Monday, December 31, 2018

Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe



Matakan rayuwar Bahaushe ba su samu kulawar masana da manazarta da ɗaliban nazarin Hausa sosai ba. Wannan takarda ta lalubo matakan rayuwar Bahaushe uku: aure, da haihuwa, da mutuwa. Ta ɗauki kayan cikin littafin Ruwan Bagaja gaba ɗaya ta ɗora su a kan waɗannan turaku uku. An nazarci rawar da suka taka wajen kai littafin zama zakaran gasar 1933. An yi garkuwa da matanonin nassoshin littafi wurare ashirin (20) a ƙunshiyar kayan cikin takardar. An gano wurare goma sha uku (13) da aure ya taka rawar gani. An ƙyallaro saƙonni goma sha uku (13) da aka isar ta fuskar haihuwa. An tantance wurare ashirin da bakwai (27) da aka yi garkuwa da mutuwa domin isar da saƙo ga masu karatunsa. A jimlace matakan rayuwar…
Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe

Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina.
08034316508


TSAKURE

Matakan rayuwar Bahaushe ba su samu kulawar masana da manazarta da ɗaliban nazarin Hausa sosai ba. Wannan takarda ta lalubo matakan rayuwar Bahaushe uku: aure, da haihuwa, da mutuwa. Ta ɗauki kayan cikin littafin Ruwan Bagaja gaba ɗaya ta ɗora su a kan waɗannan turaku uku. An nazarci rawar da suka taka wajen kai littafin zama zakaran gasar 1933. An yi garkuwa da matanonin nassoshin littafi wurare ashirin (20) a ƙunshiyar kayan cikin takardar. An gano wurare goma sha uku (13) da aure ya taka rawar gani. An ƙyallaro saƙonni goma sha uku (13) da aka isar ta fuskar haihuwa. An tantance wurare ashirin da bakwai (27) da aka yi garkuwa da mutuwa domin isar da saƙo ga masu karatunsa. A jimlace matakan rayuwar Bahaushe sun taka rawar gani a wurare hamsin da uku (53) ana warwarar jigo da saƙar zaren tunanin saƙon littafin. A kula, gutsattsarin labaran da aka gina littafin gaba ɗaya hamsin da biyar (55) ne. sakamakon bincike ya feɗe biri har wutsiya. Da haka, takardar ta yanke hukuncin kowane irin sashe na adabi ana iya kallonsa a matakan rayuwar mutanensa. Yin ko oho da waiwayen matakan rayuwar mutane wajen nazarin ayyukan adabinsu da hikimominsu, kure ne babba ga ɗalibai da malamai da manazarta da masana. Da adabi da harshe, duk al’ada ta haife su. Don haka, dole ne a kula da ita idan ana son a fahinci hankalin ‘ya’yanta.



GABATARWA:
Dalilan da suka sa littafin Ruwan Bagaja ya lashe gasar rubutattu ƙagaggun labarai a shekarar 1933 sun cancanci a yi bitarsu.[1] Ba ina nufin bitar dacewar hukuncin alƙalan ko akasin haka ba.[2] Manufata ita ce, a ji mazan jiya, a saurari mazan jiya, a karanci mazan jiya, a ɗora su a sikelin tunanin zamaninmu.[3] Yau[4] kimanin shekaru tamanin da haihuwar littafin amma koyaushe kamar shekarar da ake ciki aka rubuta shi.[5] A hangen manazarta fannoni daban-daban, duk da wani abin da manazarci ke buƙata, ba a rasa wurin da za a nazarce shi a littafin ba.[6] Ganin haka, wannan takarda ta himmatu ga leƙen “Matakan Rayuwa”[7] da yadda aka yi sinadari da su wajen ƙulla zaren tunanin littafin.



MATAKAN RAYUWA:
A falsafar al’ada, kowane mutum matakai uku yake hawa a rayuwarsa.[8] Matsalar da masana da manazarta al’ada suka daɗe suna fuskanta ita ce, tsayayyun hujjojin jeranta matakan.[9] A tunanin Bahaushe, matakan su ne, aure; da haihuwa; da mutuwa. Taƙaddamar da ke nan ita ce, da aure da haihuwa wane aka fara yi a duniya? Idan an bi mahangar addini muhawarar ƙurarra ce.[10] Idan aka shimfiɗa ta a faifan nazarin al’ada da kimiyya da hankalin tuwo abin zai fi zare tsawo.[11] A ganinmu ɗaliban al’ada, duk wani mutum da ya rayu a duniyar mutane, waɗannan matakai uku su ne turakun rayuwarsa. Ba za su taɓa riskuwarsa gaba ɗaya ba.[12] Babu yadda zai tafiyar da su gaba ɗaya. Ala tilas, kowannensu turken kansa yake da shi, sai an fita turke ɗaya, a faɗa ɗaya, bi da bi. Don haka muke ganin, komai kaifin tunani da basirar mutum, da zantukansa da rubutunsa da ayyukansa da tunaninsa a kan turakun suke tafiya sau da ƙafa.[13] A nawa nazari, waɗannan matakan suka taimaka wa Abubakar Imam ga fitar da basirarsa yadda Bahaushe zai saurare shi ya fahince shi.
Kowane irin tubali wani manazarci ko masani ko ɗalibi zai yi hasashen da shi aka gani tubalan littafin Ruwan Bagaja; idan bai waiwayi matakan rayuwa ba, bai yi wa nazarinsa susa gurbin ƙaiƙayi ba. Masu hangen tubalan ta adabin Larabci, Larabawa na da matakan rayuwa.[14] Masu bin diddigin adabin baka, su sani cewa, kowane adabi a kan matakan rayuwa yake sheƙe ayarsa.[15] Babu shakka, duk abin da bakin ɗan Adam zai furta ko alƙalaminsa zai rubuta, dole a samu nason matakan rayuwarsa kane-kane a ciki. Taƙaddamar jeranta matakan rayuwa ba abin da za a gama ba ne.[16] Don haka, zan tattauna su yadda na ambace shi.

AURE:
A mahangar al’ada, aure shi ne amintuwar jinsi biyu mabambanta (mace da namiji) masu rai na zama tare da miƙa wuya ga juna.[17] Idan sandararrun abubuwa ne na itace da tsirrai sai an haɗa jinsinansu kalmar aure ke tabbata.[18] Da mutane da dabbobi da ƙwari ana tantance aurensu ta fuskar yadda suke hulɗa da juna.[19] Ma’anar aure takan faɗaɗa zuwa kusantar juna da haɗa jiki[20]. Burin takardarmu gano gurbin aure a mahaɗin tunanin Abubular Imam ga ƙulla zaren gutsatsarin labaransa a shahararren littafinsa Ruwan Bagaja.

TUNƘA ZAREN TUNANI A KAN MATAKAN AURE:
Zaren tunanin gina labaran littafin Ruwan Bagaja ga aure ya samu tushe. Yayin da Koje[21] ya sadu da Imam ya zuba labarai daga safe har magariba (Imam, Ruwan Bagaja. 2:3). Ba a gaya muna labaran da Koje ya bayar ba. Da Imam ya so ya mayar da zubin adashin magana sai ya ce:
Na farko dai in ji maigida, sunana Alhaji Imam. Ubana kuwa wani babban malami ne na Sarkin Sudan. Sunansa Malam Na-Bakin-Kogi. Sai da ya kai dattijo har ya tsufa, ba a taɓa ko ɓari ba gidansa. Abin da ya dame shi ƙwarai ga wagagen littattafai ba mai gado. Amma ko da shike malamin nan ba shi da ɗa nasa na cikinsa yana da wani agola, shaiɗani ana kiransa Saƙimu, kome uban nan nawa ya yi masa uwar ba ta godewa, shi yaron ba shi godewa.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, Shafi na 3, sakin layi na 1).

Wannan ɗan bayanin shi ne tushen littafin. Da za a cire shi, an gurgunta duk abin da zai biyo baya. Imam ya fara gabatar da sunan mahaifinsa. Ishara ce mai nuni da cewa, sai an yi shuka ake zancen tumu.[22] Ambaton ubansa da sunan “ubana”, ko ba a kawo sunan mahaifiyarsa ba an san da aure aka haife shi. Bugu da ƙari, aka sake bijiro da wani babban turke daga turakun aure wato samun rabuwar aure ta rashin fahintar juna ko mutuwa. Dalilin haka ne uwar Saƙimu ta zo da ɗanta agolan malam (Saƙimu) a gidansa. Da Imam ya so ya ƙara ɗaure turken aure sosai, ya nuna bayan Saƙimu ya aikata abin da ya aikata, sai ya ce:
Matan suka yi ‘yan koke-kokensu na al’ada suka bari. (Ruwan Bagaja: Babi na 1, Shafi na 4, Sakin layi na 2).

Kalmar matan ta nuna ba mata ɗaya ke ga malam ba. Babban dalilin aure na kowane jinsi shi ne samun zuri’a. Bahaushe idan bai samu zuri’a ga mace ba zai ƙaro wata domin neman dacewa ko da kuwa matsalar haihuwar daga wajensa take. Wannan wani babban turke ne ga littafin, domin da zaren labarin ya so ya tsinke, sai aka kuɓutar da Yaƙutatu mahaifiyar Imam yana cewa:
Uwar nan tawa kuwa ana ce mata Yaƙutatu. Da ta yi arba’in aka ɗaura musu aure da Liman.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, Shafi na 4, Sakin layi na 2).

Da ba a kuɓutar da mahaifiyar Imam ba, da zaren tunanin Abubakar Imam ya tsinke.[23] Ƙara kawo tubalin aure na Yaƙutatu da Liman ya sake raya riwayar ta ci gaba da ɗinkewa da ginuwa har ƙarshen littafin.
Da gutsattsarin labaran da aka tsara a babi na farko aka tuƙe su. Babin ya ƙare, sai aka buɗe sabon babi na biyu. A babin, Imam ya isa birnin Yamel. Tafashen kalangai da gangunan da ke tashi da kakaki da algaita da farai, su suka yi wa Imam maraba a garin. Ya tambayi yara me garin yake ciki. Suka gaya masa:
Mowar sarki aka kawo wa mata yau.
Na ce, “Daga ina?”
Yaron ya ce, ‘yar Sarkin Ƙaryatun Ni’am aka gama su.
(Ruwan Bagaja: Babi na 2, shafi na 10, sakin layi na 1 – 2)
          Da wannan shagalin aure aka yi wa babin turke duk gutsattsarin labaran da suka biyo baya ‘yan rakiya ne.[24] Haka kuma, auren shi ne maganaɗinson ƙulla zaren tunanin babi na biyu da uku. Da an yi kuren wannan turken, da fasahar da aka tsaro ta bargaje. Cikin rigimar bikin auren aka zarce zuwa garin Sasa. A can aka gamu da Ƙwara. Da aka tsere wa Ƙwara,[25] aka haɗu da Baƙauye mai jaka.[26] Aka faɗa kurkuku, aka fito aka haɗu da mahaukacin raƙumi aka haɗa shi da Fulani,[27] har dai aka shiga birnin Ris. Daga haka har labari ya zo na rabuwarsa da Zurƙe. A nan babin ya tsinke ko ya tsaya.
          Turken babi na uku garin Ɗandago aka fara yada zango. Yana shiga garin garin Ɗandago ya ce:

A can na sami wata yarinya, ‘yar wani malami, ana ce mata Jamilatu. Ka san ni da rigima, sai na shiga biɗar aure. Muka shiga kai toshi, yarinya kuwa ba ta fid da wanda take so ba. Kai, muka yi ta cacar kuɗi dai ba haddi. Rannan fa sai na je na gaya wa uban, na ce ya kamata yarinyan nan ta fid da wanda take so, kowa ya huta.
(Ruwan Bagaja: Babi na 3, shafi na 14, sakin layi na 2).

A turken aure aka ƙaddaro da makaftarsa.[28] A turken aka sada shi da Arme.[29] Daga nan sana’ar ‘su’ ta shigo don ta sake sada shi da Zurƙe.[30] Bayan nutsewarsa a kogi da haɗuwarsa da ‘yan ruwa sai garin Baku. Aka ƙulla gutsattsarin labaran Zandoro ɗan Zotori. Daga nan aka kawo labarin gawar bawan sarki. Bayan abin da ka aukuwa ya auku, aka ja zaren labarin zuwa babi na huɗu.
          Zaren tunanin babi na huɗu da turken aure aka sarrafa shi. Domin kuwa bayan ya tambayi fatake labarin Zurƙe da gawa, aka gaya masa ba a kashe Zurƙe ba an dai ɗaure shi, sai ya ce:
Ina yawo a kasuwa ran nan ina tambayar labarin Ruwan Bagaja, sai na ga wata yarinya na ce zan aura. Ashe tana da miji ba ta sonsa ne kawai. Na kira ta muka shirya ta ce in zo yau da dare. Daren kuwa aka yi maraice da ruwa. Cikin ruwan nan mijin ya dawo, ta hura masa wuta yana ƙahon dandi.
(Ruwan Bagaja: Babi na 4, shafi na 19, sakin layi na 7 – shafi na 20, sakin layi na 1)

Da neman aure aka ƙulla zaren tunanin wannan babi. Da kuma auren dole ko auren ƙiyo aka fara warware jigon babin aka daidaita masa fuska.[31] Duk auren da ba a gina a kan soyayyar ma’aurata ba, ƙarshensa a shiga wani hali mawuyaci. A kan wannan tunani ne Abubakar Imam ya sakaɗo da matsalar kwartanci da zina.[32] Auren dole na sa mata fita ba da kamun kai ba. Yana sa mace neman mazaje irin waɗanda take so. Da aka fara tunƙa akalar gutattsarin labaran da ke ƙunshe a babin. Yunƙurin kore kunya da hukuncin kwartanci ya sa aka gabato da haukar Imam da samun sarautar Wawan Sarki[33] har ya samu shiga fada sosai aka tuƙe babin daga nan.
Abin ban sha’awa, fasahar babi na biyar da tubalanin aure aka fara gina ta, aka kuma yaɓe ta da shi, katangar ta yi ƙarfi. Imam a garin Tegi ya fara yada zango. Da masarautar ta yi maraba da shi, sai sarkin garin ya gabatar da damuwarsa ga Imam a kan Sarkin Zaginsa ya ce:
Kai, ni dai Sarkin Zagi ya dame ni. Ba ya ko barina in yi barci.
Waziri ya ce, “Saboda me, ranka shi daɗe?”
Sarki ya ce, ai ka san tun watan jiya matarsa ta mutu. To, tun daga ran da ta mutu har yau, kullum ba ya barci. Da tsakad dare sai ya tashi yana waɗansu waƙe-waƙe kamar mahaukaci, yana cewa da ma shi mutuwa ta ɗauka ta bar matar da ya huta.
(Ruwan Bagaja: Babi na 5, shafi na 22, sakin layi na 1 – 2).

Daga cikin aure babu abin da ya kai soyayya daɗi. Tsananin so ke sa ma’aurata ɗokin ganin junansu. So na haƙiƙa ke sa ko an rabu a gangar jiki zuciya na ƙyallaro juna ka ce tare ake.[34] Bayan da aka ƙulla babi na huɗu a kan auren dole. Aka zo a babi na biyar, aka tunƙa zaren tunaninsa da auren soyayya wanda mutuwa kaɗai ta raba. Bayan da ta raba, mijin da ke raye ya kasa haɗiye takaicin rabuwa da masoyiya. Duk gutsattsarin labaran da aka ambata a babin suna tafiya da wannan tubalin na aure jejjere kamar kashin awaki. Da aka zo rufe babin, bayan an haɗa mata da miji faɗa kan gawa sai aka naɗe babin da cewa:
Na tafi wurin ‘yan fura in saya, sai wata mace ta taka mini hannun riga, zan yi magana ta zage ni, ta ce wai, “Lebura fa ba wanda ya fi shi izza.”
Na dubi macen da ta ce mini lebura, na ga ko tsarar ƙanwata ba ta yi ba. Na ce, “Ni ban yi sai da mijinki”.
Ta dube ni da fushi ta ce, “Ƙarya kake yi, Malam Zurƙe ya fi ka, kada ka gama kanka da shi.”
(Ruwan Bagaja: Babi na 5, shafi na 25, sakin layi na 10 – shafi na 26, sakin layi na 1).

An ƙi sa Imam ya kashe ta mari, da nan labarin ya tuƙe. Aka bijiro da martabar aure, ya sa mata ido.[35] Aka harzuƙa shi ya nemi mijinta. Aka tsokane ta aka gane tana da miji. Aka haɗa haɗuwarta da mijinta da Imam ya zama tabarmar naɗe babin.
Tunanin Imam a babi na shida bai sauya ba. Da ya shiga garin Miska ɓarayi suka dame shi daga cikin ɓarayin sai da aka kawo Malam Zurƙe. Dalilin kawo shi domin a ji abin da ya faru da shi da matarsa na kore wa kashin Imam ƙuda.[36] Aka gina babin da matsalolin da ke tattare da auren fitinannun mata mafaɗata. Aka bijiro da matsalar rabuwar aure a mataki na biyu wato jidalin mace da musibobinta da take jawo wa mai gida da gidansa. Rabuwar Zurƙe da matarsa ta sa ya zama gwauro har ɓarawo ya ziyarce shi da dare.[37] Daga cikin shika-shikan labaran babin akwai labarin marin matar Zurƙe wanda su suka ɗinke babin sosai suka yi masa turke managarci.[38]
Babuka biyu, na bakwai da takwas naɗe labaran ne. Babi na bakwai tubar manyan taurarin labaran ne. A babi na takwas, an samu biyan buƙata an dawo gida. Ko a nan aka tsaya, an san da babu tubalan aure cikin littafin da ƙunshiyar ta kasance holoƙo. Aure wani babban artabo ne a fafitikar rayuwar Bahaushe. Gwagwarmaya da adawar da ke ciki tsakanin masu nema bayyane yake a auren Jamilatu ‘yar Malam. Ranar ɗaura shi wata sabuwar salla ce ga iyaye da amare. Kaɗe-kaɗe da bushe-bushen da suka game garin Yemel a auren Mowar Sarki da ‘yar Sarkin Ƙaryatun Ni’am shaida ne a kan haka. Zamantakewar Malam Na-Bakin-Kogi da Sarkin Zagi da iyalansu wani manuni ne ga auren soyayya. An gabatar da matsalar kwartanci da zina domin a fito da hoton auren dole da aka yi wa yarinyar da ta gayyaci Imam da Zurƙe gidan mijinta. Mutuwar aure da sakin aure da zaman gwauranci duk sun taka rawar gani ga nishaɗantar da mai karatun littafin.

HAIHUWA:
Ko itace da tsirrai aka ɗaura wa aure buƙata su samar da ‘yan’yan da za a yi amfani da su.[39] Tubalin haihuwa wani babban tubali ne a matakan rayuwar Bahaushe. Turakun manyan babukan littafin a kan tubalin aka gina su. Wajen yunƙurin warware ƙunshiyar tubalan, haihuwa ta taka rawar a zo a gani. A tunanin Bahaushe, haihuwa haske ce, rashin haihuwa duhu ne, mai kashe gida, ta turbuɗe tarihin zuriya, da saka baƙin ciki ga mai shi, da danginsa.[40] Tunanin Bahaushe a kowane sassan adabinsa ‘ya’ya na da babban kaso a kayan cikinsa da saƙonnin da ke tarshe ciki. Idan aure na da muhimmanci, to haihuwa tana gaba da shi. Dalili kuwa shi ne, idan dai sai da aka haihu aka yi aure. To! Waɗanda suka yi aure yaya aka same su? Babban dalilin kowane aure shi ne haihuwa, domin da an rasa haihuwa tarihin aure ya kawo ƙarshe.[41] Wannan matakin rayuwar ya taka muhimmiyar rawa ga gina littafin Ruwan Bagaja da fito da hazaƙar murubucinsa.
Idan ana biye da zaren tunanin wannan takarda, za a ga babi na farko Abubakar Imam ya ambaci mahaifinsa babban malami ne ya ce:
Sunansa Malam Na-Bakin-Kogi. Sai da ya kai dattijo har ya tsufa ba a taɓa ɓari ba gidansa.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 3, sakin layi na 1).

Sanin darajar haihuwa da irin ƙimarta a rayuwa ya sa aka fara aza harsashen littafin da ita. Rashin samun ta shi ya ambata da: “Ba a taɓa ɓari ba gidansa.” Rashin samun ɓari ga mai mata fiye da ɗaya (huɗu) irin Malam, wata shaida ce ta nuna matsalar daga gare shi take. Duk da yake malami ne, ba a nuna ya yi wani yunƙuri na samun waraka ga matsalar ba. Haka su ma matan, ba su yi wani yunƙuri ba.[42] Duk wannan na daga cikin fasahar jan zaren tunanin marubuci. Domin nuna martabar haihuwa sai aka ce:
Amma ko da shi ke malamim nan ba shi da ɗa nasa na cikinsa, yana da wani agola, shaiɗani, ana kiransa Saƙimu.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 3, sakin layi na 1).

Kawo zancen “agola” fito da matakin rayuwar Bahaushe ne na haihuwa.[43] An auro mai yaro domin fatar a sami haihuwa. Saboda ta taɓa haihuwa, an zo da ita gidan, ko ba ta haihu ba, a riƙa yaronta kamar ɗa. Da wannan tunanin aka gina fasahar littafin gaba ɗaya.[44] Da za a cire Saƙimu da dukkanin muradin marubucin an salwantar da shi. Haka kuma, labarin wannan agola shi ne mataki na farko na saƙon littafin Ruwan Bagaja.
Mataki na biyu na saƙon shi ne, rashin lafiyar Yarima ɗan sarki. Abin da ya muhimmintar da wannan rashin lafiya shi ne kasancewar Yarima ɗan sarki ne. Da yaron sarki ne ko bafadensa ko ɗan maƙwabcinsa ko wani basarake daga cikin sarakansa, wanda ba ɗan tsatsonsa ba, da abin bai kai haka ba.[45] Ai saboda tsananin damuwar sarki na ɗansa ba ya da lafiya ya sa ya ci mutuncin Limaminsa. Cin fuskar da aka yi wa Liman ita ce mafarin fafitikar neman Ruwan Bagaja. Ga yadda aka tubka zaren fasahar:
Wai don yau ana cikin fadanci, Sarki ya ce ɗansa Yarima ba ya da lafiya, sai an kwantar a tayar. Ni kuwa na ce da za a sami Ruwan Bagaja a wani gari, da mutanen garin nan duk sun huta da masassarar zamani.
Daga wai na faɗi ‘yar wannan, sai sarki ya harzuƙa, ya ce wai ba’a ce nake jan shi da ita. Ya ce wai in ba shegantaka ba, da shaƙiyancin da na saba, ina na taɓa ganin wanda ya sami Ruwan Bagaja a duniya?
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 5 sakin layi na 7 – shafi na 6, sakin layi na 1).

Duk wata wahala da aka shiga ta neman Ruwan Bagaja wannan ne musabbabi. Duk wasu gutsattsarin labarai da aka ci karo da su a fafitikar kai-da-kawon manyan taurari da ƙananan, wannan ne dalili. Duk wani saƙo, da fasaha, da azanci da marubucin littafin ya sarrafa a kan wannan dalili ne.
Warwarar jigon littafin Ruwan Bagaja ba za ta yi armashi ba, idan ba a laluba babi na bakwai ba. A babin aka kakkaɓe wundin karatun arangamar manyar taurarin littafin Imam da Malam Zurƙe. Bayan sun tuba a nan Alhaji ya kashe wansa. Da wannan kisan kan aka kai ga samun biyan buƙata (ɗebo Ruwan Bagaja). Ga ɗan abin da nake son a kula:
Wata rana ne yana cin goriba da dare, sai ya ‘yar da ƙodagon da ya gama ci. Ashe an zo da jinjirin ɗan Sarkin Aljannu wurin su yi wasa. Abin ƙaddara sai ƙodagon ya bugi kan ɗan Sarkin Aljannu ɗaya a maɗiga ya faɗi ya mutu. Shi ya sa aka ɗauko shin an da nan a halaka shi. (Ruwan Bagaja: Babi na 7, shafi na 36, sakin layi na 4).

Haihuwa muhimmanci gare ta ga kowa. Dubi cikin rashin sani aka kashe jinjirin amma Iskoki suka ɗau fansa nan da nan. Da ba don ƙaddarar kashe jinjirin ɗan Sarkin Aljannu ba, da samun takobin da za a samu Aljanin da zai kai Imam ga Ruwan Bagaja ba ta yiwu ba. Dukkanin ƙunshiyar littafin Ruwan Bagaja, idan ba  a kai ga nasarar samo Ruwan Bagaja ba, ba a yi komai ba an raki baƙo ya dawo.[46]
Gabanin a kai Imam ga Ruwan Bagaja, duk faɗi tashin da ya yi, ba a ba su muhimmanci ba. Da martabar girmama haihuwa aka yi masa sakayya.[47] Abin da ake son wanda aka haifa ya yi, shi Imam ya yi wa wanda ba shi ya haife shi ba, don haka aka saka masa da alheri. Dubi wannan:
Lallai ka cika ɗa, tun da ka sai da ranka don uban wani. (Ruwan Bagaja: Babi na 8, shafi na 37, sakin layi na 4).

Haka kuma, kyautata wa jinjirin Aljana da uwar Liman ta yi shi ya sa su abota, har Imam ya shigo cikin wannan alfarmar ya ci nasara. Manazarci al’ada bai yi kure ba idan ya ce, mataki na biyu na daidaita ƙunshiyar littafin Ruwan Bagaja shi ne matakin rayuwa na biyu, wato haihuwa. Da an bar matakin rayuwa na aure shi kaɗai, da hoton littafin bai fito sosai ba. Da aka kawo matakin haihuwa sai abin ya ƙyallaro zukatan masu karatu sosai. Duk da haka, ruhin littafin ba zai bayyana ƙarara ba idan ba a waiwayi matakin rayuwa ta uku ba, wato mutuwa.
Bahaushe ya ɗauki haihuwa da muhimmancin gaske. Don haka, da wuya a tantance, shin ɗa ya fi son mahaifi ko mahaifi ya fi son ɗa? Da aka yi harsashen gina zaren tunani da rashin haihuwa, tubali na farko da aka fara gina da shi, shi ne agola. Abin da ake so ga ɗa ya zama mai jinƙai da tausayi ga iyaye. Da aka fara gini da shaƙiyin agola daga ƙarshe aka zo da nagartaccen agola da ya yi abin da ake son ɗa ya yi. Da jinƙayin da iyaye ke yi wa ‘ya’ya aka ci nasarar samun Ruwan Bagaja. Haka kuma, da zaren tunanin haihuwa aka gama Saƙimu da ajalinsa kamar yadda malaman duba suka dubo masa. Cikin tsanaki haihuwa ta hana zaren tunanin marubucin tsinkewa yadda aka buɗe da ita, da ita aka kammala.

MUTUWA:
A wajen manazarta al’ada, duk fafitikar da masu rai ke yi a duniya, mutuwa ake yi wa ita. Ɗan’adam ya ƙirƙiro noma domin ya yi wa yunwa barazana.[48] Idan aka ƙi noma aka sa wa yunwa ido za ta yi aikinta. Dukkanin yaƙe-yaƙen da mutanen duniya ke yi, ana yin su ne domin kariya ga abin da ke son yi wa rayuwa barazana.[49] Duk tattalin arzikinsu na inganta rayuwarsu ne.[50] Duk tanaje-tanajensu na yi wa rayuwasu kariya ne.[51] Tsananin fasaharsu, da ilminsu, na gano abubuwan da za su ciyar da rayuwarsu gaba ne. Tsarin siyasun rayuwarsu na nema wa zamantakewarsu zaman lafiya ne.[52] Zaman lafiya kuwa muradinsa rayuwa ta samu sakewa ta wartsake, ta shaƙata, ta yi kamar ba ta mutuwa.[53] Duk da haka dai, ƙarshen kowace rayuwa mutuwa.[54]
Bisa mizanin al’ada, mutuwa gado ce ga kowane mai rai.[55] Don haka, tunanin kowane mai rai a zantukansa na baka da rubuce-rubucensa da addninsa mutuwa ke shawagi a ciki.[56] Duk da yake ba a son ta, ba a ƙaunar ta, ana ƙyamar ta, amma dole a tuna da ita. Tuni da ita ke sa a keɓe mata nata gurbi a tunanin masu rayuwa. A ƙunshiyar littafin Ruwan Bagaja, da ba a keɓe wa mutuwa babban kaso ba, da kashi ya game, dole a sake rabawa.
Zancen Saƙimu da Malan Na-Bakin-Kogi su ne harsashin ginin ƙunshiyar littafin. Babban saƙon da ke ƙunshe ga matsalar da Malam Na-Bakin-Kogi ke ciki shi ne:
Ga wagagen littattafai tuli, ba mai gado.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 3, sakin layi na 1).

Tunanin ana mutuwa ke kawo zancen mai gado. Ga al’ada da addini, ba a gado sai wanda aka gada ya kau (mutu).[57] Tunanin za a mutu babu mai gado ya sa aka auro uwar Saƙimu, gudun ka da littattafai su sha ƙurar banza.[58] Kashe Malam Na-Bakin-Kogi shi ne silalin farko na zaren tunanin littafin. Bayan kisan gillan da Saƙimu ya yi wa Malam bai firgita ba, sai da ya ga mutuwarsa a fili kamar haka:
… Saƙimu ya yi mafarki, ya ga malamin a tsaye. Sai ga wani ɗan abu kamar ɗan dabino, ya fito daga zakarin malamin. Sai ya ga abin nan yana ta girma har ya kai kamar zaki. Da ya kai haka sai abin ya faɗo masa ya kashe shi.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 4, sakin layi na 2)

Gaskiyar Hausawa da ke cewa, wanzam ba ya so a jikinsa. Ina laifin masu azancin magana da ke cewa, mutuwa kashe mutane ki mutu? Duk a cikin mafarkin nan, Saƙimu abubuwa biyar ya gani: malam na tsaye, da zakarinsa, da wani abu kamar dabino, da girma kamar zaki, da mutuwa. Mutuwar nan ita ta firgita shi. Ashe idan manazarci al’ada ya ce, da matakin rayuwa na uku (mutuwa) aka shimfiɗa zaren saƙar azancin littafin Ruwan Bagaja bai yi kuskure ba.
Matakan da Saƙimu ya ɗauka na kauce wa mutuwa, su suka ba da ƙunshiyar littafin da sakamakon da aka samu. Mataki na farko da aka ɗauka sai ga mutuwa ta fito ƙuru-ƙuru:
                   Da gari ya waye, ya tara malamai don su yi masa duba.
Dukan malamai, kowa ya duƙufa ya zana ya shafe, ya zana ya shafe. Daga nan sai babban su ya ce, za a haifi wanni yaro a gidan nan, cikin matan tsohon nan da ya rasu shi ne zai kashe ka.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 4, sakin layi na 2 – 3).

Ƙoƙarin da Saƙimu ya yi na kuɓuta daga tarkon matakin rayuwa na ƙarshe (mutuwa) ya sake haifar da wata mutuwar kamar haka:
Abin da ya fi kyau sai in halaka matan huɗu duka masu  takaba, don ka da maganar masu dogwayen geman nan ta zama gaskiya.
Saboda haka ya samu guba, ya yi ta ba su ɗai ɗai suna mutuwa ana cewa baƙin cikin rabuwa da malamin nan ne ya kashe su.
(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 5, sakin layi na 1 – 2).

          A nan aka rufe shafin matan liman uku. Da ana son a ci gaba da ƙulla zaren tunanin gaba tare da mahaifiyar Imam, aka nuna ita ba ta gidan, tana garin iyayenta wani ƙauye can na daban. Duk da haka, sai da aka aika mata nata manzon mutuwa da dokinsa. Aka ba shi damar isa gare ta, ya ɗauko ta kan doki, ya shiga daji da ita. Ga yadda aka ruwaito:
Ya aza ta kuturi, ya yi dawa da ita. Ya yi ta kutsa daji da sukuwa, har kusan asuba, sa’annan ya tsaya. Ya ɗauki takobi zai kashe ta, sai ya taka wutsiyar wani kumurci, ya sare shi. Nan ya faɗi ya mutu. Doki ya yi dawa da gudu! (Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 5, sakin layi na 2).

Kuɓutar da mahaifiyar Imam ga mutuwa da mutuwar ɓarawon mahaifiyarsa su ne tubalin ginin ƙashin bayan littafin Ruwan Bagaja. Da ba a ƙaddaro da kumurci ya kashe baƙin bawan nan ba, da shi zai kashe mahaifiyar Imam. Da ya kashe ta, da zaren labarin ya tsinke daga nan. Kuɓutar da ita da cikin wata uku shi ya ƙaddaro zuwan Imam duniya har ya nemo fansa ga muzanta mijin mahaifiyarsa da aka yi. Da wannan aka gina gutasttsarin labaran babi na farko. Zaren labaran ya kai babi na biyu. A babi na biyu, da ana son a sake jan zaren fasaha sai aka kawo haɗuwar Imam da Ƙwara. A haɗuwar, da mutuwa aka yi garkuwa. Mutuwar ƙarya ta Ƙwara ita ta ja tsawon gutsattsarin labarai na babi na biyu har aka shiga babi na uku.
A babi na uku, da ana son a ɗinke shi sosai, sai aka kawo zancen mutuwa tsakanin Imam da Zandoro ɗan Zotori. Ya zo yana yawo da sa yana cewa:
Wa zai amshi sana, in an yi kwana bakwai in zo ya taɓo kaina?
(Ruwan Bagaja: Babi na 3, shafi na 16, sakin layi na 6).

Daga cikin sharuɗɗan da ya bayar su ne:
Ya kuwa riga ya ce in na kasa, zai yanka ni, ya ba gunkinsa jinin.
(Ruwan Bagaja: Babi na 3, shafi na 16, sakin layi na 7).

Ashe da mutuwa aka yi garkuwa a nan, kuma ita ce ta jawo hankalin ‘yan kallo su zo su ga yadda za a kwashe.
Haɗuwar manyan taurari a garin Hindu da mutuwa aka ja zaren labaran. Bawan sarki da aka kashe, Malam Zurƙe ya kai gawar gidan Imam. Imam ya zuƙe, Zurƙe ya kwan ciki ya ɗanɗani kuɗarsa. Wannan ta sa, Imam gudu ya bar gari, labari ya kai babi na huɗu. Gutsattsarin labaran da suka biyo baya ‘yan rakiyar labarin gawa ne, har labarin ya kai babi na biyar.
A babi na biyar, da mutuwar matar sarkin zagi aka gina shi. Bayan da aka magance haukar kewar da ta kama Sarkin Zagi, kunyata Sarkin Zagi ya sa Imam barin garin Tegi. Gabanin ya kwashe kayansa da mutuwa aka yi korar fagen babin. A gidan da Imam ya sauka, mai masaukinsa ya kashe ɓarawo. Imam ya samo kulkin da ya kaura wa mummuƙen Sarki Zagi yana barci. Da wannan dabarar gawa da mummuƙen Sarkin Zagi, Sarkin Zagi ya shiga kurkuku shekara ɗaya.[59] Barin ƙauyen ke da wuya, aka sake ƙulla zaren labarin da mutuwar wani baƙauye da ɗan’uwansa yana cewa:
Ina yawo rannan cikin daji sai na ga wani baƙauye na faɗa da ɗan’uwansa. Ina kawowa sai na ga guda ya sa kulki ya fyaɗe guda ya mutu.
(Ruwan Bagaja: Babi na 5, shafi na 24, sakin layi na 4)

Da wannan gawar aka haɗa Malam Zurƙe da matarsa faɗa da rantse-rantse wanda sanadiyar haka Zurƙe ya yi layar zana ya gudu ya bar garin. Da labarin ya kai babi na shida, a garin Nasarawa da mutuwa aka shimfiɗa wundin karatu. Dalili kuwa, mutuwar ‘yar sarki ya sa aka tabbatar da walittakar Imam.[60] Bayan abubuwan da ke faruwa sun faru aka shiga babi na takwas.
Babi na bakwai, da mutuwa aka yi masa matashiya cewa: TUBAN ALHAJI DA MALAM ZURƘE, ALHAJI YA KASHE WANSA. Duk abubuwan da suka biyo baya cikon sunna ne makaho da waiwaye. A babi na takwas aka naɗe littafin domin a nan ne buƙata ta biya. Yadda duk al’ada ke kallon mutuwa haka nan aka sarrafa ta a gutsattsarin labaran littafin. An kawo mutuwa ta kisan gilla da gangan.[61] An kawo ta ƙaddara.[62] An kawo ta rashin sani.[63] An kawo ta sakayya.[64] An kawo ta tsafe-tsafe.[65] An kawo ta ƙarya.[66] An kawo ta al’adar rashin lafiya ko tsufa.[67] An kawo ta sunu.[68]

SAKAMAKON BINCIKE:
Muradina in fito da wata mazhabar al’ada da ya kamata a dinga kula da ita idan ana nazari da tarken adabi. Nazarin wannan littafin ya gano wurare fiye da hamsin (50) da aka sarrafa matakan rayuwar Bahaushe domin isar da saƙon littafin Ruwan Bagaja. A gurguje an sarrafa matakan aure kamar hake:
1.                 Imam da mahaifinsa.
2.                 Malam Na-Bakin-Kogi da matansa huɗu.
3.                 Auren mahaifiyar Imam da Liman.
4.                 Auren Mowar Sarki.
5.                 Auren Zurƙe da matarsa.
6.                 Auren Jamilatu ‘yar Malam.
7.                 Auren da aka yi wa wata yarinya na dole.
8.                 Ɗan Sarki da iyalansa da aka washe wa masai.
9.                 Sarkin Zagi da matarsa da ta mutu.
10.             Zurƙe ya rabu da matarsa mafaɗaciya.
11.             Matar Sarkin Aljannu.
12.             Matar Imam da ta yi buƙatar ganin iyayenta aka murza zobe.
13.             Auren uban Saƙimu da mamarsa gabanin ta fito gidan.

Idan aka waiwayi matakin rayuwa na biyu (haihuwa) za a ga abubuwa kamar haka:
14.             Rashin haihuwar Malam Na-Bakin-Kogi.
15.             Agola Saƙimu.
16.             Haihuwar Alhaji a gidan Liman.
17.             Ɗan Sarkin Aljannu jinjiri.
18.             Mowar Sarki da ‘yar Sarkin Ƙaryatun Ni’am.
19.             Yaron Zurƙe Armi.
20.             Ɗan Sarkin Aljannu da mahaifiyar Liman ta ba ruwa.
21.             Yaron da ya ba Imam labarin auren Mowar Sarki.
22.             Faɗar Imam na cewa “Yara sun ɓata gidan da miya.”
23.             ‘Ya’yan Sarkin Aljannu da suka kamo Saƙimu.
24.             Yasifi ɗan Nuhu.
25.             Iyayen mahaifiyar Imam da ke wani ƙauye.
26.             ‘Yar Sarki da aka je jana’iza.

A ɓangaren matakin rayuwa na uku (mutuwa) muna da:
27.             Mutuwar Malam.
28.             Mutuwar Matan Malam uku (3).
29.             Mutuwar ɗan samame (ɓarawon mahaifiyar Imam).
30.             Mutuwar ‘yar Sarki.
31.             Mutuwar Ƙwara ta ƙarya.
32.             Kashen wan Liman.
33.             Kashe ɗan Sarki Aljannu.
34.             Zakin da ya kashe Saƙimu a mafarki.
35.             Faɗar malaman duba za a kashe Saƙimu.
36.             Ɓarawon da ya kashe bafaden sarki.
37.             Mai masaukin Imam da ya yi kisan kai.
38.             Baƙauyen da ya kashe ɗan’uwansa.
39.             Faɗar Sarki ga zargin da ake yi wa Zurƙe “ku buge shi sai ya mutu.”
40.             Mutuwar Matar Sarkin Zagi.
41.             Imam ya zama mutuwa.
42.             Faɗar Zurƙe cewa da bai rabu da matarsa ba ta sa an kashe shi.
43.             Faɗar Imam a ɗakin samarin da ya yi wa sata “Wayyo ya kashe ni!”
44.             Faɗar Sarkin Zagi cewa da shi mutuwa ta ɗauka ba matarsa ba.
45.             Faɗar Imam cewa na ƙwaƙwata rairayi na shiga. Na yi na yi in mutu.
46.             Faɗarsa “Ina nan cikin ramin nan ina jiran mutuwa.”
47.             Faɗarsa na “Kafin a zo a kashe ni na rama wa baba.”
48.             Faɗarsa na cewa: “Na yi kamar in ce masa ya kashe ni don in huta da azaba…”
49.             Yasifi ɗan Nuhu har ya ƙaura.
50.             Faɗar Sarkin Aljannu: “… ka kashe mini wanda ya kashe ɗana!”
51.             Faɗar Sarkin Aljannu “In ka ɗebo da yawa ka halaka.”
52.             Faɗar Sarkin Aljannu ga Imam: “Ka kuru da sun kashe ka!”
53.             Faɗar Sarki ga Yarima “…mun fi so ya mutu ma yanzu ya huta.” (Ya kashe ɓarawo).

Aure ya taka rawa sau goma sha uku (13). An sarrafa haihuwa sau goma sha uku (13). Mutuwa ta kafa turaku ashirin da bakwai (27) a saƙon littafin. Wace rawa aka taka ba da su ba a littafin Ruwan Bagaja?

NAƊEWA:
Na tabbata kowane masani ya ɗauki alƙalaminsa ba zai rasa abubuwan da zai harara ba na fanninsa a cikin littafin Ruwan Bagaja ba. Duk da haka, kasancewar marubucin mutum mai rai, Bahaushen ƙasar Hausa dole a samu nason rayuwarsa a ciki. Da za a tambayi marubucin yadda ya gina zaren tunaninsa na rubuta gawurtaccen littafin da ya yi wa tsara fintinkau! Da wuya ya ambato matakan rayuwar Bahaushe. Don haka ɗaliban al’ada muke cewa, mutum ba zai iya yin wani tunani wajen al’adarsa ba. Dole kowane mutum ya yi tunani irn na mutane ko dai irin na al’ummarsa ko irin na wasu. Haka kuma, a kan kowace al’umma zai rayu ko ya rayu, tunaninsa ba zai tsallake matakai uku ba: aure; haihuwa; mutuwa. Rubutun kowa ko fasahar kowa aka ɗora kan wannan falsafar al’ada za a tabbata wurin da babu ƙasa ake gardamar kokuwa. Gwargwadon ƙwazo da hazaƙa da basirar mutum na sarrafa waɗannan matakan a tunaninsa, gwargwadon yadda ayyukansa ke shiga jikin mutane. A fahintata ta ɗalibin al’ada, marubucin littafin Ruwan Bagaja ƙwazonsa na sarrafa waɗannan matakai na rayuwa a littafinsa, shi ya ba shi nasarar cinye gasar kai tsaye. Tabbas wanda duk bai kalli littafin Ruwan Bagaja a kan waɗannan matakai ba, a karkace ya dube shi, ya sake duba ya gani.


MANAZARTA
Abdullahi, A. M. 1998. “Abubakar Imam: Nazarin Tubali da Ginuwar Ayyukansa na Adabi.” kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Abdullahi, B. H. 1981. “Kwatanci Tsakani Salon Ruwan Bagaja da kuma Nagari Nakowa.” cikin Ɗagel Journal of Faculty of Arts and Islamic Studies, Sokoto: Uniɓersity of Sokoto.
Bunza, A. M. 1991. “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” Muƙala - Makon Hausa, Sakakwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A. M. 2006. Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nig. Ltd.
Daura, R. M. 1996. “Jirwayen Al’adun Hausawa cikin Littafin Ruwan Bagaja.” kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Elias, T. O. 1957. “Hausa Marriage in Nigeria.” A Ƙuarterly Magazine of General Interest. No. 53, Lagos: Federal Goɓernment of Nigeria Eshibition Center, Marina.
Garba, A. 2002. “A Stylistic Study of Hausa Classical Noɓels: Shaihu Umar , Ruwan Bagaja and Kitsen Rogo.” PhD thesis, Kano: Bayero Uniɓersity.
Guga, S. B. 2010. “Hoton Sarauta a Cikin Littafin Magana Jari Ce na Abubakar Imam.” kundin digirin MA, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
Gwarzo, Y. T. da wasu 2005. Aure a Jihar Katsina. Katsina: Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu.
Hassan, S. 2013. “Nazari a kan Mutuntaka da Adabi: Tasirin Abubakar Imam a Magana Jari Ce.” kundin digirin PhD, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
Ibrahim, M. S. 1985. Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci. Zariya: Hausa Publication Center.
Imam, A. A. 1966. Ruwan Bagaja. Zaria: NNPC.
Imam, A. A. 1978. (Ruwan Bagaja) The Water of Cure. Zaria: NNPC
Kafin-Hausa, A. A. 1985. “Nazarin wasu daga Rubuce-rubucen Marigayi Abubakar Imam.” Muƙala, Zariya: Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka.
Madauci, I. da wasu 1968. Hausa Customs. Zaria: NNPC.
Magaji, A. 2002. “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-yanayensu a Ƙasar Katsina.” kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Mairukubta, H. 1999. “Jego da Reno a Ƙasar Hausa: Tsokaci kan Hausawan Kabi.” kundin digirin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Malumfashi, I. A. M. 2005. “Kama da Wane ba Wane ba! Kakkaɓo Littafin Ruwan Bagaja daga cikin Taskar Adabi.” cikin Birniwa, H. A. da wasu (editoci) Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies. Ɓol. 1. No. 2, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Malumfashi, I. A. M. 2009. Adabin Abubakar Imam. Sokoto: Garkuwa Media Serɓices.
Mora, A. 1985. “Wani Ɓangare daga Tarihin Rayuwar Marigayi Alhaji Dr. Abubakar Imam da Aikace-aikacensa Daga 1911-1981.” Taron Ƙungiyar Haɓaka Hausa, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
Mora, A. 1989. Abubakar Imam Memoirs. Zaria: NNPC.
Nyamwaya, D. and Parkin, D, 1987. Transformation of African Marriage. United Kingdom: Manchester Uniɓersity Press.
Ottenberg, P. and Simon (ed) 1960. Cultures and Ethics of Africa. USA: H. Wolf Book Mtg. Con., Inci.
Pweddon, N. 1977. “Thematic Conflict nad Narratiɓe Techniƙue in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja.” PhD thesis, Madison: Uniɓersity of Wisconsin, USA.
Sallau, B. A. 2011. “Raɗa Suna Jiya da Yau.” Cikin Himma Journal of Contemporary Hausa Studies. Katsina: Umaru Musa ‘Yar’aduwa Uniɓersity.
Sarkin Sudan, I. A. 2008. “Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Smith, M. G. 1957. “The Hausa System of Social Status.” In Africa. Ɓol. ɗɗɓii. No. 1
Tambuwal, M. S. 2001. “Mutuwa a Idon Bahaushe: Nazari daga wasu Ƙagaggun Labaran Hausa.” kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Temple, C. L. (ed) 1965. Notes on the Tribes, Proɓinces, Emirates and States of the Northern Nigeria. London: Frank Cass and Company Ltd.
Traɓitt, L. 1973. “Attitudes and Customs in Childbirth Amongst Hausa Women in Zaria City.” Saɓana. No. 2 ɓol. 2, Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity.
Umar, M. B. 1980. Al’adun Haihuwa a Ƙasar Hausa. Zariya: Hausa Publication Center.
Umar, M. B. 1987. Dangantakar Adabi da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishers.
Usman, M. 1998. “Tarsashin Adabin Baka a Magana Jari Ce.” kundin digirin MA, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
White, H. 1980. “Literature and Social Action: Reflection on the Reflection Theory of Literary Art.” New Literary History. Ɓol II, No. 2. The John Hopkins Uniɓersity Press.
Yahaya, I. Y. 1989. “The Literary Works of Alhaji Abubakar Imam in Perspectiɓe.” Harsunan Nijeriya ɗiɓ. Kano: Bayero Uniɓersity.
Yunusa, M. M. 1985. “Kasancewar Tatsuniyar Ruwan Bagaja Tushen Littafin Ruwan Bagaja na Dr. Abubakar Imam.” kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.


[1] Don samun cikakken bayani a dubi: N. Pweddon, 1977, “Thematic Conflict and Narratiɓe Techniƙue in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja, un published PhD, Uniɓersity of Wisconsin – Madison.
[2] Na yaba da aiki aƙalan, don haka nake son in tabbatar da gwarzonsa ya yi gwarzo a ko’ina za a gwaje shi, musamman idan aka ɗora alƙalancinsu a kan faifan al’ada.
[3] A zamaninmu da ilmi ya kai ƙololuwar bunƙasa har yanzu ba a samu littafin da ya dushe hasken littafin Ruwan Bagaja ba. Buƙatarmu a sake nazarin ƙunshiyarsa, na baya su ga ƙwazon na gaba. Haka kuma, a bi wannan salon ga nazarin sauran sassan adabi domin a ciyar da ilmi gaba gwargwadon ci gaban zamaninmu.
[4] Yau, ina nufin shekarar 2013, da littafin ya share shekara tamanin a duniyar bokon arewacin Nijeriya. Kamata ya yi a ce an yi tunanin irin wannan aiki tun shekarar 1983 da ya cika rabin ƙarni.
[5] Takardun da za a samu a kan wannan bincike su za su tabbatar da wannan hasashe nawa. Cikin harsunan Nijeriya, babu mai rubutaccen adabin da zai iya gwada tsawo da na Hausa. Da manazarta Hausa sun sa himma da yanzu an wuce haka.
[6] Na tabbata da lauyoyi da masana walwala da tarihi da tattalin arziki da kiyon lafiya da addini da harsuna da ilmi da kimiyya da falsafa, kowannensu na da ta cewa a littafin. Wannan ya nuna, tunanin da ke ƙunshe cikin littafin sun zarce na shekarun marubucinsa, a lokacin da ya rubuta shi yana ɗan shekara ashirin da huɗu (24). Wannan ya nuna tunanin mutanen ƙarnin da ya gabace mu ya fi namu kaifi da fasaha da hangen nesa. Ta tabbata da tsohuwar zuma ake magani.
[7] Ban ga wani aiki da aka taɓa yi a Hausa da ya gabaci wannan ba. Don haka, wannan zakaran gwajin dafi ne. A taya ni gyara, ba ni na kashe zomo ba rataya aka ba ni.
[8] Da haihuwarsa yana yaro, sai ya girma ya zama saurayi in ya balaga ya yi aure ya zama mutum. Yin aure ya sa ya hau mataki na ɗaya. In ya haihu ya shiga mataki na biyu. In ya mutu ya shiga na uku da ba a sake wani mataki bayan shi.
[9] Har yanzu masana ba su kai ga matsayin shin aure aka fara yi ko haihuwa? In aure aka fara, wa ya haifi waɗanda suka yi auren? In kuwa haihuwa aka fara, ta wace fuska aka haihu? Ga su nan dai!
[10] A addinin Musulunci da Kirista da na Yahudu, an aminta da Adamu da Hawwa’u su ne mutane na farko. Alƙur’ani ya ce, daga haƙarƙari (awwazun) Adamu na ƙasa aka halicci Hawwa’u.
[11] A kimiyya da al’ada, ana ƙoƙarin a kore addini a halittar mutane. Mr. Darwin ya fara hasashen daga birai aka fara har aka waye aka koma mutane. Wannan tatsuniyar an shara ta cikin Tarikh ɓol. 1, No. 3.
[12] Ba za a taɓa haihuwar mutum da mata su zo duniya tare da ɗaurarren aurensu. Haka, ba za a haifi mutum tare da mutuwa ba. Sai dai ta riske shi a cikin ciki, ko lokacin da zai faɗo, ko bayan ya faɗo duniya. Don haka ɗaliban al’ada muke son a yi nazarinsu a rarrabe kamar yadda aka san su a rarrabe.
[13] Da an yi aure, haihuwa za a sa wa gaba gadan-gadan. Cikin haife-haife ma’aurata ke tsufa a fara tunanin barin duniya.
[14] Matakan rayuwarsu irin na Bahaushe ne babu wani bambanci. Alfu lailatan wa laila. Da Muƙaamatul Hariiri. duk a kan matakan rayuwa aka gina su. Masu ganin a can fahintar ta samo asali, to su san da cewa, ko a can bisa ga matakan rayuwar masu adabin aka gina ƙissoshi kuma Imam ya sarrafa su a matakan rayuwar Bahaushe.
[15] Masu ganin daga tatsuniyar Ruwan Bagaja aka ciro shi, sun yi canjaras! Dalili kuwa babu tatsuniyar Bahaushe da ba ta hawa a kan matakan rayuwarsa. Don haka, waƙa ɗaya ce ake rerawa da muryoyi daban-daban.
[16] An ce, wannan taƙaddama ta taɓa aukuwa a kacici-kacicin Bahaushe da ke cewa: Da ƙwai da kaza wa ya riga wani zuwa duniya? In ka ce, “ƙwai” a ina ya fito? In ka ce, “kaza” a ina ta fito? An taɓa tabka irin wannan muhawara tsakanin Sarkin Gardi Ƙyanƙyashe na Giwa-ta-zo da Sarkin Sarkin Gardi Bela na ƙasar Argungu. Ƙyanƙyashe ya fara kirari ya ce:
            Ƙyanƙyashe:    Ai sai an kai ga ƙyanƙyashe
                                    :Sannan bela ka bayyana!
Bela ya yi kuwwa ya ce:
            Bela:                Sai bela ta ci ta wuce
                                    :Sannan aka kai ga ƙyanƙyashe
            Gindi:              Sa maza gudu
                                    :Sa arna sake shawara
[17] Dole sai sun aminta su kwanta tare aure ke tabbata.
[18] Idan za a aurar da icen mangoro ko gwaba sai an dasa wani cikin wani. Idan dabino ne, sai an buga masa kilili. Haɗa su da ake yi tare, ɗaya ya yi barbarar ɗaya shi ne aure na itace da tsirrai. Me ya bambanta wannan da auren ‘yan Adam in ba kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da biki ba? Duk dai ma’anar a ƙara miya, ba a ƙoshi ba.
[19] Da an ga dabbobin daji mace da namiji tare babu tsangwamar juna an san mata da miji ne. In an ga ɗa, a ce ga ɗansu, ko da kuwa na wani uba ne ba na wanda aka gani ba.
[20] A wajen wasan dambe, idan an yi arangama an rungume juna, sai a ce an yi “amarya”. Ke nan, haɗuwa a gama jiki, a rungume juna, ko don murna ko don soyayya ko don buƙata ko don wata wuya ko wani abu can daban, shi ne aure a harshe. Auren duk da bai samu kai ga irin wannan matakin ba, ba aure ba ne ko a al’adance ko addinance.
[21] Wani motsattsen mutum ne da aka yi a zamanin Shaihu ɗan Ziyazinu ana kiransa Koje Sarkin Labari. Haukarsa ba ta zagi ba ce, ba ta duka ba ce, ta jin labari ce da bayar da shi. (Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 1, sakin layi na 1). Duk da haka, a haƙiƙanin gaskiya, an yi wani mahaukaci a Katsina kimanin shekara ɗari da suka gabata mai suna Koje. Imam suna yara suna biyar sa da ‘yan waƙe-waƙe idan ya fito a kasuwa. Da yake ya tsufa ƙwarai tun a zamanin su Abubakar Imam dole a samu cikinsa cike da labarai mabambanta. Ga alama a wannan magarya ya ɗaure akuyarsa.
[22] A al’adance, Bahaushe da ya faɗi sunan mahaifinsa ba a neman sunan mahaifiyarsa an dai san dole mace ta haife shi. Haka kuma, da an ji sunan uba, an san da aure aka haife shi. a al’adar Bahaushe, da uba ake kuri don haka suke cewa, kyawon ɗan ƙwarai ya ɗauko ubansa.
[23] Da ya ci nasarar kasheta tana da cikin Imam na wata uku. Imam kuwa shi ya je ya samo Ruwan Bagaja. Da an kashe uwarsa yana ciki magana ta ƙare. Maƙoƙo ya fito a bakin zabiya.
[24] Nan ne Imam ya shiga shagalin aure sosai ka ce na ɗiyansa na farin ne. Da haka ya samu shiga fada, har ta kai ko neman sarauta ake yi gare shi ake kamun ƙafa.
[25] An cinye dukiyarsa ya so ya kama Alhaji Imam da wayo, Imam ya nuna, kamin ka ga biri, biri ya ganka. Da Ƙwara ya ce ya mutu, Imam na shakka. Da ya gan shi baki buɗe, sai ya ce, an ce, Ƙwara ba sa mutuwa baki buɗe. Halinka da wawa, sai ya rufe bakinsa. Nan Imam ya gane da lauje cikin naɗi, ya tsere.
[26] Aka karɓe wa Baƙauye kuɗinsa, aka kai shi gidan Yari, wai, ya laƙa wa Imam (ɓarawo) sata. Baƙauye bai ƙare fursuna ba sai da Imam ya tarar da shi da wani laifi na sata, irin wanda ya laƙa wa Baƙauyen. Haƙiƙa ko bayan tiya akwai wata caca.
[27] An zagi Fulani domin su zo a yi faɗa. Su ba su sani ba, mahaukacin raƙumi ya tsare masu zaginsu, mafita suke nema. Suna zuwa sai raƙumi ya ce, ga abokan faɗa, aka shiga yi wa iska adashi.
[28] An nuna magafta suka yi masa asiri ya makafce domin ya kasa su ga auren Jamilatu ‘yar Malam
[29] Da ya makafce, ya sami wani yaro mai tsananin haƙuri wai shi ‘Armi’. Yaron ya riƙa yi masa jagora, saboda sabon makafta wuyan zama da shi. Ya dace da yaro mai haƙuri, komi aka yi sai ya yi damo.
[30] Zurƙe ya yi sanadiyyar ya faɗa kogi ya haɗu da ‘yan ruwa. Daga nan aka shiga duniyar tatsuniya har aka kai ga samun nasarar ɗebo Ruwan Bagaja.
[31] Domin an nuna yarinyar da Imam ya gani ya ce yana so, ta nuna ba ta da miji. Imam ya gano tana da miji, son sa ne ba ta yi. In haka ne kuwa, auren dole aka yi mata. Don haka take fita irin ta budare ba kamun kai neman wanda take so daidai da ita.
[32] Yarinyar dai ƙazama ce, bayan ta kira Imam, ashe ta gayyato Malam Zurƙe. Ga kuma miji tana da shi. Wane ƙazanta ya fi haka? Tir! Da mugun hali na ɓata mutunci da zuri’a.
[33] Idan Imam bai haukace ba, hukunci mai tsanani za a yi masa. Haukarsa ta ƙarya ta sa aka ba shi sarautar Wawan Sarki. Fadar Katsina ta daɗe da Wawan Sarki. Wataƙila wannan ce ta yi naso ga rubutun Imam kasancewarsa ɗaya daga cikin sarakunan Sarkin Katsina na lokacinsa.
[34] Kewar matarsa ya sa ya haukace bayan ta mutu. Haƙiƙa kusan kashi goma (10%) na mahaukata, za a ga tushen haukarsau daga mata ne. In dai sun kasa aure, ko an raba su da matansu ko matansu sun mutu ko an karɓe musu mata. Irin wannan hauka a Larabci ake cewa namiji mai ita Uutuu. A kanta ne aka gina shahararren labarin nan na Larabci “Majanun Laila”.
[35] Al’adar Bahaushe ce ba a faɗa da matar aure sai dai a yi da mijinta. Dalili shi ne, wace ɗaukaka ƙato zai samu idan ya yi faɗa da mace? Na yarda da makaɗa Bawa Ɗan’anace da ke cewa:
            Jagora: Ka da ka kashe Na’ila wanzami na!
                                    :Shi ka yo muna gyara
                                    :Ka ga kashe Na’ila bai yi wuya ba
                                    :Kamar a tunkuɗe turmi
                                    :Kamar mutum ya mari budurwa
            Yara:               Don ka mari macce ba garari ba
[36] Imam shigan mahaukata ya yi ya tsorata Malam Zurƙe. Duk da haka bai kamata namiji ya ji tsoron namiji ba har da kore wa kashin ƙato ƙuda gaban uwar gida. Duk zamantakewar aure ce ake warware jigo da ita.
[37] Ya nuna matar ‘yar bala’i ce dole ya rabu da ita. Wannan shi ya ba ɓarayi damar su ziyarce shi domin sun san gidan na mutum ɗaya ne, babu mai agaji in sun shiga da yawa. Ka ga ashe da aure aka yi garkuwa rashin sa ke sa a ce wa mutum gwauro.
[38] Wannan labari ya yi tasiri sosai a ƙasar Hausa wajajen shekarun 1962 – 1980, ka ce shekarar abin ya wakana. Katsinawa su ce, Bakano ne ya yi haka. Kanawa su ce, Bazazzagi ne ya yi.
[39] Da Bahaushe ya tabbata ko ya yi aure ba ya samun ‘ya’ya, ba zai kashe lokacinsa da dukiyarsa na yin aure ba. Kowace irin biyan buƙata za ka hanga a cikin aure, haihuwa ta fi ta. Don haka auren da babu haihuwa ke ba Bahaushe tausayi.
[40] Wataƙila don samun damar kama hankalin alƙalan gasar ya sa Imam ya gina labarinsa a kan rashin haihuwar Malam Na-Bakin-Kogi.
[41] Matan Hausawa da yawa ko suna son miji rashin haihuwa na sa su fito su nemi gidan haihuwa komai ƙasƙancinsa su zauna. Haka shi ma namiji, ko mace ta wuce sa’arsa, idan ya san tana haihuwa yakan auro ta domin ya samu.
[42] Da wuya a samu mata ba su shiga bokaye a kan haka ba. Domin ba a son su shiga bokaye aka nuna babban malami ne. Haka kuma, da an bari sun shiga bokaye da an ɓata zaren tunanin marubucin.
[43] A ƙasar Hausa, ‘yan uwa na ba ɗan uwa ko ‘yar uwa yara riƙo, in sun san ba sa haihuwa, domin a natsar da su. Wasu yaran har su girma ba za su tantance ba wannan ne mahaifinsu ko mahaifiyarsu ba. Da yawa yaran akan yi musu suna da ‘ɗan’ kamar; Ɗanmanu, ‘Yarladi, Ɗanjimma, ‘Yarmairogo ga su nan dai. Wai a danganta su ga mariƙansu domin mariƙan su ji sanyi a rai.
[44] An ko riƙi Saƙimu kamar ɗa. Domin son da ake yi masa ya zama nagari har tsare shi aka yi wata uku ko ya horu ya shiryu. Da yake ƙaddara ta rigayi fata, haka nan aka ƙare da shi, kare jini biri jini. Allah ba ka da dole.
[45] Ai da aka nuna Sarkin Zagi ya haukace, Sarki sa ya yi a yi masa maganinsa ya daina damuwarsa da hana shi barci. Da aka buge masa mummuƙe ɗaure shi aka yi. Da aka kashe Bafaden Sarki ba a kashe Zurƙe ba.
[46] Tun daga sunan littafin mai karatu zai fara ɗokin ya ji yaya za a samo ruwan? In ba a samo su ba za a ji labarin bai kammala ba. Yaya ruwan suke? Me ake nufi da su? Wane wuri za a tarar da su? Waɗannan tambayoyin cike suke a ƙirazan masu karatun littafin matuƙar ba a yi musu susa gurbin ƙaiƙayi ba, za su ji kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
[47] Ya girmama wanda ba shi ya haife shi ba, amma yana aure da mahaifiyarsa. Ina laifin Aƙilu Aliyu da ke cewa:
            In da fahinta da kula ba da musu ba,
                        Dole ma’auri iya a ce mishi baba.
[48] Da babu noma sai ƙarancin abinci. Da ƙarancin abinci sai yunwa. Idan yunwa ta bayyana mutuwa ba ta nesa.
[49] An san yaƙi kisa ake yi. Duk abin da ya sa yaƙi domin kare rayuwar wasu waɗanda ba su ji ba, su gani ba, a kashe su. Dole a yi garkuwa da mutuwa a kare mutuwar walaƙanci.
[50] Idan rayuwa ba ta inganta ba cutuka za su biyo ta. Daga nan sai annoba ta bayyana.
[51] A ko’ina aka tanadi tsaro ba don kaya ko ƙadara ake yin sa ba, ana yin sa ne domin rayuwar masu kayan da ƙadarorin da rayuwa ta samo. Duk tsaron da ya kasa kare rayuwa, ba tsaro ba ne, tsawo ne.
[52] Sai da zaman lafiya rayuwa ke da amfani. In an rasa zaman lafiya, rayuwa ta ƙare amfanin mai ita sai sauraren lokacin da za ta ƙare ake yi.
[53] Idan Bahaushe ya samu wani abin raha, ya yi dariya, yakan ce, kaico! Na yi dariya kamar ba ni mutuwa. Wai! Halin duniya na yau rai, gobe an mutu, ya sa Yaro Hore mai kiɗan noma ke cewa:
            Jagora: In nit tuna halin duniya,
            Yara:               Take raina ya yamutce!
            Gindi:              Aiki yai ma daɗi ƙwarai
                                    :Gungaman noma Ɗanbala
[54] Dole kowane mai rai ya yi kuka da ranar da zai bar duniya. Littafin Allah ya ce, “Kowace rai mai ɗanɗana mutuwa ce.” Tunawa da ranar baƙin ciki ya sa Hali Rayya Makaɗa ke cewa:
            Jagora: Wayyo! Duniya ‘yal baya
                                    :Kob bi ta taki bai kai waje.
[55] Masu wasan dambe sukan yi kirari da cewa:
                        “Kunya muka tsoro
                        Mutuwa ta zama gado”
[56] Kowane irin adabi aka ɗora kan matakan rayuwa, za a ga an feɗe shi cikin tsanaki. Hausawa na cewa, da rashin tayi akan bar arha. A gwada a gani. Wurin da babu fili ake gardamar kokuwa.
[57] Idan mutum ya rayu da ɗansa, ɗan nasa ya ɗauko irin halayensa muddin suna raye su duka, sai dai a ce, ya ɗauko uban. Ba za a ce ya gado shi ba. Idan uban ya mutu, kai tsaye za a ce ya gado shi. A addinin Musulunci, shariɗin gado na farko shi ne mutuwar wanda za a gada da rayuwar wanda zai yi gado bayan mutuwar wanda za a gada.
[58] Ba wai wagagen littattafai ake son a gada ba, ilmi ake son a samu ɗa mai shi. Mai ilmi zai gaji littattafan ba jahili ba. Da jahili ya gaje su, za su koma masara ko shinkafa, a yi tuwo, a kai wa masai kayanta.
[59] Tsoron da Imam ya ke ji na kar Sarkin Zagi ya ƙare hursuna ya dawo ya ce, sai ya rama. Don haka ya gudu, ya bar garin. Da an samu shaidu da Sarkin Zagi ya fuskanci hukuncin kisa.
[60] Imam ya san shi ba waliya ba ne don haka ya tabbatarwa mai karatu cewa shi, tiƙar gudu ya yi. Halinka da rashin sani, ya fi dare duhu. Jahilai ba su hango ba, har faɗar suke yi “masu abin.” Haka ake ko yanzu, malamai sun mayar da mabiyansu tamkar makaman farautar cefane sun kasa ganewa in an yi yunƙurin lurar da su malaman su yi ta jifan mutane da jafa’i da ƙasafai, jahilai su yarda cikin rashin sani.
[61] Wadda Saƙimu ya yi Malam Na-Bakin-Kogi.
[62] Wadda mai masaukin Imam ya yi wa ɓarawo da gawar da aka yaudari Sarkin Zagi aka buge masa mummuƙe ya yi hursuna shekara ɗaya.
[63] Irin wadda aka kaɗa ɗan goruba a kan ɗan Sarkin Aljannu ba da sani ba. Nan ya mutu, Aljannu suka ɗauki fansa ba da jinkiri ba.
[64] Irin wadda Imam ya yi wa wansa.
[65] Irin wadda Zandoro ɗan Zotori ya ce zai yi wa wanda ya karɓi sansa bai iya taɓo kansa ba.
[66] Irin mutuwar da Jamilatu da ta Ƙwara. Duk a kan shiri aka yi su kuma Imam aka yi wa su, ya gano.
[67] Irin wadda Saƙimu ya ce Malam Na-Bakin-Kogi ya yi. Ya ce cikin dare ya cika, wa zai musanta haka ga wanda ya tsufa? Nan kuwa Saƙimu ya kashe shi da takobin yaƙi.
[68] Irin wadda aka yi zato ga matan Malam Na-Bakin-Kogi bayan da Malam ya rasu.

No comments:

Post a Comment