duban bakin gatari. A wajenmu ɗalibai, duk
garin da ya samu ɗan bokon da
ya hau kujerar Farfesa sun riga sun yi wa jahilci ƙofar raggo.
In jahilci matar aure ce, sun yi mata saki uku. In jahilci dabba ce, sun yi
mata duka/bugun kawo yuƙa. Daga yau masu lissafa Illela cikin ƙananan
hukumomin da aka baro baya ga Ilmin boko an sa wa bakinsu takunkumi, daɗa babu sauran kukurukudu Inyamuri ya harbe
kurciya.
Dare ka yi Maraice ya yi
Hausawa na cewa, hankali ka gani ba
ido ba. Mun san abin da wayo ya ɓoye hankali
na gano shi. Abubuwan da ke faruwa a ƙasarmu sun
fara zarce aya zaƙi. Kisan gilla da cin zarafi da wulaƙancin da ake
yi muna da sunan ƙabilanci da bambancin addini da ɓangaranci ƙarƙashin
yaudarar dimokoraɗiyya ya wuce
gona da iri. Ala tilas mu yi amfani da bokonmu da addininmu da siyasarmu mu
‘yantar da kanmu cikin wannan bala’i. Dole mu yi watsi da bambance-bambancen
fatin siyasa, da ƙabilanci, da saɓanin
fahimta ta addini da wayewa, mu fuskanci bala’in da ake son a haddasa wa yankunanmu
saboda ƙiyayya da mu da addininmu. Mu kafirce wa kowane
fatin siyasa da ke cikin ƙasa mu kafa sabon fati mai take: YANKINMU
ADDININMU AL’ADUNMU DA ‘YANCINMU. Abin da ya gabata ba mu yafe ba Allah Ya isa.
Abin da ake ciki yanzu Allah Ya yi muna maganinsa. Shirin da aka yi na gaba
Allah Ya wargaza shi. Addu’a makami ce, amma waɗanda
ke gallaza muna yau ba da addu’a suke gallaza mu ba. Don haka, karen da duk ya
yi cizo da gashinsa ake magani. In til in kwal rinin mahaukaciya. In ta yi ruwa
rijiya, in ba ta yi ba masai. Haƙiƙa Larabawa
sun faɗi gaskiya:
Mallam ya
mut bis saifi
Maata bi gairihi
Tanawwa’atul
asbaabu
Wal mautu wahidun
Ashe gaskiyar Ɗan’anace bai
yi laifi ba da yake ce wa Shago:
Jagora: Tafi a kashe ka gaba ɗai,
:
Wandara mi kakai da rai ga arna,
:
Ai ko an kashe ka ba a da suna,
:
Don ɓannad da kay yi ta aka gyara,
:
In ko ka kashe su ka yi gaba ɗai,
: Wandara maso rai wawa!
Matsoraci da raggo ba su da rana ga
addininmu da al’adunmu. Hatta a fagen rashin gaskiya in ta yi cin alewar
kuturu. Dubi yadda Alhaji Gambo ke ce wa ƙwarinsa:
Jagora: Mi kaka shakka ga ni ga ka!
:
Ɗauri
kaka shakka ko kashewa?
:
Kaicon na kaina!
:
Gambo mai taɓa turayen
mugunta.
Naɗewa
Bokonmu ba
ya da amfani in bai ƙwato muna ‘yancinmu ba. Al’adunmu ba su amfane
mu ba, in ba su kare mutuncinmu ba. Harshenmu ba ya da wata rana, in bai ɗebe muna takaicin maƙiyanmu ba.
Wayonmu bai amfanar da mu da komai ba, in mun kasa ƙwace goriba
hannun kuturu. Yawanmu bai amfane mu ba, idan mun kasa fitar da suhe wuta. Wace
sabuwar waƙa za a sake ji idan maƙoƙo ya fito a
bakin zabiya? Mun gaji da aikin banza wa kare wanka. Da ƙarfinmu da
lafiyarmu a sa mu jiran gawon shanu. Wane sakaci ya fi wannan gyaran zama na
baya ga walle. Haba! A ce ƙaton raggo da bai taɓa kashe wa kansa nama ba, mu kamo mu ba shi, ya
cinye, ya sa wawayen makaɗansa yi muna
kiɗa har da rawa da waƙa:
: Kai mai kiɗi kiɗa in jiya,
: Ba ka da aiki mu ba mu da,
: Mu taru mu lalace mu duka.
: Kai!
Kakanti! Katingam! Tingam!
No comments:
Post a Comment