Mahalicci halitta da Ya nufi ƙaga halittocinSa da Ya shimfiɗa su a duniyarmu da muke zaune, a kan tsarin shugabanci ya tsara abinSa.
Buwayayye Ya wanzu gabanin kowa da komai. Tun a nan, mai hankali ya san ana
karantar da shi muhimmancin gabaci. Ya mamaye komai da komai bayan da Ya
halicci komai da komai. A nan, ana yi muna hannunka mai sanda, ga martaba irin
ta gabaci. Zai ci gaba da wanzuwa bayan fakuwar duk wani wanzajjen abu a bangon
duniya. Wannan ishara ce ta tabbatar mana da cewa, umurnin gabaci na aiki da
furuci sun cancanci su soke aiki da furucin duk wani….
---------------------------------------------
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
Jahar Katsina, Nijeriya
--------------------------------------------
Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ‘yan’uwa
Musulmi ƙarƙashin Jama’atul Muslimin, jagorancin Malam Muhammadu
Bello Ɗanmalam a makarantar Nana
Asma’u ranar Alhamis ta ƙarshen Safar, 1435 daidai
da 2 ga Junairu, 2014 da ƙarfe takwas na yamma
Da suna Allah mai rahama mai jinƙai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Muhammadu ɗan Abdullahi (SAW) da iyalansa da sahabansa da waɗanda suka yi koyi da su ya zuwa ranar sakamako.
Gabatarwa:
Mahalicci halitta da Ya nufi ƙaga halittocinSa da Ya shimfiɗa su a duniyarmu da muke zaune, a kan tsarin
shugabanci ya tsara abinSa. Buwayayye Ya wanzu gabanin kowa da komai. Tun a
nan, mai hankali ya san ana karantar da shi muhimmancin gabaci. Ya mamaye komai
da komai bayan da Ya halicci komai da komai. A nan, ana yi muna hannunka mai
sanda, ga martaba irin ta gabaci. Zai ci gaba da wanzuwa bayan fakuwar duk wani
wanzajjen abu a bangon duniya. Wannan ishara ce ta tabbatar mana da cewa,
umurnin gabaci na aiki da furuci sun cancanci su soke aiki da furucin duk wani
mahaluƙi. Da Allah bai kasance haka ba, muna da damar mu
zaɓa wa kanmu tsarin da ya dace
da son zuciyarmu. kasancewarSa yadda Ya kasance, Ya rufe muna kowace ƙofar tunanin kanmu ga abin da ya shafi siyasar rayuwarmu
face sai mun tuntuɓe Shi domin ta yau muka sani,
ta jiya wajenSa aka samu labarinta, ta gobe kuwa Ya keɓanta ga ilminSa. A bisa ga wannan salo, za mu gina
tattaunawarmu. Allah Ya yi muna jagora.
Mene Ne Shugabanci?
Shugabanci ya ƙunshi abubuwa biyu manya-manya a tsarin tafiyar da
rayuwar ɗan Adam. Na ɗaya shi ne, shugabanci kansa. Na biyu shi ne
“mulki” wanda yake ɗa ne daga cikin ‘ya’yan
shugabanci. Sunan jikansu “Iko” shi ya sa suka fi jikansu hankali da sanin ya
kamata. A kowace irin fasara ta addini ko ta zamani waɗanan abubuwa uku: shugabanci da mulki da iko
jejjere suke tafiya kamar kashin awaki.
A luga shugabanci na da
ma’anar rigaya ko gabacin abu na haihuwa ko shekaru ko sani ko ƙwarewa a sana’a ko a fahimtar wani abu. A wata luga yana
iya ɗaukar ma’anar “Jagora” kamar
makaho da majayi. Ba kuskure ba ne a fassara shi da “Zagi”, domin a Hausance
sarki “Uban Zagi” ake ce masa. An yi daidai idan aka ce masa “Madugu”, domin
ayarin fatake ba su san wani ba shi ba. A dabin caca shi ne “Kartagi” ba wanda
ya isa ya buɗa bajau ba da umurninsa ba. A
fassarar jinsi a kira shi “Maduga” saboda mata ba su san kowa ba sai ita. Idan
ta hau karagar mulki ita ce “Magajiya” a fagen bori take da suna “Inna”.
A wajen Bahaushe, kalmar
“Sarki” baƙuwa ce, wadda aka sani “Gogarma”. Da aka ɗan ja zango kalmar “Shugaba” ta karɓe tuta. Kalmar “Shugaba” ita ta haifar da
“shugabanci”. Dukkaninsu sun ƙunshi kalmomi biyu ko uku a
doguwar fassara. Kalmar farko ita ce “sha” wadda ta koma “shu” a gaɓoɓin. Kalma ta biyu ita ce “gabaci” ko “gaba” da “ci”. “Sha” ɗin nan ko “shu” an gajarta su ne, ga alama
ma’anarsu “shiga” idan aka haɗa da “gaba” sai a samu “shiga gaba”. Haka kalmar Larabci “ra’is” daga
kalmar “kai” na ɗan Adam aka cirato ta. Dalilin
Larabawa ke nan na yi wa kai kirari “sayyidul jasadi” shugaban jiki. Turawa su
ce da ita “President” a ma’ana su ce: The elected head of a republic ko The
head of an organization. A kowace fassara daga fasarorin an samu kalmar
“head” wadda ta yi canjaras da ma’anar Bahaushe da Balrabe, don a fuskar
“shugabanci”, za mu ce, shi ne jagorar jama’a wanda suka aminta da shi wajen jiɓintar al’amuransu na siyasa, zamantakewa da addini.
Don haka shugabanci shi ne tafiyar da al’amuran jama’a bisa ga yardarsu da
amincewarsa ga dokokin da suka yi imani da su. Shugabanci shi ne waƙiltar mutane ga abin da suka miƙa wuya gare shi bisa ga tafarkin da zai ciyar da su gaba ga manufofinsu da
daidaita tunaninsu. Wanda aka damƙa wa shugabancin shi ne
“shugaba” don haka ala tilas shugaba ya kasance:
i) Waɗanda yake jagoranta suka zaɓe shi shugaba.
ii) Waɗanda yake jagoranta sun yarda da shugabancinsa.
iii) Yana
jagorantar mutane bisa ga abin da suka yarda a kai.
iv) Ya yi imani da aikin da aka waƙilta shi ba wanda yake so na ransa ba.
v) Ya ɗauki waɗanda yake jagoranci iyalansa domin da haɗin kansu ya kasance shugaba.
vi) Idan aka rasa ɗaya daga cikin (i-v) matsala ta tashi daga shugabanci ta koma mulki.
Mene Ne Mulki?
A hankalin tuwo muna hangen
mulki a matsayin wani zamani na shugabancin wani shugaba. A bayyananiyar magana
mulki ya fi da haka. Mai mulki shugaba ne amma ba mai shugabanci ba. Wataƙila yana shugabancin bisa irin tsarin da ya ƙirƙiro da kansa. A wani lokaci a
same shi bijirarrare ga buƙatun mutanensa. Wanda ya hau
gadon da ƙarfin tuwo ko ƙarfin maguɗi ko yaudara mulki yake yi ba
shugabanci ba. A tsarin mulki, ba a kula da bin wata doka ta addini ko ta
hankalin tuwo ba, shugaba shi ne wuƙa, shi ne nama, shi ne ɗan doka, shi ne alƙali, shi ne yari kuma shi ne ma’ajin baitalmalin hukuma. Waɗanda duk ake gani da waɗannan muƙamai a tsarin shugabanci na
mulki, hoto ne kawai je ka na yi ka. Shugabancin irin na mulki ba a sassauta wa
adawa, na ƙasa bai isa ya ci gyaran na sama ba. A kujeran
mulki ganin mai mulki shi ne gani, ganin waninsa makafta ne. Dalilin Larabawa
ke nan na kiransa muluuku Turawa su ce dictator don haka Hausawa
ke kiransa Iko.
Wane Ne Shugaba?
Masu zargin Musulunci da
rashin wayewa ga tsarin shugabanci adawar gado ce suke son su tabbatar da ƙarfi da yaji. Gabanin a samu kyakkawan shugabanci sai an
samu shugaba nagari nagartace da ingatattun nassoshi suka ce a kula da:
i)
Yadda ya shigo majalisa. Zaɓensa aka yi a addinance bisa ga shura? Ko zaɓensa aka yi a al’adance bisa ga gadon-na-gaje ka?
Ko zaɓensa aka yi bisa ga
kafirtaccen tsarin da ya ce (wai!) babu ruwansa da kowane addini? Ko shugaban ƙaddara ne irin na juyin mulki ko mulkin mallaka? A tsarin
shari’a zancen “shura” kawai ta sani. Sauran fuskokin ba su da sahihin nassi,
sai dai ba ta ce, a yi fito-na-fito da su ba idan sun kai ga karaga. Yi musu ɗa’a wajibi. Gaggauta neman mafita daga tsarinsu
wajibi ne. Wane tsari ya fi shari’a ido biyu na hangen lamari?
ii)
Addinin Musulunci ya shafe dukkanin addinan da ke
gabaninsa. Don haka, a wajen Allah babu wani addini sai shi. Wanda duk ba shi
yake yi ba, ya kafirta sunansa kafiri. A sahihin nassi dole shugaban da Musulmi
zai zaɓa wa kansa ya kasance Musulmi.
Komai saɓon Musulmi yana nan tare da
sunan matuƙar bai halasta saɓon Allah ba. Komai adalci da natsuwa da ƙima da fasaha da basirar kafiri yana nan kafiri matuƙar bai miƙa wuya ga saƙon Manzo (SAW) ba. Duk wata jam’iyyar da Musulmi ya shiga
ba ta soke Musuluncinsa, kamar yadda duk wata jam’iyyar da kafiri ya shiga ba
ta goge kafircinsa. Miƙa wuya ga dokar da ta yi takin
saƙa da dokar Allah kafirci ne ƙarƙashin kowace jam’iyya yake.
iii)
A mahangar shari’a, shugaba dole ya kasance baligi mai
diwani a wajen Allah. A hankalin addininmu dole ya zamo “namiji” ba mace ba, ba
mata maza ba, ba zulumbu ba. Kasancewarsa daddaƙaƙƙe masana sun daɗa juna sani. Bisa ga wannan tunani ne nassi ya kawo
kasancewarsa mai cikakken hankali domin wanda bai balaga ba ruwan faranti ne,
mace kuwa hankalin bai rinjayi tunani da wayo ba. Wanda ya rasa al’aurar da za
a tantance shi ba ya da madogara ga nassi. A umurnin addininmu zaɓen mace ko yaro yin fito-na-fito da dokokin da
Allah Ya aiko Manzo (SAW) da su ne.
iv)
Sahihan nassoshi sun ce, a kula da hankalinsa da ilminsa
da wayonsa da lafiyarsa. Babban hankali a wajen nassi shi ne gane Allah a
tauhidance. Jagoran ilmi a nasshi shi ne sanin littafin Allah a tsaftace. Wayo
shi ne rarrabe halas da haram a tsanake. Lafiyar jiki ta haɗa da gaɓɓai manyansu da ƙananansu domin samun damar waƙiltar al’umma a mutunce.
Faƙihun Shugabanci A Nassoshin Shari’a:
A ganin addininmu ba dole sai
shugaba ya fi kowa komai zai zama shugaba ba. Haka kuma, mai da shi abin gado
bai tabbata ga sunna ba. Ƙabilantar da shi, da ɓangarartar da shi, da jinsartar da shi, fitina ce
babba, dole a kiyaye da haka. A fiƙihun shugabancinmu akwai:
i) Shugaba mai cikakken iko: A nan, ba mu ce mai cikakken
shugabanci ba ko mulki, “Iko” muka ce. Nassi ya tabbatar da Allah kawai ke da
wannan matsayi a sammai da ƙassai. Shi kaɗai ke halastawa da haramtawa dokokinSa tsalkakakku
ne hukuncinSa ba ya tashi. Duk hukuncin da ya saɓa wa nasa ƙetare haddi ake kiran sa.
Hukuncin miƙa wuya gare shi “ridda”. Yaƙar masu tabbatar da cikakken ikon Allah shi ne fasadi da ta’addanci da
shisshigi mai kai ga hushin Allah ga makangara.
ii) Manzanci da Annabci: Waɗannan nau’in shugabanci daga shugaba mai cikakken
iko suke. Wanda duk aka zaɓa Manzo ko Annabi naɗaɗɗe ne daga Allah, bin sa wajibi
ne. Adawa da shi da yaƙarsa da ƙin bin tsarin da ya zo da shi kafirci ne a sahihin nassi. Wanda Allah Ya
aiko, da aikinsa da furucinsa da yin shirunsa da kau da kansa da inkarinsa da
yardarsa duk hukunci ne saukakke. Don haka, duk wani tsari da za a yi na gyaran
fuska ga nasa ko soke shi gaba ɗaya ko soke sashensa ko faɗaɗa shi wurin da ba a faɗaɗa ba ko taƙaita shi wurin da ba a taƙaita ba shisshigi ne da ta’addanci. Shugaban duk da ya hau karaga a irin
wannan tsari cikin duhu ya hau, cikinsa yake tafiya, ciki ake yi masa rakiya,
yaya zai dace da kyakkyawan shugabanci?
iii) Allah bai taɓa aiko Manzon da ba ya mutuwa ba: Idan ya mutu tsarin da an ka
ba shi yana nan sai mamaya su bi kawai. Ashe! A tsarin kyakkyawan shugabanci
ana son ci gaba da dogewar dokoki da tsare-tsare. Saɓa wa dokokin da tsare-tsaren da Allah Ya aiko bayan
wucewar manzaninsa shi ya sa Yake aiko wasu manzani su jaddada. Tsarin duk da
ba bisa na Allah yake ba safe duk cikin gyara yake kamar na tsohuwar mota a
hannun tsohon bakanike. Shugaban da aka ɗora a kansa an wahalar da shi domin ba a ba shi tazarar
yin kyakkyawan shugabanci ba.
Ayyukkan Shugaba:
Daga cikin ayyukkan shugaba
akwai kariya. Ya kare rayuwar mutanensa da lafiyarsu da dukiyarsu da ƙasarsu ta fuskar tanada mata kyakkyawan tsaro. A tsari,
shugaba na da ikon zartar da kowane hukunci da shari’a ta ba shi. Haƙƙensa ne tsare dokokin ƙasa ga ‘yan ƙasa da masu shigowa ƙasarsu. Yana da hurumin tabbatar da dokoki da hukunce-hukunce da aka
tabbatar. Ba dole ne sai ya fi kowa zalaƙar magana ba. Babu tilas ga
kasancewarsa mai iya rubutu ko karatun rubutu ba. Waɗannan duk yana daga cikin ayyukansa samar da su. Ƙasa duka shugabanta ne fuskarta, dole ne ya yi tsayin
daka na fito da ire-iren martabobinta da kare mutuncin mutanenta na ciki da
waje da tsare musu al’adunsu da addininsu da bunƙasa tattalin arzikinsu.
Shugabancin Yau A Sikelin
Jiya:
Turawan mulkin mallaka suka
fara ɗora turbar akalar
shugabancinmu a kan yaudara. Sun tarar da tsari gawurtacce ya riga ya cika
jama’a sun miƙa wuya gare shi, sun yi imani da shi, a kansa suna
dadaukar da rayuwarsu. Da tsarin aka yaƙe su, aka fatattaka su, aka
murƙushe su, aka gargaɗe su, aka yi musu koran kare a farfajiyar bilad
as-Sudan. Da suka ga ruwan masu yawa ne, kuma masu zurfi, suka yarda da Limancin makaɗa Narambaɗa:
Jagora: In ka ishe gulbi ya cike,
: In ba
kowa ko ka iya.
Yara : Koma ka tsaya ganga ka kwan
Gindi: Ya ɗau girma ya san yabo
: Mu zo mu ga Alƙali Abu.
Turawa bayan da suka kwana a
ganga, sai suka ci gaba da shirin yadda za su sake shiga ko ba kowa. Cikin
dasisarsu ce aka ɗebe zancen addini ga tsarin
shugabanci. Don haka zance zama Musulmi ko ba Musulmi ba, bai taso ba. Batun
jinsi mulkin mace ko namiji ba matsala ba ce. Yarda da wani tsari saukakke daga
kowa ya fito a watsar da shi a zauna a sake tunani. Waɗannan abubuwa duk a munafunce aka tsara su, domin
masu tsarin ba su shafa da kare aƙidojin addininsu a cikin
tsarin ba. Shi kansa tsarin nasu ne. Masu zartas da su da kare su nasu ne. Duk
wani mataki da aka ɗauka na kare haƙƙi da ‘yanci da doka daga cikin addininsu aka cirato su.
Tsarinmu bai yarda a laɓe ga wani abu a kare shi ba,
sai dai a laɓe gare shi a kare. Yau yaya
ake?
A tsarin shugabancin yau,
adalcin shugaba da nagartarsa kare Fatin jam’iyyarsu da manufofinsu.
Jam’iyyoyin nan an tsara su bisa ga sharaɗi babu zancen wani addini ko wata aƙida in ba tata ba. Bin wani hani ko horo na wani addini ko wata fahinta
irin ta addini saɓa wa jam’iyya ne mai haranta
wa ɗan jam’iyya zama cikinta. A
ciki ba a yarda wani addini ya fi wani ba don haka babu kafiri babu Musulmi
bale mushariki maganar fasicci ba ta taso ba. Dokokin jam’iyya su ne nassi abin
dogaro wani ba su ba abin watsarwa ne. Kowace ƙungiyar jam’iyyar siyasar demokraɗiyya da wannan manufa aka kafa ta. Ta wace hanya za a bi
a samu kyakkyawan shugabanci irin wanda Allah da ManzonSa suke son mu yi alhali
mun riga mun ce a aje su gefe ɗaya? Wannan mugun rutsi da ƙangi shi ya tilasta wasu bayin
Allah tawaye ga tsarin demokraɗiya ‘yan bokon da ke cin gajiyarta suka dinga yi musu sunaye daban-daban na
halastar da jininsu.
A gajeren tunaninmu, adalcin
tsare dukiyar mutane da zaman lafiyarsu da bunƙasar tattalin arzikinsu da zamansu kara zube kowa yana da ‘yancin kansa wai
shi ne kyakkyawan shugabanci. Masu wannan makahon tunani a koyaushe ƙasashen Turai da ‘yan barandarsu ne abin ba da misalansu.
Idan za a waiwayi kundin tarihi na jiya da yau da muke ciki, wace al’umma ta fi
al’ummar da addini ke shugabanta ci gaba da zaman lafiya? Wace ƙasa ta rungumin addinin demokraɗiyya ba ta shiga cikin fitinonin da suka fi ƙarfinta ba? Shugabanci nagari ba ya taɓa shimfiɗuwa sai da tsari nagari. Wanda ya yi mutane shi ya fi kowa sanin tsarin da
ya dace da su. Ƙirƙiro wani tsari saɓanin nasa shi ne zalunci. Komai adalcin mutum aka ɗora shi a kan zalunci aka ce ya yi aiki da shi a
matsayin shugaba, wane suna ya kamata mu kira shi da shi?
A baƙauyen tunaninmu ilmin boko da wayon zama da mutane da fuska biyu, da wayon
ci da ceto da ci da addini da ƙabilanci da ɓangaranci da samun farin jini ga ‘yan dandin
zamaninmu, wai, shi ne tafarkin hawa karagar mulki! Wanda duk ya jahilci
addininsa ya rasa hankali da basirar jagorantar mutane sai dai a yi kama-kama.
Tun farkon duniya zuwa yau, ba a samu wanda ya shugabanci mutane da hankalin
tuwo da wayon adana dukiya ya gama lafiya ba. Shugabanni uku ne: wanda aka yi
wa wahayi, da wanda ke biyar abin da aka yi wahayi da wanda ke biyar son ransa
da son ran jama’arsa. Duk shugaban da ya samu kansa cikin na uku ya yi ban
kwana da adalci ya ba fitina maƙulin buɗe ƙofar shiga ƙasarsa. Da shi, da waɗanda suke ɗora shi a kan karaga, da waɗanda ake shugabanta, da tsarin da ake ciki, duk sun
shiga ɗemuwa. Kowa ya zama mai laifi,
wane laifi za a tsawatawa?
Taliyon Tarihi:
A zamanin Annabi Ibrahim (AS)
addinan gargajiya ke tashe da jagorantar mutane aka aiko shi da gaskiya ya rusa
su. Tattalin arzikin Masar ya bunƙasa bisa ga tsarin sarautun
gargajiya, aka aiki Yusuf ya daidaita shi. Babu irin cigaban da Fir’auna bai
kawo ba a shugabanci aka aiko Musa (AS) ya gyara masa tsari. Bilƙis ta kai duk wurin da sarauniya ke kai, aka sa Sulaiman
(AS) ya yi mata kakkaɓan gara. Cigaban Samudawa ya ɗara namu ban al’ajabi aka sa Shu’aibu ya kafa musu
harsashe. Makka ita ce cibiyar duniya da wayewa da bunƙasa, duk wani gari da ita ba, sunansa ƙauye, sunan jama’arsa ƙauyawa, aka ba Muhammadu (SAW)
hasken da ya fi wayon mai wayo wayo. Wannan wata ishara ce gare mu cewa, da
dabarunmu da fasahohinmu da ilminmu na cin tuwo suna iya tserar da mu, da ba a
turo annabawan da suka gabace mu ba. Ashe! Yanzu wanda duk ke ganin mun ishi
kanmu don ‘yan takardunmu na shaidar zur wasa yake yi. Wannan ita ce matsalar
shugabancin ƙasarmu Nijeriya ta yau (2014).
Kundin tarihi ya tabbatar muna
da cewa, sarakunan gargajiya da aka yi tun gabanin Musulunci a ƙasar nan zalunci ya rusa su. Daulolin da aka yi bayansu
ba su kai labari ba. An yi ƙarnin da addini ya shugabanci ƙasar nan, ba a taɓa yaƙi na ƙabilanci da yanki da ɓangaranci ba a farfajiyar ƙasarmu. Mulkin mallaka ya zo,
ba da shiri ba ya gangame ‘yan kwalayensa na kunya ya san inda dare ya yi masa.
Jamhuriyya ta farko ba ta sallame salla a zaune ba. Mulkin Soja na Oransi faɗaɗa maƙabartu kawai ya yi. Mulkin soja na Yakubu Gawon da
Murtala dutse hannun riga aka ƙare. Obasanjo ya zo, ya yi
muna kashin mummuƙe ya assasa harsashen bambancin addini da ƙabilanci makamai suka fara tsada. Shagari na batun miƙe ƙafa aka sallame shi. Buhari ya
goge allo ba a fara rubutu ba aka sallami ‘yan makaranta. Babangida ya rubuta
huɗuba aka tilasta shi ba
Shonikan ya karanta. Shonekan bai ƙare muƙaddima ba, Abacha ya yi iƙama. Abacha na batun a
daidaita sahu aka sallame salla. Abdussalam ya zo amincin bai samu ba, Obasanjo
ya shigo da bababr riga. Cikin ƙoƙari na ta miƙe ta miƙe da shi, ‘Yar’aduwa ya zauna.
Babban guzurin ‘Yaraduwa gare mu ba da izni a kashe mu da sunan da ba mu sani
ba wai! BOKO HARAM. Jonathan ya yi garkuwa da wasiyyar ‘Yaraduwa aka girke
bala’i a ko’ina Musulunci yake a ƙasar nan. Da wanda ya ce, a
kashe ka, da wanda ya ba da umurni a saka maka wuta tun ba ka ida shurewa ba,
wane ne ya fi ƙiyayya da kai? Danƙari! Sunan wasu littafai Ku Yi Karatu, Ku Ƙara Karatu, Ku Yi Ta Karatu, Ƙaramin Sani Ƙuƙumi ne.
Baya Ta Haihu:
A iya fahimtar duk wani mai
hankali a Nijeriya. A tarihi tsarin mulkin soja ya kasa fitar da suhe wuta. Ɗan lokacin da talaka ya san akwai hukuma shi ne zamanin
Gowan da Murtala da Buhari. Mulkin farar hula, a koyaushe gara jiya da yau. Su
Sir Ahmadu Bello sun ɗara su Shagari. Su Shagari sun
fi su Obasanjo. Obasanjo sun gota ‘Yar’aduwa. Yar’aduwa shi ya haifi bala’in da
muke ciki a yau, ka da Allah Ya maimaita muna. Har ‘yan Nijeriya sun fara
mantawa da batun yaƙin ƙabilanci da ɓangaranci da addini da siyasa
yau ga su a cikinsa tsamo-tsamo. Jin tsoron haka wasu ke ganin baya ta haihu.
Ga tsarin shugabancin da muke
ciki a yau, an fito ƙiri-ƙiri an nuna akwai addinin da ba a son kowane fati ya fitar da shugaban ƙasa a ci. Akwai yankin da ba a son shugaban ƙasan ya fito ko shi waye? Akwai ƙabilar da ake son komai farin jininta ka da a samu shugaban a ciki. Akwai
addinin da ake so dole shi zai ja akalar wannan ƙasa, in ba haka ba, sai dai a tashi baram-baram in shataf-shataf in
jina-jina. Allah Ya kare mu. Ga ‘yan hujjojin da suka sa muke ganin baya ta
haihu:
i)
Yaƙin da aka jibge a yankunanmu
ba a sa ranar tsakaita wuta ba. Haslai ma, a kasafin kuɗin shekarar 2014 makamai aka keɓe wa kaso mafi tsoka.
ii)
Cikin dabara an gayyato UN ƙasashen duniya sun karɓa mata kira bisa ga sunan da ‘yan ƙasarmu suka ƙirƙiro muna, an halastar da
jininmu saki ba ƙaidi.
iii)
In da yawa muke taƙama, akwai raɗe-raɗin cewa, a yankunanmu da ake yana ba za a yi zaɓe ba. Masu karatun jaridu sun san biri ya yi kama
da mutum.
iv)
Wai! Yanzu ƙasarmu ta binciko akwai ‘yan
Nijeriya fiye da miliyan arba’in da biyu a ƙasashen duniya. Zaɓen da za a yi na (2015) ana
son a ba su damar jefa ƙur’a daga ƙasashen da suke zaune. Kun dai gane.
v)
Matsalolin da ke tattare ga tantancen adadin masu zaɓe ga abin da jaridu ke sunsunowa ya yi yawa. Ka da
ku yi mamaki a haramta wa duk ɗan ƙasa da ba ya da takardar I.D ta zama ɗan ƙasa ba jefa ƙur’a. Idan aka zo da wannan salo za a sa mu tagumi. Don
haka, kura gare ku masu awaki.
vi)
Taron tarayya na ƙasa da ake so a yi da lauje
cikin naɗi. Wasu maƙiya wannan ƙasa da sun ka gaji da zama da
mu buƙatarsu a samu kafar raba ƙasa ko yaƙi ya ɓarke a yi tamiƙen dole. Mu tabbata ka da a yi
komai duƙunce a yi shi ta-da-ta wankin ɗan kanoma mashaya. Ba mu ce ka da a raba ƙasa ba, amma in rabo za a yi a hura wuta kowa ya ga
rabonsa.
Naɗewa:
Tilasta zama ƙasa ɗaya dole ga mutanen da hankalinsu ya riga ya tashi ga juna wata babbar
matsala ce. Da zama ana zubar da jini koyaushe gara a raba gari kowa ya yi
tuwonsa. Samun shugaba adili da zai daidaici kowa cikin irin wannan tsari
mawuyaci ne. Ganin laifin juna a koyaushe dole ne domin kowa takaicin ɗan uwansa yake yi. Sake baki a bi ƙungiyoyi ko jam’iyyun siyasa ido rufe ba ya yi muna
cefanen da za mu more romonsa. Da an yi kuren addini ga shugabanci an yi fargar
Jaji. A shiga a gyara mun yi mun fi mai kora shafawa. A tsaya gefe a ƙi shiga mun yi, an yi ba da mu ba. Mun sa hannu mu gyara
an yaƙe mu. Mun sa baki mu gyara an ɗaure mu. Mun ƙi abin a zuci an yi saniyar
ware da mu. Wace dama muke da ita wadda ta rage? Ina sauraren ku.
Na gode.
No comments:
Post a Comment