Halittun
da suka mamaye duniyar matane guda biyar ne: Mutane da dabbobi da tsutsaye da kwari da tsirrai. Mutane tsuntsaye da
dabbobi da ƙwari da tsirrai ne abincinsu. Tsuntsaye a kan su suke shawagin biɗan abinci su. Dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da tsirrai suke kalaci. Tsuntsaye a kan
su suke shawagin biɗan abincinsu. Tsirrai da toroson Mutane da dabbobi da
tsuntsaye da ƙwari (da nasu) ke rayar da su. Wanda ya jahilci wannan ya yi wa duniya
zuwan kare ga aboki. Wanda ya haƙiƙance su bai zuwan sunge duniya ba. Sarrafa rayuwar waɗannan gabaɗayansu, su amfani mazauna duniya, yana ga hannun manoma.
Ashe idan aka ce ga ƙungiyar manoma kowa na cikin ko….
Noma: Igiya Mad’ura Kaya In An Yi Ba Da Kai Ba Su Watse
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua
Katsina Nijeriya
Takardar da ake gabatar a taron ƙungiyar Manoma
ta tarayya, reshen Jihar Sakkwato (AFAN) a makarantar Ilmukan Ƙur’ani
ta Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
Abubakar III ranar Lahadi 31-05-2014 a bukin ƙaddamar da
kalandar manoma da karrama fitattun manoma da masu agaza wa aikin noma
Gabatarwa:
Halittun
da suka mamaye duniyar matane guda biyar ne: Mutane da dabbobi da tsutsaye da kwari da tsirrai. Mutane tsuntsaye da
dabbobi da ƙwari da tsirrai ne abincinsu. Tsuntsaye a kan su suke shawagin biɗan abinci su. Dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da tsirrai suke kalaci. Tsuntsaye a kan
su suke shawagin biɗan abincinsu. Tsirrai da toroson Mutane da dabbobi da
tsuntsaye da ƙwari (da nasu) ke rayar da su. Wanda ya jahilci wannan ya yi wa duniya
zuwan kare ga aboki. Wanda ya haƙiƙance su bai zuwan sunge duniya ba. Sarrafa rayuwar waɗannan gabaɗayansu, su amfani mazauna duniya, yana ga hannun manoma.
Ashe idan aka ce ga ƙungiyar manoma kowa na cikin ko bai zo ya yi rejista ba
murhun gidansa wata babbar hujjar zama ɗan ƙungiyar AFAN
ne. Don haka nake ganin ba sai an wasa wannan ƙungiya ba, domin masu
hikima ce wa suka yi annurin fuska kaurin hanji.
Maƙasudi:
Maƙasudin taronmu a yau shi
ne, ƙaddamar da kalandar masu hankali, ‘yan kishin ƙasa, ma’arzitan duniya.
Masana al’ada sun ce hankali cikin gona yake yawo da ya yi ɓatan hanya hauka za ta zo, da an koma gona santi da saiɓi za su farfaɗo da shi. Babu ɗan kishin ƙasan da ya kai
manomi, domin ƙasar da duk babu shi komai ƙarfin arzikinta dole ta ragaice. Da noma aka fara girka
arzikin duniya. Duk tattalin arzikin da babu noma ciki yunwa na wargaje shi.
Tabbata burinmu na karrama noma da manoma da masu agaza wa noma da manoma wani
sabon alƙawali ne na ceton al’ummar jaharmu da ƙasarmu baki ɗaya. Haƙiƙa, ma’aikatar kula da al’amuran noma
ta jahar sakkwato ta cancanci yabo ga kowane irin manomi na jaha. Irin ƙwazon
ma’aikatanta na ganin kayan tallafa wa manoma sun sadu ga manoma shi ya sa muka
shirya wannan taro na godiya ga gwannatin Jihar Sakkwato da ita kanta
ma’aikatar da ma’aikatanta da masu agaza mata. Allah Ya yi muka jagora ya ƙara ƙarfafa ku.
Goyon bayan da kuke ba mu, ya ƙarfafa mu muka ba yauwa tsoro ta yi hijirar da babu ranar
yada zango ƙasarmu
Gurbin Manoma
A tunaninmu kowa manomi ne, da mai riƙa kwasa da mai
riƙa kuyafa da mai riƙa cokali. Ƙarfafa sana’armu na rage ta’addanci a ƙasa. Inganta ta
na kawar da rikice-rikice ƙabilanci. Mutunta ta na kawar da rikicin addini. Ba ta
cikakken goyon baya na yayyafa wa rikicin siyasa ruwa. Ba ta goyon baya na hana
wa matasa ragaita. Kula da ita makamin yaƙar ɓata gari da zauna gari
bunza ne. A ba mu dama a gani, mu yanke wa yunwa hukuncin kisa, mu rataye ta,
in ana sake jin ɓular cutar zawo da amai da maci-ɗan-wawa da gyambon ciki da juwa da hauhawan jinin da babu dalili. Na yarda
da tunanin Garba Gwandu da ke cewa:
Noma jigon gari shi zan bai
watse ba,
Noma ganɗon ƙasa ta zan ba ta yoye ba,
Gari duka in babu noma ba zai zauna ba,
Barden duniya a ko’ina ba ɗwaɗi ba,
Kai ka tashi mu yo girgiza gaba ɗaya ga manoma.
A
kirarin Aƙilu Aliyu cewa ya yi:
Noma kashe bashi ɗan Sabtau,
Wawwargaza yunwa ɗan ƙartau,
Mai daɗɗaga martabar Nomau,
Madalla abin kirari nau
Kai ba dodorido ne ba.
A ra’ayin Sani Ɗambolɗo noma layun tsari ne.
Jagora: Kun san layun tsari gare ni
: Dunƙullan dawo gami
da noma
: Kowas
sha su ba ya jin kasala,
: In
ko an yi gardama a dama
Gindi: Rabbana Allah ka taimake mu
Mu Samu bitar kai cikin tukunya.
Burinmu,
a zabura zuwa gona, kamar yadda Aikau Jikan Tayawa ke yi (in ji makaɗi Amali). Yin haka, zai sa a kauce wa tarkon Ɗan’anace (a waƙar Mijin
Danjimma). Ai sai damina ta yi kyawo su Hantsi Hore ke nuna buwaya (in ji Gambo
Mijin Kulu).
Yaba kyanta tukunici:
Tsananin ba noma da manoma muhinmanci ya sa mai girma Gwannan Jihar
Sakkwato Alhaji (Dr) Aliyu Magartakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato) ya ba ƙungiyarmu mota.
Babu shakka, a ko’ina ake taron manoma, manoman sakkwato na daban ne domin ba
mu taɓa jiran mai kai mu ba, sai dai mu nemo direba. Haka kuma,
a fagen hulɗa da manoma mai girma kwamishinan ma’aikatar gona da
babban sakatarensa da daraktocinsu da sauran ma’aikatansu sun share muna
hawaye. Ba su taɓa yi wa manomi kallon wa ya aiko ka ba. Ba mu taɓa kai buƙata ta barkace ba. Ba mu taɓa neman agaji suka yi
kasala muka koka ba. Duk da haka muna roƙon:
i.
A ƙara tallafa wa
manoma ga sayen kayan da suka noma domin su ƙara ƙarfin guiwa.
ii.
A ƙara fito muna
da iraruwan shuka da ke yi wa sauyin yanayinmu barazana.
iii.
A cece mu a buɗa kamfunan hukuma na sarrafa abincinmu domin jahar Sakkwato ta sake
jagorancin jihadin noma a Nijeriya.
iv.
A riƙa kula da waƙilcinmu a
kwamitocin jaha da na tarayya domin mu ke ba da agajin farko gabanai a kurɓa nagaske (Shayi).
v.
A fito da wani
shirin da zai taimaka wa matasan da suka kammala karatu na noman rani da
damina.
Naɗewa
Da ƙara yawaita ma’aikatau tsaro da faɗaɗa asusun tsaron ƙasa, da sayen makamai, gara a fito da wani salon kashe
rabin kuɗin ga noma. A iya tunaninmu, ƙabu ƙasar da ke sayar da
abincinta ta saye makamai. Ƙasashen da ke sayar da makamai abinci suke saya wa
jama’arsu. Idan ba a shafa ba, an yi lokacin da dukkanin ɗawainiyar wannan ƙasar a wuyan Arewacin ƙasar nan yake da ya ginu a
kan noma. Maƙiya sun lura da cewa, abincin da muke da shi wani makami ne da ba ya yaƙuwa. Don haka
ake son a tarwatsa muna manoma da makiyayya a karkashe su, su gaji ƙasar afafa. Ƙungiyar AFAN na
tabbata wa mai girma Gwannan jihar Sakkwato Alhaji (Dr) Aliyu Magatakarda
Wamakko (Sarkin Yamma Sakkwato) cewa, tana baya ga ƙudurinsa na ƙwato wa Arewa
haƙƙinta. Muna tare da kai sai an karɓe goriba ga
hannun kuturu. Ka da ka ja da baya, sai an hura wuta kowa ya ga rabonsa. Mun ji
an ce, wai, mai ɗaki ya san gefen da yake tarara. Mu ko za mu tabbata mai ɗakin cewa, mai baibaya ya san wurin da ya toshe makwararar ruwa. Masu cewa,
cikin kashi babu wanda ya fi wani wari. Yaran makaɗa Narambaɗa sun ƙaryata su ga faɗarsu:
Jagora: Da Mai hashin wuta da mai kashin wuta
: Da
mai rabon faɗa da mai haɗin faɗa
: Su
duk huɗu sun taru game
: Ba
mu samu guda wanda yaf fi ba.
Yara: Narambaɗa koma ga gaskiya
Mai kashin wuta ya fi mai
hashi
: Mai rabon faɗa ya fi mai gami
: Ni kan ga irin wadda nag
gani
: Ka san jimina ta fi zarɓi babban guru ko tai masassara.
Gindi : Ta
tabbata gwarzon uban gida namijin jiya ka tsere ‘yan’uwa.
No comments:
Post a Comment