Magana ita ce
mutum, da ita ake rarrabe shi da sauran halittun dabbobi, ƙwari da tsuntsaye. Kowace iri martaba da ɗaukaka ɗan Adam yake da ita idan ya rasa magana ba su da wani tasiri
a rayuwarsa. Magana ita ce cigaban ɗan Adam ta farko gabanin ya iya sarrafata a rubuce wani ya karanta ta a
fahince shi. Tunanina na gabatar da wannan muƙala shi ne, a fayyace nahawun magana gwargwadon yadda ɗalibin harshe zai gano cewa, lallai nazarin harshe ba ƙaramin ɗaukaka gare shi ba ga rayuwar ɗan…
NAHAWUN MAGANA
(Jereƙen Biyar Diddigin Ma’anar Magana da Rabe-Rabenta a Bahaushen Tunani)
Aliyu Muhammadu Bunza
Faculty of Humanities and
Education
Department of Languages and
Cultures
Federal University Gusau.
Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu Augi
College of Education Argungu, Kebbi State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga
Maris, 2017 da ƙarfe 10:00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa
Gabatarwa:
Magana ita ce mutum, da ita ake rarrabe shi da sauran
halittun dabbobi, ƙwari da tsuntsaye. Kowace iri martaba da ɗaukaka ɗan Adam yake da ita
idan ya rasa magana ba su da wani tasiri a rayuwarsa. Magana ita ce cigaban ɗan Adam ta farko
gabanin ya iya sarrafata a rubuce wani ya karanta ta a fahince shi. Tunanina na
gabatar da wannan muƙala shi ne, a fayyace nahawun magana gwargwadon yadda ɗalibin harshe zai
gano cewa, lallai nazarin harshe ba ƙaramin ɗaukaka gare shi ba
ga rayuwar ɗan
Adam. A fahintarmu, mu ɗaliban Hausa, sirrin sanin magana da iya ta yana cikin sanin
nahawunta. Matuƙar ba a san nahawunta ba, ba a gane bakin zarenta. To, mene
ne nahawun magana?
Nahawun
Magana:
A iya ɗan bincikena, Farfesa Isa Mukhtar ne manazarci na farko da ya
yi zuzzurfan bincike kan “nahawun Waƙa” a digirin MA
Jami’ar Bayero, Kano. A taƙaice, nahawu kalmar Larabci ce. A Larabci tana nufin “ma’ana”
ko a ce “kamar” ko “misali” ko “daidai”. An ce, Sayyidina Aliyu (RA) ya fara
fito da ita ga ajamawan da ba su iya Larabci ba, in sun karanta ko faɗa a kan kuskure, ya
ce “nahwi haazaa” ko “nahwu kazaa”. A fagen karatu, “nahawu” ya fara cin gashin
kansa da sunan daidaita magana da biyar ƙa’ida ga
ma’abotanta bisa ga tsarin yadda suke faɗarta, furtata, jeranta kalmominta su gina jimlar da za ta
fito da ma’anar da za a gane abin muradi ba da mamare ba. Ashe ke nan, nahawu
shi ne fasalta abu dalla-dalla yadda za a kakkaɓe masa kowace irin ƙurar da za ta hana
a fahimce shi. Burina a wannan ɗan bincike shi ne, fayyace ma’anar abin da ake cewa “magana”
wadda ɗaliban nazarin
Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa za su yi madogara babba a kai. Haka kuma,
ma’anar ta fito da sigogin da kowane Bahaushe ɗan asali zai kama ma’anar abubuwan da aka ƙwalailaice kai tsaye.
Sunayen
Magana:
A nawa tunani, ina ganin zai fi dacewa mu fara bijiro da
ire-iren sunayen da Bahaushe ke yi wa “magana” domin da an ji su, an san magana
yake nufi. Bahaushe na yi wa magana suna da: magana, batu, zance, shirme, shiɓa, batutuwa, ɗumi, maganganu,
sabbatu da sauransu. Bari mu ƙwalailaice su mu gani:
Magana: wadda ake furtawa a baki ko a yi nuni da wani abu da za a
fahinci abin kai tsaye. Ga wata waƙa ta Tashe da yara
suka fassara magana:
Jagora: Ke magana ke!
Wata magana ta wuce baki
Yara : Da
ɗuwawu aka yin ta.
Batu : Yana ɗaukar wata magana ta musamman kamar zancen sharholiya in ji
Narambaɗa.
Gindi: Gwarzon shamaki na malam toron giwa
: Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Zance: Magana ce musamman a fagen yin hira da
wani ko wasu a faɗar Aƙilu Aliyu
Hana mata leƙa wajen matanka
Don kar tai musu zancen banza.
(Waƙar ‘Yar gagara).
Shirme: Maganar da ba ta da gaɓar kamawa. Ma’anarta ta ƙi fita
sarari.
Ban gane abin da yake faɗa ba. Shirme kawai yake yi, ba ya da hankali.
Shiɓa: Maganar da ba ta kama hankalin kowa. A fassarar Kaftin
Umaru Ɗa Suru ita ce.
Bakunansu sai warin taba
Me suke faɗa in ban da shiɓa.
Batutuwa: Jam’in “batu” ke nan, amma ana amfani da ita ga
maganar fitar hankali irin kirari kamar yadda Sambo Wali Giɗaɗawa ke cewa a waƙar Janborodo:
Da sunanka Alla za ni fara batutuwa
Tunawa da manya masu yaƙi da garkuwa,
Fito-na-fito ka yi ta ba ta ƙidayuwa,
Yabon bajini ad dole don ba ya gasuwa,
Zaman ba a giwa da raskwana ba ya faruwa.
Jagora: Ya watse batutuwa na Jekada ya taho gida
Yara : Kunya
ga ta nan gare ku mutanen banza
Gindi : Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
: Baban
Dodo ba a tamma da batun banza.
Jagora: Batutuwan
da nikai don mahassada su ji haushi
Yara: Waɗanga yanga da kara, wa ka rufa ma baki?
Gindi: Koma shirin daga gwarzon bahago ɗan Iro.
Dumi: A Sakkwatance idan an ce ɗumi ko ɗumumuwa ana danganta su da magana maras tushe ko ta banza.
Magangannu: Magana tilo ce jam’inta maganganu. Maganganu su ne zantukan
fitan hankali na ruɗewa da raki da jin tsoro.
Sabbatu: Magana ce da ake yi cikin ɓatar hankali. Ga yadda Sambo Wali ya ruwaito ta:
Idan an ka ce ga Bube duk sai su raurawa,
Maza sai su zan mata suna ‘yan batutuwa
Na saiɓi da sabbatu ƙafafunsu na rawa.
(Waƙar Janborodo).
Nauyin Magana:
A tunanin Bahaushe, cikin fashin baƙin nahawun magana akwai nauyin magana. A awon nauyinta, a wajen Bahaushe,
akwai babba, akwai ƙaramar magana. Babbar magana ita ce ke buƙatar kulawar gaggawa da fuskanta gadan-gadan. Gaskiyar Bahaushe da yake da
karin maganar: babbar magana ɗan sanda da ya ga gawar soja. Ita kuwa ƙaramar magana, ma’anarta na kai tsaye shi ne tsegumi ko tsince ko
an-yi-an-ce. Ita ƙaramar magana tana da harshen damo. Takan kasance doguwar
magana wadda sai an yi tonon silili da taliyo. Tana kuma zama gajeruwar magana
kamar a ce, wanda ake bi bashi ya tabbatar da ana bin sa, kuma yana da abin
biya, sai biya kawai, maganar ta zama gajera.
Sifofin
Magana:
Duk da yake magana ba a ganin ta, jin ta ake yi, a wajen
Bahaushe tana da sifa ko sifofi. A tunain Bahaushe akwai, Baƙar magana da maganar arziki. Duk wata magana da ba ta arziki ba, baƙar magana ce don haka idan aka yi masa ita yakan ce: “Barka da ta fito
bakin mai ita ba ta kashe shi ba”. Bakar magana maganar jin haushi ce da
takaici da jiyewa mai mugun zafi ga rayuwar wanda aka yi wa ita. Malamin kiɗi Narambaɗa na cewa:
Jagora: Baƙar magana ba ɓaci ce ba
Yara : Amma
ta ɗara, ɓaci zahi
Gindi : Gogarman Tudu jikan Sanda
: Maza
su ji tsoron ɗan mai Hausa.
Maganar arziki sananniya ce, irinta ce wadda Garugaru ya yi
wa Kassu Zurmi yana cewa:
Jagora: Maganar garugaru tai mani daɗi,
: Tamkar
na dama zuma na sha.
A ganin Bahaushe, kowace magana mai daɗi maganar arziki
ce, wadda duk ba ta da daɗi bakar magana ce.
Hukuncin
Magana:
A al’adance, ana hukunta magana ta fuskar nahawun ma’anarta.
Kai tsaye za a ce: Wannan maganar daidai ce, kure ce, gaskiya ce, ƙarya ce, ba’a ce, raki ce, saiɓi ce, ga su nan dai. A nahawun waɗannan zantukan za
mu yi musu turke da waɗannan sassan adabi:
Daidai: Ɗan’anace na
cewa:
Jagora: Mai son miya ya auri
tsohuwa
: Mai son shimfiɗa ya auri budurwa
: Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
(Waƙar Shago)
Wa zai ji wannan ya ce ba
daidai ba ne.
Kure: “Muna cikin
tuwo muna cin zaure ko da an ka yi kura ga
walƙiya tsugunne”. Babu gaɓar da babu kure a wannan maganar.
Gaskiya: Narambaɗa ya kawo bayaninta da yake cewa:
Jagora: Na hore ki gaskiya
bari tsoron ƙarya
Yara : Mai ƙarya
munafuki Allah su yaƙ ƙi
: Har yau ba mu ga in da an ka yi mai ƙarya ba.
Jagora/Yara : Amma
ita gaskiya gari da mutane tay yi
Gindi : Gwarzon Shamaki na
Malam toron giwa,
: Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Ba’a: Magana da za a yi don
raha da nishaɗi,
kowa ya ji ta ya san ba’a ce, ba da gaske ake ba. Tsawon hancin Bazaurar da
Sani Ɗanbolɗo
ya so ya aura ya ce:
Jagora: Ya kai mil goma misalin dogon hanci.
(Waƙar Zaura: Sani Ɗanbolɗo).
Idan hancin ya yi mil goma, yaya misalin tsawon ƙafa da hannu da faɗin kai da tsawon wuya? Wa zai gan ta ya tsaya zancen aure?
Tun da cikin waƙa maganar ta fito Bahaushe zai ce: “Kai wannan mutum da ba’a
yake”.
Raki: Magana
ce da ake yi cikin tsananin sumalin zafin rauni ko wani bone da aka faɗa a ciki. Dubi
yadda Bakwai ya yi da kunama ta harbe shi in ji Garba Maitandu Shinkafi:
Jagora: Yay yi kwance yac ce: “Yo, na mace”
: Ku
ba ni ruwa in mace ga sanyi ga maƙoshi
: Danginai
sun ka ce: “Mun ɗaukai mu aza shi
: Nan
ga jakinmu mu kai gida”
: Yac
ce: “In kun aza ni, to ita wannan ƙafar
: Ina
mai ɗauka muku”?
: Ni kun san ba ni son tana
reto
: Ba ni son ta sha hantsi
: Na hi son ku ruga ku biɗo gado
: To kuma in na mace
: Ku kaɗa ni cikin haki
: Da kaina da ƙafafu da baina ciwo sukai
: Kunama ta sa ni dumdumi Ala
ebe mata,
: Ni ko nac ce: Bakwai ka bar
zagi
: Tun da in kana zagi ba ta
faɗuwa sai ciwo take
: Bakwai yac ce: “Nai shiru
rufa kat ta jiya
: Tana cikin ɗaki ban kashe ba
: Ka san in taj jiya kare in
kai ma kiɗi.
Gindi : Kunama
zan wa kiɗi
: Zaman
ciwo ag gare ta
: Ta
halban na jiya
Waɗannan kalamai masu kama da na fitar hankali da aka yi saboda
raɗaɗi da zagin ciwo su
ake cewa “raki”. Duk wata magana irinta sunanta raki.
Saiɓi/Santi: Magana
ce wadda ke fita a bakin wanda matsananciyar
yunwa ta kama, yana cikin juyayi aka gabato masa da abinci
mai kyau mai daɗi irin wanda ransa ke so. An ce, wani Bafulatani ya sha furar
shinkafa mai zuma a garin Maradun, yana cikin sha sai ya tuno da wani ɗan waƙa cikin waƙoƙin Shata ya ɗora hannu a kunne ya rera.
Ɗanfulani : Kaka ta yi uban zimma
: Gyara ta fara zar fata!
Zamfarawa : Haji Garban Bici yai damu.
Azancin
Magana:
Fagen ƙididdige azancin magana nan sirrin nahawunta yake. Cikin azancinta
za a ci karo da: Kairn Magana, Salon Magana, Kirari, Daɗin Baki, Waƙa, Zantukan hikima, da sauransu. A nan ce zuciyar nahawun magana yake,
domin nan ne za a fito da nahawun azancinta duka.
Karin Magana:
Zantukan hikima ne da aka gada kaka da kakanni. Jimla ce
gajeruwa mai ɗauke
da ma’ana mai faɗi:
Magana zarar bunu
Maganar duniya iyawa ce,
Magana ba taka ba bi ta da ihm!
Wata magana sarakuwa baki ce
Baki abin magana
Magana daga bakin wawa.
Salon Magana:
Maganganu ne na nuna ƙwarewa ga harshe da
iya sarrafa shi. Ga ɗan misali:
Da Kalla da abokin Kalla sun tafi kallon kalangu, sai aka
kalle Kalla mari wajen kallon kalangu, sai aka ce wa abokin Kalla maza kalla
gida da gudu ka gaya wa matar Kalla ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon
kalangu. Ya kalla da gudu, ya kalla wa matar Kalla kira cewa, ga Kalla can an
kalle da mari wajen kallon kalangu. Ta kallo kara, da gudu domin ta kalla wa
wanda ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu. Da ganin ta da kallallen
kara ya kalla da gudu don kat ta kalla masa shi da ya kalla wa Kalla mari wajen
kallon kalangu.
Kirari: Magana ce da aka tsara cikin tsayayyun kalmomi masu shiga
zuci da kururuta wanda ake yi wa shi ko babu kiɗa ya tsimu. Ga yadda makaɗa Ɗan’anace ya koɗa Shago:
: Kutuɓi abin aza wa ruhewa
: Samji irin hakin da ka
ramno
: Burundumi abin zuba shara
: Yaro hattaraka ga sababi
nan
: Ka da aradu ta farma
: Halan dai ba ka san halin ƙanen ajali ba?
: Laapirwaa! Akai miki gawwa!
: Sanu da ɗibas sheɗa
: Mutuwa ke daɗe kina kashe bayi
: To, to, to!------
Duk Bahaushe ya ji saukan amon waɗannan kalmomi zai
ce, an zuga Shago ko ya ce: “Wannan kirari ya yi”. Hawa da saukan kalmomin
kirari ba irin na yabo ne ba ko roƙo ko waƙa. A ko’ina aka ji zugugutawa da cicciɓawa ta yi yawa za a ce kirari ne aka yi.
Zantuka
Hikimomi/Waƙa/Daɗin Baki: Waɗannan duk nau’o’i
ne na magana kuma duk sai sun bayyana a cikin waƙa za a ce, ta waƙu, ko ta yi daɗi. Azanci da hikima da daɗin baki su ne waƙa. wani mawaƙin tashe na cewa:
Jagora: Sai dai a fi mu kalangu da kurkutu
Yara : Amma
ba a fin mu daɗin baki,
Gindi : Yau da borin goje,
: Kana
da borin tashe.
(Ayya Mai Waƙar Tashe Taƙaji).
Maganar Zuci
da Nahawunta:
Maganar zuci ita ce maganar da ke cikin ƙirjin mai ita, amma ta kasa ta bayyana saboda wani hali da aka shiga ciki
ko wani yanayi da aka samu kai a ciki. Garba Ɗanwasa Gummi ya
hikayo maganar zuci wurin da yake nuna bala’i ya kai ga sarki ya fito ba naɗi, a bar gari ba
shiri, ba a san ina aka dosa ba. A cikin wannan hali ya ce:
Jagora: Maigida bai kula mata ba
: Rannan
ko da ana ɗumi sai maganar zuci.
Gindi : Ya san ‘yan maza gudu ba da laɓewa ba…
Idan ana cikin wannan hali wasulan da ke sa a daidaita
nahawun maganar zuci su ne: tsaki, nishi, kuwwa, ajiyar zuciya, kuka, dariya….
Sakamakon
Nazari:
A tunanin Bahaushe ma’anar magana ya fi zare tsawo. Duk abin
da baki ke furtawa a fahimce shi, ya zama magana. Hanyoyin da ake bi na nuna
duk suna cikin nahawun magana amma maganar da ake furci da baki ita ce maganar
da nahawunta ba ɓoye yake ba ga manazarta. A fagen nazari, matuƙar ana son a fayayce magana, kalmomin da ke cikinta, da yanayin da aka
furta ta, da mai furucinta, ba su ne nahawunta ba. Nahawunta na nan cikin
sunanta daga cikin ire-iren sunayenta da za ta ɗauka, da nauyinta a sikelin nahawun al’adar magana, da
sifarta ga yadda ma’anar ta zai ɗauka, tilas a fayayce hukunce-hukuncen da za ta hau in ana
son a yanke mata hukunci. Magana tana ƙunshe da azanci mai
yawa, a nan za a yanke mata hukunci kasancewarta waƙa ko wata taska daga cikin taskokin adabin baka. Duk waɗannan abubuwa suna
rataye ga maganar da aka furta, maganar da ba a furta ba, ita ce maganar zuci
‘yan rakiyata su ne tsaki, ƙyaci, nishi, kuka da sauransu. Yana da kyau kowace magana aka
tunkara a bincike a san ina gurbinta.
Naɗewa:
Da gangan na yi wa takardata taken: “Nahawun Magana” domin na
san kowace magana da muhallinta shi ne nahawunta kuma da shi za a yi mata hukunci.
Ba a ɗauko zancen waƙa a salon kambamar zulaƙe a ce, ƙarya ce aka shara domin muhallin waƙa muhallin ba’a ne da raha. Da jin maganar Santi ba irin ta raki ba ce.
Idan ɗalibin bincike zai
ci karo da kowane irin magana a fagen nazari ya tabbata ya aza ta a kan
gurbinta wanda shi ne nahawunta gabanin ya feɗe ta biri har wutsiya. Sanin nahawun magana shi zai sa mai
magana ya lura da maganar da ake so da wadda ba a so. Kasawar sanin nahawun
magana alamun taɓuwar hankali ce, in ji Malamin waƙa Narambaɗa,
domin ya ce:
Jagora: Kai magana an ce maka tsaya
: Ka sake an ce maka bari
Yara: Kai magana ka san ba a son ta
J/Y : Ka ƙi bari waz
zan mahaukaci?
Gindi: Ya ci maza ya kwan yana shire
: Gamda’anan sarkin Tudu Alu.
MANAZARTA
Bunza, Aliyu
Muhammad, 2002. Yaƙi da Rashin Tarbiya, Lalacignnb
nb ,
Cin Hanci da Karɓar Rashawa cikin Waƙoƙin Sambo Wali
Basakkwace, Lagos: Ibrash Publishers.
Bunza, Aliyu
Muhammad, 2002. Narambaɗa, Lagos: Ibrash Islamic
Publicaiton Centre.
Bunza, Aliyu
Muhammad, 2017. “Raaki a Tunanin Bahaushe”,
Takardar da aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Gusau: Jami’ar
Tarayya.
Furniss, Graham,
1996. Poetry, Prose and Popular Culture
in Hausa,
London: Edinburgh University Press, for International Africna Institute.
Gusau, Sa’idu
Muhammad. 2009. Diwanin Waƙoƙin Baka:
Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Kano: century Research and Publishing Limited.
Mukhtar, Isa. 1984.
“Nahawun Waƙa”, Kundin
MA, Kano, Jami;ar
Bayero.
Shinkafi Rabi’u
Hassan. 2001. “Garba Maitandu da Waƙoƙinsa”.
Kundin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahaya, Ibrahim
Yaro. 1988. Hausa A Rubuce: Tarihin
Rubuce-
Rubuce Cikin
Harshen Hausa, Zariya: NNPC.
No comments:
Post a Comment