Farfajiyar
ƙasar
Hausa tana da nagartattun dauloli bakwai da suka mamaye duniyar adabin
Bahaushe: Kano, Katsina, Gobir, Zazzau, Zamfara da Kabi[1][1]. A Kano,
Bagauda ya kere kowa. A Katsina kamar ba kowa sai Katsi. A Gobir, Jangwarzo ya
hana a ji wani gwarzo. A Zazzau, Amina ta yi wa rawuna da wanduna fintinkau. A
Zamfara, ‘Yargoje ta ciri tuta. A Kabi, Kanta ne kan kowa. Muradin wannan
takarda kallon Daular Kabi a dunƙule, tare da
baje hajar nazari a kan ikon Sarkin Kabi Muhammadu Sama cikin taskar
bakandamiyar mawaƙin masarautarsa Buda Ɗantanoma mai
take: “Gagara Ƙarya Sadauki; Sama Gwarzon Alƙali”. Alƙiblar
nazarina ba ta rena...
--------------------------------------------
Daga
Aliyu
Muhammadu Bunza
Department
of Languages and Cultures
Faculty
of Humanities and Education
Federal
University Gusau
----------------------------------------------------
Takadar
da aka gabatar a Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo
University Sokoto, Second National Conference: Theme: History, People, Religion
and Culture of Kebbi (Kabi) Kingdom since 1515, 10th-12th
July, 2017
Gabatarwa
Farfajiyar ƙasar Hausa
tana da nagartattun dauloli bakwai da suka mamaye duniyar adabin Bahaushe:
Kano, Katsina, Gobir, Zazzau, Zamfara da Kabi[2][1].
A Kano, Bagauda ya kere kowa. A Katsina kamar ba kowa sai Katsi. A Gobir,
Jangwarzo ya hana a ji wani gwarzo. A Zazzau, Amina ta yi wa rawuna da wanduna
fintinkau. A Zamfara, ‘Yargoje ta ciri tuta. A Kabi, Kanta ne kan kowa. Muradin
wannan takarda kallon Daular Kabi a dunƙule, tare da
baje hajar nazari a kan ikon Sarkin Kabi Muhammadu Sama cikin taskar bakandamiyar
mawaƙin masarautarsa Buda Ɗantanoma mai
take: “Gagara Ƙarya Sadauki; Sama Gwarzon Alƙali”. Alƙiblar
nazarina ba ta rena da kallon zubi da tsari, salo da sarrafa harshe da fyace
diddigin jigo/jigogin waƙar ba. Na bar su ga ƙwararrun
masana adabi su yi nasu buki a kan waƙar. A nawa
tunani, zan yi amfani da ma’auni al’ada na biyar ƙididdiga da
fashin baƙin kuramen ɗiyan waƙar da ke da ɗaukar hanakli da shiga zukatan waɗanda aka wa waƙar, da
abokan gwagwarmayar su. Wanda duk ya saurari fasahar Buda cikin bakandamiyarsa
ya san waƙar yaƙi ce, waƙar tarihi
ce, waƙar tankiya ce, waƙar tawaye
ce, kuma waƙar gwagwarmaya ce, kar ta san kar, aljani ya
taki wuta.[3][2] Waɗannan su ne
gurabun da ake son a harara a cikin waƙar.
Wane ne Buda Ɗantanoma?
A
iya sanina, Sa’idu Muhammadu Gusau ya sha cewa wani abu a kan Ɗantanoma a
rubuce.[3] Ƙari bisa ga
binciken Sa’idu shi ne, Buda Ɗantanoma mutumin ƙasar Yabo
ne. An ce, shi ne babban makaɗin sarkin
Yabo Shehu. Tun fil azal makaɗin tankiya
ne. Idan ya ɓaro kiɗinsa na tankiya ya yi jaye-jaye, ya yi wa
Sarkinsa Shehu laifi aka koro shi, sai ya ruga Argungu ya ɓoye wajen maigidansa Muhammadu Sarkin Muza
Bawaya. Da dubu ta cika, ya dinga yi wa Sarkin Kabi Sule habaici a waƙa aka tare shi
aka karɓe turayensa aka rataye su
gidan Sarki[4]. Bayan rasuwar Sarkin Kabi Sule, maigidansa
Muhammadu Sama’ilan Nabame ya hau, ya dawo Kabi ya kama halinai.
Asalin
sunan Buda Muhammadu, sunan “Buda” suna ne na yanayi na wanda aka haifa ana
matsanancin hazo. A ƙasar Hausa, sunan “Muhammadu” ba ya ambatuwa ƙarara gaya
domin kamar sunan uban kowa ne. Ana yi wa Buda laƙabi da “Ɗantanoma” ya
yi rinjaye. Yana da ‘yan karɓi a waƙarsa, an ce,
kotso yake kiɗa. Yana da
‘ya’ya biyu sanannu, ɗaya mace mai
suna “Abingani” da namiji “Muhammadu”. Abingani a Argungu ta rasu, Muhammadu
kuwa ya fara ‘yan waƙe-waƙen gado, ya
bari, ya shiga duniya babu ɗuriyarsa.
Akwai saɓani da yawa a kan barin waƙar Buda da
rasuwarsa[5].
Salsalar Sarkin Kabi Muhammadun Sama (1920-1934)
Bayan
Sarkin Kabi Kanta babu sarkin da ya yi amo a daular Kabi da zukatan Kabawa
kamar Sarki Sama. Sarkin Kabi Sama’ila jikan Sarkin Kabi Sama’ila Karari ne
kuma ɗan tsatso ga Sarkin Kabi Yakubu
Nabame. Shi ya gaji Sarkin Kabi Muhammadu Toga. Yakubu Nabame yana kan karagar
mulki daula ta rushe ‘ya’yan sarauta suka warwatse don kare mutuncin gidajensu
ga hannun maƙiya. Wasu suka yi Mungadi, wasu suka doshi
Kamba, wasu suka yi Argungu, wasu suka yi Arewa (cikin Arawa da Zabarmawa da
Buzaye)[6].
Yakubu Nabame kakan Sarki Sama ya nufi Arewa wajen mahaifiyarsa Ba’ara. Da ya
dawo Kabi da iyali ya dawo, ita ta haifa masa Sarkin Kabi Muhammadu Ba’are. Ya
auri Bafulatana a Gwandu ta haifa masa Sarkin Kabi Sama (Mayaƙi).
Bayan
da Nabame ya dawo gudun hijira daular Fulani ta kafu aka kama shi aka tura
Sakkwato. A Sakkwato aka saka shi cikin mayaƙa, ya yi
fice sosai[7].
A Sakkwato ya haifi Sarkin Kabi Sama. An ce, ɗai
rana aka zana musu suna shi da Sarkin Musulmi Audu Ɗanyen Kasko[8].
Nabame a cikin gumuzun jihadi shi ya kashe wa Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo ɗa. Gorin da Sarkin Gobir Bawa ya yi masa ya sa,
ya yi murabus daga sojojin Fulani ya nemi ya dawo gida, Sarkin Musulmi na
wancan zamani ya aminta. Aka yi masa rakiya har Gande ya ƙaraso Gudale
ya sauka. Daga nan, ya shigo Argungu ya fitar da su ƙangin Fulani
ya ƙwato
ƙasarsu
ta gado duka ya kafa sabuwar duniyar Kabawa[9].
Bayan ya rasu, Yusuf Mainasara ya gaje shi. Bayan mutuwar Yusuf, Sarki
Muhammadu Ba’are (ɗan Ba’arar
da Nabame ya auro ƙasar Arewa) ƙasar
mahaifiyarsa ya yi mulki. Daga gare shi sai Sarkin Kabi Abdullahi Toga wanda ya
sa aka tsagaita wuta na yaƙe-yaƙe da Fulani[10].
Toga na gurgusawa Sarkin Kabi Sama ya hau karaga, ya tsinke/farke layar
tsagaita wuta da Fulani ya ci garuruwan Fulani (99) da yaƙi.
Bayan
rasuwar Sarkin Kabi Sama (1883-1915) ƙanensa
Sulaiman ya gaje shi 1915-20. Bayan rasuwar Sulaiman, Muhammadu Sama ɗan Sarkin Kabi Sama ya dawo 1920-1934. Bayan
wucewarsa ɗansa Muhammadu Sani (jikan
Sarki Sama) ya hau 1934-1942. Daga riƙon Muhammadu
Sani sai Sama’ila Mudi daga Kamba (fararen Lekawa) ya hau 1942-53. Daga nan,
sai Muhammadu Shehe 1953-59 (kuma ƙanen Sama).
Daga nan, sai Muhammadu Mera 1959-1996 (Tankaɗa
Hauɓin Sama). Daga gare shi sai Sama’ila
Muhammadu Mera (1996-yau) (Taka Kusheyin Sama) ya hau. A bisa diddigin tarihi
Sarki Sama Mayaƙi har yanzu bai kau ba yaƙe-yaƙe kawai suka
kau.
Na
yarda da faɗar Aliyu Ɗandawo:
Gindi : Shugaban
tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
: Ila
marin rugga ɗan Yakubu sa
gurfani
Jagora: Ko yanzu mai rabo ya samu ya gaƙe kowa an
nan
Yara : Mahassada
su kau an bar su suna shawagi
Hoton Daular Kabi:
Ƙasaitacciyar daula ce a ƙasar Hausa
wadda Sarki Muhammadu Kanta ya kafa shekaru (502) da suka gabata. Farfajiyar
daular ta kai har cikin Nguru ta daular Borno. Mayaƙanta sun
dardaza faɗin ta har cikin ƙasar Oyo.
Silalen ikonta ya kai har cikin ƙasashen
Benin da Niger da Burkina Fasso ta yanzu. Sarki Kanta na daga cikin dakarun yaƙi na Sarki
Muhammadu Askiyya. Da ƙarfi ya kawo tsoro ya ɗebe, ya ɓalle ya kafa
tasa daula ta daban mai suna Kabi[11].
Daula ce da aka kafa tsakanin yaƙi, cikin yaƙi, da
rigingimun hare-hare da ɗaukar fansa.
Addinin Musulunci ya yi shekaru aru-aru a cikinta. Asalin sarautar Kabi takenta
Amirul Muminiina, (Sarkin Musulmi)[12].
Ɗaya
daga cikin manyan ƙabilunta Kyangawa, Sarkinsu Kyanga Manu ya yi
aikin Hajji a ƙarni na (17ƙn)[13].
Daula ce da ta tattara Hausawa da Arawa da Zabarmawa da Nufawa da Dakarkari da
Fulani da Azbinawa da Larabawa da Wangarawa da Shangawa da dai sauran ƙananan ƙabilu. A
tarihance, daga Sarki Muhammadu Kanta zuwa Sarkin Kabi Sama’ila Muhammadu Mera
(1996-yau) an yi sarakuna (33). Cibiyar daular ta taso daga Surame zuwa Birnin
Kabi lokacin riƙon Sarkin Kabi Tomo, Sarki na (13). Ta sake
dagargajewa Argungu lokacin Sarkin Kabi Yakubu Nabame Sarki na (22). Daular ta
shigo mulkin Turawa lokacin Sama
(1883-1915) Sarki na (26). Gwagwarmayar Kabawa da Fulani ya sa daular durƙusawa
lokacin Sarki Sama’ila Karari Sarki na (21) Sarkin Kabi Yakubu Nabame Sarki na
(22) ya dawo mata da ruhinta[14].
Wannan gwagwarmayar ita ta haifar da darusan adabi da dama tsakanin Kabawa da
Fulani wanda wannan waƙar da za mu yi nazari ta yi wa kakkaɓan gara[15].
Dabarun Bincike:
Tunanina
na nazarin waƙar makaɗa Buda Ɗantanoma bai
ba ni mamaki ba sai da na shiga aikin gadan-gadan. Na farko dai, Buda ba shi a
raye. Na biyu, babu yaronsa ko yaransa na waƙa a raye. Na
uku, Sarkin da ake yi wa waƙar shi ma ba shi a raye. Abin
ban haushi, babu wurin da za a samu waƙar rerawar
Buda da muryarsa. Don haka, dole matakin bincike na farko shi ne, neman ɗiyan waƙar ga waɗanda suka ji ta suka kama wani abu a ciki. Jerin
kayayyakin rubuce-rubucenmu na bincike da kundaye babu wurin da za a tsinci waƙar bale
bayananta. Dole na shiga masarautar Kabi da Gobir domin samun wasu ɗiyan waƙoƙin daga
bakunan manya. Haka kuma, na dawo masarautun Sakkwato da Gwandu da Kano da
Katsina domin samun wasu ɗiyan waƙar da ba a
rasa ba. Na bi sawun tattaunawa da gidajen wasu fitattun mawaƙan
masarautun Kabi da Gobir da Yawuri da Sakkwato domin samun ɗan abin da ba a rasa ba. Bayan tattaro waƙar, na sake
tsara ta, da bitar ta, na kwatanta ta da ainihin tarihin da take son
tabbatarwa. Wannan ta sa dole a tuntuɓi fitattun
ayyukan da aka yi a kan daular Kabi domin kwakkwahe zaren tunanin Buda Ɗantanoma[16].
Shiga ɗakunan karatu da gidajen
adana tarihi musamman na daular Kabi da Sakkwato ya agaza ainun. An tattauna
muhimman mutane a fadar Kabi da Sakkwato da ke da alhakin sanin wani abu a kan
daulolin da shi kansa Ɗantanoma da waƙoƙinsa. Na yi
amfani da ɗiyan waƙar da na
samo babbarkatai domin daidaita tunanin waƙar a tsarin
salon waƙar baka.
Bakandamiyar Buda:
A
tarihi, Kabawa ba su da wata waƙa a masarautarsu da ta
cancanci sunan bakandamiya in ba wannan ba. Fitattun jaruman mawaƙan
masarautar Kabi irin su Ata da Kaaree (makaɗin jama’a)
da Aliyu Ɗandawo (makaɗin Mamman
Shehe) da Gero Zarto da Ɗan Kawu da Jatau (makaɗin S. Shiko) da Ata (makaɗan Nabame) ba su yi wa masarautar Kabi waƙar ɗebe takaici irin waƙar da Buda Ɗantanoma ya
yi ba. Gindin waƙar shi ne:
: Gagara ƙarya sadauki
:
Sama gwarzon alƙali.
Asalin
waƙar
ita ce, bakandamiyar da yake yi wa Sarki Sama[17].
Babban abin da ya sa ta yi fice sosai shi ne, a taron dabar da aka yi a Kano
zamanin Sarkin Kano Shehu na tarbon ɗan
sarauniyar Ingila Prince Edward 1925. A taron, Sarkin Kabi Sama ya fita da doki
(500) mayaƙa yan baka (500) masu harugga (500) dakaru
(1500) ke nan. A gaskiya, Sarki Sama fitan yaƙi ya yi, don
haka duk wani basarake da ya halarci taron tsawonsa bai kai na Sarkin Kabi Sama
ba. Sarki Sama bai sauka cikin garin Kano ba, ya nemi a ba shi babban fage da
zai sauka da dakarunsa. Sarkin Kano Shehu ya ba shi farfajiya babba a wajen
birnin Kano aka sauke kayan yaƙi. Wurin ya zama wata babbar
matattara, a zo a ga Sarki, a ji Sarki, a ga dakarun Sarki. Bayan ƙare taro,
wurin ya zama babbar unguwa mai suna “Fage”[18].
Bakandamiyar ta kakkamo duk abubuwan da suka faru, tun fitan Sarki Sama daga
Argungu har ya je Kano ya dawo, da abubuwan da suka faru a taron daba.
Bakandamiya waƙa ce, ba dole duk abin da ta kamo iya tsawonsa
da faɗinsa ke nan ba, wani a ƙara masa
tsawo, wani a rage masa faɗi, wani a
bar shi yadda yake. Duk da haka, bakandamiyar Ɗantanoma
daular Kabi ta kasa a faifai ga mai tababa ko musun ɗaukakarta da ƙasaitarta a
duniyar zamaninta.
Zaren Tunanin Bakandamiyar Buda:
Ga
ɗan abin da na kalato na waƙar bayan na
yi tankaɗe-da-rairaya sosai na
riwayoyi daban-daban da na samo. A ɗan ma’aunina
ana iya regon kayan cikin waƙar Buda kamar haka:
Ƙasar
Kabi da Abokanta
A
cikin amon turun Buda ƙasar Kabi ba ta da abokiyar da ta kai Gobir. Da
Kabi da Gobir ba su taƙama da komai face yaƙi na kare
martabar gida da darajarar kakanni[19].
Bugu da ƙari, da Kabi da Gobir su ne alaƙaƙai ga Fulani
da mulkinsu tun gabanin jihadin ƙarni na (19ƙn) da
lokacin jihadin, da kuma bayan jihadin. Da yaƙe-yaƙen addini,
da na faɗaɗa ƙasa, da na
mulkin mallaka suka lafa, aka share jini abin ya koma wasa. Buda ya taɓo wannan silalin tarihi a turunsa da ke cewa:
Jagora:
Kanta da Bawa nis sani
: Jangwarzo ba mu san Hillani ba
: Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon Alƙali
Wane ne Sarki Sama a Tafashen Ɗantanoma?
Sarkin
Kabi Muhammadu ɗan Sama’ila
wanda aka fi sani da Muhammadun Sama ko “Sama” kawai a tafashen Buda, ba kanwar
lasa ga abokan adawa ba ne. Tsananin yaƙin Sama ya
sa ake yi masa laƙabi da “Mayaƙi" Buda
ya taɓo gwarzantaka da muhibba da
buwayarsa kamar haka:
Jagora: Sama
na Audu mai hawan ban kashi
: Mai tamburran fama
Gindi:
Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon Alƙali
: Ba cin yaro na ba.
A
ganin Buda, babu wani Sarki a farfajiyar Sudaniyya in ba Sama ba, domin jarunta
ce sarauta, Sama ko a ko’ina ya kai. Dubi yadda Buda ke ciciɓa shi da faɗar:
Jagora:
Sarkin sarakuna shiryayye
: Ba kowa nan sai kai
Gindi:
Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon Alƙali
Jagora: Ka
ji Sarki ka zo ka iske Sarki
: Ba Sarkin ƙage ba.
Bayan
Buda ya kore duk wani sarki in ba Sama ba, ya kuma jaddada faɗar duk wani sarki a sudaniyya in ba Sama ba ne
Sarkin ƙage ne. Sarkin ƙage shi ne
Sarkin da ke karɓar umurnin
wani Sarki domin haka Ɗantanoma ya tabbatar da cewa:
Jagora: Ɗan nana
Hausa ba a mai da awa shi,
: Dac can kuma ba a yo ba[21].
Gindi:
Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon Alƙali.
Jagora:
Mamman mai komi mai kowa
: Kuma kai aw wan kowa
: Ba matsuwa na Bubakar
: Sa tuba ba sake faɗin na yi.
Waɗannan ɗiyan waƙoƙi duk suna
hararar sarakunan daular Sakkwato ne da ke hannun Fulani. Don haka “kowa” ga
Fulani take komawa. Haka kuma “Sarkin Sarakuna” ya haɗa da Fulani. Tirƙashi ji
wannan:
Jagora:
Mamman mai wada yas so
Matsayin Sarautar Kabi:
A
al’adance, sarauta ba ta amo ta yi tasiri sai ta yi gwagwarmaya da abokan
hamayya ta fatattake su, a kama na kamawa, a kashe na kashewa, mai rabon ganin
baɗi ya tsere ko ya yi hijira. Daular
Kabi tana tinƙaho da nagartattun kakanni da ba su miƙa wuya ga
kowa ba kamar ragon suna. Don haka, Buda ke kiran mai Kabi Sama da cewa:
Jagora: Sama
maganin ƙiyayya rabuwa
: Kore ƙaton banza
Gindi:
Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon Alƙali
Jagora: Sama
kore tsagera ba ni gidanai
: In sa turayena.
Ɗantanoma na tabbatar da cewa, masarautar Kabi ba
ta da sauran maƙiya domin ta ƙore Fulani.
An raba su da ƙasar Kabi, kare jini biri jini, don haka yake
son a kore sarakunansu a karɓe gidajensu
a matsayin ganima, makaɗan fadar
Sama su samu wurin rataye turayen fama. Buda ya sake nuna irin matsayin
sarautar Kabi da ta ci Fulani da karɓe musu
tamburan kakaninsu.
Jagora: Ga
wani ya ga tamburan kakanai,
: Ba za a kiɗa mai ba.
Gindi:
Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon Alƙali
Dukkanin
makaɗan masarautar Kabi sun tafi a kan
cewa Sarautar Kabi ita ce shakundum. Da yawa sukan ambaci sarakunansu da:
Shugaban dama da hauni, ko babban bajini, ko shugaban tahiya, ko sarkin
sarakuna, ko mai dama da hauni ga su nan dai.
Kushe Sarkunan Fulani:
Babban
dalilin da ya sa Buda Ɗantanoma da waƙarsa suka yi
fice shi ne zambo da habaicin da yake yi wa sarakunan Fulani. Da Buda ya fara
da babbar sarautar daula ya fara da ita wato sarautar Gwandu yana cewa:
Jagora:
Sarkin Gwandu ya nashe mu da yula
: Hat taf hwaɗa
gulbi
Raddin da
Buda ya bayar kan nashinsu da yula da aka yi shi ne:
Jagora:
Sarkin Gwandu ɗan gajere
: Daidai kwaɓin laka.
Bayan
an taɓo Sarkin Gwandu, sai aka bi ƙananan
sarakunansa, ɗaya bayan ɗaya, ana muzantawa. Ga ɗan abin da aka ruwaito daga Ɗantanoma:
Jega :
:
Sarkin Jega yau tsawo yai kauri
: Daidai kamun
kura.
Ɗakingari :
:
Sarkin Ɗakingari dogo rusheshe
: Daidai takin dambe.
Tambuwal :
:
Sarkin Tambuwal Ba’uden banza
: Sheshenai na jimen
: Runji shi ka wa yanka[23].
Alero :
: Alero nig ga
guntun Sarki
: Daidai kwaɓin laka.
Ambursa:
: Ni na zo Ambursa
na ga Sarki
: Da baƙi ƙoƙe ɗan mai shuni
: Sarki da ƙuraje ga
jikinai
: Ƙoƙe ɗan mai ƙwarya.
Wajen Ƙasar Hausa:
Hatta
da sarakunan da ke hulɗar arziki da
ƙasar
Gwandu Ɗantanoma bai sa musu ido ba. Da ya je Doso
Zarmakwai ya ji an ce, yana zagin Sarkin Gwandu sai ya ji tsoronsa, ya ba shi
doki kyauta toshiyar baka, kar a tallata halayensa ga abin da Ɗantanoma ya
ce:
Jagora: Doso
nig ga wawan Sarki
: Shi had doki yab bai.
Yawurawa
ba su ce masa uffan ba, amma saboda dangantakarsu kyawawa da Gwandu da kuma
daular Sakkwato Ɗantanoma ke cewa:
Jagora: Ɗansanholama
na bakin kogi
: Ba mu san tushenai ba.
Gumuzun Sarkin Kabi da Sauran Sarakuna a Kano
(1925):
Dabar
da aka shirya Kano 1925 ƙasaitacciya ce. Kowane Sarki ƙwazo yake
son ya yi, a ga ya cira tsara, a hawan dabarsa. A fagen dabar, babu Sarkin da Ɗantonoma ya
ragawa, sai in bai gan shi ba. Ga yadda Ɗantanoma ya
fasa baƙi.
Haɗuwar
Sarkin Musulmi Tambari da Sakrin Gwandu Shehu da Sarkin Kabi Sama a Bunguɗu kan Hanya zuwa Kano
An
ce, Sarkin Musulmi Tambari ya fara riskar Sarkin Kabi Sama a Bunguɗu. Ya zo ya tarar da su, karo na farko da suka
fara gaisawa ta girma da arziki. Sarki Tambari ya ce wa Sarkin Kabi Sama: “Mai
Kabawa muna lahiya”, Sarkin Kabi ya amsa da cewa: “Mai Hillani lahiya lau”[24].
Yana cikin motarsa, Sama na kan dokinsa. Nan Ɗantanoma ya
ce:
Jagora: Ga
wani ya shigo barayar kusa[25]
: Yac ce mota yah hau
: Ga wani ya shigo cikin kwandonai
: Yac ce mota yah hau
: Motar ƙwarai tana
ga Nasara
: Katako na Hausa.
Bayan
da Sarkin Musulmi Tambari ya fito mota aka gaisa, ya shiga mota aka ruhe gam! Ɗantanoma ya
ce:
: Mu
sarkinmu bai shiga zunguru[26]
: Don ba
balli na ba
: Ko dai an
tai Kano da sauri
:
Jayen munta an kai.
Jim
kaɗan ga Sarkin Gwandu cikin mota “A
kori kura” da shi da Sarkin Kabin Jega Modi suna gaba, sauran ƙananan
sarakuna na bayan bodi zaune. Suka gaisa da Sarkin Kabi, sai kallo ya koma ga
waɗanda ke cikin mota, ana ta kururuwa
da mamakin yadda mota ɗaya ta ɗauko manyan mutane haka. Ɗantanoma ya
hau bakinsa:
Jagora: Na
hore ka kak ka sai katako
: Saye ɗan
Azbin Sarki!
:
Doki shi ka taƙama a yi kallo,
:
Ba katakon wofi ba,
: (Ƙyale iskan
banza)
:
Motaƙ ƙwarai tana
ga Nasara
:
Katako na Gwandu.
Ganawar Sarkin Zazzau da Kano da Sarki Sama:
An
ce, sun zauna wuri ɗaya suna
tattaunawa a dandalin taro. Sarkin Kano ya sha alkyabba da naɗi da sandar sarauta da kayan alfarma. Sarkin
Zazzau ya shawo babbar riga mai aiki ɗaba-ɗaba a fuskanta mai ɗaukar hankali. Sarkin Kabi Muhammadun Sama ga
al’adansa, koyaushe fararen kaya yaka yi ba su da aiki gaba da baya, tun fil
azal malami ne. Da Ɗantanoma ya ga kallo ya koma sama shaho ya ɗauki raƙumi, domin
aiki Sarkin Zazzau na riga ya burge ‘yan kallo sai ya ce:
: Sai dottijon banza,
: Kai Sarkin Kano taho ka ga Sarki
: Ba ɗai
ga waɗannan ba.
Shirin Hawan Sarkin Kabi Sama da Ƙwarjininsa:
A
ganin Ɗantanoma wajen hawa wani Sarki ke tsere wani
Sarki. Sarauta iko ce, iko ko da ƙarfi ake yin
sa da gwarzantaka. Tun a cikin gida Fulani suka fara firgita. Ɗantanoma ya
ce:
Jagora:
Sarkin Isa ya ga damman masu
: Bai san yaƙi na ba.
Da
aka biyo ta Sakkwato suka firgice sosai domin ganin irin shirin da Sarkin Kabi
ya fito da shi. Ɗantanoma ya ce:
Jagora:
Hawan da yay yi Sakkwato
:
Sada zumunta na
:
Bai so su ji tsoro ba
Da aka shiga birin Kano cewa aka yi:
Jagora: An
ce ba a wa Kano takakka
:
Mamman ya tattake ta
:An
ce ba a zo a Kano takakka
:
Amma Mamman ya yi
:
An ce ba a wa Kano takakka
:
Sama ya tattake ta
:
Don mun zo Kano da dambun masu
: Ba mu samo
gaba ba[28].
Ƙarfin Sojan
Daular Kabi:
Idan
aka ce waƙa bakandamiya ce, babu abin da ba a iya samu a
ciki. Ga al’adar waƙa, bakandamiya ba a ƙare ta domin
duk wani muhimmin abu da mawaƙi ke son ya adana, a ciki
yake kai shi. A cikin ƙoƙarin fayyace
Dabar Kano, Ɗantanoma ya baje kolin irin ƙarfin
dakarun daular Kabi da ya gagari Fulani, kar ta san kar! Dantanoma na cewa:
Jagora:
Taron Kano da an ka yi
:
Sama shi Allah Yas so
:
Shi Sarkin Kano da yas san daidai
:
Tarbon bahago yay yi
:
Ko sarkin Kano da yas san daidai
:
Tarben manya yay yi
:
Sarkin Kano da shi da garinai
:
Rannan daji yak kwan
:
Malaman gari ka cewa Sarki
: Taso ka
shige birni.
Iya
irin makaman zamaninsu Daular Kabi ta tanada wa dakarunta, don haka ba ta kwana
da fargaban kowace daula ba, a ƙarƙashin kowane
suna aka kafa ta. Ɗantanoma ya fi kowa sanin haka, don haka yake ce
wa Sarkin Kabi Muhammadun Sama:
Jagora:
Gyara takubba na Yari tallabi masu
: Shiga
birni ba kowa.
Cikin ɗawainiyar
tafiya zuwa Kano Buda na cewa:
: Ba
a sake haye mai ba
: Nan
yai karo da Sarkin Ƙaura
: Yaw watce mutanenai.
Ga
alama, irin wannan arangamar ya sa Sarkin Bunza ya ji tsoron kai wa Gwandu
gudunmuwa a yi karo da Sarkin Kabi. Buda cewa yake yi:
Jagora: Bunza nag ga karnan Sarki [30]
: Ɗan Gurumaɗan Bunza
: Da
yaj ji za a gamamma
: Rancen ciwo yay yi.
A tsarin ƙarfin sojan
Sarkin Kabi akwai dawaki da raƙumma da dakaru ‘yan ƙasa. Da za a
je Kano taro Buda yi lisafo su kamar haka:
Jagora: Doki ya yi fiffike ya yi baƙi
: Ba
mu gane iyaka ba.
: Dan
nan baya raƙumi ya fi dubu
: Tsinin
mashi zalla
: Can
gaba ko uban dawa da ɗiyanai
: Tsinin
kibiya zalla
: Ga
sulke da bindiga ga masu
: Ga tamburran fama.
Taron
Dabar Kano:
A
hanyar zuwa Kano Sarkin Kabi sama ya bi hanyar Shuni ya sauka Dange wajen
Sarkin Bauran Dange Hassan Ɗan’mu’azu (1931-38). Ya kwana
Sanyinna da Shagari da Kamɓama da
Tsamiya da Tureta da Murai da Bunguɗu da Kwatarkwashi
da Gusau. Ya bi ta Tsahe da ‘Yankuzo, darzaje daki-daki[31].
Sarkin Kabi gamgami ya yi sosai zuwa taron domin Buda ya ce:
Jagora: Daga Ilo hak Karekare
: Duka
sun zo jiɗag gwannan farko.
Makaɗa Buda ya ba Sarkin Kabi haƙuri cewa ba
kiran Fulani ne ba, taron gwannati ne.
Jagora: In ba don yana kiran taro ba
: Sama ba mu zuwa Hausa
: Bahago kak ka ji komai
: Ba nasu kira na ba
: Mamman kak ka ji komai
: Ba
su ka kiran nan ba.
Duk
da haka, Ɗantanoma ya ce, su suka ci ƙwallo a
taron domin a tasa faɗi cewa ya
yi.
Jagora: In a je gida a ce wa Tsahara
: Mu
namu nuhi ya kai
: Don
kai gwanna yam miƙa ma hannu
: Sannan
yab ba kowa.
A
zaton Ɗantanoma, in an zo dabar Kano, Sarkin Nupe Kabi
zai mara wa ba Sakkwato ba, domin daular Kabi ta kai har ƙasar Yarbawa
kuma Nufawa sun more wa tsaron daular Kabi[32].
Da Ɗantanoma
bai ga sarkin Nupe bayansa ba, ya ce:
Jagora: Ga wani ya zo Kano
: Kamar bai zo ba
: Inda
ɗan mai koko.
Ana wata ga wata:
Baya
an kammala dabar Kano, aka fahimci akwai buƙatar a samu
haɗin kan sarakuna gaba ɗaya, a share jini a koma wasa. Daga can aka
shirya yadda za a yi sulhu tsakanin daular Kabi da Sakkwato kowa ya fahinci
juna[33].
Wurin da Gizo ke saƙa shi ne: wace ƙasa za a yi
zaman sulhu? Wa zai kira wa, a yi sulhu? Wa zai jagoranci taro? A wata riwaya
an ce, da aka dawo daga Kano a kan hanyar zuwa gida a mararrabar Kanoma aka ce
Sarkin Kabi ya biyo Sarkin Musulmi Tambari a bi hanya ɗaya. An ce, nan Ɗantanoma ya
hana ya ce:
Jagora: In an je gida a ce wa Tsahara
: Tabkin da tas sani bana ya koma laka
: In an je gida a ce ma Tsahara
: Kabi ta koma rugga
: In an je gida a ce wa tsahara
: Gaba ta koma baya
: Don sarkinmu bai biyan wani Sarki
: In ba Allah na ba.
Da
jin haka, sai Sama ya ɗan jinkirta
aka sake shawara. Da Ɗantanoma ya ga ‘yan shawara na son su ci nasara,
a bi hanya ɗaya da
Sarkin Musulmi, a fara shiga ƙasarsa (wato Hausa) yana gaba
Sarkin Kabi na baya. Kai! Wane mutum in ji mutuwa, ya dafi tafashen fama ya hau
bakinsa da cewa:
Jagora: Haba Sama in biya ka kai
: Ka zo ka bi Turai in san manya kab bi
: Kanta da Bawa nis sani
: Jangwarzo ban san Hillani ba.
Da
furta wannan ɗan waƙa, miki ya
koma sabo, aka tashi baran-baran, kar ta san kar, kowa ya kama hanyarsa.
Tsarin
Hawan Daba:
An
tsara hawan dabar bisa tsari irin na hukuma ba na gargajiya ba. A tsarin,
Turawa ne na farko, don haka dai ana nan zaman bayinsu biye da su ake a
koyaushe. Wannan abin ban haushi ne ga wanda ya fahinci wulaƙanci irin na
mulkin mallaka. Wajen da aka taɓo Ɗantanoma sai
aka ce, bayan Turawa sai waƙilan gwannati bayansu.
Sarakuna su biyo baya a bisa tsarin darajar da gwannati ta yi. A tsarin Sarkin
Kabi shi ne Sarki na goma sh uku (13). Ɗantanoma bai
yarda ba, sai ya tsare ido a fagen, ana fara kiran Turawa ya dafi turunsa ya
kira Sarkin Kabi Sama da cewa: (Sama/Haba!)
Jagora: Zaburo biyo Turawa
: In
san manyan Kab bi
Jagora: Maza furce gabansu
: Bi
ma Bature in san manya kab bi.
Wayyoyoyo! Ɗantanoma ya
yi makaɗi: Sama ko ya yi Sarki ko’ina
aka Sarki. Haba! in kai ne yaya zaka yi?
Barazanar Daular Kabi ga Daular Fulani (Hausa)
A lisafin Kabawa, duk wata ƙasa da ba ta
Fulani ba, kuma Fulani suka ƙwaci mulkinta sunanta
“Hausa”. A tarihin artabun Kabawa da Fulani, Kabawa suna iƙirarin su
suka ci nasara. Dalilan Kabawa kuwa shi ne, Sama ya ci garuruwan Fulani (99).
Kabi ta ci Ambursa, ta kuwa ragargaza Fulani a yaƙin Alwasa.
Ba za a musanta cewa, Fulani sun taɓa cin galaba
a kan Kabawa ba musamman idan aka nazarci karon battan Sarki Muhammadun Sama da
Sanyinnawa ƙarƙashin
jagorancin Mijin Jewo[34].
A koyaushe, idan ana bukin shekara-shekara na salla da kamun kifi da shan
kubewa da gaɗa da
annashawa taken Kabawa shi ne:
Jagora: Kabi ta ci Hausa
: Da mi tac ci Hausa?
: Da
ƙarfi
da yaji
Wannan
barazanar har gobe ba ta guje ga bakunan Kabawa ba, wai ko ana taya fansa.
Tsananin tsoron da ake yi wa Sama ya sa Ɗantanoma
cewa:
Jagora: Wani ya faɗi ya kare ga
tsaratai
: Bai san rame na ba.
: Wani Sarki shina biɗan barwanai
: Bai san jama’atai ba
: Da dai a yamutsa na
: Da
wasu sun yi baran ƙosai.
Matsayin Waƙar Buda Ɗantanoma
a Ƙsar Hausa:
A
wajen Buda da Kabawa babu wata waƙa da ta fi
waƙar
Buda tasiri. Waƙar Buda bakandamiya ce, komai ake son adanawa a
ciki ake kai ta. A ɗan nawa
bincike, tsofafi da Sarakunan Kabi na da wannan waƙa tarshe
take bakunansu kamar Fatiha a bakin liman. A gaskiya, talakawa na ɗan jin tsoro rera ta saboda cin zarafin Sarakuna
da ke ciki. Mawaƙan Gobir da Kabi, bayan mutuwar Ɗantanona
suka dinga rera ta da muryoyi daban-daban da ‘yan ƙare-ƙare da
rage-rage. Waƙar Ɗantanona
wata taskar tarihi ce da ba a yi kamarta ba a gabaninta, a bayanta ba a samu
ba. Don haka, za mu iya cewa; waƙar Gagara ƙarya ta
Buda:
1.
A
wajen Kabawa furen kallo ce domin kakaninsu ake zugugutawa da cicciɓawa a kan abokan adawa.
2.
A
ɓangaren daular Sakkwato wani ƙalubale ne
ga Sarakunanta da jama’arta a kan daɗaɗɗiyar adawa.
3.
Waƙar wata
taskar tarihi ce, duk da sanin cewa, ba a rasa hazon soyayya da ƙiyayya a
ciki, wanda zai kawo cikas ga haƙiƙanin tarihi.
4.
Waƙar wata
allura ce da a koyaushe za a ji da sauran rina a kaba. Tattare da sanin cewa,
rinar ta tafi abinta, amma waƙar Buda ta yi wa kabar da
rinar ta yi wa gije kadada don tuna baya.
5.
A
hangen Buda, abin da ke tsakanin Kabi da Sakkwato ba addini ba ne, siyasar
mulki ce, don haka bai taɓa kawo
zancen addini ciki ba, wannan wani haske ne na fuska biyu da wasu Hausawan ƙasar Hausa
ke kallon jihadin ƙarni na (19ƙn)[35].
Sakamakon Bincike:
Yadda jihadin ƙarni na 19ƙn ya yayatu
a ƙasar
Hausa; haka waƙar Buda ta yayatu a ƙasar Hausa.
Da su Kabawa da Fulani duk suna rera ta a matsayin tuna baya da raha. Mafi
yawan daulolin duniya da ƙasaitattun Sarakuna da masu mulki sukan yi
amfani da haziƙan adibbai/mawaƙan lokacinsu
domin kare kansu da sarautunsu. Da ba don waƙar Buda ba,
da tuni an manta da irin artabun da Kabawa suka yi da Sakkwato. Daga cikin abin da na hango akwai:
1.
Da
ɗan gari akan ci gari. Asalin Buda ɗan Yabo ne ƙarƙashin riƙon Sakkwato
don haka Kabawa ke amfani da shi a matsayin ɗan leƙen asirinsu.
2.
Bakandamiyar
Buda tattare da farin jinin da ta yi a halin yanzu, babu ita a rubuce, babu ita
a kowace irin taskar taskace adabi[36].
3.
Dalili
da wannan sai a ga kowa abin da ya ga dama yake faɗi a kan sarkin da yake so ko baya so sai ya ce:
inji Buda[37].
4.
Babu
Bakaben asali da ke tir da waƙar Buda, haka kuma babu
Bafulatanin ƙwarai da zai yi madalla da ita.
5.
Ɗa ba don Buda ba, da dabar da aka yi wa Prince
Edward, a shekara (1925) ba ta samu shiga adabin Hausa ba.
6.
Da
Kabi da Gobir yaƙi da Fulani ya haɗa
su zumunta, kowanensu abokin adawa ne da daular Sakkwato. Haka kuma, daulolin
biyu da yaƙi suke bugun gaba, makaɗin yaƙi ya fi karɓuwa gare su da samun yardarsu, don haka Buda ya
samu karɓuwa kabi da Gobir.
Nasarar
da wannan bincike ya yi ita ce ƙwaƙwalo ɓatattun ɗiyan waƙar Buda daga
bakunan da suka san shi, suka ji shi, ko suka kwaikwaye shi. Samar da ɗan wani abu a rubuce nata cigaba ne tare da
fashin baƙin kuramen wasu ɗiyan
nata.
Naɗewa:
Raya
daula da ɗaukakar martabarta yana a
hannun masarautanta. Sarki shi kaɗai ba ya
mamaye daula/ƙasa sai da cikakken goyon bayan mutanenta.
Daular Kabi ta samu wadatattun Sarakuna ‘yan kishin ƙasa da
amintattun talakawa ‘yan ga-ni-kashe-ni. Cikin wannan ɗawainiyar aka ci karo da fasihin mawaƙin tankiya
da ba a yi kamarsa ba a ƙasar Hausa. Makaɗa
Buda Allah Ya haɗa jininsa da
daular Kabi, babu yadda Sarakunan Yabo ba su yi ba, su tsayar da shi ƙasarsu ya ƙi. Kabawan
ma da suka yi masa ɗawainiyar
nuna isa don ya tabbata ƙasarsu ya gaya musu cewa, ƙauna ce yake
da ita gare su ba don abinsu ba, kamar yadda yake cewa:
Jagora: Algargi ba ta wa mai turu
: Da ya koma Yabo[38].
Haƙiƙa,
gawurraccen makaɗi shi ne
rayuwar kowace daula da adana martabartar ta. Ba don Buda ba, da sunan Kabi bai
mamaye ƙasar Hausa ba. Ba don Narambaɗa ba, wa ya san Isa da Sarkinta. In ba turun
Dan’anace ba, sunan Shago ba zai wuce Mafara ba. Ba don Gambo ba Muhammadu
Inuwa Danmaɗacci ko Jega
ba a ji ɗuriyarsa ba. Lallai makaɗa Aliyu Ɗandawo ya
tabbatar da ƙunshiyar bakandamiyar Ɗantanoma a
faɗarsa.
Jagora: In hadari ya taso
: Cikin iyawar Allah
: Giragizai su ka zuwa
: Su taushe kaihin rana
: Mutane waw waye duhu
: Nabame yaw waye duhu
: Yay yi ma azna fitila
: Yag gaƙe Torankawa
: Gudunmuwa kaz zaka ka ya ishe shi ya
sha kaihi
: Mutun guda ya hi gaban mutum dubu
: Magabata abin da sun ka hwaɗi
: Ai mai da hwaɗi ɓanna na.
Gindi: Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
: Ila
harin rugga ɗan Yaƙuba sa
gurfani.
Manazarta
Adamu Mahdi 1978 The Hausa Factors in West African History,
Zaria:
Ahmadu
Bello University Press.
Adeleye, R.A 1971 Power and Dipplomacy in Northern Nigeria
1804-
1906: The Sokoto Caliphate and Its Enemies, London:
Logman Group Limited.
Al-jahh, M.A. 1967 “ A Seventeeth
Century Chronicle of the Origins and
Missionary
Activities of the Wangarawa,” Kano studies, 1,4.
Alkali, Muhammad Bello 1969 “ A
Hausa Community in Crisis: Kebbi in
the
19th Century,” MA Thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Auta, A.L. 1986 “ Gudumuwar Waƙoƙin Makaɗan Baka Dangane da
Adana
Tarihi,” Kundin MA, in Kano: Jami’ar Bayero.
Balogun, S.A 1970 “ Gwandu Emirates
in the Nineteenth Century, with
Special
Reference to Political Relations: 1917-1903,” PhD Thesis Ibadan University of
Ibadan.
Besmer, F.F 1971 “ Hausa Court Music
in Kano, Nigeria,” PhD Thesis
Columbia:
University of Columbia.
Birnin Tudu, M.S. 1984 “Kamun Ƙafa A Ƙasar Argungu
Kundin BA
Sokoto:
Jami’ar Sokoto
Blackwell, H.F 1927 The Occuaption of Hausaland, 1900-1904, Lagos.
Bunza, A.M. 2016 “Agitation and
Dialogue in Hausa and Fulɓe
Encounters:
(Reassessing the Hausa Version aa Depicted in Hausa Orature)” Paper Presented
at International Conference or Fulɓe Language, Literature and Culture Organized by
the Centre for the Studies of Nigeria Language and Folklore, Kano: Bayero
University 28th – 30th March, 2016.
Bunza, A.M 2016 “Ƙunar Baƙin Wake: Ƙalubalen Tsaron
ƙasarmu
(Daba Cikin
Tunanin Bahaushe: Abin da ya Karo Ɓera
ya-------)” Takardar da aka gabatar a
taron ƙasa na ƙara wa juna
sani a Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato, March, 2016.
Dokaji, A.A 2002 Kano ta Dabo Ci Gari, Zaria: NNPC.
Gusau, S.M. (1996) Makaɗa
da Mawaƙan Hausa Kaduna. Fisbas Media Services.
Hogben, S.G. 1967 An Introduction to the History of Islamic
State of
Northern Nigeria, Ibadan.
Hisket, M. 1994 The Sward of Truth, Evanson.
Hisket, M. 1984 The Development of Islam in West Africa, New York.
Hopen, C.E 1985 The Postoral Fulɓe Family in
Gwandu,
London.
Hopkins, A.G.H 1975 An Economic History of West Africa,
London.
Johnston, H.A.S 1967 The Fulani Empire of Sokoto, London:
Oxford
University
Press.
Johnston, Samuel 1921, The History of Yorubas, London.
Junaidu, Alhaji 1957 Tarihin Fulani, Zaria: NNPC
Last, Murray 1968 Sokoto Caliphate, Ibadan University
Press.
Magaji, A. 1980 “Alhaji Kassu Zurmi
da waƙoƙinsa,” Kundin BA,
Kano:
Jami’ar Bayero.
Mangati, B. 1985 “Waƙar Gagara Ƙarya Sadauki
ta Marigayi Buda
Ɗantanoma”
Kundin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Meek, C.K. 1971 The Northern Tribes of Nigeria General Studies no 97
vol.
1 Frank Cas and Co.Ltd.
Muhammadu, D. 1981 “Bakandamiya”
Towards a Characteristics of the
Poetic
Masterpiece in Hausa in Oral poetry in Nigeria (ed) Abalogun and Others Lagos:
Nigeria Magazine.
Muri, Aliyu Muhammad 2003 “ The Defence Policy of the Sokoto
Caliphate,
1804-1903” PhD Thesis, Department of History, Sokoto: Usmanu Danfodiyo
University.
Nadama G. 1977 “The Rise and
Collapse of a Hausa State : A Social and
Political
History of Zamfara,” PhD Thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Njeuma M.Z 1969 “The Rise and Fall
of Fulani Rule in Adamawa, 1809-
1901,”
PhD Thesis London.
Raglan, L.F 1932 The Hero, New York: Oxford Univerdity
Press.
Smaldore, J.P 1977 Warfare in the Sokoto Caliphate: Historical
and Sociological Perspectives.
London: Cambridge University Press.
Smith, M.G. 1960 Government in Zazzau 1800-1950, London:
University
Press.
Smith M.G. 1997 Government in Kano 1350-1950, USA Westview
Press.
Umaru, A.M. 2008 Daular
Fulani a Kano, Kano: Bechmark Publishers
Usman, Y.B 1974 The Transformation of Katsina 1400-1883, Zaria:
Ahmadu
Bello University.
Zurmi, M.A. 1986 “Rayuwar Alhaji
Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa,”
kundin
BA, Sokoto: Jami’ar Sokoto.
Dabo
ci Gari da Smith,
Government in Kano, da Usman, Transformation of Katsina, da Augi
“Gobir. Factor, “da Smith Government in Zazzau, da Nadama,
“Zamfara in the 19th Century”,
1968.
tabbatar da rinjayen Kabawa
ga Fulani a fagen daga. Waƙar
tarihi ce, domin ta yi waiwaye
ainun a kan tarihin yaƙe-yaƙen Kabawa. Waƙar ta tankiya ce, babban
burinta ta hasa wuta a zukatan Kabawa su tsaya matsayinsu komi taka zama ta
zama. Waƙa ce
mai jaddada tawayen daular Kabi a kan daular Sakkwato da suke ganin daular
Fulani ce kawai. Don haka, waƙar
gwagwarmaya ce tsakanin ƙabilu
biyu Kabawa da Fulani.
Jagora : Lamso nis sani da Tsahara
: Ban san kingin nan ba
Lamso
da Tsahara su ne matan da ke yi masa kyauta. Da sauran matan kishi ya kama su
aka ce musu “kingi” suka ce, a kawo turayen a rataye ya daina waƙa. Ya mayar
da raddi da cewa:
Jagora : Turu aka amsa a rataye
: Bakin Buda yana garai.
A nawa bincike a Argungu da
Bunza da Dukishi da Geza da Zariya. Bayan mutuwar Sarki Sama
Buda ya yi hijira da yaransa
zuwa yamma. Na sami wasu tsofafi a garin Dukushi da suka tabbata cewa, sun gamu
da Buda da yaransa wani ƙauye
mai suna Balu ta ƙasar
Kabi a kan hanyarsa ta Kamba. Ana zaton can cikin ƙasar Kamba ko jamhuriyyar
Nijar ya rasu. Wasu kuwa cewa suka yi, ya roƙi Allah ya kashe shi gabanin Sama Allah ya karɓi roƙonsa.
yi hira da shi cikin Gidan
Tarihin Kabi kusan awa 2-3, ranar 20/06/2017. Suleiman yana da
digirin Hausa a Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sokoto, 2003.
aka ce a tura shi fagen yaƙi ya mutu can a huta. Da
Allah bai yi mutuwarsa ba sai da ya ɗauko
fansa. Tattaunawarmu da Sambo Wali da Yakubu Bagaye da Suleiman Nabame ta
tabbatar da wannan. 26/006/2017.
) duk rana ɗaya aka haife su.
ga naku gida can ya rushe, ƙasar kakaninka ta yamutse
babu Sarki, ga su can suna yi wa Fulani bauta”. Daga lokacin jikinsa ya yi la’asar,
ya nemi ya dawo gida. Hira da na yi da Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato, da
Suleiman Nabame da Yakubu Bagaye (Masani tarihin Sarautar Kabi) duk sun yi canjaras da wannan kalami,
26/06/2017 da 30/06/2017.
Toga (1963-1883) an yi
Lafiyar Toga (1870-1878) Shekara 10 ana yaƙi.
irin famar da ya taka. Don
haka ya yi wa Askiyya Muhammadu tawaye ya kafa ƙasarsa mai suna Kabi.
shawarwari. A wasiƙar an kira shi da suna
Amiirul muminiina na Kabi. Wannan ya nuna daular Kabi ta riga ta Sakkwato karɓar Musulunci da kafa daular
Musulunci. In babu ƙira me
ya ci gawai?
da Geshoru da Illo da Dukushi
da Geza da Argungu da Kangiwa da Yeldu da Sauran manyan garuruwa da ƙauyukan Kabi da jamhuriyyar
Nijar da Benin.
[14] . Ya
tattara ɗiyar
sarauta suka tsayu a babban gungun
farfajiyar fadamar Kabi da ake yi wa suna
“Argungu” a yanzu. Wasu na
ganin, daga yekuwarsa ta kiran danginsa Kabawa: “Ar! Ku zo nan gungu mu tsaya”
ko “Ar! Ku zo mu yi gungu” aka samu suna “Argungu”. Akwai tatsuniyar cewa, wai
haɗuwar da suka
yi wuri ɗaya maƙiya suka hange su suka ce:
“Ar! Sun yi gungu” wai daga nan aka samu “Argungu”. A nawa hasashe na ɗalibin al’ada, ina takin saƙa da su. Kalmar “Ar!” a Hausa
kalma ce ta farga ko kuɓuta,
kuma tana fita a fagen kirari. Gungu kuwa, in da tsibiri in kuwa taruwan jama’a
mai jiran dako ko firgittu ko maɗauka
fansa. Don haka, in dai ya kasance: “Arnan Gungu” waɗanda suka kafirce wa masu son
su mallake su. Ko “Ar! Ga gungu” wato ga wurin da suke can; ko kuma ya kasance
na “tsakar gungu in idan muka yi la’akari da tarihin cewa, Kabawan da suka zo
Argungu sun tarar da garin “Buntsari”. Buntsari kuwa daga kifi sai naman ruwa
ke yin sa a tsakiyar gurbi. Wato garin “Gungu” ne.
tarihihi da wasan barkwanci
da tashe da waƙe-waƙen yara maza da mata da waƙoƙin baka na manya kamar:
Iyakar Kabi Sawwa; wurin da duk ka sha furar shinkafa nan ne Kabi gare ka; ja ya faɗi ya ɗauke;
dudduƙe har Kabi; da Kabi har
Kabara karan gamba guda ne, ga su nan dai.
Aminu, 2015.
yake taƙama an ce duk lokacin da ya
je waƙa in ba ita ya yi ba, ba ya
tsima kowa. Da ya fara ta kyauta sai ya kau da kai.
[18] . An
ce, Sarkin Kabi cewa ya yi a sama masa “Fege” Kanawa ba su san “Fage” ba sai
dai jeji/daji
ko karkara. Fage a Kabawa ana
nufin babban wuri irin na noma shinkafa ko dandalin wasan dambe ko kokuwa
yalwatacce. Aka fassara wa Sarkin Kano Shehu ya gane ya je wajen gari ya ba
shi. Hira da Yakubu Bagaye Argungu 29/06/2017, gidan Sarkin Kabi Sama’ila
Muhammadu Mera.
ƙasashensu ne da ba su yarda
da gurgusa in zauna ba, su dai biya ka wuce kamar kowa.
gero ko dawa, ana ce da shi
dambun masu”. Akwai kifin da ake ce wa masu/harasu, mai ƙaya zargo-zargo in an yi miya
ko dambun kifi yaro ba zai iya ci ba gudun ya laƙe masu ga maƙogoro.
sauran ƙasashe masu ikon kansu irin
su Gobir.
Sarakunan ƙarƙashin mulkin Fulani sun rasa
wannan. Idan sarkin Kabi ya faɗa
babu wani Sarki a daular Kabi da zai faɗi
akasinsa.
sheshe kuwa Fulani Udawa masu
kiyon tumaki zalla sun fi shahara da shi. Sheshen nan da ya burge ‘yan daba
Buda ke son kushewa.
07034224741 ranar 26/6/2017 a
ranar ina Gidan tarihin Kabi da ke garin Argungu.
(kusa). Don haka aka kira ta
“barayar kusa wurin hutawar ɓera
cikin raminsa.
ciki ake tura hannu a sa
lalle. Hannu na ciki kamar kifi a cikin gora. Balli wani baƙin kifi ne mai rigima da
karmanci irin na tafiyar karuwa. Kabawa na yi masa kirari da: Balli kamar kifi”.
da fari da ja da baƙi da algashi da shuɗi ga su nan dai. Dattijon
banza shi ne Dandaudu ko cali na wasanni. Calin ‘yan dambe na sa ulu a
kwankwaso ya yi rabaja. Ke nan da mata sai dottijon biri ke sa ulu.
hamayya da sa-in-sa da
jayyaya da faɗi-in-faɗi.
bai ƙare ba. A wata fassara tana ɗaukar bai gaji ba
:Daga Sanyinna yak kwan
:Shagari ya’ aje yak
kwana
:Ga Hausa tana kallo
:Tsamiya can uban
Jibo yak kwana
:Ga Hausa tana kallo
:Ya kwan Tureta gagara ƙarya
:Ɓurmawa na
kallo
:Murai can uban
Jibo yak kwana
:Zamfara dut na kallo
:Bunguɗu can gadan-gadan yak kwana
:Zamfara duk na kallo
:Ga baƙon mutan Ƙwatarkwashi
:Sarki in don Allah ya so.
:Bahago ya zo Gusau da rarar ƙarhi
:Ba a koma haye mai ba.
:Nan yag game da Sarkin Ƙaura
:Yaw watce mutanenai
:Ni na so shi kwana Tcahe da
yaz zo
:Sai yar raɓawatai
birnin Surame da man kaɗe. Dalili da haka, an share ƙarnuka da yawa kowace shekara
idan zafin rana ya tsananta sai kufan ganuwar Surame ta nashe da masƙi. Bugu da ƙari, Nufawa abokan wasan
Katsinawa ne, Kanta kuwa mahaifiyarsa Bakatsina ce. Bai kamata Nupe ta mara wa
wata daula baya ba in ba Kabi ba.
Birnin Tudu, “Bukin kamun
Kifi a ƙasar
Argungu”, 1984, kundin BA.
Dono. A filin Fuloti na da,
nan aka yi, gumuzun ɗebe
takaici, kowanensu ya bar accakwama. An ce, shi ne yaƙi na ƙarshe da Sarki Sama ya yi a
rayuwarsa.
tu’assubanci da ɓangaranci da zalunci ya yi
katutu. Haƙiƙa, a kan haka ne Kabawa da
Gobirawa suka ja daga cewa, kowa ya kare gidansu ganin abin ya koma yaƙi ba jihadi ba.
Buda sosai. Na amfana da ita
duk da yake ban san shekarar da aka yi hirar ba. Ina godiya ga farfesa Magaji
Tsoho Yakawada da ya nemo waƙar
a Jami’ar ABU ya ba ni faifai na saurara.
[37] . Na fahimci duk garin da na je, in na tambaye su
abin da Buda ya ce a kan Sarkinsu, in mai muni
ne ba sa faɗa, sai su juya waƙar. Don
haka, waƙar na buƙatar bincike
na musamman a bi rariya-rariya a ƙasar Hausa a
tattaro ɗiyanta a tace su. Misali wasu
na cewa ya ce:
Jagora : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza
: Runji shi ka wa yanke.
Haƙiƙanin gaskiya
a ɗan bincikena ba haka abin yake ba
cewa ya yi:
Jagora : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza
: Sashenai na jimai
: Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza
:Tsoron Mamman yaj ji
Cukurfa (500) na shinkafa aka
ba shi sarkawan da za su kai mai kifin miya da rundawan da zai kai masa mama.
Ya ce, duk waɗannan
ya baro su Yabo don haka shi jaruntaka da gwarzantaka ya biyo, soyayyarsa da
Kabawa a zuci take.
No comments:
Post a Comment