Tunanin
Bahaushe na faɗar Allah ɗaya gari
bamban, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Dadaɗɗen tarihin ƙasar Hausa
sassarƙe yake da ƙurar yaƙi da gaba da
bauta tun gabanin wata duniya ta kutso cikin duniyar ƙasar Hausa.
Bayan an yi kare jini biri jini, aka rabu dutsi a hannun riga, sai tunanin a
share jini a koma wasa ya haɗu da tunanin faɗan da ya fi ƙarfinka ka
mayar da shi wasa, suka hamɓare gwannatin, kar! Ta san kar!, suka kafa
sabuwar daular zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Yadda Bahaushe ya yi
amfani da wasannin barkwanci wajen kashe wutar gaba da ƙiyayya da yaƙe-yaƙen jahiliyya
suka haifar abin a zo a gani a yi nazari ne. Dabarar mayar da dariya da tashin
hankali taubasan juna, Bahaushe ya fara kaɗaita da ita, da fice da ita a
duniyar baƙar fata. Cikin halin da ƙasarmu take
ciki a yau, Hausawa suka fi kowace al’umma….
Labarin Zuciya A
Tambayi Fuska: (Saƙon Dariya Ga Sasanta Tsaro A Farfajiyar Karatun Hausa)
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
Waya: 0803 431
6508
Takardar da aka gabatar a Bukukuwan Makon Hausa na
shekarar 2015 na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa
‘Yar’adwa, Katsina, ranar Litinin 15/06/2015 a Babban Ɗakin
Taro na Jami’ar.
Gabatarwa:
Tunanin
Bahaushe na faɗar Allah ɗaya gari
bamban, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Dadaɗɗen tarihin ƙasar Hausa
sassarƙe yake da ƙurar yaƙi da gaba da
bauta tun gabanin wata duniya ta kutso cikin duniyar ƙasar Hausa.
Bayan an yi kare jini biri jini, aka rabu dutsi a hannun riga, sai tunanin a
share jini a koma wasa ya haɗu da tunanin faɗan da ya fi ƙarfinka ka
mayar da shi wasa, suka hamɓare gwannatin, kar! Ta san kar!, suka kafa
sabuwar daular zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Yadda Bahaushe ya yi
amfani da wasannin barkwanci wajen kashe wutar gaba da ƙiyayya da yaƙe-yaƙen jahiliyya
suka haifar abin a zo a gani a yi nazari ne. Dabarar mayar da dariya da tashin
hankali taubasan juna, Bahaushe ya fara kaɗaita da ita, da fice da ita a
duniyar baƙar fata. Cikin halin da ƙasarmu take
ciki a yau, Hausawa suka fi kowace al’umma cancanta ga ba da misalin yadda za a
sallami tashin hankali, ba tare da ya yi halinsa na tayar wa kowa hankali ba.
Bisa ga wannan ƙuduri na sa wa takardarmu take: Labarin Zuciya a
Tambayi Fuska. Da fatar za ku ba ni aron zukatanku in labarta muku abubuwan na
na ƙunso,
mu ga yadda fuskokinku za su ba da labarin abubuwan da aka ɗuɗɗura musu.
Warware
Matashiya:
Karin maganganun Hausawa wata babbar
makaranta ce, babu ɗalibin da
zai ce, “Yau ya sauke karatunta” sai dai a dangane allo, in an kai walan
waladaina walan malam na ƙiya. Labari kalmar Larabci ce daga khabar al-akhbar asalin ma’anarsa a
Hausa ita ce, sabuwar magana ko ƙaramar
magana ko babbar magana ko tsegumi ko tsince ko jita-jita ko yaye-yayen maganganu.
Duk waɗannan na iya
fassara “labari” a Hausa. Duk da haka, abubuwan da suka ƙunshi tarihi
da karatu, magabata na yi musu bugun goro da sunan “kunne ya girmi kaka”.
Zuciya kuwa wata babbar tsoka ce daga cikin tsokokin kayan cikin mutum da
Bahaushe ke ganin ita ce taskar kowane irin tunaninsa da halayensa da
ayyukansa. Fuska wani madubin tantance ɗan Adam ce da ta haɗa da baki da
hanci da idanu da goshi da gemu. A ko’ina aka tunkari mutum, fuskarsa ce a bar
tabbatar da shi, da ita ake rarrabe shi da waninsa, ita ke sa ya yi kama da wani, kuma da ita ake fahintar,
kama da wane ba wane ba ne.
A al’adance, ana son fuska ta kasance
sakakkiya shimfiɗaɗɗiya domin
masana cewa suka yi, “Shimfiɗar fuska ya fi shimfiɗar tabarma.
Ba a son fuska da duhu-duhu irin ta majiyi yunwa don haka Bahaushe ke cewa:
“Annurin fuska kaurin hanji”. Ba a son a gan ta nugu-nugu wanda zai ba da
fassarar talallaɓiyar kashi
ba a faɗi ba rai ya ɓaci.
Abubuwan da ke sosa rai suna sa fuska baƙi (a
al’adance) komai farin jikin mai ita, wanda shi ne musabbabin zancen Bahaushe
na cewa; ya sha toka, ko ya sha mur, ko ya yi fuskar shanu domin maraƙi da ya ƙoshi, da
yana cikin jin yunwa, duk ba a iya rarrabewa a fuskarsa. Na yarda da kirari sanƙiran Gambo
zuwa ga Muhammadu Inuwa Ɗan’maɗacci da yake cewa:
Baƙi ƙirin ɓarin mai
toka
Sa ba ka dariya sai tuni
Kowa yag ga dariyar sa ya mutu.
Ma’abota hankali da sun ga waɗanda suka
sani da fara’a, fuska turnuƙe, sukan ce, “wane lafiya? Me
ke faruwa?” Haka kuma, idan an ga maƙetaci na yaƙar dariya
akan tuhumi masiba ta auka wa wani ko wasu. Ire-iren mutanen nan ne da Bahaushe
ke cewa: “Mugu ba ka dariya sai ta ɓaci”. A kan kowane hali, yamutse
fuska irin ta ‘yan kuwwar gobara, da dabirta ta, kamar wanda aka koro abin
zargi ne. Ba a son ta kasance tsaroro irin ta ‘yan tatsar hanji. Idan ta fi ta
Nufawa da Kutumbawa kauri ana yi mata zaton artabu. Da mai tambaya zai yi
tambaya cewa: Me ke sa a kasa gano makarin mutum? Bayani shi ne, fuskarsa. Me
ke sa a fahinci manufarsa? Fuskarsa. Me ke sa a samu tabbacin amincewarsa da
yardarsa da ganewarsa? Murmushinsa ko dariyarsa. Waɗannan
abubuwa biyu “murmushi” da “dariya” gaɓɓan da ke bayyanar da su a fuska suke
liƙe.
Don haka, muna da damar mu ce, lallai tunanin Bahaushe na labarin zuciya a
tambayi fuska ba shege ba ne da ubansa.
Ƙasar Hausa da Daulolinta:
Idan an ce ƙasar Hausa,
wata irin wagegiyar farfajiya ce da za a iya cewa, daji ba ka da gambu. A taƙaice, za mu
ce, ƙasar Hausa ita ce:
Farfajiyar
da Hausawan asali suka yanke cibi. Makekiyar ƙasar da
Hausawa suka mamaye su kaɗai, a nan
ciki kakanin kakaninsu suka tsira. Nan suka sami kansu, a nan aka same su. Ba
su san wata ƙasa ba sai ita. Ba a san su a ko’ina ba, sai a
nan. Ba su yi tarayyarta da kowa ba. Ba ga kowa suka karɓe ta ba,
kuma babu wanda ya yi musu masauki a cikinta. Da ita suka tinƙaho, domin
ba su san ko’ina ba baya ta. Da ita ake yi musu suna da garuruwansu da
daulolinsu da zuriyarsu da addinansu da al’adunsu. A doronta suka kakkafa
mazauninsu na din-din-din mannanu ƙuda ya faɗa ƙwarya alewa.
A taƙaice bayani,
wannan ita ce ƙasar Hausa. A fashin baƙinta, ta ƙunshi
dauloli irin su Kano da Zazzau da Katsina da Zamfara da Gobir da Kabi da
farfajiyar Maraɗi da Filinge
da Dogon Dutsi, da dai makamantansu. A tarihi, a duniyar baƙar fata, babu
ƙabilar
da ta kai Hausawa dauloli girkakku. Haka kuma, babu ƙabilar da ta
zarce ta faɗin
farfajiyar mazauni. Ba a ce ta fi kowace ƙasa dausayi
ba, amma a jigawar ƙasa, da karkarar kowace al’umma tana gwada
tsawo. A awon yawan jama’a, ko ba a gwada ba, linzami ya fi bakin kaza. A fagen
karɓar baƙi, da yi
musu shimfiɗar fuska, a
duniyar baƙar fata, ba sai Bahaushe ya yi kirari ba, ai ko
ba a faɗi ba, sunan
mijin iya baba. Idan ana zance harshe mai yaɗo da bunƙasa da
barbazuwa duniya kamar iskan hunturu, da an ce, “Hausa” dole a ji shiru mai kiɗin kalangu
ya faɗa rijiya!
Nagarta da basira da wayo da kazar-kazar sai mu yi na babban mahaukaci mu ce, a
ko’ina Bahaushe ya miƙe tsaye ko bai ce uffan ba, an san biri ya yi
kama da mutum. Wannan martaba ta sa, a halin yanzu, babu ƙasar da ta
kai ƙasar Hausa cika da mutane mabambanta a duniya.
Haka kuma, shi ya haifar da ƙyashi da kushewa ga magabta,
aka dinga kai mata hare-haren yaƙi. Bugu da ƙari,
albarkatunta ya jawo mata yaƙin basasa na cikin gida, tsakanin
sarakunanta kowa na ƙoƙarin ya ƙara yawan ƙasarsa
arzikinsa ya ƙaru.
Idna za mu kalli hoton ƙasar Hausa
sosai cikin taswirar ƙasashen duniya, za mu ga cewa, kwararowar
Larabawa Musulmai da Ƙibɗawa da Turawan Mishon da ‘yan mulkin
mallaka da Wangarawa da Fulani da wasu ƙananan ƙabilu
fassarar sa ita ce, da walakin goro cikin miya. Lalle, dole da dalili ƙuda a warki.
Ba a bin mamaki ba ne har yau, martabar ƙasar na nan
yadda aka san shi, domin basira da hikimar magabata ta shafe mu, ko ba mu yi
kamar su ba, za a ce, ai ɗan gafiya ko
bai yi sata ba yana dogon aro. Kai! Tilas a jinjina wa makaɗa Narambaɗa a faɗarsa:
Jagora: Ɗan bajini
shi ka zama bajini
:
Yai bobakali yai tozo
Yara :
Ɗan
akuya na kallo!
Gindi : Na yaba ka da girma
Audu ƙanen mai
daga
:
Kan da mu san kowa
:
Kai mun ka sani Sardauna.
Zaman ‘Yan
Marina:
Ga alama, zaman ‘yan marina shi ne
kowa da wurin da ya fuskanta ga abin da yake yi. Daulolin ƙasar Hausa
sun yi zama irin wannan saboda adawar yaƙe-yaƙe da ta
gabata. Al’ummomin da ke cikinsu ana iya rarrabe su da sunayensu da al’adunsu
da kirare-kirarensu. Idan muka nazarce su sosai, za mu gano dalilan da suka
haifar da yaƙe-yaƙe da dalilan
da suka haifar da sulhu aka zama abu ɗaya. Ga tsarin zuriyar Bahaushe:
Bakano, Bahaɗeje, Bakatsine,
Bazazzage, Bazamfare, Bagobiri, Bakabe, Bagimbane, Ba’are, Bagube, Badaure,
Bamaraɗe, ga su nan
dai. Waɗannan
kowannensu da karin harshensa, da tsagarsa ta gado da sunan sarautarsa da sunan
ƙasarsu
da tsarin wasanninsu da yanayin abincinsu da tarihin kakaninsu mabambanta da
al’adun matakan rayuwarsu (aure da haihuwa da mutuwa) da bukukuwansu da
magungunansu na gargajiya, da tsarin yadda suke raɗa sunayensu.
Idan muka kalli waɗannan
abubuwa da idon karatu, a ko’ina suka bayyana, dole a samu saɓanin
fahimta. Da zarar saɓani ya
bayyana, tankiya dole ta shiga, daga nan, zai zare damuttsa da takubba da
gaturra da kibau da masu na ɗebe raini da huce haushin juna. A tarihin
duniya, babu al’ummar da ba ta ratsi irin wannan jahiliyya ba, don haka
Bahaushe ba shi ne farau ba, shege kowa ya yi, ɗan karuwa na faɗa da jikan
kwarto.
A wajen ƙasa, Kanawa
sun zuba da Jukunawa. Zage-zagi sun zunguri Gwarawa. Katsinawa ba su raga wa
Nufawa hakin susa ba. Kabawa sun yi adashin kibau da masu da Fulani. Fulanin ƙasar Hausa
sun fafata da daular Borno. Zamfara da Dakarkari sun yi luguden kulake da
gaturra. Gobirawa da su da mutuwa ɗan gwaggo da ɗan kawu ne,
takubbansu ba su taɓa tsatsa
cikin kube ba, don haka yawan yaƙe-yaƙensu sai dai
abin da kunne ya ji. Waɗannan yaƙe-yaƙe da zuriyar
Hausawa suka yi da ƙabilu maƙwabta da na
nesa, shi ya sa ƙasar Hausa take zaman ‘yan marina da maƙwabtanta
domin gudun a yi mata girshi. Wataƙila irin
haka ce Aliyu Ɗandawo ke yi wa daular Kabi hasashe a
bakandamiyarsa ta yaƙi da yake cewa:
Jagora: Bayan shekara dubu biyu
:
Sannan Nabane yab bayyana
:
Yag gagari Hillani
:
Yaf fanshi Kabawa
:
Da ruwan kibau da masu
:
Ko sun yi ƙulle-ƙullensu
:
Ina ruwan sadauki
:
Ka dai buwaya ka gagara
:
Ko bindiga an tanka ƙari bai tosai.
Gindi: Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai
Sudani
: Ila marin rugga
: Ɗan Yakubu sa
gurfani!
Tirƙashi! Ruwa
na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba. Idan ba a sa tulun ruwan tobassaka ba aka yayyafa wa
turruƙun hayaƙin da makaɗa Aliyu Ɗandawo ya
turara a zukatan Kabawa ba, kuna ganin kasuwar Ambursa na sake cika? To! Waɗannan miyaku
muke son mu rego yadda magabata suka sa musu bandeji aka ɗaɗɗaure su har
suka warke aka wayi gari yau, takubban yaƙi suka koma
gidan tarihi, ana regonsu, ana nunin su, ba tare da tunanin rataya su ba.
A Share Jini
A Koma Wasa:
A tarihin ƙasashenmu ƙananan yaƙe-yaƙen da aka
sha gwabzawa sai dai abin da aka ji amma ba sa lisafuwa. Idan aka dubi irin
darzajen da Kabawa suka yi ƙarƙashin Sarki
Kanta dole a kame baki. Kaɗan daga ciki, Daular Kabi hannun rigarta na yaƙi ya kai har
Nguru a daular Borno. Ƙafan wandonta na kokuwa da mazaje ya tokare
Daular Oyo, ta tsohuwar Daular Oyo.
Tsinin kibau na masunta sun ratsa Dahomy sun ziyarci Agadas har Air. Hurjin
Mussan Kabi bai bar Nufawa ba, domin har sa su yaɓi da man kaɗe aka yi a
birnin Surame. Sarki Kabi Sama kaɗai garuruwan Filani tis’in da tara
(99) ya ci da yaƙi. Kanawa sun ɗauko sarkin yaƙi Ɗanwaire
Marin Dawa sun ci garuruwa da dama. Gwandu ta ɗauko hayar Garba Gande
(Janborodo) domin ya yi mata gambun yaƙi a Ambursa.
Yaƙe-yaƙen ƙasashenmu su
suka karantar da mu cewa, dole a share jini a koma wasa. A yau kamar ba a yi
ba, domin:
Kanawa sun zama abokan wasan
Zazzagawa
Kabawa su ne manyan tobassan Fulani
Gobir, da Fulani da Yarbawa da
Katsinawa nata ne.
Katsinawa, da Kabawa da Nufawa
tobassansu ne.
Gimbamawa da arawa sai lalewa
Katsinawa da Dakarkari ‘yan’uwan
juna ne.
Bazamfare da Badakkare an zama ɗan gwaggo da
ɗan kawu.
A taƙaice, masana
al’ada na ganin yaƙe-yaƙen da
al’ummomin ƙasar Hausa suka yi da wasu ƙasashe da
kuma tsakaninsu, su suka haifar da wasannin da ke gudana a yau. An riga an
fahinci juna, an gama jiki kowa ya san wurin da wani ya kwana. Da wanda ya yi
rinjaye, da wanda aka rinjaya, kowa ya miƙa wa zaman
lafiya wuya, an riga an karce majinar da ta toshe zuciya, fuskoki sun waye, an
shimfiɗa su ga juna
sai ‘yan habaice-habaice da ke iya kai da kawo. A shekarar da aka je tarbon
sarauniya Kaduna makaɗa Aliyu Ɗandawo ya
san, sai an ratsi ƙasar Sakkwato, ya ko san irin artabun ƙarshe da aka
yi da Sanyinnawa bayan tamburan yaƙin Fulani da
aka karɓe a fagen
gumuzu. Don haka yake cewa Sarkin Kabi Mamman Shehe:
Jagora: In tahiya ta kama
:
Ka sa a shirya dawaki
:
A ɗaura damman
masu
:
Ko suna taya fansa
:
Ka tabbata ma maza
:
Ba a girsuwan mai ƙarfi
:
Ka dai gagara (ka buwaya)
:
Don mai da hwaɗi ɓanna na
:
Shugaban tahiya sarkin Kabi mai Sudani
:
Ila marin rugga,
:
Ɗan
Yakubu sa gurhwani.
Me ya sa makaɗa ya ce:
“Mai da hwaɗi ɓauna na”?
Domin an riga an share jini don haka, sai a koma wasa kawai. Kowa ya san ƙarfin kowa,
a ba zaman lafiya dama ya ci gaba da wanzuwa a ƙasa. Haka ko
aka yi, yau auratayya da kasuwanci da addini da hulɗa da
zamantakewa sun kore dukkanin waɗannan abubuwa da ke yi muna barazana
mun zama abu ɗaya.
Wasa Da
Dariya Ga Bahaushe:
Ba al’ummar duniya da ba a wasa.
Babu al’ummar duniya da ba a dariya da kuka da murmushi da shewa da kuwwa da guɗa da kirari.
Duk da haka, dariya ta fi amo sosai a tsarin zaman lafiyar al’umma. A koyaushe,
a maganganun yau da gobe, akan haɗa kalmomi biyu “wasa’ da “dariya” su
ba da kalmomi biyu masu zaman kansu, amma masu ma’ana ɗaya. A
al’adance, ko’ina aka ga wasa, ana sa ran jin zarmoɗan dariya. A
kowane lokaci aka ga fuska ta kece da dariya, to wasa a aikace ko a lafazance ta
gabace ta. Kalmar “wasa” takan ɗauki ma’anoni da dama irin su:
i)
Wasa
da gaɓɓan jiki
domin samar da raha da wartsakewa.
ii)
Maganganun
raha na motsar da annashawa da tuna baya.
iii)
Wasu
ayyukan al’ada na burgewa da samar da raha.
iv)
Wasannin
gargajiya da al’ada ta katangance da sunan “wasa”.
v)
Yunƙurin yin
wani abu, ba haƙiƙaninsa ba,
ko ba da gaske ba.
vi)
Ƙirƙirarrun
labarai, ƙagaggun na kunne ya grimi kaka.
vii)
Dabarun
fitar da kai cikin tukunya idan ruwa sun ci gwani.
A ɓangaren dariya akwai abubuwan
ambato da yawa. A ilmance, a ƙarninmu ita kaɗai ke da ƙungiya ɗaya a
duniya, “ƙungiyar Dariya ta Duniya”. Har yanzu, ba mu ji ƙungiyar kuka
ko gudu ko kuwwa ko shewa ko guɗa ko gwalo ko jinini ta duniya ba. A al’adance,
dariya wata makaranta ce ta zuzzurfan karatun:
i) Zuciyar mai aiwatar da ita
ii) Halin da mai yin ta yake ciki
iii) Shafin da mai yin ta ya buɗa daga cikin
shafukanta (14).
iɓ) Abubuwan da mai ita ya hango gabanin ya yi
ta.
ɓ) Yadda yake cin ta, wani rukuni ne daga
rukunan dalilanta.
ɓi) Da ta bayyana fara’a da bushara sun
tabbata, a mabayyanin zance
ɓii) Ba su taɓa haɗa hanya da kuka ba, kuma ba
su taɓa yada zango
ɗaya ba.
Fashin Baƙin
Dariyar Bahaushe:
Ba Bahaushe kaɗai ke dariya
ba, amma kuma yana daga cikin al’ummomin da ke ganin da ita ake gyaran zama na
baya a walle. Sanin wahalhalun da ke cikin yaƙe-yaƙe da musibun
da suka haifar da bi-ta-da-ƙullin da zai biyo bayan su.
Bahaushe a kowace ƙasa ya kafa daularsa, ta kowace irin fuska
gwannatinsa ta kafu, yana da manyan ma’aikatun da za su kula masa da walwala,
irin ta sakewa, da wanzar da raha, dariya ta baje kolinta a bakunan mazauna ƙasarsa. Daga
cikin martabobin dariya ga masana halayyar ɗan Adam a al’adance, akwai:
i)
Duk
wani baƙin ciki ake
ciki da ta bayyana ya kau.
ii)
Duk
wata fargaba da ake ji, da an gan ta an samu natsuwa.
iii)
Komai
tsauri tsananin mutum, da ta bayyana a fuskarsa, an samu makama gare shi.
iv)
Ba
a taɓa yin ta
cikin tashin hankali ba, sai nasuwa ta wanzu za ta bayyana.
v)
Bayan
ɗan Adam, babu
wata halitta mai rai da ke dariya.
vi)
Husuma,
faɗa, yaƙi, artabu,
zanga-zanga da fito-na-fito da taho-mu-gama cikin fuskar shanu ake kwasar
adashinsu, da dariya ta gitta sun tsinke, sai zancen sasantawa.
vii)
Ɗaurewa a ƙi yin ta
da’iman rauni ne ga hankali, dogewa da ita juddadun alamar taɓuwar hankali
ce.
Ganin irin waɗannan
martabobi ya sa Bahaushe ya keɓe babbar farfajiya domin raha da dariya a
adabinsa. A adabi da al’adar Bahaushe akwai:
1.
Makaɗan Ban
dariya
i)
‘Yan
kama
ii)
‘Yan
zari
iii)
‘Yan
kacakaura
iv)
‘Yan
gambara
2.
Wasannin
Barkwanci Tsakanin ƙabilu
3.
Wasannin
Barkwanci Tsakanin masu sana’a
4.
Wasannin
Barkwanci na zumuntar jini
5.
Wasannin
Barkwanci na Takwara
6.
Wasannin
Barkwanci na Jinsi
7.
Wasannin
Barkwanci na Ƙirar Halitta
8.
Wasannin
Barkwanci na Naƙasassu
9.
Wasannin
Barkwanci na dabbobi da tsuntsaye da ƙwari
10.
Wasannin
Barkwanci Tsakanin Al’ummomi
11.
Wasannin
Barkwanci Tsakanin ƙauyawa da ‘yan Birni
12.
Wasannin
Barkwanci Tsakanin Zuriyar Bahaushe
13.
Wasannin
Tashe
14.
Wasannin
zamantakewa
15.
Wasan
Bashirwa
Kowane rukuni muka shiga cikin waɗannan rukuna
za mu ga babban fage ne abin nazari. Haka kuma, za mu taras da babban jigonsa
shi ne wanzar da raha a zukatan ‘yan kallo da masu sauraro. Da raha ta ratsi
zuciya, babbann masaukinta a fuska shi ne gangar baki, babban kogon da dariya ke
haramta wa kowane irin abu shigansa idan ta baje kolinta a ciki. Idan muka
nazarci waɗannan
rukunan wasanni za mu ga, daga cikin adabin Bahaushe, dariya ke da kaso mai
rinjaye. Yaƙi da faɗa da gaba wasu lalurori ne da
yanayin zamantakewa kan haifarwa, ba su da wani babban gurbi daga cikin gurabun
tsaftatacciyar rayuwa. Idan cilas ta haddasa su, sai a ziyarci ɗaya ko biyu
(ko fiye) daga cikin waɗannan rukuna
a tunkare su a murƙushe su gabanin su tashi. Idan sun riga sun
tashi, a yi amfani da su a yayyafa musu ruwa a kashe lagonsu. Idan an riga an
gwabza sai su biyo baya da lallashin zukata na a share jini a koma wasa.
Ƙunshiyar Karatun Dariya:
Dariya babbar makaranta ce mai suna:
“Da Wasa Ake Gaya Wa Wawa Gaskiya”. A koyaushe aka buɗe
littattafanta ana karatu, fuskokin masu karatu, da ɗaliban
ilminta, za su ba da labarin abin da ake ciki. Idan baƙon
makarantar ya zo bai san abin da ake ciki ba, ya tambayi karatun aka gaya masa
shi ma dole ya dara. Daga cikin manyan darusan da ke ƙunshe cikin
dariya akwai:
1.
Tarihin
tuna baya
2.
Kyautata
zamantakewa
3.
Tattalin
arziki
4.
Zaman
lafiya da lumana
5.
Taskace
al’adu nagartattu
6.
Kakkaɓe ƙurar gaba da
takaici da ƙiyayya a zukata
7.
Karatun
duniyar mutane da fahintar junansu
8.
Danƙon sada
zumunci
9.
Fahintar
addini/addinai
10.
Kyautata
tarbiya
11.
Kiyon
lafiya
12.
Inganta
siyasar duniya
13.
Yalwata
harshe da ɗaukaka shi
da inganta shi
14.
Dabarun
yaƙi
da dabarun tsagaita/tsakaita wuta.
15.
Kimiyyar
ƙere-ƙere
16.
Sanin
makamar aiki
17.
Fahintar
dokoki da hukunce-hukunce
18.
Dabarun
tsaro
19.
Sanin
kai da sanin yakamata
20.
Tsaron
hankali da mutunci
Abin da ake son mai karatu ya kula
shi ne, cikin kowace dariya akwai darasi ga wanda ya yi ta, da wanda aka sa ya
yi, da abin da ya sa aka yi dariya a kai. Darusa ashirin da muka tsakuro a nan
kaɗan ne ƙwarai daga
cikin darusan da ke ƙunshe cikin dariya. Kowane darasi daga cikin
darusan idan aka tsaya aka fyace shi sarai, za a tabbatar da cewa ruwa na ƙasa sai ga
wanda bai tona ba. Bari mu ɗan waiwayi wani fasali daga cikin fasulan da
muka fayyace mu gwada tsawonsa da duniyar zamaninmu da muke ciki.
Dabarun
Tsaro:
Hausawa na cewa, lokacin abu a yi
shi. Halin da muke ciki a ƙarsamu ya kyautu a ce,
dukkanin karance-karancenmu da nazarce-nazarcenmu, su tunkari halin da ƙasar da muke
ciki su ba ta kyakkyawan agaji. Abubuwan da suka haddasa taɓarɓarewar tsaro
a Nijeriya ba karatun rana ɗaya ba ne, domin ba rana ɗaya suka
faru ba, bale wata gwannatin yini biyu,
ta ce, za ta ga bayan su. Tattare da sanin haka, dole mu ce alhakin
tsaro ga hannun shugabanci yake domin Hauswa sun ce, wanda duk ya ɗauri kura
shi ke da alhakin kwance ta. Idan muka harari tunanin Bahaushe na cewa, “wanda
ya ce zai haɗiye gatari
riƙe
masa ƙota, ina laifin mariƙi ƙota/ɓota da ‘yan
kallon yadda za a haɗiye. A
koyaushe fitina ta ɓare,
Bahaushe na ganin dole shugaba ya sa gaba ya tara, domin mai sanda ke da
fasalin bugu. Idan shugaba ya samu kansa cikin rashin kwanciyar hankali ga waɗanda yake
jagoranta, ya kula da waɗannan
abubuwa ya gani:
Maƙarrabansa:
Tunanin Bahaushe na, ba a mugun
sarki sai mugun bafade dole a koma gare shi. Idan an shiga tatsaka mai wuya
dabarar shugaba kaɗai ba ta
fitar da suhe wuta. Dabarar matasa masu sabon jinin ƙara dagule
bakin zare take yi. A riwayar tatsuniyar shugaban ƙasa Zaki da
‘yan ƙasarsa dabbobi abin karatu ne.
Zaki
ya umurci kowane ɗan ƙasa ya je ya
kashe mahaifansa a manta da duk wani tsohon alkawali a kafa sabon alƙawali a
tsarin gwannati. Kowa ya zartar da umurnin da aka ba shi, sai zomo kawai ya je
ya gaya wa iyayensa suka ce: “Ka da ya yi, ya ɓoye su. Bayan an gama ta’asa,
aka je faɗa zaki ya
ce: “Ina son a gina mini babbar fada da ba ta ƙasa, ba ta
sama, in dinga lilo ina shaƙatawa”. Ya ƙara da cewa:
“Na ba da kwana ɗaya kowa ya
je ya yi tunani yadda za a yi. In an kasa kowa ya zo da likkafanin jana’izar
gawar kansa”. Da adadi ya cika, kowa ya zo yana hawaye. Zomo ya je ya gaya wa
mahaifansa suka gaya masa cewa: “In ka je ka ce, ya fara aza harsashe za ku
idar”. Zomo na faɗar haka,
zaki ya ƙauyanta da shi neman sulhu.
Wace hauka da wauta da dambala da ɗimancewa ta
fi a ba ka wuta ka cinna wa gidanku da ba ka da wani gida sai shi? Bayan ka ƙona shi ina
za ka zauna? Bayan ka kashe ‘yan uwanka da ‘yan uwan wa za ka zauna? Wanda ya
sa ka ta’asar da sunan wai! Aikin tsaron ƙasa, in ƙasar ta ɓare, ina za
ka je? Shi ko ina zai koma? Haba aboki! Ai aiki da hankali ya fi aiki da agogon
hannu.
Hankalin Jama’ar
da ake Shugabanta:
Dole ne shugaba da waɗanda ke
taimaka masa su riƙa sara suna duban bakin gatari. Idan tsaron ƙasa ya yi
cin alewar kuturu, ka da a yi zaton talakawa ba su da hankalin sanin ina aka
dosa? Tunaninsu a koyaushe shi ne, akwai ranar ƙin dillanci.
Game takai da ma’aikatan hukuma a wawuce arzikin ƙasa shi ne
musabbabin fitina da yaƙi a kowace ƙasa. Idan
talakawa suka fahinci da jininsu ake amfani, a kashe su, za su mayar da amsar
tambayar izgili da gatse. Dubi jawabin sarkin kutare da dangaladimansa da
talakawansu:
An
ce, sarkin kutare ya gaya wa kutare ya kamata a samu ranar da za a daina bara.
A shirya kacici-kaci, wanda duk ya ci nasara, a je gidansa a yi liyafar
shekara. Sarki ya game baki da Dangaladimansa, ya gaya masa tambayar da zai yi,
da irin amsar da zai bayar, domin su tsira da mulkinsu da dukiyarsu. Sarki ya
hau karaga ya ce: “Ga tambaya: Wani abu ne ƙato, mai ƙaton kunne,
mai ƙaton baki, mai ƙaton ciki
shi ake hawa zuwa bara. Mene ne shi”? Aka yi tsit! Dangaladima ya ɗagar da
daginsa ya ce, “Na san shi”. Sarki ya ce: “Mene ne”? Dangaladima ya ce: “Kifi”.
Sarki ya ce: Kayya! Ba ka gane ba”. Talakawa suka ce: “Wallahi ya gane, kifi
ne! Kifi ne!” Dangaladima ya ce: “Wallahi ban gane ba”. Talakawa suka ce:
“Wallahi ka gane, kifi ne”.
Na tabbata matsalolin tsaron ƙasar nan ya
kusa ga ya kai haka. Da shugabanni da talakawa kowa kallon-kallon yake yi wa
juna. Shugaba da kansa ya ce, ya san musabbabin rashin tsaro duniya ta jiya ta
yarda. Da baya ya dawo ya ce, bai gane ba kure ya yi, me ake son talakawa su yi
in ba zanga-zangar hankali ta fadar sarkin kutare ba? A dai ja sannu, Kabawa
cewa suka yi: “Kifi na ganin ka mai jar homa”.
Matsayin
‘Yan Shawara ga Tsaron Ƙasa:
Dole sai shugaba ya rege irin
matsyain ‘yan shawara yayin da ƙasarsa take cikin yaƙi. Wani ɗan shawara,
tuwonsa kawai yake karewa. Wani a cikin kuɗin sayen makamai yake da nasa rabo.
Wani, a fagen artabu yake kallon ganimarsa. Wani, matuƙar babu
fitina da yaƙi abincinsa ya lalace. Wani, yaƙin wurin
huce haushinsa ga wasu ne domin tsohuwar adawa ta addini da ƙabilanci da ɓangaranci da
siyasa da kishi. Tatsuniyar wani Dunya da matansa biyu sun isa misali:
Dunya
ya yi amarya, sai ya fita daji neman abincin da za a yi angwanci. Yana shiga
wani gungu tarkon ya kama shi. Da matansa suka tarar da shi ɗaure cikin
tarko suka kasa fitar da shi. Suka ga lallai an kai ga adadi domin maraice na
gwamatsowa masu haƙo na zuwa. Amarya na cewa: “Yi fakaf! Faka!
Kaman namiji kake”. Uwar gida na cewa: “Yi lahu! Kaman ka mutu”. Ya bi shawarar
amarya tarko ya ƙara ɗaure shi. Ya bi shawarar uwar gida,
bai ji tarko ya fita ba. A ƙarshe, ya yanke shawarar bin
shawarar uwar gida ya lahe ya ɓoye lumfashi kamar ya mutu. Da mai haƙo ya zo, ya
gan shi ya ga mata biyu suna kallo. Ya laluba bai ji alamun rai ba, sai ya ce:
“Allah sarki, ya riga ya mutu, ba rabo ba ne”. Ya kwance ya wurgar da shi, shi
ko Dunya ya ce: “In ba ka yi ba ni wuri”.
Idan za ku yi mini adalci haka
matsalolin tsaron ƙasarmu yake. ‘Yan siyasar da ke cin gajiyar
rashin tsaro da ‘yan tsirarrun da ake kashe wa arzikin su ka matsa cewa a ci
gaba da ɓarin wuta
sai an zubar da ruwan ɓula.
Talakawan da musibar ke ƙarewa a kansu, su ke son a zauna a sasanta. Da
an bi ta Bafulatani ta cewa, “Saki Sehu kama Jema”, da tuni ƙura ta lafa.
Karen da Duk
ya yi Cizo da Gashinsa Ake Magani
Wataƙila wani zai
ce, yaya za a yi sulhi da waɗanda ba a san wurin da suke ba? Wa zai yi sulhi
da iska? Bayani a nan shi ne, ai ba daga sama abokan yaƙi suka faɗo ba. An san
tushensa, an san waɗanda aka
kama, da waɗanda aka
kashe, da waɗanda ake
fafatawa da su. Cikin halin da muke ciki, da masu yaƙi, da waɗanda ake yaƙa, an shiga
wani rutsi da ɓaraye suka
shiga ga kyanwar da ta haddabe/addabe su.
An
ce, kyanwa ce ta hana wa ɓeraye shaƙatawa. A
kowane maraice suka dawo da kiyo sai ta kiwace su. Suka yi taro yadda za a
fuskance ta. A ƙarshe suka kai ga cewa: “A samo gwarje a ɗaura a
wuyanta duk lokacin da ta taso gwarjen da ke wuyanta zai ba su labari su
tsere”. Ƙarami daga cikinsu ya ce: “To wa zai je ya ɗaura mata
gwarjen”?
Tunanin tsaro ƙasarmu a
koyaushe manya ke sussukarsu ɗaka, shiƙa ɗaka, dahuwa ɗaka, sai ta ɓaci a sayo
makamai a ba soje da wakilan tsaro, a ce su je su kashe ‘yan’uwansu. Idan an
rinjaye su ko suka ga musibar da ke ciki da bita-da-ƙullin da zai
biyo baya suka ja da baya a hukunta su. Lokaci ya yi a yi twa-da-twa wankin ɗan kanoma
mashaya a hura wuta kowa ya ga rabonsa. A yau, daidai ne a binciki kowa, komai
muƙaminsa
a hukuma, a tabbata an kai ƙarshen yaƙin da muke
ciki domin Hausawa cewa suke yi: “In raƙuminka ya ɓata babu
laifi cikin fafitikar nemansa ka leƙa akurki
domin ɗebe tababa”.
Ka Da A Je
Gyaran Doro A Karya Gadon Baya:
A iya tunaninmu mai ɗaki ya san
gefen da ɗakinsa ke
tarara haka kuma ba mu da saɓanin cewa, mai baibaya ya san wurin da ya tsohe
makwararar ruwa. Akwai rashin adalci ga rabon faɗan baƙauye, kowane
yaro a doki kansa a ce, ya yi gidansu, ba tare da bahasi ba, an ce, gobe a zo a
ƙara.
Haka kuma, mai shiga tsakani dole a tabbata cancantarsa da dacewarsa domin a
tura Bakabe sasanta yaƙi tsakanin Gobirawa da Fulani, to! Maganar Gambo
za ta yi tasiri:
Jagora: Ko ban hwaɗi ba
:
Wanda ak kusa
:
Dut ya san nuhina
(Waƙar Kwastan).
Zumuɗin da ake yi na sawo ƙasashen waje
cikin rikicin cikin gida zai iya haifar da rabon faɗan sarkin
Aljan:
Shi ya tarar da yara uku na faɗa
Ya kama ɗaya ya jefa
matattar rijiya
Ya kama ɗaya ya ƙwaƙwale ido
biyu,
Ya kama ɗaya ya karya
wuya
Ya ce: “Ba don na taho ba da faɗa ya ɓaci”.
Waɗanda muke ta ƙoƙarin kira su
zo su kawo agaji, mu dubi yaya a gajinsu ya kasance Afganistan? Yaya aka kwashe
adashin a Iraƙi? Me agajinsu ya haifar a Libya? Wace riba aka
ci a Somaliya? Wa ya more cetonsu a Syria? Me ya haifar da fitinar Misra? Ai
mun ɗanɗana azabar
su da Ujuku ya ƙirƙiro Biafara.
Ba bita-da-ƙullinta ne ke biye da wargaza haɗin kan ƙasarmu ba?
Sanin Wurin
Bugu Shi Ne Ƙira:
Masana cewa suka yi, mutum duka
aikin da ya iya shi ake sa shi, idan dai ba so ake a ja masa wahala ba.
Kiyayewa da wannan ya sa Hausawa ke cewa: “Ba a fafe gora ranar tafiya”.
Amfanin wakilan tsaro tabbatar da tsaro amma ba su ne tashin hankali ba, ba su san
wurin da yake kwana ba, bale su yi masa kwanton ɓauna. Su kansu, idan sun gan
shi za a riƙa nesa da nesa karen mai komo. Labarin wani
mahauci da ya balbalo a guje ya faɗa motar ‘yan sanda ta sintiri, ya
isa babban misali:
An
ce, wani mahaukaci ne da abin ya motsa ya dako sura ya daka tsalla ya faɗa motar
sintiri ta ‘yan operation wurjanjan
ba su tsaya tambayan mafari ba. Nan take da saja da kofur da insifacto suka
nemi agajin dugadugansu. Aka tsallake mota da bindigogi da barkonon tsohuwa da
inkwa a wofi. Taɓaɓɓen bai ce
uffan ba, ya yi kwance ciki motar. Na bar ku da sauran bayani.
Haƙiƙa Hausawa
cewa suka yi, mai hankali idan ya ga kurma aguje ba zai tsaya neman bahasi ba,
limanci zai yi masa, domin gani ya yi, ba labari aka ba shi ba. Matsara ƙasarmu ba
tsaro suka karanta ba, yadda za a harbe waɗanda aka tunzura suka karanta. Sun
riƙi
bindiga a matsayin tsaro gare su idan suka yi ta’asa, kuma abin barazana ga waɗanda aka
tattarwarsa domin biyan buƙatar son ran waɗanda ke kan
karagar iko. Da sun san fitina farin sani, da tuni an sasanta a murƙushe
kangara. Dubi abin da ya gudana tsakanin tsohon ɗan sane da yara ‘yan sane a
kasuwar Sakkwato:
Wani
fitaccen ɗan sane
tubabbe aka sama wa aikin yi a gidan siminti. Biyan albashinsa na farko ya saka
kuɗin aljihun
gaba ya shiga kasuwa. Yana shiga ‘yan makarantarsa suka zare su. Ya kama yaron
(ɓarawon) ya ɗora a ka, ya
doshi bayan kasuwa ya sauke shi ya ce: “Ba ni kuɗina”. Yaro ya ciro kuɗinsa ya ba
shi. Ya mare shi, ya ce: “Kawo saura”. Yaro ya ciro wasu, da ba nasa ba ya ba
shi. Ya kai wa yaro ƙoso, ya ce: “Ina na aljihun baya”? yaro ya zaro
ya bayar. Ya doki cinyar yaro ya ce: “Ina ‘yan rakiyar ƙasa”? yaro
ya san in ba ɓarawo ba,
babu wanda ya san da aljihun bante, yaron ya yi dariya ya ce: “Shege baba,
halama ana da niyyar zuwa hajji bana”? Oga ya ce: “Muna da niyya”, yaro ya ce:
“Don Allah a isar da gaisuwarmu ga Manzo (SAW)”.
Idan ba ka san abu ba, yaya za ka
tunkara shi? Ƙarshen ta waɗanda ake tsaro sun fi wakilan tsaro
sanin yadda ake tsaro. Idan al’amari ya koma kiɗin ‘yan hamsin me za a ce:
:Kai mai kiɗi kiɗa in jiya
: Ba ka da aiki ni ba ni da
: Mu taru mu lalace mu duka.
Naɗewa:
Na tabbata wannan ɗan tsakure
zai ba mu hasken cewa, tsaron ƙasarmu ya koma kurar Gardi.
Yanzu mun kai kowa ya tsira da karatun bakinsa. Ayau mun kai, da mu da ake
tsaro da waɗanda ke
tsaronmu kowa ba ya da wani ilmi sai na gudu. Da ganin fuskokinmu an san
zukatanmu a yamutse suke. An ƙure tunaninmu da dabarunmu na
ɗan bokonmu
mun ƙi yarda mu ba da kai bori ya hau. Ai da mun
fahinci da ƙyar na tsere ya fi da ƙar aka kama
ni sai mu huta da dirkaniya mota cikin randa mu yarda da cewa, da tsohuwar zuma
ake magani. Yadda magabatanmu suka shashance takaicin yaƙi da dariya
da barkwanci, dole mu yarda da cewa, da yau, da gobe, da jibi, da gata, da
citta, duk daga jiya aka fara ƙidayarsu. Da ƙarfi soje ke
murƙushe
yaƙi,
da yaƙin Biafara bai sake fitowa da sabon salo ba a
yau. Karkashe abokan adawa da tarkwatsa musu iyali da gidajensu ba shi ne
ruguza aƙidarsu ba, domin har gobe akwai Satirawa cikin ƙasar Hausa.
Ka sani, na snai, kun sani, da ba don zurfin tunanin magabata ba, wa ya isa ya
haɗa Babarbare
da Bafulatani da Bagobiri da Bakatsine da Bakabe da Banufe da Kambari da
Bakyange daula ɗaya, a yi
hidima da sabga iri ɗaya har da
auratayya, Bakabe ya yarda ya yi kiran salla Bafulatani ya yi limanci a ƙare salla
Bagobiri ya yi wa’azi? Kai jama’a! Tsaron ƙasarmu na
hannumu. Mu ke tsaron, mu ke ɓata tsaron. Ku tambayi makaɗa Narambaɗa me ya ce:
Jawabi: Ga abu nan a hwaɗi
Yaro :
Babu mai hwaɗi sai ƙus-ƙus-ƙus!
:
Akai da shi
Jagora: Wa ka hwaɗi?
Yara :
Kai ɗan baka hwaɗi.
Jagora: Wai baya ka ƙwazon tunkuɗe gaba
Yara :
Shi Allah ba yarda shikai ba,
:
Mai sharri shi ɗai yaka
biya.
Jagora: Kai tashi biri tsohon maɓannaci!
Yara :
Karen ɓuki bai ɗau
shawararka ba.
:
Shi maganar giwa yaka tsare
Jagora: Ku ce ma biri
Yara :
Duk dabbar da ac cikin daji,
:
Giwa taka biya.
Gindi : Ya ci maza ya kwan shina
shire
:
Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
Jagora: Kai magana an ce maka: “Tsaya”.
Yara :
Ka sake an ce maka: “Bari”.
Jagora: Kai magana ka san ba a son
ta
Yara :
Ka ƙi
bari, waz zan mahaukaci?
Gindi : Ya ci maza....
(Ku
harari waɗannan ɗiyan waƙa da kyau ga
shugabancin mu na yau).
No comments:
Post a Comment