A
fahintar ɗaliban al’ada, a
kodayaushe akan tsinci al’adun mutane cikin harshensu da adabinsu. Al’ada
kandamemen fage ne da babu wanda zai rayu a wajen ta, komai dabararsa sai an ga
gurabunta a rayuwarsa. Don haka, ɗaliban
al’ada ke ganin waƙoƙin baka wani babban rumbun kinshe
al’ada ne da bai kamata a bari su salwanta ba a kowane zango na rayuwa. A
rayuwar kowane mutum abu biyu ke tare da shi a cikin fafitikar rayuwarsa:
‘samu’ da ‘rashi’. Ga al’adar nema, tushen neman wani abu shi ne ‘rashinsa’. Ko
dai babu shi, ana son a samo shi, ko kuma an same shi, ya ƙare, ko yana barazanar…
Huce Haushin Rashi A Kan Mai Samu
Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Waya: 0803 431 6508
Takardar
da aka gabatar a taron ƙara
wa juna sani a Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato Ranar, Talata 27
ga Nuwamba, 2012 da ƙ arfe goma na safe a babban ɗakin
taro na Tsangayar, a mazaunin din-din-din na Jami’ar.
Gabatarwa:
A fahintar ɗaliban
al’ada, a kodayaushe akan tsinci al’adun mutane cikin harshensu da adabinsu.
Al’ada kandamemen fage ne da babu wanda zai rayu a wajen ta, komai dabararsa
sai an ga gurabunta a rayuwarsa. Don haka, ɗaliban
al’ada ke ganin waƙoƙin baka wani babban rumbun kinshe
al’ada ne da bai kamata a bari su salwanta ba a kowane zango na rayuwa. A
rayuwar kowane mutum abu biyu ke tare da
shi a cikin fafitikar rayuwarsa: ‘samu’ da ‘rashi’. Ga al’adar nema, tushen
neman wani abu shi ne ‘rashinsa’. Ko dai babu shi, ana son a samo shi, ko kuma
an same shi, ya ƙare,
ko yana barazanar ƙarewa,
ana son a tabbatar da shi. A tsarin siyasar rayuwa, babu wurin da babu mai iko
da talaka, ‘yantacce da bawa, mai akwai da marashi, baƙo da ɗan
gida, ga su nan dai. A bisa ƙa’idar
al’ada, cikin kowane kashe-kashe na al’umma, marashi da mai samu, sun fi fice
da amo a zamantakewa. Ga ɗan
bincikena, wannan shi ya sa adabi da al’adar kowace al’umma na kulawa da su matuƙa. Buƙatar wannan takarda leƙo yadda makaɗa
Gambo ya fito da hoton yadda marashi ke kallon mai samu da irin hararar da suke
yi wa junansu a zamantakewa.
Karan Gwajin Dahi:
A
kowane sashe na adabi, ana samun yadda zamantakewar marasa da masu samu take.
Wani lokaci a tarar an shirya musu bayani na musamman kamar waƙoƙin Ɗanmaraya Jos (na Kai Mai Akwai Ka Gane). A
wani lokaci ya kasance matsiyatan kawai ake wasawa, kamar waƙoƙin ‘yan tauri. A wasu lokuta, a yi garkuwa
da rashi, a yi zambo, irin yadda yake aukuwa a waƙoƙin fada. A wannan ɗan
nazari, na zaɓi in mayar da
akalar bincikena a kan tauraro ɗaya
kacal, watau Alhaji Muhammadu Gambo Fagada.
Ga
al’adar bincike, sai an fayyace fitilun kalmomi sosai ga mai karatu da masu
sauraron karatun. Ɗan
bincikena ya yi garkuwa ga waƙoƙin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada
mai waƙar
ɓarayi. An haifi Alhaji Muhammadu
Gambo Fagada a garin Fagada Babba Ƙaramar Hukumar Maiyama, Jahar Kabi a
shekarar 1947. Cikakken tarihin rayuwarsa da gwagwarmayarsa an taskace su cikin
(Maiyama, 2008, da Gusau 2009, da Bunza 2011). Makaɗa
Gambo ya yi fice wajen kiɗan sata.
Ya yi luguden haushin da ke ga marashi a kan mai samu, da yadda za a hangi ƙurar takaicin a lafuzan marasa da
ayyukansu.
Gurbin Sata A Al’ada:
A
taƙaitacciyar
fassara, sata na nufin ƙoƙarin mallakar abin wani ba da
yardarsa ba, ba da saninsa ba, domin a amfana da abin, ko a lalata shi. Ma’anar
sata ruwan dare ce ga al’ada, sai dai hukunce-hukunceta ya saɓa,
daga ƙasa zuwa ƙasa, ko daga wani addini zuwa wani
addini. A al’adance, sata abar ƙyama
ce ga Bahaushe, abar kunya ce, mai fitar da mutum cikin mutane amintattu masu
faɗa a saurare su a al’umma. Wannan ne
dalilin da ya sa wa sunan mai aikata aikin baƙin jini, da ƙyama, ga duk wani mutumin kirki. Fitacci
daga sunayen akwai: ɓarawo,
mugu, matsiyaci, ɓare, mugun ɗa,
ƙwaro,
kura, duhu, macuci, fataken dare, maɗauki,
gafiya, kare, da dai makamantansu. Kowane suna daga cikin waɗannan
sunaye Bahaushe ya ji an kira mutum da shi zai nisanci mai sunan domin sanin
ma’anonin da ke cikin sunan. Bisa ga ma’aunin al’ada, sata ba sana’ar da za a yi
kirari da ita ba ce, domin al’ada ba ta yafe wa mai aikata ta. A al’adance,
tana daga cikin manyan laifuka da Bahaushe bai tanada wa mai aikata su wurin
zama ba a alƙaryarsa.
Me Ke Sa A Yi Sata?
A
cikin kiɗin sata wannan
takarda za ta kafa hujjojin da za ta kare iƙirarinta. Don haka, babu makawa, sai an
fayyace abubuwan da ke sa Bahaushe ya ɗauki
sata tafarkin rayuwarsa. Abubuwan da ke sa a shiga sata a wajen ɗaliban
al’ada sun kasu gida biyu: na ɗaya na
kira su ‘Azaliyya’ na biyu kuwa ‘Hali’. Azaliyya, ina nufin ɗabi’un
da mai su, bai da hannu a kansu, da su aka haife shi, ko sun ci karo da shi riƙis! Wato abin da Bahaushe ke ce wa,
ta tsaka mai wuyar sani. Daga cikin Azaliyya akwai: Ciwon sata, sammu ko jifa,
gado (shan sata a nono) ko ga mahaifi. Waɗannan
abubuwa uku, al’ada na ganin sun fi ƙarfin mai su ya kauce musu, domin ba da
saninsa suka shige shi ba.
Muhallin
‘Hali’ ga sata shi ne, mutuwar zuciya wanda ke haddasa lalaci, da ragganci, mai
kai ga, roƙo,
da bara, da ɗauka, idan masu
abu ba su ankara ba. Wanda ya ginu cikin wannan kashi, tushen satarsa daga
rashi ne, idan aka zure, a gunguma, a wuce gona da iri. Ga al’ada waɗannan
ɓarayi su ne, matsiyata ko marasa
masu takaicin mai samu. Akalar takardarmu gare su zai ba da ƙarfi domin su suka sa kansu cikin
halin da suke ciki, ba su suka fi kowa tsiya ba da rashin haƙurin zama a ciki. Idan kowane
marashi sai ya yi sata, da ke nan, rukuni biyu kawai muke da su a
zamantakewarmu, daga masu samu, sai ɓarayi.
Assha! Da tarbiyarmu ba ta kawo yau da nagarta ba.
Idan
muka faɗaɗa
bayanin sata zuwa halin da muka samu kanmu ciki a yau, sai mu ce; abu biyu suka
ɗaure wa satar biro da ta ɗauka-ruga
gindi a ƙasashenmu:
rashin adalcin shugabanni da rashin nagartaccen hukunci. Idan shugabanni sun
kiyaye kansu a kan taɓin
dukiyar hukuma, ba sai an ce wa talaka ya kama kansa ba. Idan shugabannin da
talakawa duk jirgi ɗaya ya ɗauko
su, tsaftataccen hukunci na sa dole a tsare gaskiya ko a sha kaifin takobin
adalci. Rashin waɗannan abubuwa
bala’i ne ga kowace al’umma komai wayewarta da ci gabanta.
Wane Ne Mai Akwai/Samu? Wane Ne
Matsiyaci?
Kalmar
‘samu’ da ‘akwai’ suna da fassarori biyu: gajeruwa da doguwar fassara.
Gajeruwar fassara ita ce, mutum ya kasance mawadaci ga buƙatun lalura na ɗan
Adam. A samu mutum na da wuri irin na tsara. Yana da abinci irin na, ku zo mu
ci a raga. Yana da sutura irin suturar da al’adarsu ke kira sutura. Idan mutum
ya hau wannan fassara a al’ada yana cikin masu samu, don haka ya cancanci a
kira shi ‘Mai Akwai’. Doguwar fassarar kalmar ita ce, a ƙara da gajeruwar fassara. A haɗa
da abubuwan da ke ƙawata
rayuwa, su fito da mai ita a sarari, a ƙara saninsa, ya gwada tsawo da zamaninsa.
Wato ya kasance mai ilmi, ko mai ‘ya’ya da yawa nagartattu, ko mai wata alfarma
ta musamman. Wanda ya samu wannan, ko da bai mallaki komai na duniya ba, ba ya
daga cikin marasa, kuma ba za a ce masa, matsiyaci ko mai babu ba. Aƙilu Aliyu ya raba muna gardama a
cikin waƙarsa
Kadaura ya ce:
Sai
ga mutum ba ilmu ba mulkin ba,
Shi ba kuɗi
sha’anin akwai rikitarwa.
Ƙanta ƙalai gashe babu mai ko naso,
Dahe babu romo ko na ɗan
lasawa.
Bisa ga al’ada,
idan mutum ya kasa shiga cikin gajeruwar fassara da doguwar fassara ta mai samu, to ya shiga
cikin marasa ke nan, su ake kira ‘matsiyata’ na haƙiƙa. Idan mutum ya fi haɓar
sama lafiya, idan bai shiga cikin fassarorin nan biyu ba, ya shiga cikin
matsiyata. Tabbas! Idan ya fi dila wayo. In ya fi aula dabara; in ya fi biri
azanci; in ya fi kowa hankali da zumunci a garinsu. Muddin ba ya da kuɗi
da ilmi, ba muƙami,
sunansa ‘matsiyaci’. Dangantakar waɗannan
mutane da masu samu ita ce maƙasudin
wannan ɗan rubutu.
Dangantakarsu Ta Al’ada:
Dangantakar
mai samu da marashi ta ƙud-da-ƙud ce, irin ta jini da tsoka. A
koyaushe, marashi wurin mai samu yake shan iska. A wajen mai samu za a bautar
da jiki, a samu na shagali. Idan aka yi masa hidima ya biya. Abin da za a saya
a more rayuwa, a wurinsa za a je a saya. Ya ba da bashi a saya dukiyarsa, a
mayar masa da kuɗin da aka karɓa
bashi gare shi. Ya ba da kyauta, a saya dukiyarsa da kuɗin,
su koma gare shi. Ya yi sadaka, a saya dukiyarsa jallin da aka tara wajen bara
ya koma gare shi. Idan ya yi arha ga kayansa ya ci riba, idan ya yi tsada dole
a saya, ya ci riba da ribibi. A yi noma, a tara abinci a kaka, ya saya da arha
kamar kyauta, ya ɓoye, sai rani ya
kai rani ya fitar da abincin, waɗanda
suka sayar da shi, dole su saya ko su mutu ko su bar ƙasar. Wai, duk wannan dangantakar
mai sauƙi
ce ga marashi domin ana yin ta ne da mai samun da ke tausayawa ne.
Wurin
da ake hararar juna shi ne, wurin da mai samu ya kasance mai alfahari,
marowaci, matsolo, macuci, mamugunci, marashi tausayi da tausayawa. Mafi
rinjayen masu samu a wannan ɓangaren
suka faɗo. Mai samu zai
yi amfani da samunsa ya ƙwace
wa moro (mataulaci) mata, ya ɓata
‘ya’yansa mata, ya kunyata ‘ya’yansa maza da kushili, ya haukata wasu, ta
hanyar ba su kayan shaye-shaye, su yi masa banga a gari, da sunan siyasa, ko
addini, ko ƙabilanci,
ko barantaka. Bayan an bautar da marashi ga ƙwadago, a bautar da shi ta fuskar bashi da
ruwa, tun bai gama biya ba, a bi shi da kamuwa. A koyaushe moro cikin ƙangi yake na masu gari da masu abin
hannunsu.
Taimakon
da wasu masu samu ke yi wa marasa, na dariya ne, da nuna, ga shi nan an san na
fi ka. Idan za a ba shi sutura, taɓa-jiki
za a ba shi, kowa ya san kuncen wane ce. Idan abinci za a ba shi, idan ya yi
bara, saura za a ba shi, ya sha saleɓar
yara. Idan dabba za a ba shi ya kiwata ya samu ta haifa masa, ramamma za a ba
shi, ya sha wahalar kiwo, wasu a ba su juya, su gama kiyo a kai gidan mai abu a
yanka a ci gajiyar wahalarsa, in ya yi sa’a, a ba shi fata da ƙassa. Idan aka ba shi gona ya noma,
ba da abin da ya noma zai biya ba, sai ya je gandun mai gona ya kashe ƙarfinsa can gabanin ya dawo ya nomi
nasa gaɓɓansa sun yi
laushi ba zai noma abinda zai ciyar da kansa ba. Idan ya shiga wata matsala sai
ya bayar da kayansa jingina zai fice ta. Ire-iren waɗannan
abubuwa suka haifar da rashin jituwa, da samun natsuwa a fahinci juna tsakanin
marashi da mai samu. A koyaushe marashi ganin yake, mai samu yake yi wa
wahalhalun duniya, don haka daga nan ne ƙyashi zai shiga, takaici ya biyo baya,
daga nan sai tunanin hanyoyin da za a huce haushin da aka ƙunshe shekara da shekaru. Wataƙila, daga nan ne wasu ke tunanin
raba mai samu da samunsa ta kowace fuska, sai tunanin sata ya fara memen
zuciyar marashi. Idan marashi ya kai ga wannan tunanin, ya kai bagiren da
Bahaushe ke cewa, kome taka zama ta zama. Ashe gaskiyar wani mai bara da ke
cewa:
Ranar
da ba ka da shi,
Mai
ba ka ba shi da shi
Rannann
da kai da ɓarawo
Shawararku
guda.
Hoton Takaici Da Haushi A Lafazin
Mai Jin Su:
Babu
wani ɗan Adam da ya kuɓuta
ga shiga ƙunci
na damuwa da zai haifar da takaicin wasu ko wani abu, ya ɗuru
cikin hushin abin har ya yi ɓarin baki
a gane a lafazinsa. Daga cikin abubuwan da suka fi bayyana a gane akwai takaici
da haushi akwai:
i.
Furucin takaici tsirara
ii.
Kushewar samu kai tsaye
iii.
Muguwar fata ga samu
iv.
Zagi na fitar arziki
v.
Mutuwar mai samu
vi.
Ganin hasara ga mai samu
vii.
Ƙyacewa
da haƙewa
Furucin Takaici Tsirara:
Bisa
ga al’adar magana, akan ɗan sakaya
wasu abubuwa, ba sai an yi musu wuƙa zage ba. Idan marashi ya ga mai samu
yana damawa a kan ingarmarsa ko motarsa sai ya ce: “Allah da Ya ba ku raƙumi Ya ba mu zakara”, an san ya
sakaya, duk da yake ya furta abin da ke yi masa ƙaiƙayi. To, yaya za ka ce? Idan ya ce: “Allah
da Ya ba ku raƙumi,
Ya ba mu wuƙa,
raƙumin ya
ci ubansa.” Da ji, wannan lafazin ya fi wanda ya gabace shi zama tsirara. Dubi
wannan lafazin na marashi ka gani:
Jagora: Ni dai ko da subahin ko da yamma
:In
ishe mai kuɗɗi tsugunne
:In
ga yana naso ga goshi
:Kama
da kunama sun ka kauru
:Shi
ɗebi gumi bay yo guda ba
:Gambo
in ji awa na taki Arhwa
:Tun
da mai abu ya koma matcaci
Mai
samu ake son, in dai ya yini cikin baƙin ciki, irin na marashi, in ko ya kwana
cikinsa. A ganin marashin, idan ya ga haka buƙata ta biya, domin su marasa sun ƙara yawa ke nan. A nan, ana zance
ne kan wanda ya tara tsabar kuɗi ne, da
aka zo ga mai ƙadara
cewa aka yi:
Jagora: Gaya wa baƙauye mai tumaki
:Wai
ya ga kiyo ya fara tcada
:Ya
ga awa sun tara jalli
:Wallahi
suna kwana matcata
:In
je Mafara in iske Ja’e
:Shi
gargaɗa ko ɗai
bai ragawa
Babu
shakka, a nan, haushin abin da aka tara ne marashin ke yi. Idan kiyo ya fara
tsada, su marasa ba su da abin sayen bisashe ko da lalura ta riske su. Domin
kakkaɓe wannan takaici za a kira Ja’e.
A
waɗannan wurare duk, takaicin bai kai
gaya ba, da aka bai wa Dikko Canda (ɓarawon
bisashe da shanu) shawara cewa:
Jagora: In Canda na bin ta tawa
:Ana rasa ko bundi Kuwara
Ya
kira marashin abokinsa (Canda) da cewa, ya samo kwari da baka irin na farautar
namun daji, ya sa musu dahi irin na Bargu da an harba sun mutu, wanda ya ci
nama ya mutu, ga faɗarsa:
Jagora: Duk ka bi su ka harbe
:’Yan
gaton uwa
:A
bar su ga kolaye su canye
:Dikko
ban yi hasarar ko kwabo ba
Takaicin
ya fito tsirara, son ake, mai abu ya yi rashi, ya dawo cikinsu, a ƙara yawa. Kuwara can ne Madinar
shanu a Nijeriya ta Arewa, duk wani Bafulatanin da ke jin ya taki ƙasa ga samu na dabbobi sai an je
Kuwara za a tantancewa. To! A cikin Madinar shanun Arewa marashi ke son a rasa
ko wutsiya. A lura ba Gambo ne ke magana ba, marashi ne ke furta takaicinsa a
bakin Gambo. Dalilin haka kuwa masu samu suka sa aka ɗaure
Canda ya yi hursuna, ya ƙare
ya dawo. Don haka ake son ya rama abin da aka yi masa. Wa ya kai shi gidan
Yari? Masu samu. Mene ne matsayinsa? Marashi. Me ya kamata ya yi? Huce haushi.
Kushe Wa Samun Kai Tsaye:
Irin
nuna rashin tausayi ga marashi da masu samu ke yi, shi ke sa marasa ke nuna
kushewa ga dukiyarsu. A al’adar huce haushi, idan ba a fito tsirara aka furta
ba, ana nuna kushewa, da ko oho, ga mai samu. A fagen kushewa, ko da gaskiya
aka faɗa, mai hankali
zai gano cewa, akwai abin da ya sosa wa mai kushewar rayuwa don haka ya yi
furucin. Nazarci wannan ɗan waƙa sosai:
Jagora: In don waɗanga
Musulmi na na yanzu
:Masu biɗan
matan maƙwabta
:Musurmuƙa duk na ‘yan gaton uwa
:Kuɗin
lukudi na ag ga shaggu
:A ɗunguma
kowa ban hana ba
Tirƙashi! Daga cikin abin da ke ci wa
marasa rai ga masu samun zamani akwai amfani da abin hannunsu su ɓata
musu mata da ‘ya’ya. Haka kuma, suna ganin mafi yawan dukiyar ta tsafi ce da
aka yi da ‘ya’yansu ko dabbobinsu. Wannan takaicin ke sa, ko an yi musu sata,
ba a tausaya musu, domin ana ganin ɓarawo
haƙƙinsa ne
ya ƙwato da ƙarfi, kamar yadda aka yi amfani da
wayo aka karɓe masa. Da
Musulman na tsare haƙƙin
amanar dukiya da mai bayarwa ya ba su, da ba su saɓa
masa da ita ba. Idan suka yi masa ɗa’a
da ita babu marashin da zai ji haushinsu bale ya huce haushin a kansu.
Muguwar Fata Ga Samu:
Idan
takaici ya yi takaici, marashi buƙatarsa a yi marus, mai samu ya rasa kowa
ya rasa. Da an yi fatar, ya rasa, wani ya tafi da samun, za a ce, da dama-dama.
Makaɗa Gambo cewa ya yi, shi idan ya
tunkari gari zai shiga ciki, ya dai san da samu ake kafa gari ba da rashi ba.
Duk wanda ke cikin garin samu ya zaunar da shi. Don haka, yake son, ya tarar
garin ƙurmumus
da wutan gobara, kowa ya fita tsila, a faɗarsa:
Jagora:
Ni dai ga irin magun nuhina
:In
na tunkari gari
:Tun
da shiga in taki toyi
:In
ga labaye sun yi malle
:Gambo
in ji awa na taki Arhwa
:Tun
da mai abu ya koma talakka
Idan
aka sa natsuwa sosai aka saurari Makaɗa
Gambo ɗiyan waƙoƙinsa cike suke da ire-iren waɗannan
kalamai masu nuni ga samun mai samu. Toyi yana nufin sauran hauɗin
da wuta ta ci. Labaye su ne: sabara da geza da ƙananan tsirrai idan sun ci wuta sai su lanƙwashe ganye ya ƙone su yi sifar baka ko lauje shi
ne “malle”. Malle wani abinci ne mai kara da ‘ya’ya irin na dawa idan ya nuna
hogen sai ya lanƙwashe
ya dubo ƙasa
saɓanin na dawa da zai yi sama. Idan
Bahaushe ya ce ‘an yi malle’ an soke kai ƙasa ke nan.
Zagin Fitan Arziki Ko Na Ɗiban Takaici:
Akwai
zagin na haife ka, akwai zagin na grime ka, akwai zagin burgewa, akwai zagin
kar ta san kar, akwai zagin fitan arziki. Zagin fitan arziki, na nuna takaici
ne, da huce hushi a kan wanda ake jin haushinsa. Irin wannan zagin an fi yin sa
ga iyayen wanda ake jin haushi, ko a ce ‘Shega’ ko ‘ɗan
kazan uwa/uba’. Da makaɗa na ba
Alu na Tambuwal shawarar yadda zai yi wa mai kuɗi
fashi gidansa ya ce:
Jagora:
Kak ka yi mai sata hina kwance
:Jijjigas
shi in shege ya ta da kainai
:Tari
bakin shege da bingida
:Ce,
“In ba kuɗɗi ba ranka”
:Ai
shi ka gwada ma wurin da duk suke
:Bai
fitina bai tad da yaya
Da
aka ɗauko Inuwa (fitaccen ɓarawo
tauraron Gambo) da keke zuwa garin Romo aka tarar da Tsoho Tudu (buwayayyen
tajiri) makaɗa ya ce:
Jagora:
Nac ce Inuwa ga Tudun can
:Shegen
tsoho ah hakan ga
Bayan
makaɗa ya je ya wasa Tsoho da kirari ya
dawo kan Inuwa sai ya ce:
Jagora:
Inuwa ka jiya hwa
:Yac
ce: “Mu je ka majiɗi kak ka damu”
:Wancan
shege ni ka bi nai
Da Canda
(fitaccen ɓarawon tumaki)
ya kawo wa makaɗa ragunan layya.
Makaɗa ya tambaye shi ina aka samo su?
Ya ce:
Jagora:
Uban wani yaɗ
ɗaure su cana
:Sad
da zai musu wanka
:Da
sun ka ɗau dara
:Sai
yag gilma nay yi ƙyacci
:Nac
ce masa shege ba ka cin su
:Mai
jinjina turaye ka cin su
Duk
wuraren da aka yi amfani da kalmar ‘shege’ zagin ɗibar
takaici ne ga mai abu. Wannan na nuna, an daɗe
ana jin haushinsa, tun ba a kai ga dukiyarsa ba sai an zage shi an ɗebe
takaici, idan aka je ga dukiyarsa, in ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba masai.
Idan
aka samu tazara, za a yi zagin yankan ƙauna da za a kai ga iyaye kai tsaye. A
nan, makaɗa ya fi amfani
da kalmar “’yan gaton uwa” ƙarshen
zagin ya kasance ‘shaggu’, jam’in ‘shege’. A cikin taken Dikko Canda, makaɗa
ya san Dikko na sauya wa dabbobi launi. In baƙaƙe ne, su koma farare, in farare ne su koma
jajaye, ga su nan dai. Komai wayon mai samu, ba ya kama dabbar da ba irin
launin tasa ba, ko ya gan ta ga hannun sanannen ɓarawo
Canda. Ba a bar mai abu da wahalar neman dabbarsa ba sai da aka ce:
Jagora:
Mai biɗar
akawal
:Bai
kama danda
:Komai
wayon ɗan gaton uwa
Da
yake ba ɓarayin shiga ɗakuna
shawara cewa ya yi:
Jagora: Ɗebo wuta sa ta ga bunu
:Har
ta ruru
:Ka
sa ta ga zauren ‘yan gaton uwa
:Lokacin
da wuta tat turnuƙe
sama
:Ba
ta ɓarawo za a yi ba
Da
makaɗa ya juya wajen masu kuɗi
ya ce:
Jagora: Mai kuɗɗi
in ba shi kyauta
:Sara
nika dubin ɗan gaton uwa
:Don
akwai ni da mai ɗiba ga bainai
Waɗannan
zage-zage duka, na fitan arziki ne, na yankan ƙauna, ba a yin su, sai rai ya ɓaci,
an ɗebe kunyar wanda ake sa-in-sa da
shi. Bisa ga ma’aunin zamantakewa, mai furta su, wani ƙurjin takaici ne ya yi masa maruru
a zuciya da babu wata sakiya da zai yi wa ƙololon, face furta zagin yankan ƙauna. Idan aka furta zagin sai a ji
ɗan sanyi-sanyi na rashin da ake
dambe da shi, sauran marasa su dara haushin ya rage.
Mutuwar Mai Samu:
Marashi
ba ya da kowane irin tausayi ga mai samu idan ya tuna da irin wahalar da mai
samu ke son ya gan shi a ciki. Da yawa za ka ji, idan lebara na faɗa
da uban-gidansa, zai nuna bai ƙi
uban gidan ya mutu ba. Wai shi a ganinsa, mutuwar mai samu ita ce mutuwar mai
rai, amma ta marashi ai mutuwar matacce ce. Makaɗa
ya ziyarci irin wannan ra’in wurin da yake nuna ba ya son a yi sata, a ƙyale mai samu ba a kashe shi ba. Buƙatarsa ita ce:
Jagora: Kway yi sata day yanzu
:Yab
baro mai kuɗɗi da rainai
:Allah
Ya isa min za ni cewa
:An
yi ta ne don ta da yaya
:Kyawon
sata ta satu
:Ba
a ga kuɗɗi babu mai su
:In
ishe tsohi na hawaye
:In
ishe mata sun yi yakkwat!
Muradi
dai a kashe mai samu kamar yadda ya kashe marasa da ransu. Takaicin ya kai ga
ba kuɗɗin kaɗai
ake son a raba shi da su ba, ransa ma dole a raba shi da shi, domin ka da a
raba shi da kuɗi, ya rayu, abin
ya sake dawowa, ya ci gaba da shan jinin marasa. A ganina, wannan takaici shi
ne na ƙoli,
domin Hausawa sun ce, ƙarshen
tika-tika tik! Ashe gaskiyar Kassu Zurmi da yake cewa:
Jagora: Mai abu ja, marar abu ja!
:Wallahi mai abu kauce
:Ka da wahala tai she ka
Ganin Hasara/ Ruɓushi:
A
al’adar rayuwa, duk mai burin ganin hasara, bai mallaki abin hasara ba. Wanda
duk ya mallaki abin da ba ya son ya yi hasara, ba ya son ya ga hasara. Irin
wannan fahinta ce wasu ƙasashen
duniya ke bi, su haɗa jari da
talakawa da ma’aikata a gina gidaje, da kamfuna, a saka jarin kowa a ciki.
Falsafar ita ce, ko da za a yi wa gwannati zanga-zangar ba-mu-so, ba za a yi ƙone-ƙonen gidaje da masana’antu ba, domin
hannun kowa na a ciki. Don haka, babu mai son jawo wa kansa hasara. Marashi,
saboda irin takaicin da yake da shi, ga mai samu, sai a ga yana ta ɗokin
ya dai ga hasara, ya je ya ba da labari. Makaɗa
ya tabbatar muna yana daga cikin marasan da ke da irin wannan tunanin ga masu
samu. Nazarci wannan ɗan waƙa ka gani:
Jagora: Don ɗai
in ga hasara
:An
ka haihe ni
:In
tahiya ta in da za ni
:Ba
don wani daɗi mai yawa ba
A
wani ɗan waƙa yana cewa:
Jagora:
Ni dai in ga hasara ɗanya-danya!
:Ko
ba a ban sisin kwabo ba,
:Gambo
in ji awa na taki Arhwa
:Tun
da mai abu ya koma matcaci
A
wani ɗan waƙa irin wannan yana cewa:
Jagora: In dai ji hayagaga ina tsaye
:In
ji gari ya ɗebi yaya
:In
ji maƙwabta na
hwaɗin: ‘Ar!’
:Mun
ji awa an taki darni
:An
taɓi soro an tumaye
A
cikin waɗannan ɗiyan
waƙa uku,
babu wurin da makaɗa ya nuna abin
da ya samu ko zai samu. Ya dai nuna, an riga an yi hasara. Wa ya yi harasa? Mai
abu. Idan da bai mallaki komai ba, ba zai yi hasara ba. Tunanin marashi ga irin
halin wasu masu miyagu, maƙetata,
shi ya sa wasu marasa ke son ganin hasara a kan tunanin nan na Bahaushe da ke
cewa: ‘In don kare a yi gobara, ya laƙe bundi (wutsiya) ya bi kassuwa.’ Karen
bai samu komai ba, bai fita da komai ba. Haka marashi ke so ga mai samu ya dai
gan shi:
Jagora: Ya yi saƙwamƙwan!
:Ya
yi jangwan!
:In
ga hawaye na zubo masa
:Ko
na abin shan koko bai da
:Sai
dangi sun ba shi rance
:Gambo
in ji awa na taki Arhwa
:Don
uban wani ya koma matcaci
Ƙyacewa Da Haƙewa
Tsakanin
mai samu da marashi haka yake kamar dangantakar ɓera
da kyanwa. A koyaushe marashi yana ƙyace wa mai samu, shi kuwa mai samu yana
haƙe da shi.
Idan takaici ya yi takaici, za a ji, wanda takaicni ya kai wa ko’ina ya yi na
jaɓa (kulɓa)
wato ƙt! A
kowane baki waɗannan harufa
suka fita, cikin ƙirjin
da babbar magana ta takaici. Da makaɗa
na hira da Tsoho Tudu gabanin su fara shiga manyan labaye cewa ya yi:
Jagora: Ga mu nan tahe da ni da baba
:Ƙemus-ƙemus! Ni da baba
:Rangai-rangai!
Lahiya lau
:Hirab
banza ta ni kai mai
:Nic
ce: “Ƙt!
Wallahi kana gane kurenka baba.”
Bayan
an ƙyace wa
baba, aka sake haƙe
shi. Idan haƙewa,
da ƙyacewa,
suka haɗu, sai rai ya ɓaci
fuska ta sauya, kamar dai yadda Gambo ya taras da Inuwa, bayan ya wasa tsoho
Tudu yana cewa:
Jagora: Kan da in dawo in da Ɗanmoɗwacci
:Mugu
na taunan haƙora
:Nag
ga hina murza’ idanu
:Nag
ga idanun sun yi jawur
:Yac
ce: “Kt! mu je ki mashiɗi kak ka
damu”
:Wancan
shege ni ka bi nai.”
Ban
musanta akwai ciwon sata ga Sani na Zauro (ƙwararren ɗan
sane ne) ba, amma irin takaici da haushin da yake da shi idan ya ga mai kuɗɗi
a kasuwa, ya kwararo shi, bai kai ga aljihunsa ya yanka ba, makaɗa
na cewa:
Jagora: Mai kamas shi yi ƙwace
:Sani
ɗan moɗen
Zauro
:Aradu!
:In
yak koro bai cika ba
:Sai
ka cimma hawaye na zuba mai!
Modde
ya’e! Haba! Ka san takaici ya yi takaici, ƙyacewa ta yi ƙyacewa, domin abin ya zarce ƙyaci, da cizon haƙora, da cizon yatsa, ya kai ga
zubar hawaye, irin na mujahidi idan ya rasa shahada. Wallahi kowane mahassadi
haka yake idan hasada ta zaburo masa, ba zai san ya yi ƙyaci ba, ko launin idanunsa ya
sauya, wani lokaci hawaye kan zuba bai farga ba. Haka hasada kan tona wa mai
ita asiri ba da saninsa ba, a gane shi.
Sakamakon Bincike:
Rashi
wani abu ne mai muni da kowa ke gudu rayuwarsa. Samu wani abin so ne ga kowa ƙin wanda ya rasa. Yadda samu yake
da wuya, a faɗar Bahaushe, kuɗi
masu gida rana. Wani lokaci ya ce, “Kowa ya ci zomo ya ci gudu;” ko “Zomo ba ya
kamuwa daga kwance;” ko “Babu maraye sai raggo.” Duk isharorin na nuna wa
jama’a cewa, mai nema yana tare da samu. Duk irin wuyar da aka sha gabanin
samu, irinta ce marashi ke ciki. Idan marashi na tunani da irin tunanin da
al’adarsa da adabinsa suka tanada, batun ya shiga tunanin ya yi sata ba ta taso
ba. Dalili kuwa shi ne, wanda duk ya samu, sai da ya sha wahala. Don haka, duk
wanda zai raba shi da abin, sai ya sha wahalar gaske ta neman dabarun da zai
bi, da yadda zai fita, idan ta rutsa da shi. Da yadda zai tsira da mutuncinsa,
idan ba ta rutsa da shi ba. In haka ne, ai gara a yi tunanin yadda za a nemo na
kai ya fi. Dukkanin tunanin da makaɗa
Gambo ke yi, na nuna haushi da takaici, bai nuna wurin da ya yi ɗan
yunƙurin
neman na kansa ba. Da ya yi yunƙurin
na kansa, da zai ci karo da samu, in kusa in da nisa. Abubuwan da ke tattara
takaici da haushi a zukatan marasa zuwa ga masu samu su ne, rashin ƙoƙarinsu na tashi su nemi na kansu.
Duk
da haka, Hausawa na cewa, idan an ga ta ɓarawo,
a dubi na mai kaya. Nason mulkin mallaka da ya haɗo
da hayaƙin
gurguzu, da jari-hujja, da tsarin demukraɗiyya
ya barbaɗa a daulolin ƙasar Hausa, ya ci zarafin tunanin
Bahaushe ainun. Rashawa, toshiyar baka, alfarma, zurmuguɗɗu,
da ci-da-ceto, su suka rikita ƙarshen
zamanin da muke ciki. Mai bakandamiya ya yi wannan hasashe a ƙarshen zamani yana cewa:
Mai akwai a hana masa godiya,
Mai babu ko a hana masa
dangana.
A koyaushe, mai
akwai buƙatarsa
ya ƙara, a
taru wajensa ana bauta. Marashi ya kasa dangana ya ari halin da ba nasa ba, ba
na iyayensa ba, ya yi ƙaurin
suna cikin mutanen alƙaryarsu.
Wayyo! Da marasa za su ɗauki ƙaddara, su dangana su nemi ɗan
abin da ya sawwaƙa,
da sai mai samu ya rasa wanda zai bautar, ko dai ya yi kyauta, ko dukiyarsa ta
ruɓe.
Naɗewa:
Kiɗan
satar da Gambo ke yi, wata makaranta ce ta fayyace falsafar rayuwar duniyar da
Bahaushe ya rayu cikinta. A bayanin Gambo, ɓarawo
matsiyaci ne, maras zuciya, da kishin kai. Masu samun zamani kuwa, da yawansu
musiba ne ga al’ummar da suka rayu a ciki. Da masu abin hannunsu na taimakawa,
da ɓarayin ɗauka-ruga,
ba su yawaita ba. Takaici da haushin da ke tsakanin mai akwai da marashi, a
koyaushe zuba suke a bakin marashi, domin su zama hannunka mai sanda ga masu
samu. Na jinjina wa Malam Muhammadu Gawo Filinge da ya yi wa talakawa gargaɗi
da cewa:
Jagora: Talakka ba shi cin kifi soye
Yara: Balle ya sha roson zabbi
:Hi
tai mahauta ga ƙiren
hanji
:In yac ci guda biyu ya ƙoshi
Gindi: Ya Allah gyara
:Wahabu
Ka taimaki ‘yan Nijar
Jagora: Miyal kuɓewa
ba tau ta ba
:Mu
samu dai yoɗonmu ya gyaru
Yara: Mu samu wake da ruwan toka
Jagora: Haka nan na!
Gindi: Ya Allah gyara Wahabu
:Ka taimaki ‘yan Nijar
Matuƙar kowa bai tsaya matsayinsa ba,
takaici da haushin juna, ba ya gushewa a zukata. Babu wani magani, face samun
daidaitaccen tsari da zai tanada wa gaskiya wurin zama na gari. A ganina,
shari’ar Musulunci kaɗai ce
mafita.
Manazarta:
Aliero, H. M. 2000: “The Implication of Money Laundering on
the Nigerian Economy”, paper, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Aliyu, A. Fasaha Aƙiliya, NNPC, Zaria.
Auta, A. L. 1988: “Gudummuwar Waƙoƙin Makaɗan Baka Dangane da
Adana Tarihi.” Kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. 2009: Narambaɗa, Wallafar Lagos:
IBRASH, Publishers.
Bunza, A. M. 2011: “Rashin Sani ya fi Dare Duhu.”: Jami’ar
Umar Musa ‘Yar’adua.
Bunza, A. M. 2012: “Lalurar Kiɗa a Bakin Makaɗa” muƙala, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Bunza, A. M. 2012: “In ba ka San Gari ba Saurari Daka:
Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo”, kammalallen bincike ba a wallafa ba.
Burton, S. H. 1954: The
Criticisms of Poetry, London: Longman.
Daba, H. B. 2006: Ɗanmaraya Jos in
Hausa Folkloric Perspectiɓe, Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S. M. 2009: “Waiwaye a kan Tarihin Rayuwar Alhaji
Muhammadu Gambo na Kulu Makaɗin Ɓarayi”, muƙala: Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Maiyama, U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar Hausawa: Nazarin
Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Muhammad, D. 1977: “Indiɓidual Talent in
Hausa Poetic Tradition a Case of Aƙilu and his art”,
PhD, London: SOAS.
NNPC, Gangar Wa’azu,
Zariya.
Rasmussen, D. 1974: Poetry
and Truth, Paris: Monton.
Rodney, W. How Europe
Under Deɓeloped Africa,
Tukur, T. 1984: “Mawaƙa da Matsayinsu a
Al’umma” cikin: Studies in Hausa Language
Literature and Culture, The First International Hausa Conference, Kano:
Jami’ar Bayero.
Umar, M. B. 1977: Ɗanmaraya Jos da Waƙoƙinsa, Zariya: Hausa Publication Centre.
Umar, M. B. 1980: “Tattalin Arzikin Hausawa na Gargajiya”,
Kano: Jami’ar Bayero.
Yahya, A. B. 1996: “In Praise of Theiɓes: An odd Category
in Hausa Oral Poetry” Paper, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Zurmi, M. A. 1986: “Rayuwar Alhaji Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa” Kundin
digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
No comments:
Post a Comment