Monday, December 31, 2018

Sakkwato Ce Tushen “Hausa” In Ji Narambad’a: (Laluben gudunmuwar mawaƙa a kan asalin Bahaushe da harshensa)



Irin matsayin harshen Hausa da Hausawa a duniya ya kyautu a ce, an kakkaɓe buzun karatun binciken tarihin asalinsu da harshensu tuni. Matsalolin da suka yi wa binciken asalin Bahaushe tarnaƙi sun haɗa da; shigan sharo ba shanu da wasu masana fannoni ke yi wa karatun. Haka kuma, ƙarancin masu bincike, da kasa daidaita akalar bincike, da ƙin aminta a yi taron dangi ga abin da ake bincike cikas ne babba. Babbar matsala duk ba ta fi saki zari kama tozon da aka sha yi wajen assasa tushen bincike ba. Ga maciji ana gani a dinga biyar shayinsa da sanda wai don nuna ƙwarewa, a ƙarshe, ya tsere, a yi ɓatan ɓaƙatantan. Wannan takarda ta himmatu ga tauraro ɗaya Ibrahim….

Sakkwato Ce Tushen “Hausa” In Ji Narambad’a:
(Laluben gudunmuwar mawaƙa a kan asalin Bahaushe da harshensa)

-----------------------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina
Waya: 0803 431 6508 Ƙibɗau
mabunza @yahoo.com
-------------------------------------------

Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Tsangayar Fasahar Ɗan’adam Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina a babban ɗakin taron Tsangayar Fasahar Ɗan’adam, ƙarƙashin Jagorancin shugaban Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Dr. Atiku Ahmad Dumfawa, ranar Alhamis 05/05/2011 da ƙarfe goma na safe

TSAKURE

Irin matsayin harshen Hausa da Hausawa a duniya ya kyautu a ce, an kakkaɓe buzun karatun binciken tarihin asalinsu da harshensu tuni. Matsalolin da suka yi wa binciken asalin Bahaushe tarnaƙi sun haɗa da; shigan sharo ba shanu da wasu masana fannoni ke yi wa karatun. Haka kuma, ƙarancin masu bincike, da kasa daidaita akalar bincike, da ƙin aminta a yi taron dangi ga abin da ake bincike cikas ne babba. Babbar matsala duk ba ta fi saki zari kama tozon da aka sha yi wajen assasa tushen bincike ba. Ga maciji ana gani a dinga biyar shayinsa da sanda wai don nuna ƙwarewa, a ƙarshe, ya tsere, a yi ɓatan ɓaƙatantan. Wannan takarda ta himmatu ga tauraro ɗaya Ibrahim Maidangwale Abdulƙadir (Narambaɗa) ga irin gudunmuwarsa a wannan fagen. An tsinto ɗiyan waƙoƙinsa ashirin da huɗu (24) daga cikin shahararrun waƙoƙinsa goma (10) da ya yi da kansa da muryar bakinsa domin kwakkwahe hujjojin nazari. An gayyato shahararrun mawaƙa biyar (5) a fannonin waƙoƙin sarauta, sana’a, maza, sha’awa, yaƙi, da suka raka shi a fahinta. An yi amfani da ɗiyan waƙoƙinsu tara (9) domin a daddage hukuncinsa. An ɗauraye hujjojin da tulu bakwai, aka rataye sakamakon a itace biyu nagartattu domin manazarta su harare su sosai. Makaɗa Narambaɗa sun ga jiya, sun ga yau, gobe ba ta zaunuwa lafiya idan aka yi watsi da batunsu. Narambaɗa ya yarda da cewa, mawaƙin fadar Fulani (Torankawa) ne amma mazauna ƙasar Hausa. Don haka ya yanke hukuncin Sakkwato ce ƙasar Hausa, wanda duk ke cikinta da bazar Bahaushe yake rawa. Bahaushen da duk ke wajenta cibiyarsa na Sakkwato in an bi diddign tarihi.
Gabatarwa
Manazarta da masana da dama sun yi bayanai muhimmai na fayyace asalin Hausawa da harshensu da al’adunsu. Asalin Hausawa da harshen Hausa ya samu kyakkyawar gudunmuwa daga bakunan masana ‘yan ƙasa da na waje. Muhawarori da sa-in-sa da taƙaddama a kan wane ne Bahaushe? Ina ya fito? Yaya harshensa da al’adunsa suke? An sha yin su a tarukan ƙara wa juna sani da gidajen rediyo da telebijin na cikin ƙasa da waje musamman gidan rediyon BBC, VOA, Radio Kaduna da kafofin yaɗa labarai na janhuriyyar Nijer da Ghana. Waɗannan abubuwan duk sun tiamaka wa karatu da masu neman karatu a kan yadda ya kyautu a tunkari biyar diddidin asalin Bahaushe. Da gangan na zaɓi tauraro ɗaya domin mu kalli yadda ya kalli ‘Hausa’, ‘Bahaushe’, da ‘Ƙasar Hausa’. Na zaɓi in karkata akalar nazarina kan zantukan malamin waƙa Ibrahim Maidangwale Abdulƙadir (Narambaɗa) domin cancantarsa a wannan bagiren.
Wane ne Narambaɗa?
Narambaɗa mutumin ƙasar Isa ne da aka haifa a garin Tubali. Ya rayu bayan jihadin ƙarni na goma sha tara. Ya rayu gabanin mulkin mallaka. Allah Ya ƙaddare shi da ganin bayana. Turawa da shimfiɗa mulkinsu har ya zuwa jamhuriyya ta farko a Nijeriya. Bai gaji waƙa ba wajen uba ga uwa ya gaji waƙa. Kiɗin kokuwa ya fara daga nan ya shiga kiɗin noma da likafa ta ci gaba ya shiga kiɗin sarauta. Babban uban gidansa da ya yi wa bakandamiya shi ne Sarkin Gobir Amadu Bawa, kuma shi ne sarkin Gobir na ƙarshe da ya yi wa waƙa. Wannan ɗan tsakuren nuni ne kawai da ba da haske kan cewa, tauraronmu ya cancanci a saurare shi. Domin samun cikakken bayanin Narambaɗa a dubi, Gusau, 1988, Furniss, 1996, Bunza, 2009, Yaro Sodangi 1979, Mazawaje, 1985.
 Bagiren Nazari:
Burina a wannan takarda shi ne, tabbatar da zancen Bahaushe da ke cewa, da tsohon zuma ake magani. Haƙiƙa gaskiyar Bahaushe da yake cewa, komi zafin Larba tana barin Talata ta wuce. Na hangi malamanmu da magabatanmu da wasu daga cikin takwarorinmu suna yi wa tarihin asalin Bahaushe kwasan karan mahankaciya. Da haka sai karan ya yi yawa a kasa ɗaukarsa a ka, a rasa mai taimaka maka ka ɗora a ka, da ƙarshe sai a bar kowa da kayansa babu mai taya wani ɗauka. Idan bincike ya kasance an bar kowa da ra’ayinsa abin nema bai samu ba. Kyawon bincike shi ne, a taru, a haɗu wuri ɗaya a rairaye ra’ayoyi da hasashe-hasashen kowa a samu wata magana mai kauri da za a yi gora da ita domin dukan kan duk wani mai ra’ayin a ware kowa ya bi hanyarsa. Daga cikin abubuwan da na gani na cikas garemu mu ɗaliban Hausa da tarihi su ne:
i)                   Rashin tsayar da daidaitacciyar magana a kan cewa, ina ne ƙasar Hausa take?
ii)                Rashin tantance wurin da Bahaushe ya fito ko ya tsira da yadda ya samu kansa a yau.
iii)             Kasawarmu ta fito da wasu matakan bincike na ƙwararru da za a bari masana su bi har sai sun kai ga sin-wau-raa-takuri su ba mu bayani.
iv)              Rashin keɓe darasi na musamman a kowane matakin digiri (1-3) da zai himmatu ga biyar diddigin tarihin Bahaushe, asalinsa da al’adunsa.
v)                Babban kurenmu shi ne, sake wa masana tarihin akalar binciken asalin Bahaushe mu tsura musu ido muna jiran sakamako. Rashin sani ya sa karen gwauro ya kori bazaura, su kansu masana tarihi da bazar masana al’ada da adabi da harshen Bahaushe suke rawa. A ƙarshe, aka yi haihuwar guzuma, ɗa kwance, uwa kwance.
vi)              Kasawarmu ta rashin kiran gagarumin taro na musamman a kan asalin Hausawa da harshensu ba ƙaramin kure ba ne. Lallai sai an kira taron masana Hausa a yi wankin ɗankanoma mashaya, kana a nemi gudunmuwar masana na fannoni daban-daban domin a kakkaɓe buzun karatu.
Idan muka dubi waɗannan abubuwa shida da idon nazari, za mu ga cewa, masana da malamai da ɗaliban Hausa ba su da wani muhimmin abu a gabansu face na tantance tarihin Bahaushe sahihi tare da fayyace tantagayyar asalin harshensa. Duk wani digiri, da babban digiri, da rawanin Farfesa, da za a naɗa wa wani ɗalibi ko malamin Hausa a yau, Hausa da Hausawa na bin sa bashi idan bai ba da gudunmuwarsa a wannan fanni ba. Abubuwan da suka mamaye littattafan nazari da kundayen binciken ƙanana da manyan digiri da tarkardun shimfiɗa buzun karatu na wasu fitattun masana a kan asalin Bahaushe da harshensa cike suke da tarihihi da tatsuniya da jita-jita hadisin Bamaguje. Tunkararsu gaba ɗaya a takarda ɗaya ko littafi ɗaya ba zai yi wu ba, don haka na ga ya kyautu in ɗan tsakuro kaɗan da fatar ƙiliu ta tono balau. A taƙaice, nazarce-nazarcen da suka gabace mu za a ga sun karkata zuwa ga:
i)                   Tarihihin Bayajida da asalin Daura.
ii)                Kwararowar baƙi daga gabas da samuwar Bahaushe da ƙasar Hausa.
iii)             Matsalolin Habasha da Misra da Sudan a kan ginuwar ƙasar Hausa.
iv)              Rigingimun tantance daidaitacciyar Hausa tsakanin Kano da Sakkwato da Zazzau da Katsina da Saharar Nijar.
v)                Ƙoƙarce-ƙoƙarce tantance addinin Bahaushe da al’adunsa na asali da waɗanda ya aro da waɗanda aka ara daga gare shi.
vi)              Tarihihin Hausa Bakwai da Banza Bakwai ya daɗa dagula al’amarin aka bar Bahaushe cikin ƙila-wa-ƙala.
Hangen waɗannan abubuwa bakwai suka ba ni ƙarfin gwiwan tunkarar wani gwarzo daga cikin gwarajen ƙasar Hausa, domin in isar da saƙonsa da irin gudunmuwarsa tun gabanin rikice-rikicen da masana suka shiga a yau na tantance ina ne ƙasar Hausa. Gabanin yin haka, ya kyauttu mu ɗan yi waiwayen fitattun masanan da suka yi rawar gani a wannan bagire.
Waiwaye:
Ban ga laifin magabata da suka yi binciken asalin Bahaushe da harshensa ba, sai dai ina son in yi yaɓi ne a kan katangarsu. Bayan na yi yaɓi, in buɗa wata ƙofa mafi kusa ga a kai ga buƙata mu jarraba ta mu gani. Da na yi waiwayen ayyukan magabata na hangi akwai cikas a wasu wurare da ya kyautu a agaza musu. Daga cikin masanan da suka yi fice a bincike-bincken asalin Hausawa akwai: M.G Smith da Murray, Last, da Hisket, da Abdullahi Smith da Lange da Smith da Lavers da Shea da dai sauransu. Daga cikin matsalolin da za a ci karo da su a cikin ayyukansu sun haɗa da:
i)                   Masana tarihi ne suna kallon abubuwan ta fannin tarihi da dogara da bincike-binciken da ya gabace su a tarihance. Wannan babban cikas ne, domin ba makami ɗaya za a yi amfani da shi a irin wannan yaƙi ba.
ii)                Babban abin ban tausayi shi ne su ba Hausawa ba ne. Rashin kasancewarsu ba Hausawa ba, ba ƙaramin cikas ba ne domin wanda ya san daɗin sure ke yi wa fadama shinge. Manufarsu a koyaushe ita ce, da sun ji abu za su rubuta shi, su ɗora shi a kan mizanin tunanninsu. Da yawa tunane-tunanensu na takin saƙa da Bahaushen tunani, su yi tsaye su maƙala wa Bahaushe shi, bai ji ba bai gani ba.
iii)             Akwai mamaki ƙwarai a ga waɗannan fitattun masana ba sa jin Hausa bale karance-karancen abubuwan da aka rubuta da Hausa ko su yi nazarin adabi da harshe da al’adun Bahaushe a rubuce-rubucensu. Rashin jin Hausa, da iya rubuta ta, da iya karanta ta, wata babbar hujja ce ta sa ayar tambaya ga rubuce-rubucensu da suka shafi asalin Hausawa da harshensu.
iv)              Makamin farautar asalin Bahaushe na cikin harshensa da adabinsa da al’adunsa. Waɗannan abubuwa kuwa wasu masana da suka gabace su sun ce wani abu cikin Larabci da Ajamin Hausa da Zabarmanci da Azbinanci da Fulatanci. Ga alama, waɗannan wasanan ba sa jin kowane daga cikin waɗannan harsuna bale su karanci abubuwan da aka rubuta cikinsu. Don haka, ƙolin hujjojinsu su ne, abubuwan da suka sani a harshen Turanci da waɗanda aka yi fassarar (ba ni baƙi in ba ka fassara) daga harshen aslai zuwa Turanci ko Faransanci. Da haka dai sakamakon bincikensu zai koma, ba ni na kashe zomo ba rataya aka ba ni.
Abdullahi Smith ya fara hango daular Bahaushe da ƙasar Hausa. Waɗannan abubuwa da muka lisafa suka yi wa ayyukansa tarnaƙi. M.G Smith ya wallafa shahararrun ayyuka biyar da ba irinsu ga zamaninsa (watau Daular Zazzau, Kano, Sakkwato, Daura da Katsina). A ayyukkan tarihi ne aka ba amana aka manta da gudummuwar adabi da harshe da al’ada. Hisket, ya yi abin a zo a gani cikin waƙoƙin Hausa da rubuce-rubucen ajami, sai dai rashin jin Hausa, da iya karanta ta, da rubuta ta, ya yi wa tunaninsa cikas. Murray Last, da Lange da Lavers duk wannan matsala ta ci su. Philip Shea, ya kuɓuta ga jin Hausa da iya magana da ita, sai dai tarihi ya karanta ba Hausa ba, ga shi kuma ba Bahaushe ba ne bale ya san adabin Hausa yadda ya kamata.
Ayyukan masana da suka kuɓuta ga wannan tarnaƙin sun haɗa da Mahdi Adamu, Garba Nadama, Abdullahi Rafi Augi, Bala Usman, Hambali Jinju da sauran ɗalibansu. Ayyukansu suna hararar fannonin da suka ƙware ne kawai kuma wasunsu ba su yi wa adabin Hausa da al’adun Bahaushe karatun Fatiha ba. Da dai sun sami wani wuri ɗaya sun laɓe su tusa shi gaba suna daddaga da basirar fannoninsu da yanzu su ya kai gurbi ga tantance asalin Bahaushe da harshensa. Da wannan zan ce, ga ɗan abin da na hango a cikin waƙoƙin Narambaɗa:
Ƙasar Hausa:
Babu mai musanta kasancewar Bahaushe mutum daga cikin mutanen da ke rayuwa a bangon duniya. Wasu masana na hasashen ƙaura Hausawa suka yi daga wani wuri suka zo ƙasar da suke a yau. Wasu na ganin a nan ƙasar da suke aka halacce su. Ga iyakan bangon ƙasar Hausa in ji makaɗa Narambaɗa:
Jagora  :Ai dag ga Kaduna har Gusau ƙarewar Hausa,
Yara     :Kowace shawara ta labarin Turawa
                    :Amadu ba a yin sa sai ya sa hannunai,
                   :Zamakin ƙoƙari garai ga sanin hujjoji.
Gindi          :Gwarzon shamaki na Malam toron giwa,
                   :Baban Dodo ba a tammai da batun banza,
A ganin Narambaɗa, iyakan ƙasar Hausa ya ƙare daga Zamfara a babban birninsu “Gusau”. An samu ka-ce-na-ce da yawa a kan wannan ɗan waƙa na Narambaɗa. Daga cikin abubuwan hasashe a wannan ɗan waƙa akwai:
i)       Daga Gusau zuwa Kaduna ne ƙasar Hausa?
ii)      Daga Sakkwato zuwa Gusau ne ƙasar Hausa?
Hasashe na biyu shi ne ya fi daidaituwa da ra’ayin Narambaɗa. A ganin makaɗa Narambaɗa da’irar ƙasar Hausa daga Zamfara (Gusau) ne zuwa Sakkwato. Tun gabanin haihuwar Narambaɗa da bayan haihuwarsa haka nan ake kiran farfajiyar ƙasar duka da suna “Hausa” ba ƙasar “Hausa” ba. Wataƙila sauran daulolin ƙasar Hausa duk haka nan ake kiransu gaya ba tare da sa kalmar “ƙasa” ba, kamar a ce: Katsina, Zazzau, Zamfara, Kabi, Gobir da dai sauransu.
Farfajiyar Ƙasar Hausa:
Idan aka ce “Hausa” Sakkwato za a zo in ji Narambaɗa. Idan aka ce iyakokin cibiyar ƙasar Hausa Narambaɗa cewa ya yi:
Jagora         :An gamu Hausa kulluhun jama’a duk an zo
                   :Kamfunnan ga arba’in da bakwai duk sun zo
                   :Kowane kamfani shi na tsaye bakin garka,
Yara:           Maiduka yah hito da shi da su Gatau
                   :Amadu duk magana wadda kay yi
                   :An ka ji daidai kay yi
                   :Tun ran nan Amiru yaƙ ƙara ma girma,
                   :Kuma ran nan Waziri yaƙ ƙara ma girma
                   :Amadu bai hito ga dattijon banza ba.
Gindi :         Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
                   :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

Kalmar “Hausa” a nan tana nufin “birnin Sakkwato” kai tsaye. Zancen da ya yi na kamfuna arba’in da bakwai yana nufin gundumomi (Districts) arba’in da bakwai (47) na jahar Sakkwato da Kabi. Kabi ta ƙunshi Argungu da Gwandu da Yawuri da Zuru. Sakkwato da Zamfara kuwa kamar yadda suke a da. A tarihi ba a ci Yawuri da Zuru da yaƙi ba ƙasashe ne ko Dauloli masu zaman kansu. Zamansu ƙarƙashin Sakkwato ba ya rasa nasaba da kariya ta yaƙi bayan ƙare jihadi.
A nan, Narambaɗa ya ƙara faɗaɗa yawan iyakokin Hausa wanda ya haɗa da gundumomi (47) da ke ƙarƙashin Sakkwato. Abin kulawa a nan shi ne, mutanen ƙasar Yawuri da Zuru, idan za su je Birnin Kabi ko Sakkwato sukan ce, za mu je “Hausa”. Ba su cewa, za mu je “ƙasar Hausa ba” sai dai za mu je “Hausa”. Yanzu haka, akwai wani zana da suke yi mai kauri su gewaye gidajensu da shi, a Zuru da Yawuri duk sunansa “Ba-ka-zuwa-Hausa”. Makaɗa ya ƙara yi wa maganarsa daddage a wani ɗan waƙa da yake cewa:
Jagora:        Na tuna wata shekara
                   :Da an ka yi taro Hausa
Yara:           Kamfunan ga arba’in da bakwai duk sun zo
                   :Ni ba ya ga Isa ban ji labarin kowa ba.
Gindi:          Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
                   :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

Wani taro na da gundumomi arba’in da bakwai da aka yi na Daular Sakkwato, ya ambace shi da cewa: “an ka yi taro Hausa”. Abin nufi, an ka yi taro a Sakkwato. Ya ƙi ya ambace ta da sunanta Sakkwato ya ce “Hausa” sunan da aka fi saninta da shi a tarihance. Wannan ya nuna gabanin a naɗa wa Sakkwato sunan Sakkwato “Hausa”ake ce wa farfajiyar ƙasar duka. A taron, Narambaɗa yake cewa, bayan labarin gundumar Isa bai ji wata gunduma da ta yi fice ba.
Mutanen Ƙasar Hausa:
Makaɗan bai manta da yawan mutane su ne kasuwa ba. Don haka, a cikin waƙoƙinsa akan yi tsintuwar dami a kala na tantance mutanen da ke ƙasar Hausa. A cikin wani habaici da yake yi wa magabtan Sarkin Gobir Amadu yana cewa:
Jagora         : Yau mai ashararu ya kaɗe
                   :Dunya ta yi mai hwashi
                   : Babu zama garai
                   :Zama fitina yar tayas
Yara            :Ya san ba a ƙwarijini
                   :Ga mutanen Hausa
                   :Kowac ce shina iyawa
                   :Ga fili nan
                   :Sai ya ƙetare gidanai
                   :Ba ban kwana
Gindi:          Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
                   :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.
A nan, ana magana ne kan magabtan sarkin Gobir na Isa aka nuna ba a nuna iyawa “ƙwarjini” ga mutanen Hausa. Hasashen Narambaɗa a nan shi ne, Amadu Batoranke (Fulani) ne, amma mutanen ƙasarsa Hausawa ne. Don haka, mutanen ƙasar Isa, Gobirawansu da Zamfarawansu Hausawa ne, kuma mutanen Hausa aka ce musu. Domin ƙara tabbatar da wannan da’awa yana cewa:
Jagora         :Uban Malami ka kai
                   :Wurin da Ibrahim duk yak kai,
                   :Zamakin an kira shi
                   :Sarkin Gobir Hausa
                   :Kai ko an kira ka
                   :Sarkin Gobir Hausa
Gindi          :Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
                   :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.
A kaikaice, Narambaɗa na gaya muna gabanin jihadi ƙasar Isa da Gobir Hausa ake kiransu. Ana kira kakansa Ibrahim Sarkin Gobir na Hausa, shi ko an kira shi Sarkin Gobir na Hausa. Da sarkin Gobir na Sabon Birni da Sarkin Gobir na Isa sarakunan Hausawa ne mutanen da suke sarauta Hausawa ne, sunan ƙasar, “Hausa”.
Harshen Mutanen Hausa:
Ɗan’adam na da ‘yanci sa ƙafarsa duk wurin da ya so ya rayu. Duk da haka, idan aka samu cinkoson mutanen da suka mamaye wuri da yawansu da al’adunsu da harshensu ya zama na ɗaya bisa ga sauran ƙabilun da ke zaune da su. Ga tsarin adalcin zamantakewa su za su karɓi jagorancin siyasar ƙasar ta fuskar tattalin arzikinta da tsaronta. Mutanen da ke zaune a farfajiyar da Narambaɗa ya kira “Hausa” wurare daban-daban a waƙoƙinsa su ne Hausawa, sunan harshensu “Hausa” don haka suke da mawaƙa Hausawa kamar yadda ya tabbatar da cewa:
Jagora          :Amadu bana Hausa ka yi rinjaya ni na yi
                   :In an ce Isa ba ka jin an ce wani sarki
                   :Ni ko duk Hausa ba ka jin waƙa bayan tau.
Gindi:          Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
                   :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.
Da harshen Hausa Narambaɗa yake rera waƙa, mawaƙin ƙasar Hausa ne na basarake Batoranke (Bafulatani). Ga dukkanin hasashe ‘Hausa’ a nan yana nufin Daular Sakkwato, wanda yake ganin ita ce “Hausa”. Narambaɗa bisa hanya yake domin bayan rusa daulolin ƙasar Hausa na Gobir, Zamfara da Kabi da Katsina da Kano da Gimbana da dai sauransu sai aka kafa sabuwar daula ta masu jihadi duk da haka ƙasar ba ta sauya suna ba tana nan zamanta “Hausa” tattare da sanin Fulani suka mamaye gurabun sarautar Hausawa. Komai ƙasaitar sarautar Bafulatani ko Batoranke, dole ya aminta, ƙasar wasu suka kafa ta gabaninsa, kuma sunansu ya mamaye sunan kowane irin mai mulki da zai mulke ta. Narambaɗa ya tabbatar da haka a gindin waƙar da ya yi wa Amadu yana cewa:
Gidin :         Gogarman Tudu jikan Sanda
                   :Maza su ji tsoron ɗan mai “Hausa”.
Ana son a nuna dole maza su ji tsoron sarkin Amadu domin ɗan Sarkin Musulmi ne, shi ko sarkin Musulmi shi ne mai ƙasar Hausa. Ai Narambaɗa ya furta wani ɗan waƙa da zai fayyace wannan gindi kamar haka:
Yara: Sun san Garba ɗan Hasan
          : Shi yah hau gadon Hassan
          :Shi as shugabansu
:Kai ab babban ɗanai
          : Komi kay yi ba a cewa ba daidai ba
:Nasabas Shehu ba ta ɗai
          :Da ta kakan kowa.
Gindi: Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
          :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.
Garba ɗan Hassan a nan, shi ne, Sarkin Musulmi Abubakar III. Hassan shi ne sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu’azu, wanda Abubakar III ya gada (mahaifinsa). Waɗannan ɗiyan waƙar tagwaye ne, na biyun na ƙara tabbatar da na ɗaya. “Ɗan mai Hausa” na nufin ɗan Sarkin Musulmi domin shi ne sabon Sarkin ƙasar Hausa bayan da aka ci Hausawa da jihadi. Hausa a nan, tana nufin Sakkwato, don haka muke hasashen tushen Hausawa Sakkwato. Harshen da Sakkwatawa ke magana da shi, shi ne Hausa da kare-karen harsunan da ya haifar.
Cibiyar Hausa:
Ba ni musun zaman Kano Jalla babbar Hausa kamar yadda Kanawa ke yi mata kirari. Buƙatata a nan shi ne, in ɗan binciko ko Narambaɗa na da wannan labari? In ba ya da labarin wane labari yake da shi game da Kano? Zancen da Narambaɗa zai faɗa ba zai zama wata tabbatacciyar hujja ba ga mai bincike. Duk da haka, wata babbar fitila ce mai dogon haske ga mai son yin magartaccen bincike. Narambaɗa cewa ya yi:
Jagora:Da Kano sa Kaduna sa Jos
          :Su duk waɗanga
          :Babbar aiki Hausa
Yara  :Kul dottiɓe sun haɗe
          :Kowace shawara a kai
          :Sai ya sa hannu
          :Sai ka ji dariya ana ta hwaɗa daidai
Gindi :Kai bajinin Namoda
          :Gagara Gago na zagi.
          :Iya gaba na Rwahi
          :Baban Yarin Ƙaura.
A zamanin da Narambaɗa ke waƙa, Kaduna da Jos da Kano da Sakkwato su ne duniyar Nijeriya ta Arewa. To, makaɗa ya nuna da Kano da Kaduna da Jos manya ne amma babbar cibiya tana “Hausa”. A faɗarsa ya ce:
Jagora: Su duk waɗanga
          :Babbar aiki Hausa”.
A fahintarsa Hausa ce cibiyarsu, Hausa kuwa a wajensa ita ce “Sakkwato” ko cibiyar da masarautar Sakkwato take da fadar mulkinta.
Ina Ne Hausawan Suke?
Makaɗa Narambaɗa bai ƙuƙunta bayaninsa ga birnin Sakkwato na yau ba, a kan amfanin da yake yi da kalmar “Hausa”. Yana sane da kyau cewa, Hausawa ‘yan dangi ne, kuma sun kasu dangi-dangi, zuriya-zuriya wanda shi ne  musabbabin kasuwarsu daula-daula. A ko’ina aka samun wata zuriya ta Bahaushe Hausawa ne, in sun yi ƙasa tasu ce, amma ‘Hausa’ na nan wurin da take “Sakwkato”. Ga ɗan misali:
Zazzau:
Narambaɗa ya yi wa fadar Zazzau waƙa sosai amma bai taɓa kiranta Hausa ba ya kuma san tana cikin ƙasar Hausa domin da Hausa ya yi wa masarautarta waƙa. Dubi yadda yake cewa:
Jagora:Sardaunan Kaduna ya yi jawabi
          :Duk ga Zage-zagi zaune
          :Yac ce ku bar hushi da danginku,
          :Sarauta tana ga Allah
          :Kun ga gidan Alu gidan sarauta na,
          :Gidan Yaro gidan sarauta na
Yara: Shi wannan da kun ka so a naɗa
          :Allah bai yi mai sarauta ba.
Gindi:Mijin Nana Yelwa ɗan sanda
          :Gulbi ka wuce kwalhewa.

Narambaɗa ya ambaci wata zuriya daga cikin zuriyar Bahaushe Zage-zagi a waƙar yana cewa:
Jagora:Jikan Shehu mai ƙasar Zazzau
Yara: Gogarman Makama ɗan Kwasau
A gindin wata waƙar masarautar Zazzau cewa yake yi:
Gindi:Gaskiya to yi halinta
          :Sai mu koma Zazzau
          :Mui ta kiɗan murna
          :Ga Muhammada ya zan sarki.

Ya tabbatar da kasancewar Zazzau ƙasa daga cikin ƙasashen Hausa amma bai kira ta Hausa ba. Domin a ganinsa cibiyar Hausa na Sakkwato.
Katsina:
Narambaɗa ya san Katsina da fadarta sosai domin ya yi wa sarki Ɗankulodo na Maraɗi waƙa. Haka kuma, an neme shi da ya je Katsina ya yi waƙa har yake neman iznin Uban gidansa da cewa:
Jagora:Bisa yarda na Garba
          :In ya sa min hannu
Yara: Bana yawo nikai
          :Zaman dangina sun yi
Jagora:Katsinawa suna biɗa ta
          :Ban je can ba
Yara: Dan nan in yi Buza
          :In zarce Madawa.
Gindi:Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
          :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

Ya ambaci Katsina da zuriyarta duka wato “Katsinawa”, ya kuma yi wa sarkin Katsina Maraɗi Dankulodo waƙa amma bai ambace su da sunan “Hausa” ba.
Zamfara:
Makaɗa cikin ƙasar Zamfara yake amma bai ce mata Hausa ba. Ya ambace ta da sunan da aka taras na tarihinta. A nan cewa ya yi:
Jagora:Zamfara ba makaɗin da ka ja mini
Yara  :Baya ga Jankiɗi
          :Sai ko Ɗandawo
          :Sai ɗan Dodo Alu mai taushi
          :Amma ba makaɗin gayya ba
Gindi:Gogarman Tudu jihan Sanda
:Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.

Narambaɗa ya zaɓi wasu fitattun ƙasashen Zamfara ya yi wa sarakunansu waƙa. Haka kuma, a cikin bakandamiya ya yi wani darzaje na nuna sanin Zamfara da Zamfarawa kamar haka:
Jagora:Moriki Ƙaura da Zurmi
          :Dut maganar ta zan ɗai
Yara  :Bunguɗu sa Gusau,
          :Kwatarkashi ga ‘Yandoto
          -        -        -        -        -
Gindi:Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
          :Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

Dukkanin zuriyar Zamfara da za a iya lisafawa masu magana da harshen Hausa za a same su a nan, watau: Moriki da Ƙaura da Zurmi da Bunguɗu da Gusau da Kwatarkashi da Tsafe (garin ‘Yandoto). Makaɗa bai taɓa ambatunsu da sunan “Hausa” ba, duk da kasancewarsu Hausawa masu magana da harshen Hausa da al’adu na Hausawa.
Ɗaurayar Zantukan Narambaɗa:
Narambaɗa ya tabbatar da cewa, ba a samun harshe ba tare da samun masu magana da shi ba. Haka kuma, samun cunkason masu harshe wuri ɗaya ya tababtar da samuwar ƙasar da suka rayu wadda za a ce ita ce ƙasarsu. A ganin Narambaɗa, idan wasu mazauna suka zauna ƙasar, suka shimfiɗa mulkinsu, suka kafa daula, ta zama ƙasarsu. Narambaɗa na ba mu labarin cewa, duk da kasancewar an ci Hausawa da yaƙin jihadi ƙasarsu tana nan tare da sunansu da sarautu irin nasu kamar dai yadda yake ce wa sarki Amadu:
Jagora:Gawurtacce na Magajin Rafin Hausa.
Gindi:Gwarzon shamaki na malam Doron giwa,
:Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

A ganin Narambaɗa, kowace sarauta aka naɗa ƙasar Hausa, kowane irin aiki ake yi cikinta tana nan da sunan “Hausa” daidai yadda yake ce wa wani ma’aikacin hukuma:
Jagora:Malam Jelani malamin shanu
          :Ya yi ƙoƙari
Yara: Na ji ana hwaɗin
          :Irin aikinai Hausa.
Gindi:Gwarzon shamaki na malam toron giwa
:Baban dodo ba a tamma da batun banza.

Haka kuma, a waƙar da ya yi wa Alƙalin Alƙalai ya ƙara tabbatar da bayanan da ya sha yi da cewa:
Jagora         :Alƙalin Alƙalai na Hausa
Yara            :Ko wai kaura da kai
                   :Kana turmuje shi.
Gindi          :Alƙali shiri nai da kyawo
                   : Shi yai zaune daidai wa daidai.

A da, idan aka ba ma’aikaci muƙami a Lardin Sakkwato (wadda ta haɗa da Kabi da Zamfara). Za a ce shi ne, wane a Hausa. Yadda Narambaɗa ya ambaci Alƙalin Alƙalai na Hausa, haka kowane muƙami ke tafiya. Muƙaman da ke wajen Lardin Sakkwato kamar Kano da Zazzau da Katsina ba a kiran su yadda aka kira a Sakkwato wato “Hausa”.
          Gudammuwar da makaɗa Narambaɗa ya ba mu ita ce:
(i)               Ƙasar Hausa ɗaya ce wadda ke da cibiya Sakkwato.
(ii)             Idan an ce Hausa Sakkwato ake nufi daga cikin garuruwan Hausawa.
(iii)          Ba birnin Sakkwato ne Hausa ba, faɗin gundumar duka shi ne Hausa.
(iv)           Babu wata gunduma da ake ce wa Hausa bayan ita a duniya.
(v)             Sarakunan daular Sakkwato sarakunan ƙasar Hausa ake ce musu, bayan su babu sarakunan da ake kira haka a zamaninsu. Me ya sa haka?
(vi)           Wanda duk ke riƙe da cibiyar Daular Sakkwato a ko’ina aka sauya ta, shi ne mai Hausa. Ƙasarsa ita ce Hausa. Mutanenta su ne mutanen Hausa.
(vii)        Duk zuriyoyin Bahaushe da suka kafa daulolinsu wajen Hausa, Hausawa ne amma tushensu na Hausa a farfajiyar Sakkwato.
Taron Dangi:
Na zaɓi ni yi amfani da Ibrahim Narambaɗa domin fito da irin tsintuwar dami kala da za a iya yi a cikin adabinmu a kan tarihin asalinmu. Babu wai, da za a bi diddigin fitattun tsofafin mawaƙa da yawa, za a samu abin cewa a kan asalin Hausawa da wane ne Bahaushe? Takwarorin Narambaɗa da yawa sun ba da irin gudunmuwar da ya bayar a kaikaice.
Aliyu Ɗandawo:
Yana daga cikin shahararrun mawaƙan sarauta na ƙasar Hausa. Ya yi wa fadar Shuni waƙa da fadar Sakkwato da fadar Isa da fadar Augi da fadar Argungu da fadar Zabarkana ta Nijar (daular Shonghai) a ƙarshe ya ƙare a fadar Yawuri ga gindin bakandamiyarsa ta sarki Abdullahi:
Gindi: Mai Yawuri bangon duniya
          :         Abdullahi sadaukin maza
          :         Allah Ya yi ma ɗaukakar
          :         Da kowa ba shi da ita Hausa dut.

A halin da yake waƙar, mawaƙin daular Yawuri ne. Da masarautar Sakkwato ta sa a kore shi, ya bar ƙasar ya koma daular Kabi. Daga nan aka sa masarautar ta kore shi. Wannan ne dalilin ƙarshen zamansa Yauri. “Hausa” a nan yana nufi Sakkwato da gundumominta. Ai fadar Sakkwato ba ta yi na’am da waƙar ba. Aliyu Ɗandawo fahintarsa a kan ƙasar Hausa ya yi canjaras da Narambaɗa ka ce dai game baki suka yi. Dalilin wannan shi ne, a zamanin da suka rayu da wanda ya gabace ce su, da an ce “Hausa” Sakkwato ake nufi kai tsaye.
Ɗan’anace:
Bari in haɗa ku da makaɗa Dan’anace mutumin Gandi ta Sakkwato da yake yi wa Shagon Mafara waƙa na ‘Yarkahoji ta ƙasar Zamfara. Bayan da ya yi yawo da Shago ko’ina aka rasa mazan da za su fito a yi adashin ƙulli yana cewa:
Jagora       :Na koma Kano da ‘yar gangata
:Ban dai iske kai kaɗai gayya ba
:An ce Hausa na da runjin dambe
:(Bakandamiyar shago)
Da ya zo ambaton Sakkwato cewa ya yi, “an ce Hausa”, duk da ƙasancewarsa Basakkwace yana yi wa Bazamfare waƙa ya ambaci Sakwato da sunan Hausa amma bai ambaci Kano da Katsina da sunan ba domin cewa ya yi:
Jagora       :An ce Katsinan Dikko
:Na da manyan fama.

Da Ɗan’anace na ambaton mazajen da ke iya dambe da Shago ya tuna da wani goga mutumin ƙasar Sakkwato ga abin da makaɗa ya ce:
Jagora:        Sai ko Yari wanda ab bisa Hausa,
Marigayi Bawa Ɗan’anace ya kwakkwahe jawabinsa na cewa, Lardin Sakkwato ne “Hausa” a cikin waƙar Nadelu da yake cewa:
Jagora         :’Yan makaɗa ku na nan arewa,
                   :Masu laƙa ɗan abin kiɗi
                   :’Yan waƙoƙi ƙire-ƙire
                   :Makiɗa ku dai ka hassadanmu.
                   :To mu dai ba mu hassadakku.
                   :Hwaɗa musu ko sun yi hassadanmu
                   :Ga banza an nan
                   :Makiɗa sai dai ku dangana
                   :Wani mai roko ba a....
Yara            :Ba a sake mai da kamata Hausa,
Gindi          :Kai maza suka shakku ko can
                   :Kiro Nadelu kutunkun ɓauna.
Cikin salon bugun gaban wannan ɗan waƙa Ɗan’anace ya nuna ba za a sake samun kamarsa a ƙasar Hausa ba, wato Sakkwato.
Muhammadu Gambo:
Muhammadu Gambo ya ƙara wa Borno dawaki domin ya tabbatar mana da cewa duk ƙasar da ke ƙarƙashin mulki ko sarautar Sakkwato Hausa ake ce mata. Gambo Bagimbane ne mutumin Fagada ta ƙasar Jega riƙon Gwandu amma ya ce:
Jagora       :An ɗau na maraye an miƙa min
:Abin mabaraci an miƙa min,
:Mun ci na Alƙali uzurce
:Mun canye na malam mai karatu
:Balenta na boka ɗan gaton uwa
:Bale mai kuɗɗi bawanmu wannan,
:Mun canye na limami laɓin nan
:Gambo ga ni da raina lahiya Hausa
:Ban taɓa ko ciwon ido ba,
:Komi adadinai na tahowa
:Gambo da sauran gargarenai.
Mutumin ƙasar Jega, yana zaune Jega cikin Gimbanawa, amma bai ce ga shi ƙasar Gimbanawa ba sai ya ce “Hausa”. Gaskiyar Gambo, idan mutumin Zuru zai je Birnin Kabi ko Jega, cewa yake yi, zai je “Hausa”.
Garba Maitandu Shinkafi:
Marigayi Garba Maitandu Shinkafi da kunama ta yi masa halinta ya waƙe ta. Maitandu mutumin Shinkafi ne amma ga irin sunayen wuraren da ya lisafo na maɓoyar kunama:
Jagora        :Maraɗawa na hwaɗin
:Ga tankan ɗaki tare
:Hillani na hwaɗin
:Cikin ɗan rame tare
:Kanawa na hwaɗin
:A gindin dutse take
Yara:         Su ko ‘yan Hausa
:Suka ka ce ga ciyawa take
:Buzu ya ce Galif talif a bakakamba
:Ko’ina dai dakinta ne.
Gindi:                Kunama zan wa kiɗi
:Zama ciwo ag gare ta
:Ta halban na fiya.
Maitandu ya ƙara tabbatar da hasashen Narambaɗa, ya kuma ƙara ba da fatawar cewa, babban birninmu Kano ba garin Hausawa ba ne. Haka kuma, da an ce, Hausa ko ‘yan Hausa a faɗar Maitandu Sakkwatowa ake nufi da gundumominta arba’in da bakwai:
Makaɗan Yaƙin Kabi:
Gangunan Kabawa da suke kaɗawa na bukin cin daular Sakkwato da yaƙi ya isa ya yi wa zantukan waɗannan mawaƙa kwakkwahe. Idan ana bukin cin Fulani da yaƙi a ƙasar Kabi ga saƙon da turayen Kabawa ke cewa:
Jagora:       Kabi ta ci Hausa
Makaɗa:    Da mi tac ci Hausa?
Jama’a:      Da ƙarhi da yaji
Idan Kabawan Argungu na ganin Sakkwato “Hausa”, kuma ba su da fitaccen harshe a lokacin waƙar sai Hausa. Haka kuma, da Hausa suke isar da saƙonsu na gwazangwari (cin nasara). Wannan zai nuna muna Sakkwato ce Hausa, ita ce cibiyar Hausa, Hausawan da ke gewaye da da garin da wajen ƙasarta Hausawa ne, amma tushensu Sakkwato a ko’ina suke. Kasancewarsu wajen riƙon Sakkwato ya ba su damar kafa daulolinsu da sarautunsu kamar yadda Ɗantanoma makaɗin Kabawa ke cewa:
Jagora:       Mu sarkinmu bai biyan wani sarki
:In ba Allah na ba.
:Sama in bi ka kai
:Fito bi Nasara
:In san manya kab bi
Ya rera wannan waƙa ga Sarkin Kabin Argungu da aka ce ya je ya tarbo sarkin Musulmi a Faƙon Sarki. Ashe gaskiyar Narambaɗa da yake zargin Argungu da ta yi dabar dawaki da ta yi wa Sakkwato (Hausa) barazana yake cewa:
Jagora:       Ai wani rincimi
:Da Argungun tak kawo
:Ga dokinmu ya iso
:Su kau nasu ya iso
Yara:           Kuma ga Bubakar cikin mota ya kawo
Jagora:       Yac ce Amadun Muhammadu
Yara:         Allah Ya bar ma kowa babban ɗanai
:Sarkin Gobir na Isa
:Kak ka ji tsoron komi
Gindi:                Gwarzon shamaki na malam toron giwa
:Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Narambaɗa ya ƙara tabbatar da zancen Kabawa cewa Argungu ba ƙarƙashin Hausa take ba. Tana cin gashin kanta, don haka ya kira ta Argungu.
Sakamakon Bincike:
Kalmar Hausa bayan ma’anar ta, ta fasaha, da azanci, da basira, a wajen Bahaushe tana da ma’anoni na daban. Maƙwabtan cibiyar Daular Sakkwato duka, kamar Zamfara da Yauri da Zuru da Kabi da Dandi suna kiran Sakkwato da gundumominta “Hausa”. Mutanen ƙasar Nupe da Kwara idan sun ce, “Hausa” Sakkwato suke nufi. Mutanen ƙasar Ghana da Saliyo da Togo da Benin, da Libya da Sudan, idan suka ce “Hausa”, Sakkwato suke nufi. Fitattun garuruwanmu na tarihi irin Kano da Katsina da Zariya da Gobir idan ana zancensu a rubuce-rubucen magabata na tarihi akan ambace su da sunansu ba “Hausa” ake ambato su da shi ba. Rubuce-rubucen masu jihadi duk wurin da suka ambaci “Hausa” Sakkwato da gundumominta na yanzu zai shafa. Idan za su yi magana kan fitattun biranen da na ambata sukan ambace su da sunayensu da aka san su da su ba sa ce wa “Hausa”. Hasashen Narambaɗa na kiran ƙasar Sakkwato Hausa, ba shege ba ne, da ubansa. Rashin kasancewarsa a rubuce bai cuta wa gaskiyar da ke ciki ba. Ba garin Sakkwato ba ne Hausa duk da kasancewarsa Hausawa suka kafa shi, masarautar dai ce “Hausa”. Ai an ce masarautar ta yi zama Wurno da Cimmaula da Sifawa gabanin a kafa birni a Sakkwato. Tun fil azal masu ƙasar na asali “Hausa” suke kiran ta.
Idan dai mun tabbatar da cewa, ba Nrambaɗa ɗai ke da wannan hasashe ba, takwarorinsa mawaƙa na da shi. Marubuta tarihi masu ziyarce-ziyarce suna da ra’ayin. Daulolin ƙasar Hausa na Hausawa sun yarda da Sakkwato ce Hausa. Masu jihadi da suka tumɓuke daular Hausawa, sun yarda da Sakkwato ce Hausa, labudda a miƙa kai bori ya hau. A ko’ina Bahaushe ya fito a duniya ba ya da wurin da ake kira Hausa bayan Sakkwato bisa ga abubuwan da ɗan bincikenmu ya ƙyallaro. Yanzu mun ji Sakkwato ce Hausa, binciken da ya kyautu a duƙufa shi ne, me ya sa ake kiranta “Hausa”?. Da ɗaliban Hausa da Tarihi sun mayar da akalar bincikensu ga ire-iren waɗannan tussa na adabi, da ‘yan kallo ba su yi muna katsalandan su ɓata muna asali da tarihi bisa karkataccen bincike da aka gina a kan ƙila-wa-ƙala.
Gurbin Sakkwato a Tarihin Bahaushe:
Hasashen Narambaɗa idan aka ɗora shi a gadon feɗe al’ada da adabi da harshen Hausa akwai ɗimin gaskiya ciki sosai. Sakkwato a matsayinta na gari Hausawa suka sare ta shi. Mutanen da ke karkarar su ne Sakkwatawa. Da sunan garin da mutanen ƙasar duk Narambaɗa ya ambace su, a wurare da dama kamar haka:
Jagora         :Ka gama lafiya uban Ajiya
Yara            :In ji Sakkwatawa na Amiru
                   :Ko Amiru munai ma hwata
Gindi          :Gwarzon shamaki na Malam toron Giwa
                   :Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Da Amadu ya je Sakkwato garin Sakkwatawa su na yi masa addu’ar gamawa lafiya. A nan, ana ce wa Sakwkato “Hausa” kasancewarta cibiyar daular Hausa, jama’ar da ke cikin su ne Sakkwatawa kamar yadda jama’ar garin Isa Gobirawa ne amma a ce wa Isa “Hausa” zaman ta a farfajiyar ƙasar Hausa. Narambaɗa ya ambaci garin da sanannen sunansa wurare daban-daban kamar yadda yake cewa:
Jagora:        A runguma uban Yari
Yara  :         Mazan gabas ga Sakkwato
Gindi:          Yai halin mazan jiya
          :         Ɗan sanda mai Kwatarkwashi.
Kasancewar Sakkwato cibiyar Hausa take da sarautun yanki-yanki, irin su: Sarkin Yamma, Sarkin Kudu, Sarkin Gabas, Sarkin Sudan da dai sauransu domin a samu haɗa ƙasa ɗaya bayan jihadi. An ci nasarar jihadi a addinance, a siyasance ƙasa na nan daram da sunanta “Hausa”.
Idan za a yi wa tunanin Narambaɗa adalci, za a ga ba shi ya fara kira ta “Hausa” ba. Ya tarar ana kiranta haka, ba shi ya kashe zomo ba rataya aka ba shi. Babu shakka, batun Narambaɗa zai sa ɗaliban adabi da al’ada da harshen Hausa tunanin cewa:
i)                   Fitattun makaɗan sarautar ƙasar Hausa duk a Sakwkato ake samunsu. Daga cikinsu akwai: Salihu Jankiɗi, Dandodo Alu mai Taushi, Narambaɗa, Aliyu Ɗandawo, Ɗanƙwairo, Kurna, Dantanoma, Ɗankyana, Sa’idu Faru, Alhaji Muhammadu Shata.
ii)                Fitattun makaɗan sana’ar Bahaushe duk a Sakkwato ake samun su, daga cikinsu akwai: Makaɗan noma, makaɗan ƙira (zari), makaɗan farauta, kamar su: Yaro Hore, Bawa Ɗan’anace, Amali Subugu, Kassu Zurmi, Ladan Tuji, Bawa mai Zari, Namata Mai Zari, Garba Ɗanwasa Gumi, Ɗanbuga na Sabon Sara, Bala Lahodu, da dai makamantansu.
iii)             Fitattun mawaƙan sha’awa da holewa na ƙasar Hausa a Sakkwato suka tattara. Daga cikinsu akwai: Ɗanmaraya Jos, Garba Maitandu Shinkafi, Kaka Dawa.
iv)              Fitattun makaɗan miyagun ɗabi’u da suka yi wa ƙasar Hausa shigon kutse irin su; Sata, Caca, Shaye-Shaye, Zina, da dai sauransu, duk a ƙasar Sakkwato suke cure, irinsu; Alhaji Gambo Fagada, Kassu Zurmi, Bala Karhe, Faru, Yahayya, Goloƙo.
v)                Fitattun makaɗan wasannin ƙasar Hausa, dambe da kokuwa Sakkwatawa ne ga abin da aka tabbatar. Daga cikin su akwai: Bawa Ɗan’anace, Alh. Muhammadu Narayau, Sagwalo, Naramabaɗa, da sauransu.
A iya bincikena, fitattun wasannin Bahaushe Narambaɗa ya ambace su a cikin waƙe-waƙensa. Dubi waɗannan ɗiyan waƙa sosai:
Jagora: Bamin Kokawa bai iya ba
          : Shi aka shammata kodayaushe
Yara  : Ga wata kokawwa an wuce da shi
          : Karsanai kakkaɓe mishi ƙasa.
Gindi : Ibrahimu na Guraguri
          : Mai Shinkafi bajinin zagi
          : Mu dai Allah Ya bar muna kaya.
Jagora: An ce mini an yi kokuwa
          : Ban san kan ta ba
          : Da na dac ciki
          : Da na daw wuri
Yara  : Amfana ta na dac cikin ga
          : Ya kada na daw wuri
Gindi: Jikan Mamman Tukur
          : Maza ba mata ba ne
          : Ɗan namijin duniya
          : A gai she ka Guraguri.
Yara: Uban zakara mugun madambaci
Gindi: ya ci maza ya kwan shina shire
          : Gamda’aran Sarkin Tudu Alu,
Dalilina ke nan na ganin Narambaɗa ya san Bahaushe sanin hatsi, ya san al’adun Hausawa gwargwado, ya san ƙasar Hausa sani, ya san siyasa da sarautar Hausa sosai. Don haka, ya cancanci ya ce wani abu cikin tarihin Bahaushe. Daga cikin abubuwan da za su ƙara wa jawaban Narambaɗa amo a kan asalin Bahaushe akwai:
i)                   Ire-iren kare-karen harshe na Hausa na cikin kamfanunan Sakkwato arba’in da bakwai babu wata alƙarya daga cikin alƙaryun ƙasar Hausa da ta tara su. Kaɗan daga cikin akwai: Gobarci, Gimbananci, Arabci, Kabanci, Sakkwatanci, da dai sauransu.
ii)                Ga alama, cuukoson tsofaffin kalmomin Hausa da ake iya tsinta cikin Sakkwato da karin harshen Sakkwatanci ba a samunsu a wasu sassa na ƙasar Hausa. Don haka Sakkwato tafi yawan mawaƙa da babu mai masantawa. A nazarci waɗannan kaɗan a gani:
-        Cissawai      - ratsen hasken rana cikin inwa
-        Kushuli       - liwaɗi
-        Lantago       - busasshen rogo da ake tuwo da shi ko ɗan wake
-        Dibilwa       - wayon wayo
-        Kashereƙe   - namijin bubuƙuwa
-        Accakwama - matattu da raunannun yaƙi da aka kwaso.
-        Sambari       - Adon da mata ke yi a leɓe na katambiri (mai baƙi)
-        Kashindo    - ragowar kayan sata (laɓo)
-        Daƙwalwa   - budurwa
Naɗewa
Yayin da nake fafitikar neman kayan aikin wannan takarda na tattauna da jama’a da yawa. Wasu na ganin, a ce wa Sakkwato “Hausa” ba za a rasa amon siyasa ba. Wasu na ganin, Hausawa kawai ne ke ce mata “Hausa” domin tabbatar da martabarsu. Wa su na ganin masarautun ne suka aminta da haka domin samun karɓuwa da yayyafa wa turnuƙun siyasa ruwa. Ga abin da ya tabbata da Hausawa da Fulani da masu sarauta da talakawa da makaɗansu duk an aminta da amfani da kalmar “Hausa” ga Sakkwato kaɗai koma bayan kowace ƙasa daga cikin ƙasashen Hausa. Da dai an ɗauki adabin Bahaushe da al’adunsa a matsayin makaman gano asalinsa da harshensa da an rarrabe zare da abawan tarihin Bahaushe ba da wata wahala ba. Hausawa kan ce gaskiya ta yi halinta; ana cikin gina ga wutsiya. Wani ɗan jaridar Jahar Zamfara mai suna Ibrahim Aliyu Mayanci ya rubuta tarhin Gwamnan Jihar Zamfara mai ci yanzu, Muhammadu Aliyu Shinkafi sunan littafin: Wane ne Dalhatu? A cikin hirar da ya yi da yayan Gwamna Muhamamdu Namoriki. Da ya tambaye shi tarihin iyayensu, ya fara da mahaifiyarsu sai ya ce: “Ita tsohuwarmu asalinsu mutanen ƙasar Hausa ne daga Raɓa” (2011). Ashe mutanen zamani su suka cancanci su ba da labarin zamanin da ya gabace su. Wannan ita ce hujjata ta gayato Narambaɗa da takwarorinsa su ba mu labarin abin da suka ji daga magabatansu. Na gode Narmabaɗa, Allah Ya gafarta maka.
MANAZARTA
Adamu, M. (1976) “The Spread of Hausa Culture in West Africa” Savanna 5, 3-
13.

Bunza, A.M. (2008) Religion and The Emergence of Hausa Identity: An Enquiry
into the Early Traditional Religion in Hausaland, paper presented at International Conference titled: Hausa Identity: Religion and History, Organized by AHRC and ESRL held at University of East Anglia (Norwich) U.K, Friday 11- Saturday, 12 July 2008.

Bunza, A.M. (2009) Narambaɗa, Wallafar IBRASH, Lagos.

Bunza, A.M. (2010) “Fashin Baƙin Waƙar Mai Yawuri Bangon Duniya ta Aliyu
Ɗandawo”, takardar da aka gabatar a bukin ƙaddamar littafin Mai Yawuri Bangon Duniya da ɗaliban Jami’ar Sakkwato suka yi a Fadar Masarautar Yawuri, a ƙarƙashin Jagoranci mai Martaba Sarkin Yawuri Alhaji Zayyanu Abdullahi, PhD.

Fisher, H.I (1975) “Leo Africanus and the Shonghai Conquers of Hausaland”,
African Historical Studies 11, 86-112.

Fuglast ed, F. (1978) “A Consideration of Hausa History Before the Jihad”,
Journal of African History, 19, 319-339.

Gusau, S.M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin
Baka Na Hausa.

Haour, A and Rossi, B. (ed) (2010) Being and Becoming Hausa, Interdisciplinary
Perspectives, Africna Social Studies Series, Brill, Leiden-Boston.

Hill, R. (1972) Rural Hausa a Village and Setting, Cambridge, Cambridge
University, Press.

Johnston H.A.S. (1967), The Fulani Empire of Sokoto London, London Oxford
University Press.

Last, D.M (1967) The Sokoto Caliphate, Ibadan and London Longman.

Lauge, D. (1987b) The evaluation of the Hausaland story: From Bawo to
Bayajida”, Africa und Ubersee 70, 195-209.

Meck, C.K. (1926) The Northern Tribes of Nigeria, Oxford University Press.



Muhammad A. (1972), “Individual Talent in the Hausa Poetic Tradition: A study
of Aƙilu Aliyu and his Art”, PhD Thesis University of London.

Muhammad, D. (1981), Bakandamiya: “Towards a characteriazation of the poets
master piece in Hausa”. In Oral poetry in Nigeria (eds) By Abologun and others Lagos; Nigeria Magazine.

Muhammadou, K. (2006) “Asalin Hausawa da Rubutun Hausa na Ainihi”,
Takardar da aka gabatar a ƙarƙashin Inwar Kwamitin ƙasa Nijeriya kan Nazarin Haruffan Hausa, Kaduna, Litinin 24 ga Yuli, 2006.

Philips, J.E. (1989), “A History of the Hausa Language”. In Barkinɗo B.M. (ed)
Kano and some of her Neighbours. Kano/Zaria, Ahmadu Bello University Press 37-58.

Schuh, R.G. (1982), “The Hausa Languges and its nearest relatives”, Hausa
Nijeriya 17, 1-24.

Smith, A. (H.F.C) (1970) “Some Consideration to the formation of state in
Hausland, Journal of the Historical Society of Nigeria, 329-346.

Smith, M.G. (1960), Government in Zazzau: A study of governemnt in the Hausa
Chiefdom of Zaria in Northern Nigeria from 1800 to 1950 Oxford, Oxford University Press.

Smith, M.G. (1960) Government in Kano. 1350-1950, Westview Press.

Smith, M.G. (1978) The Affairs of Daura. History and Changes in Hausa States,
1800-1958 Barkeley and Los Angeles: University of California Press.

Sutton, J.E.G. (1979) “Towards a less Orthodox history of Hausaland”, Journal of
the African History 20, 179-201.

Vansina, J. (1985) Oral Tradition as History, James Currey Ltd 73 Botley Road
Oxford OX2 OBJ.

Westley, D. (1986), “The Oral Tadition and the Begining of Hausa Fiction”, PhD
Thesis University of Wisconsin- Madison.

Yaro Sodangi B.A. (1979) “Narambaɗa da Waƙoƙinsa” Kundin digirin BA   Jami’ar Bayero, Kano.

No comments:

Post a Comment